BIYAYYAH BAYAN RAI COMPLETE

 BIYAYYAH BAYAN RAI COMPLETE

BIYYAYA BAYAN RAI
A

aa

NAH

UMMU A’SMAU (SA’ADATU)

DEDICATED TO NABEELERT ZANGO(LADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM

Page 1-5

Zaune take a bayan class  dinsu kasan wata bishiya ta kifa kanta saman kafafuwanta banda kuka babu abinda takeyi. Taya ummunsu zata kawo mata wani bakon al’amari lokacin da zuciyarta ta samu abokin rayuwa.

Kafin Abbansu ya rasu shi bai fada mata kudirinshi akanta ba? Me yasa ummansu takeso ta hadata da wani daban? Kodan taga yana da kudi gashi  yanzu ita daya take kula dasu? Idan har tana so nayi aure ai sai ta barni na auri zafina.

Saboda taga Abbanmu ya rasu shiyasa ta hado maganar aurena dashi? Mai yasa takeso dole sai nayi BIYAYYA BAYAN RAI? Gaskiya bazan iya wannan abun da take bukata ba.+

Tabbas nasan ince zan cutu, gashi yana da mata har da yara, shikenen ni bazan yi rayuwata kamar yanda muka dade muna mafarkinta ba? Ni nasan da Abba yanaso ya hadani dashi bazai boye mani ba.

Saboda anga baya raye akeson afito da wata wasiya kuma a danganta ta dashi. Dago kanta tayi tana goge idonta da bayan hannunta wanda sukayi jawur saboda tsabar kuka.

Dole ce tasa tazo makaranta saboda tanaso ta hadu da muradin ranta, sai gashi abin haushi ma baizo ba, ta kira wayar shi akashe. Hakan ne yasa takasa zaman ajin tafito nan ko zata samu saukin zugin da takeji a zuciyarta.

Gashi lecturer dinsu ya shiga amman bata jin zata iya shiga aji ayanda idanuwanta suke, duk wanda ya kalleta yasan tasha kuka. Maida kanta tayi saman kafarta yayin da wata zuciyarta take saka mata kawai ta gudu tabar gidan.

Domin sai tana gidan ummansu zata iya aura mata mutumin da bata so, don a zuciyarta takasa yarda da maganar ummansu na cewar auren da takeso tayi wasiyyar Abbansu ce, kawai tana gani son zuciyar ummansu ne shiyasa tace haka.

Ta rasa dalilin umma nason ta hadata da wannen mutumin, bayan ummansu tana matukar son yaranta, suna rayuwar jin dadi mezai sa yanzu kuma canjin rayuwa ta dalilin wani aure can

Jinjina kai tayi tana fadin komai zai faru bazan taba bari na auri mutumin da zuciyata bata so ba. Babu wata BIYAYYAR DA ZANYI BAYAN RAI. Na gode Allah da  Abba baya raye, nasan idan yana raye ya yanke wannan hukunci bazan iya mashi musu ba.

Nasan idan nabar gidan navwani lokaci ummana zata sauko domin tana da saukin kai.murmushi tayi tana kara goge idonta lokacin data gama gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta yanke mata.

Dafata taji anyi, a firgice ta juyo, ajiyar zuciya ta saki ganin kawarta ce maryam juyawa tayi tana kara goge idonta saboda bata son kowa yasan halin da take ciki. abinda bata sani ba duk maganganun da tayi na karshe duk afili tayisu kuma maryam kawarta taji.

Murmushi tayi tana tun yaushe kikazo? Zama maryam din tayi fuskrta cike da damuwa saboda jin abubuwan da Na’ima take fada, gashi idanuwanta sun kumbura saboda kuka, ko bata fada mata ba tasan tasha kuka sosai.

Kallonta tayi tana fadin Allah yasa abubuwan da naji ba gaskiya bane? Haba Na’ima da hankalinki kike tunanin aikata abinda naji kina fada? To wai ma menene yake damunki? Ashe akwai abinda zaki boye mani? A tunani na babu  abinda zaki boye mani.
Yashe aka sa maki rana bamu sani ba? A cikin kalamanki na fahimci kamar auren dole zaayi maki ke kuma kike son ki bijerema ummanku. Haba Na’ima, da hankalin ki kike fadar guduwa kibar umma da kannanki? Kada kimanta duk wata diya mace mai hankali da tarbiya ta zauna agaban iyayenta shine gatan ta.

Wallahi matukar kika sa kafa kika bar gidanku da niyar guduwa duk inda kikaje kallon karuwa zasuyi maki,  babu wanda zaiyi maki kallon mutuniyar arziki, domin duk Da na halak agaban iyayenshi yake daraja.

Dago kai tayi tana kallon maryam hawaye suna cigaba da zubo mata. Hannu tasa ta goge idonta tana fadin bazaki fahimci abind nakeji bane.kinfi kowa sanin irin son da muke ma junanmu da kabir, taya ummu zata zo mani da maganar Alhajin da suke tare da Abbanmu kafin ya rasu wai Abba yabar  mata wasiyyar ko BAYAN RANSHI na aureshi.

Kawai gani nakeyi umma tanaso na aureshi ne shiyasa tace wasiyar Abba ce, koda ace wasiyarshi taya kike tunanin zan iya yin BIYAYYA BAYAN RAI? Ai tunda Abba ya rasu kawai abarni na auri wanda nakeso.

Tunda har ba shind ya fada mani da bakinshi ba kona auri wani Allah bazai kamani da laifin komai ba. Saboda haka guduwa zanyi, idan umma taga na gudu zata fasa abinda tayi niya daga baya sai na dawo nasan ummana tana saukin kai zata fahimceni

Murmushi maryam tayi tana fadin kina tunanin saboda Abba baya raye shikenen duk doka daya kafa kafin ya rasu zata daina aiki? Wallahi duk yaran da suka san abinda sukeyi  har su mutu bazasu taba watsi da duk wata huduba ta iyayensu ba koda basa raye.

Ai kyan ‘ya’ya su kasance masu yima iyayensu BIYAYYA KO BAYAN RANSU NE. Idan har zaki iya yima mahaifinki BIYAYYA lokacin yana raye banga dalilin da zaisa ki kasa  mashi BIYAYYA BAYAN RANSHI BA.

Nide na fada maki iya gaskiyata, kiyi hankuri da zafin Abbanki, ummunki bazata taba fada maki karya ba, duk abinda zata fada tabbas wasiyyar da Abba ya bar mata ne, ribar mezataci idan tayi ma mamaci karya haba Na’ima kiyi tunani mana.

A tunaninki saboda kudin Alhaji umma takeson ki aureshi, kisan dai umma bata cikin talaucin da zata bayar da ke saboda kudi. Kawai tanaso  kisamu kwanciyar hankali ne, Allah kadai yasan Abinda Abba ya hango maki awajen Alhajin tunda kince Abba yasanshi sosai.

Shi kanshi Abba da yasan mutuwa zaiyi kafin ya rasu zai fada maki kudirinshi, kuma na tabbata lokacin da zai bakwa kusa da sai ya fada maki, tunda ummanki kawai take kusa dashi dole ita zai fada mawa.

Mikewa tayi tana girgiza kai tana fadin nagode da shawararki, amman kisani bazan iya cutar kaina ba, idan nayarda nice zan zauna ba wani ba.

shikenen haka rayuwata zata kare, ita ummu ai auren soyayya sukayi da abba, ke kanki wanda zaki aura zafin kine bana wani ba, shine ni kuma kike kokarin tursasani na auri wani can. Matukar ina raye babu wanda zan aura sai zabi na. Bazan taba amincewa da wata BIYAYAYA BAYAN RAI BA. Wucewa tayi tabarta zaune awajen ta nufi hanyar fita daga makarantar.

ASALIN LABARIN.

Kubiyoni zuwa next page don jin asalin labarin BIYAYYA BAYAN RAI.

Ummun As’mau(sa’adatu

BIYAYYA

BAYAN RAI

NAH

UMMU ASMAU(SA’ADTU)

DEDICATED TO NABILAT ZANGO(LEADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 5-10

Asalin labarin

Dr muhammad imam, haifafen garin zaria ne, a cikin sabon garin zaria, mahaifin sa malan musa bature, malamin makaranta ne, dr muhammad su ukku ne wajen mahaifan su, sadiya ce babba sai Aisha, da muhammad imam, mahaifin su malami wata secondry ne a nen zaria, da mahaifiyar su inna fatima, su ukku ne wajen malan bature, inna fatima ta haifi wasu yaran kamin su Aisha suna komawa, a Aisha ne yaranta suka fara tsayawa, malan bature fari ne sosai shiyasa mutane ke kiran sa musa bature, rayuwar iyalin shi gwanin shawa bai rage su da komai duk da zaman sa malamin makaranta.+

Inna fatima ma tana sana’onin  ta cikin gida irin na mata, cikin rufi asiri suke rayuwa, sun aurad da Aisha da sadiya bayan sun kare secondry.

Mijin sadiya dan zaria ne, a kaduna yake aiki, a kaduna anka kai Amarya. Mijin Aisha dan zaria a nen zarian yake aiki, auta imam dai ne  a gaban inna yana aji hudu a makarantar secondry, haka rayuwata ta cigaba da tafiya.

Dr imam na ajin karshe secondry, Allah yayi mahaifin su malan bature rasuwa, sun shiga cikin tashin hankali rashin mahaifin su, inna fati tayi kuka, da baya suka yi tawakali, bayan rasuwar mahaifin dr imam yasamu Admission a state universty kaduna da taimakon mijin yayarsa sadiya.

Da taimakon mijin sadiya da Aisha dr imam ya hada first dgree din sa a state university kaduna.

Bayan yayi bautar kasa yasamu aikin karantar wa a wata secondry a zaria, lokacin inna fati shekaru sun ja, su sadiya da Aisha kowa nada yaransa, inna fati ta matsa akan dr imam yayi aure tunda yasamu aikin yi, a samaru zaria ya samu yarinyar da yake so mai suna zainab, zainab yarinyar  ce kyakyawa , ta gama secondry school akayi auren ta da dr imam.

Bayan shekara daya lokacin zainab nada ciki, dr imam ya koma yin masters din sa a ABU zaria, bayan wasu watani zainab ta haifi kyakyawa yarinyar ta, mai kama da mahaifin ta, fara sosai tayi gadon farin kakanta malan bature, anyi suna lfy, yarinya tace sunen Na’ima , lokacin dr imam ya kamala master din sa yasamu lecture  a kaduna polytecnic, Na’ima nada shekara daya, Allah ya yiwa inna fati rasuwa.

Bayan wasu shekaru dr imam ya koma nen ABU Zaria,  yayi phd in sociology, bayan ya kare ya dawo nen ABU da lecturing lokacin yaransa biyar, Naima, ummi fatima, sadiya, fahad da kabir, ummu zainab dr ya saka makaranta har tayi dgree din ta a islamic study, tana karantar wa a FGGC zaria

Rayuwa gidan dr imam, abin koyi ce,  yaran dr imam a shekaru goma suke  sauke qu’rani, sun samu kyakyawa tarbiya a wajen ummu zainab yanda suke kiranta, dr kuma abba,  yaran dr imam a therbow duk suke karatun su.

Kawancen Na’ima da maryam ya farane tun a secondry school,  ajin su daya har suka kamala secondry school, sosai zumunci ya kulu tsakanin umman Naima da mahaifiyar maryam.

Bayan kammalawaarsu suka samu admission atare. Cikin saa suka fara  karatunsu basa kula kowa, maryam tana matukar son Na’ima ita ma tana sonta.

Halinsu yazo daya, duk abinda daya zai zartarwa sai da shawarar daya, mutane da yawa suna son su, yanda suke tafiyar da rayuwarsu. Har suka gama aji daya basa gama aji daya basu bama, kowa fuska domin yayi masu magana ba.

Yayin da wani Hafis course mate dinsu ya kamu da soyyyar Na’ima,  duk abokansu sun san irin son da hafis yake ma Na’ima, babban abokinsa Imran shike karfafa mashi guiwa akan yaje ya fada mata sirrin zuciyarsa.

Amman sam yakasa samun kwarin guiwa daga zuciyarsa. Da haka har suka kammala hundred level.

Bayan sun dawo makaranta, Hafis kullun tunanin yake yanda zaima Na’ima magana, watara sun kare lectures, ranar Na’ima dai ce ta shiga makaranta lokacin hafis na tare da Imran, Na’ima tafiya take yi tana jin wani irin rashin zuwan maryam makaranta, ta kira wayarta tace mata bata jin dadi.

Da tunanin zataje ta diba maryam ta isa inda tayi parking motar ta, lokacin da zata shiga univarsity dr ya saya mata karamar honda civic bata dade ta iya, har tana zuwa makaranta da kanta, watarana ita ke zuwa ta dauki maryam ko driven su ya kaita.

Da kyar lmran ya matsawa hafis yaje ya yiwa Na’ima magana, tana cikin kokarin bude mota taji salamar su, tana juyo tana amsa masu, sun gaisa don tana ganin su in zasuyi lectures, imaran yayi karfin halin ce mata abokin na keson magana dake tayi shiru tana sauraren su, Hafis yana

tsaye ya kasa cewa komi,  imran yaga shirun yayi yawa yace Na’ima hafis abokina ya dade yana son ki, ya kasa fada maki.

Na’ima ta dago ta kali imran, tace mashi ta gode, amnan su yi hankuri ita ba soyyaya ya kawo ta ba karatu tazo yi, ta shiga mota ta wuce, hafis jikin shi yayi sanyi, lmaran ke karfafa mishi da yayi hankuri watara zata so shi.

Na’ima kai tsaye gidan su maryam ta wuce da tunanin me hafis din ke nufi, ta isa gidan su maryam dake pz, tayi hon maigadi ya bude ta shiga tayi parking, a kicin tasamu mamar maryam sun gaisa tana tambayar ya jikin maryam, tace da sauki ta shiga tana cikin, nasan zaki zo yau mutuniyar ki bataje makaranta ba,  tayi dariya ta wuce dakin maryam din kwance ta same ta, Na’ima tace na zaci is serious,   maryam tayi dariya tace nadai ji sauki da fever na kwana jiya ban jin dadi, Na’ima tace Allah ya baki lfy ai zaki je makaranta goben ko, maryam tace zanje   naji sauki, Na’ima tace bari inje gida ban ma fada ma umman mu zan zo, hankali ya tashi na zaci sosai ne, maryam ta rako ta har wajen mota suka yi sallama.

Na’ima ta isa gida kusa ukku da rabi na yamma, ta yi parking ta shiga cikin gidan da sallama, ta samu umman su falo kannanta na shirin zuwa islamiya don ka’idan dr ne ko Na’ima dake university in batada evening lectures tana bin kannen ta zuwa islamiya, umma tace yau kin dade nasan biyu kuke gama lectures, tace maryam ce batazo makaranta bata da lfy naje na dibata, ummu tace da saukin jiki nata, zan kira hajiya saudatu mahaifiyar maryam, Na’ima tace da sauki gobe ma tace zata shiga makaranta, ummu tace kiyi sauri ku shirye zuwa islamiya hudu ya kusa.

Bayan sun dawo islamiya duk yaran gidan na tare da dr falo suna kallon news , ka’idan dr ne baa kallon firm ko series gidan sa,   news ne ko history, islam channes sune yaransa ke kallo, da an kare news sun kare homework zasu je  kowa ya kwanta, Na’ima in tana exams zata wuce dakin su tayi karatu.

Da safe  maryam da Na’ima sun hadu school, sam Na’imar ta mance maganar Hafis, sai da suka shiga lecture, bayan sun fito take ba maryam labari, maryam tace to ke me kice masu , tayi dariya tace mi zan ce masu bayan ba soyayya ce gaba na ba.

K

kullun hafis na bibiyan Na’ima tun basa kula shi har suka fara gaisawa, sannu sannu soyyaya mai karfi ya shiga tsakanin su.

Tushen labarin

Muje zuwa☘

BIYAYYA BAYAN RAI 15-20

NAH

UMMU AS’MAU(SA’ADATU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LEADY), NAGODE TAWAN

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 15-20

Wannen pagen naku ne Diyar katibi, maman waleed, Allah ya bar zumunci.

Bayan MD ya koma gida

tunanin Na’ima ya tasoshi gaba, adaren sam kasa bacci yayi daya rufe idanuwansa ita yake gani.

Abu kamar wasa yana kwance yaji kiran sallar farko, da kyar yatashi yayo alwala ya fara sallah. Bayan yadawo daga masallaci yadan kwanta nan bacci ya daukeshi, acikin baccin ma mafarkinta yayi.

Zaune Hafiz da Na’ima suke asaman wasu kujeru bayan fitowarsu daga lectures. Hafiz yace dear kinga yanzu muna aji 3, yakamata ace zuwa yanzu agidanku asan da zamana, koba komai idana muka gama karatu bazamu sha wahalar sanar da Iyayenki maganar auren ku ba.

Na’ima kinsani babu wata mace da nakeso sama dake, duk wata rayuwata ta nan gaba na shiryata ne dake, idan har na rasaki ban san wane hali zan shiga ba. Dan Allah kada kibari wani yazo ya kwace mani ke.

Murmushi tayi tana fadin kaima kasan agidanmu ba’a barina kula kowa, taya kake tunanin wani zai zo ya kwace maka ni. Abbanmu baya zaba ma,mace abinda yakeso.

Shi mutum ne mai bama kowa ‘yancinsa, hatta da biro idan zai saya maka sai wanda kakeso, sam baya tauye mana ra’ayinmu. Kada kayi tunanin Abba zai zaba mani wanda zanyi rayuwa dashi. Kawai ka kara bani lokaci mu shiga final year nasan Abba zai amshi maganata tunda yaga munzo karshe, nasan zai yarda da maganar mu, Hafis yace shikenen tunda kince haka, amman in wani lokacin sai nayi ta mafalkin wani yazo da jirgin sama ya dauke man ke. Na’ima tayi dariya tace haba, mafalki ai baya zama gaskiya, a haka Maryam ta taradda su, tana dariya tace romio an juliet, Na’ima ta tashi tsaye

tana fadin aike nake jira mu wuce gida, sukayi sallama da Hafis suka wuce.

Bayan wasu watanni shaquwa ce mai karfi ta shiga tsakain Dr da MD har ma da family both side, ko aure ake a family Dr zai gayyaci MD haka MD zai gayyaci Dr, suna waya sosai zuwa lokacin MD ya kare master programme dinsa dama 1yr ne,Dr kan shi yayi mamakin basira MD don result din shi yayi kyau sosai, haka son Na’ima ya yi yawa a zuciyar MD, basan ya zai tunkare ta ba, ko ya zaima Dr maganar, so dayawa in yaje gidan bai cika samun ta ba, wani zubin ko tananen da sun gaisa zata wuce ta barsa da kaninta, yayi sabo da su fahad sosai, duk zuwan da yayi gidan da kallar tsaraban da zai masu, Na’ima haka nen haushin MD take ji, sai tace ya cika shishigi shi ba danuwansu amman komai na family da shi ake, ko yaushe ta gansa sai taji gabanta na faduwa.

A gefe daya Dr kullun ayyana yake ina ma MD zai neme auren yar sa, har ga Allah MD ya kwanta masa, ya binciki family sa sosai, mahaifinsa dattijo ne, mutunin kirki,  sai dai yasan bazai yuyu shi ya fara yi masa maganar yar sa ba, haka rayuwa ta cigaba da tafiya, zumuncin su yayi karfi sosai, MD son Na’ima na ta cin sa yakasa neman mafita, rashin kunyar da Hindatu keyi masa sai abinda ya ci gaba, daman shi ba mutunin hayaniya bane. Abinci gidan ko yaushe yar aiki keyi, yaran komai mai aiki ke masu, har gefen mai gidan yar aikinta ke gyarawa, bata lokacin komai sai biki da yawon kawaye, mai gidan in ta je makwancin sa, tana bukata da shi, ko kudi ko tace tazo a bata hakkinta,  haka zaman yake duk hindatu tayi masa abin arziki, to akwai abinda take so a wajen sa har ya saba da hakan, yan uwansa ba wani dogon hulda tsakanin ta dasu.

Bayan shekara daya lokacin su Na’ima sun shiga level four, soyyarsu da Hafis yayi nisa, har daya na gani baya iya rayuwa batare da yan ba. Haka son Na’ima na Azalzalan MD ya kasa fada mata. Akwai watarana ya shiga zaria da yammah, kai tsaye gidan Dr ya wuce, yayi parking wajen gidan ya shiga cikin harabar gidan yana shiga da Na’ima ya far haduwa tana wajen kan kujeren dake harabar gidan tana rubuta project dinta, tunda ta dago taga mai sallama yana shigowa ta hade fuska, ciki ciki ta gayar da shi, ya amsa cikin sakin fuska, gabansa na faduwa don bai zaci da ita zai fara haduwa ba, kai tsaye falon gidan ya shiga da sallama, su ummi kanen Na’ima na zaune, da fara’a suka tarbe sa, ummu zainab tace muhammadu ne sannu da zuwa ya duka har kasa ya gaida ta, sun tafa fira yace Dr fa tace yana evening lecture yaje makaranta, amman nasan bayana nesa zai dawo, yace daman na shigo gari ne nace bari inzo mu gaisa, ya tashi yana cewa a gaida shi zan wuce, ya kira fahad ya basa kudi ya bawa umman su, ya na fitowa sukayi karo da Na’ima zata shiga falon, da sauri taja baya, shiko ya tsura mata ido, ya yi seconds yana kallonta, gabansa na faduwa, a fito falon a hanakali ta wuce ciki.

Fahad ne ya dawo da kudi yace umma tace bata karfa mata, MD yace ka maida mata, kace albarka ta nake nema matsayinta na uwa, yace fahad level nawa yayar ka take fahad yace final year take, su zasu kare wannen shekara, MD yace to in Dr yazo ka gaida shi zan wuce. Bayan ya bar kofar gidan ya fara tunanin mafita kamin garin kallon ruwa, yarasata, babban abokin shine ya fado masa a rai, Shehu hassan zai ne me shawaran shi.

Abinda MD yaje yi a zarian bai yi haka ya dauki hanyar kaduna cikin mintuna arba’in da biyar ya isa kaduna kai tsaye, gidan Shehu hassan ya wuce, friend dinsa ne tun a secondry school shi ma shehun dan zaria ne, kaduna yake aiki banker ne. In akwai wanda yasan halin MD bayan shehu yake, so dayawa wayanda suka san su, suna mamakin abotan su, don Shehu ba raini yana da zafi sosai in an tabo sa tun a makaranta, so dayawa shi ke shige MD fada lokacin suna secondry school, ko ya yake neman MD baya zuwa gidansa, ya tsanin halayen Hindatu, yana mamakin wane irin rayuwa ke ga MD da bazai daukar mata mataki ba, Hindatun haushe Shehu take ji, tana ce masa munafiki, basa shiri ko kadan, matar Shehu bata hulda da Hindatu.

Ya isa cabalar road unguwar gidan shehu, yayi hon maigadin ya leko, ganin motar MD jiki na rawa ya fito don MD ba dai Alhairi ba, ya rusuna yana kwasar gaisuwa, MD yace maigidan na nen ko, kamin mai gadin ya yi magana. Suka ji hon waje alamun mai gidan ya dawo, bayan shehun ya shigo ciki da fari’a ya tarbi MD yana cewa ya baka shiga ciki ba, MD yace isowa na kenen ka dawo, yace to bismillah, suka kara sa cikin compound din gidan, MD yace mu tsaya a waje maganar da nada muhimmanci, su ka karasa wajen round hot din dake cikin compound din suka zauna, MD yayi shehu bayanin halin da yake ciki na son Na’ima amman bai san yanda zai tunkari Dr da maganar ba,  Shehu yayi hamdala yana cewa wallahi naji dadi abokina kuma nasan Dr zaiyi farincikin haka, don Shehu ya san Dr saboda M,   kuma atlist ko bazaka iya rabuwa da Hindatu ba, don BIYAYYA BAYAN RAN Alhajinku, zaka ji saukin matsalolin ta, Shehu yace mafita daya ce muyi magana da Dr kamin mu yi ma yarinyar magana, in zanje  zaria goben, don ko yau ba dan dare yayi da yau zan je. Amman gobe da yarda Allah zanje nayi masa bayanin abinda kenen, kuma ka kwantar da hankalinka har na hango Na’imar ta zama taka MD yayi dariya, Shehu yace naso ganin yarinyar ta cira tutu tun muna secondry ban tafa jin kace kana son mace sai kanta, kiran sallar da aka fara ne, yasa mikewa don zuwa masallaci.

Bayan sunyi sallah sun dawo, suka shiga falon gidan,  Shehu ya wuce ciki yana ce ma matar Samira tazo ga MD, ta fito suka gaisa da tambayar su Nuwaira da maman su, yace duk lafiya suke, bayan sun kare fira MD ya wuce gida da alkawalin Shehu zai je wajen Dr goben.

Muje zuwaBIYAYYA BAYAN RAI 20-25

NAH

UMMUN ASMA’U(SA’ADATU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LADY)

BISMILAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 20-25

Sosai Dr yayi farin ciki akan maganar da abokin MD yazo mashi da ita, dama abinda ya dade yana jiran ji daga garesa kenan, saboda bayaso shi ya fara masa magana kada yaga kamar yana tallar diyarsa ne.

Gyran murya yayi tare da kallon abokin Md yace ai wannan ba wani abu bane, dama yana sonta shine yakasa fada mani? Ai matsayinmu ya wuce haka, na daukesa tamkar dan uwana.

+

Babu abinda zance sai Allah yasa muna raye, kuma nayi matukar farin ciki da wannan magana, Alhamdulillahi Na’ima bata da wani wanda takeso domin tasan bana barinsu kulawa kowa sai sun gama karatu.

Kuma ni sheda ne domin tunda Na’ima tashiga makarantar nan ban taba ganin kowa yazo wajenta da sunan fira ba. Tunda yanzu suna a final year na bashi dama ya nemi so awajenta, kuma nasan Na’ima bazata kishi ba.

Allah ya zaba abinda yafi alkhairi. Sosai abokin MD yaji dadin abinda Dr, yace. Godiya yayi mashi sukayi sallama yatafi. Cike da farin ciki Dr yashiga dakin Umma dan ya fada mata labari mai dadi.

Yana shiga ya ssmeta har tayi bacci. Murmushi yayi yana fadin sarkin bacci, bara na kyaleki zuwa gobe mayi maganar. Bayan ya gama shirin bacci sako yashigo mashi ta wayarsa. Yana dubawa ya dafe kai.

Tsaki yayi yana fadin bana son irin haka, tun tuni sun san da tafiya bazasu fadama mutum da wuri ba, sai yanzu karfe 9 sannan zasu fada kuma ace anaso gobe atafi da safe. Wayarsa ce tayi kara.

Yana dagawa wanda yakira yace Dr kayi hakuri kaga sako late ko? Wallahi muma daga sama muka samu takardar kuma akace dole kaine zakaje shiyasa na turo maka yanzu. Dr yace ai ina nan na fara jin haushi kun aiko mani da sako very late.

Daga dayan bangaren yace kayi hakuri kila suma ahaka suka samu sakon. Dr yace shikenan babu damuwa, Allah yabkaimu goben. Yace amin. Yanzu zakaji alert sai ka dawo Allah ya kiyaye. Dr yace amin.

Tashi Dr yayi ya dauko jakarsa ya zuba kayansa kala biyu domin kwana biyu zeyi agarin Abuja.

Washe gari bayan yadawo sallar asuba yake fadama Umma maganar tafiyarsa. Cike da damuwa tace gaskiya wadannan mutanan sun cika shiga hakkin mutum, duka yaushe kadawo daga tafiya ai sai su tura wani ko.

Murmushi Dr yayi tare da kamo hannunta ganin yanda ta bata ranta. Zama yayi kusa da ita yana fadin kada ki damu, kinsan idan akace mutum yana rike gaskiya akan aikinsa kowa yanaso ya yaga ya hada alaka dashi.

Sanin kanki ne mutane da yawa suna son nashige masu gaba akan duk wani aiki daya taso. Kawai kitayami da addu’a wata rana dana aje aiki shikenan zan zauna tare daku. Murmushi tayi tana fadin Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya. Yace amin.

Bayan yagama shiryawa yatara yaransa sukayi addu’a kamar yanda ya saba idan zeyi tafiya, kallon Na’ima yayi yana fadin Na’ima ina fatan kin kusa kammala project dinki? Na’ima tace E Abba.

Jinjina kai yayi yana fadin da kyau, Allah ya bada sa’a, ki kara maida hankali banaso ki fadi ajarawarki ta karshe idan ba haka ba sai kin sake maimaita shekara daya. Kinga kece babba duk yanda kikayi haka nakasanki zasuyi.

Allah yayi maku albarka, ku kula da gida kwana biyu kawai zanyi insha Allah, banaso na samu labarin kunyi wani abu na rashin ji. Kiyi hakuri da kannanki. Na’ima tace insha Allah Abba.

Kudi ya ciro ya bama kowa. Godiya sukayi mashi suka gita rakashi, bayan sun dawo Dr ya kalli Umma yace idan nadawo akwai labari mai dadi. Murmushi tayi tace Allah ya maido mani da kai lafiya. Yace amin.

Haka yashiga mota tanadaga masa hannu shima yana dago mata har sai da ya fice sannan ta juya. Tana juyawa taga su Na’ima suna mata dariya. Hararsu tayi tana fadin sarakan sa ido me akayi? Na’ima tace Umma gani mukayi kamar bakiso Abba yatafi.

Murmushi tayi tace ai dole na damu, kema wata rana zaki fada mani irin haka. Dariya Na’ima tayi tashige ciki tana fadin zan baki labari mai dadi da Abba ya dawo.

MD kowa farin ciki baya misaltuwa, da ya tuna yanda shehu hassan ya fada masa sukayi da Dr, sosai kwananen yake cikin farin ciki.

Dr ya kusa shiga kaduna ummu zainab ta kira shi, tana tambayar sa ya hanya yace ya kusa shiga kaduna, tayi  masa Addu’an sauka lafiya sukayi sallama

Kadan Dr ya rage ya shiga kaduna, wata mota da ke bayansa driven yazo yayi overtaking motar Dr sai motar ta kwace wa driven ya tura motar Dr a jeji,  motar ta kubcewa Dr ta fara juyawa, sai da tayi juyi sosai ta daki wani katon ice ta tsaya, mutanen da ke wucewa ne suka tsaya  domin su taimaka Dr, da hanzari masu motar farko da sukayi tsaya suka nufi motar Dr, koda suka isa da kyar suka fito da shi jikin shi duk rauni ne da jini, daya daga cikin su yace su diba motar ko zasu samu information din shi, cen a karkashin sit, suka ga wayarsa da id cards din sa,  sun diba last call suka num ummu zainab, suka kira num ta, tana kitchen wayar ta dake gefenta ta fara kara a hankali ta dauki wayar gabanta na faduwa, daman tun safe take jin faduwar gaba, ganin num Dr sai ta dauka tana cewa ka shiga kadune, cen daya bangaren taji ance bashi ba, ummu zainab bakin ta na rawa tace waye, mutumin ya fadi mata, ya samu hadari ne a hanya, zasu wuce da shi asibitin shika, su hadu cen.

Ummu zainab tace innalilahi wa inna ilaihin rajiun, cikin rawar jiki ta wuce daki ta dauki hijab da keys din motar ta, ta fito falo lokacin hankalin ta yakai kan su fahad dake kallon tv, duk suka tashi suna tambayar ta lafiya, gudun kar suce zasu bita, tace masu a wajen aiki a ka kira ta yanzun zata dawo, lokacin Na’ima ta na makaranta, ta wuce cikin sauri tana ce  wa maigadin ya bude mata get, cikin mintuna ashirin ta isa shika teaching hospital, tun a  hanya take kiran num Dr mutanen da suka taimaka masa suke ce mata sun kusa, ta isa da mintuna suka isa, suna parking mota, ummu zainab ta isa, tana ganin halin da Dr yake ciki ta fasa kuka,  nurses ne suka zo da sauri da gadon daukar mara lafiya  aka dora Dr jini duk ya bata masa jiki kai tsaye emergency suka wuce da shi ummu zainab na kuka tana bin su.

A baki shiga emergency Dr ya bude idanunsa cikin zafin ciwo,  yace nurse su tsaya zaya yi magana da Ummu zainab, ta duka dai fuskan shi,  cikin tsananin juriya yake magana yace zainab kiyi hankuri da rayuwa duk yanda tazo maki, ki kula da yaranki, MD ya aiko man yana son ya neme auren Na’ima, zainab ko bayan raina ku aura ma sa Na’ima Muhammadu nasan zai rika ta da amana, ki fadima yan uwana su yaya sadiya su yafe min, nurse din da sauri suka wuce dashi ciki, don ceton rayuwar sa, wayyannen mutane da suka taimaka Dr su ne ke ta Ummu zaibab hankuri da ta daina kuka, Allah zai bashi lafiya su zasu wuce, ta yi masu godiya, ta kira sadiya da Aisha yayun Dr ta fada masu, ta kira yannen ta, ta fada masu, cikin tsananin tashin hankali ta kura ma kofar emegency ido tana Addu’a Allah ya tashi mijinta, likitoci ke ta shiga suna fita, bayan wani lokaci Aisha ta iso, Ummu zainab na gani ta, ta fada kanta tana kuka, Aisha ma kuka takeyi.

Babban likitan ne ya fito yana share zufa, da sauri suka nufe sa, suna tambayar Dr ya dago ya kalle su, ya jijiga kansa, yace sai kuyi  hankuri, Allah yayi masa cikawa, ya samu internal injury ne a kai, cikin karaji ummu zainab ta kurma ihu, ta fadi sume, Aisha ma tafasa kuka mai cin rai, a haka babbar yayar Dr sadiya da mijinta suka iso, da sauri a dauki ummu zuwa emergency, da taimakon likitocin ta bude idanuta sai take ganin kamar mafalki ne, ganinsu sadiya ya tabbatar mata ba mafalki take  yi ba, mijin sadiya ya cema likitan zasu iya wucewa da Ummu zainab gida , likitan yace eh zasu iya shock ne ta samu.

Matan ne suka wuce da ita gida, mijin Aisha da sadiya suka tsaya domin wucewa da gawar Dr gida, bayan sun karfi gawan ne suka wuce,  da kiran  dukkan dangi da abukan arziki suna fadi ma mutane, don hallarta jana’izar Dr.BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸☘☘🌸🌸

NAH

🌸

UMMUN ASMA’U (SA’ADTU)

DEDICATED TO NABILAT ZANGO(LADY)

Bismilahi rahamanir rahim.

Page 30-35

Na’ima kuwa suna fitowa exams last paper su, project dai ya rage masu, take cewa maryam gaban ta take jin yana faduwa bata jindadin jikin ta su wuce gida, ta aje maryam ta dauki hanyar gidan su da ke zaria city, daman tun rasuwar mahaifiyarsu Dr bai bar ainihin gidan su ba, da baya ya sayi filin da ke kusa da gidan aka hade aka gyara gidan.

Tana shiga layin nasu ta hango mutane sun fara taru kofar gidan, cikin sauri ta isa kofar gidan, waje tayi parking, ta wuce ciki da sauri ganin mazan gwaggonin ta da da dangi mahaifiyar ta tasan ba lafiya, ta karsa cikin gidan, tana kiran umman su, jiyo kukan umman da kanninta yasa ta yi tsaye, autan umman ne ya zo ya rike ta, yana cewa yaya abban mu yayi hadari ya rasu, Na’ima ta fasa kara mai karfi ta fadi kasa, yaya sadiya sister Dr ce tazo ta ja ta zuwa cikin dakin mahaifiyarta, umma zainab naganin an jayo Na’ima ta kara fasa kuka, duk wanda ke gidan ya tausaya masu, kuka sukai mai cin rai, Umma zainab ta jayo wayar ta, ta shiga neman layin MD.+

Yana tsakiyar aiki a office call din Umma zainab na shigowa, hakanen yaji gabansa ya fadi, da sanyi jiki ya dauki call din, yana cewa Assalamu Alaikum sai tace masa muhammadu yau mun rasa Dr, babu Dr, da karfi MD ya tashi, cikin tashin hankali yake cewa hello ta kashe wayar, da sauri ya dauki keys dinsa ya fito, masinjan na oga lafiya bai saurara masa ya wuce, ya kira abokin sa shehu hassan ya fadi masa, shehun yace su hadu su wuce zari’a.

Allah ne kurum ya kai su lafiya, saboda gudun da MD ke zubawa, shehun kan sa cikin tashin hankali yake yana tuna zuwan sa wajen Dr.

Koda suka isa ana shirin kai Dr makwancinsa, fahad naganin MD da gudu yazo ya fada masa yana kuka, MD kuka ya fashe da shi, mutanen da suka san alakar MD da Dr sun tausaya masu, shehu ya kira yan gidan su MD da nasu gidan duk ya fada masu, jamma’a da dama ne suka raka Dr makwancin sa, mutane da yawa suna fadin alhairin sa.

Bayan an dawo ne mazan suka shiga cikin gidan don yi masu gaisuwa, MD da yan gidan su da suka zo da yan gidansu shehun suka shiga, sun shiga wajen ummu zainab, MD kasa magana yayi sai kuka, Ummu zainab naganin sa tasa kuka, mutane ke ta basu hankuri cewa yanzu addu’ar su yake nema.

Haka aka cigaba da zaman makoki har akayi sadakan ukku, lokacin kowa yaga iyalain Dr zai tausaya masu, har Na’ima da mahaifiyar ta, duk sun rame, maryam gidan su Na’ima tavdawo tana bata baki, ita ma mutuwar ta shigeta.

MD hutu ya dauka office ya dawo zaria, gidansa dake GRA, ba yanda baiyi da Hindatu tazo taki, cikin yayi hidama sosai an aje abinci har abin sha.

Da akayi sadakan ukku ne, ranar da zai wuce ya shiga don yima ummu zainab sallama a falo ya taradda su da yan uwan Dr, Na’ima da maryam na gefe zaune, yayi masu sallama zai wuce, har ya mike Ummu zainab tace masa in an kwana biyu akwai maganar da takeso yazo zasuyi, ya insha Allahu in an kwana biyu za dawo ya masu sallama ya wuce.

Na’ima ta jinjina meyasa umman su keson ganin Mutumin nen ko yana bin mahaifin su kudin bata kawo komi a ranta ba, ummu zainab, cikin damuwa take ga rashin Dr ga wasiyar da ya bar mata, abinda ke damun ta, zuwan Hafis da mahaifan sa gaisuwa da sunen mane min Na’ima,

ina zata fara kuma ta fahimci Na’imar na son sa, ta yanke shawara zata tara dangin Dr ta fada masu abinda kenen.

Washe gari, Umma zainab tace ma sadiya da Aisha yayu Dr akwai maganar da takeson suyi, sadiya tace yana da kyau in abinda ya shafi Dr ne su kira kanin mahaifiyarsu da kanin mahaifin su, tun da duk suna raye. Bayan duk sun halara ne ummu zainab tayi masu bayanin wasiya da Dr ya bar mata, kamin Allah yayi mashi cikawa, sunyi shiru na wani lokacin kamin kawu Abdullahi yayi gyaran murya yace muhammadu bazai zafa Na’ima abinda yasa zata cutu ba, saboda haka ya zama dole a cika masa kudirin sa, kuma yasan Na’imar bazata ki, abinda mahaifin ta ya zafa mata ba, yasan zatayi masa BIYAYYA BAYAN RAI, yace ma su sadiya ko akwai mai magana sukace suma suna bayan maganar danuwan su, ya juya wajen dayan kawun nasu shima yace hakan zaa yi, sun yake shawaran su sadiyan su kira Na’iman suyi mata bayanin abinda kenen, amman sunce zasu barsa har ayi sadakan arba’in dai hankalin Na’ima ya kara dawowa jikin ta.

MD kuwa bayan ya bar zaria yake tunanin ganin da Ummu zainab keson masa, bayan ya isa zaria ya kira shehu hassan yana masa bayani, shehun yace ya kwantar da hankalin sa, zai yuyu Dr ya fada mata ne. A haka sukayi sallama, kwanen biyu MD cikin tunani yayi su Allah yake kwana biyun yayi, bayan kwana biyu MD ya shirya zuwa Zarian, sayayya sosai yayi, tun kan abinci har sabulun wanka, ya isa gidan ana kiran laa’asr ya fitar da kayan ya bawa maigadin ya wuce masallaci, bayan ya dawo ne, ya shiga cikin gidan sun gaisa da ummun tare da kara yima ta gaisuwa, tayi masa godiyar kayan da ya kawo, tana cewa hidimar yayi yawa, yace ba komai albarka ta yake nema. Sunyi shiru na wani lokacin kamin ta kirasa muhammadu ya dago kansa tace Kamin Allah yayi wa Dr rasuwa, ya fadamin ka aiko masa kana son Na’ima da aure, tace ya bar wasiyyar ko bayan ransa a aura ma Na’ima, nayi ma dangin mahaifin ta bayani, sun aminta da wasiyyar sa, sunce haka zaayi, sai dai zasu ba da lokaci kamin suyi mata bayanin abin da kenen, ka bada lokaci kadan ka turo magabatanka don a tsayar da rana, tun da ta kammala karatun ta. MD da ji abin kamar a mafarki, yayi hamdala a ransa, cike da girmamawa yace umma kina ganin ba matsala gefen Na’iman, Umma tayi jim na wani lokacin kan tace bana tunanin haka saboda bana tunanin Na’ima ta tsallake ummunin Dr, yayi mata godiya sosai, sunyi sallama da Alkawalin in anyi sadakan Arba’in zai turo magabatan sa.

Bayan wasu kwanaki akayi sadakar arba’in Dr anyi addu’oin sosai, bayan ankare sadiya da Aisha suka kira Na’ima a dakin Dr, sun mata nasiha sosai kamin su fada mata wasiyyar da mahaifinta ya bari, Na’ima cikin tsananin tashin hankali ta mike tsaya, tace wallahi bazan yi ba, Abban mu bazai ce haka ba, ina wanda nake so ta fashe da kuka mai tsanani, Ummu zainab dake falo tana kai tana komowa tasan zaa rina, don ta lura ko kadan Na’ima bata son ko maganar MD, kamar su ummi da suka mayar da shi dan uwa.

Sadiya ta jawo Na’ima cikin sigar lalashi tace kiyi hankuri Na’ima Dr bazai tafa baki abinda yasan zai cutar dake, Na’ima kuwa sai kuka takeyi tana cewa bazata yi ba, karya ake ma mahaifin ta, Ummu zainab ta shigo cikin dakin ta zauna tace ma Na’ima tabbas abinda gwagwanin ki suka fada haka yake in mahaifinki ya barma wasiyya, Na’ima cikin kuka tace Abbana bazai min haka ba gaskiya ne ba, ummu zainab cikin bacin rai tace wazai maki karya in ko gwaggo in ki, to kiji da kyau aure da MD anyi ankare, don baki san ciwon kan ki bazakiyi wa mahaifinki BIYAYYA BAYAN RAI? Mi ya rage ku da shi wane irin gatane bai baku ba. Cikin bacin rai ta fita daki, Gwaggonin ta ne, suka ciga ba da bata magana ganin ta kiya su ma suka mike cikin bacin rai suka tabbatar mata sai sun cika wasiyyar kanin su.

Muje zuwa🌸🌸🌸☘🌸🌸🌸

BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸🌸☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU AS’MAU(SA’ADTU)

DEDICATED TO NABILA ZANGO(LADY)

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 30-35.

Washe gari Na’ima tana daki tana kuka har ‘yan uwan Abbanta suka tafi bata fito ba. Umma kuma taki shiga dakinta saboda tanajin haushin abinda tayi jiya, duk da tana tausayinta amma tana ganin meyasa bazatayi hakuri ta karbi zabin Mahaifinta ba.

Fahad ne yazo kusa da Umma yana fadin Umma dan Allah kiyi hakuri, wallahi bama jin dafin gidan gaba daya. Gashi babu Abba, ke kuma kina cikin damuwa. Ga Yaya Na’ima itama tana cikin damuwa.

Meze hana Umma ki bari ta auri wanda takeso tunda Abba baya raye, kuma shima besan akwai wanda takeso ba da baze zaba mata MD ba. Murmushi Umma tayi tace Fahad kai yaro ne, baza fahimci abinda muka hango ba.

Na’ima da wanda takeso class mate ne, taya kake tunanin aurensu zeyi karko bayan su duka yara ne? Amma idan ta auri Md zataji dadi saboda yasan gidansu, baze taba wulakanta taba.+

Badan kudinsa yasa mukeson ta auresa ba. Saboda nagartasa yasa mukeso ta auresa. Ko bayanzu ba ni nasan Na’ima zatayi farin ciki da zabin mu. Tabbas nasan akwai ciwo rabuwa da masoyi amma kuma idan tayi hakuri zataci riba.

Fahad yace haka ne Umma. Amma dan Allah kidena fushi da ita, kinga zafin zai hade mata biyu. Umma tace shikenan Fahad, bara naje na sameta. Tashi tayi ta nufi dakin Na’ima.

Kwance take tana ta kokarin kiran wayar abun sonta amma taki shiga. Bude kofar dakin ne yasa ta aje wayar tare da tashi zaune. Umma ta gani a tsaye. Dukar da kai tayi tana fadin Umma ina kwana? Umma tace daban kwana ba ai bazaki ganni ba.

Wato daban shigo ba kinfi karfin kije ki gaisheni ko?? Bakin da suke gidan ma basu isa ki gaishe su sai kin nuna masu yanzu wuyanki yayi kwari, saboda babu Dr, yanzu ban isa dake ba.

Kinyi dai dai, duk abinda kikayi dai dai dake ne. Idan nima kika sa mani hawan jini aka wayi gari zuciyata ta buga kinga sai na bar maki duniyar ki auri wanda kike so. Kuka Na’ima tasa ta duka tana bama Umma hakuri.

Zama Umma tayi tare da rage murya tace haba Na’ima, kina tunanin zamu zaba maki abinda zai cutar da kene? Tunda har kika ga Dr ya zaba maki miji kinsan akwai abinda ya hango. Meyasa bazaki amshi zabinsa ba domin ki samu albarkarsa.

Cikin kuka Na’ima tace dan Allah Umma ki janye wannan maganar, wallahi bana son MD, akwai wanda nakeso. Umma idan ban auresa ba mutuwa zanyi muna son junanmu. Kuka me karfi tasa.

Murmushin takaici Umma tayi tace shikenan Na’ima tashi ki shirya kitafi makaranta kada ki makara idan kika dawo zamu karasa maganar. Amma inaso kisa aranki, matukar nice na haifeki bakida miji sai MD

Tashi tayi ta fita. Sosai Na’ima tasha kuka kafin tashiga wanka. Tana fitowa mai da turare kawai tasa tashirya ko karyawa batayi ba tayima Umma sallama ta fita zuciyarta tana mata zafi a haka ta nufi makaranta.

****** ******

CIGABAN LABARI

Na’ima tana barin wajen Maryam motar ta ta nufa ta bar makarantar zuciyarta tana cigaba da bata shawara akan taje ta hada kayanta tabar garin kawai, idan komai ya lafa sai ta dawo. Tana isa gida dakin su ta wuce, ta kwanta tana tunanin, yanda zata bar gidan, ta jawo wayar ta, ta kira num Hafis, still num baya zuwa damuwan bai fi miya samu wayar sa ba, kuma bai zo school yau ba, ko sun kare final exams din su, tasan shima bai yi submittin project din sa ba. A haka Ummi sister ta shigo dakin tace Umman su tace a fada mata, MD zai zo, zasuyi magana, don bayan fitar Na’iman makaranta, Shehu hassan ya kira Umman a cewa zasu don MD ya gana da Na’ima don bayan gaisuwa basu tafa haduwa sunyi magana ba, Na’ima shiru tayi batace wa ummin komai ba, da ummin taga shirun yayi yawa ta wuce abinta.

Taje ta fadawa Umman cewa ta fada mata, su kansu yaran gidan abin na damun su, ga rashin  abba ga rigimar da takuno na auren yayar su, ba wani shiri da Na’imar tayi don zatayi bako, Umman dai ce tasa akayi masu girkin abinci da abin sha.

Bayan sallar la’asar ne MD da Shehu sukayi parking a kofar gidan Dr,

Maigadin gidan ne ya fadawa Umma zuwan su,  bayan sun shiga falon Umma tasa an fitar masu da abinci da abin sha, ta leka dakin su Na’iman ta fada mata ga MD nen yazo in zata nuna masa bata tarbiya ne bismillah, ta wuce ta barta, tafi mintuna goma kafin ta tashi toilet ta wuce ta wanke fuskan da kukan da tayi idon ta duk yayi ja abinka da fara mace, powder ta shafa da kwalli , bakar jallabiyace jikin ta, mayafin rigar ta yafa ta wuce falon, da sallama ta shiga, MD sai da gaban sa ya fadi, Na’iman ma taji faduwar gaba da suka hada ido, shehu ne ya amsa sallama a hankali ta shiga cikin falon nesa dasu ta zauna, ta duka kanta kasa ta gaishe su ciki ciki, still shehun ne ya amsa ta din MD duk jikin shi rawar yake, ya rasa wane irin so ne yake ma Na’ima ko sunen ta yaji zai ji faduwar gaba.

Shehu ya kara yimata gaisuwan Dr, ya  dan jata da fira da tambayar ta, game da karatun ta, ta amsa ba yabo ba fallasa, shehun yace MD zai je ya dawo. Bayan shehun ya fita sun yi shiru dukkan su kowa da abinda yake sakawa, MD ganin shirun bazai yi ba, yayi gyaran murya kara yimata gaisuwan Dr da tambayar ta ya gida da fatar ba wani problem?ta yi shiru bata ce masa komai ba, ya kara tambayar ta karatu nen ma shiru bace komai ba, yayi ta magana ta ki cewa komai, cen shima yayi shiru da ma MD ba gwanin magana ne ba, a hankali Na’ima ta dago kanta tace masa ita fa tana wanda take so, bata son sa kuma bazata tafa son sa ba, kuma ba wata BIYAYYAR da zatayi BAYAN RAI don tasan mahaifinta bazai ce dole sai ta aureshi duk shirin Umman tane da gwaggonin ta.

MD da tunda tafara magana gabansa yaci gaba da faduwa ya tsura mata ido ya bala’in jin sonta cikin rasan, gashi gaba da gaba tace bata son sa, in ko har bata son sa gara ya hankura da nashi son, tana gama fadi ta fita falon. Ya bita da idanu  har ta bace ma ganinsa, ya mike da shirin barin falon, Ummi tayi sallama ta shigo tace Umman su tace a fada tanason magana da shi, ya koma ya zauna,  Umman ta shigo kenen Shehu ya dawo har zai fita tace ya shigo mana, ya shigo falon sun gaisa cikin girmamawa, ta ce ma MD tana son kwananen ya turo magabatansa, suje wajen yan uwan Dr tana son a tsayarda magana, MD yayi shiru na wani lokacin kamin yace ko zaa kara ba da lokaci su fahimci juna shida Na’ima don baya son a yi mata dole, Umma zainab tace ai ba maganar dole ne ba, maganar yiwa mahaifinta BIYAYYA ne ko BAYAN RANSA, kuma da yarda Allah yanda Dr ce haka zaa yi yaje ya tura magabatan sa wajen dangin mahaifin ta. Umma tayi masu sallama ta koma cikin gida a haka sunka fito gidan MD da duk jikin sa yayi sanyi, bayan sun shiga mota ne yake ma shehu bayanin yanda sukayi da Na’ima  yace ma shehu ya zaiyi, shehun yace ya kwantar da hankalin sa da yarda Allah komai zaiyi dai dai, duk kiyayar da zata nuna masa na wani lokacin ne yasan komai zai daidai ta shawara daya zai bashi yayi hankuri, shehun yace su wuce wajen kannen baban MD don suyi masu bayanin zuwa neman auren.

Na’ima kuwa dakin su ta wuce cikin bacin rai, ta tsanin mutumin tun farkon ganinta da shi, ashe da rabon zai zame mata matsala rayuwar ta,    ranta ya kara baci da jin umma ta aika su jira tayi magana da su, fahad ne ya shigo dakin yace yaya magana zamuyi don Allah ki kwantar da hankalin ki, kiyi abinda Umma keso nasa bazata cutar dake ba, ckin fada ta tasowa fahad ya wuce ya bata guri ko ta mare sa, cikin kuka ya fita dakin Umma zainab da ke jin duk abinda ke faruwa, cikin bacin rai ta shigo dakin ta fara Fada cikin bacin rai, tacewa ko mutuwa zatayi sai dai akai gawanta gidan MD. Ta fita dakin cikin bacin rai ranar duk yaran gidan kowa sai da yayi kuka.

Har dare gidan shiru abinci ma duk yaran basu ci ba, Umma zainab kuwa duk abin duniya ya taru yayi mata yawa ga rashim Dr ga bakin cikin da Na’ima ke sa mata, bata tafa tunanin akan son wani diyar da take ganin ko layi ta zana baza tsalaka. Ranar tayi kuka har kanta ya fara ciwo, ta kira baban yayansu akan tanason ganinsa, gara ayi ma Na’ima aure ta huta.

Na’ima kuwa ta sha alwashi yau zata gudu ta bar gidan, ta hada kayanta kala biyu a hand bag, Atm din dai ta dauka, don duk wata Dr na tura mata kudi don makaranta da wasu bukatun, ta kira num Hafis stil bata zuwa, ta yanke, ta kwanta da tunanin lokacin subahin zata gudu abinta, da kyar bacci barawo ya sace ta, 4:30 ta farka, daman ka’idan gidan Dr ne yaran na tashi kamin lokacin subahin suyi nafiloli da karatun qur’ani, akwai masallaci a kofar gidan, su fahad suna zuwa sallar subahin masallacin kofar gidan, tayi arwala ta dade tana nafilolin da suka saba yi, tayi subahin tun kamin masallacin su tadda sallah don tasan Umman su jam’ie take bi, bayan taji an tadda sallah a hanakali ta fita dakin su ummi duk suna dakin Umma sunbi jam’ie, ta kofar baya ta fita, ta lafe sai da akayi sujada sannen ta bude get din a hankali ta fice gidan.

Muje zuwa.BIYAYYA BAYAN RAI 35-40

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

☘☘

UMMU ASMA’U (sa’adatu)🌸🌸

Dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi rahamanir rahim..

Page 35-40

Sai da Na’ima tayi nisa sosai, lokacin gari har ya gama haske sannan ta samu wani waje ta zauna, a hankali ta fara tuno irin gatan da Dr ya nuna mata, akwai lokacin da batada lfy tana fever sosai, ranar Dr baiyi bacci ba, shike rike da ita har gari ya waye, lokacin tana secondry School.

Runtse ido tayi tana tuna rayuwarsu kafin Abbansu ya rasu.

Ta dade ahaka tana tunani. Ajiyar zuciya tayi tana girgiza kai, a fili tana fadin  bazan iya ba, wallahi bazan iya guduwa na bar Ummana da Kannaina ba, idan na gudu kafin na kai inda zanje nayi hadari na mutu fa? Shikenan na mutu na bar mahaifiyata da bakin cikina.+

Idan kuma Umma ta tashi ta gane na gudu idan zuciyarta ta buga ta mutu shikenan nayi sanadiyar mutuwar Mahaifiyata? Bakomai, bade ya rusa duk wani farin ciki na ba? Shikenan zan auresa.

Amma wallahi shima sai farin cikinsa  ya koma bakin ciki, zai aure ni saboda farin ciki to wallahi zai auri bakin ciki. Wayarta ta dauko tashiga rubuta ma Hafiz message tashiga fada masa abubuwan da suke faruwa.

Tana gamawa ta kara fashewa da kuka, ta dade ahaka kafin ta ta shi, ta wuce gida. Tana zuwa bakin gate ta iske ‘yan gidan a waje da alama ita ake nema.

Bayan ta fito da gudu kannanta suka je suka rungumeta. Girgiza kai Umma tayi tabar wajen ta koma ciki. Jansu Na’ima tayi suka shiga ciki. A falo suka iske Umma, dukawa Na’ima tayi tana kuka.

Umma tace kukan me zakiyi mani kuma? Ba guduwa zakiyi ba waya baki shawara kika dawo? Cikin kuka Na’ima tace dan Allah Umma kiyi hakuri, wallahi laifin zuciyata ce dan Allah kiyafe mani.

Fahad yace Umma dan Allah ki yafe mata tunda ta dawo. Umma tace shikenan, naji dadi tunda har kika iya tunanin dawowa, kiyi hakuri Na’ima, wallahi da ace ba Wasiya Dr ya bar mani akan ki auri MD ba babu abinda zai sa na aura maki shi.

Insha Allah wata rana zakiyi farin ciki da Zabin Mahaifinki, nasan ayanzu zaki shiga damuwa, amma idan kika daure komai zai wuce. Kada ki boyema Hafiz, ki fada masa komai kada yace kin yaudaresa.

Na’ima tace wallahi bazan kara bata maki rai ba, na yarda zan auresa kiyafe mani Umma. Dafata tayi tace na yafe maki Na’ima, tashi kije kiyi wanka kizo kici abinci. Allah yayi maki albarka.

Shigowar Hafiz kenan cikin gari,wayarsa tayi kara alamun sako yashigo. Dama tafiyar gaggawace ta kamashi zuwa kauye, gashi babu network acan shiyasa wayarsa bata shiga.

Yana dubawa yaga Na’ima ce. Murmushi yayi ya maida wayar aljihu yana fadin sai na kimtsa sannan zan karanta.

Bayan Na’ima tayi wanka taci abinci, suka koma falo ita da kaninta suna fira har Umman su, Na’ima daurewa dai ne take batason Umman su ta gane tana cikin damuwa ko kannenta da lokacin tausai suke bata. Umma ko sarai ta fahimce ta, amman batason ta nuna mata hakan, sun dade suna fira, zuwa karfe biyu, cousins din Dr suka zo da kudin neman aure da sadakin da yanuwan MD suka zo da shi, a cen gefen dangin Dr akayi tambayar auren.

Sun tsayarda rana, in Umma zainab ta kare wanka da wata daya,  Na’ima kuwa tunda suka shigo falon taja kannenta suka bar falon, tasan maganar MD ce ta kawo su, bayan sun wuce Umma ke mata bayanin abinda kenen tayi shiru, cikin jin nauyin Umman, tace duk abinda dangin mahaifinta suka tsara yayi, Umman ta kara yimata nasihar tayi ma haifinta BIYAYYA KO BAYAN RANSA, tasan zata ga ribar biyayyan.

Hafis kuwa, bayan ya natsue ne, ya dauko wayar don karanta sakon Na’imar cikin tashin hankali ya mike tsaye yace bazai yuyu ya rasa rayuwar sa ba, Na’ima ita  rayuwarsa, ya wuce dakin Ummansa cikin damuwa yace mata zai je zaria, tace masa lafiya cikin damuwa yayi mata bayanin Na’imar da yake bata labari, ta aiko masa cewa anyi mata miji aure zaa yi mata, Umman Hafis ta yi shiru cikin damuwa tace masa yayi hankuri, tunda har mahaifan yarinyar sun mata miji, ko yaje zaria meye amfanin zuwa, kuma yana da kyau, kayi ma mahaifanka BIYAYYA KO BAYAN RAN SU, ganin yabnda ya tadda hankalin sa, Umman tace yayi hankuri da safe  zasu je da mahaifinsa tare dashi, da kyar ya yarda goben su je. Bayan ya fita dakin Umman Hafis din tayi shiru tasan tabbas Hafis zai shiga damuwa don yasa yarinyar a ranshi,  zata yiwa mahaifinsa bayanin, in ya Amince suje zarian suji gaskiyar maganar.

A gefen MD kuwa duk da kudin auren da aka kai  gidan su Na’ima ya kasa samun natsuwa cikin zuciyarsa,  sai yake ganin riba me zai samu in ya auri yarinyar da bata son sa, ya sha daukan waya ya kira Ummu zainab ace wan yana son a bar maganar sai yaji ya kasa, Shehu hassan ya fada masa sai yayi hankuri komai zai wuce, yasan ko don Dr zai jure duk abinda zai je ya dawo, yayi ma alkawalin komai tsanani zai yi hankuri da Na’ima zai cigaba da addu’an Allah yasa taso shi kamar yanda yake sonta.

Hafis kuwa bayan Umman sa tayima mahaifinsa bayanin abinda ke faruwa, yace suje zarian ko don hankalin Hafis din ya kwanta, sun shirya zuwa zaria, da safe sammako sukayi, da wuri suka isa zarian, kai tsaye gidan su Na’imar suka wuce, ya kira num Na’imar bata shiga, daman tunda ta tura masa text ta kashe wayarta, har suka isa kofar gidan num bata zuwa, da fahad suka fara haduwa bayan sunyi parking, fahad yazo ya gaishe su, shine yayi ma Umman Hafis jagoran zuwa cikin gidan, cikin karamci Umma zainab ta tarbe ta, Umman hafis tayi mata bayanin tare suke da Hafis da mahaifinsa da dalilin zuwan su, Ummu zainab ta kira Fahad ya shigo da su Hafis din cikin falo, bayan sun gaisa an kawo masu abinci sunci Ummu zainab tayi masu bayanin wasiyyar da Dr ya bari har sadakin da aka kawo.

Tace masu tana son cika umurnin mahaifinta ne, bawai don bata son Hafis din bane, ko wace uwa tafi son takai yar’ta a inda take so, mahaifin mahaifin Hafis yayi ma Umma godiya sosai akan karamcin da aka yi masu,  daman aure mukaddari ne daga Allah, sunyi masu godiya sosai suka yi ma Umman sallama zasu koma kano, Hafis kuwa tun da suka fara magana yake zubar da hawaye, zuciyar sa na masa zafi, shikenen ya rasa Na’ima kenen, da kyar mahaifinsa ya jasa suka fita falon, Umma zainab kanta jikinta yayi sanyi, yaran sun bata tausayi.

Na’ima kuwa tana daki ta kasa fitowa sai kuka take yi, tsanen MD ya kara shiga zuciyar ta, ta sha alwashin sai yayi nadamar saninta rayuwarsa. Bayan sun fita falon ne, Hafis cikin kuka ya roki mahaifinsa da su barsa ya yi bankwana da Na’ima, Umman Hafis ce ta sake komawa cikin gidan tayima Umma zainab bayanin in zai yuyu Hafis yayi sallama da Na’ima, Umma zainab tace ba komai Ummi ta fada ma Na’imar a kofar fita wajen gidan Na’ima ta same su, ta gaida mahaifin Hafis, suka wuce mota suka barsu su gana, shiru sukayi suna kallon juna, Hafis ne ya daure yace wa Na’ima yana mata fatan alhairi, Na’imar kuka takeyi sosai ta kasa magana a haka Hafis ya juya ya wuce, Na’ima cikin kuka ta koma gida, duk kannen ta sun tausaya mata, Umma zainab daurewa take yi batason nuna ma yaran.

A gefen MD kuwa shirye shirye auren yake amman kasan zuciyarsa ya na tsoron abinda zaije ya dawo don ya hango kiyaryar sa a idon Na’ima, son ta kuwa kullun karuwa yake a ransa, a zaria zaa a kai Amarya kamin su wuce kaduna, kowa da gefensa ita da hindatu.

Muje zuwa.🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU ASMA’U(SA’ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango leady

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 45-50

Na’ima ta dade kwance kamin bacci ya dauke ta, karfe hudu da rabi ta farka, sabon tashi da sukayi tun gidan su, tayi arwala ta fara nafiloli, MD ma lokacin ya tashi ya fara nafilolin sa, zuwa lokacin sallah subahin ya fito domin zuwa masallacin dake gaban gidan sa, ya wuce dakin Na’ima domin ya tadda sallah, yayi mamakin jin karatun qu’arani yana tashi ya yi mintuna yana saurarenta, ya gode Allah tabas ya samu irin matar da ya jima yana rokon Allah ya bashi. Ya wuce gefen Hindatu don yasan in ba tashinta akayi bazata tashi sallah ba, ya dade yana kwankwasa kofar gefen kamin mai yi mata aiki tazo ta bude, ya wuce dakin ta bacci abinta, sai da yaga ta shiga toillet ya wuce masallaci don yasan halin Hindatu zata iya komawa ta kwanta.+

Bayan ankare sallah ya jima masallaci yana karatun qur’ani so da yawa mutanen unguwar har mamakin halinsa suke, kowa zai watse ya barsa masallaci bayan sallah subahin ba irin wasu masu kudin da ankare sallah zasu wuce, wasun ko sallah basa fitowa. Sai da gari ya waye ya fito masallaci, Shehu ne ya kira sa, yana tambayarsa hope komai daidai, MD yayi masa bayanin tun jiya bai ganta ta rufe dakin, ya kara fada masa yayi hankuri komai zai wuce, Shehu yace zuwa ajima zaa kawo masu break fast daga gidansa, kullun zaa kawo for a week don yasan Hindatu bazata basu abincin ba, MD yayi godiya sosai don yana tunanin yimata take away don yasan Hindatu.

Cikin gidan ya wuce gefen Na’ima kamshin turaren wuta ne ya tarbe sa, ko’ina tsaf da ganin yasan ta fito ne, kamar ya dibata sai yawu ce bedroom dinsa, wanka yayi ya shirya cikin wani hadadan material milky yayi kyau sai kamshi turare yake yi, yana fitowa falon yaji sallama maigadin yana fada masa ga driven gidan Alhaji Shehu an aiko, ya fita kofar gidan sun gaisa da driven ya amshi abincin cikin baban basket, falo ya wuce ya aje abincin a dining table.

Da faduwar gaba ya wuce bedroom din Na’ima yayi mamakin ganin kofar a bude, ya shiga da sallama tayi wanka ta shirya cikin kyakyan lace army green don kowane lokacin dark collar tafi sawa zamanta fara sosai, siket an bulawus ne sun amshi jikinta, shiru tayi masa taki amsa sallamar, ya sake sallama sanin hukunci sallama ta amsa masa ciki ciki, ya tsura mata ido yana kallon tayi masa kyau sosai, duk zamansa da Hindatu duk tayi kwaliyya fita zatayi, wani lokacin da daurin kirji take yini. Ganin bata ce masa kala ba, yace mata antashi lafiya still bace masa komai sai dane danen wayar ta take, yace akwai abinci a dining, still shiru ta masa,  ya yi seconds yana kallon kamin ya fita dakin, kichin ya wuce ya dauko plates da cups ya dawo falon, ya bude warmers din masa ce da miyar ganye, farfesun kaza da kunun tsamiya, yayi murmushi, yace Shehu kenen duk favorites din sa ne ya dibi abincin kadan yaci, hankalin sa na wajen Na’ima kamar ya koma ko ya dibi abincin ya kaimata, wata zuciyar na kwafarsa da ya kyaleta.

🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

☘☘

UMMU ASMA’U (SAA’DATU)

🌸🌸🌸

Dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 45-50

Na’ima ta dade kwance kamin bacci ya dauke ta, karfe hudu da rabi ta farka, sabon tashi da sukayi tun gidan su, tayi arwala ta fara nafiloli, MD ma lokacin ya tashi ya fara nafilolin sa, zuwa lokacin sallah subahin ya fito domin zuwa masallacin dake gaban gidan sa, ya wuce dakin Na’ima domin ya tadda sallah, yayi mamakin jin karatun qu’arani yana tashi ya yi mintuna yana saurarenta, ya gode Allah tabas ya samu irin matar da ya jima yana rokon Allah ya bashi. Ya wuce gefen Hindatu don yasan in ba tashinta akayi bazata tashi sallah ba, ya dade yana kwankwasa kofar gefen kamin mai yi mata aiki tazo ta bude, ya wuce dakin ta bacci abinta, sai da yaga ta shiga toillet ya wuce masallaci don yasan halin Hindatu zata iya komawa ta kwanta.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ankare sallah ya jima masallaci yana karatun qur’ani so da yawa mutanen unguwar har mamakin halinsa suke, kowa zai watse ya barsa masallaci bayan sallah subahin ba irin wasu masu kudin da ankare sallah zasu wuce, wasun ko sallah basa fitowa. Sai da gari ya waye ya fito masallaci, Shehu ne ya kira sa, yana tambayarsa hope komai daidai, MD yayi masa bayanin tun jiya bai ganta ta rufe dakin, ya kara fada masa yayi hankuri komai zai wuce, Shehu yace zuwa ajima zaa kawo masu break fast daga gidansa, kullun zaa kawo for a week don yasan Hindatu bazata basu abincin ba, MD yayi godiya sosai don yana tunanin yimata take away don yasan Hindatu.

Cikin gidan ya wuce gefen Na’ima kamshin turaren wuta ne ya tarbe sa, ko’ina tsaf da ganin yasan ta fito ne, kamar ya dibata sai yawu ce bedroom dinsa, wanka yayi ya shirya cikin wani hadadan material milky yayi kyau sai kamshi turare yake yi, yana fitowa falon yaji sallama maigadin yana fada masa ga driven gidan Alhaji Shehu an aiko, ya fita kofar gidan sun gaisa da driven ya amshi abincin cikin baban basket, falo ya wuce ya aje abincin a dining table.

Da faduwar gaba ya wuce bedroom din Na’ima yayi mamakin ganin kofar a bude, ya shiga da sallama tayi wanka ta shirya cikin kyakyan lace army green don kowane lokacin dark collar tafi sawa zamanta fara sosai, siket an bulawus ne sun amshi jikinta, shiru tayi masa taki amsa sallamar, ya sake sallama sanin hukunci sallama ta amsa masa ciki ciki, ya tsura mata ido yana kallon tayi masa kyau sosai, duk zamansa da Hindatu duk tayi kwaliyya fita zatayi, wani lokacin da daurin kirji take yini. Ganin bata ce masa kala ba, yace mata antashi lafiya still bace masa komai sai dane danen wayar ta take, yace akwai abinci a dining, still shiru ta masa,  ya yi seconds yana kallon kamin ya fita dakin, kichin ya wuce ya dauko plates da cups ya dawo falon, ya bude warmers din masa ce da miyar ganye, farfesun kaza da kunun tsamiya, yayi murmushi, yace Shehu kenen duk favorites din sa ne ya dibi abincin kadan yaci, hankalin sa na wajen Na’ima kamar ya koma ko ya dibi abincin ya kaimata, wata zuciyar na kwafarsa da ya kyaleta.

Bayan ya kare breakfast, side din Hindatu ya wuce as usuall bacci take yi mai aikin ce keta hidimar gidan ya wuce dakin ya tasheta  tana ji tayi masa banza, yasan tanajin sa, tunda maganar auren sa da Na’ima ta taso, sai taga dama take yi masa magana, dakinsa ma sai tana da bukatar sa dariya ma take bashi   yace Hindatu nasan kina jini daman zan ce in akwai abinda kike ki so ne  a kawo, still bata ce masa komai. Ya wuce abinsa, ya fito cikin harabar gidan maigadin ne keta wanke motocin masu share share nayi, ya tsaya sun gaisa ya wuce parking space ya shiga wata hadadar benze, family house din su ya wuce bayan rasuwar mahaifiyarsu akwai kaunar babarsu dake zama gidan sun mayar da ita tamkar mahaifiyar su don bata tafa haihuwa ba, sai da ya gaisa da mutanen dake wajen gidan tare da yimasu alhairin da yasa ba, kamin ya wuce cikin gidan, akwai sauran yan biki da suka zo da kauye dangin mahaifin sa da umman su, ya sallame da kudin mota, abokanin wasan sa sai tsiya suke masa ga ango, yayi masu godiya, sun kefe da baba larai kaunar Ummansu tana tambayarsa ba wata damuwa ko? Don tasan Hindatu yace ba komai kowa na gefen sa, ta kara yimasa nasiha da ya yi adalci tsakanin matan sa kuma yayi hankuri, yayi godiya ya mata sallama, ya fito ya shiga motar sa.

Cen bayan gari ya wuce ya samu waje yayi parking, cikin damuwa yake tunanin haka rayuwar zata kare ba farin cikin aure, yayi wa mahaifin sa BIYAYYA BAYAN RAYUWAR Sa, ya auri Hindatu ba wani jin dadin aure, Na’ima tayiwa mahaifin ta BIYAYYA BAYAN RAN SA, bata son sa, gaba bai san yanda zaman zai kasance ba, tun yana university bai tafa kallon yar mace da sunen so ba sai akan Na’ima, yana son ta sosai amman bata son sa, wannen dake kishin tana son sa baya samun kulawa, tara mata baya cikin tsarin sa mata daya yaso rayuwar sa. Ringin wayar sane ya dawo dashi tunanin da yake, Shehu ne ke kiran sa sun gaisa yana tambayar ango nazo gidanka baka nen ya fada inda yake, Shehun yace ya jira yana zuwa cikin mintuna ya isa wajen a gaban motar MD ya zauna, yace lafiya kazo nen, MD yayi masa bayanin damuwar sa, Shehun yayi shiru yana sauraren sa, kan yace masa yanzun sai fa kaza namijin gaske rainin da Hindatu ke ma yayi yawa,  dole ka tashi tsaye a gidanka, Na’ima ka bata time in ba cenji in zan samu Ummanta, bazai yuyu ka zauna ba farin cikin aure ba sanyinka yayi yawa, kar ka kuskura Hindatu ta gane me ke tsakaninka da Na’ima hakan zai bata damar kara yima rashin mutunci, sun jima suna magana kamin su koma gidan MD, falon yake ganawa da baki suka zauna lokacin kowane gefe cike yake da baki, abincin ranar har dare daga gidan Shehu aka kawo gefen Na’ima, sai yammah khadija matar Shehu taje gidan, gefen Hindatu ta fara shiga, sun gaisa sama sama ta wuce gefen Na’ima Maryam da wasu kawayen Na’ima da yan uwanta ne sun tarbe, ta gane Na’ima a yanda Shehun ke mata bayanin ta, Khadija tace in ce matar Shehu hassan sun kara gaisawa da Na’imar da tambayar yara, Khadija tana ta mamakin kirkin Na’ima lailai in har suka fahimci juna da MD zasu zauna lafiya, haka sukayi fira sai kusan magrib, suka yi mata sallama zasu wuce, kamin su wuce da kyar Maryam tasa Na’ima tayi wanka ta cenza kaya, tayi kyau cikin dark blue super holland dinki siket an bulawus das da jikinta, zasu fita ne, Hindatu ta shigo da yan gidan su sai da suka matsa mata ta yarda zata je, don ganin take yi tafi karfin shiga gefen Na’imar,  cikin sakin fuska Na’ima ke masu sannun da zuwa sun zauna na mintuna sukayi mata sallama zasu wuce gaba daya har sun maryam suka fito, Hindatu kuwa wani mugun kishin Na’imar taji ya taso mata, ganin irin gyaran da akayi mata, ko ita da ke kurum kudin gidansu komai bazata nuna mata, nesa ba kusa Na’ima tafi kyau ga faran faran da jamma’a.

Bayan sun koma gefen Hindatu yanuwanta ke fadi in zata gyara ta gyara yanzun ba kamar da ne ba wannen yarinyar yanda ta dauke ta wuce nen. Na’ima kuwa bayan ta rakasu, shirin sallah magrib tayi, sai da akayi isha’i ta dade tana addu’oin ta mafi yawan addu’an ga Dr yake zuwa. Bayan ta kare ta koma falo tana kallon news, MD kuwa sai da akayi kare sallah Shehu yayi masa sallama a cewan gobe zai je kaduna zai bar su Khadija zasu kwana biyu kamin su MD su tashi komawa, MD yace zuwa bayan kwana biyu zai koma don ba hutu ya dauka. Bayan ya raka shehun gefen Hindu ya shiga yayi mamakin samun ta cikin kwalliya abin har ya mance rabon tayi, don bata kwaliyya in ba fita zata yi ba, ta masa sannu da zuwa ya zauna yana tambayar ta yara tace duk sun yi bacci, yasan yan uwanta suka bata shawara kamin taje kaduna kawayenta su hure mata kunne yayi ta rabu da su taki, yai mata sai da safe ya fi zuwa gefen Na’ima, kamshi turare ne tun farkon isar side din.

Ko ina a gyare tsaf don su Maryam su gyara mata kamin su wuce, da sallama ya shiga bata falon ta koma bedroom, nashi dakin ya wuce yayi wanka ya cenza kaya zuwa farar jalabiya ya fesa turaruka masu kamshi sosai, dakin Na’ima ya wuce da sallama ya shiga, tana ji ta share shi gefen stand din mirrow ya zauna yana tambayar ya jamma’a nen ma shiru tayi bai jira ko zatayi magana yana mai bata hankuri shiga rayuwar ta da yayi, har ga Allah bai san abubuwan zasu kasance haka ba, tayi masa afuwa su zauna lafiya tunda an riga an daura masu aure, Yace bayan kwana biyu zasu wuce kaduna kamin result dinta ya fito sai lokacin ta daga ta kallesa ta ce ba inda zanje, me nayi maka ka shiga rayuwata? Bana sonka kuma bazan tafa son ka, hannun sa ya dora a nata hannun cikin wani irin shock ta ture sa tana cewa me zaka yi min mugu azzalumi, bana son ka, da sauri MD ya fita dakin cikin tsananin tashin hankali wace irin kiyaya ce yarinnen ke masa? Anya bai kure auren ba? Dakin sa ya wuce ya jawo wayarsa yasa kira’ar sudess ya dade yana sauraren karatun a hankali yaji natsuwa na zo masa.

Na’ima kuwa bayan fitarsa wani farin cikine taji tana addu’ar Allah yasa yayi fushi ya sake ta, haka zatayi ta kumsa masa bakin ciki sai ya gaji ya saketa, tayi aure da Hafis dinta, tashin hankalin ma wayarsa bata zuwa me ke faruwa da shi.

Muje zuwa🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

Unedited

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

UMMU ASMA’U(SA’ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango leady

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 50-55

Haka  Na’ima ta cigaba

da gasa ma MD aya a hannu, ta ko ina baya samun sauki. A haka suka koma kaduna inda yake aiki, kadunar ma sai da shehu ya mata magana ta yarda zata tafi, a kadunar zaman ba dadi shida ake aure ayi kiba amma shi rama yakeyi, sam beda kwanciyar hankali, ko aiki yaje baya da nutsuwa, Hindatu kishin hauka, Na’ima kuwa ba kallar kiyayar da bata nuna masa ba,  har hakan yaso ya shafi aikinsa. Kullum addu’arsa idan Na’ima ba alkhairi bace agaresa Allah ya basa karfin guiwar rabuwa da ita.

+

Sai dai duk lokacin da yayi sallah ya roki Allah bayan ya kwanta banda soyayyar Ni’ma babu abinda yake karuwa azuciyarsa, ganin zai zefa kansa cikin halaka yasa kawai ya fara azumi. Sam ya fita harkar matansa, Shehu ne ya bashi shawarar yin hakan , ya yi MD ya bari ya samu Ummu zainab ya fada mata abinda ke faruwa yaki.

Duk wani hakkinsu na abinci da abubuwan bukata yana kokarin sauke masu, amma ya dena shiga dakin kowa, abinci ma awaje yake ci, idan yadawo gidan sai da dare, kuma idan yayi sallar asuba daki yake shigewa har sai lokacin fitarsa office yayi yake fitowa.

Ko Yaransa yanzu ba sosai yake haduwa dasu ba, duk lokacin da ya hadu dasu sai dai yajasu dakinsa suyita fira, wani lokacin kuma ya daukesu sutafi yawo. Sosai wannan abun ya fara damun matarsa, domin tana matukar sonsa kawai kishi ne yasa take masa wulakanci.

Na’ima halin ko in kula da MD yake mata ya fara damunta, sam bata ganinsa bare tayi masa rashin mutunci harya saketa, gashi Maryam na zariabare tazo su tattauna, kuma idan takira wayarta kullum maganarta dayace tayi hakuri tunda anyi auren ta zauna da mijinta lafiya hakan shine zai nuna tayi BIYAYYA ga Mahaifinta.

Wannan dalilin ne yasa ta rage kiran Maryam. Wata rana bayan ta gama shirin kwanciya ta kulle dakinta kamar yanda ta saba, wayarta ta dauko sai taji tana son jin muryar Hafiz, lambarsa ta nemo tana mai addu’ar Allah yasa yau ta samesa.

Cikin sa’a tana kira tashiga, sai da kiran ya katse sannan ta kara kira, kamar baza’a dauka ba sai kuma taji an dauka, shiru tayi tana hawayen farin ciki. Kamar daga sama taji muryar mace tana fadin Salamu Alaikum.

Saurin cire wayar tayi daga kunnanta ta kara duba lambar data kira, tabbas ba kuskure tayi ba, sake maida wayar tayi a kunne tana fadin hello ina mai wayar? Daga dayan bangaren akace ke wacece da zaki kira lambar mijina kuma kirika kiran ina mai wayar? Na’ima ta maimaita mijinta? Na’ima tace baiwar Allah Hafiz fa nake nufi.

Tsaki taji anja ana fadin shegiya karuwar banza mai bin mijin mutane, banda jaraba yanzu karfe 9:00 na dare zaki kira mani miji, abin haushin ma baki sani ba ko sunanki be rubuta ajikin wayarsa ba. Kitt taji an kashe wayar.

Wasu irin hawayen bakin ciki da kishi mai tsanani Na’ima taji suna zubo mata. Shin da gaske Hafiz yayi aure? Ya goge sunanta daga wayarsa? Lallai Maza basu da amana, ni ina nan ina kokarin kashe aurena sabodashi, na hana mijina hakkinsa duk sabodashi ashe yana can yana rayuwarsa cikin farin ciki da iyalinsa.

Karar wayar ta taji hakan yasa ta dauka batare data tsaya dubawa ba. Muryar dataji ne yasa saurin tashi zaune tana fadin Hafiz. Ajiyar zuciya Hafiz ya saki tare dajin wani abu ya sokesa azuciya, tun bayan da akayi masa rokin Allah ya hakura da tunanin Na’ima, amma ayau dayaji muryarta sai yaji wani yanayi yana shigarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Ada ya samu kwanciyar hankali musamman daya samu mace mai sonsa kuma wadda take kula dashi. Duk da shima BIYAYYA yayi ma Iyayensa ya aureta domin zabinsu ne, amma da yayi hakuri gashi yana zaune da ita lafiya.

Muryar Na’ima ce ta kara katsesa tana fadin dan Allah Hafiz kayi mani magana kozanji dadi, dan Allah kace mani abinda naji ba gaskiya bane, taya zakaje ka auri wata bayan kasan munyima juna alkawarin rayuwa tare? Kullum ina tunanin hanyar dazanbi domin na kashe aurena nazo muyi aure amma sai naji wata tana kiran kanta da Matarka.

Dan Allah kada kayi mani haka Hafiz, kasan ina matukar sonka, ban taba soyayya da kowa ba sai kai, bana jin zan iya rayiwa da wani idan ba kai ba. A’uzubillahi, Na’ima hankalinki daya kuwa? Kinsan mai kike fada kuwa? Ko kin manta kedin macen aure ce? Kinga dan Allah ki aje wannan maganar ki saurare ni.

Ban kiraki saboda muyi firar haramci ba, ni yanzu na haramta agareki kamar yanda kika haramta agareni, dalilin kiranki saboda na fada maki gaskiya ne, domin ada danaga baki kirani ba na dauka kin hakura, amma ayau da Matata ta fada mani wata ta kirani, ina dubawa naga kece hakan sa nace ya kamata na tunasar dake abinda kika manta.

Na’ima nasan ke macece mai ilimin addini, duk wannan abubuwan da kikeyi son zuciya ne da rudin shedan kawai yake sa kina aikatawa bawai dan bakisan illar aikata hakan ba. Ya kamata kidawo cikin hankalinki.

Miji ba abin wasa bane, haka zalika Aure ma ba abin wasa bane domin sunnar Annabi ne, kuma duk wanda yayi wasa da ita tabbas yabar koyarwar Annabinmu. Idan har kika cigaba. Da aikata abinda kikeyi ina mai tabbatar kina gab da jefa kanki cikin wutar jahannama.

Domin duk matar auren da take kauracema mininta, bata basa hakkinsa, tana soyayya da wani can daban hakika Allah zai sakata wuta matukar bata tuba ba. Kowane bawa da tasa Kaddarar, haka Alah ya tsara mana meyasa bazamu ansheta hannu biyu ba, nida nayi ma Iyauena BIYAYYA duk da suna da ransu gashi ina zaune cikin,kwanciyar hankali.

Kuma idan na saba masu zan iya zuwa na nemi yafiyarsu domin suna raye, kefa? Mahaifinki yabar maki Wasiyya domin yana tunanin Allah zai dauki ransa ba tare daya ga wane irin miji zaki aura ba, baki taba kai,masa kowa ba bare yayi bincike yasan kalar mijin dazaki,aura.

Na tabbata da ace Abbah yasan irin mijin dazaki aura baze taba damuwa ba dan ya mutu ya barki bakiyi aure ba. Amma ganin Allah zai dauki ransa batare da ya aurad dake hakan yasa yayi maki zabi wanda yake tunani ko BAYAN RANSA zaki samu kwanciyar hankali.

Kowane bawa idan zai mutu yana mai cike da firgici, amma shi kokarinsa daya ya samu ya bar wasalcin irin mijin dazaki aura kada kije ki auri wani ki,wulakanta. Amma da irin abinda zaki saka masa kenan. Gaskiya Na’ima kiji tsoron Allah.

Kayima Iyayenka BIAYAYYA BAYAN RANSU yana da matukar amfani, domin hakan zai nuna cewar ka ‘Da na halak ne, domin duk ‘Da na halak yana ma Iyayensa BIYAYYA koda ganin idonsu ko babu. Daga karshe ina maki nasiha da kiji tsoron Allah.

Kisan cewar ke matar aure ce, kuma kinsan cewar wata rana zakije inda Abbah yaje. Yanzu idan Allah ya dauki ranki kina cikin wannan halin mai zaki fada masa? Kisani babu wanda yasan rana, da kuma lokacin da zai mutu. Gara kiyi amfani da damar da Allah ya baki tun kafin lokaci ya kure maki.

Kuma ina fatan daga yau bazaki kara kwatanta kira na ba, domin ko kin kira bazaki kara samuna ba, ina maki fatan alkhairi arayuwarki, kuma Allah ya yafe maki kuskiren da kika aikata abaya, idan kin kara aikata wani kuma to ni dai harga Allah na fita. Allah ya bamu alkhairi.

Kashe wayar yayi ya bar Na’ima a zaune kamar wacce aka dasa tana zubar da hawaye. Ko amafarki bata tab tunanin Hafiz zai fada mata irin wadannan magnaganun ba. Ashe ita hauka ma takeyi. Runtse ido tayi tana zubar da hawaye. Komawa tayi ta kwanta tana kuka da haka har bacci ya dauketa.

Can cikin dare ta farka agigice saboda wani irin mafarki da tayi. Abbanta ne yazo,mata cikin fararan kaya fuskarsa babu alamun fara’a, tana kwance taji yana fadin kin bani kunya Na’ima, nagode da kika kasa yi,mani BIYAYYA, ashe dama wadda kike mani ta ganin ido ce? Allah wadaran ‘Dan da yake kasa yima Iyauensa BIYAYYA BAYAN RANSU.

Kuma ina mai tabbatar maki tuda har kika kasa mani BIYAYYA akan aure MD, to kisani zan sashi ya sake ki, idan yaso kije ki auri wanda kikeso, amma ki saninkema ba zaki taba samun ‘Ya’yan da zasuyi,maki BIYAYYA ba koda kina raye.

Kiji tsoron Allah Na’ima, kijitsoron Allah. Batt, ya bace. Wannan dalilin ne yasa Na’ima ta farka afirgice, gaba daya zufa ta gama jika mata jiki, ta ko ina jikinta rawa yakeyi, kuka tasa tana fadin na tuba Abba, wallahi bazan kara ba. Hannu tasa ta lalaubo wayarta.

Lambar Hafiz ta fara gogewa tana fadin wallahi,na rabu dashi har abada, zan gyara halina Abbah dan Allah kada kayi fushi dani. Saukowa tayi daga gadon ba shiri ta bude kofa, sam bata kula da yanayin shigarta ba haka ta nufi dakin MD tana kuka.

Muje zuwa.

🌸🌸🌸☘☘☘
BIYAYYA BAYAN RAI
☘☘☘🌸🌸🌸
NAH
☘☘🌸🌸

UMMU ASMA’U (SA’ADTU)

Dedicated to Nabeelat zango (lady)

Bismillahi rahamanir rahim.

55-60.

Da karfi Na’ima ke kwankwasa kofar bedroom din Md, lokacin yana kan sallaya ya kare sallah cike da mamakin me ke faru, ya je ya bude kofar, d Na’ima ce tsaye jikinta sai rawa yake yi
cikin kuka take cewa.
DonAllah kayi hakuri kada kace zaka sakeni, wallahi na yarda zanyi ma Abbah BIYAYYA, zan zauna da kai har kashen rayuwata, zan baka duk wata kulawa da kake bukata, wallahi yanzu ina sonka.

Runtse ido MD yayi wasu hawayen farin ciki suka gangaro masa, hannu yasa ya dagata yana fadin ya isa haka, kije daki ki kwanta zanyi tunani kafin safe, juyawa yayi ya rufe kofar tare da jingina yana hamdala ga Allah.+

Yaso ace yashigo da ita ya lallasheta, amma yayi hakan ne dan yakara tsorata ta. Na’ima kuwa gaba daya hankalinta tashi yayi dajin abinda Md ya fada, ta dade awajen kafin ta koma daki. Alwala tayi ta fara sallah tana rokonAllah yasa kada Md ya saketa gobe.

Da safe Na’ima kicin ta shiga ta hada md hadaden breakfast, kamshi ne ta ko’ina ta gyara gidan ta saka turarunk wuta da na ruwa oily ones ko’ina gidan sai kamshi ke tashi, bayan ta kare aikin, wanka tayi ta dade tana kwaliyya don rabon tayi irin wannen kwaliyyar tun kan maganar auren ta da md ya tashi, ta shirya cikin dark purpule boyel jakad sikit an bulawus sun fito da sharp din ta sosai, falo ta wuce ta zauna don cike take da tsoron wane mataki md zai dauka a kanta, ko zai sake ta ne, don tasan iya rashin mutunci ba kallar da batayi misa ba, tabbas tayi kure rayuwar ta, amman zata gyara in har md bai yanke mata hukunci sallamar ta.

Cike da tunanin me zaije ya dawo take zaune falon, idanunta na kan kofar bedroom din sa, md kuwa cike da farin ciki yake shirin zuwa office, ya matsu ya fita dole zaije ya ba shehu labarin abinda ke faruwa.ya fito cikin shirin zuwa office yana fitowa suka hada ido da Na’ima da sauri ta mike tana ce masa ina kwana, ya amsa cikin dan daure fuska, bayason ya saurin sakin jiki da ita yana son ya fahinci da gaskiya ne ko akwai abinda take nufi, tace masa akwai abinci table, kamar yace aa sai dai yace ok, abin Na’ima batasani tun fitowar shi kwaliyyar ta, ta tafi da imanin shi, tayi mai kyau kamar ya hadiye ta sonta ko yaushe karuwa yake cikin zuciyar sa, ganin yake yi yafi kowa sa’a a duniya, table din ya wuce yanda ta tsara table ya birge shi, dan baka saba mijin Hindatu😀, ya bude hadadun warmers din fry patotos ne da kwai, farfesun kaza da kunun tsamiya, ya diba abincin kadan ya fara ci, wani test ya ziyarci bakin sa, abincin yayi masa dadi, ya kara hamdala wajen Allah. Na’ima gefensa ta zauna still a dare take, sunyi shiru shi yana aikin kallonta ita kuwa ta kasa hada idanuwanta dashi, ya kusa gama cin abinci yace mata bazata ci abincine ba, tace ta koshi, ya aje spoon din yana kallon, kuka ne ya kubce mata, tace masa tasan tayi kure but tana rokon sa da ya yafe mata, tayi alkawalin zatayi wa mahaifinta BIYAYYA BAYAN RAYUWAR SA. Md hamdala yake cikin ransa, yayi shiru yana sauraren ta, yana ayyana abubuwa da yawa a rayuwarsa tabbas maharkuci mawadaci, sai da ya kammala cin abinci, ya mike tsaye, yace zai je office ta sake tunani kamin ya dawo bayason ya tauye mata hakki, in har yanzun tana son Hafis shi zai iya sawaka mata ta auri zafinta, ya tsura mata ido ya ga reaction din ta, kuka ta kara ace tana son sa ya yafe mata, ya wuce yana cewa ta dai yi tunani,  har zai fita falon ya jita bayansa tana cewa ya kawo brifcase din, zata raka shi, ya mika mata suka fito side dinta, a harabar gidan suka hadu da Hindatu, zata fita, Na’ima mamaki ne ya kamata, ina zataje da safe haka lokacin taran safe ba ma’aikaciyar gwannati ba.

Na’ima ce ta fara gaidata, ko kallon su Hindatu batayi ta wuce abinta, tana tsuki, abin yayiwa Na’ima ciyo, md kuwa bai yi mamaki don yafi kowa sanin halinta, har baki mota ta rakashi tare da yima sa a dawo lafiya, sai da ya fita get ta koma cikin side dinta tana mamakin halin Hindatu daman haka takeyi ma mijinta, lailai tayi kure wato su biyun ba inda yake jin dadi, wayar ta dauka ta kira num Ummanta, ring daya ana biyu ta dauka, sun gaisa Na’ima ta sa kuka tana rokon Umman ta yafe mata, ta tuba hamdala Umma zainab tayi tace ta yafema ta, tayima mijinta biyayya Allah yayi mata albarka sun dade suna magana kamin suyi sallama, ta nemo maryam cikin kuka take fada mata abinda ya faru da mafalkin abbanta da tayi, maryam tayi murna sosai da kawarta ta gane gaskiya, sun dade suna tataunawa yanda Na’imar zata jawo hankalin md, maryam tace ta kwantar da hankalinta tasan md bazai iya sakinta ko don abbanta, sunyi sallama, Na’ima ta kwanta tana tunanin yanda zata jawo md ko zatayi ma shehu magana ya roke shi? Batasan yanda zatayi ba, tana kwance tana nazarin me ma zata girka masa lunch, ga shi da yammah gefen Hindatu zai koma, a haka bacci ya dauke saboda rashin baccin jiya.

Md kuwa yana fita ya kira shehu, shehun cike da tsoro ya amsa wayar don yasan abokin shi bayada kwanciyar hankali gashi da safe, md ya labarta masa abinda kenen Shehu kuwa yayi yace na fada maka, Allah bazai bar ka haka ba, naji dadi abokina, nen ya masa bayanin me yace mata, shehu yace ya bata zuwa kwana biyu,yasan ta sauko ne, tunda ita ta same sa, a haka sukayi sallama da cewan zasu hadu anjima.

Na’ima kuwa sai kusan shabiyu na rana ta farka, ganin yanda lokaci ya tafi,  da hanzari ta wuce kichin da tunanin me zata girka, fried rice an cos low ta with chiken tara hadawa,  sai bayan karfe biyu ta kare aikin, ta sake wanka ta shirya cikin gwon din dark green  shadda tayi kyau sosai. Md kuwa da kyar yakai karfe biyu office ya ji duk zaman office din ya ishe sa, gida ya wuce, side din Hindatu yafara zuwa har lokacin bata dawo ba, har su Nuwaira yaranta an dauko su makaranta amman bata gida, abin yayi masa ciwo, yana tunanin in ya kare da matsalan Na’ima zai daukar Hindatu mataki ya gaji, ko bazai saketa don BIYAYYAR mahaifinsa, zai gyara mata zama ya gaji, a haka ya wuce side din Na’ima tun farkon kofar ya fara juyo kamshin turaren wuta, ya yi sallama ya shiga cikin falon tana zaune tana kallo ta amsa tare da mikewa ta amshi brifcase dinsa tana masa sanun da zuwa, kamar ya rugemeta, ya daure, dakinsa tavwuce da jikar, ya bita baya, yai mamakin gani dakin ko’ina a gyare an saka turaren wuta, toilet ta wuce ta hada masa ruwan wanka, ya shiga wanka ta koma falo, ya shirya cikin jalabiya ya fito da tunanin anya zai iya kwana biyun da Shehun yace, ko yanzun daurewa yake,  kamin ya zauna tace ga abinci, table ya wuce, ya fara cin abincin Shehu ya kira yana fada masa yazo, tare suka ci abincin suna fira, Na’ima kuwa bayan sun gaisa da shehu daki ta wuce duk jikinta yayi sanyi, ganin take kamar md bata gabansa, bata san mutunin daurewa kawai yake ba. Bayan sun kare cin abincin suka fita wajen gidan sun jima suna hira, Shehu yayi masa sallama ya wuce yana ta yaba girkin Na’imar, Md kuwa cikin gidan ya koma Na’ima tana daki kwance tana tunanin mafarkin da tayi da abbanta kuka take yi sosai, Md ganin bai jita ya wuce dakin yayi mamakin jin kukan ta, da sauri ya shiga dakin ya isa har saman gadon ya ce mata lafiya kike kuka, tayi shiru sai da ya kara maimaitawa tace masa ya yafe mata tayi kure, ya hau saman gadon sosai ya jayota zuwa jikinsa, ya rungumeta sosai jikinsa, a hankali ya sauke ajiyar zuciya Na”ima ma wani sanyi taji a zuciyarta sun dade a haka, Md yace ta kwantar da hankalinta ba abinda zai rabasu yana sonta har gobe, jin abinda yace yasa ta kara shigewa jikinsa, ya kara rugumeta jikin shi.🌸🌸🌸☘☘☘

BIYAYYA BAYAN RAI

☘☘☘🌸🌸🌸

NAH

🌸🌸🌸☘☘

UMMU ASMA’U(SA’ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango leady)

Bismillahi rahamanir rahim.

Page 60-65

Rungumeta yayi sosai cikin jikinsa, kiran sallar la’asar din da kayi ne a masallacin dake kofar gidan yasa md ya janye ta jikin sa, muryar a kasa kasa yace zanje masallaci kije kiyi sallah dakinsa ya koma yayi shirin zuwa masallaci.

Bayan ankare sallah, shirin fita yayi akwai gaisuwan rasuwar da zasuje da yan office din su, ba don fitar ya zaman masa dole ba in da zai je,  ga shi abin takaicin da dare gefen Hindatu zai koma, tun safe rabon sa da ita, wannen karon zai gyara mata zama ya gaji da iskancin ta, bazai sake ta ba, saboda BIYAYYAR mahaifinsa, amman tabbas zai bi shawaran Shehu zai koya mata hankalin, bedroom din Na’ima ya wuce, yana shiga tana fitowa wanka daure da towel daya a hannunta, duk saurin da take ta isa wajen da hijab din sallah ta yake, ya riga ya shigo dakin, wani irin abu ya ji a jikinsa ganin ta haka, duk shape din hips dinta ya fito, a hankali ya taka zuwa inda take tsaye har suna jin numfashin juna yace mata zasu je jaji wajen ta’aziya wani a office dinsu mahaifinsa ya rasu, kanta a kasa tayi masa a dawo lafiya, ya dago habar ta yana kallonta cikin idanunta ta rufe idonta cikin jin nauyin sa, kiss ya mata a kumatu kamin ya saki fuskar ta, ya juya ya wuce, tayi seconds a tsaye tana shafa inda yayi mata kiss, wani farinciki da son sa ke shigar ta.

+

Sai bayan isha’i Md suka dawo, gefen Hindatu ya wuce ta dawo zuwa lokacin tana hakince falo tana kallo, yayi sallama su Daddy da nuwaira ne yaran sa suka rike shi suna masa oyoyo daddy, Hindatu kuwa ko kallonsa batayi balle tayi masa sannu da zuwa, bai ce mata kalla yaja yaran suka wuce bedroom dinsa, ya dan tafa fira dasu yace suje falo zai yi wanka, ya fito wanka ya sanya jallabiya mai guntun hannu, falon ya koma lokacin Hindatu bata falon sai yaran dake kallo, yaran ya ja zuwa Side din Na’ima, tun zuwan Na’ima gidan shigar yaran side din ta kidayaye ne, maman su bata bari suje ko sun je zata sa yar aikinta ta dawo da su, a falo suka tarada ita, tayi masa sannu da zuwa tare da jan yaran, daman ita tun gida tana son yara, kicin taje takawo masu dambun nama da drinks, nen suka zauna suna ci. Md sai kallon ta yake yi, bayan yaran sun kare yace zai wuce sai da safe har kofar side ta rako su, zata juya ya riko hannunta, wani shock suka ji yace mata take care, ya ja yaran suka wuce. Yana shiga falon Hindatu na fitowa cike da masifa tace ina yakai mata yara, kar ya kara kai mata yara wajen wata banza, yaran ya tura dakin su, baya son yaran suga abinda ke faruwa, ya ce mata bata isa ta hana yaransa zuwa wajen matarsa ba, yana sane da yanda take hannsu zuwa side din Na’ima, wallahi ko ta gyara ko ya dauki mumunen mataki a kanta, duk da ta dan tsorata da shi don cikin fushi ya ke magana still bai sa bakinta yayi shiru, ganin kar ya biye mata yar aikinta najin su, yasa yayi wucewar sa bedroom dinsa.

A matse yayi kwana biyu gefen Hindatu, duk safe da dare zai shiga side din Na’ima ya dibata,  Ranar da zai koma gefen Na’ima yana office Shehu ya same sa yayi ta masa tsiya, sai yammah sosai ya bar office ya wuce gida.

Na’ima kuwa tun bayan la’asar take kichin ta girka lafiyayen tuwon shinkafa da miyar kuka da manshanu, ta hada zobo da fineapple, da farfesun kan sa, Bayan ta kammala girkin ta gyara ko ina gidan, ta saka turaren wuta, tayi wanka tai kwaliyya sosai, ta shirya cikin wata fitted gwon ta robber tayi rolling kanta da mayafin rigar, rigar ta fita mata da duk shape din ta.

Ko da Md ya iso gida ana sallar magrib saboda hold off an taso aiki, masallaci ya wuce sai da akayi isha’i ya shiga gidan side din Hindatu ya wuce, tana falo da yara ko kallon gefen sa batayi ba, ya diba yaran ya wuce side din Na’ima.

Koda ya shiga tana bedroom dinta tana karatun qur’ani gidan tsaf sai kamshi ke tashi, dakin sa ya wuce ya yi wanka, jin shigowar sa yasa ta rufe qu’arnin tayi addu’oin ta, koda taje ya shiga wanka, falo ta dawo tana jiran fitowar sa, bayan ya kintsa falon ya wuce, ya dade tsaye yana kallon ta, sam bata ji shigowar shi hankalinta na kan tv, kamshin turaren sa ne yasa taji alamun sa, tayi masa sannu da zuwa , yazo inda take zanu ya zauna jikinsu na gugar juna wani yar Na’ima taji duk ta daburce cikin ina ina tace abinci na table, ta mike zuwa table din ya jawo ta, ta fado jikinsa, rugumeta yayi tare da sakin ajiyar zuciya. A kunne ya rada mata kiyi kyau sosai, ya gangaro da bakin sa zuwa wuyanta, numfashin ke fita da sauri da sauri kamar wanda yayi tsira guda, Na’ima kuwa wata kasala ce ta saukar mata, cikin wani irin murya da batasan tana da ita tace ga abinci fa, lokacin har ya kangaro zuwa wajen kirjinta, nishi kurum yake, karar wayar sa ta dawo dashi duniyar da ya fara shiga, ya sake tare da jawo wayan dake gefensa sai da ya saita kansa ya fara magana da wani abokinsa ne. Bayan ya kare wayar dining ya wuce, tare suka ci abinci ya yaba girkin sosai, bayan sun kare, bayan sun kammala cin abincin falo suka dawo kujeran da yake zaune yace tazo ta zauna, tana zama ya jata zuwa jikinshi, jikinta kamshi yake sosai daman Na’ima gwanar sa turare ce, fira suke yi cike da nishadi, sai goma yace ta tashi suje su kwanta, bedroom dita ta wuce ta cenza kaya zuwa night gwon black doguwa ce mai shara shara, ta wanke bakinta da mouth wash, ta kara sa turaruka, tana tsaye da tunanin ya zata tunkari dakin Md a haka taji yana kiranta zane ta daura tasa hijab, har ya kawo falo suka hadu, dakinsa ya jata, yace tayi arwala zasuyi sallah, tace tayi arwala don ko yaushe tana arwala kamin ta kwanta. Raka’a biyu suka yi, sun dade suna addu’a, bayan sun kare saman gadon ya je ya kwanta ya ce tazo ta kwanta, da hijab din ta kwanta gefensa, ya juyo da ita tare da cire mata hijab din da zannen da take daure dashi, ta koma da night gown kadai, ya jawota zuwa jikinsa, wasanin yake yi da ita har ya gangaro a kirjinta, numfashin sa na fita da sauri da sauri, ita kanta Na’imar tana enjoying abin,   zafin da tafara ji ne a kasanta, ta fara kokarin turesa lokacin Md bai masan tanayi ba, yayi nisa sosai, abin biyu ya hade masa ya dade rabonsa da mace kuma abin yazo da sabuwa a leader. Tun ana mintuna har akayi awa, lokacin Na’ima ta jigata, sai bayan wani lokaci ya samu natsuwa Md da kukansa sambatu dai yakeyi Na’ima ta gigita sa, bayan ya samu natsuwa ne ya kara rungume ta lokacin  ajiyar zuciya dai takeyi ta wahala iya wahala, batason nuna masa hakan, baccin wahala ne ya dauke ta, Md kuwa toilet  wuce ya tsalkake jikin sa, sallah ya fara yi, ya dade yana godema Allah, sai ukkun dare ya kwanta, tare da rungume Na’ima jikinsa, ya dade yana kallonta tana sauke numfashi a hankali dagani kwanen wahala ne takeyi.

Sai subahin Na’ima ta falka saboda tashi lokacin ido ta tsura Md tana kallonsa wani irin son sa ke shigarta, ta gode Allah da yasa tagane bata kai ga rasa shi ba, kyakyan ne sosai, duk da baiyi farinta shima fari ne, abinda batasani tun falkawar ta shima ya falka, ganin lokacin sallah yayi yasa ya bude idanun sa, shi ya taimaka mata tayi wanka hadi da arwala mamakin karfin halinta yake, yasan tana jin zafi amman batson ya gane.

Sai da gari ya waye ya fito masallaci, ya kira family dr sa, yayi masa text maganin da zata sha pharmercy yaje ya sayo drugs din, kichin ya sameta tana hada break fast, yayi mamakin karfin halinta, tare suka kammala aikin wanka takarayi ta sha magani, yace ba zai je office taje yaje taji sauki, bayan ya shirya sai da ta kwanta har bacci ya fara daukar ta don akwai maganin bacci cikin drugs din, side din Hindatu ya shiga kamin ya wuce office lokacin taran safe batayi amman har tayi shirin fita.

Ransa ne ya baci sosai ya ce mata ina zata je, ba inda zata je yau, jin abinda yace yasa ta taso masa tana cewa bai isa ya hana mata fita ba, duk shekarun bai hana ta fita ba, yace yau wallahi duk ta fita sai ya dauki mata akanta, tace duk abinda zai ya je yayi, in akan yar iskar matar da ya auro yake tunanin ya wulakanta zata dauki mataki kan su,  ya wuce cikin tsananin fushi, yana fita ta dauki mota ta fita. Ko me zai faru.

Muje zuwa.☘☘☘🌸🌸🌸

BIYAYYA BAYAN RAI

🌸🌸🌸☘☘☘

NAH

☘☘🌸🌸🌸

UMMU ASMA’U (SA’ADATU)

Dedicated to Nabeelat zango (lady)

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM.

Page 65-70

Last page.

Kodalast page.o, Hindatu bata dawo ba, haka yshiga yaci abinci shida Na’ima, suna zaune a falo suna fira

yaji karar motar ta, ya tashi yayi yace ma Na’ima yana zuwa. Bakin kofar gida yaje ya tsaya.

Haka tafito tana ya mutsa, ta gefensa tazo wucewa ko,kallonsa batayi ba ta rabe zata wuce. Da karfiya fisgota sosai ta tsorata ganin yanda ta kusa faduwa. Daure fuska tayi tana fadin meye haka? Fuska adaure Md yace ina tunanin nan gidan beyi maki kama da gidanku ba.

Duk duniya agidan Iyayenki ne kawai zakiyi abinda kija ga dama domin can ne kike da iko dashi. Saboda haka kamar yanda kika fita ina so ki juya ki tafi gidanku, sai na neme ki, tayi shewa tace ai ka kasan in ka isa ka sake in mana, gidan kuma na barsa har abada, md kuwa taikaici kamar ya kashe sa, badon BIYAYYAR mahaifinsa tabas da yau zai saki Hindatu, but ko yanzun zai kyaleta sai gidan su sun nema mata sakin da kansu, cikin bacin rai yace.+

Kuma idan zaki shiga ki dauki kayanki na baki mintuna biyar ki bar mani gida.

Nagode Allah duk cikin yarana babu wanda ba’a yaye ba, dan haka bana son ki daukar mani yaro ko daya saboda anan kika samesu. Cike da masifa tace sai me. Dama taya za’a kawoni ni daya sannan ka koreni na tafi da nauyi gidanmu.

Allah nagode maka da ba’a daji ka dauko ni ba, kai kanka kasan muna da gida. Kuma mintuna biyar sunyi mani yawa. Butulu kawai. Rabasa tayi ta wuce. Na’ima da side dinta sama sama take jin hayaniya, jin abin yayi yawa yasa ta bude tagar falon ta, ganin yanda Hindatu ke cin mutunci Md gaban maigadi da masu hindimar gidan kasa motsi tayi, Na’imar fitowa tayi da niyar ta basu hankuri.

Haka Hindatu da kwashi kayanta na sawa tarika fitarwa har ta gama, ko,kallon Na’ima  batayi ba ta wuce. Rufo kofar Md yayi ransa abace ya kama Na’ima suka shige side din dama Yara suna makaranta. Bata hanasa kanta ba saboda tasan ransa abace yake, sosai ta dage wajen faranta masa rai har sai da ya manta da wani bacin rai.

Kasancewar Na’ima Ummanta ta koya mata yanayin zaman gidan miji musamman idan kana da mata yasa sam bata tambayi Md abinda ya faru ba, domin Ummanta tace idan kana da kishiya dan kaji sunyi fada da mijinku kada kace zaka ria zakewa kana tambayar abinda yafaru.

Matukar ba shine yayi maki maganar ba to kada ki tambayesa, kiyi kokarin kyautata masa, idan kuma yayi maki maganar kada ki sake ki fada masa muguwar shawara domin alokacin zai kara gwada kyawun halinki.

Wannan dalilin ne yasa Na’ima batayi masa maganar ba, ita dai tana kokarin faranta masa rai. Lokacin da Yaran suka dawo haka suka zauna ta sa masu abinci sukaci tayi ma kananan wanka sukayi ta wasa, ko takan Mamarsu  basu bi ba.

Da Md ya dawo sosai yaji dadin yanda yaga Na’ima taja Yaran ajiki, hakan yasa hankalinsa ya kara kwanciya dan yasan ko ya rabu da Hindatu har abada Yaransa bazasuyi kuka ba.

Mahaifiyar  Hindatu tasan kome yake faruwa na zaman aurenta, hakan yasa datazo ta fadi karya da gaskiya tacce

Allah ya kyauta sai taje ta share dakinta ta zauna, Allah ka zaba abinda yafi alkhairi.

Mamanta tace in dai gidan ne   gaki gashi ita Hindatun taji dadi, hakan yasa tashige daki hankalinta kwance ta cigaba da hidimarta, dan tace bazata koma gidan Md ba.

Na’ina da Md da Yaransa ne suka fito daga wata super market, yaran kowa da kayan makulashansa sai dadi sukeji. Sunzo shiga mota kenan Na’ima taji an kira sunanta, tana juyawa taga wata mata dauke da koyo kayan jikinta da ka gani kasan tana cimin wahala saboda yanda suka kode, fuskarta kamar wacce ta tashi daga ciwo.

STORY CONTINUES BELOW

Tsauwa tayi tana kallonta. Murmushi wancan tayi tana fadin kema baki gane ni ba? Aisha Bello Nagari ce fa clasa mate dinki. Zaro ido Na’ima tayi tana maimaita sunan. Jinjina kai Aisha tayi tace nice fa.

Na’ima tace Allah sarki ashe kema anan kike aure? Murmushi Aisha tayi tace gidana yana can tsallaken, yanzu haka nazo wancan shago ne zan sayi abu.

Kefa a wace unguwar kike? Nan Na’ima tayi mata kwatance tace kawo na sa maki lambata sai muyi waya. Wata karanar waya ta mika ma Na’ima duk taci duniya. Sosai Na’ima take cike ta mamakin ganin Aisha ahaka.

Tun daga shigarta, wayarta harma da yanayin ta kasan akwai matsala. Amasa tayi tasa mata lambar tana fadin bani taki, rubuta mata tayi tana fadin insha Allah gobe zanzo. Na’ina tace Allah ya kaimu.

Md ga kawata Aisha school mate dina ce. Murmushi yayi suka gaisa. Dubu biyar ya bama Na’ima yana fadin bata asayama yaron biscuit. Cike da farin ciki Aisha ta amsa tana masa godiya hada kwalla.

Salama sukayi mata suka tafi. Tun amota Na’ima take tunanin halin da Aisha tae ciki. Yarinyar ‘yar gayu, mai rike wayoyi masu tsada amma yanzu itace ahaka. To wace irin rayuwa Aisha ta cinci kanta haka? Hannun Md taji a hanunta yana fadin ko ba’a tambaya ba kawarki tana cikin wani hali, hakan yasa na bata kudi.

Na’ima tace tunanin da nakeyi kenan, muje gida kaji labarinta sai ka kara tausaya mata, amma gobe idan tazo nasan zata fada mani halin da take ciki.

Da safe bayan Md ya wuce office yara sun je makaranta, Aisha ta isa gidan Na’ima sosai ta tarbeta, bayan sun gaisa ne, Aisha ke bama Na’ima labarin mijin da mahaifinta ya zafa mata kamin rasuwar sa.

tayi tsaye tace bata son sa ba yanda umman ta batayi ta kiya, karshe taje ta fadawa kanin mahaifinta tare da kai masa wanda take so, ya rufe masa baki da kudi, kanin mahaifinta yace dole wanda takeso zaa aura mata.

Haka yasa mamanta tayi fushi da ita, duk hidimar kanin mahaifinta ne ya tsaya mata, mamar sama sama akayi bikin. Bayan bikin ta gane mijin nata duk karya ne gidan ma ba nasa ne ba, karatun kwrai baiyi ba, ga neman mata, saboda kada ayi mata dariya yasa take ta hankuri da shi.

Sam baya tausayinta, yaransu 3 kullun cikin wahala take, Aisha tace Na’ima nayi nadamar kin yiwa Mahaifiyata BIYAYYA Kin ga inda rashin BIYAYYA ya kai in.

Na’ima kuwa jikinta ya mutu ta godewa Allah, nen take bama, Aisha labarin auren ta da Md, sosai Aisha tayi nadama,  Na’ima tace da yarda Allah zata taimaka ma iya karfin ta, sunyi sallama Na’ima tayi mata alhairi, ta kai ta har gida don ta ga gidan, ta kara tausaya mata da taga inda suke rayuwa.

Bayan ta koma gida, ta kara godewa Allah, zata kara dagewa wajen kula da mijinta da yaransa, gata bawanda baya bata, ko motsi tayi zai bar abinda take sai yaga ta koma daidai, Ummun ta da kannenta komai shi ke masu, basu rasa komai ba.

Da yammah suna zaune harabar gidan suna shan iska, yaran na wasa da kayan wasan su, take bawa Md labarin Aisha da yanda taga inda suke zama, ya ce zai karfi takadun ta ya nema mata aiki Na’ima tayi masa godiya sosai.

********************

Bayan shekaru biyu

Na’ima result dinsu ya fito har tayi servuce ta fara aiki, ta haifi identical twince duk maza, yaran gwanin shawa, da mahaifin su suke kama amman farin Na’ima suka yi, dady da Nuwaira sun kara girma, Md arzikin sa sai gaba yake yi yasamu karin girma sosai a office.

Macca Na’ima taje har ummra, ta kara kyau, maryam ma tayi aure suna zumunci sosai da Na’ima.

Hindatu kuwa ansha gida har ta raina kanta, anyi anyi Md ya dawo da ita yaki, tun tana daukan abin ba komai har ya fara damunta, da kanta ta roki yayunta su bama Md hankuri, sai da suka jamata rai suka same sa.

Md yaji nauyin yayun ta yace zai zo, amman zai yi tafiya in ya dawo, bayan wata daya, sun masa godiya suka wuce.

Ba inda zai je yaji nauyin ce masu aa ne, da kyar bayan wata daya ya aika mata ta dawo bai je ba.

Bayan ta dawo sai da ya gindiya mata sharudda tace ta yarda ya yafe mata, yaranta sun ki yarda su koma gefenta suna wajen Na’ima.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Md da Na’ima zaman su gwanin shawa, tana kyautata masa, kullun sonta karuwa yake yi a ransa, ita ma haka.

Hindatu ko kadan tasan bazata hada kanta da Na’ima ba, cikin Md na kwatanta adalci tsakanin su, suna zaman lafiya don duk iskancin Hindatu ta aje sa.

Alhamdulilahi

A nen na kawo karshen Biyayya bayan rai abin nayi kure Allah ka yafe min.

Kalubalen ku yan mata, tabas biyayya bayan rai gaskiya ne

Taku

Ummu Asma’u (sa’adatu)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *