CIKAKKEN TARIHIN NUHU ABDULLAHI

Cikakken tarihin nuhu Abdullahi

SUNA: Nuhu Abdullahi

SHEKARU: 3 January 1991 (shekara 31)

AIKI: jarumi, me shirya fim

AURE: Jamila Abdulnasir

GARI: Kano

KASA: Nigeria

 

Cikakken tarihin nuhu Abdullahi

WANENE NUHU ABDULLAHI

Nuhu na daya daga cikin jarumanda suka taka rawa a masana’antar shirya fim din Hausa da ake kira Kannywood. Jarumin wadda haifaffen garin Kano ne yayi suna a fadin kasar dama sauran nahiyar Africa. Bayaga shirin Hausa jarumin yanayin shiri da harshen turanci wadda finafinansa na turanci sun hada da there is a way, this is a way, Yellow paper, heart beat, light and darkness dadai sauransu.

HAIHUWARSA

An haifeshi a 3 January 1991 (shekara 31) a jihar kano

yakuma yi karatunsa a cikin jihar.

Karanta CIKAKKEN TARIHIN ADAM A ZANGO

FARA FIM

Jarimin yashigo masana’antar kannywood tin a shekarar 2009. Shirinsa na farko itace Ashabul kahfi wadda shirin yasamu karbuwa kuma takasance sillar Samun daukakarsa Jarumin yasamu Karin sanuwa ne a shirin kanin miji wadda yafito tareda jarumin Ali Nuhu hakan tasa Taurarinsa suka kara haskawa sannan yasamu karbuwa dakuma tarin masoya. Ashekarar 2020 yafito a cikin shiri mai dogon zango wadda ake sakewa a manhajar Arewa24 shirinda Naziru, Nazifi Asnanic dakuma Aminu saira suka shirya mesuna labarina

Bayaga haka yakasance mai shirya fina finai a masana’antar inda yashirya shiri irinsu Baya da kura, Mafarin tafiya, ta leko ta koma, Rana Tara, Fulanin Asali, gamunan dai dasauransu.

AUREN NUHU ABDULLAHI

Nuhu yana da mata daya Jamila Abdulnasir wacce ya aureta a shekarar 2021

 

Cikakken tarihin nuhu Abdullahi
Jarumi Nuhu Abdullahi

FINAFINAN NUHU ABDULLAHI

Jerin finafinansa sun hada da
-Aisha
-Ana Wata ga wata
-Ashabul Kahfi
-Ba’asi
-Baya da kura
-Dattijo
-Gamu nan dai
-Gaba da gabanta
– Haseena
– Hajjaju
– heart beat
-Kanin miji
-Mafarin tafiya
-mugun zama
-Ta leko ta koma
-Tsammani
-thorny
-yellow paper
-light and darkness
-there’s a way
-Wata tafiya

HADAKA

Sannan jarumin yafito a fina finai da dama tare da jarumai da dama kamarsu
*Adam a zango
*Ali nuhu
*Nafisa Abdullahi
*hadiza Muhammad
*Sadiq Sani Sadiq
*nazir sarkin waka
*Ramadan booth
*Hafsat Idris
Dadai sauransu

Karanta CIKAKKEN TARIHIN RAMADAN BOOTH

domin Karin bayani dangane da cikakken tarihin nuhu abdullahi a YouTube Nw Hausa Tv

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *