Cikakken tarihin Zainab indomie
SUNA: Zainab abdullahi
INKIYA: Zainab indomie
SHEKARA: 17/May/1996
AURE: Babu
MATAKIN KARATU: Diploma
AIKI: Jarumar kannywood
GARI: Abuja
KASA: Nigeria

WACECE ZAINAB INDOMIE
Jaruma zainab abdullahi wadda akafi sani da Zainab indomie ta kasanke shahararriyar jaruma a masana,antar shirya fina finan hausa na kannywood dake arewacin Nigeria duk da cewa iyayenta sun kasance yan kasar Sudan ne.
Sannan Kuma tana daga cikin jaruman da suka samu daukaka cikin kankanin lokaci a masana’antar shirya fina-finan hausa kasancewarta kyakkyawa Wanda duk a cikin matan dake Masana’antar Babu wacce tafita kyau a lokacinda take tafiyar da nata zamanin cikin Masana’antar ta kannywood.
Karanta: Cikakken Tarihin Khadija Yobe ( Karima izzarso)
HAIHUWAR TA
An haifi zainab indomie a babban birnin Nigeria (Abuja) a shekarar alib 1996.
Amma iyayenta sun kasance yan kasar Sudan ne.
KARATUNTA
Jaruma Zainab indomie tayi karatunta na primary da secondary ne a garin abuja babban birnin Nigeria
sannan kuma tayi diploma a fannin kimiyan computer (computer science).
FARA FIM
Zainab abdullahi ko kuma Indomie ta fara film ne a masana’antar shirya fina finan hausa na kannywood tun a shekarar dubu biyu da takwas (2008) inda a cikin kankanin lokaci tayi suna Kuma ta samu daukaka a masana’antar ta kannywood.
Sannan Tafara film nata na farkon a wani fim mesuna Ali, daga bisani tayi garinmu da zafi, da wali-jam.
Dadai sauransu.
Bayan wani lokaci jaruma tadan dakata da fitowa a fim Wanda har izuwa yanzu ba’asan menene dalilin hakan ba.
Saidai Bayan shekaru kadan kafafen sada zumunta kamar su Facebook da Instagram da Twitter anyi tasamun labarai na karya wanda ake cewa jarumar zainab indomie ta rasu.

DAWOWARTA
Bayan kimanin shekaru biyar 5 da barin ta masana’antar fim na kannywood Jarumi Adam A Zango ya Kara baiyanarda ita a matsayin sarauniya a cikin wani vidiyon wakansa da yayi a kamfaninsa na (white hause family) Wanda hakanne yatabbatar da cewa Tana raye kawai bata fitowa a fina finan hausa ne na masana,antar kannywood.
karanta: CIKAKKEN TARIHIN NURA M INUWA
JERIN FINA FINAN TA
_Ga duhu ga haske
_Garinmu da zafi
_Ahalil kitab
_Yar agadaz
_Adon gari
_Bilal
_Fataken dare
_Zarar bunu
_Ina nan
_Zuri’a
_Somai sonka
_Raliya
_Sani nakeso
_Hadizalo
_Bana bakwai
_Kundin tsari
_Rai dai
_Romeo da jamila
Dadai sauransu.
HADAKA
kana jaruma Zainab indomi ta samu damar fitowa a fina finai tare da jarumai da dama
Kamarsu
*Jarumi Ali nuhu
*Jarumi Adam A Zango
*Jaruma saima Muhammed
*Jarumi Sani danja
*Jarumi Ahmed Ali nuhu
*Jarumi sultan abdulrazak
*Jaruma Nafisa abdullahi
*Jarumi Al,amin buhari
Dadai sauransu
Kana daku iya ziyartarmu a shafinmu na YouTube mesuna NW HAUSA TV dangane da cikakken tarihin Zainab indomie