DA MA NI CE CHAPTER 16 BY JAMILA UMAR TANKO

sauri ta juya baya ta cinye tas ta wurgar da takarda, ya zaci wasa ne. Ya ce ta dauko masa abincinsa na dazu zai ci. Ta harare shi ta ce “ai ka yiwa kanka wallahi mun cinye tas ka je ka nemi abincinka.

Tunda kai ba’ ayi maka gwaninta, kamar wacce ta samo kudin haram har da kin ci kuma wallahi duk ran da ka dake ni ka daki aurenka.” Shamaki ya zauna yayi shiru yana kallonta yunwa yake ji ta gaske kuwa, dan tun kokon safe ne a cikinsa gashi ba shi da ko sisi.

Bashi da karfin yin magana ma balle fada, sannan baya son ma a Kara tayar da zancen dan daga baya da ya huce sai ya ga bai kyauta ba kamata yayi ya yiwa Nasria kyakyawan zato tunda taimakawa ta yi.

Ya yi ta karanto istigfari a cikin

zuciyarsa. Duk abinda Malaika take fada masa kalma daya yake fada yana ta nanatawa kamar karatu ” yi hakuri, yi hakuri, bazan sake ba.”

Har sai da Malaika ta ji ya fara bata tausayi sannan ta daina tsigale shi. Ya tashi ya fita kofar gida ya je wajen mai shayi da biredi na kan kwanar gidansu anan ya ci bashi ya cika cikinsa ya dawo gida. A ranar dai Malaika bata kula shi ba, baya ta juya masa ya gaji da magiya ya rabu da ita.

Asuba ta gari!

***

Shamaki ya shiga cikin matsananciyar rayuwa, ko inaba dadi, can garinsu yana kula da mahaifiyarsa wacce bata da komai tana neman taimako, kannensa gaba daya babu mai shi babu wanda ya yi karatu a jikinsa ma suke nema, ‘ya’yansa abin tausayi ya kamata an saka su a makaranta amma suna zaune a gida, ga marar lafiya kuwa wani lokaci sai dai a hakura a zuba masa ido yana ta kuka babu kudin magani, Malaika abar kaunarsa ta tsane shi ta juya masa baya, ya manta rabon da ta yi masa hira mai dadi.

Baya gushewa da yin tsayuwar dare da addu’a yana kuka yana fadawa Allah. Ya na nemawa Malaika gafara da shiriya dan baya fatan Allah Ya kamata da laifin kin yiwa miji biyayya da butulcin da take yiwa Ubangiji. Malaika kuwa ga ni take kamar duk rashin gata da rashin sa’a akanta ya Kare, gani take tamkar ta rako mata duniya. Idan ta tsaya a titi ta hango mace ta na kotsewa a cikin mota mai kyau ta gani ta fada sai ta ji ta tsani kanta.

Dan haka itama rayuwar ta yi mata kunci bata walwala ko kadan.

Al’amarin Nasrin kuwa ta shiga rudani matsalar Malaika da Shamaki ta tsaye mata a rai, ta shiga aikin tunanin tantance waye mugu a cikinsu kuma waye yayi mata karya, a haka dai kowa ya nuna mata shine abin tausayi dayan ke cutarsa.

To Allah Shine Masanin badini da Zahiri.

ABUJA:

a misalin karfe goma na dare

Nasrin tana sanye da kayan bacci tana kwance akan gadonta

tana ta danna Computer ta har yanzu dai tana biye da Dr.Jalo mutuminta, ta ga ya yi sababbin rubutu ya turo. Tana ta bibiyarsa a hankali tana karantawa sai ta ci karo da wani rubutunsa wanda ta ke neman karin bayani akai, yadda ya yi rubutun ma kai kace da Shamaki da Malaika yake, ma’auratan da suka kasa fahimtar juna. Sai ta je tayi comment a kasan posts dinsa. Bai bawa kowa amsa ba, dan ta iske daruruwan mutane da suka tofa albarkacin bakinsu, mata da maza suna ta mahawara. Gogan naka bai tanka ba shi dai ya zuba bayanai ya kara gaba, ya bar mutane da hayagaga. Ta dubi lokacin da ya turo sakon, a ranar ne da safe.Ta dauko wayarta zata kira shi sai ta kalli agogo ta ga dare ne bai kamata ta kira mai aure da daddare ba dan ta tabbatar yana da mata kada ta hada su fada.Ta dubo cikin hotunansa ta ga ya sake ‘profilepicture’ insa, tabbas ya yi kyau matuka kamar ka kira shi ya amsa. Idanuwan nan dara-dara, hanci dodar, hakora a jere reras gwanin ban sha’ awa ya saka wani farin gilashi wanda ya yi masa kyau, kana ganinsa kaga cikekken likita, likitan da yasan abinda yake yi. Ta dade tana kallon hoton nan a ranta tana mamakin yadda ta sami mutumin da yake birge ta.

Dr.Jalo ne kadai mutumin data taba haduwa da shi take binsa ya ke ja mata aji.

Shima babban abinda ya birge ta shine tunaninsa da fasaharsa lallai duk wanda Allah ya bawa fasahar rubutu ko ta magana lallai ya godewa Allah, ba kowa ne yake samu ba kuma ba’a saya a kasuwa, haka ba’a koyo a makaranata.

“DA MA NICE Dr Jalo! Dr. Jalo.” Ta fada abayyane a lokacin da ta ci gaba da kallonsa.

Hmmm