Cikakken tarihin saratu gidado
SUNA: Saratu gidado
INKIYA: Daso
SHEKARU: 17 JANUARY 1968 (shekara 53)
AIKI: Jarumar fim
YARA: Yaro daya
MIJI: Muhammed lawan
GARI: Kano
KASA: Nigeria

WACECE SARATU GIDADO
Saratu gidado wacce akafi sani da (DASO) ta kasance jaruma a masana’antar shirya fina-finan hausa na kannywood. Wanda ta Jima Tana taka rawar gani a harkan film a cikin shekarun rayuwanta.
Jarumar tafi fito a matsayin Mai fada ko munafurci a Shirin Hausa amma a Shekarar 2019 tace zata daina fitowa a wannan sigar domin Yanasa mutane suna mata ganin haka take a rayuwarta ta asali.
Ta kasance Daya daga cikin shahararrun jarumai mata na masana’antar kannywood wadanda suka jajirce wajen ganin masana,antar ta daukaka.
Saratu gidado takasance itace mace tafari da take da aure kuma take fim a masana,antar kannywood.
karanta: CIKAKKEN TARIHIN HAMISU BREAKER
HAIHUWA
An haifi saratu gidado ne a cikin kwaryan garin Kano a anguwar gwale dake cikin jahar. A shekarar alib 1968
Sannan kuma tayi wayo ta girma a cikin garin kano daga bisani ta fara harkan film wadda hakan nema yayi sanadiyar sanuwanta a fadin Nigeria da wasu kasashen
DAUKAKAR TA
Saratu gidado wadda kafi sani da daso Tasamu shahara a harkan film a cikin shekaru uku 3 bayan fara fim nata na farko mesuna linzami da wuta a shekarar alib dubu biyu 2000.
Jarumar tasamu daukaka sosai ganin yadda takeda kwazo da basira a cikin harkan fim. Hakan yasa haryanzu tana cigaba da gwagwarmaya a cinkin masana’antar ta kannywood.
karanta: CIKAKKEN TARIHIN UMAR M SHAREEF
FARA FILM
Gidado ta fara harkan fim na hausa ne tun a shekarar alib dubu biyu (2000).
Sannan Tafara yin film ne a cikin shirin linzamin da wuta Wanda sarauniya movie suka dauki nauayin shirin.
Daga bisani Kuma tayi sauran Fina finanta kaman su mashi, nagari. Kawo yanzu tayi film a masana’antar kannywood kimanin guda dari 100 Koma fiye da haka.
Hakan yasa jarumar ta shahara a cikin masana’antar ta kannywood domin Ana lissafata na daga Daya zuwa shida na manyan mata masu fitowa a iyaye cikin shiri.

JERIN FINA FINAI
Jaruma saratu gidado tafito a fina-finai da dama kamarsu
_Yar maiganye
_linzami da wuta
_Sansani
_Mashi
_Fil’azal
_Oga abuja
_Gidan iko
_Gidauniya
_Mazan baci
_Mazan fama
_Shelah
_Rintsin kauna
_Yammaci
_Uwar kudi
_Daham
_Gani gaka
_Sammeha
_IBRO ba sulhu
_Akwai mafita
_Ba tabbas
_there’s away
_Cudanya
_Gidan danja shiri Mai dogon zango
_wutar kara
Dadai sauransu
HADAKA
Sannan tafito tare da jarumai da dama a fina finai da dama a tarihin rayuwarta
Kamarsu
*Jarumi Adam A Zango
*Jarumi Alinuhu
*Marigayi Rabilu Musa ibro
*Jaruma Maryam Yahaya
*Jaruma Amal Umar
*Jarumi Musa me Sana,a
*Jarumi Rabiu rikadawa
*Jaruma jamila nagudu
*Jarumi Nuhu abdullahi
*Jarumi Sani danja
Da dai sauransu
Sannan daku iya ziyartarmu a shafinmu Na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin saratu gidado daso