DA MA NI CE CHAPTER 19 BY JAMILA UMAR TANKO

-kawo mata farmaki saboda mijinta kadara ne.

Kin ji muryarsa kuwa . . Hmmmm, ba

magana ke guy din ya hadu daga kafa zuwa tsakarkai.” Suka sheke da dariya suka tafa hannu.

Dina ta ce, “Nasrin kina son likitan nan ko?” Nasrin ta yi fari, ta da gaido sama tana tunani ta ce “not really but. Dina ta katse ta, ta bangaji kafadarta ta ce “but me? Kawai ki fada min gaskiya kawata. Ina zaki ajiye Engr. Fu’ ad?” Nasrin ta ce, maganar gaskiya Dr.Jalo

yana burge ni amma ba don kyansa ba, dan in karu da iliminsa kin san ni da son aikin jarida, bayan haka ina son mutum mai aji. Duk ya hada.?

• Dina ta ce, *idan na kula kina son alaka da shi ta kurkusa bata nesa ba.”Suka yi dariya suka tafa.

Nasrin ta ce, “ke muyi wata hirar mu share wannan dama bai san abinda muke yi ba.

Allah Ya bamu maza na gari muma.”

Dinah ta ce “da dai ya fi.” Wayar Nasrin ceke Kara Dinah ta miko mata da sauri, Nasrin ta na dubawa taga sunan Malaika, sai ta yi tsaki ta ajiye wayar a gefe. Dinah ta ce, “wacece Malaika?”

Nasrin ta yi dariya ta ce, “sabuwar kawa na yi a Kano idan na baki labarinta zaki yi kwana uku kina dariya dan nasan halinki abu kadan ma dariyar awoyi ki ke yi kina yi.”

Dina ta tuntsire da dariya ta ce,” dan

Allah ba ni labarin Malaika.”

Malaika ce ta ci gaba da kira, Nasrin ta ki dauka.

Dina ta ce “ki dauka dan Allah ki saka min ita a hand’sfree mu ci dariya.

Nasrin ta ce, “dan Allah rabu da itaba zan dauka ba, surutu zata yi ta yi. Ke! zama ki santa. Ina wacce aka taba nunawa a labari har kika kira ni kina ta shan dariyar turancinta, sati byu da suka wuce? To itace fa.

Dinah ta yi tsalle ta dire tana ta dariya ta ce “Wallahi sai kin dauki wayarta, in ba zaki dauka ba ki bani lambarta ni in kirata mu gaisa.” Nasrin ta hana ta, wayar dai har yanzu

Kara take yi, kira ake yi ana sakewa.

Can Dinah ta tsallaka ta dauko wayar acan Kuryar gado inda Nasrin ta wurga ta, tana dubawa sunan Dr. Jalo ta gani.

..Ta zabura ta mikawa Nasrin ta ce,

“ke mutuminki ne, Dr.Jalo ne yake kira, ba

Malaika bace.”ko jikina dukka kunne ne ba zan yardaba, ba wani Dr. Jalo.” Nasrin ta fada yayin data juyar da kanta gefe ta ki kallon inda wayar take.

Dinah ta dungura mata wayar wajen idonta tana kalla kuwa sunansa ta gani, sai ta karba da sauri ta danna, ta ci sa’a bata katse ba.

Rigijigafi! Wani kaya sai amale! Zo kaga ladabi a wajen Nasrin da nutsuwa. Ta koma gefe ta sami kujera ta zauna ta na magana kamar tana gaban sarkin Kano. Da turanci suke magana kuma cikin rada. Dinah ta gama kasa kunnuwanta iya kasawa amma ta kasa jiyo abinda take fada, har suka yi sallama suka kasha wayar. Nasrin da Dinah suka dau ihu suka rungume juna har sai da Zainab ta fito daga kicin da gudu ta zaci gobara ce ta tashi a dakin, sai ta iske su suna rawar ‘kerewa’ a tsakar daki.

Ta tabbaye su suka shaida mata Dr.jalo ne ya

– kira a waya. Haushi ya kamata ta yi tsaki ta fice, ta tabbatar basu da matsala a duniya shiyasa suke wannan tabarar. Har dare basu daina murna ba sai da

Dinah ta tashi tafiya suka fito daga cikin dakin, bayan sun Ki fitowa su ci abinci, Zainab da

Salis sun gaji da kira har sun ci abincinsu.

Sai a lokacin suka zauna suka ci nasu abincin

Zainab tana bawa mijinta labarin shiriritar da suke yi, ya sha dariya.

Ya fada a bayyane “yarinta mai dadi .»

Nasrin ta raka Dina wajen tsaleliyar motarta, ta shiga ta tafi.

Jama’a ga tambaya? Ina Malaika? Ta zo taga yadda matan Abuja suke matsa sitiyarin tsala-tsalan motoci.

RANAR ASABAR…

ASIBITIN NASSARAWA KANO

Malaika ta yi tagumi akan gadon asibiti ta zurawa Ahmad ido tana kallo, yana ta numfasawa

sama-sama. Hankalinta a tashe yake matuka

dan bata taba ganin ya galabaita haka ba, ta je

wajen Ma’aikatan jinya *Nurses ya kai sau

goma tana nuna musu yaddah numfashin danta yake

yi, tun Nurse tana bata baki har ta shiga tsuye ta, ta balbale ta da fada ta ce ai ba laifinsu bane laifin mijinta ne an ce ya je ya siyo allurai

tunda ya fita wajen awanni uku bai dawo ba.

Malaika ta dawo kan gadonta ta zauna tana

kallon matan da mazansu suke ta yi musu

hidima, ana ta ajiye kayan shayi da kayan

marmari na itatuwa, ita kan lokarta wayam

babu ko pure water.

Hmmm