DA MA NI CE CHAPTER 9 BY JAMILA UMAR TANKO
almajiranci da maula a kasar Hausa wanda ya zama ruwan dare. Abokansa na facebook su nata ruwan sharhi (comments) sai ita ma ta tura nata dogon sharhin. Gogan na ta dai bai amsa musu ba, ya tafi abinsa.
Ta kai karfe dayan dare tana karance-karance akan rubuce -rubucensa sannan ta kwanta amma ba dan tana jin bacci ba sai dan kada ta kasa yin sammakon zuwa ofis gobe, da tunaninsa ta kwana tana mafarkinsa domin hoton fuskarsa ya dasu a kahon zuciyarta.
Asuba ta gari
*****
Tana tashi da asuba ta yi sallah ta yi addu’a Allah Ya bata basira irinta Dr. Jalo
tana so ta kware akan harkar jarida itama.
“DA MA NICE Jalo.” Nasrin ta fada a bayyane yayin da take linke abin sallah.
Bayan ta yi wanka, ta shirya cikin shigar riga da wando (Suit) sai dan gale data daura a kai shimaba yafawa ta yi ba, kamar kullum kamar yadda ta saba shigarta. Ko karya kumalloma yau ba zata yi ba ta dauki mukullin motarta ta rata yakar Laptop ta fito. Ta iske yayarta da angonta Salis a falo suna karya kumallo. Bayan ta gaishe su suka yi mata tayin abinci.
Ta girgiza kai ta ce,
“na makara ina da shirin da zan aiwatar (program) da sassafe.
Zainab ta kalle ta ta ce,”ai kuwa daga ganinki bacci bai ishe ki ba, ga idanuwaki sun kunbura. Wannan wane irin sammako ne haka har zaki riga mai aikin banki fita?”
Salis ya yi dariya ya ce, “wayar soyayya ta raba dare tana yi tare da Fu’ad.”
Suka kwashe da dariya su dukka yayin da Nasrin ta Kara gaba dan taga alama zasu bata mata lokaci. Kai tsaye ta wuce wajen taron da ‘yan majalissu tarayya zasu dan dauko rahotanni, acan zata hadu da abokan aikinta.
Tabbas taron nan ya caja kai dan ankai ruwa rana akan banbance-banbancen ra’ayi.
Karfe biyu na rana ta samu ta fito daga. majillassa (House of reps) ita da abokan aikinta suka nufi gidan NTA dan mika rahotanni.
KANO
Zaman
Malaika da mijinta ya faskara kowannensu ra’ayinsa ya banbanta, Malaika na kan bakarta
na son masu kudi da tsanar talaka, haka Shamaki yana ta nuna mata wannan hanyar ba mai bullewa bace gara ta dawo kan hanya.
Zaman doya da man ja ake a matsayinsa na mijinta komai ya fada mata bata ji bai isa ya sakata ba ko ya hana ta ba. Haka bata kula da yara balle shi kansa. Wani abu dole sai yayi magana, wani abu kuwa ya kawar da kai ya tashi ya yi abinsa da kansa.
•Tunda ta sami lambar Nasrin bata taba fashin kiranta ba, a kullum sai ta kira ta sau biyu ko fiye da haka a rana, sai dai taqi amsawa amma sai ta kira. Jifa-jifa dai Nasrin tana amsawa idan bata komai, amma ko Nasrin
Hmmm