Tana cikin- wannan hali sai gashi ya hau
• facebook. Ta zabura ta bishi ta ‘ inbox ta yi masa magana. Salama ce da gaisuwa ta tura masa, nan da nan ya amsa mata. Sai ta yi mamaki. Daga nan da kwarin guiwarta ta tura masa jinjina da yabo akan rubuce-rubucensa.
Sai bai bata amsa ba kuma tana ganinsa
* ‘online.’ Ta sake tura masa cewar tana so su dinga gaisawa ya dinga bata shawarwari.
-Bayan ta jima da tura sakon bai bata amsa ba
ma sai ya sauka daga facebook din ma. Ta san , kuwa ba zai dawo a yau ba, ko ya dawo ba zai bata amsa ba.Ta ji kwallar takaici ta sumano mata ta fara
• tsanar kanta da kanta ma da take jawowa kanta wulakanci, tana mamakin masu wulakanta mutane dan sunga mutane suna sonsu. A sanadiyyar Allah Ya yi musu wata baiwa, tabbas ita bata da wulakanci tun ma bata fara hulda da mutane haka ba, yanzu data fara harkar rahotannin nan ana nuna ta a talabijin ta samu masoya da yawa da suke turo mata da sakonni ta waya ko ta Email dinta. Tana kula
kowa yadda ya kamata shiyasa ma ta tsaya ta kula Malaika har suka saba. Ta fara ji a ranta ba zata Kara kula Dr.Jalo ba bare ya sake yi mata wulakanci, eh yana da kyau, yana da ilimi, yana da kamun kai , yana da aji, watakila attajiri ne ko dan gidan attajiri. Sai aka yi yaya kuma? Da me ya fita?
Koda ace ya tara duk wadannan abubuwan da aka zano Nasrin tana da linkin nasa.Ta fara tunanin kai zuciyarta nesa ta manta da matsalar mutumin da bata sani ba.
Washe gari da safe ta shirya zata fita wajen aiki ta jawo computer ta zata kashe saita iske amsar Dr.Jalo da asuba ya turo mata.
Ta ji dadi a ranta harda rufe ido da budewa dan ta gasgata ba mafarki take yi ba ido biyu ne. Ya tabbatar mata yana farin cikin haduwa da ita kuma kada ta damu a shire yake ya bata shawara koma wacce iri ce. Hannunta na rawa ta rubuta masa godiya da nuna farincikinta. Baya kan layi amma ta san idan ya dawo zai gani. Ta fito falo tana walwala har sai da Salis da Zainab suka fahimce ta, yau tare da su ta karya kumallo sabanin idan ta fito da fushi bata tsayawa ta ci abinci. Zainab ta harare ta, ta ce “kin yi chats ko? Kin ji wani abu mai dadi dan nasan baki da abokai sai a socoalNetwork kullum kina kan computer, haka Kawawenki mutanen boye ne duk anan ku ke haduwa.”
Salis da Nasrin suka kwashe da dariya.
Nasrin ta ce, “ka ji wai muatanen boye
kamar wasu aljanu.
Da suka gama cin abinci Salis da Nasrin kowa ya dauki jakar laptop dinsa ya fita, Zainab ta rako su har wajen motocinsu kowannesu ya shi tsaleliyar motarsa ya nufi wajen aiki. Sai yamma kuma ko da magriba, Zainab * ita kadai take yini kuma bata sha’ awar •yan aiki saboda matsalarsu ta ishe ta.
Nasrin ta isa ofis, basu zauna ba yau, suka fita da motar ofis dauko rahotanni, acan ta yini basu dawo ofis ba sai da yamma likis wayarta ma a ofis ta bari a caji, ta zo ta iske missedcalls Malaika babu adadi bata damu ta kira ba dan ta san kiran kawai take yi dan bata da abinyi. Kullum sai ta kira ta ta ishe ta da surutu marar ma’ana. Dan haka ba zata kira ta ba itama sai ranar da bata da abinyi, sai su hadu su yi ta hirar rashin abin yi. Kafin ta tafi gida ta bankado Facebook dinta sai kuwa taga mutuminta yau ‘yan siyasa ya ragargaza ya kawo musu misalai da manyan ‘yan siyarsar kasashen da suka ci gaba wadanda suka san darajar bil’ adama. Ya kawo misalai da ‘nelsan Mandela’ da ‘General Muhammad Buhari’ z0 kaga ruwan yabo da jinjina da ake yi masa.
Nasrin ma ta shiga ta zankada turanci irin na su • na gwanaye, ta yabi gwaninta Dr.Jalo, ta yaba masa akan fadar gaskiya komai dacinta.
Tana shiga cikin inbox dinta sai taga ya turo mata da sakon gaisuwa, daga nan dadi ya kusa tafiya da ita dan ji ta yi ta yi luuuu® kamar zata shide dakyar ta dawo daidai. Ta godewa Allah da Ya sa wanna hazikin bawan ya san da ita. Nan take ta bashi amsa tana mai tabbatar masa tana nan lafiya cikin Koshin lafiya tare da tambayarsa lafiyarsa shima.
Tana turawa ta tashi rataya jakar laptop dinta ta fito daga ofis tana tafe tana rangwada, tafiyar ma yau sai da ta canja ta. Har sai da abokan aikinta suka fahimci yau nishadi take ji, masu gadi sun sha kyauta tunda daga reception take kyautar kudi har zuwa get. Ita a ranta sadaka take yi, da neman yarda Allah, Ya Kara dorata akan miskilin hazikin nan, gwaninta Dr.Jalo.
Ta iske yayarta Zainab a kicin bayan sun gaisa ta shiga daki ta yi wanka ta fito sanye da riga shimi da wando iya guwa (Three Quarter)
za ta tayata abinda zata iya yi dan ita bata son aiki musamman na kicin, dan bata sababa.
Nasrin ta na ta yiwa Zainab tsiya saboda bata daukar kuku da masu aiki, sai bayan kwana bibibiyu wata inyamura take zuwa ta Kalkale mata gidan ta tafi ba zata dawo ba sai bayan wata kwana biyun kuma kullum, ita ke yin girki da kanta. Dan haka ne bata son ta yi aikin gwamnati alhali har masters gare ta.
Hmmm