DA MA NI CE CHAPTER 10 BY JAMILA UMAR TANKO

bata fadaba daga yadda take amsa mata itama ta san ta gallabe ta. Sai lallaba Nasrin Malaika ke ta yi tana kwantar da kai akan ta yarda su yi kawance, har ma tana so ta kawo mata ziyara Abuja.

Nasrin ta ce sai ta dauki hutu yanzu kullum a wajen aiki take yini.

Nasrin ta na ganin kokarin Malaika na kiranta da take yi a kodayaushe, tana kashe kudin katin wayarta kullum gashi ba karfi gare ta ba, sai ta dinga turo mata katin waya na Dubu daya da dari biyar-biyar jifa-jifa, yayin da farin ciki ya lullube zuciyar Malaika ta ji ta Kara son Nasrin, ta tabbatar mai kyauta ce kuma zata karu da ita.

Shamaki ya zuba musu ido yana kallo kullum aka turo mata katin waya sai ta nuna masa gami da tsuyuwa ta tsawon awa goma a ramar, tana kiransa da wanda ya kasa. Wata rana Shamaki ya faki idon matarsa ya dauki lambar wayar Nasrin daga cikin wayarta.

Ya labe ya yi ta kira tunda safe ba’a dauka ba sai cikin dare misalin karfe goma sha daya na dare ta ga missedcalls dinsa rututu sannan ta kira da sauri ba tare da ta sanin mai kira ba. Aka ci sa’a kuwa Malaika tana bacci, ya fito falo ya labe ya amsa wayar.

Ranta ya baci da ta ji muryar namiji ne kuma wanda bata sani ba. Ya gabatar mata da kansa sannan ta tsagaita, tana sauraronsa cike da mamaki kai tsaye ta zaci halin maza zai nuna mata, irin cin amanar matansu a bi kawa a ce ana so. Amma da Shamaki ya fara koro mata bayanai cikin ilimi da muryar tausayi sai Nasrin ta dakata ta nutsu tana sauraronsa.

Shamaki yace, “a yanzu haka duk duniya

Matata bata ganin daraja da mutuncin kowa sai ke, Nasrin ki taimaka min kiyi mata nasiha, akan ta yarda da kaddara, ta yarda da yadda Allah Ya ke son ganinta. Ta kula da ni ta kula da yaranta amma ko da yaushe so take ta balle auren ta fita gari neman kudi. Ita a dole sai tayi arziki karfi da yaji.”

Nasrin ta yi shiru ta kasa magana tana mai tausayin Shamaki, tabbas yana cikin masifa.

Ta yi ajiyar zuciya sanna ta ce, “Ka yi hakuri da tambayata Shamaki, watakila ta bata maka rai. An ya matarka bata da tabin hankali?”

Nasrin ta tambaya cikin muryar girmamawa.

Shamaki ya girgiza kai, yace, *ko daya tana da cikakken hankali. Mace ce dai mai kwadayi da duban wadanda suka fita.”

Nasrin ta ce, «bata da ilimin addini da na boko ne?”

Shamaki ya gyada kai yace, “zan iya cewa “Eh’ zan iya cewa ‘A’a° saboda tana da shi daidai gwargwado dan tafi wasu da yawa amma basa yin irin halin da take yi. Kin ga kenan halinta ne ba jahilci ba.”

Nasrin ta yi ajiyar zuciya ta ce, “hakika na tausaya maka Shamaki kuma duk yadda ka fada na gasgata bazan musa ba, dan a yini daya yadda ma Nasrin take magana Hausar ma tana kwace mata, turancin Amerika take yi, dakyar in ba girman can ba ce. Lallai Malaika da Karfin hali take, ita da ta taso a Kauye Allah ya rufa mata asiri ta dawo birni da zama amma tana hangen ‘yan Abuja da ‘yan kasar waje. Ya ci gaba da tunanin yadda rayuwarsa da ta matarsa zata kasance nan gaba, saboda a kullum kutsa kai ta ke, kuma haduwa da manyan mata take sake yi,

tana sake tabarbarewa a koda yaushe. Ya ci gaba da addu’a Allah Ya sa ta gane.

Gari na wayewa Malaika ta tashi da fushi tana ta kunzumawa yara asharai Kwando-Kwando, wani ya yi kashi a kwance, wani ya yi fitsari, daya kuwa amai ya kelaya mata.

Shamaki yana jinsu yana so ya fito ya taya ta yana tsoron masifarta.

Ta taho a fusace ta daga labulen falon ta dube shi sama da kasa ta ce, “sannu hamshaki, Shamakin Muntsira wanda bai san wahala ba. Ka zo ka hakimce akan kujera an aura maka baiwa ko? To ka fito ka kula da yaranka gaskiya bazan iya ba da rayuwar talaucin nan, dan tsiya ko me aiki ma ba zaka iya samar min ba.”Shamaki ya yi murmushi ya fito tsakar gida, yace “ina jim  ku ai ina so in fito ina tsoron masifarki.”

Ta fusata ta koma daki ta kwanta akan gado ta ce, “ga su nan sai ka gyara su kayi musu wanka, kuma na gaji da wankin nafkin pampers zaka siyo min irin na ‘ya’yan kowa su yini da ita su kwana da ita.”

Shamaki ya gyada kai yace, “Cafdijam!

Allah Ya hore.” Ta zabura ta tashi zaune cikin tsiwa ta ce, “Daga anyi magana sai kace sai albashin wani watan. Wai kai nan dan albashi komai sai an yi albashi. Ni fa gaskiya bazan iya ba Yana jinta tana ta bala’i, bai kula ta ba, ya lallashin yaran, nan da nan suka yi shiru suna wasa da dariya ya wanke su tsaf ya shafa musu mai ya dora musu koko ya basu suka sha, kanana biyu suka yi bacci ya je ya shinfidar da su sannan shima ya yi wanka zai tafi makaranta dan yana da lacca karfe sha biyu. Ya tsaya akan Malaika tana ta danna waya bata kalle shi ba, ya mika mata kudi Naira dari biyu ya ce, “ga wannan a yi cefane a sayi ruwa.”

Ta daga kai ta kalla a shelake, ta ce,

“Dubu ce ko dari biru?”

Bai bata amsa ba ya ajiye a gabanta ya fice, yana fita tsakar gida, ya ji ta a guje ta tare gabansa ta ce “wallahi ba in da zaka je sai ka Kara min dari uku, kudin cefanena daga yau naira dari biyar ne kullum. saboda kowacce mace kullum sai mijinta ya saka mata katin waya. Idan da ka ce ba wandazan kira yanzu ina da manyan da nake magana da su kuma harkar karuwa ce harda kai. Sannan na gaji da cin mai da yaji miya zan dinga yi da nama kamar kowa. Kai hatta da kayan sakawata canjawazan yi, na gaji da atamfofi Kanana, leshina masu tsada irin na su Nasrin zan fara sakawa.

Ya tsaya yana kallonta, yanajin abinda take fada tamkar almara, ko mafarki. Ya ja hannunta suka shiga falo suka zauna ya jima yana kallonta ya yin da ita kuma take gatsine- gatsine.

Ya fara magana cikin sanyayyaiyar murya. “Malaika! Shin ada a haka muke, ba a Kauye muke ba gidan kasa da kara? Allah Ya daukaka mu muka dawo bimi har na kama gidan haya na siminti. Da a kauye ba tallar goro kike ba ni nake sayar da rake daga baya na sami aiki har na samu na dawo jami’a? Kika san babban aikin da zan samu idan nagama karatun nan? Haba Malaika, Dan Allah ki nutsu ki yi hakuri na dan lokuta Allah Zai warware mana. Babban tashin hankalina ma shine yaran nan musaminan marar lafiyar nan.

Malaika bakya kula da shi kin san yanayin ciwonsa sai da kula. Ki taimake ni Malaika ki taimaki yaran nan. Kin ga Aliyu ya isa shiga ” makaranta ko Nursery cikin unguwa ina so in saka shi amma asibiti duk ya cinye kudin.

Yanzu kina maganar in saka miki kudi a waya ki dinga kiran manya. Su waye manya?

Kada son zuciya ya kai ki ga fadawa ga halaka.” Ta zabura ta harare shi sama da kasa ta ce, “zargina zaka fara kuma? Ni Nasrin nake nufi da Dr. hala.”

Shamaki ya gyada kai yace, “ba zarginki zan yi ba, Malaika ban taba zarginki ba. Amma bai kamata ki fi ganinsu da daraja ba fiye da ni, ni mijinki ne kuma aljanarki tana Karkashin tafin Kafata. Ban rage ki da komai ba, bakya raga min. Abin ya kai ma mun raba shinfida daga na doso ki sai tsaki da hantara. Menene laifina? Dan Allah Ya halicce ni a talaka?

Malaika talauci ne laifina?”

Sai hawaye ya surnano daga idanuwansa yayin da Malaika ta kura masa ido itama

Idanuwanta sun cika da kwalla, ta yi sauri ta mike zata fice daga falon.

Ya jawo hannunta ya ce, “kiyi min alkawari daga yau kin daina duk abinda kike yi min. Kiyi min alkawari za ki gyara mu zauna lafiya. Ni kuma na yi miki alkawarin zan ci gaba da fada miki gaskiya da samuna da rashina. Albashin ma duk wata zan dinga kawo miki shi dukka kina kasaftawa, dubu goma sha takwas ne albashin.”

Malaika ta fisge hannunta ta fice da sauri ta koma daki ta kwanta. Ya fito yana goge hawaye da takardunsa a hannu, ya hau babur dinsa daya ajiye a zaure, ya tafi. Aliyu ne ya raka shi har kofar gida yana ta cewa “Baba ka siyo min alewa. Wayar Malaika ce ta hau kara jim kadan bayan fitar maigidanta, tama dubawa taga sunan Shamaki ne. Ta ki dauka gami da yin dan siririn tsaki ta ce, “me zai yi min kuma?”

Ya ci gaba da kira sannan ta dauka a fusace ta san dai wani abu zai ce ta saya duk a cikin dari biyu kamar wani kayan gabas. Ta fada a fusace “ina jinka.”

Ya yi murmushi yace, ina cikin

makaranta yanzu zan shiga Lacca nace bari in Kira ki inji muryarki gimbiyata.”

Haushi ya tokare ta, takaici ya baibaye ta yayin da dacin kunar zuci ya yi ta taso mata a makoshi. Ta yi tsaki ta kashe waya. Ta wurgar da wayar gefe ta kwanta tana takaici, ita fa duk wannan soyayar da zai nuna mata ba zata wadatar da itaba, ba zata zauna ta kare a cikin lungu ba bayan ga mata can suna fantamawa a cikin manyan motoci da manyan gidaje. Ta tuno yadda ta hango Dr. Hala a cikin motarta, ta hango Nasrin yarinya kamar furen fulawa saboda kyau da gayu, ga kamshi. Ta kalli kanta sama da kasa ta ganta kamar wata bushashshiyar bishiyar da ta bushe

a sanadiyyar fari, wacce ba’a bata ruwa da taki, hakika wataran faduwa zata yi ta zama bushssheshan itace daga nan kuwa sai sara a kwasa akai gida a dafa tuwo ya kone, ya zama toka.

Ta fada abayyane ba zai yiwu ba wallahi.”

Wayarta ce ta ci gaba da Kara ta maqi kallon wayar balle ta dauka sai a karo na uku ta sa hannu ta dauka a fusace ta san Shamaki ne, ta fada cikin tsawa bayan ta danna wai meye?”

Sai ta ji wata sanyayyiyar murya mai kama da ta busar sarewa, aka yi mata sallama.

Hmmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *