DA KAMAR WUYA CHAPTER 2 BY ZULAIHATIDRISMISAU
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana rungume da ita, sai faman sauke ajiyar zuciya yake, ga wani annuri daya cika fuskarsa. A hankali yake tapping din bayanta, tare da yi mata kiss saman goshinta.+
Gaba daya jinta take kamar a sama, jikinta ko ina yayi tsami, ajiyar zuciya take, zuwa lokacin hawayen sun riga sun kafe daga kwayar idonta. Iyakar wahala yau kam tasha ta, duk da dauriya da juriya da tayi, dole ta gaza. Don gaba daya yusuf yayi losing control dinsa.
Baccine ya dinga fizgarta a hankali, in no time ta shilla 😴 ajiyar zuciya yayi, ganin bacci yayi gaba da ita. Kiss ya mata tare da kyara matakwanciya a jikinsa, ya Kara rungumeta Kamar zaa kwace masa ita. Murmushine ya subuce a fuskarsa, kansa ya dan shafa, tare da kara godiya ga Allah, daya kaddara masa samun hubby a matsayin matarsa, tabbas ba karamin baiwa Allah yayi masa ba, da samunta cikin rayuwarsa.
Duk yadda yaso bacci ya daukesa amma ina Abu ya gagara, still wani sabon filling yake ji yana taso masa. She can take it, yasan tayi hakuri dashi,, he don’t want to hurt her. He has to control him self. Shi kansa bai San yana da bukata haka ba, sai yau. He have 3 row supper, but still filling for it.
Sai gab da asuba, bacci mai dadi yayi awon gaba dashi, hakan yasa suka makara. Sai 6 ya bude idonsa a hankali, bakinsa dauke da adduar farkawa daga bacci. hasken da gari ya fara ya hango ta labulen window. ” subhanallah ” ya fada under his breath, rabonsa da missing sallah a jam’i har ya manta when last yayi sallar asuba a makare.
Kallon ta yayi, murmushi yayi, har lokacin tana manne a kirjinsa, she sleep like child. A hankali ya gyara mata kwanciyarta, ya nufi toilet.
Tana jin lokacin da yake gyara mata kwanciya, don tun da ya farka itama ta farka, amma bata son ya gane idonta biyu, don bata San da wane ido zata kalleshi ba. Tana jin karar Kofa alamar ya shiga toilet. Ta bude idonta tana bin dakin da kallo.
Kokari tayi ta Mike, da kyar don duk da ruwan zafin data shiga at night, still. Jikinta gaba daya ciwo yake, musamman kasanta. Din gisawa tayi zuwa dakinta, tana Mai zubar da hawayen azaba. Don duk taku ji take har kwanyarta.
Ruwan dumin ta Kara hadawa, kamar yadda ya hada mata da daddare, ta shiga tana mai Kara fashewa da kuka. Hubby akwai raki, bata son duk wani Abu daxai taba lafiyar jikinta☺.
Koda ya fito, yaga bata dakin, kasa tada sallar yayi, ya nufo dakinta, don tabbatar da lafiyarta. Jin motsin ruwa a toilet ya nufi kofar, amma to his surprise tasa key. Murmushi yayi, ya Kama kan carpet din sallah dake dakin ya kabbara sallah.
A hankali ta fito, tana din gisa kafa. Wood rope ta nufa ta, dauko doguwar Riga arebian da hijab. Sai da ta gama kimtsawa still tana share hawaye da cije lips duk lokacin da tayi taku. Juyowar da zatayi sukayi idon hudu, da sauri ta dauke idonta, ziciyarta na bugawa da sauri da sauri. Wani kunyarsa da tsoronsa ne suka cika zuciyarta. Kasa motsawa tayi daga inda take.
A hankali ya tako inda take, rungumota yayi zuwa jikinsa, tare da sauke ajiyar zuciya. Sumbatarta yayi saman goshi, sannan ya dauketa bridle style zuwa kan abun sallar.
Ganin ta kabbara sallah, ya nufi kitchen kettle ya jona, tare da hada kayan tia a wani hadadden trey, yayi worming gas meat, ya zuba a wani hadadden bowl. Koda ya shigo already ta idar da sallar, ta koma ta kwanta.
Kujerar mirrow ya janyo gaban bed din ya daura trey din akai. Shigowarsa yasa hubby Kara dukun kunewa wuri daya.
Rungumota yayi jikinsa ” princess!! Tashi ki sha tia, ko zaki Kara jin dadin jikinki.
Kuka Mai karfi ta barke dashi, tana Kara shigewa jikinsa. Lallashinta ya hauyi, cike da so da kauna, dakyar ya samu tasha tia din, ya bata pain killer. Kwance suke yana rungume da ita, kalmomi masu dadi, yake gaya mata, tare da shafa kitson dake kanta.
Har a zuciyarta tana jin dadin wannan yanayin da suke ciki, tare da jin dadin kalmominsa, na nuna soyayya, da yabo gareta.
Cikin muryarta Mai sanyi tace ” dama haka aka nuna ma mutun soyayya, a kusa kashe shi? “
Murmushi yusuf yayi ” hakan ma ai duk cikin soyayyarne princess, da kin san yadda matsayinki, da kimarki suka Kara karuwa tsakanin jiya da yau da ke da kanki zaki ce a maimaita ” ya fada yana dariya kasa kasa
Share hawayenta tayi ” Allah ya kiyaye, wallahi ni auren ma gaba daya na fasa, don bazan yadda ina ji ina gani ka kashewa gwaggo niba”
Kara matseta yayi ganin tana kokarin kwace kanta.
” waya ce miki aure na kashe mutun? Ko kin taba ganin wanda aure ya kasheshi? “
Tura baki tayi, cikin shagwaba ” gani!!! Numfashi ne kawai ajikina, meye ban banci? Ni ka kiramin gwaggona, in ganta Kafin in karasa. “
Dariya yayi cike dajin dadi ” don Allah karki tafi ki barni, kinga ban gama shanye zumana ba, dan taimaka ki Kara min koda rown daya ne .”
Kuka ta Kara fashewa dashi, tana yarfe hannu, bayan ta kwace jikinta dakyar ” wallahi ban yadda ba, dama tun jiya nasan ka daina sona, shi yasa ka gana min irin wannan izayar, duk bai isa ba Sai ka kara sa sauran dan numfashin da yayi saura a jikina? Allah na fasa auren ka kiramin gwaggona nace “
” me zaki ce mata in na kirata din? ” ya fada yana dariyar ganin yadda ta tsure.
” zuwa zatayi mu tafi, nasan baza ta yadda ka kashe mata jika, a banza ba “
” ke yanzu kina tunanin akwai abunda zai rabaki da yusuf? Ni dake mutu ka raba, takalmin kaza. Gwaggo kam taji abinda yasa kika sa a kirata fada zaki ci, ni kuma in sha yabo, don I’m good taken care of u. “
Ya fada yana mata dariya
Haushi ne ya cika hubby ganin yana mata dariya. Ga kafarta ta rike, jikinta ya Kara tsamin. ” please and please ka kiramin ita, na yadda tamin fadan, mutuwa zanyi ” yayi dai dai da durkushewar da tayi a tsakiyar room din,. Tana zubar da hawaye
Da sauri ya nufo wurinta, dagota yayi zuwa bed din ” I’m joking, ba abunda zan sake miki, me yake damunki yanzu?” Kamar bazata tanka shi ba cikin jan hanci tace ” wurin na ciwo, kafata da jikina ko ina ciwo, ta Kara fashewa da kuka. “
Lallashi sosai yayi, da kyar ya samu tayi shiru. ” Bari in sake hada miki ruwan dumi, ki shiga, zuwa an jima in ba wani improvement dole muje hospital a dubaki sosai. Very sorry I’m at fault “
Ganin ya nufi toilet din, ta janyo wayarsa dake kan bedside drawer numbar gwaggo tayi dialing, bugu biyu muryar gwaggo ta cika kunnenta..
******************
Wasu kam basu more aure ba, wallahi. Allah ya kyauta, a ce gari ya waye tun dazu, yanzu kusan karfe 7 na safe amma mata bata fito don kimtsa gidanta ba, balle nemawa mijinta abunda zai ciba. An bar komai hannun yan aiki. Wallahi da ba daon gudun bacin ran malan ba, ba abunda zai Hanani yima wannan yaro aure, har yaushe zaka zauna da mata, komai Sai yan aiki zasu maka, ita tana can tana faman gantalin aiki, in ma tana gida ba abunda zata tsinana na ayyukan mata a cikin gida.
” wai gwaggo ke da wa kike faman mita da safen nan?” cewar daya Matar dake kwance kan katifar kusa da gadon da gwaggo ke kwance.
Tsaki gwaggo tayi ” lamarin rayuwar gidan nan ke damuna, duba kiga gida cike da baki, amma matar nan ta lunkume a daki, Sai yan aiki keta hidima, ko ba komai ai ta fito ta kula da kowa ya samu kulawar daya dace”
Tashi Matar tayi ta zauna tana gyara zaninta daya yaye ” ki gode Allah, ko ba komai Alhaji bai taba kawo miki karar iyalinsa ba, ko ba a fada ba suna zaman lafiya. Bazan boye miki ba wani lokaci ina kishinki, ganin yadda Alhaji da iyalansa suke kyautata miki, ga jikokinki Masha Allah. Ni kuwa yanzu yaushe rabon nawa dan yazo inda nake, in ban manta ba yayi wata uku, Sai aike, bani da ikon zuwa gidansa, daga ni har yan uwansa, saboda wulakanci da izzar matarsa. Rabon matarsa da kankiya tun bikin auta na, yau shekara ta hudu ake nema, haka yaransa. Ke fah!? Duk Hutu suna tafe, baa cikakken wata uku bai kwashi iyalansa sun zo muku weekend ba. Ina rokonki daki dauke idonki kan rayuwarsu, karki manta yan Boko ne, kuma yan zamani, rayuwar ta ban banta da ta da. Ba komai ki dubi tarbiyyan yaran, Masha Allah basu da aibu.”
numfashi gwaggo taja ” duk Abinda kika fada gaskiyane, ni aikin nan da take fita ne kawai ke cimin tuwo a kwarya. Yaron nan nada arzikinsa dai dai gwargwado me zai Hana ta zauna ta kulamun dashi da jikokina.?
Murmushi Matar tayi ” let dai ki zuba musu ido, ki bisu da addua “
” Sai nayi magana Kafin in tafi, don nakai makura “
Kada Kai matar tayi tana murmushi sanin halin gwaggo na kafiya “ai shi kenan ” ta fada
“yar albarka na can ko ya take? Gaba daya yau ban iya bacci ba, hankalina na wurinta. “
Dariya Matar tayi ” ke kam da takwararki sai a hankali, ana can ana cin amarci “.
Wayar gwaggo ce ta hau Kara, kasan cewar Bata iya karatuba, alamamomi ne ake sa mata akan numbobin, Wanda yake taimaka mata wurin gane mai kiran. Hoton yara ukun da ta gani yasa tayi murmushi cikin jin dadi ta daga da sauri. ” yan halas Sunki ambato. ” Salamu Alaikum ” gwaggo ta fada
Jin muryar gwaggo, hubby ta fashe da kuka, tuni hankalin gwaggo ya tashi, cikin kidima ta hau tambayarta lafiya.
Cikin muryar kuka tace ” don Allah gwaggona kizo, zan mutu ” ” subhanallahi mutuwa kuma? To to!!!! Gani nan ” ko Kafin ta karasa hubby ta kashe wayar.
Mikewa tayi, ta Zari gyale, already tayi wankanta, don ta Saba tana sallar asuba take wanka, Kafin ta fara aikace aikacenta.
” ba dai gidanta zaki tafi ba, da farar safiyar nan? ” matar ta fada tana kafeta da ido
” hafsi kenan, ina naga ta zama? “
” Sai naga bai dace ba, ki je gidan yanzu. “
Harara gwaggo ta zuba mata ” se ki rike kafata ai. Yarinyar ta kirani Tana kuka, in kasa zuwa Inga dalili? “
” sabon aurene fah? Wane dalili kike nema banda hakan? “
” Sai kiyi kuma hausi, ni na tafi, in sauran sun tashi ban ce ki fada musu inda naje ba “
Da kallo hausi ta bita har ta fita a dakin.
Kitchen ta nufa, maaikata na ta faman hada break fast. Gaisheta sukayi, cike da girmamawa, don sun San matsayinta a gidan. Daya taga tana hada abinci a kan wani hadden trey.
” wannan fah? Ta tambaya
” abincin Alhaji ne ” ta Bata amsa cikin girma mawa.
Tabe baki tayi. ” kuna da wandon Dakar abinci ko? ” shiru yarinyar tayi don bata gane abinda gwaggo ke nufi ba.
Dayar ce tace akwai, taje ta dauko. ” shirya min waannan kwanukan a ciki ” tana nuna abincin da aka shirya na Alhaji.
Cike da jimami yarinyar ta Fara jerawa a basket din.
” kwa dafa mishi wani, dauki muje ki rakani wurin mota, Allah ya sa drevan naku yazo.”
A bakin kofar kitchen sukaci Karo da mommy Hauwa. Cike da girmamawa ta gaishe da surukar tata.
Ganin zata fita, ga yarinya da basket na binta. Mommy Hauwa ta ce ” fita zakiyi ne?
Yatsina fuska tayi ” eh!!! Saina dawo, kya nemawa mijin naki abinda zaici, don nayi gaba da nashi ” murmushi mommy Hauwa tayi tare da cewa ” adawo lafiya ” ta shige kitchen din.
Jafar, jabir da wasu daga cikin baki mazan da basu koma ba. Suna zaune kan kujerun compound din, da baa kwashe ba, Har lokacin.
Bayan sun gaisheta, tare da Wasa irin na jika da kaka. Ta Kalli jafar ” solobiyon mijina muje, ka kaini unguwa ” gaba daya kallon jafar sukayi suka fashe da dariya.
Harararta yayi ” nemi direbanki, ni kam bacci zan tafi nayi.”
“baccin lafiya, da ranar nan? Har yaushe ka tashi da zaka koma? “
“oho dai ban zuwa ko ina ” ya fada ya nufi cikin gida
Da kyar ta samu jabir ya yadda zai kaita.
Sai da suka fito, ya kalleta ” ina zan Kai kine, ranki ya dade? “
Murmushi tayi ” gidan takwara ” wani uban burki yaja, da badon Safiya bane da ba abunda zai hana Karo.
Ganin yana kokarin juyawa ta bata rai tare da rufeshi da masifa, harda cewa ya kuskura ya maida ita gida, to ubansa ne zai kaita da kansa.
Sanin halin jarabarta yasa ya nufi gidan hubby rai bace. Da lamarin gwaggo da hubby.
” ai sai ka dauko kwandon ka biyoni ” ta fada tana maka masa harara, ganin yadda yake cika.
A kofar shiga ya ajiye mata kwandon ya juya abinsa, tana masa maganar ya Jirata kar ya tafi. Shiko Allah Allah ya bar kofar gidan Kafin yusuf ya fito. Key yayiwa Motarsa ya yi gaba.
Tsaki gwaggo tayi ” kai ka sani kuma dai “
Door bell ta dan na kusan sau 5, ta dan dade tsaye kamar baza a bude ba, can taji karar bude key, tsayuwarta ta gyara…………….Duk yadda taso ya barta tayi wankan da kanta ki yayi, tana noke noke ga hawaye shabe shabe, tana ji tana gani ya zaunar da ita cikin bap din wankan.+
” naga alama yau dinnan hawayenki zai Kare, kuka tun jiya yaki karewa ” ya fada yana murmushi
Harararsa tayi, zuciyarta cike da jin haushinsa.
” kika sake hararata, zamu hadu yanzun nan ” ya fada yana kafeta da mayun idonsa, masu rikitata. Sunkuyar da kanta tayi, tana Jan hanci.
Da kansa ya mata wanka, ya nadota a towel kamar wata baby. Futowarsu a toilet din yaji kamar door bell na ringing. Ajiyeta yayi, saman kujerar dressing mirror. ” I’m coming princess ” ya fada yana barin dakin.
Ganin gwaggo tsaye bakin Kofa, ya cika da mamaki, cikin girmamawa ya bata hanya ta shigo, tare da karbar basket din hannunta.
Cike da kunya da jin nauyinta yake gaisheta. Itam ma cikin sakin fuska ta amsa tare da tambayarsa hubby.
Yana gaba tana baya, har dakin hubby da tun fitar yusuf ta kifa kanta kan dresser din, tana sauke ajiyar zuciya. Sallamar gwaggo yasa ta dago da sauri. Mikewa tayi ta fada jikin gwaggo tare da sake sabon kuka.
Sum sum sum yusuf yayi waje, yana murmushi, tare da jin jina shakuwar hubby da gwaggo. Yau kam ya yadda da son jiki irin na hubby. Hirar su Hajiya ce ta fado masa a rai. Inda suke hirar halayyan yaran family dinsu. Hajiya ke cewa ” ai ni kinga habiba da Aisha ba mai sani rakasu labour room, sai dai ke, tana nufin Mmn samira, kuje tare. Yara sai son jiki, basa son komai ya taba lafiyar jikinsu? Dazu da naje gidan gaba daya Habiba ta hargitsasu da koke koke, wai ta yanke a hannu. Na dauka zanga wani katon yanka, sai naga yan kan ma ba wai ya shiga bane, jinin da ta gani ne, duk ta rudasu da kuka, kamar yadda Aisha ke wannan iskancin a gidan nan. ” murmushi ya Kara yi, tare da shigewa wanka.
” ai ni kin ban tsoro takwara!! Mutuwa fa kika ambata min, kin sani fitowa ba shiri “
Baki ta tura cikin shagwaba, ga hawaye ta ce ” numfashine fa kawai ajikina, gara kizo in ganki Kafin na mutu. “
Dariya gwaggo tayi ” baza ki mutu ba Sai kin santalo min kyawawan tattaba kunne. Allah ya miki albarka da kika tsare mana mutuncinmu, kika kawo budurcinki dakin aure, ni kam kin gama min komai. “
” kafata kafarki, bazan yadda a kashe miki niba. Dama ke kika zugani in ce aure nake so, na dauka auren dadi ne ai? Ashe anani burdade ake ci. Kuma a haka kice kina sona? ” ta fada cike da shagwaba
” gatan kenan takwara, da kin warke shi kenan, na dan lokaci ne. Yan zu dai Bari kiga ” ta nufi toilet
Harararta hubby tayi ” kiji mata wai na Dan lokaci, bayan duk ke kika jamin ina zaman zamana. In da nasan dawan garin ai da sai dai mu karaci soyayyarmu a gida, in da ko hannu na bazai iya rikewa ba, balle.
” tashi muje ki gani ” ” wayyo Allah na yanzu fah na fito daga wanka “
” ke dalla rufamin baki, muje ” ta hade rai. Dole hubby tabi bayanta tana dana sanin kiranta.
Ruwa ta hada mata, da wasu itatuwa. Sai da ta tabbatar ta zauna Kafin ta fito. Ta barta a toilet din.
Dube duben inda zata ga kasko take, bata gani ba, ta koma ta tambayi hubby.
Gawayin kanti ta hada a kaskon, ta dauko kujerar dorot ta daura a kai, hubby na fitowa ta zuba wani gari a ciki mai azabar kamshi, Tasa hubby zama a kai.
” da nasan kema izayar da zakimin ke nan da ban kira ki ba ” hubby ta fada tana kunbure kumbure.
Murmushi gwaggo tayi ” yanzu ya kikaji jikin naki? “
Shiru ta mata, amma har ga Allah taji dadin jikinta, zata iya cewa ma ta daina jin ciwon da take ji a kasanta. Sai abunda baa rasa ba.
” tashi ki shirya, kwalliya nake son kiyi sosai. Bari in dauko abincin da nazo miki dashi.
Baki hubby ta washe jin harda abinci gwaggo ta kawo mata, duk da bata jin yunwa.
Super exclusive mai launin brawn and black, Sai shade din light yellow. Dinkin Riga da skeet 8 pierces dinkin ya zauna cas a jikinta, kamar wata yar tsana don kyau. Jelar kitsonta da suka sakko har kafadunta ta tattara ta daure da ribbon. Simple daurin Dan kwali tayi. Da simple makeup, tayi kyau sosai, ga kamshin turaruka da humra dake tashi a jikinta.
Washe baki tayi ” Masha Allah, in ce ko kina gode Allah bisa wannan sura da ya miki ” kallon gwaggo tayi tana murmushi
Gwaggo ta Kara da cewa ” abinda nake so dake shine, hakuri da juriya, duk mace da kika ganta a gidan mijinta ta kwashe shekara da shekaru to ba komai ya Kawo hakan ba Illa hakuri, juriya da jajircewa. Yanzu ne zaki natsu ki gane me dame mijinki yafi bukata a tare dake, don ki Kara in ganta zamanku. Tsafta kula da jiki, kula da muhalli, tsaftar kitchen dinki da duk abinda zaa sarrafa a cikinsa. Tsaftar ban daki, da uwa uba turakar miji. A kalla kina samun wanka Kamar sau uku, zuwa biyar a Rana, na safe Kafin ya fita daban, na rana daban, sannan na dare watau na tarbar megida. Don Allah takwara ban da son jiki, nasan baki da kazanta, ki Kara dagewa, San nan kar ki yadda ki nunawa miji gazawarki ta wurin daukar nauyin bukatarsa. Ki zama me juriya. Ki dage ki koyi girki nasan wannan uwar taki bata koya miki komai ba. Kin dai san gidan da mijinki ya fito. Kowa yasan akwai cima Mai kyau a gidan Jamal,. Karki biyo uwarki da komai Sai masu aiki zasuyi. Don in baki dace da suruka Irina ba, tuni zata auro masa wadda zata kula mata da danta da kyau. Ko ta tasa min ke a gaba da rashin mutunci. “
Murmushi hubby tayi ” nifa ban son kishiya, naga kema baa miki ba, kike min fatan amin” ta fada tana tura baki
“ba fata na miki ba, amma kika sake kikayi halin hauwa, kin hadu da kishiya kin gama yarinya. Ki zauna gidan mijinki ki kula da mijinki da yayan da Allah zai azurtaku dasu. Mijinki Nada halin da zai kula da duk bukatunki, in ma kina bukatar wani abun ne, GA Sana oi nan da zaki iya yi a gida, sun isa basai kin wahalar da kanki ba. “
Shigowar yusuf ya katse musu hirar. Sanye yake da lallausan voil fari kar da hula wadda ta dace da kayan sosai. Kana ganinsa kaga balarabe sak, haskensa ya Kara fita sosai, ga wani kamshi Mai dadi da San Yaya rai na tashi.
“Yau wa, zo kaci abinci ” gwaggo ta fada tana janyo masa basket din.
Murmushi yayi, tare da zama a bakin gadon, hada ido sukayi da hubby dake kwasar farfesun Kayan ciki. Murmushi suka aikawa juna, yayi mata blowing kiss. Sunkuyar dakai tayi ta ci gaba da cin farfesunta. Ya mata matukar kyau da kwarjini, wani Karin son shi taji ya na bin jinin jikinta.
Shi din ma haka, ya kasa dauke idonsa a kanta. Duk da kokarin saita kansa da yake, tayi kyau sosai, komai Masha Allah. Beyond what he expected.
Nasiha gwaggo ta musu mai shiga rai, Kari kan Wanda aka musu.
Mika masa wayar tayi ” Kira min wannan mai ranta memen kan” mirmushi yayi don yasan Wanda take nufi. Saida ya Kira sau biyu tukunna aka daga, ya Mika mata.
” to dan nema, zaka zo ka dauko nine ko na Kira tsohonka shi yazo? “
Hararar wayar yayi kamar gwaggon na gabansa.
” kirashi man, sai me? “
“au!!! Haka kace? To shi ke nan ” ta kashe wayar.
” Dani kake magana, ta fara lalubar number daddy su hubby. Kira ne ya shigo wayar, yasa kiran daddy katsewa.
Dagawa tayi, muryar jabir ne ” gani nan zuwa ” ya fada Kamar zai fashe da kuka
” Dan nema, da karka zo man “
” da baki kirashi ba, muje in mai dake “
” aa, barshi yazo, Dani yake magana ai. Ina ni ina fitar da ango daga gidansa. ” ta fada tana kokarin tattara wormers din. Da sauri hubby ta karbeta ta jera mata su.
“ina kika samo wormers masu kyau haka? ” hubby ta tambaya tana juya karamin.
” abincin ubankine nayo gaba dashi ” daga hubby har yusuf tsayawa sukai suna kallon gwaggo. Cike da mamaki
” to shi kuma yaci me? Hubby ta tambaya
” wan nan ruwansu kuma ” tayi ficewarta daga dakin
Da kuka suka rabu da hubby, Sai da ta mata alkhawarin sake zuwa dubata Kafin ta koma tukunna,.
******************
Gaba daya ranar a cikin baki suka yishi, masu zuwa Ganin dakin Amarya. Tun daga ranar hubby ta San akwai babbar matsala tsakaninta da dangin Mmn yusuf, don da yawansu sun kasa danne kishinsu gareta.
Sai yamma can, su yusuf suka tafi bangajiyar surukai, yabar su yusra suna taya hubby gyaran gida.
Nocking sukaji, suna tsaka da gyaran falo. Asiya ce taje ta bude.
Hayder, junaid, alim, amir, Hafiz da Hafiz omer. Kayayyakin cefane sukai ta shigo dashi da su bottle water, drinks, juices.
A kitchen suka jibge musu. ” a taimaka a shigar dasu store mana ” Aisha ta fada tana kallonsu, sunyi dai dai a falon.
“aikin me kuke dabaza ku shiryasu da kan kuba? Mu kam munyi namu, ya rage naku kuma, in kun so ku barsu a wurin ” Hafiz ya fada yana kallon ta
Harararsa tayi ” dadin abun ba kutare muke ba “
” na dauka ai kutarene “
” ina wuni yayarmu, suka fada a tare, banda haydar dake danne danne a wayarsa.
Suka fara gaishe da hubby data fito daga daki.
Amsawa tayi tana murmushi, tare da tambayarsu gajiya.
” Asiya kawo musu ruwa ” ta fada tana kokarin zama a daya daga cikin kujerar dinning din.
” barshi kawai yayarmu, Sai mun sake zagayowa, sauri muke, dama Yaya ne yace mu kawo sako ” Hafiz omer ya ce yana mikewa.
” na gode, sosai ” ta fada tana hararar haydar da suka hada ido. Kauda kansa yayi, yay gaba abinsa. Dublan alkaki, nakiya cin cin da sauransu tasa aka kulla musu Leda guda Asiya ta Kai musu har mota.
” yayarmu za tayi kirki, yaushe zamu koma? ” Hafiz omer ya fada yana cika baki da cin cin.
” dole mu dinga zagowa, don nasan Anty Da kwadayi, zamufi maida komada da wuri. ” amir ya fada
Haka sukaita hirar, a tsakaninsu har suka isa inda zasu.
****************
Amarci sosai hubby da oga yusuf suka sha, na tsawon sati biyu ba tare da ya fita ko ina ba, daga masallaci, Sai mein house da yake zuwa every 2days ya gaishe da iyayensa.
Wani kyau ta Kara, da murjewar jiki, na ban mamaki. Ita kanta bata gajiya da kallon kanta, balle yusuf daya Kara susucewa a kanta.
****************
Turaren ta karba tana fesa masa, kallon yake yana faman murmushi, ganin yadda ta turbune fuska, kamar zatayi kuka. Hannunsa duka biyu ya daura a kafadarta.
” kiyi hakuri, it’s just 2 days zanyi in dawo, in sha Allah. Ke kanki kin San yanzu bazan iya yin nesa da keba na tsawon lokaci. So please ki kwantar da hankalinki, ki kulamin da kanki, yanzu zan sa hayder ya kawo miki su Aisha su tayaki zama, Kafin in dawo. Rungumeshi tayi, tare da sake masa kuka, Mai cike da shagwaba, tana dan bubbuga kafa. Tuni ya Kara rudewa, tausayinta ya kamasa. Rungumeta yayi sosai, yana bubbuga bayanta a hankali.
Cikin murya Mai zaki, cike da shagwaba ” how can princess survive without her king? 2 days it’s like 2weeks to me “
Dago kanta yayi, yana murmushi, tare da kada mata kai, alamar tabar kukan. Bakinta takai kan nashi ta fara aika mai da hot kissing, sun kai 10min suna abu daya. Dakyar ya samu yayi controlling din kansa, don ya san plan tayi don ta hanashi tafiya. Da gyar ya zameta daga jikinsa, tana Kara narkemasa.
Har mota ta rakoshi, Sai da taga fitar su daga get din, ta juya, cike da kewar mijin nata.
Hubby na zaune a falo, ita da yarinyar da take mata aikace aikace. Ladi. Suna kallon Hausa Film. Su Aisha sukayi sallama. Amsawa tayi cike da murnar ganin aminiyar tata. Da sauri ta Mike suka rungume juna, suna ihe ihen murnar ganin juna.
” ke kam baki da kirki, ban ma san me yasa na wani tare ki ba? A ce tun washe garin ranar da aka kawoni, da kika zo, ban sake ganin kafarki a gidan nan ba, yan zuma nasan da badan yayanki ba, da yau ma banga ko keyarki ba “
Dariya Aisha tayi ” tuba nake matar yaya. Dama nayi niyyar xuwa miki weekend, ki tambayi yusra ma kiji, in baki yadda ba. “
Harararta hubby tayi ” daga ke har itan ina nan daku, Sai na shuka muku rashin mutunci. Tunda baku da kirki”
” kiyi hakuri dama tare mukayi niyyar zuwa miki wuni “
Sai lokacin hubby ta Lura da abida, dake zaune kan kujera ta daura kafa daya kan daya, tana kadawa a hankali, idonta na kansu, tana harararsu, cike da jin haushinsu.
” kiyi hakuri Anty abida. Ban Lura tare kuke ba, kwana biyu banga mutuniyar ba ” ta fada tana Kara sawa kusa da abidan fuskarta cike da faraa.
Kallon uku kwabo abida ta bita dashi, ta kwabe baki. ” naga alama ai ” ta fada a ya tsine. Hubby bata damu da yadda abida ke yatsine yatsine ba. Don zuwa lokacin tasan matsayinta a wurinta. Tun last zuwan abidan 5 days ago taga take takenta. Murmushi hubby tayi tana gaisheta tare da tambayarta mutan gidan. Kamar an mata dole take amsata, tare da jin haushin hubby ganin yadda tayi kyau cikin lokaci kadan.
” ina haydar din? Kar ace a waje kuka barshi? ” hubby ta tambaya tana kallon Aisha da suke magana da ladi.
” kema kin fi kowa sanin halin mutuminki, yana ajiyemu ya juya abinsa. Dama da kyar ya yadda ya kawo mu”
Murmushi hubby tayi ” Allah ya shiryi haydar da bakin hali, na rasa inda ya samo bakar zuciya”
” jininku ne, kawai bai hadu ba, amma kowa yasan he’s good boy” Aisha ta fada tana dariya
” arrogant boy dai ” ta fada tana kin kimar jakar kayansu zuwa dakinta.
*****************
“Yau wa, make some things delicious, kin san ina koyon girki ne, yanzu ” hubby ta fada tana kallon Aisha. Dariya Aisha tayi ” yafi miki ai, ina can ina tunanin yadda zaki Kare, don nasan banda indomie, farar shinkafa, sai supergettie, kika iya. Ina tausayin yayana, ya Saba da kwasar delicious food. “
Dukanta hubby tayi, “kin san yanzu na fara iyawa, yayanki na koyamin, next week zan fara zuwa catering school”
” so dama duk wannan kadifirin da fiffika da ake, baa iya girki ba!! Amma dai anji kunya wallahi ” duk kansu suka juya suna kallon abida dake tsaye a bakin kofar kitchen din.
” haba ke kuwa, wane irin magana ce wannan. ” hararar Aisha tayi ” ke Waya kasa dake? “
Hubby tayi murmushi, tare da ma Aisha alamar tayi shiru.
” Anty abida ke ya kamata ma kina zuwa kina koyamin wasu abubuwan please”
Tabe baki tayi da Jan dan guntun tsaki ” ki nemi mai koya miki, tun dare bai miki ba, da can me ya hanaki ki tsaya ki koya? Muddin dai mukaga Yaya na rama, mataki zamu dauka, Wanda ba zai ma yarinya dadi ba wallahi. Meye anfanin macen da bata iya girkiba? “tayi tsaki tare da barin kitchen din. Tana kada jiki. Suka bita da ido, cike da mamakinta😶😶😶……….
Don’t mind her” Aisha ta fada tana kallon hubby. Murmushi hubby tayi , tare da kada kai. “Me zamu girka Ne?”+
“Ehmmm!!! Fray rice, chicken deise, natural mango juice.”
“Good idea” hubby ta fada tana murmushi. ” ni fa zanyi kawai ki dinga nuna min yadda zanyi”
“Lallai Matar Yaya a serious, hakan ya Nuna min yadda ake ji da yayana, I’m so happy about that.”
” I will do any thing for My king “
Dariya Aisha tayi ” su King many a, Allah ya bamu masoya na Kwarai muma muji yadda ake ji, ko ma huta da iyayin hubby “
Murmushi hubby tayi, ” amin dai in da gaske kike. Kuda kuka CE sai kunga karshen Biro, tukunna”
” in sha Allah kam, sai na zama doctor Aisha Jamal Yusuf Oregon.”
” Allah yasa”
” ya labarin karatu? Ko har yanzu kina nan akan bakanki?”
Tabe baki hubby tayi ” Ku dai da kuka kwallafa ranku, kuyi tayi. Hubby kam aure bautar ubangiji ta zaba,.”
” ilmi Nada dadi , ki daure ki ko ma school ko Kettering kiyi, zai anfaneki sosai a rayuwa. Ki daina bin zugar gwaggo don nasan duk hudubarta CE kike bi.”
” in muna magana ki daina sako gwoggona a ciki, raayina ne ba ruwan gwaggo. Zan dai ko ma islamiyya, don inji dadin Neman Aljan’nata”
Haka Aisha taita nuna mata yadda zatayi, suna hirarsu gwanin shaawa. Har suka gama girki.
” uhmm!!!! Gaskiya randa hannunki ya fada a girki, yayana zai kwashi gara. kinji yadda girkin yayi dadi?”
Dariya hubby tayi ” bar zugani yar uwa, a dai ci da hakuri kawai.”
” da gaske nake, ba wasa ba “
” thanks, irin shi zan Ma king ranar da zai dawo “
” good idea “
****************
Suna zaune a falo bayan sun gama kwasar girki. Abida na dakin hubby, don tun da suka mata tayin abinci, ba Wanda ya kara bi ta kanta.
Kallon kallo aka fara tsakanin hubby da Aisha. Abida CE ta fito daga dakin Yusuf daure da towel, ta Shiga dakin hubby minti kadan ta sake fitowa ta koma dakin Yusuf.
Mamakine ya cika hubby, tabbas dakin a kulle yake ,ta Yaya abida ta samu keys din har ta bude? Ke nan bincike ta mata a daki? Dole ne ta taka mata burki don taga alamar in ta ci gaba da yi mata kawaici, ba karamin takata za tayi ba.”
Mikewa tayi ta nufi dakin Yusuf din, ranta na zafi,.
Zaune ta sameta kan stool din gaban madubi tana kwalliya, kallonta tayi cike da raini ta ci gaba da abinda take yi.
” duk dakunan dake gidan nan ki rasa India zaki baje hajarki sai nan? Bayan na tabbatar kin San hakan bai dace ba”
Kallon sama da kasa tawa hubby ” au!! haba? Ashe bai dace kanwa ta shiga dakin yayanta ba? A wace mashabar kenan? Don bani da masaniya”
” ki Sani yanzu ba da bace, dakinsa sirrinmu ne, baya halatta gareki shigansa ba tare da iznin daya daga cikinmu ba. Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki shigomin dakin miji kai tsaye, zan day komai amma ba zan yadda da tozarci ba”
” ke har kin isa ki hanani shiga dakin Dan uwana? Da har kike gindaya min sharudda. Kin yi kadan wallahi”
” kar ki yadda Dan sauran mutuncinki da nake gani ya zube, tun nuna shaida juna ki fita a dakin nan in ba haka ba, abun bazai mana kyau ba.”
Duk da abida ta tsorata da yanayin hubby, amma taurin rai ya hanata koda motsi daga in da take.
Basu ji shigowar Aisha ba, sai maganarta da suka ji duk suka juya suna kallonta. Cikin harshen larabci ta farama abida magana ” me yasa zakiyi haka? Kin San cewar hakan bai dace ba, Yaya ko lokacin yana gida baya yadda mu shiga masa daki balle yanzu. Kin manta fadan mom kenan? Duk gargadinmu da tayi amma na lura tun da suka zo kike nemanta da magana, bakya ko tsoron bacin ran Yaya, don muddin kika batama matarsa kamar kin bata nasa ran ne. Ina rokonki da kiyiwa Allah ki rufa mana asiri mubar gidan nan lafiya. “
Jikin abida yayi sanyi, musamman data tuno irin farin cikin da ta gani a fuskar Yusuf lokacin da race itama zata biyo Aisha suzo tare, har alkhawarin sabiwar waya ya masu. Tabbas ko lokacin da take gida tun da suka fara tasowa ya hanasu shiga dakunan samarin gidan. Amma ya zatayi da dunbin haushin hubby da take ji? Hakika batason yarinyar ko dama can balle da ta zama sanadin rashin auren kawarta, yar uwarta da Yusuf.
Kayanta dake kan madubin ta tattara, cikin jin haushi,. Ban gaje hubby tayi tare da Jan tsaki ta fice a dakin. Jingina hubby tayi da bangon dakin ta runtse idonta tana ambaton sunan Allah. ” kin ci daraja daya, yau da kin gane ko wacece hubby, gobe ko an ce kiyi min iskanci bazakiyiba” ta fada a ranta tana Jan numfashi.
Aisha CE ta dafa kafadarta ” I’m very sorry, Anty abida bata kyauta ba, amma don Allah kiyi hakuri”
Murmushi tayi ” it’s OK “
Bayan fitar Aisha tabi dakin da kallon. Tsaki taja, iskancin abida har gadonsu sai da ta hau, ga alamar zama nan, gyara dakin ta karayi, ta nufi toilet anan ranta ya kara baci ganin kunfa ko Ina ga ruwa duk an zubar a kasan tails din, kamar ba bap a toilet din. Sai da ta tabbatar ta gyara ko Ina, ta saka turaren wuta, ta kulle dakin.
A falo ta samesu, Aisha da Ladi na ci gaba da kallo, abida na kan dinning sai lokacin take cin Nata abincin. Direct wurinsu Aisha ta nufa, suka ci gaba da shaaninsu, like notting happen.
***************
” wai me kuke nufi ne? Bafa zata sabuba, in ci abinci da rana in sake ci da daddare.” Da kallo suka bita, tana kwance a kan 3 sitter rike da wayarta.
Aisha ce ta bata amsa da cewa ” a kawai sauran abincin da zai ishesu, ba sai sun yi west din abinciba,”
Harararta tayi ” bashi nake son ci ba, don kinsan ko a gida, bancin abinci sau biyu, naci da rana, ya isa Ku tashi Ku nema min abinda zanci.”
” ki dai ce in tashi, ita kam ai yanzu Matar Yaya ce, sai dai mu mu girka mata, ba Musa ta girka mana ba.”
Cikin larabci abinda ta fara masife Aisha ” kefa naga wani raini kike son kawo min tunda muka zo, ki shiga hankalinki dani, ita har ta isa in shiga kitchen in mata girki? “
” Allah baki hakuri, me zan dafa mini?”
” tsaki taja, barshi banso aikin banza kawai , baa iya komaiba sai kadifirin tsiya” ta fito da wayarta tayi searching number tare da barin falon tana harararsu.
Hubby da tunda suka fara ta dauke kanta kamar bata falon. Don gaba daya tun da taga take taken abida, ta fita hanyarta, duk da Dama itama ba wani shiga harkarsu take yiba.
” me kikaga ya kamata a dafa mata? “
Kallon hubby Aisha tayi ” rabu da ita kawai, in yunwar ta kwakule cikin ta nemi abinda zataci, Neman maganane kawai, ko a gida ba wani abinci take ci da daddare suya
Suna nan zaune abida tazo ta wuce su.
” Anty abida ina zuwa?” Aisha ta tambaya tana gaf da fita kofar da zai sadata da waje.
” in da kika aikeni ” ta fice a Bin ta.
” Allah ya kyauta, nasan wannan Dan iskan saurayin Nata ne yazo, shi yasa ta nace ta biyoni, tasan in a gida ne bai isa ya taka kafarsaba.”
Hubby kam shiru tayi abinta, don bata son shiga hurumin da ba nata ba. Kusan 30 min sai gata ta dawo dauke da ledoji farare masu dauke da tambarin special suya.
Ladi ta kalla cike da raini ” ke maza ki hadomin tie, sauran kimin kazanta.”
Duk Kansu ba Wanda yabi ta kanta. Wayar hubby ce ta fara ringing, ganin mai kiran yasa ta daga, tare da nufar dakinta, don ta samu dama da sakewa tayi hira da King dinta. Wanda take cike da kewarsa.
” hello princess, how’s your day? “
Tura baki tayi kamar yana kallonta cikin muryar shagwaba da Jan hankali ” boring!!! I miss my King so much, how are you “
” how can I be fine, without u by my side”
Murmushi tayi cike dakin dadin kalamansa.
” ya sokoto? Bayan kasha fura, kaci bula, da kilishi, ina zaka ita tunawa dani? Tun dazu nake expecting call dinka shiru, na kira ka yaki shiga.”
Dariya yayi, cike da jin dadin ya ce ” very sorry tunda na shigo garin nan, sai yanzu na samu natsuwa, ga network ba kyau.
Hira sukayi sosai, mai cike da nuna so da kauna, ko wanne yana kokarin nuna yan da yayi missing din dan uwansa.
*****************
Yanzu nan da ku ka baje ina zan kwanta? Aisha ta kalleta tare da kara matsawa kusa da hubby. ” wannan wurin ai ya isheki ” tsaki tayi Allah yasa akwai mai banzan bacci a cikinku in koya mata hankali wallahi.”
Shiru suka mata, don sun San duk neman magana takeyi. Hubby ce ta musu sai da safe….
******************
Yau 1 year ke nan da auren hubby da Yusuf, abubuwa da yawa na dadi, da akasinsu sun faru. Zama lafiya da kwanciyar hankali tare da tsantsar so da kaunar juna, kamar sa hadiya juna.ke tsakanin hubby da Yusuf, har lokacin hubby ko batan wata bata yi ba. Wanda ya kara hura wutar kiyayyarta a zuciyar dangin Mmn Yusuf. Hatta Mmn Yusuf din da take sassaucinta wasu lokutan, itama yanzu ta fara nuna damuwarta. Ganin duk Wanda sukayi aure a tare duk ko wanne nada dansa.
Su haidar sun tsufa a Cyprus, in da suke karatu a Cyprus International University ( CIU ) shida friends dinsa. Inda yake karantar Computer science.
Shida junaid, sai Alim da Hafiz health science, Hafiz omer da Ashir Jamil medicine.
Aisha na Kaduna state university ( KSU) tana karantar health science, yusra na karantar geography.
Hubby dai an samu da kyar anyi training na Kettering na 3 months. Yusuf yaso tayi joining dinsu Aisha tunda result dinta yayi kyau, amma ta nuna bata shaawa. Ganin hakan yasa ya rabu da ita.
Islamiyya dake unguwarsu ta shiga daga 10 to 12. Mummy ta tayi fada sosai kan kin ci gaba da karatunta amma ko a jikinta. Don harga Allah karatun boko baya gabanta, tunda ta samu na karatu da rubutu and she can speak very well ai shi kenan.
******************
Gaba daya hankalinta a tashe yake, hada Maya kawai take tana tunanin yadda zata kwashe tsakaninta da yan uwan Mmn Yusuf, a Nigeria ma ya ta kare dasu balle kuma ta bisu har Niger. Niger din Ma bikin wadda itace tushen tsanar tata da sukayi. Babban damuwarta kasan cewar ba tare zasu wuce da Yusuf ba, Mmn Yusuf ta kasa ta tsare lallai sai ta bisu su wuce tare. Shikuma sai ana gobe daurin aure zasu iso da daddynsu.
Aisha ma bazata samu damar zuwa ba, don suna tsakiyar semester. Abu ya hade mata goma da shirin. At lest da da Aisha zatafi jin dadi da sakewa. Don duk sauran matan dakin su Yusuf ba shiri suke yi dasu ba.
Gin gine yake a jikin kofar dakin yana rungume da hannu idonsa na kan duk kan movement dinta. Ita kanta bata San da shigowarsa ba. Kallonta yake cike da tausayawa, ya lura tun da magana tafiyar nan ta taso, bata da walwala. Duk da tana kokarin boyewa karya gane halin da take ciki, wani sonta yaji ya kara mamaye zuciyarsa. Duk halin da take ciki da yan uwansa ba Wanda bai Sani ba, hatta da danben da suka kusa kwasa ita da abida, a gidan Ahmad yana da labari, amma dai dai da rana daya bata taba kawo mai kara ko korafin duk abunda zaa mata ba.
Shi kansa zai so su tafi tare, amma ya ya ita dole yabi umurnin mummynsa, sai gargadi da Jan kunne da yama kannen nasa. Daga baya ya hada da lallashin su kula masa da ita sosai.
Murmushi ta sake mai, lokacin da idonta yakai kansa, da gudu tazo ta dafeshi, bai yi wata wata ba ya cabeta sama ya fara juyi da ita kamar yadda ya saba, suna dariya……..wai yarinyar nan kwana biyu kin kara nauyi ” Ya fada yana direta a tsakiyar dakin. Gimtse dariyar tayi tana masa harara mai hade da kallon love, ” yar ni dinnan har zakace nayi nauyi? Randa na zama katuwa kuma fa? Kasan dai baka isa kace bazaka iya daganiba!! Don ba yadda zan ba, tunda ka saba min”
” so dai kike ki buda min kirji, naga alama amma yar lukuta na nawa kuma, bayan yadda kike a yanzu?”
Kafa ta fara bubbugaga cike da shagwaba,Wanda yasa duk kan jikinta juyawa, dama sanye take da kayan bacci. Rigace aimless da gajeran wandonta ko ciya bai rufe ba, Wanda ya fita da kyan sigarta. Tsayawa yayi yana kallon yadda komai ke juyawa gwanin shaawa, da burgewa. wani Abu yaji yana kara taso masa tun daga babban yatsansa har ysakarka.
Jinshi shiru yasa ta tsaya da juye juyen da take. Kallo daya ta masa ta karanto tsantsar fitinan dake dankare a kwayar idonsa. Ido daya ta kashe masa, tare da daga kanta kadan alamar tambaya. Ajiyar zuciya yayi tare da murmushi, smacking ya mata tare da sanya hannu ya jawota. Kwasa tayi da gudu, still fuskarsa na dauke da murmushi ya bita, suka fara zagaye bed din dakin. Cafkarta yayi bai direta ba sai tsakiyar bed din dake cike da kayanta data barbaza tana zabar na tafiya.
Dariya take tana maida numfashi, magana take son yi amma ko kalma daya ta kasa furtawa.
Sun Dade suna kallon juna, cike da so da kauna, kafin yakai bakinsa kan nata ya fara kissing dinta. Ganin yana son wuce gona da iri, da kyar ta kwaci bakinta a nashi cikin maida numfashi tace ” abincinka fa na jira a falo ” kara jawota yayi jikinsa, ganin abun ba sauki yasa ta tallafi mijinta ta fara aika mai da nata salon cike da kwarewa da sanin ta kan mijin nata.+
Kukan shagwaba ta fara ” Allah bazan yadda ba, ji yadda kamin da kayana” dakin yabi da kallo. A kwatin can gefe ya kusa bakin kofa, sai kayan da suke da a goge kowanne ya kama gabansa baa maganar guga. Shi kansa gadon da suke kwance kan wasu daga kayan ne, wanda fadin yamutsewarsu bata baki ne.
” it’s your folt princess, you look hot, “
Kara shigewa jikinsa tayi
Allah ya miki albarka, you make me a happeyers man on earth. Na gode Allah daya sakoki cikin rayuwata, Allah ya bamu zuria tsarka kakkiya. I’m very sorry da abinda ke faruwa tsakaninki da yan uwana, I known everything, I try my best to make things right. I known your worries, mu ci gaba da addua, wataran sai labari, ki dauka taki jarabawar kenan, don ko wanne Dan Adam da kika Ganshi yanada irin tashi jarabawar. Ki kula min da kanki sosai, na jama su abida da aira kunne sosai, in sha Allah ba wani matsala. Zanyi iyaka kokarina in ga na yi scuising time in zo da wuri, don nima hankalina ba zai taba kwanciya ba.”
Kwantar da kanta tayi a kirjinsa tana shafawa a hankali, ajiyar zuciya tayi ” baka ci abinci ba fah?”
Hancinta ya danja, yana murmushi, ” me kike dafamin ne?”
” you’re favorite “
Goshinta ya sumbata ” thank u, I’m going to miss u”
Hawayen da taji na Neman fitowa yasa tayi saurin mai dasu. ” me too. “
Bayan sun tsarkake jikinsu, suka nufi falo. Da kanta ta dinga ciyar dashi har ya koshi. Ga labarai na ban dariya da ta tanada, musamman don ta sashi nishadi. Cikin nishadi take ciyar dashi tare da bashi labarin dan fillo da babarbare, dariya sosai suke kwasa. Duk rashin son surutu irin na yusuf, in yana tare da hubby zaka sha mamakin yadda shima yake iya kokarinsa, wurin biye mata, hira sosai yake zagewa ya mata,don ya lura shiru baya cikin kundinta. Duk yanda ta motsa idonsa na kanta. He never except irin wannan kulawar daga gareta, duk da auren soyayya sukayi,. Tsawon shekara dayan nan ba zai ce ga wani aibunta da ya ganiba. Kullun tana cikin tarairayarsa, da bashi kulawa, hatta abinci ya rasa when last da yaci abinci da kansa. Ta riga ta shagwabashi karshe, duk inda yaje Allah Allah yake yadawo gida.
Idonsa ta hure cikin salon daukan hankali, ganin yadda ya zuba mata mayatattun idonsa baya ko kiftawa. Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Sai daya hadiye ruwan tie din daya kurba. Ya kalleta da dara daran idonsa, yana shigar dasu a hankali ” I love u” murmushi tayi don inda sabo ta saba, akalla a rana takanji Kalmar a bakinsa ba adadi. Kiss tama bakinsa, da ta Dora goshinta kan nasa hancinsu na gogar juna ” I love u more ”
Sun Dade a na nuna ma juna kauna, kafin suka koma dakin ya tayata hada kayan da zata tafi dasu. Ranar kwana sukayi basuyi bacci ba.
****************
Karfe 2:43 dai dai jirginsu ya sauka a Miami na kasar Niger. Mota biyu suka zo daukarsu,.
Alhaji mamuda Hammani, ya ya ga Mmn Yusuf, kuma marikinta. Hamshakin Dan kasuwane, Wanda yayi fice a kasar Niger, wurin shigowa da Samar da kayan masarufi. Sannan dan siyasa, mai rike da mukamin dan majalisar tarayya.
Alhamdulillah sun samu karba sosai, cikin mutunci da karramawa. Gidan cike yake da baki na nesa, yan kusan ma sun samu halatta saboda shirye shirye.
Abida kam tuni ta shige cikin kawayen Amarya. Dayawansu dama duk yan uwan junane.
Hubby na zaune ita da Aira, sai kannen Hajiya Ai dake ta aikin ware kayan Amarya. A hankali Aira ke janta da hira, tana gaya mata matsayin kowa a wurinsu. Ajiyar zuciya hubby tayi don bata taba zaton family din suna da yawa haka ba. Kwanciyar hankalinta, da tun da tazo bata samu matsala da kowa ba. Hatta abida silent treat ta mata. Kamar yadda Aira ke mata a da. Ita dai bata nuna bata son taba, amma ba ruwanta da duk wani harkarta. Daga gaisuwa shi kenan bata kara bi ta kanta. Amma ikon Allah yau ita Aira kewa hira?
Muryar Aira ce ta dawo da ita daga dogon tunaninta. ” nifa gidan Innani zan gudu, don gaskiya gidan nan ba dadi zai yiba, duba tun yanzu har gida ya cika.”
Murmushi tayi don tana yawan jin labarin innani a bakin Yusuf. So she known who she is. ” kiyi hakuri mu zauna a nan, ban son zama ni kadai”
Tabe baki Aira tayi ” ba nisa fa, 3 houses ne kawai a tsakaninsu, in zaki je muje, amma ni bazan iya zama a nan ba gaskiya, ko dama can nafi sauka a gidanta, in munzo”
” OK zan tambayi mommy in ta yadda sai muje”
Saurayine da ba zai wuce 25 years ba,dogo wankan tarwada, yana da kyau sosai, ga alamar Hutu, da kwalisa bayyane a tare dashi, kallo daya zaka masa kasan irin mazan nan ne masu aji. Kyau, kudi, ilmi.
Shigowarsa na uku kenan falon in ba batan lissafi nayi ba. Daya daga cikin matan dake jera decorations a cikin kwali ta dago ta kalleshi tana murmushi ” lafiyarka kake ta mana sintiri a kai?”
Keya ya dan shafa, yana murmushi idonsa na kan su Aira dake can gefe, suna hira sama sama da hubby. ” kaji cikin ummana? Naga duk dakin nan iyayenane? Meye a ciki don na shigo?”
Dariya sukayi gaba dayansu. Dayar ta ce ” kaji da gulmarka, nasan sintirin da kakeyi ai, Mara kunyar banza, ina tun safe muke nan muna aiki? Ko keyar ka bamu gani ba sai yanzu, zaka ishi mutane da sintiri, bako kunya “
” wayyo!!! Ai sai yanzu na harbo jirgin” wadda ta fara magana ta fada
Ganin duk sun hayayyako masa yasa cikin borin kunya ya ce ” nifa ba wannan ya kawo niba, kuke Neman fassarani, snacks nake so, Hajiya tace in zo wurin cikin umanta in karba”
” kadai ji dashi, yaro” suka fada suna masa dariya.
Kallon Aira yayi ” please sister ki karba ki kawo min ina waje, kafin wa annan matan su tsitstsigeni” ” OK” ta fada tana mikewa daga inda take zaune.
Wani mayataccen kallo ya bi hubby dashi, kafin ya fice a falon. Hubby kam bata ma San wainar da suke soyawa ba, don idonta na kan waya, suna charting da junaid, sai Aira da ke mata hira jefi jefi.
A waje ta sameshi da friends dinsa, sun shinfida katuwar dadduma, ga kayan shayi nan birjik ko wanne da kofinsa a hannu.
“Mai hali bai fasa halinsa, iya saninta da Yaya Khalil duk yamma yake hada wannan majalisar ta abokansa, asha shayi, ayi musu, ayi hira da dariya. Da alama shi zai gaji Alhajin su ta fannin siyasa, don yanzu haka ya kammala degree dinsa na biyu akan political science. Duka duka satinsa daya da dawowa gida Niger. Sabanin sauran yayyensa dake harkar kasuwanci.
Sallama tayi cikin muryarta mai sanyi. ” Yaya Khalil gashi! ” ta mika masa trey din.
Murmushi yayi, Wanda ya bayyana kyawawan hakoransa farare masu dauke da wushirya. ” thanks siste”,
Gaishe da friends dinsa tayi, sannan ta juya zata koma ciki.
Biyota yayi da sauri ” 2 min sister” tsayawa tayi, tana kallonsa tare da jiran mai zai ce.
Murmushi yayi, yana shafa dan kyakykyawan gajeren gemun da ya bari. ” na ganki da wata? I don’t know her, please wa ce ce ita?”
Gaban Aira ne ya mugun faduwa, mu samman ganin yadda yake ta sake mata murmushi.
” she is our Anty, Matar Yaya Yusuf ce”
Nan take annurin fuskarsa ya kau, hannu yasa yana shafa lallausar sumar kansa. Ji yake kamar ya kwala ihu, saboda abinda ya tsaya masa a kirji. Tunawa yayi Aira fa kallon sa take, zata iya harbo jirginsa, Wanda hakan bazai musu dadi ba. Murmushi ya yi, cikin basarwa ” amma baki da kirki, shine baki min bayani ba in kwashi gaisuwa”
Murmushi tayi ” sorry na shaafa ne”
” shike nan, bari in je na bar friends dina, zan shigo anjima in kwashi gaisuwa “
” OK no prb”
Jiki a salube ya koma wurin friends dinsa, nan suka dinga tsokalarsa wai yayi new catch.
Ajiyar zuciya tayi ” iko sai Allah, bisa duk kan alamu ya kamu da son hubby, shin bai San da alkawarin hadin aure tsakaninta dashi bane? Bisa dukkan alamu bashi da masaniya a kai. Bayan hadin auren Yusuf da Hafsat ya wargaje, shine suka maida abin kan abida da Khalil, nan take abida ta nuna ita bata yadda ba don akwai Wanda ta ke so, juyin duniya taki, ganin haka yasa aka yanke shawarar a hada Aira da Khalil. Baa samu matsala a wurin Aira ba, don lokacin ko secondary school bata gama ba, bata fara kula samariba. Wannan kenan.
Jikinta a San yaye, ta koma ciki, don gaskiya tana matukar son Khalil, tun ba yau ba, yana burgeta sosai,.
******************
Sosai innani ta karbesu, mu samman hubby. Abin ya matukar burge hubby, yanda innani ta dinga nan nan da ita.
Innani kanwa ce gasu Mmn Yusuf, su uku Allah yaba iyayensu. Itace karama. Yaranta uku. Khadija ( kadi) wadda saa ce gasu abida, sai Fatima ( ya fati) Saar su aira, sai auta umar, Wanda duka duka shekarunsa biyar kenan, don har ta cire ran sake haihuwa, sai ga ciki, on expected. Mijinta Dan kwangilane, yana da rufin asiri sosai.
Dakin kadi aka sauke hubby, kasan cewar kadi na cikin kawayen Amarya, yasa ya xama hubby ce kawai a Dakin. Sai Aira da ta sauka a dakin Best friend dinta yah fati.
***************
Lallausan cotton less ne a jikinta kalan lilac da milk, dinkin straight skirt, dinkin rigar ambreller ne, zuwa gwuiwa. Dinkin yasha aiki ga stone sai daukar ido suke, set din White gold tasa mai hade da siraran bresslet guda biyu. Dan kwalin less din tayi hadadden dauri dashi Wanda ya kara fito da kyan fuskarta sosai, simple makeup tayi, ta feshe gikinta da turaruka masu matukar kamshi da tsada. Don hubby akwai son kamshi, ta hadu da oga Yusuf da baya jin tsadar siyan turare komai tsadarsa. Gyale milk color ta yafa, sai takalmi da Jakarta milk and lilac. Juyawa tayi tana kallon kyan da tayi ta jikin dogon mirrow da ke manne a side din dakin, Wanda zai baki damar ganin Head to toe dinki.
Gadiya tayi ma Allah daya kagi halittarta. Take Yusuf ya fado mata. Murmushi tayi. Shigowar yah fati ne ya dawo da hankalinta.
” woww!!! Masha Allah, Matar Yaya kin hadu ba karya wallahi” yah fati ta fada tana bin hubby da kallo, fuskarta fal murmushi.
” yayanmu ya iya zabe, irin wannan full option haka”
Murmushi hubby tayi tare da hararar yah fati, don dan zaman da tayi da ita daga jiya zuwa yau ta lura yarinyar akwai barkwanci, ga saukin kai,.jininsu ya hadu, kamar yadda ya hadu dana innani. Kadi ce dai har lokacin basu haduba.
Ganin hararar da hubby ke aika mata, yasa tayi dariya, “Matar Yaya kefa muke jira, don in mun rakaki can gidan, mu kam gari zamu shiga”
Nan danan fuskar hubby ta canza. su tafi su barta da wa? Bayan dasu kadai take iya sakewa, su ke debe mata kewa, tunda ba sanin kowa tayiba.
” ban gane zaku shiga gari ba?”
” zamu je gidan wata friend din mu ne, daga nan Yaya Abba zai kaimu yawo, kin San kanwar taki, kamar shan shani take,.”
Marai raice fiska tayi ” please karku tafi Ku barni ni kadai, kunga Ku kadai na saba da, kuyi hakuri mu zauna”
” wai zaman me kuke a daki? Daga bari in je in kirata kin zauna kamar an aiki bawa garinsu!”
Da kallo tabi hubby ” kinyi kyau ” ta fada tana murmushi
” thanks, don bakuga kanku bane, na tabbatar kunfini yin kyau” hubby ta fada tana mayar mata da murmushin
Kallon Kansu sukayi, tabbas ba karya sunyi kyau sosai, sanye suke da atamfa super exclusive Riga da skirt Wanda kowacce yabi jikinta das gwanin shaawa. Komai nasu iri daya. Don dama haka sukeyi in sun hadu, komai iri daya suke sawa like twin’s. A fisge kuma akai saa suna kama da juna ta wurin hasken fata, da yanayin bakinsu. Don itama yah fati badai kyau ba, babanta buzune, mahaifiyarsa kuma babarbariya.
” kin dai zagemu kawai, ” yah fati ta fada tana dariya.
” zagi ko gaskiya. Look at you” hubby ta fada tana nuna su jikin mirror din.
” kina wuri ai bamu isa yin magana ba. I had a lot about you. Ashe ma kinfi yadda ake kwatan tawa ” ya fati ta fada tana murmushi
” haka dai kika ce, but ban yadda ba “
Haka sukayi ta musu, cikin anna shuwa. Kafin daga karshe zuna nufi gidan bikin.
Mmn Yusuf ce ta bukaci su aira dasu zagaya da hubby ta gaishe da sauran muta nen gidan. Sai a lokacin hubby ta tabbatar da girman gidan, don hatta yaran gidan manya su uku a nan cikin gidan suke zaune da matansu, kowa part dinshi daban.
A part din babban Yaya badamasi suka samu sauran matan. Matar badamasi hilwa, ta karbesu cike da faraa. Tana Jan yah fati da wasa, da a lama mutuniyarta ce. Ya fati ce ta gabatar musu da hubby. Sannan ta fara introducing dinsu ga hubby, hilwa Matar yaya badamasi, sai yasin Matar yayaKabir, sai humaira Amarya a wurin Yaya Abba. Ya fati ta karashe tana dariya.
Dariya humaira tayi ” fadi ki kara, uwargida, kuma amarya. In zaki zage ki nemo naki, ki zage don na tare gaba na tare baya. Don haka a kara gaba a daina shin shina min miji.”
Duka dariya suka sa, ganin yadda humaira keyi. Banda yasin data hade fuska sai wani harare harare take.
” oh !!! Ji yadda kike wani tada jijiyar wuya. Kisa ranki a inuwa da ina da bukatarsa da baki samu shigowa ba, don kiji. Ni nan da kika gani sai na zaba na darje. Mijinki ya zama second hand yanzu. Ki rike kayanki.”
” kin dai ji tsoro kawai” humaira ta fada tana dariya
” Allah ya kiyaye in ji tsoronki. In ina da bukata, kwace shi ba zai min wuya ba, ke kinsan haka.”
” oho dai abi wani sarkin ”
Hilwa ce ta katsesu da cewa ” kun bani kullun kuka hadu sai an zubar da hali. Wannan ma ya hadaku ai karasashi zakuyi”
” barta kawai, yanzu haka ma dashi zamu fita, please Anty hilwa ga amanar Anty hubby a hannunki yanzu zamuje mu dawo.”
” lallai ne, ke yanzu kina kallo yarinya karama tana kokarin juya miki miji.? Kar kiji tana wani dadin bakin ba son shi take ba. ki sake jiki a miki sakiyar da ba ruwa.yan matan yanzu da suke neman miji ido a rufe, balle an samu ready made. Kina nan sai dai kiji labari yasha ban ban.” Yasin ta fada cikin yatsina tana kallonsu a Dage.
” iko sai Allah, cin dankon har da su kaza.? Ina ruwan agwagwa mai bakin baki. Allah mun gode maka da kasa sauran garin ba baki bane kamar dayan, da kunun ba zai shawuba.” Ya fati ta fada tana kafeta da ido cike da rashin kunya.
” karki fara!!! Ko yanzu in tattaka yarinya a wurin nan”
” tafdijan!!!! Da kin tarowa kanki mach wallahi. Kuma kashedi ban saka mutun ba ban son ya tsoma kansa. Ehe!!!!!!! Shish shigi ba aji”
Tashi yasin tayi zata fallawa yah fati mari, da sauri humaira ta tare, tare da janye yah fati da sauri.
” haba ke kuwa? Wannan ai ba girmanki bane.” Humaira ta fada tana janye yah fati.
” abinda kike bakya kyautawa, na ga dai ba da ke take ba? Bana son irin haka. Ke ce babba ya kamata ki kama kanki. Da baki tanka taba ai bazata gaya miki magana ba.”
Harara yasin ta makawa hilwa ” dama ai ke kike daure mata gindin yiwa mutane rashin kunya.”
Kallon su yah fati hilwa tayi ” ki wuce ku tafi kayanku.”
Harara ya fati ta jefawa yasin tare da Jan tsaki, ta ja hannun Aira da tun dazu ta daskare a wurin tana kallon ikon Allah. Sukayi waje.
Hubby ji tayi kamar ta bisu. Don gaba daya jinta take kamar akan kaya. Ga wani kallon banza da yasin ke aiko mata, kamar ita takar zomon.
” gaskiya ce bakwaso, ni kuma sai na fada, kina wani yashe mata baki, ke a dole wasa, baki San a wasa ake cutar ka wani lokacin ba! Ga example nan a gabanki ai.” Ta nuna bubby da yatsa
Cikin bacin rai hilwa ta ce ” kinga ban son dibar albarka, zo ki wuce gidanki tunda ke har abada baa iya zama lafiya dake.”
” ko baki ce in fita ba, tafiya zanyi. Don bana zama inuwa daya da snatchers. Gashi nan Allah ya kama su ai, dan farin cikin nan da kowa ke samu, da karuwa sun rasa, har yanzu shiru. Waya Sani ma ko juya ce, an gama gantali a titi, an ga sankacecen yaro an manne masa. “
Duk inda bacin rai yakai hilwa da humaira ransu ya baci. Hubby kam baa magana zuciyarta ce taji tana mata wani zafi, ina ma ace ba bakunta taxo ba, da yau yasin sai ta raina kanta, sai tasan ta taba hubby. Duba da duka duka bazata wuce Saar taba.
Kallon yasin take, mai cike da maanoni da dama.
Har zata fita ta juyo, tayi saa kuwa duk suna binta da ido.
Murmushi tayi ” da kika tsareni da ido, in fitsarin kaza kunfa ne, wata tayi mana. Nan da wata Tara muzo suna. In har ba juya aka kwaso mana ba. Snatcher kawai” tayi tsaki ta fice………kiyi hakuri don Allah, wallahi halinta ne, duk nan hakuri muke da ita.” Humaira ta fada cike da damuwa+
Hilwa ta kara da cewa ” karki sa abinda ta fada a ranki don Allah. Nasan da zafi, kwata kwata bata iya magana ba, bata iya ban bance kalaman da ya kamata ta gayawa mutun, komai yazo bakinta fada take.”
Murmushi hubby tayi mai ciwo. ” ba komai ya wuce”
Hira sosai sukayi ta Jan hubby dashi, cikin kan kanin lokaci ta sake jikinta, don hubby akwai saurin sabo.
*******************
Yau kwanan su hubby biyar a garin Miami. Zuwa lokacin ta saba dasu hilwa da humaira sosai, in ka gansu kamar dama can sun San juna. Hubby mai farin jini ce, da shiga rai muddin zaka zauna da ita na dan lokaci, tuni zata shige ziciyarka. Kamar yadda ta samu masoya haka ta samu makiya da yan hassada (Allah ka mana tsari da hasiduna)
Yasin da mukarrabanta dama kadan suke jira, su dinga yada mata da habaici da mafanganu,dasu gori. Bata daga kanta ma balle ta nuna musu ta damu da abinda suke yi, sau da yawa su humaira ne masu shiga mata suyi uwa suyi makar biya.
Hakika sun nuna mata kauna wadda bazata misaltu ba.
Sai ana gobe daurin aure su Yusuf suka sauka a Miami. Shida Alhaji jamal, Ahmad, Sai Mmn samira da ummu sulaim.
Wai zo kaga murna wurin hubby, ganin ummu sulaim. Don tun bikinsu da suka raka ummu khulsum gidanta a Lebanon suka riketa a can.
******************
Alhamsulillah yau su hubby suka dira gida Nigeria.
Da kyar ta lallaba ummu sulaim ta bita su kwana biyu. Don ba karamin kewar juna sukayi ba. Koda ummu khulsum tazo haihuwa gida, lokacin ummu sulaim na shirye shiryen exams a can aka barta.
****”””*””**********
A kwana a tashi asarar mai rai, inji masu iya magana ( but nah true oo) yau auren hubby da Yusuf 4years kenan. Abu buwa masu dadi, da akasasinsu sun faru. Har lokacin ko batan wata bubby bata taba yiba. Su Kansu abin ya damesu, Sai dai duk asibitin da sukaje a ka gama gwaje gwaje zaa ce musu komai normal. Ba wata matsala a tare dasu.
Yanzu haka satinsu daya da dawowa daga Egypt, ganin doctor, suka wuce saudi don yin umra.
A hankali ya tako in da take tsaye a gaban mirror tana shirin tafiya suna gidan Ahmad. Matarsa munaya ta haifi second yaronta namiji.
Rungumota yayi jikinsa yana shakan kanshinta, yana faman limshe ido. Murmushin karfin hali tayi, duk a kokarinta na boye damuwarta. Don tun da akayi haihuwarnan take fuskantar wulakanci da gori iri iri. Hatta Wanda bata taba tsammanin haka daga garesu ba. Balle yau da gidan zai cika.
Shafa lallausar sumarsa tayi tana kallonsa ta mirror din. ” nayi latti fah!!!” Ta fada cikin shagwaba
“I know ” ya fada yana juyo da ita, suna fuskantar juna.
Kallonta yake cike da tausayinta, yayi mata kiss a goshi, hannunta duka biyu cikin nashi ” take good Care of your self. Karki bari maganar wawayen cikinmu ta dameki, Allah shike ba da haihuwa ga Wanda yaso, ya hana, Wanda yaso, A lokacin da yaso.Keep that in mind.”
Murmushi tayi ” in sha Allah “
Yana rike da Jakarta suka fito, tana bashi labarin yah fati da yasin suna dariya. Don lokacin yah fati na matsayin Matar Yaya Kabir, kishiya ga yasin. Zo kaga drama.
Sai da ya tabbatar ta zauna dakyau ya mika mata jakar, ya rufe mata kofar, ya koma driver sit, yaja suka nufi gidan Ahmad, dake kusa dasu.
Sai da ya tabbatar ta shiga tukunna yaja ya tafi.
Da Anty samira suka fara cin karo,. ” manyan mata, sai yanzu ake ganin Ku?” Ta fada tana karewa hubby kallo.
Murmushi hubby tayi ” kai bisa wuya, ina kwana”
” lafiya kalau, gimbiya a gidan Yaya Yusuf. Zan zo dai abani sirrin nan”
” Anty samira kenan, sirri kam ai yana wurinku “
Ido samira ta dan fito dashi ” suwa ? Ke dai kice bazaki bani ba kawai.”
Ganin Jan maganar zaiyi yawa yasa hubby saurin katseta, ” su Aisha fah?”
Tabe baki tayi ” suna ciki “
Da sauri tabi hanyar da zai sadata da falon gidan.
Da kallo samira ta bita tana tabe baki.
**************
” kai amma less dinkin nan yayi matukar kyau, baki ga yadda ya fito da keba wallahi” hubby ta fada tana kallon munaya
Murmushi munaya tayi don irin matan nan ne masu son ace sunyi kyau, ko kuma abunsu ya burge. Don yar karyace ta karshe. A kwai daukar wanka kam.
” thanks Matar Yaya. Kin ganshi musamman nayi oder dinsa daga England. Da aka kawo sai naji bai yi min ba. Amma sweetheart ya ce ya masa kyau, shi yasa na dinka, da kyauta zanyi dashi.”
” yayi kyau sosai, ba karya kin fito “
Murmushi munaya tayi cike dajin dadi ” thanks “
Anties dinsu Ahmad ne suka shigo. Dayar ta kalli munaya tana murmushi ” mejego ta fito ras, wannan kwalliya haka kamar zaki gasar sarauniyar kyau.”
Dayar ta amshe da ” masha Allah kyau ya tarda kyau “
Hubby ce ta fara gaishesu, ba yabo ba fallasa suka amsa.
Dayar ce ta dawo kusa da hubby ” yauwa dama ina son magana dake, “
Gyara zama hubby tayi tana kallon ta cike da ladabi, don ta girmeta nesa ba kusa ba.
” yanzu don Allah Habiba me yafi wannan dadi?” Tana nuna munaya mace duk kyanta duk kudinta, duk nasabarta in bata haihuwa meye anfaninta? Ina baki shawara tun wuri in har kin San da gaskene kwayoyin hana daukar ciki kike sha, ki shafama kanki lafiya ki bari. In kuma matsala ce Ku nemi magani tun kan lokaci ya kure miki. Don mace lokacinta takai tacce ne, ba kamar namiji ba. Kar kiga kin mallake miji, sai yadda kikayi dashi, akwai ranar kin dillanci. ban da haka ma ai haihuwa rahama ce. Shawara ce, don ni bazan fada a bayan idonki ba, kuma ba zan iya shiru ba.”
Tunda ta fara maganar kan hubby na kasa, duk kokarinta na danne kukanta ya gagara. Hawaye ne suka fara bin kuncinta.
Jin Matar tayi shiru dayar ta amsa ” gaskiya kam, surutu yayi yawa a kanki. Naji ma kamar aure uwarsa take nema masa “
Da sauri hubby ta dago tana kallon matar.
Itan ma kallonta take yi ” da gaske gara kinsan abinda kike ciki.
” haba Ku kuwa, Ku kyaleta taji da abunda ke damunta. Ni nasan hubby bazata taba yin abin da ake fada a kanta ba, suma sun San haka, son zuciya ne, kawai da kin gaskiya. Haihuwa kuma ta Allah ce, ni nasan da ana siyarwa da kun samu sun kai goma a wurinta, yanda take son yara.” Munaya ta fada tana zama kusa da hubby
Maganganu masu sanyaya rai ta dinga gaya mata, har ta samu natsuwa, suma hakuri suka bata . tace ba komai ta gode.
A ranar hubby tasha bakaken magan ganu da habaici iri iri. Su Aisha ne su ka dinga shiga mata, su dinma daga baya hanasu tayi.
A daddafe takai 5, ta zame jikinta tayi gida. Kuka ta sha kamar ba gobe, sai da tayi mai isarta sannan ta nufi toilet ta wanka ta dauro alwala.
Ko da yaje daukarta su Aisha suka shaida masa ta Riga ta tafi.
Kamar yadda ta saba masa komai yauma haka, ko afuska bazaka taba ganin damuwa ba. Shima bai tada maganarba duk da Aisha ta gaya masa komai. A kullun addua da godiya yake ma Allah daya azurtashi da mata ta gari. Duk abunda yan uwansa zasu mata bata taba kawo masa kararsu, saanninta in sun mata ta rama, in ka girmeta ta kauda kanta. Ko a fuska bata taba nuna masa an bata mata, ko an mata ba dai dai ba.
*******************
Zaune suke a babban falon yaran gidan, bakajin komai sai karar cokula da tashin muryoyi maban banta, da dariya.
Ummu sulaim, Ummul khair, Aisha, sai yaran uncle omer asima da asiya. Ko wacce na cikin farin ciki sai zolayar juna suke. Gwanin shaawa.
Da sallama ta shigo falon. Wani ihu Aisha tasa ta rungumota tana murnar ganinta.
Ita din ma dariya tayi tana kara rungumeta. ” ke karfa ki karya mana Matar Yaya” asima ta fada tana dariya.
” congratulation my betsy ” hubby ta fada tana mikama Aisha hannu bayan sun saki juna.
” thanks, na dauka ai bazaki zo ba “
” ni a wa? “
Hubby ta fada tana dariya. Sadi driver yayi sallama sai da suka bashi izni bayan sun amsa ya shigo da wasu manyan kwalaye guda biyu ya gaishesu, ya ajiye ya fita.
Gaisuwa suka fara cike da kaunar juna. Suna tsokanan hubby.
” congratulation to you too ” hubby ta fada tana rungume ummu sulaim.
” thanks sister “
Zama hubby tayi kusa da Aisha. ” to su alhuda huda, an kammala degree an dire, what is next? “
Duka Aisha ta kai mata. ” tun da kin ji tsoro kinki direwa. Mun dire kuma sai A B U, kin ga mun zama daya kenan.”
Dariya hubby tayi ” wane ke yarinya, kya hada Wanda ya ke da 4 years experience da Wanda ya shiga new? Na gaba yayi gaba,.”
Dariya sukayi ” gaskiya ne kam, za muzo daukar lectures, don gaskiya kina bala’in burgeni, yan da ake kula da yayanmu, ina son nima in sace zuciyar sweety na, da irin waannan salona. Ya zama ba kowa a gabansa sai ni.”
Asiya ce ta tashi tsam daga inda take zaune ta koma kusada hubby dake zaune kusa da Aisha, ta zauna.
” gaskiyarki sister Aisha, nima please zan zo a bani horo na musamman.”
Dariya sukayi gaba daya. Ummul khair ta rike haba tana dariya ” amma dai rashin kunyarki yayi yawa, ki bar manya suyi maganarsu, ba ke ba dako secondary yanzu kika kammala. Amma kike maganar koyon zaman aure, anyah???”
Harararta Asiya tayi ” wa yasa dake? “
” gaskiya ta gaya miki, muna maganar manya Ku daina sa mana baki.” Ummu sulaim ta fada
” kefa surukata ce be kamata kina min haka ba. Kamata yayi ki roki antinmu ta bani hints na yadda zan sace zuciyar !! Eh !!!! Kin gane ba sai na fada ba”
Dariya ummu sulaim tayi tana nuna Asiya da yatsa ” ina warning Dinki bakyaji, I don’t want u to get hot at end”
Bata rai Asiya tayi cikin tura baki ” just pray for me “
Asima ta tabe baki cike da jin haushin kanwar tata ” ki kyaleta Wanda yayi nisa baya jin kira, jiki magayi ai, in ji masu iya magana “
Hubby dake zaune tana jinsu. Aisha ta kalli Asiya ” rabu dasu sister, ba dai kina son shi ba? I will teach u, how to woo him, he felt for u, like crazy.”
Dariya ummu sulaim tayi har da rike ciki. Da ido suka bita, sai da tayi mai isarta sannan.
” lafiyarki kuwa? Mu gudu ko mu tsaya ?” Hubby ta ce yana tsareta da ido. Don sun San muddin kaga ummu sulaim tana irin wannan dariyar to ko dai ta mugunta ce, ko kuma ta gama raina maka hankali.
” waannan har yau baku gama sanin waye haidar ba!!! Ya wuce da sanin da kikai masa can baya. Ina gudun miki wulakancinsa, in kinga yadda yake gara yaran jamaa a IUC zakisha mamaki. Bashi da mutunci ko kadan. Kin San Afrin ai? Yarinyar uncle Harris. Kwanciyarta a hospital 2, akan haydar dan banzan daga karshe dukan kawo wuka ya mata, wai ta addabi rayuwarsa. Dole uncle Harris ya dauketa ya mai da family house a Oregon, Saboda abun yaki ci yaki cinyewa. Kadan ke nan wasu ma ban iya fada, shiyasa na baki shawara matsayina na yayarki, but tunda kinji kin gani, shi kenan. Allah ya baku saa keda teacher din taki”
” zai aika abin da yafi haka ma, in dai wannan mai idon a tsaitsaye ne ” hubby ta fada
Jikin Asiya yayi sanyi, don tasan afrin farin Sani, duk wani Abu da take takama dashi, bata kama kafarta ba. Don uncle Harris babban mai kudine da duniya gaba daya an San da zamansa. Yana cikin top 20. Haka ta fannin kyau, da wayewa. Mamakin haydar ya cika zuciyarta lallai halinsa sai shi, yanzu haka a gidan uncle Harris din suke zaune, shida yayanta Hafiz omer da friends dinsu. Amma ya iya karfin halin dukan yarinyar da ko kaffara baza ta yiba in ta ce baa taba dukanta ba, tunda tazo duniya. Don yar gata ce ta bugawa a jarida, ya daya mace tilo a wurin iyayenta. Amma ina so ya gama rufe mata ido. Take wata zuciya ta fara ayyana mata ita zata iya samun matsayin da sauran suka kasa samu. Don abun daga jini ne. Mu samman in tayi laakari da yadda suke shiri dashi.
” Wanda yai nisa baijin kira.” Asima ta fada in I don’t care tone
Ummul khair ta ce ” Ku kyaleta ta gwada saarta. I’m so happy in har hakan ta kasance. Nasan kanina is in good hand. Dama ni bana wani son afrin din nan. Jin kanta yayi yawa, ga izgilabci. Gara ma daya mata haka, ko tayi hankali.”
” me kika kawo mana gift ne,?” Aisha ta tambaya tana kokarin janyo kwalayen da driver ya shigo dashi.
Murmushi hubby tayi. ” open it and see!”
Wanda sunan ummu sulaim ke jiki, ta mikawa Asiya ” mika mata nata” ta fara kokarin bude nata kwalin don ganin abinda ke ciki. Su Ummul khair suka matso su tayata ganin abin da ke kunshe a kwalin da yasha rapping sheet mai kyau da daukar ido…..
wowwoo!!!!” Suka fada a tare, Ummul khair ce ta zaro hadaddun gowns guda biyu. Red, Navy blue and black. Masu masifaffen kyau. Kowacce da takalminta da jaka to mach, Sai congratulation cards. Gaba daya saboda farin ciki Aisha daskarewa tayi a wurin. Don kayan kyansu da darajarsu sannan her favorite color yasata kasa ko da kwakkwaran motsi, sai bin kayan take da kallo duk wanda ya daga.+
Rungume hubby tayi cike da matukar farin ciki. ” thank u very much, besty. Your the best “
Dariya hubby tayi ganin yadda ta makalkaleta. ” is Notting kunfi haka a wurina, I hope shi zaku sa a party?”
“Sure” Ummu sulaim ta fada lokacin da ta iso. Itama rungume hubby tayi tana mata godiya.
Every thing the same, except color. Na ummu sulaim purple, blue and pusher pink. Suma da takalmi da jaka kowanne. Nan suka kwasa zuwa nunawa iyayensu. Cike da farin ciki.
**************
CYPRUS
” dud, abinda kake baka kyautawa, tun dazu muka shirya muna faman jiranka, don iskanci, Ashe kai ko shiryawa ma bakayi ba”
Tsaki yayi still idonsa na kan system din gabansa. Wata hadaddiyar murya naji, mai matukar dadi, da kwantar da hankalin mai saurare, ” sorry dud, ina tunanin Ku tafi kawai, ina kokarin solving issue din kayan nan ne, bana son su wuce gobe. So I need more time. “
” u can do it letter, “
” no dud, kai kanka kasan in kayan nan basu isa cikin satin nan ba zaa samu matsala. It won’t be good for us”
Janye system din da akayi ne yasa shi dago idonsa. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Masha Allah. Na fada ganin kyan fuskar wannan saurayi, da kwarjini. Farine tas, hotonsa na yarinta na hango tabbas ba kowa bane a gabana sai Aliyu haydar zubair Yusuf Oregon. Tabbas yaci agric chicken din da hubby ke kiransa ganin girman da yayi, dogone, mai murjajjen jiki,. Kyan sufa, da kyan siga baa magana, kamar shi yayi kansa. Daga shi sai singlet da shot nicca.

HAYDER
Wanda ya janye system din nabi da kallo, tabbas da gani ba tambaya don suna yanayi kadan da hayder, sai dai hayder ya fishi kyau da tsayi. Hafiz omer kenan.
Sai wanda ya fara shigowa, da sai lokacin nakai idona Kansa. Da gani ba tambaya junaid, kyakyawan saurayi wankan tarwada, tsayinsu zai zo daya da haydar, sai dai hayder ya fishi sufar karfafa. Shi din siriri ne.
Masha Allah gaskiya Guy’s din nan sun hadu.
” mayen kudi, kai kam ban San in da zaka da jarabar neman kudi ba. Duk tsiyarka ka hakura muje mu dawo. Don zumunci ya wuce wasa. ” Hafiz omer ya fada yana ajiye system din kan wani kyakyakyawan center table.
Harararsa hayder yayi. ” alhamdulillah I’m looking for my halal my own sweating. “
” please tashi ka shirya muje, auren mutuniyarka fa ne, mu nan duk yan rakiya ne, amma don wulakanci mune masu zaman jiranka, abin da ya dace ace ka riga kowa shiryawa.”
” bazaka gane bane, new customer ne uncle ya hadamu dashi, this is the first time, kaga bai kamata a samu matsala tun daga farawa ba. That why.” Ya fada yana mikewa daga tsaye.
” duk da haka, muje u can finish it after we’re back, Anty bata can canci haka daga gareka ba. “
” I known, just 10min” ya fada yana shigewa wata Kofa dake daya side din.
” don Allah banda irin wankan kan nan na 2 hours. ” junaid ya fada yana zama a 3sittr din dake falon.
” muna waje in kun gama, amma please ka azalzala masa don ya shirya da wuri u known him”
Murmushi kawai junaid yayi ya kunna TV yana kallon kwallo cikin kwanciyar hankali. Don ya San haydar bai dade ba yayi 1 hour.
*****************
Hayder da junaid sun gama degree dinsu, one year back. Suna courses ne a kan software development. Sai Hafiz da alim su kuma suna rubuta final exams don shekarun course din su daban, su 4 years ne, su kuma su hayder 3years.
Sai Hafiz omer da Ashir Jamil. Already suna horsemanship, but suma watanni ya rage musu su kammala.
Business sosai hayder da friends dinsa suke yi. Tun first year dinsu a school.
Amir ne ya fara kawo shawarar,. Lokacin da suka aika masa da wasu belts. Daya ke shi ABU Zaria ya tafi.
Ganin kyan belts din da abokan karatunsa da suke ta yaba belts din yasa ya ce musu mai zai hana su siyo su turo masa ya siyar musu, don shi iyayensa basu kai karfin nasu hayder ba.
Kamar wasa ya matsa musu. Kudinsu da aka basu suka har hada suka sayi 10 dozens suka tura masa. Cikin yardar Allah wata na karewa sai ga alert a wayar hayder na kudinsu, da riba, ta kusan Rabin kudin.
Nan da nan suka kira amir, anan yake shaida musu still ana neman belts din. Shima ya gaya musu abinda ya samu daga ribar da a kaci. Don dama sun ce mishi ya dauki 20% .
Kusan 1 year suna tura masa belts, lokacin sun tara riba mai yawa, sai hayder ya bada shawarar su hada da takalma, don ya lura suna da takalma masu kyau da in ganci. Suma sun samu karbuwa sosai. Don tun amir yana siyarwa cikin school har ya zama yan wajen school ma suna oder ta anfani da whasapp, Facebook, Instagram da sauran su. Har ya kasance yan kasuwa kanana na Sara a wurinsa.
A cikin 3 years da sukayi yanzu suna wannan business din. Ba abunda basa sayarwa daya dan ganci bukatar gayu. Har da su perfumes. Ta ko ina customers suke samu, jarinsu yayi karfi sosai. Yanzu haka amir dake kula da komai a nan gida Nigeria ya mallaki muhallin kansa, ga motar hawa,.
Duk abinan da sukeyi ba wanda ya sani, sai daga baya. Hakan ya matukar burge uncle omer. Don haka ya kara musu jari, sannan ya hadasu da kampanonin da zasu dinga sarar kaya a wurinsu, ko su sasu suyi musu irin wanda suke so. Daga kasashe daban daban. a farashi mai sauki. Sannan ya hadasu da costumes da zasu dinga sarar kayan da xarar sunyi ready.
To wannan shine first customer daya fara yin ordering kaya a wurilimited iyasa hayder rashin sukuni, na ganin basuyi dis appointing din saba.
Every month suke lissafin ribar da a kaci, su ware wanda zaa kara a kan jari, su raba a junansu sauran. 7frinds for ever company limited shine sunan company din nasu.
Yara da kudi, abokan tafiyarmanya. Duka dukan su basu wuce 20years ba, don harder da junaid are 19years old.
Amma sun San zafin neman na Kansu.
Above of that. Hayder and junaid a software developers, duk da basu gama course din ba, amma har sun fara cin moriyar abun ta hanyar creating din applications, kamar su games, learning applications da sauran su. Wanda kullun kwanan duniya alart ne ke shigowa ta account dinsu.
1 hour ke nan suna faman jira, banda tsaki ba abinda Hafiz omer ke yi. Su Hafiz kam kowa ya kama loja a Sit din katuwar jeep kirar Mitsubishi, din da zasu tafi da ita. Sun sake music. Ashir da amir suna gefe suna dan hirarsu.
A cikin takunsa na kasaita mai cike da natsuwa ya fito da ga main door din. Sanye da back trouser sai White and red shart da jacket dinta black and red, black facing cap, white canvas. Ya yi kyau matuka. Harararsa Hafiz yayi. Murmushi ya sakar masa tare da daga masa gira daya. Key din motar ya jefa masa, ya cafe su ko tsaf duk da Nisan tazarar dake tsakaninsu.
” this is you’re punishment, for letting us waiting “
Wurga key din yayi sama ya cafe, driver sit ya bude ya shiga. Bai yi wata wata ba ya bata wuta suka hau main hanya.
Wani hadadden hotel suka nufa, Khuzaifa sultan motel. Naga an rubuta da manyan baki.
A daya side din hotel din ne naga an kawata wutin sosai, ga sweemig pool a tsakiya.
Haka sukayi ta gaisawa da friends dinsu, har suka isa wurin Amarya da angonta, wanda sun sha kyau. Da faraarta suka fara gaisawa idonta na kan harder dake Sosa sajensa da key din hannunsa, alamar rashin gaskiya. Ganin kallon da take masa yasa yayi murmushi tare da rike kunnensa, “im very sorry uhteee” kada kai tayi tana murmushi ” na Sani ai, tun da naga 5 ya wuce, ban ganku ba nasan Kaine.na rasa lokacin da zaka dinga daukar Abu so serious “.
Hafiz ne ya amshe ” kamar kin san tin 3 o’clock muka shirya”
” I known ” ta fada tana Harararsa.
Sai lokacin ya samu gaisawa da angon nata. Ta hanyar rungume juna, sannan ya sumbaci hannunsa, yana masa congratulation tare da bashi hakurin zuwansu late.
Wata kyakykyawar budurwa ce ta karaso in da suke.
” yau wa khairat, kai su wan can table din” tana nuna mata table din dake kusa dasu. Wanda aka tanada mu samman saboda special quest.
Kallon hayder tayi ” kai kuma zamu hadu an jima.”
Murmushi yayi, yabi bayan su ammar da already sun ma isa wurun table din.
Da kallo yake bin wurin, duk ya wanci yan school dinsu ne. Kowa ka kalla ya kure adaka. Cikin farin ciki.
Uhtee kamar yadda ya kira amaryar. Ai nihin sunanta Sadiya Shehu sambawa. Haifaffiyar garin Kaduna. Mahaifinta Shehu sambawa, shine. Mataimakin Governor of Kaduna state. Karatu ya kawota Cyprus. Same school dasu haider. Jininta ya hadu da haydar duk da ba department dinsu daya ba. Sun hadu a restaurant din cikin school. Sadiya zata ba hayder good 2 years. Zakayi mamakin yadda hayder ke girmamata. Don Sadiya akwai kamun kai, bata da rawar kai irin na yaran masu kudi. She is simple person. Da farko su junaid sun dauka soyayya suke, don abune da basu taba ganin hayder na hira da Mace ba, har kaga 32 teeth dinshi. sai akan Sadiya. Sai daga baya suka fahimci kawai shakuwace da haduwar jini.
A nan Cyprus Sadiya ta samu miji, maaikacin costume, Osama bin hashim. A Nigeria aka sha biki, bayan ta kammala course dinta. So yanzu sun shirya yar kwarya kwaryar liyafa ne, saboda friends dinsu da basu samu damar zuwa Nigeria ba, Irin su hayder.
Ashir ne yama hazif signal. A tare suka mike ” one min” Hafiz ya fada yana Jan hannun ashir.
murmushin gefen baki hayder yayi. ” Allahu yaha dikum.”
Dariya sauran sukayi baki daya.
A hankali take takowa, kamar tana tausayawa interlocking din dake shimfide a gasan. Sanye take cikin ashobin yan matan Amarya. Grown marron da black, kanta daure da wani net mai adon flowers multicolor, kafarta yasha high hill black. Kallo daya zaka mata kasan ta hadu ta ko ina. Gaba daya hankalin da yawan mazan wurin yana kanta.
Nasrin ke nan, balarabiya haifaffiyar Egypt, karatu ya kawota Cyprus. Shekara biyu da ta wuce. Kyakykyawace ta bigawa a jarida yar kimanin shekara 17 to 18, tun da Allah yasa ta daura idonta a kan haider taji duk duniya ba wanda take so da kauna sama dashi. Sai dai babbar matsalar duk yadda taso ta fahimtar dashi irin dunbin kaunar da take masa, bata samu wannan damar ba. Don tun da ya lura da take takenta, ya sanya duk wata Katanga da zata zama sha maki tsakaninsu.
Yau kam taci alwashin Isar da manufarta gareshi. Zuwanshi wurin babban dama ce a gareta.
Daga nesa junaid ya hangota. Kallon hayder yayi yana murmushin mugunta. ” gafa mutuniyarka nan tafe” haider da idonsa ke kan wayarsa yana sipping coke a hankali, ya dago yana kallon junaid, kafin ya mai da kallon sa in da suke kallo. Tsaki yayi ya ci Gaba da abinda yake yi.
” masha Allah, gaskiya yarinyar nan ta hadu karshe, ” Hafiz omer ya fada yana kare mata kallo, kamar ranar ya fara ganinta.
Alim da shima baa barsa a baya ba ya shafa sajensa, ” gaskiya kam ta wanku”
Sallamarta ne ya sa su dan risinawa daga kallon kurillan da suka kafeta dashi. Lumshe ido Hafiz omer yayi, jin zazzakar muryarta. Alim da junaid ne suka samu damar amsa mata salkamar, tare da fara gaishe gaishe.
Gogan ko ko daga kansa bai yiba balle ya samu damar amsa gaisuwar da tayi.
Junaid ta kalla, cikin fuskar ban tausayi. ” ina son ganin abokinku minti biyu don Allah “
Murmushi junaid yayi, tare da kallon haydar dake faman danne danne a waya. Cikin harshen Hausa ya ce ” don Allah hayder ka saurari yarinyar nan kaji abinda zata ce, ” kallon kasan ido yabi junaid dashi, ganin haka ya sa junaid kara marai rai cewa ” please mana, tun da kaga ta tako har nan kai ma kasan maganar mai muhimmanci ce “
Kallon sa yakai kanta, ido hudu sukayi, ta sake masa wani kayataccen murmushi. Kansa ya kawar gefe, tare da furzar da wata iska mai dumi daga bakinsa.
A hankali ya mike, ya nufi can gefe dake da karancin jamaa. Nasrin ta take mai baya.
Akwai irin dogayen kujerun nan a wurin, don haka yana isa yayima kansa mazauni, wurin tamkar lambu haka yake, sai kamshi, saboda flawers kala kala dake shuke a wurin.
Same kujerar ta zauna, sai dai dan nesa kadan dashi.
Sun kai 5 min ba wanda ya cewa dan uwansa komai, kallonsa kawai take, tana faman sauke ajiyar zuciya jefi jefi, tana tunanin ta inda zata fara. Don gaskiya yana mata matukar kwarjini, balle yanzu da take gabansa.
Shi kuwa zaman ne ya fara isarsa, ga haushinta da ya cika zuciyarsa. Ya ci a ce ta gane baya muradinta tun ba yauba. Amma ta kasa ganewa, shi ya rasa me yasa wasu matan basu da tunani, ya kamata in mutun ya nuna baya muradinki ki hakura, amma wasu a lokacin ne suke kara zage damtse, sun manta baa soyyaya dole, kamar yadda baawa zuciya dole. Tunawa yayi da karon battarsu da naufal, tsaki yaja a hankali.
“Sorry na San na takura maka da yawa, amma kasan ba laifina bane, laifin zuciyata ce, data kasa amincewa da rashinka a kusa da ita. Na dade ina neman irin wannan damar da zan bayyana maka sirrin xuciyata, ban samu ba, ko kuma ince baka bani dama ba. Ko ban fito na fada da baki ba, nasan ka dade da fahimtar dunbin soyayyata a gareka. Don idanuwana da gabbaina sun dade da nuna hakan. Ba zan boye maka ba, gaskiya zuciyata ta kamu da matsananciyar soyayyarka, wanda har nake jin bazan iya rayuwa ba, matukar babu kai a cikinta.” Shiru tayi tana son ganin reaction dinsa. Amma ko kadan bata iya gane komai ba.
Sun dau some minutes ganin bashi da alamar tanka mata, ta kuma kasa karantar yanayinsa. Yasa ta marai rai ce fuska ” please hayder don say u not love me, Allah zuciyata bugawa zatayi” kyawawan idonsa ya zuba mata wanda ya sata dan rawar jiki, da nemo Karin natsuwa ta sawa kanta.
” wane irin soyayya ne kike magana? A iya sanina soyayyar da zaa yi for some time ayi aure, right? ” kai ta daga don muryar ma ta kasa fitowa, saboda tsoron amsar da zai fito daga bakinsa.
Kai ya kada tare da gyara zamansa ” look at me ” ya fada yana tsareta da ido.
Kasa kallon kwayar idonsa tayi, ta sunkuyar da kai, tana wasa da phone dinta.
” I’m just 19 years all. At lest nan gaba ina bukatar 5 to 7 years kafin in yi settling in fara maganar aure. Ta Yaya kike son in fara soyayya dake bayan nasan bani da feature dake? Nan da 2 to 3 years nasan ko baki fitar da miji ba iyayenki zasu fito miki dashi, su aurad dake. So ta Yaya kike son mu yaudari kanmu? Bayan kin Sani na sani wannan is not a good idea, and it’s not work.”
Shiru sukayi, kowa na nazari . cikin miryarta mai zaki ” I’m wait for u, ni dai fatana ka soni ko da rabin son da nake maka ne, nasan iyayena baza su takura min ba, musamman in sun tabbatar da kayi alkawarin aurena in har lokacin yayi. Ni kadai iyayena suka Haifa, suna son duk abinda na keso, already sun dade da jin labarinka, ganinka ido da idone kawai basu yi ba.”
Kallon ta yake, tabbas iya gaskiyarta take fada.
” I need some time, to think about it” ya fada yana mikewa.
Jiki a sanyaye ta mika masa wayarta ” you’re number please ” wayar ya juya yana kallon yadda aka kawatata da flawers sai katon heart a bayan wayar dake daukar ido MY HEART BELONGS TO YOU A. Da manyan baki cikin harshen larabci.
Tabe baki yayi, ya typing number ya mika mata wayar.
“Thanks”
A hankali suka tako zuwa table din su hayder,
Tun da suka doso idonsu junaid na Kansu. Ganin kallon yayi yawa yasa haider aika musu da harara. Sallama ta musu ta nufi wirin zamanta. Ko yanzu ta samu peace of mind duk da tana taraddadin amsar da zata fito daga gareshi.
” kai dud, amma fa kun balain matching,. Gashi kuma da alama wannan ta samu babban matsayi tunda har aka saurareta, har da jerowa tare.'” Alim ya fada cike da murmushi a fuskarsa.
Harara haider ya aika masa, tare da Jan kujera ya zauna. Plate ya jawo ya fara serving kansa, da abubuwan cin, da sha, da aka cika table din dasu. Yana jinsu suna ta masa tsiya yaki kulasu, don yasan so suke suji kanun labari, shi kuma bai shirya ma topic din ba.
Sai lokacin su Hafiz suka dawo, daga shan shisha, da aka ware guri duda ga masu bukata.
” Allah ya shiryeku kullun mutun yayi ta durama cikinsa hayaki, kamar wani gafiya, Ku ko Dan tsoron cututtukan nan bakwayi? Please anaiwa kai fada mana?”
Dariya su ashir sukayi ” lallai kam, ba gara mu ba da muka tsaya a hayakin! Kai har kanada bakin yiwa wani fada, ka fara da kanka tukunna” Hafiz ya kara da ” namu ai mai sauki Ne, baifi ace your die Young ba, kaifa hatsarin dake cikin naka yafi namu sau dubu”
Hafiz omer yayi dariya ” shi ke nan ai, tunda bakwa son gaskiya. U will die young “
” better to die young than to die in shame” ashir ya fada yana Jan plate.
Junaid dake faman musu dariya ya kalli ashir ” surukin naka kake gayawa haka? “
Baki ashir ya rufe yana kallon Hafiz omer dake faman aika masa da harara. Kunnensa ya rike da duk kan hannayensa ” I’m very sorry dud, subutar baki Ne.”
Duk Kansu sai da sukayi dariya yadda ashir din yayi da fuska yana bada hakuri.
” kaga ai ni ban ce wani Abu mai zafi ba, duk wannan dan iskan ne, yake son hadamu” ya kaiwa Hafiz duka. ” daga yau ko kallon in da ake shan shisha ban sake yi, balle in sha, sai in tsautsayi Wanda baya wuce ranarsa. Kamar yadda kai ma tsautsayi ke giftawa tsakaninka dasu Linda. “
Murmushi Hafiz omer yayi, tare da kauda kansa gefe. Har ga Allah yaji wani iri a ransa. Ya zai yi he can control his desires, shi yasa yana komawa gida aurensa zaiyi, don baya son irin wannan rayuwar ta zamo masa jiki. Don ko yanzuma sai abun yafi karfinsa yake Dan ganawa da Linda.
” yayi kyau ka gama gyara fadarka, zamu hadu ne” Hafiz ya fada yana murmushi
Haka sukai ta hirarsu da raha, ga kayan ciye ciye. Har to 11, sukayi sallama da Amarya tare da bata gift din da suka kawo mata suka tafi.
Hafiz ne ke Jan motar wannan karon
Duk Kansu San darewa sukayi a tsaye, ganin wadda ke tsaye a bakin kofar da zata sadasu da apartment din su, jin gine jikin kofar ta rungume hannayenta. Gaba daya idonta na Kansu……………Wani wawan kallo harder ya yiwa Hafiz omer. Murmushi yayi tare da tabe baki, yana daga kafada alamar he has no idea.+
Da sauri ta matsa a jikin kofar ganin yadda ya taho cikin fushi, ga uwar harara da yake narka mata. Hatta hantar cikinta rawa take, don tana matukar tsoron haider, bata manta warning dinta da yayi.
Tsaki yaja ya wuce ciki. Da sauri Hafiz omer ya ja hannunta sukayi gefe.
” what bring u here? After all the warning? Na gaya miki koma menene mu hadu a inda muka saba haduwa, ban son na kara ganin kafarki a nan.”
Marairace fuska tayi, tare da shigewa jinsa. ” I’m very sorry, na nemi wayarka na kasa samu, kuma I need some money”
Tsaki yaja ” what is your problem? Nafa fara gajiya da yawan tambaye tambayenki. Ke kullun baki da aiki, sai a baki, a baki. Banki ne ni aka gaya miki, ko bishiyar kosai ne, kika shuka?”
Kirjinshi ta fara shafawa da hannunta da yasha adon fake nails. ” haba nawan! in ban tambayeka ba wa zan tambaya? Kasan kai kadai nake kulawa,. So u have to take care of my needs. In kuma kaga ka gaji shi kenan their so many ways to the market “
cikin fushi ya dago fuskarta yana faman aika mata da kallo mai kama da harara ” me kike nufi?”
Murmushi tayi tare da zuba masa kananan idonta masu kama da na Chinese ” na San ka fahimci abun da nake nufi.”
Furzar da iskar bakinsa yayi, tare da lashe lips dinsa. ” I don’t have money, so it’s good idea to go our separate ways. I had enough of u.”
Da ido waje cike da mamakin kalamansa take kallonsa, don bata taba zaton zai ce su rabu ba. Ko da ta ce masa zata bi wasu, ta dai fada ne kawai. Ita da take fatan ta zamo matarsa ta ina zata yadda ta rabu dashi? Duk wani Abu da take bukata ga namiji ya na dasu, to ita kuwa ina zata nema, bayan gashi a gabanta.” I’m very sorry, karka sa zuciyata ta buga, u know how much I love u? Ya zan iya rayiwa ba tare da kai ba? You’re my everything. In na bata maka rai kayi hakuri. Dama foodstp dina ne suka kare, shi yasa kaga na biyoka nan.”
Kallonta ya keyi cike da tausayawa.
Linda Matthew haifaffiyar kasar Ghana ce, karatu ya kawota Cyprus. Yawancin responsibility din karatunta ita take fafutuka ma kanta, don iyayenta basu da karfi. Ko da tazo Cyprus aiki ta fara a wani restaurant, ta nayi a lokutan da ba a karatu, da kudin take tallafawa kanta. Haduwarta da Hafiz omer yasa ta samu sauki sosai ta fannin bukatunta. Hatta da aikin restaurant din ta ajiyeshi a gefe.
Kallonta ya keyi cike da karantar yanayinta. Tabe baki yayi ” ki je zan tura miki ta account, but ya kamata ki San yadda zaki dinga managing abubuwa, don na kula yanzu abin naki ya fara wuce tunanina.”
Rungumeshi tayi, tare da kai bakinta kan nashi, ta fara kissing dinshi, da kyar ya banbareta daga jikinsa, don shima ta fara sashi a wani yanayi. Da sauri ya shige ciki yana jaddada mata zai tura mata.
Da kallo ta bishi tana murmushi. ” I love u so much ” ta fada a hankali kafin ta juya ta nufi super market don tasan tunda yace zai tura mata, zai tura within no time kuwa.
Zaune yake gaban sa computer yana faman danne danne. Gefe daya cup din black tea ne ya na sipping a hankali, sai su junaid dake faman kallon boll a katon TV dake manne a falon. Da alama dawowarsu har sunyi wanka. Don dukkansu sanye Duke da kayan bacci.
11:23 dai dai Hafiz omer ya fito, shima sanye da kayan bacci a jikinsa. ” kaga angon Linda ” ashir ya fada yana murmushi.
Harararsa Hafiz omer yayi. Sai da ya hada tea mai kauri ya koma kusa da junaid ya zauna.
Hayder ne ya dago yana kallonsa, with seriousness ya ce ” mai zai hana in son yarinyar nan kake ka aureta kawai a huta, amma gaskiya bana jin dadin abunda kuke yi.”
Sai daya kurbi shayin tukunna cikin dariya ” baka da hankali, in rasa wadda zan aura sai wannan? In mafarki kake ka farka, kai yanzu in nace zan aureta sai ka yadda!?”
” mai zai hana, da zaman haramci ai gara halalin. Meye marabarta da Matar taka a yanzu? Hidimar da kake yi mata ai tafi ta wani mai iyalin. Please stop all this, in aure kake so just married her”
Kallon hayder yake yi cike da mamakinsa, sauran kam sai dariya suke musu kasa kasa.
” in mafarki kake ka farka. Haduwar bariki, rabuwar bariki, me zanci kuma da ita? In aureta in ce na auri wa? Ko ka manta fadar manzo S.A.W da ya ce Ku zabawa yayanku uwa ta gari? Wace irin tarbiyya ka keson yayana su taso dashi? Salihatun, mu’uminatin, kanitatun, sa’i’hatun, wa’ ab’ khara. Ita zan nemo ba wannan da ta gama ganyali a titi ba”
Gaba dayansu dariya suka fashe dashi, su Hafiz har da rike ciki.
” amma guy din nan Dan rainin hankali ne. Ta yaya zaka ce bazaka iya aurenta ba? Bayan duk kan alamu sun nuna da kai kadai take yarayya. Ai kawai ka aureta musha biki kaji.” Alim ya fada still yana kwasar dariya.
Junaid ya ce ” kai kafi dacewa ka aureta”
” inah!!!! Sabuwa dal zan baro, ba second hand ba. Don haka wallahi ya isheku haka. In kuma da mai so to bisimilllah.
” Allah ya kiyaye” kusan a tare alim da ashir suka fada.
” kai ma da ka mori gangan mai yasa baka killace ta ba, sai mu da ko kamshinta da amonta bamujiba.”
” Allah ya shiryi yan matan da suke sakema yan iska irinku jiki, Wanda da zaran kun gama morar ganga sai Ku yada korenta. Don duk Dan iska in ya tashi aure baya neman yar iska yar iwarsa, neman salaha yake ya aura. Ita kuma an mai data taxi no gari, daga wannan ya Mora yayi dumping sai wannan ya amsa, a haka rayuwar zata kare ba albarka.”
Hararar junaid Hafiz omer yayi. ” ni nema dan iskan ke nan?”
Baki junaid ya rike yana murmushi ” ni na isa, in ce maka dan iska. Musali kawai na kawo.”
Kada kai Hafiz omer yayi, ya ci gaba da shan tea dinsa.
” ka gaya mata kar na sake ganin kafafuwanta anan, in ba haka ba daga kai har Ita Will pay the price “
Kallon hayder yayi cike da jin haushin maganarsa.
” bazan fadan ba, naga kai ma kana da baki, me yasa da ka ganta baka gaya mata da bakinka ba.”
Murmushin gefen baki hayder yayi ” ok, in sake ganinta kaga”
Tsaki Hafiz omer yayi ” kar ka manta I’m older than u, so respect me for that “
Kada kai hayder yayi, ya ci gaba da aikinsa.
Hafiz omer ya taso ya dawo kusa dashi ya zauna.
” I’m sorry, na tabbata bazata kara zuwaba, already na mata warning”
Gaba daya dariya suka sama Hafiz omer.
Harararsu yayi.
” better for u, dan wallahi muddin ta kara takowa nan, ka tabbata ka aureta ka gama. I have a lot of probe da zanyi sending yanzunnan kaga aiki da cikawa.”
Marai rai cewa yayi “i say sorry mana” don yasan halin kayansa tsaf zai aikata abunda yafi haka ma in dai hayder ne.
” it’s OK”
” ammafa gaskiya kasan ka takura mana ko? Kamar ba matasa ba, ka mai damu ustazan karfi da yaji!! Dan club din nan bada mu ba, dan night party din nan shima. Nayi regrating biyoku Cyprus, da yanzu ina England ina shanawa abuna.”
Da kallo suka bi Hafiz omer ganin yanda ya haki kance, alamar anfa takura masa. Ashir ne ya bude baki zaiyi magana hazif omer ya daka masa harara, ya na zaro ido.
Murmushi Ashir yayi ” mai da wukar, bani na kar zomon ba. Sai dai ina laifin wanda ya ce ka gyara kayanka? Te makonmu yayi, aboki na gari shine Wanda zai ga kana ba dai dai ba ya nuna maka kurenka, ya kuma nuna maka hanya mai kyau, wanda zaku tsira duniya da lahira. Ina amfanin kuruciyar da mutun zai yita cikin sabon Allah? Kyakykyawar kiruciya Ita ce wadda zaa yita cikin tsoron Allah, biyayya gareshi da kiyaye dokokinsa. Sai mutun yaci ribar kuruciya, yaci ta tsufa, San nan ya samu kyakykyawan karshe. Don haka ka dai na ganin hakan a matsayin takurawa, nasan wataran zakayi alfahari da hakan.”
” I know, but kasan zuciya, na son walwala, komai kan kantarsa.”
” baka yadda da maganar ashir ba kenan? Naga duk da sa idon nasa, still a hakan bai hanaka shanawa ba? Junaid ya fada yana murmushi
” kai ma ai danuwan dayan ne, na rasa daga kauyen da kuka fito?” Yayi tsaki
” Lego’s boy ” suka fada a tare suna dariya, don dama in ya kwafso musu wani abun haka suke masa kirari. Don so da yawa yakan ce musu yan kauye, su basu waye ba, balle Susan takan rayuwa.
Banda Haider dake kan system dinsa, ko dago kai bai yi ba balle suyi tunanin zai amsawa Hafiz omer maganarsa. Daga karshe ma daukan computer dinsa yayi, ya musu “good night” ya shige warsa.
Haka suka ci gaba da hira suna kallon boll har to 1am kafin kowa yayi makwancinsa.
******************
” princess ” cike da mamaki ta juyo. Gani tayi ya bude kofar ya fito.
Rungumeta yayi, ba tare da ya damu da salis abokinsa dake drive sit yana kallonsu.
Ajiyar zuciya suka dinga saukewa a tare, ya dauki lokaci yana rungume da Ita, kafin ya lalibi lips dinta ya fara aika mata da hot kisses. ” I’m going to Miss u, ji nake kamar in fasa tafiyar nan” ya fada yana maida numfashi.
Murmushi tayi tare da rike hannayensa duka biyu. ” Allah ya dawo min da kai lafiya, ni kai na ba na son tafiyar nan, tun da kake tafiyar ban taba jin haka ba.”
Murmushi yayi ” ko dai, ko dai “
Dariya tayi ganin yadda yake mata da ido. ” yes!! I’m jealous, ko laifine in yi kishin mijina?” Ta fada tana masa fari da idanunta masu matukar burgeshi.
Murmushi yayi yana dage mata gira daya ” I’m only yours, daga ke ba kari, sai hurul “ain in munje can, In sha Allah. Can kuma kinga baa kishi. So sa ranki a inuwa.”
Rungumeshi tayi, sannan ta sumbaceshi a chick ” I love u so much my king “
” love u too princess “
Hon salis ya fara sake masa, kiss ya mata ya juya da sauri, yana dannawa salis harara.
Murmushi salis yayi yana shafa kai. ” yanzu don kuturun wulakanci ka shanyani anan kaje kana kwasar love!!! Time yana ta tafiya”
Kwantar da kansa yayi jikin kujerar motar idonsa a rufe, sai murmushi yake sake wa. ” u won’t understand ” ya fada a hankali ba tare daya kalli salis din ba.
Tsaki salis yayi ” Allah ya bamu ikon shigowa daga ciki, ko ma huta ganin wulakanci. A yi ta daga ma mutun hankali a banza.”
Dariya Yusuf yayi ” da dai yafi, sa ido sana’ ar banza, ni ban San abinda yakai idonka, in da baa so ya kai ba.”
” Abu a gabana!! Sai a hanani bama idona abinci, ai da baa so na gani, da an shiga ciki. Ammafa gaskiya mutumin you’re very lucky. Allah ya samu a danshinka.”
Murmushi Yusuf yayi ” mu fara zuwa main house.”
Agogo salis ya kalla ” amma kasan time ya tafi ko?”
Kamar bazai bashi amsa ba. ” please muje I need to see my parent before I go.”
” why not in mun dawo mu biya? Kasan su auwal ba hakurine dasu ba, dama tun dazu suka isheni da waya.”
” don’t mine them, just 10min.”
Badon salis yaso ba, ya nufi main house. Don sun so shiga garin abuja da wuri, kafin lokacin daurin auren.
Yusuf maitama yelwa, shine sunan abokinsu da zaiyi aure, a garin abuja yake da zama,. Sun yi karatu tare da su Yusuf. Akwai zumunci sosai tsakaninsu.
****************
Sai da taga fitar motarsu kafin ta nufi cikin gida. Gaba daya ganin gidan tayi ya mata wani fayau. Zuciyarta ba dadi, ga faduwar gaba da ta addabi rayuwarta, tsawon sati kenan in har bata manta ba, gaba daya satin bata da wani kuzari, jinta take tamkar wadda ta tashi daga cuta. Ga yawan faduwar gaba. Shi kansa mai gidan nata ta lura ya rage walwala, ga yawan tunani data lura some time yana yi, ta dauki hakan kan tsananin takura da take ciki na dangin miji. Don ta kai har Hajiyasu Yusuf da takan samu sauki a wirings ta fito kiri kiri ta shaida mata dole Yusuf ya kara aure, don ba yadda zaa yi ta rungumi hannu tana ganin dan da tafi ji dashi duk cikin yayanta, ya kare da juya.
So koda taga rashin walwalar mijin nata, sai ta dangana shi da waccan maganar. Daga ita har shi suka maida komai zuwa ga Allah. Don gaba daya a satin mijin nata ya canza, duk da dama mutun ne mai matukar rikon addini, amma abin sai ya nunku a kan da. Ga yawan waazi, mai kama da wasiyya da yake yawan yi mata da zaran sun zauna zaman hira.
Don bata manta ranar da take ce masa. ” ni kam ban gane maka kwana biyun nan, ka kara zama shiru shiru, ga waazi kamar sabon liman, wani lokaci kalamanka suna ban tsoro, har inji hanjin cikina na kadawa. Please me yake faruwa ne.?
Murmushi yayi kanta a kan cinyarsa ya Sumba ceta. ” kin San rayuwa bata da tabbas, dole sai anayi ana tuno da gidan gaskiya, wanda a nan duniya dan adam ke tana dawa kansa shi. Fatana mu samu kyakykyawan karshe. Kwanan nan wasu irin mafarkai ke damuna, wanda suke sa in ji imani, da girmama karfin mulkin ubangiji, sun mamaye zuciyata. Jina nake kamar wani bako matafiyi, wanda ke kan hanyarsa ta komawa gida.”
Kallon sa take cike da tsoron kalaminsa, tana kokarin hasaso inda maganganunsa masu kama da juna suka nufa. Hure mata idon yayi yana murmushi. ” don’t worry ba mutuwa nake nufi ba, in sha Allah sai naga kwanmu nida ke, naga kuma abin cikin kan.”
Kwal kwal tayi da ido ” in sha Allah my king. please ka daina min irin wannan maganar, hankalina tashi yake.”
Murmushi yayi yana Kada kai ” i’ihim i’himm”
Bakinsu ta hada wuri daya, ta fara aika masa da hot kisses.
Ganin zaman gidan bazai mata ba, ta kirashi a waya, lokacin sun fita daga garin Kaduna. Kan zata main house, bai hanata ba. So a gurguje ta shirya ta Zari key din motarta tayi waje.
15min ya kaita main house. A harabar gidan ta faka motarta kirar CRV2018 jeep black. Ahmad ne da Abdul majid kanin Yusuf tsaye jikin daya motar dake kusa da inda hubby tayi parking.
Da faraa suka fara gaisheta. Don gaskiya bata da matsala ko kadan dasu suna matukar girma mata. Anty sama Anty kasa. Itama cike da faraa take amsawa tare da yambayar Ahmad munaya, da yara. ” kai kam kayi wuyar gani, naga alamar nan gabama sai mun cike form tukun nan zamu samu ganinka” ta fada tana kallon Abdul majid
Dariya suka yi gaba daya ” sai hakuri Anty kin San yanayin aikin namu, da kyar na samu far mission na one week, dazu nake maganar da mijinki zan zo kwasar gaisuwa sai gaki.”
Murmushi tayi.
Ahmad ya ce ” wannan aikin naka kam bai yi ba Sam wallahi, ina tausayin Matar da zata yadda ta aureka, kullun mutun yana cikin teku kamar wani kifi. Baka da lokacin kanka ina ga iyali?”
Dariya Abdul majid yayi ” kaji brother mai zai hanani samun mata? Haka zatayi hakuri dani, har ta saba.”
“Lallai kam”
Ahmad ya fada. Sallama sukama hubby zasu dan fita, Abdu majid “ya ce bari muje in gaishe da kakus I hope zan sameki?”
” a gaishe min da su da kyau, sai yamma zan koma” ta musu sallama ta nufi cikin gidan.
Part din Maman Yusuf ta nufa. Don tunda ta auri Yusuf Mmn Yusuf ta sa dokar bata yadda ta fara zuwa ko ina ba, sai ta fara zuwa wurinta tukunna. Duk shakuwarsu da Hajiya yanzu kiri kiri bata isa tayi good 20min a part din Hajiya ba, sai Mmn Yusuf ta hauta da balain wai ta zauna a can suna kulle kullen makircin da suka saba. Ganin hakan yasa dole take kiyayewa don a zauna lafiya, don bata son ya zama duk zuwanta ana samun matsala tsakanin Mmn Yusuf da Hajiyan. Sai dai a waya, zata kira hajiyan su sha hirarsu, tare da bata shawarwari masu nagarta, wanda take ganin fa idarsu da anfaninsu.