DA KAMAR WUYA CHAPTER 1 BY ZULAIHATIDRISMISAU

DA KAMAR WUYA CHAPTER 1 BY ZULAIHATIDRISMISAU

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Hubby please kar ki ci masa abinci, kin san yau full day ne, ya kike so yayi, kinsan baya cin abincin kowa a school din nan.+

Harararta tayi ” ai dama haka nake so, kinga jikinsa zai gaya masa kenan. Zai ji anani burdade yau.

“amma dai kin san abinda kikeyi bakya kyautawa ko? Koba komai ai ke babbace, bai kamata ki dinga cin zalin yaron mutaneba don kinga kawai baya shiga saugarki.

“Kinga yusra ya isheki haka!!! Ke bakya ganin irin rashin mutuncin da yake min ne. A matsayina na yayarsa ban isa ya gaisheni ba, sai wani ji da kansa yake kamar baya kashi. Ai ko don junaid ya dinga girmamani.

“Wow!!! Hubby ki rage son girma, kin San halinsa ba kowa yake kulawa ba, me yasa zaki damu kanki?

Banza hubby tayi da ita, ta ci gaba da cin jollop rice din da tasha hadi, ga kifi nan Manya Manya, yamafi rice din yawa. ” dan banzan yaro, shiyasa kullun yake Kara kumatu. Dole yaki cin abincin jamaa, don shima kar aci nasa. Kin San kalar dadin abin cin nan? Ta fada tana gutsuran kifi, ko cokali bata bukata ba, don tunda taga abincin miyanta ya tsinke.

” kice dai yau kwadayinki ya motsa “

“Kema da kinsan kalan dadin abincin nan da baki ki ci ba. Dagaji girkin maman Aliyu ne, bana yan aiki bane. Dan Menan yaro yana wahalar min da innah.

“kyadai ji dashi, Allah yasa ya zo ya sameki, kina cinye masa abinci.

Dariya hubby tayi, da dai wani ne, ba wannan muskilin banzanba.

Ya kamata ki hakura haka, kija girmanki, kinga shi kwata kwata bakya gabansa.

Rufe curler din tayi, bayan ta cinye abincin tas, ko kwayar rice bata bari ba. Duk da ji da take cikinta kamar zai fashe, don koshi. Oya muje in wanke hannu Kafin a dawo class. Ta fada tana lashe hannu.

” naga ranar da zaki canza? Har yau halin yan kauye bai bar kiba. Yusra tace tana binta a baya.

” naga dai duk tsiyar mutun asalinsa kauye ne. Ke barima kiji, ni wallahi da zaa Mai Dani kauyen dana fi farin ciki. Inda zan sakata in wala, in tsula tsiyata yadda nakeso. Nayi missing kakus fiye da zatonki.

Har yajin aikin cin abinci nayi,  amma mutanen nan, ko a jikinsu. Sai da naga haza, in na mutu basu da asara  tunda bani kadai suka Haifa ba. Yasa na dawo aikin cin abinci. Don lokacin har na fara ganin kamar kowa ma farin kaya yasa a jikinsa. Kin ga alamar mutuwa ta matso kenan..1

Dariya yusra keyi harda rike ciki. ” ke din ce zaki iya wani yajin cin abinci?  Azumi ma da yaya kike kaiwa, balle ba’a azumi? 

Suna fita class din, su kuma suna shigowa. 

Wani hadadden matashi na gani, Wanda bazai wuce shekara sha biyar, zuwa sha shida ba, yana sanye da kayan kwallo na kamfanin NIKE farare,  kafarsa na sanye da farin canvas shima na kamfanin NIKE da farar safa. Fari ne sosai, yanada tsayi,  bayi da jiki. Amma da gani za’ayi hadadden guy mai kyan jiki,  da kira.

Kyakyawane na bugawa a jarida. Fiskarsa doguwa,  Mai dauke da dogon hanci,, ma-dai -dai tan ido,  masu matukar haske, sai Dan madai daicin baki , mai dauke da jerarrun hakora,  farare tas,  gasu sunada tsayi kwanin sha’awa. Yanada dimple both side din fiskarsa. Gashinsa bakine sidik, mai matukar laushi. Wanda yasha gyara. Yanada gashin gira baki Mai yalwa, ga baki, gashin idonsa kamar anyi piecing din su.

Shine a gaba, sai sauran tawagar student din. Ko wanne da kayan kwallo a jikinsa, duk sun hada zufa. Alamar daga field suke.

“Anty -Anty Allah ya bar mana Anty. Wasu daga cikinsu suka fara fada ganin hubby da ke fitowa a class din.

Hararar na gaban tayi,  Kafin ta wuce abinta,  yusra na binta a baya. Ko kallon inda take baiyi ba ya wuce locker dinsa.

Kayansa ya gani a bar baje, da sauri ya karasa wurin.  Da food placks dinsa ya fara cin Karo. Ganin ba komai a ciki,  yasashi mai da hankalinsa kan kayansa. A can gefe ya hango rigar uniform dinsa. Daukowa yayi. Dubawar da zai yi duk shatin mai da alamar da rigar aka goge hannu,  bayan an cinye masa abinci.

Wani bakin ciki da takaicine ya lullubeshi. Don yasan duk fadin school dinnan. Habiba (hubby) ya rasa mai ya tsare mata a rayuwa, ta takura masa. Shi ba shiga harkarta yake yi ba, duk da tana yar uwarsa. Zai iya cewa jinin sa bai hadu da nata ba. Shiyasa ko kallo bata ishe shiba. Don shi haka yake,  in ransa baya son mutun no matter how close they are. Ba ruwansa dashi. In ka girmeshi dai zai gaishe ka,  amma banda gaisuwa ba zai taba yadda wani Abu ya hada ku ba.

Ita din yayar sa ce, a kalla ta bashe good 6year’s,  but amma yanayin childish behavior dinta yasa ko kallonta baya son yi. Don ba karamin haushi take bashi ba.

Kafadar sa da aka dafa,  yasa shi waigowa.  Daya daga cikin student din ne, ” I’m very sorry broth ” ya fada da yanayin damuwa a fuskarsa.

Murmushi ya kago ” never mind, it’s OK ” ya fada, tare da tattara kayansa.

Wanda ya dafa shin ne ya miko masa shirt ” take this. I were the one she spoil”

” no I will manage.

Zama yayi kan sit dinsa. Food Plack’s student din ya ajiye akan table din,  tare da Jan yo kujera ya zauna.

” please haydar kar kace min bazakaci abincin nan ba.

Murmushi Wanda aka Kira da haydar yayi.  Junaid you know me very well, I’m not eat that food.

” so what do you eat?

Jakarsa ya dauko ya fito da dairy milk, Wanda ya tabbatar bata gan shiba da bai tsira ba. Ya fara ci. I will manage with this.

Girgiza Kai junaid yayi,  yana jinjina halin abokinshi kuma Dan uwansa, A ransa.

Duk yadda junaid ke jin yinwa, ganin Dan uwansa bai ci komai ba, yasa shima kasa cin nashi abincin.  “Have some” haydar ya fada yana Mika mishi chocolate din.

Tsaki junaid yayi,  tare da hararar chocolate din. ” amma kasan you have a problem ko?

Murmushi yayi,  ya ci gaba da shan chocolate din shi.

Ransa ba dadi, har aka tashi daga school.

             *******************

Alhaji yusuf zubair Oregon. shine asalin sunan kakansu.  Dan a salin kasar Lebanon (Lebanese ) middle East. Wanda take boda da Syria, Israel da kuma Cyprus.

Aiki ya kawo yusuf garin kaduna. Wanda Allah ya kaddara zamansa a nan. Matarsa Hajiya Aisha Aliko. Haifaffiyar garin kaduna ( malali) sai yaransu uku: jamal,  jamil, omer.

Mutun ne na mutane. Yanada arziki dai dai misali.  Bayan ajiye aikinsa ya koma harkar restaurant Wanda dama tun yana aiki ya Fara bude su.

Kammala karatun Jamal na degree, yasa shima ya fan tsama sanaar mahaifin nasa.

A yanzu Alhaji jamal nada matan aure uku, : Hajiya Hadiza mai yara biyar.  Ummu kulsum, ummu Aiman,  ummu sulaim, ummul khair,  sai auta Aliyu haydar.  Sai Hajiya Amina mai yara uku : samirah, Ahmad, Abdulkharim . Sai Hajiya saadatu Mai yara biyar : yusuf,  Abdul majid,  Abida,  Aisha,  Airah.

Alhaji Jamal yanada arzkiki sosai, shine mamallakin gidajen abinci,  da ake ji dasu a jahohin Nigeria,  wato eat more restaurant.

Mutun ne mai son addini,  Wanda yakewa addini hidima da dukiyarsa, da karfinsa. Ya na son jamaa. Mutun ne mai jin kan iyaye, da kula da hakkokinsu,  mutun ne jajirtacce adali mai kyautatawa iyalansa. Sai dai fa in ka tabosa akwai fada 😎 akwai doka da oder sosai a rayuwar gidansa.

Alhaji jamil maaikacin currant affairs dake Abuja. Rikakken dan boko,  amma Wanda aka surka da ilmin addini 😊 yanada arziki dai dai misali. Yanada mata daya Hajiya maryam, da yara hudu : Aslam, Aaryan, Aashir,  Abdul Alim. Rayuwar gidansa rayuwace ta wayewa. Amma ba wadda ta kauce sharia ba.

Alhaji jamil nada kirki kamar Dan uwansa.

Sai Alhaji omer business tycoon.  Mazaunin Lego’s duk ya fisu dukiya.

Yana da mata biyu Hajiya Zuwaira da yara hudu: Aisha (nana) Asima, Asiya, Asnah. Sai hajiya Bilkisu mai yara uku : Arif (omer), Abdul fatta, Abdul Hafiz. Mommy Hauwa kanwace a wurin Hajiya Hadiza. Su biyu iyayensu suka Haifa, suna kanana Allah ya yi musu rasuwa.  Sun taso a hannun kanin babansu, Malan tsalha. sun samu tarbiyya  dai dai kwarkwado, da ilmi na addini dana boko. Duk da kalubalen da suka samu da maidakin nasa umma larai.+

Bayan auren Hadiza da yan watannin ta dauke kanwarta,  ta ci gaba da kula da ita. Anan Allah ya hada Hauwa da Munir, abokin omer ne tare sukayi karatu a malesia. Shi dan ainihin katsina ne,  cikin kankiya local government. Yana zuwa Hutu kaduna wurin yayyen mahaifinsa da ke nan kaduna. Kasan cewarsa aboki na kut da kut ga omer,  yasa kowa ya sanshi a family din.

Ummu Habiba ita ce yarinyarsu ta farko,  sai jabir, jafar sai junaid Wanda yake sa an Aliyu.

Ummu habiba ta taso wurin kakarta,  wadda ta dauketa a nono. So ko bayan ta isa makaranta gwaggo kin dawo da ita tayi. Munir shi kadai suka Haifa,  daga kansa basu sake haihuwa ba. Wannan yasa ta ki mayar musu da habiba.

Rayuwar habiba a kankiya,  rayuwa ce ta ba sawa ba hanawa,  abinda take so shi gwaggo ke mata,  don ma Alhaji kawu na taka musu birki, in yaga abun yayi yawa.

Rashin kunya,  tsokanar fada,  Rashid son karatu,  kazanta, duk halin habiba ne. Batajin magana ko kadan,  ga dan banzan barna.

Tanada shekara goma,  amma har lokacin ajinta uku,  a primary school duk da kyan makarantar,  amma rashin maida hankali a karatu yasa ake mata repeating.

Ko kadan bata kaunar zuwa kaduna wurin iyayenta Hutu. A cewarta sun cika takura. Ganin haka gwaggo tace ba mai takura mata, tunda batason zuwa a gyaleta.

Wannan halayya na habiba na cin ran iyayenta. Musamman ta bangaren karatu. Habiba Nada shekara sha hudu sai lokacin ta gama primary school duk abokanta suna ss 1,  wasu na js3.

Ganin haka ya sa Alhaji kawu budewa gwaggo wuta, kan ta mayar da habiba, GA iyayenta, don ya Lura in ya ci gaba da zuba ido abun ba zaiyi kyau ba. Don habiba bata son Karatu ko kadan,  Sai tayi sati bataje school ba. Shi kuma ba mazaunin gida ba,  in ya fita Sai yamma can,  koma dare.

Da kansa ya dauki waya ya Kira Munir,  yazo ya dauki yarsa. Da kuka da birgima haka suka nufo kaduna. Suka bar gwaggo cikin matsar hawaye. Don ba kadan ba take son habiba. Har ciwo tayi na rashinta.

Lokacin jabir da jafar  sunyi exams din jsce.  Junaid na js1.  Dakyar suka samu aka dauketa a js1 saboda ko spelling mai kyau bata iya ba,  bata iya karatun Hausa ba ma balle English.  Sun amsheta da sharadin zaa nema mata lesson teacher. 

Aji daya aka sata da su junaid da Aliyu.

Son girma, mu samman da taga duk ajin ta fisu shekaru, duk da bata da girman jiki. Wannan yasa duk ta fitini kowa, musamman in zaka ganta kaki gaishta,  ko ta kamaka kana mata dariya,  in an tambayeta amsa bata sani ba,  To ka shiga uku. Kusan ko yaushe a cikin fada take,  ba maza ba mata. Dole yasa suke ce mata anty don gudun jarabarta.

Duk wannan abun da takeyi ko kallo bata ishi Aliyu ba, so da yawa har desk dinsa zata zo, ta duddungure shi,  tana masifa,  ko daga kansa bazai yi ba balle yasan tanayi. Wannan shi yake Kara bakanta mata rai,  baya ko kallonta,  balle ya gaisheta kamar yanda yan ajin keyi,  ko anty din ma bata samu arzikin sa ba.

Ko a gida suka hadu,  shi yazo ko ita taje, Ba ruwansa da ita. Tasha Kai kararsa wurin mommy da Haj amma ba abunda ya canza.

Wannan shi yasa tadau damarar yi masa rashin mutunci,. Tun daga lokacin ta maida rayuwarsa living he’ll..

Sai dai abinda ke Kara bata haushi har yanzun nan da suke Shirye shiryen zana final exams dinsu, bai taba tanka duk abinda zatayi masa ba. Wanda ita ba haka ta so ba.

Aliyu najin zafin abinda take masa,  amma kullun maganar Haj in ya gaya mata, shine yayi hakuri,  ya rabu da ita, in ta gaji zata daina abinda take masa. Kuma yar uwarsa ce bai kamata ya biye mata suna fada ba. Duk da ta zubar da girmanta to shi ya dauki girman yayi hakuri.

             *********************

School bus dinsu na shigowa, bai tsaya baba ya Gama ko parking ba, ya Saba jakarsa ya balle murfin motar ya fito. Da kallo baba da sauran kannen nasa suka bishi.

“Shida mutuniyar ne ko?” baba ya tambayi su abida.

” kai ma kasan Sai ita,  don yaya bashi da abokin fada. Aisha ta ce tana Saba Jakarta.

“kai wannan yarinya,  Allah ya yi fitinanniya. Baba ya fada

Da Yaya Ahmad sukaci Karo,  yana fitowa. “Sweet broth well come “

” thanks ” ya fada yana kokarin wucewa ciki,  ba tare da ya Kalli yayan nasa ba.

” what happened to you?  Ahmad ya fada yana juyo dashi. Ganin yadda yake faman huci,  yasan ran kanin nasa a bace yake.

” I’m sick and tired of that useless girl, I have to teach her a big lesson of her life.

Murmushi Ahmad ya yi,  don yasan yau ma an kuma. ” me kuma tayi yau?

” she finish my food,  don wulakanci a jikin uniform dinsa ta goge filthy hands dinta.

Dariya Ahmad yayi, ” lallai wannan yayar taku,  bata kyauta ba.

” Ba yayata ba. Allah ya kiyaye inyi yaya da wannan good for nothing din.

” don’t say that.  Ni na rasa gane meye yake hadaku, ko kana mata wani Abu ne da bata so?

” me zan mata,  yarinyar da ko kamarta,  bazan iya tan tan cewa ba. Daga yanzu na daina kyaleta, zan gwada mata nawa rashin mutuncin. Dama hajiya ke cewa inyi hakuri, da tuni nayi maganinta.

” Aa Aliyu, ko Ba komai taci albarkacin mommy da junaid.  Zan sameta zamuyi magana.

Zuwan su Aisha yasa suka katse zancen,  ya shige part dinsu,  yabar Ahmad suna gaisawa da su Aisha.

A falo ya samu hajiya da mmn samira.  Suna duba wasu lessis da aka kawo na siyarwa.

Gaishesu yayi,  ya wuce dakinsa.  Mmn samira ta Kalli hajiya, yaya yau mutumin naki,  a sama yake.  Tabe baki hajiya tayi ” nasan baya wuce shida habiba,  na rasa me yasa basa iya zama inuwa daya. ita son girma,  shi kuma kinsan halinsa sarai.

Murmushi mmn samira tayi ” lamarin Aliyu sai shi. Na dauka yana girma abun na raguwa,  amma kullun gaba yake karawa.

” kedai bari,  nayi fadan,  nayi dukan duk a banza. Addua nake masa Allah ya yaye masa wannan halayya.

Fitowa yayi, ya wuce main kitchen. A nan ya tarar da mmn yusuf na kokarin daura abincin dare.

Gaisheta yayi cike da girmamawa.  Murmushi tayi ” haydar an dawo? 

“Eh ” ya fada yana bude fridge.

” ga abincinka nan,  yanzu nayi worming. Tana nuna masa microwave.

” thanks,  you are the best.  Ya fada bayan ya dauko bottle water da maltina.

Bude microwave din yayi ya fito da plate din.  Murmushi yayi saboda favorite dinsa da ya gani.

” Wow!!!!  Na gode sosai, kamar kinsan yunwa sosai nakeji, ina bukatar favorite,  don inji dadin ci.

Murmushi tayi. Shigowar hajiya ya sa ya dauki plate dinsa yayi gaba, da harara ta rakashi.  Kafin ta maida kallonta zuwa ga mmn yusuf da ta ci gaba da aikinta,  ba tare da tako Kalli hajiyar ba.

Tsaki taja, ta wuce fridge ta dauki abunda zata dauka ta fita……….Falon da yake mallakin yaran gidan ya nufa. Su Anty khulsum ya samu a folon suna kallon series a Tashar zee would. Sallama yayi, ya wuce dinning ba tare da yace musu komai ba. Suma bayan amsa sallamar da kallo suka bishi, har ya zauna a kan kujerar dinning din,  ya fara cin abincinsa.+

“Muskili kafi mahaukaci ban haushi, wannan dashi aka fara haifa a gidan nan da mun bani” cewar Anty Aiman.

“da gani yauma wani ya taboshi” sulaim ta fada idonta a kansa.  ” brother ba gaisuwa?

Kamar bazai amsa ba,  da dago ya kalleta ” nayi sallama ” yace a takaice yaci gaba da cin abincinsa.

” munsan da kayi sallama, amma ka gaishe mu ko? Anty khulsum ta ce tana harararsa.

Abincinsa ya ci gaba daci, ko dago Kai bai yi ba,  balle tasa ran zai amsata.

Khair ce tace ” haba haydar ba dakai ake magana ba,  kayi mata banza.

Harararta yayi, don duk cikin yayyen nasa yafi rainata, saboda shi yake binta.  ” sallama itace wajibi kuma nayi.  Ya fada

Tsaki tayi Allah ya yaye maka mugun hali,  wata rana ayi abun arziki dakai wata rana iskancinka yafi na tsohuwar mota.  Khair ta fada tana harararsa, wanda bai ma San tanayi ba.

” naga dai mmn yusuf aiki take a kitchen, ne makon kuje ku tayata, kunzo kuna kallon abinda bazai anfane kuba ”  ya fada yana kallon su

” Zanci gidanku kam yanzu,  mu Kake gayawa muje muyi aiki a kitchen?  Anty khulsum ta fada cikin fada da jin haushinsa.

” zo ka kwashemu ka kaimu,  Dan ban zan yaro, Mara kishin uwarsa. Sulaim ta fada

Bakin shi ya tabe, tare da daukan plet dinsa yayi waje.

“Allah yaron nan sai hajiya ta tashi tsaye a kansa, in ba hakaba wata rana cewa zai Ba ita ta haifeshi ba.  Khairi ta ce

Anty Aiman tayi murmushi “lamarin haydar sai a hankali, tunda kunsan halinsa, meye na tada jijiyar wuya, wani irin fada ne hajiya batayi ba,? amma me ya canza?  So ku Dena bata bakinku a banza.

Sallamar su Abida, ya katse maganar da sukeyi.

           ********************

Hajiya hadiza (hajiya) uwar gida a gidan Alhaji Jamal. Auren hadi aka musu da ita. Mahaifiyarsa ta zabo masa ita, kasan cewarsa mai biyayya ya amsa da hannu biyu.

Matace mai kirki dason jamaa,  but akwai son iko, da nuna isa.  Bayan aurensu da she kara biyar,  ya auro Hajiya Amina itanma kusan zamu iya cewa hadine yar aminin babansa ce.  Mata mai hakuri,  da biyayya. Duk iya abunka baka taba ganin bacin ranta.  Haihuwarta daya ya auro Hajiya saadatu itan ma hadi ne, kanwar abokinsa ce dake Niger.  Akwai kirki, sai dai bata daukar raini.

Hajiya hadiza da Hajiya Amina kansu a hade yake, koda Hajiya saa tazo, sai ta zama wararriya a cikinsu.  Ba shiri ko kadan tsakaninta da uwargidan. In kaji fada ya tashi, ko ana sulhu to tsakanin hadiza da saa ne. Don ita Amina bata da abokin fada a tsakanin su.

Tun tasowar haydar Allah ya hada jininsa Dana Hajia saa, yana sonta. Haka favorite brother dinsa yusuf, yaronta na farko,  suna matukar shiri.

Wannan Abu na matukar bata ma hajiya rai,  tayi fada har duka amma ba abunda ya canza.  Musamman ganin duk yadda take da Hajiya Amina amma haydar gaisuwa ne kawai ke hadashi da ita. Duk da kirkinta mu samman akan shi.

                ******************

Still hajiya da mmn samira ya samu, a falon hajiyar.  Dakin sa ya wuce ba tare da ya ce musu komai ba,  bayan sallamar da yayi.

Suma gaba daya hankaalinsu nakan kayan da suka zaba, don bikinsu anty khulsum ya matso.

” to yanzu zamu kirata ta duba ne ko ya zaayi?  Mmn samira ta tambaya.  Hararar mmn yusuf tayi ” kin jiki da maganar banza, kedai ba kin zabi naki ba?  Sauran da suka rage,  zan aika mata, ya rage nata kuma.

” bakya gudun tace bata so,  har maganar taje kunnen Alhaji?  Kin san abun bazai yi kyau ba.

” ke dai wallahi anyi matsoraciya, mai jiya tayi balle yau?  Naga mune gaba da ita a gidan nan.

” haka ne, amma kin san bata raina abin fada. Kuma ya kamata in ma zamu Fara zaba, mu zaba a gabanta. “

Tsaki hajiya tayi, tare da harararta” an dai ji haushi,  kwashe sauran kayan in kin kai ta zaba sai ki dauki sauran.”  Aliyu ta kwalawa Kira.

Fitowa yayi bayan ya amsa, fuskarsa Ba faraa, don yana jin duk abinda suke cewa, ya rasa wannan kishi dake damun hajiya. Abu yaki karewa tun kuruciya,  gashi har an Fara manyanta. Amma kullun sabon rigima suke bullowa dashi.

Ganin yanayin fuskarsa yasa ta harareshi,  ” kwashe kayan nan ka kaimin daki “. Ta nuna masa kayan da ta zaba. Kallonta yayi yana son yayi magana,  amma baiga fuska ba.

” zaka dauka ka wuce, ko sai naci gidanku,  a wurin nan ” ta fada tana ci gaba da harararsa.

Dauka yayi ya wuce dakinta dake kallon nasa.

” kinga kwashe kayan nan, kiyi gaba” ta fada tana gyara zamanta

Murmushi mmn samira tayi ” me yayi zafi, shi ba wuta ba “

” ai kece kina bani haushi wani lokaci”

” Aliyu dauki kayan nan ka kaiwa mmn yusuf” mmn samira ta fada tana nuna masa kayan da suka rage a gefe.

Ranshi bai so ba, ya dauka ya fita.

Can Sai gashi da kayan,  ” tace bata so, ku hada duka” ya fada yana ajiye kayan inda ya dauka.

Mmn samira ce ta Kalli hajiya ” kinga dama abinda nake fada ko?

Murmushi hajiya tayi ” wannan kuma ya rage nata, kaya dai dole ta amsa,  in bataso Sai ta bari, in wanda ya ajiyeta ya dawo, ta mayar masa, don ni kam na riga na zabi nawa”

Kayan ta zuba a Leda, ta fita zuwa kitchen.

Har lokacin mmn yusuf na ta kokarin hada abinci, don hajiya ta aiki Mai tayata aikin, duk don ta kun tata mata,. Su abida da ke taimakonta yau basu dawo school da wuri ba,  gashi kuma kowacce ta dawo da home work. So dole ita kadai take aikin, don tasan ko zata mutu su khulsum bazasu tayata ba, saboda suna taya uwarsu kishi,. Sannan don kuturun wulakanci Alhaji ya aiko da kaya amma bazasu kira ta ba, sai sun gama zaba sannan don sun rainata su aiko mata da abinda sukaga dama.

” to sababbiya, gashi nan in Wanda ya aiko da kayan ya dawo ki mayar masa, don nikam bazan ajiyesu wurina ba. ” hajiya ta fada tana jefa mata ledar can gefe.

zuciyar mmn yusuf ne ya fara tafasa, ba don komai ba sai jifo kayan da hajiya tayi. Cikin bacin rai ta juyo tana kallonta. ” Allah sarki duk inda akayi da jaki, sai yaci Kara, kin dai san gidan da na fito?  Ke kaya ya dama, da har kike wani takama akai,  ki hada da naki ki rike, banso, kin San zan iya siyan dubunsu in har naso, ke kike fatarar kaya. ” tayi tsaki ta juya don ci gaba da aikinta.

” kam bala’i, ni kike gayawa wannan maganar, dadin abun mun san komai, balle a mana fiffika, gidanku yafi gidan mune?  Da har kike wani ikirarin ansan gidan da kika fito?  Muko muka san gidan da kika fito. Dadin abun da gidan uba ake tinkaho,  Ba gidan yaya ba. Kaya kuwa in kinga dama ki zubar a bola, bai daman ba. Dole inyi tinkaho da kayan mijina, ba Wanda zan siya da kudin da nayiwa yayana yar murya ba.  Banza karya tseeeee!!!!!!!

” ni kike kira karyar?!!!!!!  Mmn yusuf ta fada tana nuna kirjinta, cike da bacin rai

Dariya hajiya tayi, “au!!!! Da kin dauka da WA nake??

” kun kyauta, nawa tukuicin kenan, ina can ina Nemo muku abinda zakuci kuna nan kuna tona min asiri” Alhaji Jamal da ya shigo tun fara hayaniyar tasu,  ya tsaya yana jin duk abinda suke yi ya fada cikin tsananin bacin rai.

Juyowa sukayi a tare jin muryar mijin nasu………….sannu da zuwa” hajiya ta fada cikin rawar murya, ganin yadda ransa ke bace.+

Harararta yayi,  yayi tsaki ya wuce part dinsa. Itama tsakin tayi ta koma falonta.

Mmn yusuf ta ci gaba da aikinta, cikin bakin ciki, da bacin rai. Don bata so abin ya tsaya a haka ba 😎 duk da tasan magana bata mutu ba.

                *****************

Zaune suke a falon Mai gidan, bayan sun kammala cin abinci. Yau gaba daya cin abincin ba armashi, don ran Mai gidan a bace yake dasu.

” dauko min fruit salad din da nace ki hada min” ya fada yana kallon mmn yusuf.

Shiru tayi kamar baza tayi magana ba ” bari in je in hada. Yau aiki yamin yawa shiyasa ban samu yi ba.

” ban gane aiki ya miki yawa ba?  Duk yaran dake gidan nan? ” ya fada yana kallon ta

” hajiya ta aiki ladi, su abida yau basu dawo da wuri ba, already kowacce ta dawo da home work, so I have to do it by myself “

Kai ya kada cike da bacin rai. Su kam hajiya da mmn samira ba wadda ta tofa nata suka ci gaba da kallon news.

Har ta kusa fita dakin, yace ta dawo ta zauna.  TV ya kashe tare da gyara zamansa, ganin haka, yasa kowacce shiga cikin natsuwarta.

Hajiya ya kalla ” meye maanar abinda nazo na samu kunayi dazu?

Kallonta takai kan mmn yusuf dake zaune can gefen Alhaji. Itama kallonta take yi, harara suka aikawa juna.

“dake nake ” ya fada cikin daga murya

” kayan da ka aiko mana ne, na aika mata da nata,  ta dawo min dashi wai bata so. Shine na dauka na bita dashi kitchen.”

Tayi shiru ” sannan sai akayi me? ” ya tambaya.

” magan ganu ta fara gaya min ni kuma naga bazan iya yin shiruba na Meyer mata.

Juyawa yayi wurin mmn yusuf ” me yasa kika maida kayan bayan an kawo miki “

” da aka kawo kayan, in da sun shirya gaskiya ai nima sai su kirani mu zaba a tare, in ma su zasu fara zaba, bazan damu ba. Amma basu kirani ba saida Suka gama abinda zasuyi suka aiko min da saura, bayan sun zabe, shiyasa nace ya mayar musu banso, su hada duka. “

” ke Amina ya akayi? Ya juya yana kallonta. Shiru tayi ta rasa abun cewa, don ta tsani tashin hankali a rayuwarta. Da hajiya taji shawararta da duk haka bata faru ba.

” kun kyauta. Amma ku sani bazan dauki wannan halin banzan ba,  na gaji da matsalarku, kun girma amma kullun abinku karuwa yake.  Yaran ku ake kokarin aurar wa, wannan shine tarbiyyar da zaku basu su dinga yi a gidan mazajensu?

Ku dubeni da kyau son kowa kin wadda ta rasa, kyau, kudi, Hali mai kyau. San kacecen mutun Irina 😂 na kwasoku don in rufa muku asiri, ni kuke kokarin tona min nawa ko?  To kuji da kyau duk randa irin haka ta Kara faruwa, gaba dayanku Sai kun bar min gidana. Don duk cikinku ba wadda naje na makale a soron gidansu don neman soyayyarta. Balle ta zame min matsala a gida.1

Hajiya ce cikin bacin rai tace “kai kullun Abu ya faru Sai ka mana gori?  Naga ba masoya muka rasa ba, muma ai mun rufa maka asiri”

” ja can ki rufe min baki. Duk samarin naku sun Kama kafata ne?  Shi yasa kuna ganina duk kuka rude, kunga hadadden yaro. Da nasan in na taimake ku abin da zakumin a gida ke nan da ban kwaso ku ba.  Mu samman ke da wannan yana nuna saa kunfi kowa matsala.1

Kuje ku kwaso kayan ku kawo min. Ina duk akan rabo ne fadan?  To zan raba da kaina. Tunda ni zaawa kwalliyar ko wacce nasan Wanda zai dace da ita.”

Dole kowacce taje ta dauko ta kawo masa.  Rabawa yayi da kansa ya dauka ya mikawa kowacce.

” ku Ba kyau ba, Sai Dan banzan fitina, 😂 dole ne yanzu nima in kwas kware in Nemo sweet sixteen zabin zuciyata, ko na more, sauran kuruciyata.

Duk kansu hararar sa sukayi, in da sabo sun Saba da halin mijin nasu. Duk ranar da suka bata masa rai, sun shiga uku da gori.

” Ai wallahi kai kanka kasan duk cikin mu ba mummuna, Kai din ma banda fari mai zaka nuna mana” mmn yusuf ta fada tana tura baki kamar wata karamar yarinya.

Dariya yayi ganin yadda suka Shaka, ko wacce ta cika tayi fam, banda mmn samira dake murmushi kasa kasa.

” ke kam in ana magana, be kamata kisa baki ba, ki bar Amina tayi magana, duk da ita din ma in muna wuri, bata isa zuwa ba. Ku Bari ku ga zankada ziyyar da zan kawo muku. Tattaro min kan yarana “

Ya fada yana kallonsu.

” Allah ya kawo ta lafiya,  ta makara tunda ka zama saura, sai dai ta samu sidi. ” hajiya ta fada cikin jin haushi

Murmushi yayi ya tashi yana Dan jujjuyawa a gabansu ” waya gaya miki na miji na tsufa?  Don baki san yanda yan mata keta kawo min Hari bane, Yanda kuka San zasu lashe muku ni. 😝 ba komai, zan nuna muku har yanzu irin mu ake yayi.

Sallamar yaran nasu sukayi, suka basu izinin shigowa.

Sun gaishe da iyayen nasu, suka nemi wuri suka zauna. Kallon yaran yayi cike da jin dadi, da alfahari ” Masha Allah LA kuwwata Illa billah” ya ambata Kamar yadda ya Saba in ya gansu haka a hade.

Kallonsu yayi ya nuna khulsum ” meye cikakken sunan ki?  Kallonsa tayi cikin rashin fahimta.

” ina nufin da wane suna kike bearing “

“ummu khulsum jamal yusuf “

Kai ya kada, haka ya dinga tambayar sauran ma kowa na fada masa. Bayan sun Gama ya ce ” waye Jamal yusuf zubair Oregon? “

Aaira ce tayi saurin cewa ” kai ne mana daddy “

Murmushi yayi, ya daurata kan cinyarsa ” yau wa autan kaji”

Kallon sauran yaran da suke sauraron abinda zai ce, don duk sun shiga rudani.

“kun yarda nine dai daya ubanku ko?  Amsawa sukayi da “eh !! “

” fine!!!  Na lura da wasu abubuwa dake faruwa a gidan nan, da zuciyata bazata laminta ba. Ni ne dai daya mahaifinku duka, kuk kanku daga tsatsona kuka fito,  kunga kenan Baku da ban banci, Ba nason halin yan ubanci da kuke son tsiro dashi, so nake naga kun hada kanku, ku so junanku don Allah, ku zama tsinstiya madaurinki daya, ku zama sirrin juna. Masu taimakon juna, da jin kan juna,  wannan shi nake bukata a cikin gidan nan.

Ya juya wurin su hajiya ” a matsayinku na iyayensu mata, zan so ku hada kawu nan ku, ku so juna don Allah, ku zama masu taimakon juna, da son ci gaban juna, babu bakin ciki, ba kyashi.  hadi kan ku shi zai tai maka wurin hadin kan yara na. Amma ku sani, muddin na ci gaba da ganin baraka a kan yarana.  Wallahi duk sai kun tafi gidajenku.

Magana ta gaskiya kenan, bazan lamunce, ku raba min kan yara ba, zan gwammace in rabu daku, in Nemo waanda zasu kulamin dasu.

Ban yadda yarana su raina daya daga cikin ku ba, wai don ba ita ta haifeshi ba, dole su girmamaku kamar yadda zasu girmama mahaifiyarsu. In har kuna son zama lafiya a gidan nan.

Yan mata na, dole ne ku Saba musu da shiga kitchen, in dai suna da free time. Ba ban banci da wadda take girki a lokacin.

Sannan daga yanzu har sati biyu Kafin bikin su khulsum, su zasu dinga girki a gidan nan. Kafin lokacin ko wacce ta samo Mai tayata aiki, ranar girkinta. Case close “

In akwai Mai magana yana iya yi?

Ya tambaya yana binsu da kallo.

Duk jikinsu a sanyaye,  kowa yayi shiru.

” OK kuna iya tafiya, ku kuma mazan ina da word daku “

Fita su khulsum sukayi, bayan sunma iyayen sai da safe.

Kallon shi yakai kan yusuf  ” yah!!!  Ka gama shawarar? “

Kai yusuf ya sun kuyar cikin jin kunya. A hankali ya kada kai tare da cewa ” eh!!! Daddy “

” good kana nan akan bakan ka ko ka canza shawara?

” aa “

“ka tabbata kana sonta, itama tana sonka? Kun dai dai ta? “

“eh!! Daddy ” ya fada cikin jin kunya.

Su hajiya da basu San kan zancen Ba, shiru sukayi suna sauraro.

” Masha Allah.  Wannan Abu yayi min dadi, Allah ya sa albarka a ciki. “

Amin sukace gaba daya.

” wai zancen me Kake yi ne?  Kun samu a duhu? ” hajiya ta tambaya

Murmushi daddy yayi ” maganar yusuf da yar wurin Hauwa, habiba.”

” wace habiban?  Mmn yusuf ta fada tana zaro ido.

” habiba dai daya da kika sani, yara sun hada kansu, tunda Ahmad ma ya fito da tashi, gara a hada gaba daya da nasu khulsum.2

“Tabdijam !!!!! Wallahi bazata sabu ba……… 😮😬

Har yaushe suka hada kan nasu, bamu da labari? Wannan Abu ba mai yiwuwa bane, garama tun wuri kar a farashi+

Daddy ne ya zabga musu harara ” ku kuma asu wa? Da sai da amincewar ku sannan zan zartar da hukunci? To Bari kuji da kyau gida nane, yaya nane ba wadda ta isa ta kawo min matsala a abinda yake ba sabo bane, sunnar manxo S. A. W za a hada, kuke kokarin tada jijiyar wuya? To ku sani nafi kowa murnar wannan aure, ko ba komai ya zama ishara gareku in kuna da hankali. Ku tashi ku bani wuri, ya rage naku ku fara shiri, ko karku fara, ba abunda zaa fasa. “

Samarin ne suka fara yin waje,. Mmn yusuf ta ce ” gaskiya da sake. Bayan kasan da maganar hanifa (yar wanta) amma zaka yadda da wannan hadin gwarman “?

Tsaki ya ja ” matsalana daku rashin tunanin. Ita hanifan da kike magana a kai shi yace miki yana sonta? Hadinki ne, kuma dama na gaya miki ba auren hadi, ko dole a yarana, Wanda suke so zan basu, matukar ba illah a ciki.

Hajiya da ta cika tayi fam, don fushi, hararar mmn yusuf tayi tare da ficewa a dakin cikin fushi. Itama mmn samira sallama ta musu tabi bayan hajiya.

” tsakani da Allah, ba a min adalci ba, yanzu mai Kake son in gayawa yayah? “

Cikin rashin damuwa da zancen nata ya ce ” komai ma, kina iya fada masa “

Ganin yadda ya hade rai Ba wasa a tattare Dashi yasa ta tashi ta wuce dakin baccinsa….

********************

“Yan zu yayah zero head din nan zaka kwaso mana ? Haidar ya fada bayan sun iso farfajiyar gidan

Dariya yusuf Da Ahmad SuKa yi ,” yayar taka Kake Kira zero head ” Ahmad ya fada yana dukansa a kafada

” zero head ce mana, ban san ya akayi PC ya yadda ta zana waec ba. “

“karka sake kiran wify Na zero head, she is your sister and sister in-law, so respect her for that ” yusuf ya fada yana murmushi

“ok, but ka sani bani a yan zuwa gidanka, Kafin nan ma I will teach her a lesson from tomorrow so that kar rainin yayi yawa Bayan ta shigo”

” haba brother, don’t say that, your my best, how can you be not coming to my house? ” Ahmad ya fada yana dafa kafadar haydar

” sorry I can’t help it ” haydar ya fada

Ahmad yayi dariya “wow Yau Na ganku a rana, but kanaji fa yana cewa zai koya mata hankali? But u not bothering to ask him. U know him very well “

Yusuf ya Kalli Ahmad sannan yakai kallonsa kan haydar ” what are u planning “?

” hankali zan dan koya mata kadan, my be kafi jin dadin zama da ita”

” aa haydar live my wife alone “

” your wife? What about me? Kasan kalan rashin mutuncin da take tatamin? Wane mataki ka dauka da nake kawo maka karanta? Kalli idona yau kasan rashin mutuncin da ta mun? Da ma ai promise my self saina koya mata hankali, just forget naji tsakaninku yanzu, thos not change everything “

Ganin yanda ya hasala yasa yusuf dan buga kafadarsa kadan ” take it easy, don’t forget u are man “

” forget about that ” haydar ya fada

” please karka kakkaryata kaga biki ya kusa, don akan yayanka zai Kare, tunda shi zaka Bari da jinya” Ahmad ya fada yana murmushi

Yusuf dai na tsaye shima murmushin yake, don yasan halin kayansa tunda ya furta, Ba abunda zai hanasa aiwatar wa.

******************

Waya ta dauka tana kokarin kiran kanwar tata, idonta ne ya sauka a kan agogon wayar to 11 na dare. Ajiye wayar tayi tana huci.

Yau bacci barawo, da kyar ya suri hajiya. Bawai bata son yusuf bane aa ita uwar yusuf dince da basa shiri, bata so, su Kara hada zuriya😕 (niko nace hada zuriya na nawa kuma?)

*****************

” Rike gaisuwarki, in kin samu lokaci kozo ina nemanki, ” hajiya ta fada har lokacin Ba annuri a fuskarta

“in sha Allah inanan zuwa anjima kadan, ” Hauwa ta fada cikin damuwa don tasan tabbas wani babban alamari ne, tunda taji muryar yayar tata a sama.

” hajiya ni banga abin damuwa ba anan, naga da habiba da yusuf duk daya ne, me zai sa ki tada hankalinki haka? ” sulaim ta fada

Harararta hajiya tayi. ” abinda babba ya hango yaro ko rimi ya hau bazai hango ba, don haka kar wacce ta Kara sa bakinta cikin wannan maganar “

Haydar dake hada takardunsa ya juyo yana kallon hajiya, murmushi yayi ” ni naga taimakon ku ma yaya yusuf zaiyi ya auri wannan dakikiyar yarinyar da ba komai a kanta, sai fitsara da rashin kunya”

” ungo nan ” hajiya ta masa dakuwa ” yayar taka Kake kira dakikiya? “

” tun da ta fara school din mu cikin mu 25 daga 21, 22 take zuwa sai so daya da tayi na 19. Amma a wurin rashinji da neman masifa 1 ce, ga dan banzan surutu, ina tausayin yaya yusif wallahi Sam basu dace ba “

” don ubale sai kasa ya fasa ai” hajiya ta fada cikin fushi da jin haushi maganar haydar.

” kai dai kace bata da kokari, amma ai habiba ta hadu karshe, son kowa wallahi ” khulsum ta fada

“kin san halin kaninki, yanzu haka bai taba tsayawa ya Mata kallon tsaf ba, tunda jininsu bai hadu ba ” sulaim ta fada

Jakarsa ya Saba ya musu sallama ya fice, yana tunanin hukuncin da zai fara yanke mata.

*****************

Suna zaune a class room bayan teacher ya fita. Book din physics ne a gabansa ya na solving wani question. Ji Kake fas a keyarsa. Da sauri ya dafe keyar, saboda azabar zafi da ya ziyarci kwanyarsa.

Dariya ta bushe dashi, harda shewa. Abin da ta jefeshi dashi yabi da kallo. Lemune Wanda ya wargaje can gaban board.

Cikin kunan rai ya zaro Coca Cola dake jikin aljihun bag dinsa ta waje, yana juyowa sai ji Kake bum!!! Fassss!! Ya sameta sosai a kirji, don lokacin tana tsaye. Sannan ya fashe ya bata mata uniform, mu samman farin hijab din.

Wani Kara ta sake, Wanda hatta class din sai da ya amsa. Kwanciya tayi a kasa ta dinga ihun kuka.

Hubby akwai tsokana, gashi bata son abinda zai taba lafiyarta ko kadan. Saukar wani jifan taji a bayanta, ihu ta Kara sakewa ta dafa bayan da hannu daya.

Ya daga daya canvas din zai Kara aika mata, Abdul Alim ya rike masa hannun.

“please it’s okay dud “

Gaba daya matan aji sunyi kanta, sai faman ihu take, kamar Wanda aka kwakulewa ido.

Mrs Brown ce ta shigo, ganin yadda class din ya hautsine yasa ta fara tambayar abinda ya faru.

Da kyar aka samu hubby tayi shiru. “she never expect him to do this to her “

“Take her to the PC office ” Mrs Brown ta fada ma su yusra da suka rikota.

“Aliyu follow me to the PC office ” Mrs Brown ta fada tare da ficewa a class din.

Canvas dinsa ya dauko yasa, friends dinsa Sun fito zasu rakashi ya dakatar dasu.

A hanya ya hadu dasu, saboda yadda ta langabe, sun tsaya tana hutawa, yana zuwa baiyi wata wata ba, ya kwashe kafa fuwanta sai gata a kasa, yayi wuce warsa.

PC na tsaye a bakin office dinsa Mrs Brown na masa bayanin abinda taji a bakin yan aji. Duk kansu sunga lokacin da ya kwashe kafafunta. Yana isowa PC cikin bacin rai ya Kalli Aliyu “I never expect this from u, bill down “

Kallonsa haydar yayi cikin bacin rai jijiyoyin kansa sun tashi, sai faman hura hanci yake ” don’t tell me to nill down, because I’m not doing it ” ya fada in horse tone

Kallomsa PC ya keyi cike da mamakin maganarsa. Yasan yaron bashi da matsala ko kadan, zai iya cewa tun primary zuwa secondary baa taba kawo masa karar saba. He is nice boy Wanda suke alfahari dashi. To amma sweet heart dinsa ya taba, after all har a kan idonsa yaga ya kwashe kafafunta… To fahhhhhh😯Mu shiga daga office, PC ya fada yana shigewa cikin office din. Binsa Su haydar suka yi.+

” a matsayinka na namiji, bai kamata ka tsaya kana fada da mace ba, wannan bai dace ba sam. Kai yaron kirkine, baa taba kawomin kararkaba, shi yasa zan maka alfarma wannan ya zama na karshe da zaa kawo min kararka. Amma gaskiya yau, I’m disappointed about what you did, ban taba tsammanin you stood so low by fada da mace ba, after all she is your sister,” haydar dake tsaye jikin table din PC, bai ce komai ba, sai cika yake.

Juyawa yayi wurin hubby ” shi din ba kanin ki bane? PC ya wurgo mata tambayar.

Murmushi tayi cike dajin dadi, (hubby da son girma) ” kani nane, na wurin biyu ma ” ta fada tana kallon haydar da ya Kara cika tam,

” kema be kamata ki dinga biye masa ba, nasan duk yadda akayi kin kai shi bango, ki Rike girmanki. Kar in kuma jin wani abu ya sake tasowa a tsakaninku. ” PC ya fada yana binta da wani sihirtaccen murmushi ya Kara da cewa.

” in an barki dashi kashi zaki sha tunda karfin namiji da mace ba daya bane. Karki kara neman fada dashi. “

” amma dai zaka sa a Zane shi ko? Ji yadda ya mayar Dani gurguwar karfi da yaji, kafafuwana ciwo suke min, ban iya takasu. ” ta fada kamar zatayi kuka.

” duk abinda ya faru ai, lefin kine, da baki shiga shirgin saba, ai da bai miki haka ba, haydar duk school din nan bashi da abokin fada, I know yadda kika sa shi a gaba, bai taba ramawa ko ya kawo kararki ba, yan zun ma kin kureshi ne. ” Mrs Brown ta fada

” is OK. Haydar she is your sister make peace with her, ban son sake jin irin wannan a tsakaninku. Ke kuma karki Kara tsokanarsa, kai ka tafi class, ku kuma ku rakata clinic a duba kafar. “

Kallon PC hubby take idonta cike da Hawaye, don taso PC yasa ama haydar dukan tsiya, amma ya kyale shi ya tafi, watan ya bugi banza kenan? Tafdijam Ashe bata cika habiba ba in har ta barsa yaci bulus. Koda tsiya koda tsiya tsiya sai ta dauki fansar cin zalinta da yayi. This is her promise.

PC kam gaba daya jinsa yake, wani iri, gani yake bai mata adalciba, amma ya ya iya, shaidu sun nuna karara itace bata da gaskiya, after all behavior din Haydar na yau ya tsaya masa a rai. Tabbas Mai hakuri bai iya fushi ba. In yace zai hukun tashi komai zai iya faruwa, don already ya fusata sosai.

Ko da ya dawo class bai cewa kowa komai ba, kujerarsa yaja ya zauna, ya ci gaba da duba books dinsa. Suma friends dinsa ganin yadda yake a fusace yasa suka Kama kansu.

“please hubby na rokeki ki fita hanyar yaron nan, he did nothing to u. Kin takura masa, duk abinda ya miki ke kika siyama kanki “

Kallon yusra hubby tayi cike da jin haushinta. ” Sai kiyi kuma ” hubby ta fada

“Alim ” Hayder ya kira, Wanda aka Kira da Alim ne ya taso ya nufoshi, kus kus sukayi, ko Junaid dake kusa da su baiji me suka fada ba, sai dariyar Alim yaji, yana komawa sit dinsa.

***************

“Da saninki ake wannan kulle kullen, amma kika kasa sanar Dani, don baki daukeni a bakin komai ba? A ce magana har tayi girma haka Sai dai in ji a sama ” hajiya ta fada cikin kunfar baki da bacin rai.

Hajiya hauwa da itama take cikin damuwa, ga ganin yadda yar uwar ta ta dau zafi, wadda take matsayin uwa gareta, yasa ta sassauta murya,

” ki yadda Dani yaya, ban san komai ba, sai jiya nima yake gayamin. Wallahi sam ban san ya a kayi hakan ta kasan ce ba. Don tun da mukayi magana dake na toshe duk wata hanyar da zasu hadu, waya ma har yau ban yadda an bata ba. In sun zo ma gaba daya muke zama a falon har su gama zamansu su tafi, ni kai na nayi mamakin maganar. Shi yasa jiyan na tutsiyeta. Ashe hutun da ta tafi kankiya shine ya bita anan suka dai dai ta magana, gwaggo kuwa ta goya musu baya, don dama burin ta da Alhaji kawu ummi na gama secondary tayi aure, don cewar su duk saoin ta sunyi aure wai harda yara. “

Shiru hajiya tayi tana sauraron kanwar tata ” to ita habiban ta nuna aure take so ko sune suke son tilas ta mata? “

” yaya ke nan, kina Abu kamar baki san halin ummi ba, ni dama na dade da dagota, shi yasa bata son mai da hankali kan karatu, yanzu in ma na matsa a barta tukunna, ba karatun take so ba, kin ga kuwa gara auren tunda shi take so. Ni yanzu yadda zamu bullowa abun ne don su Alhaji kawu da abbanta duk sunyi naam da abun, ita kanta na Lura tana mugun son yusuf, don jiya kwana tayi tana kuka, don nace dole ta rabu dashi ta fitar da wani tun da auren take so kuma tana da mane man.”

” bana jin yusuf, hauwa, nafi jin uwarsa da danginta, kin san tsakaninmu ba sai na fada ba, sannan abin da nafi ji shine, maman shi ta na da wadda take so ya aura. Tun ba yau ba, bana son ayi abinda daga baya za azo ana da an sani. “

” haka ne yaya, zan turo miki ummin wata kila ke, zataji abinda zaki gaya mata, don yanzu magana na wurinta, yau dama yace zai tambayeta yaji raayinta, don sunyi magana da uncle kan yana son susan raayinta Kafin su je kankiya on Saturday maganar neman aure “

” shi ke nan, ki turota, ni nasan yadda zan bullo mata ” hajiya ta fada hira sosai sukayi da kanwar tata, Kafin sukayi sallama ta tafi.

*********************

“Allah mommy ina sonta sosai, bazan iya hakura da ita ba, kiyi hakuri ki barni in aureta, ke kanki bazaki ji dadi ba in auri matar da bani da filling a kanta ba “

Harararsa maman yusuf tayi cike dajin haushinsa. ” saboda baka kishina ko? Duk yan matan dake garin nan Ka rasa wadda zaka dauko min sai jinin hadiza, to tsaya kaji tun muna shaida juna, Kafin ranka ya baci, kaje kace ka fasa. Na yadda ka nemo ko yar waye amma banda jinin hadiza. ” ta fada cike da jin haushinsa

Duk yadda ya so fahimtar da mommy kin saura ronsa tayi, daga karshe ma cewa tayi ya tashi ya bata wuri, ya kuma tabbatar yau din nan ya shai dawa daddy dinsa ya fasa.

****************

“Tabdijam yau za ayi tashin hankalin da baa taba yi ba a school din nan.” hubby ta fada tana Kara bude culers din su na abinci. Da suke empty a wanke tsaf.

” kin ga karma ki fara, duk bake kika jawo mana ba, ki barmu muji da guda daya please ” yusra ta fada cikin muryar gargadi.

Aisha dake gefe ta buga tagumi, tana tunanin yadda za suyi surviving ba tare da abinci ba, har su tashi. Don already yunwa take ji kamar taci babu. ” meye solution yanzu, don gaskiya yunwa na keji “

” I have some cash with me, muje musha drinks da meat pie, ma raka “

Harararta hubby tayi ” ke ma kin san waannan baza suyi maganin yar banzar yunwar da nake ji ba, yau ko karyawa ban yiba na fito. Yanzu haka cikina ya hade da hanji “

” Aisha tashi muje kinji, don ni 500 kawai nake da, “

Ganin da gaske tafiya zasuyi su barta, yasa ta tashi ta bisu, tana din gisa kafa. ” Allah yaron nan shima ya dana. I will deal with him later “

” kinga shawarar da zan baki, Ki fita hanyarsa, don kin shiga black list dinsa, Ba ke ba har mu, sai mun gayawa yan garinmu. Aisha ta fada

” rabu da ita, jiki magayi ai, sai randa ya karasa kafafun gaba daya ” in ji yusra

Aisha ta yi murmushi ” ba tasan halin haydar bane shi yasa. ” sun isa canting bude jaka yusra tayi ta dauko Math set dinta don anan ta boye kudin. Nan fa kudi yace dauke ni inda kika ajiye ni, zazzage jakar tayi tsaf Ba komai a ciki. Kallon kallo aka fara tsakaninsu.

” yanzu meye abun yi, wallahi da hannuna na saka 500 da safennan cikin Math set don gudun yan sibare, amma gashi ban tsira ba ” yusra ta fada kamar zatayi kuka

” kumu yafi class kawai, already lokacin break ya kusa karewa, maci hamma yau kam ” inji Aisha

Hubby kam kasa cewa komai tayi, don ba karamin yunwa takeji ba, ko breakfast batayi Ba ta fito, wai ita tayi fushi, to ga abinda fushin cin abinci ya ja mata. Don da tayi break fast bazata damu sosai ba. Gashi tasha ruwa da ta dau niyyar azumi, ko ba komai ta samu lada.

A hanyarsu na komawa class, sukaci Karo da group din su haydar da abokansa. Sun shinfida dadduma kamar yadda suka Saba, kowa da food Plack’s din abincinsa ga drinks suna ci suna dariya da iface ifacen su irin na teenage boys. Wani uban ihu suka sa, lokacin da su hubby sukazo zasu wuce, tare da kwashewa da dariya. Haydar kam ko dago Kai beyi ba, junaid shi kam tsorone fal cikinsa, don yau yasan in sun koma gida Allah kadai zai kwaceshi daga jarabar hubby. Don yayi mamakin yadda yau ta yi sanyi, ya Tabbatha da sai sunyi upside down da school din. Juyawa tayi zata isa wurinsu, da sauri Aisha tajata ” please hubby live them “

“let me go, and give them my peace of mind, ko zuciyata tayi sanyi. ” hubby ta fada tana huci

Da kyar suka hanata zuwa, suka nufi class. Ko wacce ciki na kiran ciroma.

*******************

Part din mmn samira ta fara shiga ta gaisheta, kamar yadda ta Saba duk lokacin da tazo gidan sai ta shiga part din Abokan zaman hajiya ta gaishesu, tukun ta wuce part din hajiyan. Cikin farin ciki mmn samira ta karbeta kamar yadda ta saba, suka dan taba hira, Kafin ta nufi part din mmn yusuf, kirjinta na faman dukan tara tara.

Sai da aka bata ikon shigowa, bayan tayi sallama. Ta shiga cikin tafiyarta ta natsuwa kanta a kasa. Mmn yusuf na zaune tana kallon film a tashar African magic Hausa. Zama tayi a kasa ta gaisheta, ba yabo ba fallasa ta amsa mata, tare da tambayar hajiya hauwa da sauran kannenta. Shiru falon ya dauka. Su hubby an natsu kamar wata mummuna 😷 shigowar abida yasa ta dago da idonta dake kan yan yatsunta da take wasa dasu.

Kallon uku saura kwata tabi hubby dashi, tare da Jan dan karamin tsaki. ” mama zan bi yaya Ahmad dauko su Aisha ” ta fada tana dauke kanta daga kallon hubby. ” sai kun dawo, ku biya gidan hajiya karima ki ce ta baki sakona”

“Tom ” ta fada tana kokarin shigewa dakinsu don ta dauko gyale.

” anty abida ina wuni ” hubby ta fada cikin mutuwar jiki. Jiyowa abida tayi tana wurga mata uwar harara, taja tsaki, ta shige ciki, ba tare data amsa gaisuwarba. Mmn yusuf na jinsu, bata ce komai ba, ta ci gaba da kallon ta. Hubby na zaune jiki yayi sanyi abida ta fito ta fice a dakin. Itama tashi tayi tama mmn yusuf sallama ta nufi part din hajiya. Zuciyarta a cun kushe.

******************

Da gudu ta fada jikin hajiya, kamar yadda ta saba, don ba karamin shakuwa bace a tsakaninsu. ” ni dagani, karki karasani, yar neman yarinya ” zama tayi kusa da ita tana dariya. “ni din guda nawa nake da zan karasa ki, dube nifa kamar ki hure ni in fadi ” dariya hajiya tayi ” me kike ci na baka na zuba, kiba lokacinta na zuwa, don haka ki kwantar da hankalinki ” ” wane better kika tanadar min? An ce kina nemana,. “

Zama hajiya ta gyara ” akwai better din ma, amma magana nake son muyi, na tsakanin ya da uwarta. “

Murmushi hubby tayi don ta Riga ta dago zan cen. Watau mommy nan ta kawo kararta ke nan.? “

” yusuf yaron kirki ne, bashi da matsala ko kadan, amma bakya tunanin matsalar da zaki fukanta ta wurin uwarsa da yan uwanta? Suruka da danginta na matukar taka rawa ta wurin zaman lafiyar gida ko akasin haka. Ina ji miji tsoron muta nen nan, don nasan su farin sani, basu da kir ki ko kadan. balle kuma ta gefe daya kin fito daga tsatsona ko wannan kawai zai sa bazasu kauna ceki ba. Zan so ki hakura da yusuf in har aure kike so, ki fitar da wani ko kuma ni da kaina zan zabo miki. Fiye da yusuf.” da sauri hubby ta Kalli hajiya cike da tashin hankali.

Wai me yasa sun kasa gane, soyayyarta da yusuf daga Allah ne, tana son yusuf, Shima yana sonta, wannan kawai ya ishesu, don tasu mamanshi da danginta ai bada su zata zauna ba, balle ta damu kanta. Ido hajiya ta kafeta dasu tana karantar yanayinta.

Murmushi hubby ta kakalo ” shi kenan hajiya,”

“Kina nufin kin hakura, zaki fitar da wani ko yaya abun yake? ” hajiya ta tambayeta don bata yadda da amsar hubby ba.

” na hakura ” ta fada tana murmushi

Rungumota hajiya tayi cike dajin dadi, mu samman ganin yadda bata sha wani wahala kamar yadda tai tunani Ba, wurin karkato da hankalin hubby. ” yawwa yar albarka, Allah ya miki albarka, in sha Allah da kaina zan zabo miki miji na nunawa saa “

Dariya hubby tayi a ranta, “in kun san wata ai baku san wata ba, mai rabani da hasken zuciyata Sai ya shirya. He is mine, I’m his. Try as much as u can 😎”

Hayaniyar yan matan gidan ne ya cika kunnensu………..

.hubbyn hajiya, sai yau ake ganinki a gidan nan? ” sulaim ta fada tana zama kusa da hubby tare da dada mata duka a cinya.+

” Kai Kai Kai,  kefa matsalata dake muguwa ce, ta bugawa a jarida, daga haduwa sai cin zali ” hubby ta fada tana shafa inda sulaim ta bugeta

“Haba matar yaya, ni na isa In ci Zalinki?  Kawai nayi missing dinki ne, kin Dade baki zo gidan nan ba. “

“Ke meya hanaki zuwa namu gidan in har da gaske kinyi missing dina”

” week end din nan mukayi niyyar zuwa biko, matar yaya ” khair ta fada tana murmushi

Harara hubby ta maka mata ” ke kuma waya sa dake?  Manya na magana kina tsoma baki. “

Dariya duka dakin suka sa ” kin bani da son girma, yarinyar nan?  Shi yasa bakwa shiri da autan hajiya ” khulsum ta fada

” ki barni da autan hajiya, idona idonsa, sai na karya kafarsa ko hannu.  Jibi yadda ya mai dani gurguwar karfi da yaji ” ta tashi tana nuna musu kafarta.

” autan hajiyan zaa karyawa kafa?  Ba dai nace ki fita harkar Saba kin ki? In dai aliyu ne kadan kika gani ”  aiman ta fada tana duba kafar hubby da har lokacin tana dingisa kafar.

” aliyu bai kyauta ba, ki barni dashi zaizo ya sameni ” hajiya ta fada bayan ta gama jin duk abinda ya faru daga bakin hubby

” kema bakya jiran kanki, ki fita harkarsa.  Ni na rasa me yasa jininku bai hadu da shi ba. ” sulaim ta fada

Murmushi kulsum tayi ” kema kin san halin shi, kamar wani mai Al matsutsai haka yake, in baya sonka to fa baya sonka, ba zai taba shiga harkar kaba, kallo ma baka ishe shiba. Tun da kika kureshi Allah kadai zai raba ki dashi. Shawara daya zan baki, ki bashi hakuri, ki kuma fita hanyarsa ” ai Kafin ma kulsum ta karasa hubby ta dire ” tabdijam in bashi hakuri fa kika ce?  Kanin nawa zan ba hakuri?  Yayi tsararo wallahi “

“Sai kuje kuyi tayi ai, Wanda yaji wuya ya hakura”

” ku dai barni dashi zan masa magana, ke kuma ki fita hanyarsa,  ki tashi kije gida magriba ya gabato ” to hajiya, baki bani abun dadin ba?

” uhummm  su akwa Dede, har yanzu dai hali na nan”

Fari tayi da ido ” me zaa fasa, abin da ya kawomu birni kenan, muci zaki muci maiko, tun da suka raboni da gwagwgwota ai sun hadu da ata gwangwama. ” dariya sukayi gaba daya ” zan basu shawara su mai dake, ko sa huta da halinki ” sulaim ta fada

” da nafi kowa farin ciki wallahi “

” wani lokaci kamar baki da wayau wallahi, taya mutumin da yasha ruwan birni, ya dinga mar Marin kauye? ” duka hubby ta kai ma khair ” banza waya gaya miki kankiya kauye ne? Sai kinje yarinya kisha mamaki “

“ke da zaki tafi dakin miji, ina maganar wani kankiya? “sulaim ta fada tana murmushi.

Hajiya ce ta fito, da wata Leda mai dan girma dauke da tambarin delema Beckry.  Ta mikawa hubby. Amsa tayi tana murna don tasan her favorite chocolate ne da sweets kamar yadda hajiya ta Saba mata.

” Allah hajiya kina shagwaba yarinyar nan!  Da yawa ” khair ta fada cikin fuskar fishi -shagwaba.  ” jealousy baby,  zaki kone in dai tsakanina da hajiya ne, eheee! ” hubby ta fada tanama khairi dariya tare da shafa mata fuska da ledar.

Godiya tama hajiya da su kulsum, sulaim da khair suka rakota, parking lot, In da driven gidansu ke zaman jiranta.

Ba kowa a compound din.   wait!!!  Sulaim ta fada bayan da suka kusa isa wurin mota ” yanzu hubby duk yadda Muke dake ki kasa gayamin tsakaninki da yaya yusuf Sai dai muji a sama?  Baki kyauta min ba, bankuma ji dadi ba, Aisha ma dazu da muke maganar cemin tayi baki gaya mataba, duk da ko yaushe kuna tare a school,  sai yau ta samu labari, she is not happy with u,  not telling her “

Murmushi hubby tayi ” very sorry.  Nayi tunanin matsala in har aka samu labarin nan a gida, shi yasa muka barshi a tsakaninmu har Sai magana tayi karfi tukunnan.  Amma gashi still abinda muke gudu shi ya faru. Many people are against it ” ta fada cikin damuwa

” is true, but ya kamata ku jajirce, nasan in har anyi dole kowa ya hakura, ya rungumi kaddara, hakika kun balain dacewa, ke da yaya yusuf, kinyi dacen miji, don haka ki toshe kunnuwanki da duk abin da za kiji ko zaki gani. ”  rungume sulaim tayi cikin jin dadi ” thank you sister, ke kadai kika gayamin magana mai dadi, bayan dad dasu gwaggona, “

Khair ce ta dafata ” we are all support u,  Allah ya sanya alkhairi “

” thank you ” hubby ta fada tana murmushi. From no where taji saukar Abu a kafadarta ” mieun mueum! ” gaba daya sun tsorata don khair kam har ta isa cikin gida, a 360. Mage ce kan kafadar hubby Sai makal kalewa take, tana kuka. In akwai abinda hubby ke tsoro to mage na daya daga ciki.

Garin kokarin gudu, ta Kara turgude kafarta me ciwo, ga mage ta dafe mata a wuya, ihu take tana Menan dauki tare da kokarin cire magen a wuyanta, bata san lokacin da ta saki fitsari ba, don tsananin tsoro da tashin hankali,.  Da sauri driven gidansu dake zaman jiranta ya fito, ya nufo su.  Sulaim ce ta dauke magen a wuyanta da kyar, duk ta yakushe mata wuya.

Da gudu ta fada motarsu, tana ihu, tare da numfar fashi, kamar ranta zai fita, ga kafarta data fama tana wani balain zugi. Kuka ta fashe dashi.

Da sauri su kulsum, suka karaso motar, suna mata sannu, tare da lallashinta. Suyi sunyi tazo su koma ciki, ganin yadda duk ta fita hayyacinta taki.

Tsugunnawa yayi ya dauki magensa, yana mata shillo, ya nufi cikin gida, ko kallon in da suke be yiba.

Da kallo suka bishi, ita kanta hubby dake faman kuka, tsayawa tayi Tana kallon sa. 

“anyi Dan banzan yaro ” kulsum ta fada, tare da bin bayansa ranta a bace.

Hakuri suka Kara ba hubby Kafin suka nufi cikin gida, su kuma suka tafi.

               ****************

Sosai hajiya kema haydar fada, kamar zata dukesa.  Shiru yayi kansa a kasa, ya cika yayi fam!!! Jin ta gama fadan yasa ya dago ya Kalli hajiya da idonsa da suka kada sukayi ja ” kiyi hakuri ” ya fada tare da tashi ya Mufi dakinsa.

” Allah ya shiryamin kai, da wannan bakar zuciya ” hajiya ta fada tana binsa da kallo

                 *****************

Ko Kafin hubby ta isa gida, kafa ta kumbura sintim,  mommy hauwa na ganin kafar tasa aka Nemo mai gyaran targade.

Ihu da kyar aka samu a ka gyara mata targaden data samu a kafa. Sai da yayyinta jabir da jafar suka danneta tukun na. Fadin ihun da hubby tayi baa magana. Don bata son duk wani Abu da zai taba lafiyar jikinta.

Fada sosai mommy hauwa ta mata, don tasan duk abinda aliyu ya mata laifin tane.

Sai da hubby ta kwana uku, bata iya zuwa school ba, tana jinyar kafarta, tare da shirya irin ramuwar da zatayi kan haydar, don ta kuduri niyyar sai ta fanshe no matter how.

               *****************

Daddy hubby ne, zaune kusa da ita, kan gadonta da take jinyar kafarta.

” ummina ya maganarmu?  A ina muka kwana, don gobe suke son zuwa kankiya, amma in munji ta bakinki.  Kin amince ko aa? ” ya tambayeta yana kafeta da ido.

Kallonsa tayi cike dajin kunyarsa, Kafin ta mai da kallonta kan mommy hauwa dake tsaye bakin kofa, ta kafeta da ido cike da gar gadi.  Duk da zuciyarta a kwance take, jin yadda hubby sukayi da hajiya.

Kwanciya hubby tayi a kan cinyar daddy ” na amince ” ta fada tana Kara boye fuskarta a jikinsa.  Shafa kanta yayi cike da farin ciki ” Allah ya miki albarka, yasa albarka a cikin wannan lamari “

” gaskiya abban jafar akwai matsala, ” da sauri ya dakatar da mommy hauwa ” ba na son jin komai daga bakin ki, ke zaki zauna mata dashi?  Meye aibun yaron nan.?  Ban son kana nan maganarku na mata,  ke dai a matsayinki na uwa, albarka kawai ya kamata kisa, tare da binsu da addua, amma ba ku tsaya kuna wasu kananun magana marasa tushe ba.  Ni zan fita, in na dawo mayi magana, sai ki fara shiri tun da wuri, don tare suke son a hada Dana su kulsum.  Kinga ba isashshen time “

” wai duka duka ummin nawa take, da zamu biye mata ” ” nace ya isa haka ko?  Ban son jin another word ” ya fada cikin daurewar fuska, ya Shafa kan hubby Kafin ya tashi ya fita.  Harararta mommy hauwa tayi tayi kwafa, tabi bayan mijinta.

Ajiyar zuciya hubby tayi, tare da dafa saitin zuciyarta dake faman bugawa.  Ta lumshe ido. Tana tunano Rabin ranta.

                 ***************

Yusuf Jamil Yusuf Zubair Oregon  Wanda abokansa ke kiransa da Oregon Babban da na miji ga Alhaji jamil.

Yusuf saurayi ne, Dan shekara 25 a duniya yayi degree dinsa na daya Dana biyu, duke a ABU Zaria inda ya karanci business admin. Yanzu haka shi ke kula da restaurants din Alhaji jamil dake other states.

Yusuf saurayine kyakyakyawan gaske, kamarsa sak da mahaifinsa, sai idon mmn yusuf daya dauko. Fari ne sosai, mai sirki da ja, sumarsa irin ta larabawa baka Mai matukar laushi.  Doguwar fuska gareshi Mai dauke da yalwataccen gashin gira Dana ido, gazar gazar,  idonsa Manya ne, don wani lokaci in yana kallon ka Sai ka dauka yana zaro maka sune, farare kar da kwayar baka Mai daukar ido.  Ya nada dogon hanci, Mai kyan tsari da karamin baki mai dauke da kyawawan labba pink, hakoransa a Jere suke tsaf gwanin shaawa.  Maabocin barin sage mai hada da dan gajeren gemu, daya Kara kawata fuskarsa

Yusuf mutun ne mai ilmin addini, mai hakuri, don duk yaran Alhaji jamil ba Wanda ya kai sa hakuri  da son jamaa.

Alhaji jamil na matukar alfahari dashi, saboda biyayyarsa,  duk wani hali na alhajin, yusuf ya hada su, in ka dauke zafin zuciya, don yusuf mutun NE mai matukar hakuri da dawuya kaga bacin ransa.

               ******************

Daga fannin hajiya har mmn yusuf ba Wanda ya samu yadda ya ke so.  Don alhaji jamil ya tsaya sosai ganin basu kawo wani cikas akan maganar auren yusuf da hubby ba.

An tsai da magana zaa hada da nasu kulsum. Wanda yayi dai dai da sati daya da kammala jarabawar kammala secondary school din hubby.

                 ******************

Makarantar gaba daya ta dai nama hubby dadi,  yanzu bata da kawa ko daya a school din.  Tun da ta dawo daga jinyar kafarta na kwana uku,  ba me kulata a school din.  So da yawa tana Lura da yusra da Aisha kamar zasu mata magana amma sai taga suna waige waige cike da tsoro.  Daga karshe ma canza wurin zama sukayi.

Tsare junaid tayi a gida, kan Sai ya gaya mata abinda ke faruwa.  ” dariya yayi doka ce ba mai kulaki, duk Wanda ya karya doka, zai hadu da hukunci mai tsauri, don haka live with it,  ki rabu dasu yusra kar ki sasu a Matsala, don ranar da aka kamasu suna kokarin miki magana, hukunci ya hau kansu, shi yasa suka canza sit “

” kanata maganar doka – hukunci,  uban waye yasa wannan dokar? ” ta fada tana zazzaro masa ido

” kin fi kowa sanin waya sa dokar, kin San dai duk yadda ake tsoronki a school din bai Kai yadda ake tsoron saba ko? Har yau baki San waye haydar ba, shi yasa nayi ta Jan kunnenki ki fita harkarsa, kika ki “

Duka ta dada masa ” banza sa karai, da wannan yaron ne ya saku kuke min izgilanci?  Duk Sai naci ubanku daga ku harshi, Allah ya kaimu Monday “

” aa hubby,  kibi a hankali ” ya dada cikin tone din gargadi

” fice min anan, solobiyo kawai ” ta turashi waje

               *******************

Monday tana zuwa school,   ta nufi office din PC tayi reporting din haydar

A assembly PC ya musu gargadi, tare da neman haydar ya samesa a office.

Koda ta shigo aji, already kowa yana mazauninsa.  Hararar su yusra tayi, dake sit din bayanta ta zauna.  Abinda ya daure mata Kai har aka tashi break Ba Wanda ya kulata, tana kallon kowa ya fice a class din. Su yusra ma a kan idonta suka fita. Jakarta ta dauka da food Plack’s tayi waje, cafeteria ta isa ta nemi wuri ta zauna ta fara cin abincinta, kamar yadda ta saba, kwana biyu da basu Aisha.

Su haydar ne, suka shigo da tawagar abokansa.  suta faman dariya da iface iface kamar yadda suka Saba. Kowa ya nemi sit dinsa. 

Zama yayi a saman table din teacher, gaban board.  Hannunsa rike da doguwar sanda, yana kada kafarsa a hankali.

” hi!!!!!  Class ” ya fada a yangace Kamar baya son yin magana.  Gaba daya class din ya dauka ” hiiii” ban da hubby dake faman shan chocolate dinta, tana kallon ikon Allah.

” yama Su nan alder din class dinnnan? ” ya tambaya, gaba daya suka amsa da ” Anty hubby “

” right!!!! kamar yadda PC yace, u can talk to her. Amma tunda yake ita ce alder a class din nan bakwa tunanin we have to do some changes? “

“yes!! yes!! yes ” suka dauka gaba daya

” anty hubby, bai dace da ita ba, we have to come with nice name da zaiyi fitting nata, any ideas “

Nan fa Kowa ya fara fadan sunan da yake ganin ya dace.

Hubby kam ko a jikinta, ta Kalli wanna sannan ta Kalli wan can. Tana shan chocolate dinta, hankali kwance.

” gogwgwo habi ” alim ya fada yana dariya

Shiru haydar yayi yana juya sunan. Class gaba daya ya dauka gwaggo habi!!!!= gwaggo habi!!!! ” it’s ok tun da sunan ya muku. From now on duk wani Abu na gwaggon mu ya zama namu, her food, drinks, water, chocolate, biscuits. Everything da gwaggo tazo dashi na ci, duk Wanda ya gani yana so. Just tell me. Or my friends.

Ido hubby ta zaro ” kam balai,  naga Dan iskan da zai matso kusa dani balle ya dauki abuna. ” ta fada da karfi in warning tone.

Daya daga cikin friends din haydar yace ” ina son chocolate din hannunta, Kai har ma dana cikin jakar. “

” gwaggo friend na son chocolate, so pass it here ” haydar ya fada idonsa kan Jakarta data kwakume a cinyarta………….Fito yayi,ko kafin hubby ta farga Hafiz yayi sama da Jakarta, kasa motsi tayi tana binsa da kallon mamaki, yaron dake girma mata anty sama anty kasa, yau shi ne da fisgar Jakarta.+

“Don’t worry gwoggo, we have gift for you.” ya ba Hafiz damar bude jakar.

“gwaggo na wuta fah!!!!  Na dauka manya basa shan zaki, amma wannan gwaggon  namu sha zumamu ce, zamu dan mai da komada,”

Alim kam kwashe sweet da chocolate masu tsada,  ya dura a aljihu ” godiya dubu gwaggo habi.

” wannan shine gift din mu me taken welcome to the hell 😈😈😈”

Ya daga wani ledder Mai kyau, yana nunawa class, Kafin ya jefa cikin jakar hubby. Ya duro daga desk ya koma sit dinsa.  Hafiz ne ya mayar mata da Jakarta. 

Tashi tayi ta tsaya daga sit, dinta.  Bude murya tayi yanda zasu jiyota,  fuskarta cike da murmushi.  ” thank you class,  na gode da sabon suna, I like it,  because Su nan the most  precious person in my life, my love, my life my everything my grandma,  ana kiranta gwaggo, some people call her gwaggo habi.  My parent name me after her. So no problem u can call me gwaggo habi as much as you can,  I don’t care ” har ta zauna ta Mike ” thanks for the gift”

Speech dinta bai ma friend din haydar dadi ba, don sun so tayi masifa ne kamar yadda ta saba.  Free time dinsu is off.  So teacher ya shigo kamar yadda ya saba.

Jakarta ta bude ta dauko note book dinta, sai lokacin taci Karo da ledar gift din, har ta manta da wani gift.  Tabe baki tayi, ta Fara duba book din da take da bukata.  Motsi taga kamar ledar nayi,  natsuwa ta Kara yi don ta tabbatar da abinda idonta ke gane mata, tabbas motsi ledar keyi, kadan kadan,  hannunta takai kan ledar cikin karfin hali, laushi taji da Dan karfi karfi,  bude bakin ledar tayi, don ta ga abinda ke ciki, wani tsalle tayi, tare da cillar da Jakarta gefe, tana ihu na daga hankali,  fita tayi daga class din a 360 yayin da yan aji suma suka tsorata ganin yadda ta daka tsalle da ihu tare da wulli da Jakarta, yasa dalibai da yawa rufa mata baya, suna ihu duk da basuga abinda ya firgita ta ba.

Baki teacher ya sake yana kallon yadda ajin ya hargitse, kadan ne masu karfin Hali suka rage, Sai tambaya yake “what happened”

Nesa da class din, taja birki tana maida numfashi, ta tsugunna tare da dafe kirjinta da hannu, da takeji kamar zai Faso ya yo waje. Yan class din da suka rufo mata bayama burki sukaja, suna mai da numfashi,  tare da tambayarta me NE ne?

” sneak ,maciji 🐉 I’m telling you is sneak ” ta fada cikin rawar murya tare da hada haruffan dakyar.

Aisha ce tace ” a ina kika ganshi? “

” inside my bag, the gift “

Teacher din su ne ya kwala musu Kira, yana daga brander na class din.  Duk kansu jiki a sanyaye cike da tsoro suka nufi class din.

” what kind of nonsense ne, yasa zaki tar watsa min class,  what happened ” ya tambayi hubby cike da bacin rai,  don iya dube duben su, basuga abin da zai sa ta yi haka ba.

” sir sneak inside my bag ” ta fada tana nuna masa Jakarta dake yashe gefe daya

Kallonta ya tsaya yi, for a second, jikinta sai rawa yakeyi, kana ganinta kasan a firgice take.  A hankali ya taka zuwa wurin jakar ya zazzage ta, tare da duddubawa bai ga komai ba.

” inside that leader sir ” tana nuna masa leadar dasu haydar suka bata. Leader ya dauko ya bude yana kallon abinda ke ciki. Cike da bacin rai ya dago yana kallonta ” what kind of jork is that? ” ya fada yana zazzage leader din. 

Cike da tsoro, take bin abin da yake zazzagewa da kallo lollipops ne 🍭🍬 da sweet.  Cike da mamaki take bin lollipop din da kallo. Ita tasan ko kurani aka bata zata dafa cewar maciji ta gani, but how ya koma lollipop?

Yan aji ne, suka fara dariya, waanda sukasha gudu, kuwa ransu ya baci, ganin yadda sukasha gudu a banza. Sai mita da korafi suke yi, hubby kam da mamaki ya gama kasheta, kallon ta takai kan haydar dake zaune  kafa daya akan daya, yana faman sauke murmushi. Kallon ta ta kai kan junaid, yayi saurin dauke kansa, alim ne ya daga mata gira tare da murmushin gefen baki.  ” Allah ya isa na, gudun da kuka sani” ta fada under her breath tana harararsu

Hakuri ta Fara ba teacher din, Wanda da kyar ya hakura, bayan ya mata bulala uku, sauran mukarra banta biyu biyu, Kafin ya barsu suka zauna.

                   ***************

Maganar auren hubby da yusuf ta tabbata, an tsaida lokaci dai dai danasu khulsum.  So ko wanne bangare Sai Shirye Shirye ake.  Fannin masoya kuwa abun baa cewa komai.  Don yanzu ne su hubby ke barge soyayyarsu,  wani irin so sukewa juna na ban mamaki,  tun mommy Hauwa najin haushin yadda hubby ke rawar jiki akan son yusuf, har ta dawo ta zuba mata ido, tana mai binsu da addua.  Tare da gyara yar tata, yadda ya kamata.

Ta fannin Mmn yusuf ma, hakurin da kaddara ta runguma, ganin hatta yayanta bai bata goyon baya ba, akan lamarin.  Hankalinta gaba daya a tashe ne, ba wai tana kin hubby bane,  tasan yarinyace mai nagarta, wadda ta fito gidan mutunci.  But matsalarta ta fito daga tsatson Hajiya,  wadda duk duniya ba wadda take kishi sama da ita, uwargida kuma mafi soyuwa a zuciyar mijinsu,  duk da adalcinsa, da kokarin boye filling dinsa akan matansa. Wannan yasa take kishin hajiyan sosai,  musamman ganin hajiyan bata fita da komai ba, a cewarta. sema ita da zata nuna mata kyan fiska, da ilmin Boko da wayewa. Mmn yusuf mace ce Mai kyau kallo daya zaka mata kasan ta hada jini da buzaye ko Fulani, farace fari mai daukan ido, ga gashi har baya baki mai laushi, akwai manyan ido farare, tanada hanci dai dai mai kyan tsari da madai dai cin baki, kallo daya zaka mata ka shaida kyanta, jikinta Dan daidai doguwacce mai murjajjen jiki, ita Ba lukuta ba ita ba siririya ba, ba laifi tanada kyan Kira dai dai ita.

Mmn samira Hajiya Amina mace ce mai matukar kyau cikakkiyar bafulatanar manbila. Farace sosai  tanada gashi dogo ga baki, akwai hanci har baka, idonta madai daita masu daukar ido, karamin baki, gashin idonta dana girarta gazar gazar Wanda suka Kara kawata doguwar fuskarta.  Gajera ce mai kyan diri.  Yayanta sunfi kowa kyau a gidan, in ka dauke yusuf da haydar da suke Kama da mahaifinsu.

Hajiya ba wata kyakyakyawa bace,  chocolate color ce, mai matukar kyan fata, da laushi, gashinta irin na hausa rober heir baki Mai dan tsowo, dai dai parking. rown face take da shi, mai dauke da ido madai daita sai hanci dan dai dai shiba nakushasheba shiba godo ba, bakinta karami mai dauke da red and black lips. Kallon farko baka gane kyanta, Sai ka kalleta sosai. The more kake kallonta the more kake kara ganin kyanta.  Ita ba doguwaba Ba kuma gajera ba,  akwai body na daukar hankali, don duk da girma ya fara kamata kallo daya zaka mata kasan Allah ya yi Kira a wurin. U can emerging kuruciyarta.  That’s Alhaji Jamal’s wifes.

                ******************

“Nace aba Hajiya karime aikin decorations kin ce aa, meye hujjarki na sa baki a abinda bai shafekiba,.?”  Hajiya ta fada tana huci

Mmn yusuf dake zaune a kan kujerar roba, a bakin kitchen. Ta dago tana kallon hajiyar a dage ” saboda na isa, yasa nace ba zaa bata ba, ina ita akaba contract din gidan professor wali, daga karshe me ya faru?  In banda kunya da akasha, don tana kawarki kawai Sai mu kashe kudi a banza ba biyan bukata?  To bazai yiyu ba “

Dariya Hajiya tayi Mai hade da shewa tana tafa hannu ” iko sai Allah, karki manta wannan ba abinda ya shafeki bane, iya karki ido,  bana son shishshigi tunda kudin baa aljihunki zai fito ba, don an samu matsala a wan can, bashi ke Nuna wannan ma zaa samu matsala ba. Nafa Dade da Lura da adawarki kan kawance na da Hajiya karima, to nan gani nan bari “

“miji nane, dole inyi iko dasu kamar yadda ya bukata, don bazan yadda ki mallaki naki ba, sannan ki dawo ki mallake nawa ba,  kamar yadda kike gulle gullen yi, to ki sani na Dade da gane plan dinki. Kuma it’s not work. “

” eh ehimmm!!!  Nan kuma kika nufa?  To zamu gani, tun wuri ki Kira decorator dinki ki bashi hakuri.  Maganar mallake yara kuwa ke har kina da bakin magana?  Amma ba komai time will tell “

Mmn samira ce ta fito jin haya niyar tayi yawa ” haba jamaa, wai ku bakwa gajiya?  Jiya jiya aka gama wani case din amma har kun fara kunno wani? 

“Da Kata, ” Mmn yusuf ta fada tana kallon Mmn samira ” kina ganin zan dauki, abunda ke zaki dauka ne?  Ba Wanda ya isa ya takani in kasa ramawa wallahi.  Kuma tunda mijina ya bani go ahead kan ragamar ocesions din da zaa ayi, banga wadda ta isa ta dakatar Dani ba. “

Kallon Hajiya Mmn samira tayi,  ganin yadda take cika take batsewa.  Harararta hajiyar tayi ” taya zan zuba ido ina gani, amin iko da baba kere.  Haka kurum, in gaskiyane me yasa baa dauraki a Kai ba sai ita?  Nasan kilbibin da munafurcin data Saba ne, yasa ya bata wannan damar “

” duk da haka, tunda ya bata ai shi ke nan, sai ki barta tayi abinda ya dace, bai kamata ku tsaya kuna sa insa haka ba, ba girmanku bane, ko don albarkacin wannan Sabon zumuncin da zai kullu a tsakaninku ya kamata ku manta da komai. Kudai kuyi fatan ayi taro lafiya a watse lafiya, a fita kunyar jamaar da zaa tara. “

” gaya mata dai,  munafurcin ma ai iyawane, in mutun ya isa yaje yasa a kwace , banda kaddara ma ni har yaushe!!!? “

Hajiya har ta bude baki zatayi magana, Mmn samira ta jata sukayi part dinta. Da harara Mmn yusuf ta bisu tare da tsaki. 

” Ba girmanki bane, kiyi kokari ki taushi zuciyarki, ki daina biye mata, kin san kadan take nema. “

” ta Yaya zai min haka?  Ya rasa wadda zai daura a kai Sai ita?  Ni nasan ba wani Abu bane Illa so take ta tozar tani cikin jamaa.”

” ki kwantar da hankalinki, zanyi Supervising in tabbatar bamuji kunya ba, ita ma nasan bazata fara ba, tunda fada take nema wurin shi. “

Hirar sauran Shirye shiryen daya rage suka fara, duk da har lokacin zuciyar Hajiya na zafi, game da hukuncin da mai gidan ya yanke, ba tare da shawartar suba.

               ******************

Fara exams din su hubby yasa ta samu sassauci, daga living he’ll din da haydar ya mayar da rayuwarta a wata dayan  da ya rage musu a school. Yanzu shakkarsa take, don yasa what he is capable of. 

Gashi duk abinda yake mata, ta kasa Kai kararsa gida, Don gani take taci baya. Aisha da junaid ma ido suka sa musu, don abun yafi karfinsu.

Bata manta ranar da abun ya isheta ta sameshi yana karatu a library.  Sai da ta gama masifeshi tas, ko dago Kai be yiba balle ya tankata. Haushi taji ta fige book din,  tana huce.  ” ka gama rainani after all I’m your senior sister  and I’m going to married your brother, so respect me for that” gyara zama yayi idonsa na kallon gefenta yana murmushin gefen baki ” wow!!! wow !!!wow!!! Ya kamata ace kina can kina duba books dinki, ba neman magana ba,  koda yake na manta, Zero head ce, no matter how u read u never understand. Ne man fada, tsokana, surutu shi kika kware a kai,, So please stop disturbing me, and give my book back, or else. “

” are you treating me? ” ta fada in high tone

” yes!!!!  And stop shouting at me, I’m not your kid “

” ina son ka sani, duk abinda Kake min baka ci bulus ba, no matter how sai na rama, I promise you that. Agric chicken kawai ” ta wurga masa book din tayi waje cikin bacin rai.

” zero head ……..” ya fada yana dariya kasa kasa. ya ci gaba da karatunsa…………   Shagali sosai akasha, inda naira tayi kuka, baki ta ko ina, tun daga kan gogaggun yan Boko, yan kasuwa da manyan yan siyasa na kasa.+

Mutanen Lebanon ma, baa barsu a baya ba, sun samu hallarta, maza da mata.

A babban masallacin sultan Bello aka daura auren duka, har na su hubby da Ahmad. Wanda aka samu fahimtar juna tsakanin waliyyan ango dana amaren. Don samun saukin zirga zirga.

An daura auren Ummu khulsum da zai’dul abidin,  ummu Aiman da Abdulmufassir, samira da Abu turab,  Yusuf da Habiba sai Ahmad da muna’ya.

Direct reception suka wuce bayan daurin aure, wanda aka shirya a sabon branch na eat more restaurant dake Unguwar sarki. 

Wurine yalwa tacce, da aka kawata shi sosai, gwanin sha’awa.

             *******************

Hubby chocolate color ce, fatarta mai matukar daukar ido ce, ga taushi kamar na kulba.  Doguwar fuska gareta, mai dauke da dogon hanci, mai kyan tsari,  idonta basu da girma, su kuma ba chines eyes ba, bakinta dan dai dai, mai dauke da siraran labba, masu walkiya, hakoranta a Jere farare masu dauke da siririyar wushirya sama da kasa, tana da yalwar gashin gira Dana ido da suka Kara kawata fuskarta.  Tanada yalwataccen gashin Kai, Wanda ke sauka har kafadarta. Baki Mai cika. Tanada madai dai cin tsayi, ita ba doguwa ba Ba kuma gajera ba.  Hubby akwai Kira ta daukar hankali, don ta biyo kirar su Hajiya,. Yatsun kafarta Dana hannunta dogaye masu dauke da fararen farce dogaye, kamar tayi piecing dinshi.  Hubby akwai kyau na daukan hankali, shi yasa mommy Hauwa ta saba mata da saka hijab, da dogayen riguna.

                ***************

“Wow!!!!!  Kin ganki kuwa?  Dole yaya na ya rude, irin wannan hadaddiyar beb haka ”  sulaim ta fada tana gyarawa hubby head dinta.  Murmushi hubby ta yi ” kin cika sharri duk kyauna na Kai kine? Tsoro ma nakeji kar mu fita a rasa amaryar a cikin mu. “

Dariya sukayi gaba daya,  yusra dake faman daukan su selfie ta ce ” ina ita ina kamo kyan Amarya,  ni kaina da ban sanki ba, na ganki ban iya ganeki, kinga kyan da kikayi?  Koda yake nasan harda rashin son kwalliyarki yasa muke Kara ganin kyanki, kin San Wanda baya kwalliya in yayi ba karamin kyau yake yi ba “

” wato kina nufin kice, hubby bata da kyau, makeup ne ya fito da ita? ” ido yusra ta zaro ” ke asima ki rufamin asiri, ni na isa nace hubby bata da kyau?  Ko makaho ya shafa ai yasan gidan kyau ya tarar. Nufina makeup din ya Kara fito da ita sosai.”

Dariya suka sa, suka ci gaba da hirarrakinsu, suna shiryawa, don ranar wuni ne.

Hubby sanye take cikin wani dakakken less, mai asalin kyau,  cotton yasha adon flowers da stones, kalar red and milk. Taklalmi, jaka, milk, sai head me hade dana yafawa milk and red. Maganar kyau da daukar ido baa magana. Sai glowing kawai take.  Haka yan matan Amarya kowacce taci ado, da ashobi,  na atamfar new edition. gwanin shaawa.

Part din saukar baki, na gidan aka bar mata ita da kawayenta.  Kayan ciye ciye fannin food, snacks, drinks, dessert gasu nan Kala Kala, sai Wanda ya maka.

DJ mace, suka Kira musamman tai ta sake musu sauti suna cashewa. A mai camera da video sunata aikinsu, hatta iyaye da Abokan mommy suma baa barsu a baya ba, wurin cashewa.

Phone Aisha B ta kawo mata,Bganin mai kiran yasa tayi daki da sauri inda ba jamaa.

” princess ina kika shiga, waya nata ringing? “

” sorry hayaniya yayi yawa ban jin ringing, phone din yana wurin Aisha B “

” OK.  Ya akaji da jamaa? “

” Alhamdulillah ” ta fada

” Masha Allah la kuwwata Illa billa.  Burinmu ya cika, now u are all mine, I’m yours. “

Murmushi tayi, ga kunyar da ta lullubeta. Jin muryarsa mai cike da jindadi. Daga ji yana cikin farin ciki, Mara misaltuwa.  Jin tayi shiru ”  answer me, mana.  I want to know how happy you are “

Murmushi tayi har yana jin sautin ta a kunnensa. ” shi ke nan, tun da rowar jin muryar ake min,  muna kofar gidanku, zamu gaisa dasu mommy, I want to see you, please ki dan leko in ganki. “

Dariya tayi ” this is not possible,  akwai jamaa sosai, bazan iya fitowa ba, ina jin kunya “

Murmushi yayi ” ba cewa nayi ki fito ba, lekowa nace kiyi “

” ba kyau leke fah!! ” ta fada tana murmushi

” who tell u that?  Don kin leki mijinki ai ba laifi bane ko,?  please I want to see you right now “

” sorry Yaya, I can’t “

” it’s OK, I know dama ni kadai na damu dake ” ya fada cikin dakewar murya

” is not true, sai ka shigo zakaga yanayin gidan, ba chance “

” it’s ok “

Jin yadda ya amsa ta tasan beji dadin hakan ba, yasa ta sauke muryarta cikin daddadar murya ” sorry Yaya kar kayi fushi dani. I’m sorry “

Murmushi yayi, yayin da yaji wani sanyi da natsuwa sun dirar ma zuciyarsa.  ” it’s ok, yanzu dai send me a pic of you, I miss you so much “

” right away, I miss you too ” ta fada cike da kunya.

“love you, sai mun hadu a gidana  yanzu ko? “

Murmushi tayi tare da saurin kashe wayar, don bata son ya tsokano wannan hirar, he is not a gentleman at all a wannan fannin, yanzu zai bata kunya.

Pictures ta tura masa, Kafin ta koma cikin friends nata, suka ci gaba da hidimominsu.

               *********************

An kai amare gidajensu, kamar yadda aka Saba, ummu kulsum ce kawai take gida, Sai washe gari zasu wuce Lebanon in da mijinta yake zama.  Ummu aiman gidanta na rigacukum, sai samira da aka kaita NNPC quarters, hubby da munaya millennium quarters dake malali.

Gidan hubby simple, cute and beautiful.  3 bedroom plat with 2 fallow. Kitchen da store a hade.  Ko wanne daki da toilet dinsa.  Sai main fallow ma da nashi toilet din. Ko ina yaji kaya na alfarma, masu tsada da nagarta. Don ba karamin kokari mahaifinta yayi ba, Hajiya Hauwa ma baa barta a baya ba, kana ganin gidan kaga gidan yar gata, don komai in higher class aka yishi.

Compound din yana da girma, mai dauke da dakin maigadi da toilet,  boys quarter’s 2 rooms with toilet.  Sai parking space, ga shuke shaken flowers masu kyau da kamshi.  Gida ya hadu iya haduwa, sai fatan zama lafiya.

8:30 suka fara Shirye shiryen tafiya dinner.  Da zaa Yi still a eat more restaurant.

Wurin ya kawatu, iyaka kawatuwa.  Hubby da yusuf ne karshen isowa a amaren.  Sanye take da code less light purple, sai head da Vail, dark purple, taklalmi da pose dark purple,  dinkin doguwar Riga, har tana Jan kasa, irin bridal style din nan, mai tsari da kyau. Tayi kyau har baa magana, ga dinkin ya Kara fito da ita, sosai.  Yusuf ma yasha ado da light purple shadda, mai matukar daukar ido, Tasha ado da zare dark purple, Sai cover shoe dark purple da hula, Masha Allah, kana ganinsa kaga cikakken balarabe.

Agogon I phone watch din dake daure a tsintsiyar hannunsa, ya kalla, a kalla sun kai 5min da isowa harabar wurin.  Amma damuwarsa yadda zai iya yadda su fita a haka. Don gaskiya yana ganin is a bad idea. Kallon hubby ya kara yi,  gaba daya jikinsa yayi sanyi, he knows hubby is beautiful, cute.  Bai taba ganinta a irin wannan dressing din, mai fitar da sura ba,  zai iya cewa shi dai yasan yana matukar sonta, hubby kusan ko yaushe yalwatattun kaya ne a jikinta, sau da yawa yana jin kannansa na mata tsiya,  ita goyon kaka ce, bata ko irin gayun nan na wayayyu,. Sai yau yagane hikimar yin hakan.  Tayaya zai iya yadda su fita a haka, mazan wurin su gama Kalle masa ita?  Tsananin kishinta ne ya karu a zuciyarsa. 

Gaba daya surar hubby ta tafi da imaninsa, wani mutuwar jiki yake ji, ga wani filling da bai San yana da shiba, Sai yanzu, dake Kara taso masa.   Kallon ta yake cike da so da kauna, hannunta ya kamo cikin nasa, Wanda ya haddasa musu gaba daya jin wani shock, laushin hannun ya Kara rikita yusuf.  Cikin kasa lalliyar murya yace ” princess Anya baza mu hakura da dinner din nan ba?  Gaskiya I’m jealous mutane su gama kallemin ke, I want teak it.”

Shiru tayi don gaskiya she is not comfortable, this is the first time da suka zauna so close da juna ita dashi, ga mayun idonsa dake kashe mata jiki ya zuba mata, Sai faman lumshesu yake. Zuciyarta da gangar jikinta rawa kawai suke yi, ko Kari take ta zame hannunta, don ji take Kamar wani Abu na bi ta hannun zuwa sassan jikinta.

Kwan kwasa window din motar ne, ya dawo da yusuf daga duniyar daya Lula, a hankali yakai kallonsa ga mai nocking din.  Engr Sahabi his best friend, a hankali ya sauke glass din motor.  ” what takes you so long, sauran angwaye da amare duk sun iso, ku kawai ake jira, kazo late kuma ka makale a mota, ” kallon sa yakai kan motocin dake Parke,  tsaki ya dan ja a hankali.  ” I think I have to go back home “

” what???? ” engr ya fada yana zaro ido

” I can’t take ku gama  Kalle min Mata gaskiya ” yusuf ya fada in serious

Dariya engr yayi harda rike ciki ” kai dai fadi gaskiya, kace ka kosa ka kebe da madam kawai,  stop acting Child dish please ” ganin da gaske tsakani da Allah yusuf yake yi, gashi sai faman hon ake musu, alamar sun gaji da jira daga amaren har kawayen Ba Wanda ya sakko a motarsa.  Yasa engr gyanan murya ” I understand u, ka zo mu shiga, in yaso sai ka tsare madam basai ta tashi ba, no dancing no greeting , it that OK for you? ” shiru yayi na Dan lokaci Kafin ya amsa.

” OK get ready, let me inform them .

Nan fah kawaye da abodan ango suka firfito, kowannen sun sha ashobi,  ko wanne,  kowanne kawayenta da kalan nasu ashobin. 

Kawayen hubby na sanye da code less ash sai head silver, silver shoe and pouch. Abokan yusuf sadda ash color black cover shoe.  Kwanin shaawa, suka nufo motar dasu hubby ke zaune. 

Yana rike da hannunta suka fito, abokansa da Nata suka rufa musu baya, kamar sauran amare da angwayen.

Tsaye suke jikin motar da suka zo da ita, a kalla sun kai ten, ko wanne yasha ado har baa magana (yara manyan gobe☺) ke nan haydar and his friends, sanye yake da boil light blue, janfa da Wando yasha aiki, sai black sandals anko sukayi shida junaid, sunyi kyau sosai.  Mu samman haydar.

” kai yayan kan nan ya iya yawa, fisa bilillah tun dazu munata faman jira, ya iso kuma fitowa ya gagara ” Hafiz ya fada yana duba agogon hannunsa.

Tsaki alim yayi, tare da danewa saman motar da sukaxo da ita.  ” kun San ni ban jure ma tsayuwa. Harka da gwaggo dama ai sai hakuri.

“Kai fa wulakancinka yawa ne dashi, ko ba komai kwa dinga min Kara, balle yanzu da take yayarmu ta bangare har biyu.  So stop calling her gwaggo. She is our anty know. “

” gaskiyarka junaid, dole mu koma Anty sama Anty kasa, kar muje gidan Yaya lomar tuwo tafi karfinmu, don nasan kadan daga aikin Anty. Tananan tana targeting din mu, she takes revenge on ours. ”  amir ya fada

Hafiz da Hafiz omer kam gaba daya hankalinsu na kan groups din amare.  ” wow what a nice couple ” Hafiz omer ya fada yana kara gyara zaman hularsa.

” kaifa Dan iska ne, watau har yanzu Hali nanan? ”  duka Hafiz omer ya Kai ma amir ” I will beat you, black and blue in ka kara kirana dan is. Naga I’m not different than u, ji yadda Kake faman lumshe ido kaga bebs” dariya sukayi baki daya, banda haydar da hankalinsa ke kan phone. 

” gaskiya ne, wannan da shine Lego’s boy da sai prayer ” alim ya fada yana dariya.

Haydar ne ya dago yana kallon yadda suke tama juna shegantaka suna dariya. Murmushi yayi ” let go duds ” ya fada yana yin gaba. 

Already holl din ya cika, da kyar suka samu table din zama da zai ishesu, don there in cepratable, A cewarsu.

Aisha ce tazo dai dai kunnen hubby ta rada mata ” kinyi wuta fa Matar yaya, every eyes is on u” murmushi hubby tayi ta kai mata duka kadan. ” u are joking with me?  Look ” ta nuna mata samira da ke gefen hagunta.  ” to tell you the truth, your the best ” ta fada tana kashe Mata ido daya,  let me, take selfie.  Yusuf ne ya harareta ” gulmar me like yi a nan? ” dariya tayi  ” sorry brother ” ta koma wurin sauran friends din su.

” a u ok?  Ya fada yana Kara dantse hannunta dake cikin nasa.  Murmushi tayi tare da kada kanta.

Dinner na tafiya yadda ya dace, duk yadda family and friends suka so su hubby suyi rawa ki yusuf yayi, gaba daya ya kasa ya tsare ya hanata tashi daga sit dinta, masu son pictures da ita, Sai dai su karaso nan.

” wai kai da WA Kake dariyar nan, I start to wonder, Anya kanka daya?  Or you are going nuts? ” Amir ya fada yana kallon alim.I’m pity my self, my dreams shattered in front of my eyes, I couldn’t do anything ” alim ya fada yana jijjiga kai.+

Gaba dayansu kallonsa suke, cike da mamaki, ganin yadda lokaci daya ya Koma wani abun tausayi. ” what happened dude? Don’t tell me u serious about it? ” Hafiz ya tambaya yana tsareshi da ido.

Murmushi yayi, mai ciwo. “I’m serious. I’m in love with her, I wish we are destiny to live together for ever “

” stop beating row the bosh, what is going on? “

” amir loves Anty hubby “

” what? 😱😱😱 ” kamar sun hada baki, suka fada suna zaro Ida nuwa.

Haydar kam murmushi yayi, yaja ashir, ” dud muje ka rakani in dauko Abu a mota” tashi yayi suka fita.

Murmushi Amir yayi, ” u never understand, tun da na fara ganinta, naji ta kwanta min a rai, behavior dinta na burgeni. Recently I’m totally sure I’m in love with her. Ina planning ina kaiwa 2Level zan yi proposing dinta, duk da nasan she is alder then me, yaya yamin over taking. ” ya fada gwanin tausayi 😥

” lallai kana dakon wahala, kai a tunaninka Anty ko kallonka zatayi? Kama manta wacece hubby? Da jarabar son girma? In ka manta bari in tuna maka ” ya makale murya yana kwaikwayon yadda hubby ke masifesu, wani lokaci can Baya ” yaran nan, bakuda mutunci, ina son kusan bakin rijiya ba wurin wasan yaro bane, don na Lura rainin hankalinku ya fara yawa. A haihuwar tumaki nayi jika daku, balle haihuwar kaji da nayi jika, tattaba kunne, harda ihi!! Hi!!!, don haka rai zai matukar baci wallahi kuka ci gaba da kawo min rainin hankali. In kunne yaji 🙉” ya fada yana rike kunne kamar yadda tayi, musu a lokacin. Gaba daya dariya sukayi harda shi kanshi Hafiz mai gwada war.

Alim ne ya dafa kafadar amir, ” sorry brother, Allah ya zaba maka wadda ta fita. Never mind “

Murmushi amir yayi ” thanks. Ba matsala tunda yayanmu ne, da bare ne danafi jin haushi. But know I’m happy for them, sun masifar dacewa. Luke at them ” ya fada yana kallon su

Dukansu kallon su hubby sukayi, ” gaskiya ba karya Antynmu ta hadu karshe, nima da zan samu irinta ai da anga jilali, dole a barni in shiga Daga ciki. Akwai sauran beb a gidanku? ” Hafiz Omer ya fada yana kallon junaid.

Harararsa yayi ” ba saura!! In kuna shirmenku don’t put me there. “

” Kyale yan banza, ne makon tunanin how we planned to achieve in life, sun tsaya suna shirme, soyayya ba naku bane yanzu, build your self, then you can go ahead ” haydar ya fada yana zama

“it’s true, but let’s us enjoy a little. Kalli waan can bebs din, tunda muka zauna suke faman kallonmu, let’s upper them a dance, nasan they want disappoint us, alim ya fada yana Dariya kasa kasa

Da gaske sun tafi da hankalin matasan yan matan, Wanda yawan cinsu family ne they know them well. Yanayin shigarsu da girman jikinsu Kai ka rantse wasu manyan samari ne, sai ka Kalli idonsu da yanayin hirar zaka gane there young adults.

Duk yadda yaso kaucewa shiga filin rawa, bai samu haka ba, don sister’s din Mmn yusuf suka tasa shi gaba dole suka Dan cashe, tare da daukar pictures da amaren da sauran jamaa.

Yana makale da ita kamar wani zai kwace masa ita. Gyalenta na zamewa da kansa yake faman gyara mata shi, duk da yasan ba wai yayi duhun da zai Hana hango komai bane, but ya taimaka ko ba komai.

Gaba daya hubby a takure take jin kanta. Musamman kusancin da jikin ta Dana yusuf ya samu, gaba daya ya saukar mata da kasala, wanda a wurin yusuf shi kadai yasan yadda yake yaki da gangar jikinsa da zuciyarsa kan yadda yake ji.

“Masha Allah, yusuf kam ya dace mata wallahi, dole yaro ya rude, irin wannan tsaleleyar yarinya haka. ” harararta daya Matar dake kusa da ita tayi. ” ke kam Hajiya ai baki da zuciya, yaron da Kiri Kiri yaki yarki, amma har ke ce da fadar irin wannan magana,? Ai wallahi abun yamin ciwo sosai, har me wannan zata nunawa nafisa? “

Dariya wadda aka Kira da Hajiya ai tayi ” dadina dake sakina rashin lissafi, shi aure ai nufin Allah ne, matar mutun kabarinsa, Allah ya yi ba mijinta bane, sai ku tayata da addua itama Allah ya fito mata da nata mijin, ni kwata kwata wannan Abu bai dame ni ba, tunda dama bawai shine da kansa yace yana sontaba”

Tabe baki Sakina tayi ” Allah ya kyauta, da zakiji shawarata da kun tilas ta masa ya aureta ita ma, don gaskiya naso wannan hadin, zai Kara dankon zumuncinmu sosai”. Matar dake can gefe duk hirar da suke suna sauraran su. Ta gyara zama ” banda abinki Sakina ai, abinda Hajiya ai tayi ce shine kan hanya, ina amfanin badi ba rai? Itama Allah ya bata Wanda ya fishi,.” “Amen ” sauran matan suka fada baki daya.

Dattijiwar cikin su ta ce ” kar ki mata bakin shiga gidan kishiya, kishiyar ma jinin Hajiya. Sanin kanku ne daba dan kaddarar Allah ba, da ba abinda zai sa Alhaji Jamal Kara aure. Ki Kalli yariyar nan da kyau, irin su ake Kira mowar mata, Matar da bata bora a gidan miji, hada miji da irinsu sai ka shirya. Saboda sun hada duk abinda namiji ke bukata ga mace, Wanda samun irinsu sai an tona a cikin mata. Tabbas yusuf yayi gamo da katar ya dace da mata daya tamkar da dubu. Allah ya sa halin yafi surar kyau don ya more rayuwar aure, mai dorewa. “

Da sauri ta kusa da ita ta hayayayyako cikin bacin rai ” innani ai dama na dade da sanin kina adawa da hadin yusuf da nafisa, na fada aka ce Ba haka ba, gashi yanzu anyi walkiya kowa ya ganki, in Hajiya ai na Kara ma dan yaruwar miji, ke kuma fah? Karki manta ciki daya kuka fito da mahaifin yarinyar nan? Har me waccan zata nunawa nafisa? Da kika zage kina yabonta haka? Kowa yasan Hajiya da asiri ta mallake Alhaji Jamal, ba wani Abu ba, amma ita kanta da me tafi sauran matan nasa? Hajiya saa dai ta Riga tayi sake, yanzu kuma Sai dai taji da sauran yaran, don na tabbata yanda basu bar uban ba Ba zasu bar dan ba. Tun yanzu ma Kalli yadda yake rawar jiki, kamar wani sallamamme,.”

Nan fa table ya dauka baki daya, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Hajiya ai kam da innani shiru sukayi suna kallon ikon Allah.

Kuka sosai take, yusuf na gefe yana faman lallashi, tun da sukayi sallama da family and friends dinsu, take faman kuka. Don daga wurin dinner kowa zai Kama gabansa angwaye zasu dauki amarensu. Friends din yusuf suka ne zasu mai da kawayen hubby gidajensu, tun da taga kowa ya Kama gabansa ta fara aikin kuka.

Har suka iso gidansu, tana faman kuka, shi kansa yusuf ya rasa yadda zaiyi da ita, da kyar ya samu ta fito daga motar, yana rike da hannunta suka nufi cikin gida. Direct dakinsa ya wuce da ita, ya zaunar da ita a bakin gadonsa, tsugunnawa yayi a gabanta hannunsa duka biyu cikin nata, ya zuba mata kyawawan idonsa.

” princess please stop crying, na dauka yau ranace ta farin ciki a gare mu, why do you want to spoil it for us? ” hannunta yakai kan kirjinsa ” zuciyata bazata jure jin kukan kiba, kiji yadda take faman bugu, in kuma nima kukan kike son nayi to? ” kanta ta kada a hankali, hawaye nabin kuncinta.

” to ki daina kukan haka, in ba haka ba depenetly nima kukan zanyi,” zama yayi ya jawota jikinsa, ya fara share mata hawayen. “see how u spoiled your face, look at your eyes? ” zafin da yaji a goshinta ga jijiyoyin kanta sun fiffito yasa ya tabbatar kanta na ciwo, “kinga abinda kika Jawa kanki, jikinki yayi zafi, I’m sure kanki na ciwo.

Lamo tayi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, don wani ciwon Kai da zazzabi zazzabi take ji. Tun baaje ko ina ba ta fara kewar gida. Ji take kamar tace ya maida ita gida ta fasa auren.

Kwantar da ita yayi, ya shiga toilet ya hada mata ruwan wanka, ya cika bap din ya zuba turaren wanka, da bobble liquid soap. Nan da nan toilet din yadau kamshi.

Ya fito ya samu har bacci ya fara daukarta. Tashinta yayi taje tayi wanka. A hankali ta Mike ta nufi toilet din. Kayan baccinta ya ajiye mata saman bed, ya kwashi abinda zai bukata ya nufi daya bed room din don ya shima ya kimtsa.

Masha Allah toilet din ya mata kyau sosai, white and gold. Gashi wadatacce, ban da bap ga Jacuzzi, duk Wanda Kake bukata,.

Ta dade a cikin ruwan, Kafin ta samu tayi wanka, don ruwan ya Mata dadi, ga kanshi mai sanyaya rai.

Ganin baya dakin, Yasa ta samu damar sakewa ta shirya. Rigar daya ajiye mata ta daga tana kallo, ” not bad ” ta fada tana murmushi. Cotton ce, tsawonta zuwa gwuiwa, Mai hannun brazer, sai cup da akama ado da wani silk and less mai daukar ido. Rigar farace kal. Bayan ta sa ta feshe jikinta da body splash, deodorant, perfume masu matukar kamshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *