DAN ADAM CHAPTER 1

DAN ADAM CHAPTER 1

8 Jiki na rawa take kwankwasa k’ofar d’akin da k’arfi tana fad’in. “Habiba! Ke Habiba!” “Na’am.” Ta furta cikin magagin bacci kafin ta mik’e ta bud’e d’akin. Ganin aminiyarta Saude ne ya sanyata wartsakewa babu shiri. Ta waro ido. “Lafiya dai Saude?” Saude ta rage murya. “Ina fa lafiya? Ga waccan shegiyar tana nak’uda. Ai idan ta haihu na kad’e.” Habiba ta dafa kafadarta. “Karki damu, ai idan har ni ce unguwar zoma ba zata haife d’anta da rai ba. Itama muje sai ta bar duniya.” Wani sanyi ya mamaye zuciyarta. Habiba ta dauko kayan amfani ta yi gaba Saude na biye da ita. Lokacin karfe shida na safe. Acan suka iske Malam Balarabe yanata faman zirga-zirga a tsakar gidan. Shigowarsu ne ya sanyashi nufarsu da saurinsa. “Yauwa, Habiba don Allah taimaka mata.” “Ka kwantar da hankalinka Malam Balarabe, in sha Allahu lafiya kalau zata sauka. Ka sama mana itatuwa dai na dora ruwan zafi. Daga haka ta shiga ciki, Saude na gefe tana matsar kwallar munafunci ita a lallai tausayin abokiyar zamanta takeyi. Da ire-iren kissar da take cin galabar Malam Balarabe kenan. Da sauri shi kuma Malam ya fice. Saude dake tsaye sai jin kukan jariri tayi. Gabanta ya bada ras ras! A gigice ta fad’a d’akin. Bakinta na rawa ta tambaya. “Ta..ta..” Ina maganar gaba daya ta mak’ale a saman le66anta. Habiba ta dubeta tayi mata alama da tayi shiru. Dole ta rufe bakinta ba don ta so ba. Habiba ta kammala yanke cibi ta mik’awa Saude d’iyar. Saude cikin kukan bakin ciki marar sauti ta kar6eta tana ji kamar ta shak’eta ta mutu. Ga mamakin Saude, Habiba filo ta dauko ta danne fuskarta da shi, tun Hasiya na shure-shure har tayi lakwas. Saida ta tabbatar da cewar ta cika sannan ta yi jifa da filon ta mik’e tana sharce gumi. Saude jikinta babu inda baya rawa. “Ta mutu.” Ta fad’a a gigice. Habiba ta gyada mata kai sannan ta dubeta. “Eh na cika burinki. Yanzu Malam na dawowa mu nuna mutuwa tayi bayan ta haife d’iyarta. Ko kusa kada ki nuna wata alama ta rashin gaskiya Habiba. Ita kuma wannan k’aramar alhaki ce, ni nasan yanda zamuyi da ita nan gaba kadan.” Saude ta amince da batun aminiyarta. “Shikenan.” Ai kuwa sunajin sallamar Malam suka hau salati da koke-koke. Malam baisan sadda ya yarr da itatuwan da ya riko ba. Jiki na rawa a gigice ya fada dakin yana tambayar ko lafiya. Ya dubi Saude hannunta rike da jaririya tana ta canyara ihun kuka kafin ya kai dubansa ga Habiba. Bai yi wata-wata ba ya yi kan Hasiya yana kiranta a rud’e. “Hasiya! Hasiya!!” Ina! Ya fahimci abinda ake nufi, Hasiya ta rasu. Ya hau salati yana zubda ruwan hawaye. Baice uffan garesu ba ya fita zuwa tsakar gida ya zauna. * * * Haka yana ji yana gani aka wanke Hasiya aka kaita gidanta na gaskiya batare da ‘yan uwanta sun sani ba saboda nisan dake tsakanin garuruwansu. Malam Balarabe ya shiga tashin hankali matsananci, ya rame yayi bak’i kamar ba farin mutum ba. Ga duk wanda ya ganshi dole ya tausaya mishi musamman abokansa wadanda suka riga sukasan irin kaunar da yake yiwa matarsa Hasiya don kuwa baya 6oyemusu irin yanda take kyautata mishi a rayuwa ta hanyar yin biyayya ga dukkanin umarninsa. Sai ranar bakwai sannan babban yayan Hasiya da kuma mahaifiyarta da sauran yayyunta uku mata suka iso. Sun koka kwarai da rashin yar uwarsu. Saidai babu yanda suka iya, su mutane ne wadanda sukasan ya kamata, sam basu zargi komai ba. Toh me zasu zarga? Bayan sun san irin kaunar da Saude ke nunawa Hasiya a gabansu tamkar ba kishiyarta ba. Wannan ne yasa koda Saude tace zata rik’e yarinya, babu wanda baiyi na’am ba. Haka suka tattara suka koma garinsu batare da shakkar komai ba. * * * Wahala, tsangwama da kyara, babu irin wacce d’iyar Hasiya, wacce ta ci sunan mahaifiyarta Hasiya suke kiranta da Ummi, bata gani ba wajen Saude. Saidai a gaban idon Malam Balarabe, babu abinda Saude bata yiwa Ummi na nuna kulawa da kauna. Yarinya ce mai hakuri, haka take hakura da komai ta shanyeshi, anan ma Mahaifiyarta ta dauko. Saida ta kai shekaru goma sha uku a duniya sannan Saude ta samu ciki. Zo kaga murna wajen Saude da mijinta. Sai ya zamana bayan Saude ta haifi diyarta Mariya. Ta chanja kwarai a gidan. Ta hanyar asiri da tsafi, ta siye zuciyar Malam Balarabe ya zamana ko kallon Ummi baya kaunar yi. Komai ya samo, daga Saude sai Mariya. A wannan lokacin ne, Habiba ta zo da shawarar tura Ummi aikatau. Ba musu ba jayayya, Malam Balarabe ya amince da a turata ko bangon duniya ne. Duk acewarsa, bashi da matsala ko wata damuwa…! 1 STORY CONTINUES BELOW 8 Babi Na Biyu “Wai kina ina ne? Baki kammala shirya tsummokaran naki ba?” Ummi dake d’aki tana kuka, ta tsinci muryar Baba Saude wacce ta sanyata rud’ewa babu shiri. Cikin rawar murya ta amsa a tsorace. “Na gama Baba, ganinan.” Daga haka ta mik’e da saurinta ta dauki ledarta ta fito har lokacin kuka takeyi sosai. Baba Saude na zaune tare da Habiba sai wata mata wacce ita ke dillancin mata zuwa gidajen aikatau, a gefe kuwa, Mariya ce ke faman cin masara hankalinta kwance, ta yi filo da cinyar uwarta. Wata harara Baba Saude ta watsawa Ummi. “Shegen bakin hali, kukan me kikeyi na kinibibi toh? Gwara ki share hawayenki ma, don babu abinda zai hana yau ki bar gidan nan.” Ummi ta durkushe a gefe tana share hawaye yayinda wasu ke k’ara kwaranyowa har da majina tana gogewa da hijabinta. Baba Saude ta juya ga dillaliya. “Ina jinki Yaha, yanzu dai duk wata zaki dunga aiko da albashin nata?” Wacce aka kira da Yaha ya gyara zaman mayafinta lokacin da ta mike tsaye. “Karki damu, duk wani abin arziki da ta samu ma, naki ne Saude. Komai zan tattaro na kawomaki. Kedai ki kwantar da hankalinki kamar kin kashe d’an maigari.” Sukayi dariya sannan Yahanasu ta dubi Ummi tana yamutse fuska. “Wannan dogon gashin idan bakiyi wasa ba sai na yankeshi kafin mu k’arasa, yarinya sai shegen munafunci. Zaki maidashi cikin hijabin ko kuwa?” Jiki na rawa Ummi ta ja jelar kitson kalbar da ta jagwalgwala a kanta ta maidashi cikin hijabi. Don kuwa bata isa ta je gidan kitso ba har ya saka ran samun mai kyau. Ta mike ta bi bayan Yaha wacce tuni tayi sallama da su ta bata umarnin ta taso. Suna ficewa Habiba da Saude suka tafa suna shewar jin dadi. “Ina sonki wallahi aminiya, bani da tamkar ki.” Cewar Saude wacce ke jin ranta yayi wani mugun sanyi. Habiba ta gwaguyi masarar hannunta tana wani rausaya kai. “Ni ce fa, sai ma idan kudi sun soma shigomaki a hannu zakisan cewa ba k’aramin gata nayi miki ba. Ai ba’a saurin illata d’iya mace haka, ita tamkar jari ce, ko zata bi duniya in dai zata nemo ta kawomaki to kada ki damu kanki, ke dai ki more rayuwarki ta jikinta. Amma fa ‘yar kishiya nake nufi.” Sukayi shewa da dariyar farin ciki. Koda Malam Balarabe ya iso suka sanar mishi cewar Ummi ta tafi, ko a jikinsa, karshe ma watsar da zancen yayi ya bi Mariya da tsarabar ‘yar tsanar da ya siyomata. * * * Tun Ummi na kuka a motar kasuwa, har ta gaji tayi shiru tana kallon hanya kafin bacci kuma mai nauyi yayi awon gaba da ita. Cikin baccin kuma ta ji Yaha na tashinta. “Ke! Ke!” Firgigit ta farka tana dubanta. “Na’am.” Ta amsa a tsorace don kuwa kusan zuwa yanzu Ummi ta saba da hakan, da wuya tayi bacci a tasheta batare da ta firgita ba. Don sau da yawa ruwan sanyi ake kwara mata ko kuma a sanya k’afa a haureta, wani sa’in kuwa da bulala ake tashinta. Yaha ta watsa mata mugun kallo. “Sai ki sauko tunda motar bata ubanki bace ko? Shashashar yarinya.” Ummi ta lura su kadai ya rage a motar, cikin rawar jiki ta bi bayan Yaha suka fito. Sai lokacin ta lura cewar cikin wani babban gari suke lura da yawan mutanen da ta ga suna faman zirga-zirga. Haka tayi ta bin bayan Yaha har suka fito daga tashar zuwa bakin titi. Saida gabanta ya fad’i ganin ababen hawa da yawa saman kwalta. Ta tsorata sosao da yawan mutanen da ke zirga-zirga awajen. A kauyensu na Ringim babu motoci har haka. Yaha ta tsayar da d’an sahu. Nan Ummi ta ji tace ya kaisu Gadon K’aya. A hanya Ummi tayi ta rarraba ido tana duban tituna. Abin bai gama bata mamaki ba, saida ta ga sun hau wani dogon kwalta ta sama. Ta kankame ledar kayanta, basuyi aune ba sai ji sukayi ta fashe da kuka. “Wayyo Allah zan mutu!” Ta fad’a iyakar k’arfinta. D’an sahun harda kokarin juyowa. “Lafiya?!” Yaha ta rankwashi kanta. “Ka bar ‘yar iskar yarinya mana, “yar kauye. Ta ji ta a titin ‘yan birni zata kawomin iskanci. Yanzun nan zan bubbugeki idan baki rufemin wannan karamin bakin naki ba mai kama da na tsutsa.” Dariya d’an sahun ya kwashe da shi. Ita kuwa Ummi da sauri ta rufe bakinta, tana kuka a ciki-ciki har suka sauka idanunta a runtse yayinda jikinta ke kad’awa. D’an sahun kuwa har da labarin tsohuwar da tayi makamancin hakan ya shiga bawa Yaha. Kasancewar Yahar itama ba baya ba wajen surutu, nan ta biyemishi suna tayi tana 6a6aka dariya. Ummi dai tana jinsu, alokacin ta bar kukan. Sunyi kusan rabin awa suna tafiya sannan suka iso unguwar da ta ji Yaha tayi kira da Gadon K’aya. Haka ta ji Yaha nayita zuba mishi kwatance har suka iso wani gida d’an flat da shi. Ta biyashi kudinsa sannan ta dubi Ummi. “Sauka muje.” Ba musu Ummi ta sauka da saurinta. Yaha tayi gaba ta bi bayanta tana wulk’a idanu tana duban layin. Yaha ta shiga kwankwasa k’ofar tana sallama. Can ta tsinci muryar maigadin na cewa. “Ana zuwa.” STORY CONTINUES BELOW Yaha ta rik’e k’ugu tana taunar cingam ta dubi Ummi. Ganin haka yasa Ummi kauda nata idanun cikin sauri. “Don ubanki saura kiyi min halin kauyenci sai na shak’e ki kin mutu har lahira. Banason yawan kalle-kalle. Kiyi ladabi so…” Sauran maganar ya mak’ale a fatar bakinta ganin an soma k’ok’arin bud’e k’ofar. Maigadin ya d’an lek’o da kansa. Farin buzu ne. Ganin Yaha ya sanyashi sakin fuska. “A’a mai yara, kaine?” Hakanan yake kiranta. Tayi dariya. “Ni ce dai Baba. Hajiyar na ciki ko?” Ya bata hanya ta shigo yana amsa mata. “Eh yana nan. Ina ka samo d’an garinmu?” Ya fad’a yana duban Ummi wacce ta durkusa da rawar jiki ta gaisheshi. Yaha ta dubeta tayi mata alamun ta mik’e. “Wannan ba ‘yar garinku bace. ‘Yar Maiduguri ce.” “Anya? Yana kama da mu.” Yaha dariya kawai ta d’anyi batace uffan ba. Daga haka sukayi ciki. Ummi na bin farfajiyar da kallo a sace don bataso Yaha ta kamata tana kallon bayan ta ja mata kunne. Babban gida ne sosai, an k’awatashi da shuke-shuke. Daga wajen ka rantse ba shi da wani kyau ko girma don kuwa ko fenti ba’ayi ba daga wajen. Haka suka isa har bakin wata k’ofa. Yaha ta murd’a ta shiga. Suka cigaba da tafiya a doguwar barandar dake wajen har suka iso tsakar gidan. Acan bakin rariya, wata babbar mace dattijuwa ce ke zaune saman kujera irin ta tsakar gida tana wanke-wanke. Ganin Yaha ta washe baki. “A’a, lale marhabin da Hajiya Yaha. Yau kuma zuwan rana ce?” Yaha ta numfasa fuskarta na nuna gajiya. “Bari kawai Ramma, duk a gajiye nake. Hajiyar na ciki mu k’arasa?” Ramma fuska a sake ta amsa tana duban Ummi wacce ke takure jikin bango. “Eh tana ciki.” Ummi da sauri ta gaisheta. Ramma ta amsa. Har suka kama hanya Ramma na binta da kallo, yarinyar da alamu zasu d’asa da Hajiya Madina, don kuwa da alama nutsastsiya ce. “Assalamu Alaikum.” Cewar Yaha alokacin da ta murd’a k’ofar falon ta sanya k’afa. Wata dattijuwa wacce ke zaune, wata budurwa mai kimanin shekaru sha shida. Tana zaune a k’asan lallausan kafet tana daddanna mata k’afa. Ta nutsu sosai, kamar kace arr! Ta arce. Ummi dai kallonsu take, daga yanayin yanda ta ga Hajiyar na dubanta, ta sha jinin jikinta, da alama dai matar ba ta da mutunci don kuwa fuskarnan nata babu ko alamun fara’a. “Ranki ya dad’e baya goya marayu, barkanki da hutawa.” Hajiya tayi wani murmushi, da alama ta ji dadin wannan kirari na Yaha. Ummi dai kallon ikon Allah take, yanayin shigarta da komai ma, sun isa shaidar tana cikin rayuwar daula. Wani kallo da Yaha ta watsa mata ne ya sanya ta ba shiri russunawa sosai gami da rankwafar da kanta ta gaisheta. Hajiyar bata ko amsa ba, saidai ta k’ura mata ido tana k’are mata kallo. Can kuma ta yamutse fuska ta rausaya kai gami da maida dubanta ga Yaha. “Wannan ce?” Yaha ta washe baki tana jinjina kai. “Kwarai kuwa ranki ya dad’e uwar gida ran gida, itace, sunanta Hasiya amma Ummi ake kiranta.” Ummi dai sai zazzare ido take kamar shege a rabon gado, Hajiya Madina tayi murmushi, ko babu komai takan ji dadin wannan kirari da Yaha ke mata. “Tayi sosai, na tabbatar, zata iya dukkan ayyukan da na na bata. Ince dai bata da son jiki?” Yaha har lokacin bakinta ya k’i rufuwa don ji take kamar ta shid’e don dad’i domin kuwa ta sha kawowa Hajiya Madina yara, basu yi mata ba. Ta janye k’afafunta, gami da kallon budurwar batare da tace uffan ba, ta mik’e ta wuce don ko Hajiya batayi magana ba, ta karanceta, wato dai ta basu guri. Bayan komawarta ciki ne, Hajiya Madina ta dubi Yaha. “Yahanasu, ina fatan kin shaida mata cewar banason wasa, ba kuma na son son jiki. Dukkan wasu ayyuka da na sanyata, inaso ta kammala su alokacin da ya kamata. Ba kuma na son k’azanta, ta kula sosai don kuwa naga yanayinta, da alama k’azamar ce.” Ummi ta sunkuyar da kai tana sosa gashin kanta wanda amosani ya bi ya takura mata, idan ma ance da kwarkwata lallai babu musu don bata da gatan da Saude zata wanke mata kai. “Kiyi hakuri, na tabbatar ba zaki samu wannan matsalar ba. Sau daya aka gwada mata yanda zata gyara jikinta, na tabbatar babu wata matsala da zata biyo baya.” Hajiya Madina ta jinjina kai alokaci guda ta yamutse. “Yauwa, don kinsan banason abinda wadancan shirmammun zasu samu damar zagina. Ko kusa banason wani mishkila ya fito daga d’akina.” Dariya Yaha tayi, ta gane Hajiya Madina tana nufin kishiyoyinta, Hajiya Rakiya da Hajiya Munira. “Ai kin wuce nan Hajiyata, baya goya marayu. Kar kiji komai, yarinya ce mai kaifin basira. Zata bi dukkan umarninki batare da kin 6ata rai ba. Kwarai, ta ji dadin kalaman Yaha. Daga nan ta mike da nufin zuwa gabatar da sallar la’asar, bayan ta umarci budurwar nan da ta ambata da Amina, da ta nunawa Ummi wajen kwanansu. Amina a gaggauce ta bi umarnin Hajiya. Suka wuce tarr har Yaha wacce zata d’auro alwalar sallah itama. Ummi ta dubi d’akin, katifa d’aya ce sai filo, a gefe kuma jakar kaya ne. Sai kofa daya wacce ta ga Yaha ta shiga ciki, wannan ya tabbatarwa Ummi, bandaki ne. An malale dakin da ledar tsakar daki. Fentin dakin mai wani kyalkyali ne, fari da ruwan hoda, saidai babu komai na more rayuwa ciki. Acan kusa da jakar kayanta, ta ajiyewa Ummi nata da murmushi saman fuskarta ta dubi Ummi, haka kawai ta tsinci kanta da murna sosai, ko babu komai ta samu abokiyar hira. “Nan zaki dunga kwana.” Ummi ta mayarmata da martanin murmushin, saidai har lokacin bata saki jiki ba don kuwa ko k’arar k’ofa ta ji sai ta firgita. Ta riga da ta saba da hakan. Yaba ta fito ta shimfida dardumar dakin ta tayar da sallah. Itama Ummi ta shiga, saidai tayi turus don kuwa bata saba da bandakin yan gayu har haka ba. “Bari na nuna maki yanda zakiyi.” Cewar Amina daga bayanta, wannan yasa Ummi matsawa, ta shigo. Nan ta gwada mata komai, Ummi tayi godiya cikin muryarta sassanya sannan ta shiga ta d’an kara k’ofar don ta tsorata, bata so ta rufe ta kasa bud’e kanta. Bayan tayi alwala, irin yanda ta saba ganin mutane nayi don kuwa ko alfarmar zuwa makarantar islamiyya, Ummi bata samu ba. Tayi yanda ta iya sannan ta fito ta tayar da sallar. Tasan ana yin sallah raka’a hud’u a lokacin nan hakan yasa ta soma babu wani karatun kirki don babu abinda ta iya. Ta idar ta zauna tana motsa baki sannan ta yi jugum tana kalle-kalle. Bayan Yaha ta kammala suka fita, Ramma ta basu abinci, nan suka ci sannan Hajiya ta sallami Yaha ta tafi da abin arziki. Sai lokacin idanun Ummi ya yi kwal-kwal. Ta soma matsar kwallah tana sosa kai. Hajiya ta ja tsaki ta dubi Ramma. “Ramma, fita da yarinyar nan ki dubamin kanta, idan da matsala kiyi mata dukkan abinda ya dace don Allah.” Ramma ta mike. “Angama Ranki ya dad’e.” Ta ja Ummi wacce ke faman ajiyar zuciya da sheshsheka suka fita. Bayan ta tabbatar da cewar tana da kwarkwata, ta koma ga uwardakinta ta amshi kudi ta sanya gyalenta ta ja Ummi suka fice daga gidan. Kai tsaye wani gida k’arami wanda Ramma ke zaune ciki da ‘yan marayun yaranta maza uku suka nufa, ta dubeta. “Ki zauna ki jirani ina zuwa.” Ummi ta gyad’a kanta da sauri. Ba jimawa Ramma ta dawo da kullin ledoji har da fiya-fiya. Nan ta zauna ta gyare kan Ummi tsaf, ta wankeshi da karkashi a karshe, Ummi ta sha kuka don azaba. A karshe ta mik’a mata wani zani bayan ta sanyata tayi wanka. “Goge gashin naki, yarinya mai gashi haka kin barshi ya wulakanta? Kai Allah Ya kyauta dai.” Ita dai Ummi bata tanka ba, ta kara jan zani ta rufe jikinta sosai sannan tayi amfani da wani zanin da ta mik’o mata tana goge kanta. basu bar gidan ba saida Ramma ta taje mata ta sanya man zaitun sannan ta koma ta dauko mata kaya kala d’aya na Amina don duk cikin kayan Ummi babu wani na arziki na sanyawa. Riga da zanin atamfa ne har sun soma kod’au, saidai sun fi nata daraja sau dubu, sannan suka fice. Ita kanta Ummi ta ji dadin gashinta, a farfajiyar gidan suka iske wata bus katuwa ta irinta ‘yan makaranta ta tsaya. Yanmata ne su biyar sai yan samari uku, daya zaikai shekaru goma sha bakwai, yayinda dayan zaikai kimanin shekaru goma sha daya sai na karshen wanda baifi shekaru bakwai ba suka fito daga cikin motar gaba dayansu cikin kayan makaranta. Ramma ta dubesu da fara’a. “A’a yau dai kun dawo da wuri tunda ba’a kai da kiran Magariba ba.” Ta k’arasa fad’in hakan a zolayance tana sauke idanunta akan d’anliti direba. Fuska a daure ya amsa. “Sai ki dunga zuwa daukarsu mana ke.” Gaba daya yaran suka dara, dan saurayin mai sha bakwai ya dan bugi motar. “An gaida dan autan direbobi!” Sun riga sun saba zolayarsa don kuwa wani sa’in ba shi da wasa, idan kuma ya so, wataran sukan yi raha iyakar raha. Toh haka yake da Ramma ma. Daya cikin yanmatan nan ta dubi Ummi fuska a yamutse. “Wannan kuma fa Ramma?” Ramma ta amsa fuska a sake. “Ummi ce, sabuwar ‘yar aikin Hajiya ce.” Ta bi Ummi da kallon raini a karo na biyu kafin ta kad’a kanta tayi gaba tana fad’in. “Ita kam Hajiyarku ba dai kwashe-kwashe ba.” A fusace ta ji saurayin ya bata amsa. “Ta fi wacce fad’anta ke korar ‘yan aiki. Banza kawai da ke!” Ta juyo ta dubeshi ranta a 6ace. “Uwata ka zaga?” Ya d’aga kafad’a yana duban su Ramma. “Kunji na ambaci sunan wata?” Ai kuwa ta fashe da kuka gami da yin Allah Ya Isa. Da gudu tayi ciki don kuwa tasan muddin ya cafketa ba zata ji ta dad’i ba. Danliti ne yayi saurin rik’eshi.. “Haba Adnan, kana babba kana jan kannenka da fad’a? Shige ka wuce don Allah.” Adnan yayi kwafa ya dauki jakar islamiyyarsa yayi ciki yana fad’in. ( “Stupid Girl kawai.”) Daga haka sauran suma sukayi ciki. Ummi dai tana ta kallon ikon Allah, ita tsoron budurwar ma ta ji ganin irin kallon rainin da ta bita da shi. Ta bi bayan Ramma da sauri sukayi ciki. K’aramin yaron da budurwa d’aya ta ga sun k’ara yin ciki sun mik’a hanya. Abin ya bata mamaki, tayi zaton nan kad’ai ne a gidan ashe dai yana da girma. Shi kuwa Adnan da macen d’aya ta ga sun yi inda aka kawota, wajen Hajiya Madina. Anan tsakar falon suka iske Adnan yana labartawa Hajiya abinda ya faru yana dariya alokacin da ya bud’e firij ya d’auki robar ruwa d’aya da niyyar sha. Hajiya ta girgiza kai tana nunashi da yatsa. “Ka dai kiyaye Adnan, banason tsokana.” “Eh mana, kyace bakyason tsokana tunda burinki ya cika an jefamin bak’ar magana. Toh wallahi bari Alhajin ya dawo, bazan lamunci rashin tarbiyyar yaranki ba. Banason cin kashi.” Gaba daya tuni sun maida dubansu ga k’ofar shigowa falon, Ummi ta kurawa matar ido wacce ke rik’e da labule batare da ta karasa shigowa ciki ba tana faman bambami. Bak’a ce, irin bak’in da hutu ya gama ratsawa, ta ci ado har ta gaji don kuwa ita ce a fadar Alhajin nasu. Sai zuba uban k’amshi takeyi. Hajiya Madina batace uffan ba, sai murmushi kawai da tayi. Ko babu komai har ranta ta ji dad’in abinda Adnan ya fad’a saidai dole a fili ta k’i gwadawa don ko kusa bazata so Alhaji ya soma ganin rashin mutuncinta ba. Gwara acigaba da rayuwar gidan a haka. Itama matar tsaki ta ja sannan ta fice cike da jin haushin rashin tankawar da dukkansu basu yi ba. Bataso hakan ba ko kusa. Bayan tafiyarta Adnan ya ja guntun tsaki ya dauki jakarsa ya fice yana fad’in. “Ni kaina har ya soma ciwo ma.” Sama-sama ya jiyo muryar Ramma tana magana don har ya fice daga falon zai nufi dakinsa. “Kayi sallah ka zo akwai lafiyayyen tuwo da miyar kuka mai man shanu, ka ci ka sha magani.” “Shiyasa nake sonki Rammatuwa.” Ya fad’a cikin d’aga murya har ya basu dariya. Kiraye-kirayen sallar da aka soma ne ya sanyasu barin falon. Itama Ummi ta shige dakinsu. Anan ta iske Amina tana kokarin sanya hijabi. Murmushi tayi mata. “Har an wanke?” Ummi ta gyada kanta murya ciki-ciki ta amsa da eh tana mai kunce daurin dankwalinta. Amina ta zaro ido. “Masha Allah, kina da gashi ashe.” Ummi dai murmushi kawai tayi. Jin masallacin kusa da gidan sun tayar da ik’ama ya sanya Amina shimfid’a darduma da sauri tana fad’in. “Kiyi alwala mana.” Hakan yasa itama Ummi ta shiga da saurinta. Saida ta rage cikinta ta ja ruwa bayan tayi tsarku kamar yanda Amina ta gwada mata yanda zata ja d’in sannan ta dauro alwala ta fito. Bayan sun idar suka zauna jugum, Amina na faman addu’o’i ita kuwa kallonta kawai takeyi, idan ta gaji ta hau duban dakin. STORY CONTINUES BELOW ((02)) “Sannu Ummi.” Muryar Amina ta katsemata tunani, ta dubeta, sukayi murmushi a tare. “Yauwa.” Amina ta ninke abin sallar ta ajiye a gefe. Zama tayi a gefen katifa kusa da Ummi tana dubanta. “Daga wane gari kuke?” “Ringim.” Ta amsa a takaice. “Lallai, baku da nisa sosai.” Ummi zuwa yanzu ta dan saki jiki da Amina ganin irin yanda take janta a jiki. Wannan yasa itama bata ji nauyin tambayarta ba. “Ke ba anan kusa kike ba?” Ta gyada kai. “Anan dai nayi rayuwata, amma mahaifina d’an Maradi ne can cikin jamhuriyar Nijar. Zama da neman abinci ne ya kawoshi Nijeriya sukayi aure da Innata, amma yanzu ya rasu, ya barmu mu hudu yaransa. Ni ce ‘ya ta uku a cikinsu.” Ummi ta d’an tallafi kumatunta. “Kema aiki kike yiwa Hajiya?” Amina ta murmusa. “Ni ina yiwa Hajiya Mama aiki ne, kanwar Hajiyarnan ce, abinda yasa kika ganni a gidannan, sunyi tafiya ne da mijinta da yaransu, shine dalilin da yasa na dawo nan da zama kafin su dawo.” Ummi ta jinjina kai cike da gamsuwa. A ranta ta ji babu dad’i, kenan itama wataran zata bar gidan ta barta? “Ya dai Ummi? Kinyi shiru ina magana.” Ummi a sanyaye ta girgiza kai. “Bakomai.” Jin haka yasa Amina yin murmushi. “Shikenan, tashi muje mu tattara falo da kicin kafin Hajiya tayi magana, ki dunga lura da dukkan abinda nakeyi, nasan karshe ke zaki maye gurbina.” Ummi bata ko damu ba, idan ana sabo da aikin wahala, ai yaci kuwa ace ta saba, ina take samun damar yin cikakken awa sadda tana gidan babanta batare da an had’ata da wani nannauyan aikin ba? Gashi anan har gatan da za’a gyara mata kai a bata wajen kwana tsaftatacce da abinci mai kyau ta samu. Ai babu abinda zata ce ga Ubangiji sai godiya. Haka ta bi bayanta zugui-zugui suka fita. A falon suka iske Adnan da kannensa su biyu, wadanda ta ji Ramma ta ambacesu da Ihsan, Hanifa da Fahad wanda shi ne auta a d’akin nasu. Adnan hankalinsa kacokam yana kan wayar hannunsa yana faman latse-latse, yayinda Ihsan ta dukufa wajen koyawa kannenta aikin gida da aka basu a makaranta. Shekarun Ihsan goma sha uku a duniya zata shiga na hud’u, sa’ar Ummi ce. Hanifa kuwa, tana da shekaru goma sha biyu bata da tazara tsakaninta da Ihsan, Fahad ne mai shekaru takwas a duniya. Daga kansa kuma, Hajiya Madina bata k’ara haihuwa ba. Yaranta gaba daya su takwas ne cif, mata uku ne kafin zuwan Adnan duniya, Rahila, Na’ima, Aisha, gaba dayansu ukun suna gidajen aure. Shigowarsu falon ne yasa su d’ago kai su dubesu. Adnan ya k’urawa Ummi ido fuskarsa a sake sannan ya maida dubansa ga Amina. “Ummi sunanta ko?” Amina ta gyada kai tana murmushi wanda ya riga ya zamto jikinta, ko kusa bata rabo da shi. “Itace.” Ummi ta durkusa ta gaisheshi da saurinta sannan ta gaida su Ihsan. Ai kuwa su Ihsan suka tuntsire da dariya. Adnan ya dauki filon kujera yana dariya ya jefi Ihsan da shi. “(See you), mene abin dariyar? Ai na isa a gaisheni, kune dai daga yau kada ki k’ara gaishesu, na tabbatar kin girme musu.” Ya karashe yana maida dubansa ga Ummin. Ihsan ta jinjina kai. “Tab, wallahi saidai mu tafa, na tabbatar bazata girmeni ba. Kuma idan ma aka ajiye wannan a gefe ai ‘yar aikinmu ce dole ta girmama mu.” Ta karashe tana jifan Ummi da kallon eh sun isa. Ummi dai ta kara sunkuyar da kanta. Amina batace komai ba don kuwa bata fiye shiga harkar Ihsan ba, sanin da tayi mata na cewa ta tsani wasa da duk wani wanda yake karkashinsu. A ganinta, bai kai har a zauna a sakar mishi fuska ba. Abin yakan bawa Amina mamaki, yarinya tun bata tafasa ba tana neman k’onewa? Ta tabbata nan gaba idan Ihsan tafi haka za’a ga abu. “Zaki fara ko?” Cewar Adnan lokacin da ya mike tsaye. Ihsan ta dara a karo na biyu sannan ta dubi su Hanifa. “Malamai ku maido hankalinku mu cigaba. Nasoma jin bacci wallahi.” Wannan yasa su Hanifa nutsuwa don suna d’an shakkarta kasancewarta itama wani sa’in akwai masifa. Hakanan ta iya kaiwa mutum bugu, kodan ita din tana da jiki kamar kazar gona. “Muje Ummi.” Sai lokacin Ummi ta mike, Amina daman tana tsaye bata russuna ba. Tasan Ummin itama don yau ta zo ne, amma ita kam tuni an wuce wajen, don wani lokacin bata daukar rainin Ihsan, saidai duk randa ta biyemata suka yi cacar baki ko yaya ne, toh fa tana shan zagi da gori wajen Hajiya Madina. Sam, bata daukar cin mutunci akan yaranta, komin girmanka, muddin ka ta6a mata yara toh fa zatasan yanda tayi ta rama. Idan kuwa daga matan gidan ne, acan fadar maigidan ake k’ulla musu k’ullalliya. Shi kuwa ya hau ya zauna. Haka Ummi ta taimaka suka kammala gyara komai na kicin sukayi wanke-wanke. Lokacin ana gabatar da sallar isha’i a masallacin unguwa. A gurguje suka fito suka tattara falon, Ummi na lura da komai, a karshe bayan sun kammala, Amina ta fiddo dukkan abinda tasan zasu bukata wajen cin abinci ta jera bayan ta shimfid’a babbar ledar cin abinci a tsakar falon. Daga nan ta dubi Ummi. “Jeki kiyi sallah, zan sanarwa Hajiya mun kammala.” “Toh.” Daga haka Amina ta mik’a wani d’an (Corridor) ita kuwa ta nufi dakinsu. Har ta idar da sallar Amina bata dawo ba, nan kuma ta zauna ta soma gyangyadi don kuwa ba karamin gajiya tayi ba. Ta kwanta saman katifar dake shimfide ta mutum d’aya, wani dadi taji ya ratsata, yayinda iskar fanka ke kad’ata. “Ashe nima zan kwana saman katifa wataran?” Ta fad”a a fili. Tana nan kwance ta ji shigowar Amina. Da sauri kuma ta mik’e zaune tana mutsistsika ido. “Har kin soma bacci wai? Taso mu ci abinci.” Ta mike ta bi bayanta, falon wayam, kadan-kadan ta dunga jiyo sautin dariya da hirarrakinsu daga can cikin da batasan iyaka zurfi da yanayinsa ba. Amina ta kammala kwashe komai ta wanke na wankewa, tayi mamakin yanda bata nemi tayinta ba. Suka zauna suka ci tuwo da miya sukayi nak, a karshe suka sha ragowar romon kifi wanda duk an jagwalgwalashi da k’ayoyi, haka suka dan tsinci na tsinta suka zubda sauran. Bayan sun kammala, Amina ta rufe kicin din bayan ta kashe fitila, ta rage fitilun falon sannan suka shige dakinsu suma. “Bazasu dawo falon ba?” Cewar Ummi. Ta gyada mata kai. “Ai kuma shikenan, acan babban falon Hajiya suka fi zama, matukar kinga sun shige, toh sai kuma wata safiyar, don daga nan kowa makwancinsa yake nufa.” Ummi ta jinjina kai kawai. Bayan shigarsu Amina ta dubeta. “Idan kika bi shawarwarin da zan baki, toh lallai zaki zauna da kowa lafiya a gidannan. Yanzu na lura kina tattare da gajiya, ki kwanta ki huta, gobe ma yi maganar idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya. Kinji ko?” Ta gyada kanta tana murmushi, haka kawai ta ji tana kaunar Amina. “Toh Anti.” Antin da ta kirata da shi ya sanyaya ranta sosai, itama ta ji tana kaunarta kamar yar uwarta ta jini. Tana mamakin uwar da ta haifi yarinya kyakkyawa har haka, ta kuma iya barinta ta fito aikatau. Kodayake, rayuwa ce ke sanyawa wani lokacin, ba don rai yana so ba. Ita ta ta6a zaton zatayi wani aikatau? Ko a mafarki a’a. Ta barwa Ummi katifa; ita kuwa tayi amfani da bargo ta shimfida a gefenta ta kwanta. Ummi na jin sadda take zuba ruwan addu’o’i, abin ya bata sha’awa. Daga nan bacci ya kwasheta batare da ta shirya ba.Washegari dakyar ta iya mik’ewa saboda dad’in baccin da ta ji. Amina ta jima tana tashinta, har daga karshe ta hakura tayi sallah sannan ta k’ara dawowa ta tasheta. Sai lokacin ne kuma ta farka. Ummi harda su miyan bacci. Bayan ta idar da sallah tana shirin komawa ta kwanta Amina ta dubeta tayi dariya kad’an. “Lallai Ummi kinaso Hajiya ta bud’emiki wuta. Ai muddin yaranta zasu makaranta to bacci fa ya k’are mana. Sai an had’a musu shayi an dafawa Fahad indomi don kuwa kullum da shi yake tafiya. Sauran kuma wani sa’in shayin ma ba shansa sukeyi ba haka suke tafiya basu damu ba. Sannan akwai gyaran dakunan yara da Hajiya. Sauran ayyukan da ya shafi kicin da falo da tsakar gida, duk ba namu bane, yana cikin aikin Ramma, sai da daddare ne ma tattara falo da kicin yake dole a kanmu. A yanda nasani kenan yanzu, bansani ba ko kema haka zata d’oraki akai ko kuma zata chanja tsari.” Ummi dai tayi shiru kawai tana sauraronta. Suka fita falon. Amina ta kunna fitilu wanda ta tabbatar ita da ta kashe d’in, ita ta kunna don babu wanda zai fito. Adnan ko zai tafi masallaci, zagaye yakeyi ta k’ofar waje ta d’akinsa. Ummi ‘yar mik’omin wannan da wancan ce, tana lura da abinda Amina keyi. Haka kuma tana biye da ita da fahimta. Komai suka hada, Amina ta zuba Indomin a filas din Fahad na makaranta, ta had’a shayin sannan suka fito. A falon suka iskesu, kowannensu na shiri. Ihsan ta shirya Fahad tsaf cikin riga ruwan goro da bulun wando na makaranta. Itama ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka, sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak’in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga gaba. Shima bak’in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar. Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d’aya sai ta shagaltu a kallonsu tana murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai saidai bata da mai mata gatan nan. Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta amsa tana hura hanci cike da jin ita d’in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki. “Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai.” Ihsan ta turo baki. “Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban ‘yan aiki. Kaga banason irin haka, wannan jawomin raini ne fa.” Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. “Ki zubomin shayi.” Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d’aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta ajiyewa Fahad filas d’in abincinsa sannan ta ja Ummi suka fad’a d’akin da Ihsan da Fahad ke kwana. Karamin daki ne sai gado mai hawa biyu na yara. Saman an saka zanin gado kalar ruwan hoda mai zanen (Barbie), na k’asan kuwa an saka bulun zanin gado mai zanen (spider-man). A gefe kuwa, kwabar kaya ne guda biyu, shima d’aya ruwan hoda da fari, dayan kuma bulu da fari. Sai kafet mai duka kaloli ukun da aka kawata tsakar dakin da shi, da kuma k’arami na takawa a daidai hanyar bandaki. Daga can kuwa, karamin madubi ne, sai kwaba da abu mafi yawa akansa, kayan kwalliyar Ihsan ne. Fanka ce kawai a d’akin, sai bada wadataccen iska take. Ba k’aramin burge Ummi dakin yayi ba. Ta saki baki tana kallo. “Ummi ki dunga lura kina rike abubuwan da nakeyi fa, don kuwa gobe zai iya kasancewa ke d’aya zakiyi. Da zarar Hajiya Mama ta dawo zan tafi.” A sanyaye Ummi tayi magana. “Yaushe zasu dawo?” Tana murmushinta na sabo ta amsa. “Hausa nayi miki, ni kaina bansan sadda zasu dawo ba amma na tabbatar ba zata kaisu da nisa ba tunda an koma makaranta, yara zasu je. Nufina yau idan ina nan gobe bana nan, kece zakiyi.” Ta jinjina kai. Tare sukayi aikin, har inda ake daukar sabon zanin gado idan na kai sunyi datti saida Amina ta nunamata. Suka fito, tuni yan makarantar sun tafi lokacin takwas ma ta wuce, saidai sam Hajiya bata lek’o ba. Saida suka shiga dakin Adnan nan ma suka gyarashi tas, shima madaidaicin daki ne, da katifa babba wacce bata da bukatar katakon gado. Komai na dakin adon fari da bulu ne, babu wani tarkace a dakin sosai. Amina ta barta da gyaran gado don taga yanda zatayi, sai kuma ta bata mamaki don tayi kokari ba laifi. Ta dan gyaggyara inda baiyi ba sannan Ummi ta share dakin, anan kam ko Amina ba zata nunamata iyawa ba. Bayan sun fito, shayin suka zuba suka sha da sauran biredin sannan suka maida komai kicin suka koma dakinsu. Suna daga kwance Amina ta soma magana. “Zanso kafin na fad’amaki halayen mutanen da zakiyi zama tare dasu, na soma gayamaki tsarin gidansu don ya dace kisan da wadanda zaki zauna.” Ummi ta muskuta tana dubanta gaba daya ta tattara hankali da nutsuwarta ga Aminan. Ganin haka Amina ta soma.Maigidan, sunansa Alhaji Muhammad Modibbo. Shi d’an asalin garin Adamawa ne, bafulatani ne. Hajiya Madina ‘yar uwarsa ce, saidai ita mahaifinta anan Kano ya rayu, anan ya tara zuri”arsa. Soyayya ta kullu tsakaninsu har ta kaisu ga aure lokacin shi Alhaji Muhammaf ya dawo Kano da karatu ya kuma kama aiki anan. Yana da mata biyu bayan ita, Hajiya Binta itace wacce kika gani rannan, sannan amaryarsa Hajiya Lubna, ita ‘yar Maiduguri ce, yanzun ma da baki ganta ba, taje biki can Maiduguri da yaranta su hud’u gaba d’aya. Hajiya Madina tana da yara takwas kamar yanda na fadamaki, ita kuwa Hajiya Binta yaranta shida. Iklima itace babbar budurwar ‘yarta sannan Hanif, Sadiya, Nafisa, Usman da Jabir. + Ita kuwa Hajiya Lubna, yaranta biyun farko ‘yan biyu ne mace da namiji. Hassan da Hussaina, sai Adam da Hajara. Bar ganin gidannan kamar ba shi da girma Ummi, sai kin shiga can 6angaren zaki k’ara tabbatar da girmansa. Sashe hud’u ne har na Alhajin. Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba, da girma da komai. Hajiya Madina duk ta fisu fada a wajensa, ko don tana ganin ita din ‘yar uwarsa ce kuma tana da daurin gindi wajen mahaifiyarsa Gwaggo ne? Bani dai da masaniya. Amma tabbas Gwaggo bataso ko kusa Hajiya ta kai k’ararsa wai ya 6ata ranta, yanzun nan zata bud’emishi wuta. Shiyasa daga Hajiya Binta har Hajiya Lubna, basu kaunar zuwan Gwaggo Kano, kawai saboda bambancin da take nunawa tsakaninsu da Hajiya Madina. Hakanan tafi zuzuta kaunar ‘ya’yan Hajiya Madina har yakai ma bata iya 6oyewa. Bada son ranta akayiwa Hajiya Madina kishiyoyi ba, saidai kawai don Hajiya Madina ta nunamata tafison kwanciyar hankalin mijinta akan tashin hankali da damuwarsa. Gaskiya Ummi a wani 6angaren, Hajiya Madina tana da mutunci duk kuwa da cewar bata kama k’afar Hajiya Mama ba. Hajiya Mama ciki d’aya suka fito, saidai ita bata da raina ‘yan aiki kuma yaranta sunsan girman ★DAN ADAM★ basu rainashi ko yaya ne. Toh yanda Hajiya Mama take, hakanan itama babbar yayarsu, Hajiya Fatima take. Su uku daman cif a wajen babansu, daga su bai kara haihuwar wasu ba kuma matarsa daya, Baba Ummahani. Ita a Abuja take zaune. Tana da yaranta hudu samari manya, sai yan mata biyu. Ta aurar da yaranta maxa biyu na farko, matan da ragowar mazan biyu sune dai basuyi aure ba. Mijinta tsohon soja ne kafin daga baya yayi ritaya. Amina ta d’an tsagaita sannan ta d’ora tana duban Ummi wacce gaba daya kacokam ta maida hankali gareta tana sauraro. “Hajiya tana da saukin hali idan kika zama mai bin umarninta kan lokaci, sannan tafiso kafin tayi korafi akan bakiyi aikin da kika san kina yi ba toh ki kammala shi. Ko kusa bata son kazanta, hakanan bataso kice zaki wulakanta abinda ta haifa. Batason kuma shigen d’akunan abokan zamanta, idan kika kiyaye bakinki daga daukar magana ki kai wani dakin toh fa zaku d’asa da ita. Ba ruwanki da shishshigi a lamuranta matukar ba ita ta so ki tanka ba. Ki kiyaye kawo mata gulma, nan ma zaku 6ata da ita. Sannan ko wani abu marar dacewa kikaga ta yi, bataso ki tanka mata, nan kuwa zaku 6ata. Batason ta kamaki da cin amanarta. Yaranta suna da saukin hali Ummi, matukar kika kama kanki ba zasu rainaki ba. Ihsan ce ma mai matsalar, ita kuma kiyi kokarin fita harkarta. Idan dai ta sanyaki aiki kada ki k’i, kiyi hakuri kiyishi hakan saboda itace ma musabbabin da yan aiki basujin dadin zaman gidan. A duniyar nan, kawai dai ki tsare abinda za’a ci mutuncinki ko yayane, kedai ki tsaya matsayinki baruwanki da cusa kai kinji ko?” Ummi ta danyi murmushi alokaci guda hawaye suka zubomata ta sharesu, wai yau itace da samun mai bata shawara a lamarin rayuwa? Itace ta samu wannan gatan har haka? Wani irin kaunar Amina ya k’aru a zuciyarta. Amina da mamaki ta mike zaune. “Ummi kukan kuma na menene?” Ummi ta girgiza kai. “Bakomai.” Amina ta ji wani tausayi ya dabaibayeta. Tasan akwai wata matsala a rayuwar Ummi, tafi kuma tunanin bata da iyaye. Ta numfasa, batason ta matsa mata da tambaya, ta tabbatar wataran don kanta zata gayamata tarihinta. “Komai yayi zafi maganinsa Allah Ummi. Ki bar damun kanki da lamuran rayuwa har haka kinji ko? Ki rik’i addu’a da karatun Alkur’ani da sallar dare. In sha Allah komai zakiga ya wuce.” Ummi da fuskar tausayi ta dubeta. “Nifa bansan komai na Addini ba wallahi. Kawai dai ina yin sallah idan naga lokaci yayi mutane sunayi.” Mamaki karara ya bayyana saman fuskar Amina, batasan ya akayi ta jefomata tambaya ba. “Wai Ummi, iyayenki basu raye ne? Shekarunki nawa yanzu?” Ummi tayi k’as da kanta ta soma hawaye. “Mahaifiyata ta rasu tun ina jaririya, babana yana raye. A hannun matarsa na taso.” Kwallah ta cika idanun Amina, ta gano bakin zaren. “Idan ba damuwa ki sanarmin tarihinki mana.” Tiryan-tiryan ta sanarmata da irin rayuwar kuncin da ta rayu ciki. Cikin muryar kuka tace. “Kalmar da ta kasa ficemin a rai bai wuce da babana yace wai ko birnin sin ne na tafi ba shi ba damuwarsa bace. Babana baya sona yanda yakeson kanwata Mariya.” Kuka sosai takeyi, itama Amina tana tayata. Wani kaunar Ummi ya k’aru a ranta, ji takeyi tamkar kanwarta ce ta jini. Dakyar Amina ta rarrasheta tayi shiru sannan ta dubeta da kulawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *