zuciyarta, arma de ta tuna babbar sa’ar data ci ta samu ma ya amsa wayar yau, sai ta godewa Allah.
*Mu je zuwa• wai mahaukaci ya hau kura.
Ta jawo “konfiyutarta’ ta budo hotonsa a
•facebook ta dade tana kallon hotunansa shi da wani
dan kimanin shekaru hudu,
kyakykyawan yaro da alama dai dansa ne dan suna kama kuma da shakuwar da suka yi. Ta dade ta na kallo kuma tana karanta rubutunsa (posts), hakika wannan bawa, Ubangijinsa Allah Ya cika shi da tsantsar basira da cikakken ilimi. Kalamansa yana nunawa tabbas tsantsar masani ne haka babu kalmar da bata da amfani a cikin rubutunsa. Idan kana biye da shi lallai zaka karu ta fannin addini balle a zamantakewa, haka idan kana da ra’ayin siyasa zaka ginu akan adawa mai ma’ana da tsari, babu gaba babu cin mutunci.
Ta shiga cikin sharshin da jama’a suke rubutawa a kasan rubutunsa (comments). Da alama yawancin abokansa na facebook sun san shi a zahiri dan ta lura su kan tsokane shi shima ya tsokane su, suna kiransa da Dakta ko likita. Daga nan ta tambatar da cewa da cikakken likita take tare, lallai dole Jalo ya yi tsada a waya ma balle a ido biyu. Ta ji ya dada kwanta mata a rai ba dan su yi soyayya ba tana sha’awar yin mu’amula da shi dan ta karu a harkar rubutunta na jarida.
Ta nemo shi a bangaren watsapps da lambarsa, sai kuwa ta ci sa’a ta same shi da wannan lambar da suke magana.
“Madalla da social Network”. Nasrin ta fada a bayyane, yayin da take tsalle a kan gado.
Wuyanta ya kage sai ta kwanta akan filo ta yi ruf da ciki ta ci gaba da kallonsa a hoto, sai dai taga ya dade rabonsa da hawa watsapp tun watan jiya. Ko meye dalili? Oho!
Data leka ‘ instagram’ ma ta hadu da shi acan, amma fa mutumin akwai ruwan turanci, irin turancin da wata kalmar sai ka koma ka binciki ma’anar a dictionary.. Sai ga rubutunsa da larabci ma da yake ita ma gwanar larabci ce sai da ta karance tsaf, Ko a ina ya na magana ne akan ci gaban arewa, yana kira da musulmai su hada kawunansu,ya na magana akan a daina siyasar gaba da dabanci.
Nasrin ta shiga mamaki tana tambayar kanta da kanta “me ya hada likita da rubuce-rubuce irin wannan? Tsabar kishin • yarensa da Addininsa ‘ ne ko kuwa menene ?”
Bata tsahirta ba sai da ta ji an kira sallar magriba ta tashi ta shiga bandaki ta yi alwallah ta fito ta yi salla, bata tashi daga kan abin sallar ba sai bayan data yi sallar isha’i amma tana idarwa ta dawo kan laptop ta ci gaba da bibiyar Dakta Jalo.
Karfe tara saura kwata ta ji ana buga mata kofar daki sai ta ji ranta ya baci dan za’a katse mata hanzari, dan haka ta ki amsawa ta san yayarta ce Zainab zata dame ta akan ta fito ta ci abinci ima kuwa ba abincin dare take ci yanzu ba.
Har yanza ba’a daina bugawa ba sai ta ji muryar Dinah babbar Kawarta kuma aminiyarta ce. Ta yi mamaki da jin muryarta a daidai wannan lokaci, ta yi sauri ta mike ta bude kofa, suka rungume juna suna murna, bayan sun shiga cikin dakin suka zazzauna a gefen gado. Dinah ta kalli laptop taga garjejen hoton
Jalo ya cika allon, ‘sceen’ din.
Ta zazzare ido ta tambaya cike da mamaki “Nastin! Waye wannan?”
Nasrin ta harare ta, ta ce, “dube shi da kyau dai. Ba ki gane shi ba ne? Jalo ne fa, mutumin da nake nuna miki rubutunsaa jaridu da facebook.
Dinah ta gyada kai ta ce, “eh na tuno shi.
Me ya faru kuma?”
Nasrin ta yi dariya ta ce, “ba komai abokina ne kawai a facebook. Albishirinki!
Yau kuma na ci sa’a ya amsa wayata, kinsan baya daukar waya ran nan ba muna tare ba nayi ta kira bai dauka ba.
Dinah ta yi sororo tana kallonta cike da mamaki.
Nasrin ta daki kafadarta ta ce, “ke wai mamakin me kike yi ne wai?”
Dinah ta yi ajiyar zuciya ta ce, “mamaki kike bani dai, wannan ba halinki ba ne. Yaushe kika zama marar aji har kike bibiyar mutumin da baki sani ba haka, har yake ja miki aji.” Nasrin ta yi dariya ta zungure ta da gefen hannu ta ce, *ke dalla ki kwantar da hankalinki ba wani abu ya hada ni da shi ba, nacin da nake yi masa dan in karu da shine kin san zama da irinsu akwai karuwa musamman ni da nake bautar kasa a harkar aikin jarida ina so in san makamar aiki.”
Dinah ta harare ta, ta ce, ” ina joseph Bawa, ina Mathew Haris na ofis dinku? Ba tare ku ke ba kuma suna koya miki aiki yadda ya kamata ba? Ba sai wani a facebook wanda baya son yin mu’amula da ke ya koya miki ba, ba ki san ma in da yake ba. Ko ya fada miki?”
Nasrin ta Bata fuska da alama ta yi fushi.
Dinah la zabura ta mike gami da jan hannunta ta ce, “tashi ni ki raka ni zan tafi, tare da sweetheart dina nake ya kai ni Shoprite na siyo man shafawar nan da nace zan fara shafawa wanda muka ga tallarsa a settlite.
Nasrin ta ja dankwali ta daura suka fito falo suka iske
Anty Zainab tana kallon
talabijin. Dina ta duka ta yi mata sallama suka wuce har sun kai bakin kofar fita daga falo.
Hmmm