DA SANIN ALLAH CHAPTER C KARSHE
MAHEER POV
Lokacin da mukaje asbitin taimaka mata nayi muka shiga inda likitan yana ganinmu ya saki fara’a da fad’in Mrs Rafeeq ke aka kawo da alama.
To be honest hearing Mrs Rafeeq, sounded like music to my ears.1
Bayan yayi checking heartbeat d’inta da komai da komai Still bugun zuciyar baya sauka inda yasa na riqe hannunta kada’n ina comforting d’inta don ta qara samun nutsuwa, inda akayi sa’a bugun zuciyar yake sauka ahankali.+
Waje yace muje. Bayan na bishi office ya tambayeni akan yadda takeyi na fad’a masa komai yace me yake sakata hakan?
“Tanayi duk lokacin data tsorata sosai ko kuma ta ha’du da baqin fuska da sauransu. “
Komawa mukayi ya fara mata tambayoyi yaushe tafara tace “shekara goma kenan tun rasuwar mahaifana”
Waye yake kula da ke inkin sami panic attack kamar yanzu”?
“My cousin Abdul”
” Sai kuma wa? “
“Babu kowa sai shi kad’ai”
“To atsahon wannan lokacin zaki iya tuna sau nawa kikayi”?
Inda ta girgiza masa kanta alamun a’a
Naji tausayin rashin gatan ta sosai.
Magunguna yayi prescribing yace inta shanye su inta cigaba na dawo da ita. Mukayi godiya muka wuce gida.
A mota nake tambayar ta dalilin dayasa Abdul ya gaza kaita asibiti?
“Abdul yanamin qoqari sosai sbd kawu Garba bazai ta’ba bari ya kaini asbiti ba shiyasa. Abdul sbd ni ya koyi baking cake duk shekara shi kad’ai yake min birthday wish kaga kuwa abin yafi qarfinsa ne”
Murna tafara daga tuna rayuwarsu da Abdul d’in.
She giggled. That was the most beautiful thing I’ve ever heard. Kallonta nake yadda murmushi ya mamaye duk ilahirin fuskarta.
Amma saita tsaya da murmushin tace”kawu Garba ya gane hakan ma inda nasa Abdul ya rantse da Allah bazai qaramin komai makamancin wannan ba, sai kawai ya daina”
Kwance nake akan gado amma na kasa daina tunaninta kwata-kwata.
✍️✍️✍️
Tashi yayi yafara sauka qasa ahankali haske ya hango daga kitchen.
Tana zaune acikin kitchen d’in a d’aya daga cikin high chairs na kitchen d’in.
Yana shiga ta saki wani shashashan murmushi tana lumshe idanunta tana kurb’a lemon dayake hannun ta cikin mug.
Confused look yake mata mug d’in hannun ta ya karb’a yakai bakinsa, ai gigicewa yayi yana fad’i “SAM me kike sha haka”?
Murmushin take har yanzu tace “lemunan daka aje a fridge ne naga sun dad’e kuma ina buqatar refreshments shiyasa na”…… Shaquwa ta hanata qarasawa2
Shiru yayi sanin cewa akwai giya a cikinsu mantawa yayi shaf be fita da suba gashi yanzun ko warinta baya son yaji kuma inya fad’a mata abinda tasha zata tsaneshi sai ya waske
“Kinga gashinan kinsha lalataccen lemo yana neman haukata ki haka kurum”
Karb’e mug d’in yayi daga hannun ta kwata-kwata yaja dantsen hannunta yace muje ki kwanta zamuyi magana da safe in Allah ya kaimu.
Fizge hannun ta tayi tafara magana ta tsakanin haqoranta tace”you need to stop telling me what to do. I’m not a child.
“Well you are acting like one Sam”
“Why are you calling me SAM now”?
“Sounds good SAM, from ASSAMHA to SAMHY and from that to SAM you like it?”
STORY CONTINUES BELOW

“Not at all”
“Ok to muje ki kwanta ko”?
” Fine! Amma saina gama shanye lemona tas tukunna”
D’auke mug d’in yayi ya ha’da dana kwalbar ya sakasu cikin sink ya dawo girinta yace”drink finished. Let’s go.
“No “
” What did you say”?
” I said NO”
“Sam ….!?
“NOOOOOO. I’m not going to bed”
Tashi tayi daga kujerar ta ta nufi sink ta d’auko kwalbar tafara qara sha.
Cikin zafin nama ya qwace yace”don’t make me force you.”
Murmushi tayi tace” I’d like to see you try”leb’enta na qasa tsakanin haqoranta like she was being turned on by someone.2
Duk lokacinda ya nufeta saita zille ta gudu in yayi kanta saita tsala ihu ta gudu tana giggling running away from his reach.
She was getting into his nerves kwalbar ya kama da qarfi ta janye ya fara fusata yace”give me the damn bottle.
Ya fizge kwalbar da qarfi babu zato ta sakar masa sai gashi aqasa tim inda hakan yabashi mamaki yasashi wawwaro ido. Kwalbar tafad’i ta fashe daga nesa dasu ka’dan.
She started laughing out loud, tana kallon fuskarsa his eyebrows furrowed har yanzu yana qasa inda dariyarta ta qaru.

Kallonta yake kamar batada hankali inda murmushi yacika duk ilahirin fuskarsa ganin dariyarta akaro na farko arayuwarsa.
Idanunta a rufe ta dafe cikinta tanata dariyar sa non-stop.
Kallonta yayi yace”that’s enough fun for one day” yafara qoqarin tashi tayi saurin hayewa ta zauna kan cikinsa.
Dubanta yayi yace”very childish get off”!
“Giggling tasake yi tace”Nope” tana popping d’in P d’in
“Sam get off”
Tace”say please first”
“Assamha please get off”yafad’a yana mamakin kansa yana dariyar halinda ta shiga lokaci guda.
Tasowa yayi tayi saurin saqala hannayenta a wuyansa sbd karta fad’i shi kuma ya kama waist d’inta da hannayensa.
Kallon sa tayi da wani irin adoration tace”you are really pretty”.
Girarsa ya d’aga be ma saninba sbd maganar tabasa dariya kuma ta masa rana yace”did you just called me pretty”?1
Dariya ta sakeyi tabashi amsa da” yes” tamasa kiss at the corner of his lips tace” really really pretty”.
Ta shafa sumarsa da qasunbar daya aje kwana biyu me laushi da santsi tace you are perfect.
Truth to be told Maheer yana enjoying drunk Samha.
Matsowa take gurin fuskarsa inda gashinta ya shiga tsakani tafara hureshi da iskar bakinta amma bata sami nasara ba inda Maheer ya gyara matashi zuwa bayan kunnen ta.
Kissing wuyansa tayi ta kwanta a qirjinsa tana goga hancinta a wuyansa hannayenta a kafad’arsa ta qara fad’in”absolutely gorgeous.
Murmushi yakewa kansa yace” let’s get you to bed okay”?
Daukarta yayi har d’akinta ya kwantar da ita akan gadonta ya rufeta yayi murmushi yace”sleep well Sam cos you are in trouble tomorrow”
Collar rigarsa ta kamo ta janyosa tayi kissing lips d’inta lightly ta sakeshi ta rufe idanunta tace”Good night Mr Rafeeq”
Barin d’akin yayi as quite as possible, d’akinsa ya shiga ya tsaya yana kallon kansa a mirror yana murmushin da besan dalilin yinsa ba a band’aki ma kallon mirror n yatsaya yanajin kiss d’inta still yayi lingering a labb’ansa. He whispered to himself”she is messing with my head”.
Da cold shower yayi wanka sbd jikinsa dake qoqarin d’aukan zafi akan contact da suka samu da ita.
Black sweat pants yasaka yayo dakinsa closet yaje yasama wa kansa shirt
Yana juyowa ya ganta a zaune akan gadonsa ta canza kayanta tsaf ta sami wata zipup hoodie d’insa ta burma ta smooth scarred tan legs d’inta a fili tayi crossing d’insu.
Tambayarta yayi”what are you doing here? Is that my hoodie”?
Murmushi take tana gya’da kanta. Qofa ya nuna mata yace Sam please go sleep in your room.
Tashi tayi kamar zata fita sai kuma tayi kwana ta nufe shi ahankali tana riqe da zip d’in rigar tana zuwa daf dashi tayi wani killer smile tafara zuge rigar tun daga sama har zuwa qasa inda black lingerie d’inta suka bayyana.
Da qirjinsa tayiwa nata qirjin burki inda ya tsaida idanunsa akan fuskarta zuciyar sa na azalzalar sa ya kalli jikinta amma yaqiyin hakan.
Yace “Samha bari in fa’da miki abinda baki saniba you are drunk” qasa-qasa tayi da muryarta tace” i know”
Wawwaro idanunsa yayi yace”to why are you doing this”?
Kafad’arta ta d’aga tace”Well that kiss made me want more”.
Tafara tafiya da yatsunta a jikinsa har zawa vline d’insa and he shivered under her touch. Be bari ya kalli jikinta ba har yanzun, fuskarsa ta kamo da hannayenta tace” i want you Maheer and i want you to take me here, right here and right now.
Yanayin ta yake kallo yaga gabad’aya jikinta a bayyane tabbunan da batason yagani yau gasu a fili hakan ya tabbatar masa da bata hayyacinta.
Tallafo fuskarsa ta qarayi without breaking eye contact ya d’auke ta ya kaita kan gadonsa his waist between her legs.
Qarar zuge zip taji inda ta tabbatar zip d’inta ya zuge mata kafin ta taso yace”sleep Samhy”
It wasn’t easy for him to fight the temptation amma dae duk da haka ya qoqarta yayi.
Matsawa yayi kusada ita ya kwanta shirtless.
Kansa kan hannun sa na hagu na daman kuma akan qirjinsa kallon ta ya qarayi yaga alamun bacci take yayi saurin rufe idonsa shima.
Ji yayi ta hawo kansa yayi saurin bud’e idanunsa he let out a sigh of annoyance yaqara rufe idanunsa sai ji yayi tace”not comfortable”
Banza yayi da ita sbd abin ya fara masa yawa kuma bayason wani abu yafaru ba da hankalinta ba yafison yanzu yasan matsayin sa tukunna.
Daidaita wa tayi saida taji dad’in kwanciyarta sa’annan ta lullub’e su da duvet tana kansa tasakasa a tsakiya.
Hannayenta a gefen kafad’unsa sai faman goga masa hancinta take a wuyansa tana kissing d’insa below his jawline.
Tashi tayi tana kallonsa sbd jin be rungumeta ba ya tsaya suna kallon kallo ya zama confused kissing kumatunsa tafara yayi saurin rungumeta karta jiqa masa ayyukan sa ta koma ta lafe in her previous position.
Ko second goma batayiba tayi baccinta inda tabarshi yana kallon ceiling ya kasa bacci koda b’arawo.
_____________________________
Haahahahahahahahahaha
Follow me
Comment
Vote
Safiyya_z✍️✍️✍️✍️ASSAMHA POV
Tabbas nasan natashi daga bacci amma na kasa bud’e idanuna. Ina iya jin numfashi kusada ni da wani irin d’umi me dad’i da taushin wani abu kuma kamar an riqeni.
Ahankali nake bud’e idanuna my vision met a tan body even in sleeping he looked perfect.
Saurin rufe bakina nayi da tafin hannaye na kafin in tasheshi i was sleeping on him. Right on him, thick eye lashes d’insa suna qyalli ta d’an hasken dake d’akin kamar in ta’ba.
Jinsa nayi ya motsa ya qara sakani jikinsa. I loved the feeling I couldn’t help myself but gaze at him.
Inason guduwa amma ya riqeni gashi da qarfi kamar me to amma meyasa nakejin qafafuna naked?
Me yasami kayana!? Did we had sex? Oohhhh God i had sex with him.
Now I’m panicking
I had to get up and get out but how? Kalle-kalle nake ko zan sami mafita, karaf nayi karo da manyan fararen idanunsa.
Kallona yake yanason yayi dariya zuciyata bugawa take kawai kamar zata fito na kasa kallon sa yatsunsa yasa yana gyaran gashina zuwa bayan kunnena inda hannun ya tsaya a wuyana d’ayan kuma a waist d’ina Making me feel closer to him.
Our lips almost inches apart yadda yake kallona yasa naji kumatuna namin d’umi.
D’umin yatsunsa naji ta cikin hoodie d’ina, a’a nawa kuma? Yaushe kuma nasami hoodie?
Magana zanyi naji kamar ana bugamin guduma akaina nafata groaning ji nayi yana dariya daga qirjinsa har jikinsa na vibrating.
Kallona yayi yace”i guess this was the first time you got drunk”
DRUNK? Innalillahi wa inna ilaihirraji’un DRUNK?
“What happened last night”?
“I think you know”
Dariya yafara yi kuma showing me his smile lines daban ta’ba sanin yanada su ba. He looked handsome. No,he was beautiful.
Katsemin tunani yayi da cewa”i would love to stay like this more but but i think i speak for both of us that is better you get off me.
Da sauri na miqe na zura da gudu zuwa d’akina na kulle qofa.
Jikina nake dubawa ta ciki nayi sa’a da kayan ciki aciki inda na Sabi istigfari baji ba gani.
Lokacin nafara tuna abubuwan dana aikata murmushi abin yasaka ni na kai hannu ina shafa labb’ana sbd tuna kiss d’in da muka yi.
“Ke samha ki kama kanki, kina magana nefa akan Maheer Rafeeq you are just like charity to him. Yana miki mutunci ne kawai sbd abinda ya sani akanki inba don haka ba da tuni kin cigaba dashan wulaqanci iri iri.”
Wayata na dauka iPhone xsmax rose gold ce inda yasa aka sa mata pink matte case sbd sanin inason kalar na duba lokaci har gari yafara wayewa.
Da kaina na ha’da mana breakfast daman koda ina gida idan nayiwa Abdul laifi nakan ha’da masa breakfast da safe to yauma hakan za’ayi.
Fried turkey bacon da pancakes da soyayyen qwai nayi sai kuma nayi toasting wasu breads ka’dan.
Bayan na gama komai na ha’da a dining d’in dake kitchen. Warin wannan lemon kitchen d’in gabad’aya yakeyi inda nayi saurin gyareshi ras ina gyaran ina tuna yadda abubuwan suka faru gabana banda bugu babu abinda yakeyi.
Ga wata irin kunya dana tuna sunayen dana kirasa dasu na gyara komai tas.
Na kaisu shara kenan mukayi kacib’us dashi ya sauko daga sama dogon wando ne ajikinsa da baqar t-shirt me gajeren hannu dawani baqin glasses ban ta’ba gani ya sakashi ba amma kuma ya masa kyau sosai.
Tarin abincin dana shirya ya kalla yace”what’s going on”?
Gurinsa na tafi ina had’e yatsuna batare da na kalleshi ba nace breakfast nayi maka na ban haquri da kuma godiya.
Murmushi ne ya cika fuskarsa yace “name kuma; for what”?
Yasan fa me nake nufi amma ganshi ya tsatstsareni da ido wai saina fa’da da kaina nace”nagode da yadda kayi handling d’ina jiya da dare kuma I’m sorry for the trouble dana saka aciki.
“Welcome and apology accepted”
Yanayin yadda yayi maganar yaban dariya yace”meyasa bazamuyi breakfast awaje ba naga yanayin garin yayi kyau sosai ko me kikace”?
Daman munada d’an table awaje kan ciyayi kusada pool anan muka ha’da kayan abincin inayi yana taimaka min inda nakasa b’oye murna ta.
Abincin dana zuba ya kalla yace”shikenan abinda zaki ci”? nace” eh”
Qarawa nayi da qwai da d’an wani chips dariya abin yabashi.
DARIYA!WAI?
Irin cin abincin yara yakeyi da gaske babu abinda ya dameshi banje tsakiya ba har ya gama tas.
MAHEER POV
Ina lura da ita batada appetite kwanakin nan saikace mouse haka takecin abinci kamar d’an shekara biyar.
To meyasa ban gane hakan ba da wuri kome nake tunani oho tunda na aureta ma me nake kula dashi nata?
Gabad’aya fushin banza da girman kai ya rufemin idanuna namanta zata iya neman taimako. Wane irin mutum ne ni?.
What kind of his……….amma ta d’auke ni amatsayin mijinta kuwa? Ko amatsayin macuci?
Abubuwan kika sani Grace bazan ta’ba yafe miki ba kuma saikin gane kuskuren ki duka.
Inacan ina tunani bansan tazo gabana tana ha’da kayan abincin ba ma kallon ta kawai nakeyi yadda take aiki nan da nan batareda tasa kowaba daga gani tasaba dashi sosai.
Bayan ta gama na tambayeta “zaki fita zagaye dani kuwa”?
Ban ta’ba jin tsoron tambayar wata mace wani abuba sai ita, kallona tayi tamin wani guntun murmushi, murmushin ta yana sani injini relaxed kullum. Gya’da kanta tayi, na zauna ina jiranta batafi minti bakwai ba sai gata ta sauko.
Wandon ta matsatstse ne jeans blue amma rigar tanada tsayi ka’dan don zata wuce gwiwarta sai dai da doguwar tsaga ajiki farace me adon blue zare ta nad’e kanta da wuyanta tsaf ta saka farin convass tayi masifar kyau bansan me yasata hakan ba lokaci guda.
Shiru muna tafiya, har muka shiga cikin mutane zamu tsallaka titi danja ta bamu dama amma saina ga ta rabe can gefe tafara jin tsoro hannu na na miqa mata sai ta tsaya tana kallon hannun confused inda na kama d’an hannun nata na jata ahankali muka tsallaka titin atare.
Inajin dad’in hannun ta cikin nawa murmushi nayi lokacin danaji ta qara damqe hannuna anata.
Comfortably muke tafiya yara nata wasa a gefen asli Park wasu tsofaffi suna wucewa mata da miji na kalleta shaquwar data fara abin yaban dariya sosai.
Har rana muna yawo bayan munyi sallah muka shiga dark chocolate muka sami abin tab’awa muka wuce.

I never had so much fun.
I love spending time with her. Inajin dad’in komaina tareda ita.
(edited)
__________________________✍️✍️✍️
Safiyya a_z✍️✍️✍️
💖💖💖💖💖
SAM-HEER
💖💖💖💖💖
✍️✍️✍️
Kullum in Maheer yaje asbiti yana mata abubuwa sai taita kallon sa tana mamaki kamar ba shiba sbd lallab’awar har tayi yawa.
Saidai ta fuskanci yanzu baya iya fara’a kamar da
Bayan ta shafe kusan wata guda a asbiti ta fito.
Saida tayi masa qara’in birthday d’insa da bata samu tayi ba, ganin irin dawainiyar da yayi tayi da ita a asbitin.

Tayi cakes kala-kala daga ita sai shi sai wad’anda ta suka gayyata ka’dan da su Abdul.
Kuma yayi murna sosai, saidai idan ka ganshi sai kace shine yayi rashin lafiyar ba ita ba.
Tun farkon zuwanta asbitin sun d’auki hotunanta na komai da komai sbd shaida a kotu.
Kowa ya hallara a kotu Assamha tana tsakanin Maheer da Haj Gwaggo datasan labarinta daga baya.
Hannunta cikin na Haj Gwaggo Maheer a gefenta Abdul a kusada shi.
Daman lauyan abokin Maheer ne ga kuma ku’di ya shaqa kuma Maheer ya fad’a masa komai kuma shine best lauya a garin gabad’aya.
Miqewa lauyan yayi yana b’alle rigarsa ta lauyoyi yace:
“Kamar yadda kuka sani ne mutanen banza sukan aikata sab’o kuma manya sukan d’auki advantage d’in yara.
Wato babu wani abu na zunubi da b’atanci da kuma rashin kyautatawa da Garba da matarsa mero wadda qanwa ce gurin mahaifin ita me qara da kuma y’ar su wato Aina’u basu aikatawa wannan baiwar Allah ba.
Judge yayi magana”to d’ansu Abdul fa”?
Murmushi lauyan yayi yace “shi yana cikin mutane nagari babu shi cikin dukkan abinda ake aikata mata”.
Kiran Abdul akayi yaje witness box ya tsaya. Alqalin da kansa ya tambaya”
Meyasa kai Abdul Garba baka ta’ba sanarda kowa halinda Assamha take ciki ba duk kuwa da kafi kowa sani kuma baka goyon bayan hakan?
Ai ko masu yaqi da cin zarafin d’an adam yaci ace ka nema ka musu bayani shin zaka iya fad’awa kotu me ya hanaka aikata hakan?
“Sbd tsorata ni da akeyi a kullum kuma musamman ma akan rayuwar Samha kuma nasan duk abinda sukace zasu mata zasu iya yi shiyasa nayi shiru nake mata iyaka abinda bazai cutar da ita ba wanda naga zan iya.”
Suwaye kenan suke tsorata ka”?
“Iyayena da suka haifeni da kansu”
Lauya yace haka abubuwan suka cigaba da tafiya tsanani kan tsanani ya mai girma mai shari’ah.
“Mal Abdul kaje ka zauna mun gode sosai” sauka yayi ya ha’da ido da Kawu Garba yana watso masa harara.
“Haka suka cigaba da gallaza mata ya mai girma mai shari’ah.
STORY CONTINUES BELOW

A nan aka gabatarda hotunan duk wani sashe dayake d’auke da tabo da report d’in likitoci akan sa da recordings da Abdul yayi na murya da wasu na videos daya d’add’auka du aka gabatar.
Lokacin da’aka fara kunnawa mutane dayawa cikin kotun saida sukayi kuka musamman ma Haj Gwaggo da Samha ce take bata haquri.
Da farko Kawu Garba be zaci abin zai kasance hakaba sbd besan sun tanadi wata hujjah akansaba amma yanzun har ya fara gumi inda Anti Mero da Aina’u jiki ya fara rawa musamman ma Anti Mero.
Lauyan su Kawu Garba alqali ya bawa dama da cewar”ko kanada ja akan wad’annan hujjoji”?
“A’a ya mai girma mai shari’ah”
Sbd Maheer ya ninka masa ku’di sau hud’u ya sayeshi da sharad’in kar yayi depending d’insu in an shiga.
Lauyan Maheer ya cigaba “kuma sun ha’da kai wajen kashe wa Assamha iyayenta shekaru goma da suka wuce tanar 18-02-2010 a guest house d’insu dake princess island da misalin qarfe 2:00am.
A gigice Samha ta kalli Maheer ya gya’da mata kansa alamun haka ne ta sunkuyar da kanta ta saki kuka hawaye wani na bin wani.
Wani recording d’in aka sake kunnawa muryar Kawu Garba ce yana:
“ku kashe matsiyaci kawai ku harbeshi har lahira shine buqatata”
Cika kotun tafara yi da maganaganu inda Kawu Garba ya rasa me zaiyi shi kuwa lauyansa babu ta cewa anan bangaren don be ma san da zancen kisan kaiba kuma.
Guduma alqalin ya buga aka dakata yace kotu zata dawo bayan mintina talatin.
Bayan an fita kowa kuka yake taya Samha harda Mr Adams inda Haj Gwaggo kamar zata cinye Samha sbd tausayi Maheer kuwa da ido yake bata haquri.
Kukan take sosai sbd yaune take kukan kashe iyayenta da basu jiba basu ganiba sbd abin kirkinsu daya sa Kawu Garba yake ganin abinda suke masa yayi ka’dan har saiya d’auki rayuwarsu kuma gashi bata ta’ba sani ba sai yau d’in.
Bayan an dawo mai shari’ah ya yankewa Kawu Garba da Anti Mero hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso sbd had’in baki a kisan kai shekaru goma da suka wuce da kuma yaudara da cin zarafi da cin amanar da sukayi sa’annan komai na Assamha an qwace mata daga yanzu komai nata ya koma hannunta sannan dukiyar kawu garba za’a biya Assamha diyyar cin zarafi da azabar da suka gana mata. Kuma babu beli
A bangare d’aya kuma Aina’u za’a d’aure ta tsahon shekaru shidda babu zab’in tara tareda aiki me tsanani.
Ihu Aina’u tafara kurmawa inda aka sa y’an sanda sukayi waje da ita.
A bakin qofa za’a wuce da su kawu Garba Maheer ya tsaya idonsu duk ya Raina fata jikin Anti Mero na mazari kawu Garba sai zazzaro idanu yake babu zato Maheer ya danqara masa naushi inda yafad’i atake sumamme yace:
“Wannnan sbd dad’ewa da kasani nayi ina baqinciki” 😄4
Kallonta yayi she is in shock na abinda ya aikata babu zato ya bud’e baki yace”I had to. I needed to”inda ya rad’a mata”happy freedom SAMHY”1
Abin tausayin Abdul yanda yaketa kuka dukda yana jin haushin abinda suka dad’e suna aikatawa.
Wani iri Samha takeji tana murna amma ta kasa murnar ko me yasa.?
*************
Gidan mahaifiyar ta ya dawo hannun ta. Yanzu abu daya ya rage musu a rayuwa shine haihuwa kuma babu dama shiyasa ko zancen ta fara sai Maheer ya bata rai ko yabar gurin.
Amma yana tsananin son haihuwar har besan yadda zaiyi ba.4
A bangare d’aya kuma komai yanzu kusan tare sukeyi abin har tsoro yake bata har girki yake tayata dukda babu abinda ya iya amma tanajin dad’in hakan takan tsaya kurum tana kallonsa ta fuskanci yana yawan gudowa daga office sbd rashinta acan d’in.
1
Da gudu ta taho har tayi karo da Maheer a bakin qofa yace “karkice da gudu kika taho”?
“Eh ya kake gani akan muyi adopting yaro kawai”?
“Kibari in na sami lokaci zamuyi wannnan maganar”
Ranar ko abinci be ciba ya fita ta fuskanci bayason maganar ne kawai sbd yafi bata muhimmanci akan aikinsa na office.
Ranar har biyun dare sa’annan ya dawo kuma tanata kiransa da rana amma amsa waya ya gagara.
Yanayin yadda ya shigo yasa ta fasa yi masa magana idanunsa duk sun kumbura sosai.
Ta tambayeshi “hungry”?
Ya gya’da kai kamar qaramin yaro
Bayan ya gama cin abincin ya miqe inda ya lura har lokacin tana zaune tana murza yatsunta alamun damuwa.
Dawowa yayi ya zauna yace “kinason d’aukowa dai kenan”?
Tace “eh wlh” tafad’a cikin murna ya jingina kansa a qirjinta yayi magana a hankali2
“Shikenan zan tambayi Haj Gwaggo idan ta yarda to zamu d’auko”
Murna take sosai don arashin uwa akanyi uwar d’aki.
Lokacin da Maheer ya fad’awa Haj Gwaggo cewa tayi su bata lokaci.
Inda kwanci tashi har wajen wata biyar kenan.
Da farko Samha ta qagu sosai da d’auko yaro amma yanzu harta saki jikinta sai qiba take tana wani irin cika tana wani shu’umin kyau,har Maheer baya iya kauda idonsa sai dai Haj Gwaggo in taga abin zaiyi yawa ta basu guri.
Cikin sa’a tabbunan jikinta sun fara bajewa ka’dan ka’dan sai wani qyalli fatarta kawai take fitarwa a kullum.
Abokan aikinta ne yau suka kawo mata ziyara anata raha ana cin abinci Assamha tace”to ya kamata aje ayi sallah kar lokacinta ya qure fa”
Hauwa tace” Haj Samha sarkin sallah Allah yabada ladan tuni amma ni hutun sallah nake daga Allah”
Suka fara dariya” ko kema hutun sallar kike ne kike faman kora mutane ke kina zaune”?
Assamha tace aini tunda nafara shan magunguna na nadena period gabad’aya”
“Ke Samha kije asbiti ba’ason fa mace bata al’ada wlh anfiso duk wata kiyi al’ada rashinta yana nuni da rashin lafiyar mahaifa.
“Ko kuma ciki ba” inji zeenat.
Dasss Samha taji gabanta yayi ya kuma cigaba da fad’uwa sanin ance bazata haihu ba wato yasa bata ta’ba kawo hakan ba amma batason tabawa kanta false hope amma dae dukda haka yau zataje asbiti.
Bayan sun tafi tayi sallar magrib ta sulale batareda ta fad’awa kowaba sai asbiti.
Koda likitan ya tamabayi Maheer saitace”banason yaji babu dad’i gara koma menene na fad’a masa daga baya”
Bayan ya gama mata tests d’in da yayi wajen kala uku cikin murna ya shigo yace muje za’ayi scanning kinajin sauqi sosai ga alamu sun nuna.
“Alhamdulillah” tace
Bayan ya mata scanning yace Mrs Rafeeq ina me farincikin sanar dake cewa kinada ciki wata uku.2
“You are three months pregnant Mrs Rafeeq”2
Murna tafara sbd Maheer ba sbd kanta ba sbd har yanzu batasan halin da mahaifarta ke ciki ba tukunna.
____________________________________
To ko zata iya haihuwar?
( Edited)
Whew please comment and vote
Safiyya a_z✍️✍️✍️✍️✍️✍️💖💖💖💖💖💖💖💖
💖💖💖💖💖💖💖💖
💘💘💘💘💘💘💘💘
✍️✍️✍️
Lokacin data sanar dashi labarin tanada ciki bata ta’ba ganin sa cikin farinciki arayuwarta da shiba kamar ranar.
Be qara murna ba saida likita ya tabbatar masa da cewa mahaifarta tana healing a hankali zata iya haihuwa amma CS za’ayi mata.
Suna dawowa gida ya sureta yana jujjuya wa da ita tun tana jin tsoro tafara dariya.

Babu zato Haj Gwaggo ta fito yayi saurin direta yana shafa kai inda Samha ta zura da gudu tabarsa da haj Gwaggo shi kuma yaje ya rungumeta.
Mamaki abin yaba Haj Gwaggo tace “yau kuma tab’ara ce ta tashi?”
Rasa me zaice mata yayi yace” ina cikin farinciki Kaka,irin wanda ban ta’ba yiba sbd Allah yayimin abinda ban ta’ba zato ba kuma abinda babu wani ku’di ko mahalukin daya isa yayi min shi.”
“Abinda kuma na cire ran zan samu har qarshen rayuwata”
Wawwaro idanunta tafara yi yayi sauri ya wuce yana murna sama ya hau da gudu wajen Samha, suna sama suna jiyo darar haj Gwaggo da masu aiki anata murna.
Inda suke tasu a d’aki ji yake kamar ya maida Samha cikinsa kar wani abu ya tab’asu ita da babyn sa.2
Saudiyya suka tafi harda Haj Gwaggo sbd godiya ga Allah da nuna farincikin su da neman kariya da rayuwar abinda yake cikin da roqa mata tabbatacciyar lafiyar dazata haife cikin.2
1
Satinsu uku gobe suke sakaran zasu koma gida sbd haj Gwaggo ta qagu su koma ko don ita ta saba zuwa ne?.
Ita kuwa Samha ji take kamar kar su tafi to amma babu yadda zasuyi shima Maheer yanada uyyukan da zaije ya qarasa.
Haj Gwaggo d’akin ta yana gefen nasu ta kwanta tuni sbd in sun fita harami suna dad’ewa a tsufanta takan gaji sosai yauma hakace tafaru gashi gobe da wuri zasu tafi.
*********************
Assamha tana fitowa daga toilet tayi karo dashi a bakin qofa a tsaye yanayin yadda yake kallonta yasa tafara jin sanyi atake gotashi zatayi ya tare hanyar ta koma ta d’aya b’arin nan ma ya tare.
STORY CONTINUES BELOW

Ta langab’ar da kanta yace”wato samhy yanzu sbd kinga ina lallab’aki shiyasa kikemin haka ko? tunda mukazo babu wani bayani kin manta da mijinnaki ko.”2
” Bakya laulayi kamar yadda naji ana fad’a to meye matsalar”
” Ina yi mana, ina kasala sosai fa kuma……..”
“Uhmm kasala sai kuma me Mrs Rafeeq”?
Kansa ya kwantar akan kafad’arta suna tsaye kamar basuda abinyi can yace”to ga mijinki kisan yadda zakiyi dashi”2
” Ba wanka zakayi ba shiga ka fito tukunna”
“Kin tabbata”?
“Eh na tabbata”
Da sauri ya shige toilet inda tayi saurin kwanciya ta lafe kamar tayi bacci ta rasa me yasa komai yanzun baya mata dad’i kamar da.
Lokacin daya shirya cikin wandonsa na bacci babu ko riga ya lallab’a kan gadon yace “samhy” !
Shiru tayi wai ita ala dole tayi bacci da kamar ya haqura amma sai ya kasa.
Kallonta yake yanajin kamar ana kunna shi murmushi yayi yace “bari mugani”shafata yafara yi tun daga yatsun qafarta yataho har zuwa qirjinta tayi saurin riqe hannun sa dariya abin yabashi.
“Au ashe ba bacci kike ba” mirginawa yayi ya koma samanta yafara kissing d’inta tun tana goggocewa har tafara biye masa inda daman shi haka yakeso.
Badon Haj Gwaggo ba da Maheer ba kullum zai dinga zuwa wajen aikiba.
Yanzun kullum tunda suka dawo gida bashida sana’a sai jingina kansa jikin cikinta wai zaiji hirar baby.
Yauma magana take masa ya durqusa akan gadon ya jingina kansa jikin cikin yana mata shhhhshh don karma tayi disturbing d’insu, she frown her brows in annoyance tace”My Heer please i want to talk to you since amma ka kasa saurara ta”
“Ina zuwa shhhhshh”
Ja da baya tayi kansa ya fad’i akan katifar da suke atake ya d’ago ya dubeta inda ta d’aga kafad’arta alamun oho kamota yayi tana dariya.
Yace “dole there will be a punishment tunda kika raba wannan conversation d’in”
Tace” ko ka sakeni ko kuma inyi ihu yanzu Haj Gwaggo tazo kuma kasan saita ha’da maka da duka”
“Let’s see if you can try”
A hankali ya janyota jikinsa yafara sarrafa ta har ta mance da abinda take son fad’i.
BAYAN WATA TARA
Wannan ranar daman itace za’a yiwa Samha CS.
Tsakanin Maheer da Haj Gwaggo babu me bawa wani baki kowa zirga-zirga yake tunda aka shiga da ita musamman sanin hatsarin dayake tattare da aikin.
Cikin awa biyu suka fito ana musu bushara an ciro y’an maza guda biyu, sujjada Maheer yayi ta godiya ya miqe ya rungume likitan ya koma ya rungume haj Gwaggo qwalla na zuba sbd murna itama kukan take don haka babu wanda yacewa kowa komai sai dai murna kawai.
“Dr dftn dae Samha tana lafiya ko”?
“Eh Mr Rafeeq babu kowacce matsala alhamdulillah sai ku jirata ta samu sauqi sosai don har yanzun she is under anesthesia”
Lokacin da Maheer yaga yay’an kasa me zaiyi yayi ya dad’e da matsuwa su fito yagansu yau gasu wai dukansu yay’an sane busashshen leb’ensa yake lashewa yana shafa sumar sa cikin rashin sanin ta yaya zai d’auke su don baya tuna lokacin daya ta’ba d’aukan jariri arayuwarsa.
Haj Gwaggo ce ta d’auki wanda aka fara cirowa ta miqa masa inda ya tattara y’ar nutsuwarsa ya karb’a jijiyoyin kansa har tashi suke yana wata dariya me had’e da murna da son yaran.
STORY CONTINUES BELOW

Komai iri d’aya aka sai musu sbd daman suna sakaran twins tun lokacin da’aka yi mata scanning.
5
Ya bayarda Babban ya karb’i qaramin bayan ya ajesu ya lallab’a ya tafi gurin matarsa inda yaje ya samu idonta biyu amma bata motsi sbd allurar bata gama sakinta ba kissing d’in fuskar yayi ko’ina yana yabawa qoqarinta da irin farincikin data samarwa rayuwarsu gabad’aya.
Daga nan rayuwa taqara dad’i amma fa Maheer baya yadda su kwana a ko’ina sai kusada shi duk ranar da Haj Gwaggo tace a d’akinta zasu kwana sai kaga Maheer yayi wani daban kuma sai sunyi bacci Haj Gwaggo ke korosa daga d’akin.
Ita kuwa Samha yanzu ta koma kamar itace mamansu gabad’aya sbd yanzu data fad’i magana to angama girmamata yake sosai sbd yadda take d’awainiya da yay’an sa.
Ba kuma ya qyashin kashe musu ku’din sa duk yawansu yana ganin in banda Allah da ku’din sa sunyi ka’dan suyi masa hakan.
3
BAYAN SHEKARU BIYAR
ABDUL-AHAD &ABDUS-SAMAD
Awaje suke suna wasa akan ciyayin dake harabar gidan tashinsu kenan daga bacci suka fito suna wasa.
5
Assamha tafito tana kiransu don suyi breakfast suka fara mata magana.
“Mumma ina daddy yake”?
“Daddy yayi tafiya da daddare kuna bacci amma yau zai dawo insha Allah”
STORY CONTINUES BELOW

“Mumma inya dawo zamuje shopping”?
” Kuma zamuje park”?
“Eh zamuj……..”
Maganar ce ta maqale sbd wani gigitaccen ciwo dataji a mararta ta saki mug d’in hannunta ya fad’i qasa ta durqusa nan da nan ta dena ganewa Abdul-ahad ne ya falfala cikin gidan yana qwallawa granny kira Abdus-samad kuma yana kusada mumma yana kuka yana”mumma ki tashi mana” .
Dawowarsa kenan daga tafiya yayi asbitin kai tsaye a gigice yana zuwa Dr Rasheed yayi masa albishir cewa Samha tanada ciki shigar wata hud’u.
“Har wata hud’u Dr”?
Eh to amma tana bawa kanta wahala da yawa sbd haka zaka bamu aronta saita huta tukunna zamu mayar maka da ita da zarar ta huta sosai kuma ta cigaba da hutawa in ta koma gida”
Ai gabad’aya gajiyar Maheer guduwa tayi sbd dad’in labarin dayaji daman yanaso kawai bayason zaqewa ne kuma yazo Allah be basa ba, godiya yakema Allah ganin irin sonda Allah ke masa.
Bayan an sallameta ta koma gida shikenan ta dena komai Maheer da Gwaggo suke mata komai da masu aiki ko yay’an ma ba’a bari ta musu komai su kansu yaran sun saba da sunga zata motsa za’a tafi da gudu a d’auko mata abinda takeso.
Abin tun yana bata dariya har tazo rashin motsin yafara damunta ba shiri tayiwa Dr Rasheed magana yasa aka sassauta mata.
Idan tana tuna rayuwa sai taga kamar ba itace Assamhan da ba wadda rayuwa ta juyawa baya ba amman yanzu duk inda mutum me gata yake takai hakan koda FATIMA matar Abdul ta haihu daqyar aka barta taje sbd tsaron kar wani abu ya faru kuma har yanzun Maheer ya kasa sakin jikinsa da Abdul kamar yadda ta yakeyi da kowa.
D’ansa na farko sunan baban Samha aka saka masa wato FU’AD wannan kuma aka saka mata Assamha.
Shiyasa lokacin datace asakawa yay’an ta ABDUL Maheer yaga kamar za’a rainashi ne inda yafara jin kishi sai kuma dayaga ita bata damuba sbd falalar sunayen kawai takeso sbd annabi yace sune mafiya alkhairi a cikin sunaye sa’annan ya haqura ya saka da kansa.
Lokacin da tafara naquda babu zato sbd bai kai lokacin CS d’inta ba twins ne suka kinkimo jakarta kasancewar Gwaggo batanan shi kuma Maheer ya ciccib’a ta ya sakata a baya Abdul-ahad yana baya Abdus-samad yana gaba har asbiti.
An gama shiryata tsaf za’a shiga theater faya ta fashe d’a yataho inda ta kama Maheer ta riqe atake jikinsa yafara rawa.
Ganin irin yanayin datake ciki ya fidda rai ya zata shikenan mutuwa samhyn sa zatayi yafita daga hayyacinsa gumi kawai yake had’awa sbd shi hadda tashin hankali a tattare dashi.
Lokacin data fara nishi ya cewa Dr”ka taimaka mata kar wani abu ya sameta fa”
“Babu komai lafiya qalau zata haihu insha Allah ai babu matsala”
” Ahaka kake cewa babu matsala? duk wannan wahalar datake sha?”
Addu’o’i yake ta faman yi mata yana goge mata gumi inda tayi nishi da qarfi sai kukan baby.
Mace ta haifa kamarta daya da ita murna Maheer yake yana riqe da hannunta har aka gama mata komai aka gyara baby aka bashi ita.
Sai a lokacin Haj Gwaggo tazo ta karb’e ta Maheer yace “wannan a kori Gwaggo sunanta”
“Eh ai daman kishiyata ce ga mazana nan ta janyo twins jikinta”
Sunata murna suna” wannan babyn mu ce ko granny”?
“Eh babynku ce”
“To yaya sunanta”?
“Kai sunanta baby kawai ko daddy”?
“Haj Gwaggo tace sunanta Zulaiha”
Assamha ce ta kalli Maheer ya gya’da mata kai kuka ta saka sbd murna Gwaggo tace”Allah yajiqan me sunan tayi qoqari data haifa min kyakykyawar y’a kamarki Samha kin cika mana family d’inmu da farinciki me d’orewa kin fitar damu daga kad’ai ci Allah yayiki albarka.
STORY CONTINUES BELOW

Amin sukace.
Gagarumin taron suna akayi su CEO of Zangina incorporations Alh Abdul da matarsa Fatima sune kan gaba.
Tarin ma’aikata da qawaye da abokan arziqi abin mamaki sai a ranar samha taga iyayen Maheer ashe sun gaya masa zasuzo amma be fad’a mataba.
Sunata saka mata albarka inda mamansa tace zata kwana biyu.
Ana tsaka da taro saiga Aina’u ta rame ta kod’e ta lalace babu komai sai qashi har fuskarta.
Da farko b’uya tayi saida Abdul yafad’a wa Samha tazo ta jata durqusawa tayi tafara kuka tace “kiyi haquri Samha ki yafemin abinda nayi miki kinji “?
Rungume ta Samha tayi tace “ke kad’ai ce y’ar uwata danake da ita a yanzu Allah ya yafe mana gabad’aya”
Yay’an ta kira ta nuna musu Aina’u tace “ga aunty Aina” inda suka hau rungumeta suna “Aunty Aina kina lafiya”?
Kuka tasaki tana rungumesu itama tanajin kunyarsu kamar sunsanta ada.
Magana tayiwa Abdul Aina ta zauna dashi sbd anan Maheer yaqi yarda zuwa inta sami miji zata bata gida babba guda d’aya a gidajenta.
Cikin mamaki take kallon komai na Samha abin gwanin sha”awa.
****************
D’akin Maheer ta tafi sun barbaje shida twins sunata bacci wayarta ta d’auko ta musu photo ta juya in disappointment zata tafi ya janyota ta fad’o jikinsa.
A tsorace tace “daman idonka biyu”?
“Eh ina nan ina jiranki daman nasan zakizo ai ina baby”?
“Tana gurin Gwaggo”
Janyota yaqara yi yana matseta a jikinsa yana sansanata kamar wani abinci yana shafa lips d’inta.

Gashinta ya janye yana kissing bayan kunnen ta yana teasing d’inta tana ajiyar zuciya ahankali.
Yana shafa lallausan fatan jikinta datake qyalli kamar ba itace ta da ba.
Daman gashi ko’ina Masha Allah komai yaji
Ganin al’amari ya d’auki sabon salo yasa tajashi suka koma d’akinta kar suyi b’ara daman yaran yanzu da wayo, anan tafara nuna masa kalar clean d’in datayi.
“A’a Mrs Rafeeq irin wannan qauna haka”?
“My Heer, bazaka gane irin matsayinka a rayuwata ba kaine silar du wani kyakykyawan abu dake samuna a yanzu kaine silar duk wata daddad’ar rayuwa dana ke ciki ka sani farinciki da har ta kai ina tafiya ina dariya ni kad’ai.”
” Shiyasa nakejin babu abinda bazan iya yi maka ba kuma inda zaka tambayeni ko meye a shirye nake inbaka indai inada iko” kissing goshinta yayi domin maganar ta masa dad’i sosai.

“Ki rayu dani Samhy shine burina kad’ai daga gareki karki ta’ba barina ni kuma zan cigaba da mana addu’a Allah yabamu tsahon rai me amfani ya raya mana zuri’ah kinjiko”?
“Wato My-Heer ina mamakin rayuwata yadda ta koma wahala shekarun rasuwar iyayena amma nafi mamakin yadda ta koma dad’i lokutan zama na dakai”

“Ba’a mamaki da ikon Allah kinji,ikonsa ya wuce bawa yayi mamaki kuma komai yake faruwa (DA SANIN ALLAH) canji yana nan a kusa ko a nesa domin baya bacci ba kuma ya mantuwa”.
Haka suka cigaba da fad’awa junansu kyawawan kalamai masu tausasa rai kamar kullum.
Shi yana ganin tana haquri dashi ita tana ganin yana kyautata mata suna kuma mutunta junan su.
Rayuwa me dad’i su da yay’an su da Haj Gwaggo da iyayen Maheer
💕💕💕💕💕
Sam-Heer
💕💕💕💕💕💕💕💕
💕
💕
💕
💕
💕

ALHAMDULILLAH
naso ace na qara wani sashe na soyayya sosai to amma ban sami dama ba dftn yayi dad’i kuma ya fadakar Allah ya had’amu a ladan.4
Kuskurenmu Allah ya yafe mana nagode masu karatu sosai da goyon bayanku da son littattafai na.