DA MA NI CE CHAPTER 13 BY JAMILA UMAR TANKO

*nasu, haka takälmana sun fatattake saboda tafiya 

Cikin’ ikon Allah duk wadanda muka fara karatun tare tun ba’aje ko in ba suka watsar da karatun a takaice dai a wannan lokacin ni kadai ne nagama sakandire a kauyenmu. Nima sai na yi kamar zan bari Malamin ajinniu. ya zo har gida yayi min

• nasiba dole in koma ba dan ina so ba saboda dani ake ji a makarantar ina da kokari sosai.

Kokarin da nake da shi ba irin wanda za’a ce na daya yake zuwa ba kullum, A’ a kokarin da zan gagari Malamai ina Kokarin Kure Malam a

•aji, idan aka yi jarabawa babu dalibin da yake

“samun maki kusa da nawa sai dai can kasa dani a kowacce jarabawa casa’ in zuwa casa’in da tara nakeci a cikin dari. Mutane har gani suke ko ni ba mutum ba ne ba ma.”

•Nasrin ta gyara zama ta ce, “dakyau shamaki ina jinka. Ya yi murmushi ya ci gaba da cewa, “Na fito da sakamakon jatabawa mai dankaren kyawun gaske. Malaminnan nan na ajinmu yayi iya

Kokarinsa, Wajer ganin gwamnati ta dauki

nauyin karatuna zuwa Jami’a, Ciyaman din gariamu na wancan lokacin ya ce zai taimaka min amma basu mayar da hankali ba, sun yi alkawari ba su cika, ba har aka canja gwamnati.

Na hakura da maganar karatu na ci gaba da mayar da rako a kofar gidanma, sai daga baya ina ta fadi tashin noman aiki bayan shekara na samu aiki a sakateriyar Bichi, anan nake aiki har yanza da satifiket dina na nakandire. Nasrin ta gyada kai tace da kyau.

Malaika fa’ Wacece Malaika?”*

LABARIN MALAIKA:

Yace “Malaika Dahiru Muntsira, garinmu daya layinsu a bayan layinmu yake,tare muka tashi mun girme su amma dai dukka an yi wasa tare.

Babanta Malam Dahiru shine mai garin garinmu Kuma yana da mata hudu da yara da yawa, ko a dakin su Malaika ma su tara mahaifiyarsu ta haifa.”

Nasrin ta cika da mamaki a bude baki ta kasa rufewa dan mamaki. Ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Allah ya jikan Malam Dahiru.

Shamaki ya zabura, yace, “ai bai rasu ba yana nan ya dai tsufa, ai ita ‘yar gatace da uwarta da ubanta a raye.” Sai Nasrin ta zazzare ido tana mamaki dan ta fara jin banbance-banbance a tsakanin labarinsu, tabbas akwai makaryaci a cikin su biyun nan amma dai bari sai taga abinda zai turewa buzu nadi.

Ta yi gyaran murya ta ce, “Allah sarki ai na zaci ya rasu ne, Allah ya Kara girma.”

Shamaki yace,”Amin. To kasancewar mu a Kauye, dan sarki da talaka duk talakawa ne kowa na yakin neman abinda zai ci, suma a gidansu akwai tsabar gero da masara ammafa mahadin dahuwa kowacce ita zata nema da yaranta. Haka muka taso kuma muna jin dadin rayuwarmu kamar kowa, Allah ya jarrabe ni da son Malaika itama tana sona sosai har ma fiye da yadda nake sonta. Ban taba yin budurwa ba a rayuwata sai Malaika ita kadai na tabaji ina so har a cikin raina, haka itama ni kadai take kulawa. Mahaifinsu yana tilastawa ‘ya’ yansa

mata da maza su yi makarantar firamare kasancewarsa mai gari dole sai an ga yaransa suna zuwa makaranta sannan ‘yan gari zasu yarda su bar nasu ‘ya’yan su je, dan haka Malaika ta gama firamre tas, ni na je na sami babanta na bashi shawara ta tafi sakandire ni zan dinga yi mata siyayyar makaranta da yake Makaranta kwana ta ci.

Ya amince Malaika ma bataso na lallashe ta, dan bata son bacin raina aka kaita makarantar kwana ta garin “Dan zabuwa’ nan kusa da garinmu.Garin kwaki, Kanzo, maggi, man gyada, gishiri sune dai siyayyar nake siya mata, idan ya kare ta yi min wasika wani Malamin makarantarsu ya kawo min in siya in bashi ya kai mata. Idan kuma ranar ziyara tazo wato bisiting ni nake je mata, kawayenta kakaf sun san Malaika da Shamaki, dan soyayya ma haka ta mayar da sunanta a makaranta ba’a kiranta da Malaika Dahiru. A garinmu kowa ya san soyayyata da ita, samarin da suke sonta da yawa mun sha tare ni dambe a hanya suna ganin a dalilna taqisu, haka itama ta sha

dambe da ‘yan matan da suke matukar sona bana kula su. Ina sana’ar rake bana tsinanawa kawa komai a jikin Malaika nake karewa, dangina suna ta zagina hatta mahaifiyata sai da ta fara jin zafin haka takan kira ni tayi min fada, ina tabbatar mata wani abin ma karyar ‘yan gari ne ba ayi ba.

Sai da na zamar da Malaika abar kwatance a cikin Kawayenta, nine dinkunan sallarta, nine ankon bikin kawaye da danginta, nine kudin kashewarta, ni na bata jarin da take sayar da wainar fulawa da awara a kofar gidansu idan tadawo hutu. Malaika tana da kokari matuka kuma na yi Kokarin koyar da ita abubuwa da yawa idan an yi hutu, hatta turanci ni nake koya mata. Har ya zamanto ta fi Kawayenta iya turanci, sai ayi ta mamaki idan aka ji tana turanci.

Tana matukar jin maganata kasancewar tana da tsiwa da taurin kai dan wani lokaci sai mahaifiyarta ta kira ni a kawo min kararta in yi mata fada sannan ta bar abinda take yi. Tana aji hudu na sakandire Mahaifinta yace ta isa

Hmmm