Cikakken tarihin aisha najamu
SUNA: Aisha Abdurrau’f
INKIYA: Aisha izzar so, Aisha najamu
SHEKARU: 1996
AIKI: Jarumar fim
AURE: Babu
YARA: Biyu
GARI: Jigawa
KASA: Nigeria

WACECE AISHA NAJAMU
Shahararriyar jarumar kannywood Aisha abdurrauf wadda akafi Sani da aisha izzar-so ko kuma aisha najamu takasance daya daga cikin jaruman dasuka shigo masana,antar ta kannywood da kafar dama duba da yadda ta sanu ta samu daukaka lokaci guda Musamman a cikin izzar-so shiri mai dogon zango (series film)
HAIHUWARTA
Anhaifi jarumar ne a shekarar alib 1996 a jihar jigawa dake arewacin Nigeria
KARANTA: Cikakken tarihin Abdul d one
KARATUNTA
kana jarumar aisha najamu tayi karatunta na primary hadi da na gaba da primary wato secondary school duk a mahaifarta wato garin Jigawa
Saidai har izuwa yanzu jarumar bata samu damar cigaba da karatunta na gaba da secondary ba
IYALI
Kana Jarumar wadda akafi sani da aisha najamu ta taba yin aure kafin shigarta harkar fim harma tana da yara maza guda biyu
FARA FIM
Kamar yadda jarumar ta zayyana farkon shigowarta masana,antar ta kannywood ta fara fito a vidiyoyin waka ne tare da jarumai kafin ta fara fitowa a fina-finai
Sannan ta fara fitowa a fina finan hausa ne a shekarar dubu biyu da sha tara (2019)
DAUKAKARTA
Daukakarta ya farane tun bayan bayyanarta a shiri mai dogon zango na izzar-so wadda jarumi lawan ahmed yashirya Kuma ake haskawa a manhajar YouTube
Kana Izzar-so shine jigonta domin ta dalilin izzar-so ne ta samu sanuwa ta samu daukaka har izuwa matakin da take a yanzu
JERIN FINA-FINAI
Izuwa yanzu aisha najamu ta fito a fina-fiani da dama kamarsu
_Izzar-so (series)
_Sarki Goma
_Manyan mata
_Akwai kura
Dadai sauransu
KARANTA : CIKAKKEN TARIHIN ALI NUHU
HADAKA
Kana ta fito a fina finai tare da jarumai da dama kamarsu
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Lawan Ahmed
*Jarumi Salisu S fulani
*Jaruma Khadija yobe
*Jaruma Minal Ahmed
*Jarumi Kb international
Dadai sauransu
KARIN BAYANI
Acewarta abin da yafi faranta mata rai shine ganin yadda takai wani matsayi wadda har tana daukar nauyin kanta kuma tana taimakawa iyayenta da yan,uwanta da makusantanta
Sai dai da aka tambayi jarumai shin zata iya auren dan kannywood
Sai tayi shiru ta kasa bada amsa
Zaku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin aisha najamu