Birnin gayu2

                Birnin gayu🏘️

                   chapter2

Da wadannan ‘tunane tunanen da ‘hanyar shawo kan matsala_bacci ya dauke Inna mai’ Fura’.’
‘Kiran sallar: farko akunnen Deeda,‘ akai jin kiran‘ Sallar a Cikin. Gidan ya bata mamaki, , musamman data-dinga jin k0 ta ina ‘sallah ‘ake, ‘ Masallatai daban-daban. ‘ Ta ‘mike tayi» Alwala tana” jinjina abin, a zuciyarta tayi nata gamida   godiya ga Allah da Ya sata shigo Birni. ‘ ” Tabbas ,datasan‘“ haka; Birni yake data jima dabiyo TabaWa. ‘ Kafin gari ya washe’ har ‘tama Tabawa.  shara,’ ‘gogegoge da‘ wanké-wanke-
Abin’ya yiwa Tabawa dadi sosoi.
Lallai‘zata ci Riba da Deeda, bata da kiwuya Karar Motoci “yasata fit0wa Kofar gida kasancewar bakin Titi ne, ta zauna a Karkashin wata ; Bishiya tana kallon Titi tana shakar iskar sanyin’ safiyar mai albarka, hakan “ba‘ Karamin nishadi da farinciki ya‘jefa a zuciyarta ba Tananan zaune :tana murmushi’ ta soma ganin .’yan Makarantar Boko na wucewa ,sanye‘, Riga da Wando da Hijabi;
ta miqe tabi cikinsu tana tafiya, nan ta
hango (Gate) din Makarantar; -an rubuta
“(NANA AISHA ISLAMIYYA, PRIMARY AND SECONDARY SCHOOL)”. Ta ga an rubuta a jikin bangon K0far Makaranta
Ta jima tana tsaye tana kallonsu suna shiga cikin Makarantar, Wasu sa’ann’inta, wasu kuma sun fita, wasu kuma basu kaitaba maza da’mata. ‘
Kwarai tayi sha‘awar ,itama ace tana daya
daga_ cikinsu, sai dai tasan abu ‘ ne mai matukar wahala.
Sai da‘ taga an rufe (Gate) din Makarantar . sannan ta juya ta _ daWo gida, ta ‘ samu .Tabawa tayi musu abin Karyawa zata fita.
Ta kalleta tace,””Ina kika shiga ne Deeda? Na leka waje ban ganki ba. Ki daina’nisa fa kar ki Bata”.
Deeda tayi murmushi. ‘
“Ba zan‘ Bata Ba Tabawa insha‘Allahu,
‘yan Makaranta da Shaguna na gani  a titi nabi ina kallo”. TabaWan tayi dariya tace, “Deeda kenan,
nanfa Birni ne ba Kauye‘ba, Birnin ma na Kanon ” Dabo, babban; gari  a hankali yau da gobe zaki fahimta‘, in kikace biyewa kallon
Makaranta da Shaguna‘zaki tsayayi kuwa to sai ki dau tsawon ,shekaru kina yi baki‘ gama ba Kizo ki karya ni zan fita, zan
je gidan dana ke aiki sannan inje in yiwa gidan dana daukomusu ke magana mutattauna akan yaushe za,a kaiki ki ‘
. Dam! Taji gabanta ya yanke ya fadi, tabi ‘
Tabawa da kallo yayin DA take fita daga gidan, taji
hankalintaya tashi, ta manta Aikatau tazoyi a Birni‘
shine har’ ta‘fara tunani da Wani burinta na datun
Nan da nan idonta ya ciko da hawaye. taji tana son yin kuka ta juya sukai ido biyu da kakarta ta fada’Cinyarta tana kuka.’
Tace “Kaka banason aiki gidan kowa, Kaka-ina son yin karatu”.  “Kiyi~haquri Deeda dole muyi ‘haquri da halin da muka. tsinci kanmu bake kadai bace
‘ keda wannan‘ buri ba har nima ina da wannan: buri akanki. ‘ .
Karki damu, muyi ta addu’a sanan a hankali zamu cimma nasara; A halin yanzu dole mu fara da . haka zuwa gaba muga abin,da Allah zaiyi .. Nan Kakar tayita kwantar mata da hankali har ta samu’nutsuwa.  Haka suka‘  yini har yamma lis! sannan . TabaWa ta dawo a gajiye, ta samu Inna mai Fura tayi sana‘ar nata, wato Fura, tun da bata barmusu ko abinci ba, ganin garin gero da‘ sugari yasa tayi musu lafiyayyiyar Fura, ta baiwa Deeda kudi ta siyo masu _ nono a bakin’ hanya gun: Fulani-wajenda taga suna kawowa wasu masu Gini  ‘ ‘Nanfa Tabawa-ta ‘zauna ta sha ‘Fura da nonon sosai tana santi, sannan ta tuna” Bata bar musu abinciba tayi hamdala sannan tace, “Kin kyauta Inna, tabbas,don‘kinyi dabara-irin namu na Kauye ba don hakaba da kun zauna‘da yunwa, na mancé, ina sauri na saba inna tafi ba‘ kowa a gida, don haka tunanin Abinci , , “ma bai zo min ba; kun ga-harnima nasamu na sha~ ‘ don ban tsaya cin Abinci a can ba,‘~ ina san in samu inshiga BIRNIN GAYU ne Déeda tajuya ta kalleta. inane kuma BlRNIN GAYU?”
Tabawa ta kalleta cike da mamaki tace Kina nan’cikin Kauyen Kanon nan amman baki san BIRNIN GAYU ba?” ~ Deeda ta daga kai cike da kosawa tace,‘ “ina’zan sani ina Kauyen’Kano‘ ba Birniba?”. “To Kakarki ai ta sani”, Inji Tabawai .
zatayi miki bayani, kuma shi ne Gidan da» Matar da tace- in dauko miki ita tace tana son ‘Yarinya mai kamar shekarunki, suna da masu aiki; ma‘za da ‘mata‘ na wasu qasa ma. haka~ suna da; ., manyan Mata na nan qasar sai dai ‘yan matan naga’ duk kamar ‘ba Hausawa bane, naga har wani ‘unifom) suke sakawa nasu na masu Aiki.‘ ~Sai dai duk da haka tace tana son in nemo mata ‘yar— Budurwa Bahaushiya haka wacce zata dinga; kula da Bangaren dakinta bisa ga‘ wannan, kuma-tana son yar gidan mutunci mai hankali, don hakan .shiyasa na dauko mata ke; Nasan yadda take so haka‘kike har ma kin, ‘wuce tsammaninta, kuma karki ga kamar aikin wahala ne  dan gyaran Dakinta aiba‘ matsala bane, gashi kuma kiyini a cikin A.C ki kwana a A,c  ‘kisa mai kyau, kiCi mai kyau ki sha mai kyau, to meyafi  ’ wannan ‘hutu?
, Ai da tsohuwa take so da tuni‘naje k0 da ina da ‘yar uwa k0 ‘ya k0 jikar da‘ basu yi aure‘ba dana kai mata don Zama da irin wadannan  ai alheri ne
Anyi ta kawo ‘mata yan ‘matan’Birni ma ganin duk rayuwarta a kasa‘shen waje tayi‘ tace wai ita bata son marasa. kunya Wadanda idonsu ya“ bude wadanda za suyi tayi‘mata sata ko wani mugun hali. Kin san sha’anin masu kudi sai su.
Deeda‘dai da Inna mai Fura ido sukasa mata sunaji kuma suna kallonta kamar wata Talabijin
‘Duk wannan kurara gidan da takeyi  bai sa Deeda taji tana sha,awar zuwa gidan ba  sabo da karatunta yafi mata jin dadin da Tabawa take
kirgo,mata Tabawa taci’gaba ’da’cewa, “daganan gidan na  biya na bata lokaci ina jiranta kafin ta fito nayi mata bayanin na- daukoki shi ne ta bani wasu kudade tace-.ayi .miki: siyayyar Sutura ‘mai ‘kyau da abin‘ ” buKatarki ki fito a mutum sosai, bata So kizo mata da wani daudar Kauye
‘Tun daga’ kan Sabulu, Turare, Mai; Takal’ma  zuwa Kaya tace komai Sabo” take so ‘Sannan a nuna miki yadda-zaman Birni yake da yaddah zakiyi mu,amala DA mutane
sannan tace a sakaki a Makarantar koyon Komfuta, (Computer), k0 menene sunansa, wannan abin’ latsawar kamar Talabijin.
‘ .Deeda da kanta ‘ke sunkuye tayi ~
. saurin .dago kanta, tana juya abin a ranta anya duk
duniya akwai abin da take son ,koya kamar (Computer) kuwa? Tayi dariya cikin ‘doki “tace dan Allah tabawa da gaske kike zan shiga ,wannan Makarantar?” ” kwarai”; Tabawa ta tabbatar mata
“Ga‘kudin‘komai ta bani, ‘da mutumin da zai kaiki sanda zaki fara zuwa ya
. _ miki komai, wai so take  ki dinga shigar
da Wasu abubuwanta wanda “qila sirri ne  don BABBAR MACE. ce, mai ilimin. sosai kullum, lissafi take na shigar kudi da fitarsa da’kuma‘saida Kaya harsu Gwala-gwalai da irin gadajen ‘qasar wajennan take saidawa _. Ina jin shi yasa take neman mataimakiya don abin ‘yayi mata-yawa, yayanta
biyu kuma duk suna kasar waje. Naji dai ‘ance
kwanaki akwai ‘yan uwanta masu’ ilimi da sukai ta
cutarta, amma dai jita-jita naji. Tace dai a sakaki ki koya na wata uku, sannan a wata shidan nan kafin ta dawo tana son ganinki tsab
Kinga makudan kudaden data bani, nima ai na samu rabona
Lokacin da Tabawa ta ciro kudin Inna mai- Fura ta bude baki ta kasa magana don tunda take k0 a Mafarki bata taBa ganin irin wadannan makudan kudaden ba masu yaWa haka Ba  basu ankara ba sai ga Inna mai Fura a zube a qasa, suma neta tayi k0 dai firgita tayi da‘ ‘ganin tsabar kudaden a zahiri shiya sata faduwa, oho Allah ne kadai Ya sani. ‘
. Tabawa- dai sai dariya takeyi
Deeda ta taimaka mata suka dagota’
             ↘️↙️↘️↙️↘️↙️
Deeda ‘da Inna mai Fura ba wanda ya kaisu farincikin shigarta (Computer School), duk‘ da bata gane manufar Hajiya na‘ Son taga ta koyi sarrafa (Computer) ba, ita a nata tunanin ta samu hanyar koyon wani ilimin da bata sani ba, wannan ilimin inta samu natane ba. mai‘rabata da shi sai Allah. ‘ Musamman- Hajiyar ta’ hada Deeda da Taba’wa da wata mata suka’shiga’ kasuwa don yiwo mata siyayyar irinkayan da take So taga ta saka. ‘ Kaya ne irin na zamani, wasu‘riga da wando ne, wasu riga da siket, Wasu dogayen ‘ riguna dinkakku wato (Red made), wasu kuma habayas irin na zamanine kala-kala.Haka Takalma zuwa kayan ciki;  su shimi, (vast), bra da‘ makamantansu, sannan Hijabai‘ na Sallah manya. . ‘ Ganin yanayin shigarta yasa matar ta’siya mata (Body shaft) masu kyau‘da tsada a tunaninta haka take son yanayin shigarta a matsayinta na ‘yar Bahaushiya. haka bata son barin jikinta a waje ne ko
kuma dai qila haka nata kalar gayun yake, don
Tabawa dai ta boye musu lalurar Deeda   Cikin kayayyakin Deeda ‘ kuwa harda Kwat”irin na Mata mai hade da Siket.
ita dai sawa kayan ido tayi tana mamakin ta yanda zata fara sakasu a jikinta.
Ta wani Bangaren Kuma tana tunanin wacce
irin’ Mace ce ita da zai sa ta kashewa mai aiki kudi haka, anya kuwa ba wani abu Wanda basu sani ba? , Tana cikin wannan tunanin taji mota ta tsaya kofar wani babban shago. (Beauty Palace) toga an- rubuta Tabawa ne taja hannunta‘ suka bi  matar ciki. ‘ . A nan akai ta tsiya da Deeda don da ‘kyar ta bari suka mata gyaran gashin, ta Bata rai ta dinga zazzaga musu masifa ta qara da cewa in ba zasu dauketa a yadda takeba”to ita zata FASA  don ikon da suke mata ya isheta‘ da qar Tabawa‘ta lallaBata suka dawo 
Tabawa Matar haquri. ‘ ‘ Deeda’ da Kakarta Suka tsare Tabawa da tambayar céwa ta fada musu gaskiya in tasan akwai illa k0 wani abu mara- kyau a tattare da inda zata ‘aikin, gara ta‘fada musu su sani‘ deeda tayi mata rantsuwada cewa in taje ta ‘tarar da abin da bata zata ba to zata bar Gidan sai . dai abin da zai ‘faru. ya faru Tabawa ta washe baki tana dariya. tana. qokarin kwantar musu da hankali da tabbatar musu
da cewa ba wani mummunan aiki k0 wani illa a Gidan, kawai dai su Manja ne masu zama tsab-tsab, bayan shi babu wani abu.
Da irin wannan bayanin Tabawa ta gamsar dasu, yayin da Inna mai Fura taci gaba da-burin kai
Deeda Asibiti.
              ⏬⏬⏬⏬
KWANA-A-TAShi Deeda da Kaka “suka saba da rayuwa; cikin garin Kano, ‘ wani abunda ke yiwa- Deeda dadi shine, yanda ta samu riba biyu lokaci guda, kasancewar Computer Class dinta  qarfe daya ne yasa ta lallaBa  Tabawa ta sakata a Makarantar ’dake unguwarsu,” wato “(NANA AISHA SECONDARY
SCHOOL)”wanda hade yake da. Arabic-da Boko.’ Tayi sa,a sun dauketa aji hudu bayan anyi mata
lnterview.
Tabawa ta dinka mata (Uniform) tare da siya ma ta Takardu, yayin da Kakarta tayi buga bugar hada kudi ta biya mata kudin Makarantar, . ba makarantar gwanmati bané, na kudi ce  amma dai ba zai gagari Talaka ba,
‘Ba‘shin kudi Inna mai Furta’ ta karba Wurin
Tabawa, don haka ta dage da sana’ar Furanta ganin
ya samu karBuwa sosai. ‘
Tabawa‘ ke aikawa Kauye ana siyo musu
madara mai kyau suna Nono da Fura mai dadi, yayin da masu shago ke layin zuwa sari suna sawa a
‘Fridge suna sayarwa.
Sana’ar kam ta ‘ karbu’ ‘ sosai, Allah Ya albarkaci sana’ar, daga Tabawan har Inna mai Fura
‘ ‘ Suna samu sosai a ciki, don haka Inna mai Fura ta
biya Tabawa bashinta, haka ta budewa ‘deeda asusun makaranta da Asibiti.
Deeda kam ba laifi tana fahimtar Karatunta,
Tana jin dadinsa, musamman Makarantar data shiga
tana fahimtar abubuwa da yawa
Wanda bata sani ba, wanda. ya shige mata duhu
bata Bata lokacin tambaya har sai ta  fahimta. Karfe daya suke tashi ta dawo Gida da wuri
tayi Sallah kuma ta wuce (Computer Classes) dinta wani lokaci in sun taso ta kan taimakawa Inna da
aikin Furanta tare da taimakawa da aikace aikacen Gida.
lnna wani lokaci ta kan hanata tace ta  mai da hankali tayi karatu, ita kuma zata dage da: sana’a da neman kudi da mata addu’a domin taga ta cimma burinta.
A duk lokacin da Inna mai Fura ta fadama Deeda haka ta kan fada jikinta tana hawaye tace Kaka Allah Ya barni dake, Allah Yaba ni ikon yi miki abin da kika min, Allah Ya kaimu lokacin da ‘ zaki huta, ni in nema miki in miki gata kamar yandda kika min.
Kaka ba don ke ba ban san ya rayuwata zata kare -ba..Na gode Kaka, Allah Ya biyaki duniya da ‘ lahira”. ‘ ” Inna mai Fura tayi murmushi tace, “Deeda‘ wana keda shi duk duniya idan ba keba?
Allah dai Ya cika min burina akanki, ki samu duk abin da kike so, Allah Ya baki miji na gari mai tausayinki, wanda zai kula dake.
Deeda Allah Ya baki lafiya, Allah Ya cika min burina in ganki Gidan miji kafin in mutu”
Deeda ta fada cinyar Kakarta tana juya kalaman Inna mai Fura don ya daga mata hankali, ita dai
ba tada tsammanin yin aure a rayuwarta don zaiyi wuya
ta samu namijin da zai sota harma ya yarda da
ita a yadda take.
A duk lokacin data kalli fatar‘jikinta taga
yadda ya nannade ya yamutse saita ji hankalinta ya
‘ yi mummunan tashi, ta fashe da kuka, “tausayin kanta
ya kamata, ya yin da ta shiga tunanin wane irin ciwo ne haka? K0 kuma ita haka nata halittar yake?
. Alhamdu lillah! Allah na gode maka daka
Barni da hankalina da kuma rai da lafiya ta, k0da kowa
bai soniba zan’so kaina. Haka Kakata na tare dani,
Allah abin godiya”.
             🔼🔽🔼🔽🔼🔽🔼
WATA UKU KACAL! ‘Deeda tayi ta
” san Computer da yadda ake sarrafata
kasancewar ta samu kwararrun Malamai,
“’“haka nan tana da naci da son sanin abin da bata sani ba, musamman ma dai Computér din da saninsa da koyonsa yana daya daga cikin burinta tuni Deeda da Kakarta suka saba da rayuwar Birni‘da irin yanayin yadda suke rayuwa da‘ mu’amala  jama’ar ’unguwar da dama sun santa sabo’ da suna gannin tana shiga da fita tsakanin Makaranta zuwa shaguna kai
Fura da Nono, wani lokacin haka nan tana da wani irin yanayi na daukan hankali tundagakan irin shigar data kena kaya wato dresing zuwa tafiyarta. maganarta, kalamanta a nutse take yinsa komai nata dabam, sam bata da rawan kai irin na ‘yan mata sa’anninta’ bata da shisshigi, bata shiga harkar matan makaranta  hakan yasa a Ajinsu bata da qawaye  dama makarantar gaba daya sai dai gaisuwar mutunci da maganar da ya zama dole,, bayan shi Deeda bata  mu’amala da wasu bayan  Kakarta da Tabawa,  Deeda wankan taiwada ce tana‘ da tsayi‘ kadan da Kyan Diri, wato Kira mai kyau, Ba wani kyan fuskane da itaba sai dai Allah Ya batajini, tana da saurin shiga rai, bata da magana ko raini, Miskila ce mai ra’ayin tsiya duk yadda abu koya mata dadi baiwuce tayi Murmushiba haka duk’ tsananin abu da Zafinsa bai wuce Idonta ya kada yayi Jaba ko kwallah. Tana da Dauriya da kunya.
             🔻🔺🔻🔺🔻🔺
zAUNE YAKE kan kujera ya harde hannunsa a ‘kirji gami da daura Kafa ‘ dayakan daya.
Ya sawa Sabeer ido, bacci‘ yake yi sosai bashi da k0 alamar bude ido balle yayi shirin fita. “Sabeer Ibrahim ya kira sunansa
– .Cikin nutsuWa_ bai _kula shiba yaci gaba DA  ‘ baccinsa. Ya’mike ya isa dab da gadon ya girgizashi.
“Sabeer ya ‘kamata‘ ka tashi koka manta munada shiga Asibiji yau ne? Cikin muryar Bacci yace, “please
ka barni  inyi Baccina,_Asibitin .sai gobe A Nan ya qara lumewa cikin Bargo Ibrahim’yayi murmuhi yace, ‘Gobenma sai jibi k0?”  Nan yasa hannu ya dauko Wayarsa ya soma lallatsawa, alamar waya zai kira.”Yayata”. Ya fada yana murmushi. Yace, Wannan; Babyn nakifa banajin ‘ akwai abin da zai ‘iyayi a rayuwarsa bayan ‘bacci da zuwa yawon-shaqatawa itama murmushin ta sakar masa tace na Sani qanina sanin halin babyn nawa
yasa na damqashi a hannunka kafin na dawo na san zaka ‘iya shawo kan shi   kuma naga’ – Daddy ma ya’sashi a gaba kayi kokarin tashinsa inya ki ka tuna masa sharadin Daddy zai mike da .wuri”
Ibrahim yaja” ‘dogon numfashi gami da“ ’ fadada murmushinsa yace “(Thanks) Yayata, ban  san ya Zanyi da Matsalolina ba, inda ba kya tare dani kina bani shawarwari da‘dakwarin  guiwa.ba DA bansan ya zamba Allah Ya barni dake’Yaya ta -.-Tayi murmushi (Allah Ya barni‘da kai Kanina. Ina godiya fatan kanina yana cikin koshin Iafiya”. Shiru yayi ‘nadan wani lokaci bai ‘amsa mata _’ ‘ ba, sai saukar numfashinsa data keji danta kasace masa komai,  ya katse shirun da ceWa ina’fatan kina samun nasarar abin da ya kaiki‘ “Eh”.’Ta amSa a taqaice. ‘toKi  kula-da kanki . Bai saurari amsar taba ya katse wayar ya jima yana kallon Wayar-tamkar Mai karantar wani  abu sannan ya mai data .Aljihu ya dubi gadon‘ Sabeer
yayi saurin janye Bargon gami da matsawa dab da Kunnensa yace, “Albishirinka Sabeer, Dady’yace ba kai ba komawa Canada har sai kayi aikin daya kawoka kayi.,.na san dai ,Daddy‘wata uku ya baka, inba hakaba  kuwa, kaci wata daya baka kulla komai,ba . hakan ‘yana nufin zaman naija daram idan ka sallake wata, ukun nan bakai ba komawa ‘ Sannan kuma naji labarin ya. samu’wata a can yar Kauye za a hadaku aure” wat Ya fada da karfi? gami da’ mikewa da sauri. ‘ ‘ . Ya kalli’ Ibrahim cikin zare ido da alamar tsorata yace; “Uncle IB  ka rufa min asiri Ka san na tsani jin k0 maganar Aure koda (Classy girls)ce balle’yar Kauye Ya batafuska. ‘ ‘Ka ‘san yadda na tsani abu mara kyau, mara aji‘ kuwa? Na tsani Matan Kauyen su Daddy  ‘yan’ Matan Kauyen duk munana‘ne, kuma» qazamai,‘jiki  duk Tabo (No way), ba ‘zan iya Auren (Villegers ba) Yana maganar yana ‘yamutsa fuska, ya nufi Bayi don .yin Wanka.

Hmmm Mu tara donjin ci gaba

www.facebook.com/abdullahi.ismail.salanke

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *