DAN ADAM CHAPTER 14
Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba g2udunmuwa. Sai bayan Azahar su Mami suka soma shirin tafiya. Ummi suma sun kammala hada komai nasu ta tsinci sak’on kira daga Mami. Mamin na daki daga ita sai Ihsan wacce jin cewar zata karasa hutunta a gidan su Faruk ya sanyata kasa rufe baki don tsabar farinciki. A haka Ummi ta shiga ta riskesu, Mamin na faman kimtsawa don tafiya. Bayan an gaisa ta ce. “Gani Mami.” Mami ta dubeta. “Yauwa Ummi, anan za ki zauna har muga abinda hali ya yi, saidai bayan komawata tukunna.” ‘Innalillahi wa inna ilaihir raaji’un!’ Shine abinda Ummi ke ambata a can kasan ranta, ta ya ya zaayi a barta a gidan su Faruk, ina laifin ma idan sun je Kano ta je koda gidan su Hajiya Mama ne ko gidan su Inna? ‘Ai ba danginki bane.’ Cewar wani sashen zuciyarta. Ta ji babu yanda ta iya don yan uwannata basu ma damu da sha’aninta ba. “Wai bakya ji ne wani sabon wulakanci ana ta yi ma ki magana kin yiwa mutane banza kamar tsararki?” Maganar Ihsan kenan wacce ta maidota hayyacinta batare da shiri ba. Ta dubi Ihsan din wacce a take ta watso mata harara kamar idanunta zasu zazzago, gaba daya bakin cikin jin cewa har Ummi itama anan zata zauna ta ke, kamar ta shak’eta haka ta ke ji, tsaki ta ja ma a karshe ta fice daga dakin cikin kunar rai. Ummi ta maida hankalinta ga Mami.+ “Toh Mami. Allah Ya kaiku lafiya, Ya gyara lamura.” Har cikin ran Mami ta ji dadin addu’ar. “Amin. Kina iya tafiya.” Ta mike jikinta babu kwari ta fita, tana zuwa dakinsu ta fad’a saman katifa ta yi tagumi. Haka Amina wacce ta fita kai kaya mota ta shigo ta risketa. “Aa ya ki ka zauna, yanzu fa zasu fito.” A sanyaye ta dubeta ta sanarmata yanda Mamin ta ce. Amina ta numfasa. “Allah Ya sa alheri ne ya tsayar da ke Ummi. Nidai fatana ki kiyaye dukkan nasihuna gareki, ban zama mai cutarwa gareki ba.” Ummi ta yi yak’e tana duban Amina. “Wallahi Anti babban ma fargabata bai wuce Ihsan ba, na tabbatar zan sha wulakanci daga gareta.” Amina ta girgiza kai da dan murmushi saman fuskarta wanda na yak’e ne. “Karki damu Ummi, Allah Yana tare da ke. Kedai kiyi takatsantsan da lamura, bari naje kada su Hajiya Mama su rigani fitowa.” Ummi ta mike sanye gami da zura hijabinta a saman riga da siket na koriyar atamfa ta bi bayanta. A fusace ta shiga dakin babu ko sallama, hakan yasa su Ikram, Intisar harma Anti Aisha da Rahila dubanta. “Ke lafiyarki kuwa? Ku ganemin yarinya kamar mai iskokai yanzu kika fita kina murnar za’a barki garin masoyinki, kin shigo kuma kina fushi, meyafaru?” Cewar Rahila kenan. Ihsan ta zauna gefen gado inda Aisha ke sanyawa Tahir famfas ta ja tsaki. “Wai don Allah meyasa Mami ta ke yin haka ne? Ya zaayi don nima zan zauna anan ace itama Ummi nan zata zauna? Wannan abun ya isheni, Mami bata da masaniyar yanda na tsani yarinyarnan wallahi da bata soma cewa ta zauna inda nake ba.” Mamaki ya bayyana a fuskokinsu. “Sannu sarauniyar wauta, sai akace zamanku a rumfa daya yana nufin matsayinku daya? Kai wallahi har gobe banga randa kuruciya zata fita kanki ba Ihsan.” Fadin Rahila kenan kafin ta fice daga dakin rataye da jakar kayanta. Dariya sauran suka sanya, Intisar ta ja rigar Ihsan kadan. “Kina bani mamaki, kodai kishi kikeyi don Ummi ta fiki kyau ne? Wannan tsana haka?” Ihsan ta yamutsa fuska, kusan ma har da hakan saidai ita kanta tasan da abu k’alilan zata fi Ummi, shi dinma wuyarta Ummin ta samu hutu kamar yanda ta ke samu. Saidai kuma ta fusata sosai da zancen Intisar. Ta mike a fusace ta fita suna mata dariya wanda hakan ba karamin k’ara rura wutar kiyayyar Ummi ya yi a ranta ba. Amina da Ummi sune suka taimaka wajen fidda jakunkuna, Ummi a sace sai sharar hawaye take yi don har cikin zuciyarta bata so zaman garin Abuja, ga kuma fargabar kada Faruk ya yi wani abun da zai janyo mutan gidan su fahimci manufarsa a kanta. Haka suka tafi banda Adnan wanda ya ce ko zai koma ba yanzu ba. Mami dai ganin bai gama hucewa ba ne yasa ta kyaleshi. Ummi ta juya jikinta a sanyaye zata koma ciki, Ihsan da suka hada ido harara da dallara mata, Adnan kuws murmushi ya sakarmata. “‘Yar Abuja.” Ya fada cikin tsokana, murmushin yak’e ta yi mishi. Tana shirin barin wajen ta tsinci muryar Ihsan bayan Hajiya Babba ta riga ta koma ciki tana fadin. “Rashin dangi ne yasa ta ke yawo daga nan zuwa can, duk dai abin mutum bazai chanja iyaye ba. Kauyen dai da ake gudu nan ne asali.” Daga haka ta tsinci muryar Adnan yana mata sababi bayan ya kai mata bugu ta kauce. Daidai da su Intisar basu ji dadin abinda ta aikata ba. “Bansan halin wa kika biyo ba, don danginmu ba ma wulakanta mutum, muna girmama DAN ADAM daidai gwargwado.” Cewar Intisar kenan sannan ta juya ciki ranta babu dadi. Haka suka watse suka bar Ihsan cike da k’ara jin haushi da tsanar Ummi a nata ganin duk a kanta akeyi mata hakan. Ita kuwa Ummi duk yanda ta so shigewa daki kai tsaye don kanta da ta ke ji yana sarawa ga kuma wani kuka da ya ke tahomata hakan bai samu ba sakamakon kiran da Hajiya Babba ta yi mata. Ta karasa ta durkusa cikin ladabi. “Gani Hajiya.” Hajiya ta dubeta fuska a sake. “Yauwa Ummi, sai kuma kika ga an barki a wajena ko? To ina so muyi zama na tsakani da Allah da ke, daman na riga nasan da kyawawan halayenki daga bakin Madina, ki k’ara a kan hakan. Gyaranki na dakina ne sai falon sama da kuma wannan na k’asan. Sauran dakunan kuwa suna karkashin kulawar Binta. Girki daman ba aikinku bane da wanke-wanke, kinji ko? Akwai mai yi na kwanaki ma ganin bak’i da yawa yasa nake cewa ku shiga, fatan kin fahimceni?” Ummi ta jinjina kai, ranta ko digon farinciki babu sakamakon har lokacin ranta a tsananin 6ace ya ke. “Na fahimta Hajiya kuma in sha Allah zan kiyaye zan kula.” Hajiya Babba ta ji dadin furucinta ta sakarmata murmushi. “Na lura dai ranki bai miki dadi ba akan zaman da za ki yi anan, karki damu, na dan lokaci ne, da zarar na sanya an samomin wata za ko tafo, mai yiwuwa ma tare da su Ihsan.” Jin an k’ara ambaton Ihsan sai ta ji duk zancen ya gundureta, ta daure ta k’akalo murmushi. “Lah bakomai Hajiya, ai can da nan din duk daya ne.” Daga haka Hajiya ta sallameta. Tana shiga daki ta zube saman katifa, a hankali maganganun Ihsan suka dawo mata kawai sai ta fashe da kuka sosai har tana sheshshek’a. Wannan rayuwa ta soma isarta, Ihsan ta soma kaita bango, abin nata yana neman wuce gona da iri, ko don tana ganin ita din bata da wani karfin ikon da zata kwaci ‘yancinta ne? To wane ‘yanci ma ta ke da shi a yanzun tunda ba wani babban jigo abin tunk’ahonta wanda zai iya yin wani kata6us akan lamuranta? Kewar mahaifiyarta yafi komai damunta, ko babu komai ta tabbatar ba zata watsar da ita kamar yanda Mahaifinta ya yi ga rayuwarta ba. A karshe dai wani sashe na zuciyarta ya yi ta nusar da ita da muhimmancin Yarda da Kaddara, haka har dai zuciyarta ta danyi sanyi ta mike don d’auro alwalar La’asar. Yana zaune saman kujera a ofis cike da dumbin tunani da damuwa, ya daga kai ya dubi agogon bangon dake a ofishin nasu, agogon ya nuna karfe hudu saura mintuna uku, ya ja guntun tsaki gami da dafe goshinsa. Ya san zuwa wannan lokacin sun wuce, tabbacin farin cikinsa ta tafi saidai hausawa sun ce garin masoyi baya nisa, yasan ko yaushe ya yi niyya muddin ranar babu aiki zai iya kai mata ziyara. Saidai zai so matuk’a tafiyar ta kasance babu ita. ‘Akan wane dalili?’ Cewar sashe na zuciyarsa, ya runtse ido gami da jingina kansa jikin kujera. Daidai da rana d’aya, bai ta6a kawowa zai had’u da wata d’iya mace har sonta ya ta6a ayyukansa haka ba. A wannan ranar dakyar ya jure suka kammala suka tashi, a hanya Magriba ta riskeshi haka ya karasa gidan ya yi fakin duk jiki a sanyaye. Bai zarce ko’ina ba sai sashensa. Saida ya yi sallah ya watsa ruwa ya sanya bak’ar jallabiya a saman gajeran wandonsa sannan ya yi niyyar shiga cikin gidan. Hankalinsa ya kai ga Adnan wanda ke kwance saman gado yana danne-dannen waya. Yatsun k’afarsa na hagu ya ja wanda ya tilastawa Adnan yin gefe da wayar yana mai sakin k’ara lokaci guda kuma da dariya. “Kai my best.” Faruk ya murmusa kadan. “Baka da aiki sai(chatting) kwanakin nan, ya dace na soma haramar kora ka makaranta naga ta (chatting).” Dariya Adnan ya cigaba da yi. Faruk ya zura silifas dinsa ya fice zuwa sashen Hajiyarsa. Bayan saukowarsa daga bene saida ya tsaya cak yana k’arewa hanyar dakunan yan aikin kallo, yasan Ummi zuwa yanzu ta yi mishi nisa. Ya sauke ajiyar zuciya gami da juyawa ya cigaba da tafiyarsa. A falo ya iske Ikram da Ihsan suna cin abinci suna hira. Ganinsa yasa duk suka dubeshi suna mai amsa sallamarshi. Yana duban Ihsan da mamaki ya jefamata tambaya. “A’a, baku wuce ba?” Ihsan cikin kashe murya ta ce “No sun wuce, ina nan sai bayan sati biyu zan koma.” Bai wani ji dadi sosai ba, zaman Ihsan takura rayuwarsa kawai ne, ba yau ba ya soma lura da take-takenta, shi din ya kasance mai saurin fahimtar masu nunamasa so haka. Yana sane da Iklima ma, sai yanzu ne ma ya fahimci ta dan kwana biyu bata mishi koda sallama ba a whatsapp ballantana kuma akai ga kira. “Ok.” Shine kawai abinda ya ce sannan ya k’ara gaba. Ihsan ta bi bayanshi da kallo har saida Ikram ta zungureta. “Kin shiga uku wallahi kedai, nikam har na daina mamaki.” Ihsan ta yi murmushi. “Me kike nufi?” “Ina nufin ki sanarmasa kina sonsa.” Ihsan ta zaro ido. “Zubda aji.” Ikram ta yi kwafa. “Tsaya kallon ruwa kwado ya yi miki k’afa.” “Wai kina nufin akwai wacce ya ke so?” Ikram ta yi dariya. “Bani da tabbacin hakan. Amma kada ki sake ki tsaya wani jan aji wallahi. Yayanki ne, koda zai wulakanta kowa banda ke.” Ihsan dai ta yi shiru ta cigaba da kai loma, maganar Maminta kawai ta ke tunanowa inda ta yita bata shawara akan ta yi kokarin jawo hankalinsa ta kissa. Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu ya wuce, can su Ikram suka kai musu abincinsu, har lokacin sam ba shi da masaniya akan Ummi na Abuja. Koda ya shiga wajen Hajiyarsa, bata sanarmishi ba.+ *** *** *** KADUNA Wasa-wasa karamar magana ta zama babba, domin kuwa Deen da Dija soyewarsu sukeyi son ransu, saidai hirarsu ta fi a waya ko kuma idan sun yi sa’ar rana Munira bata gida. Tun ita Munira bata ganewa har ta soma zargin akwai wani abun. Kamar yanda Deen ke damuwa da harkar Dija sosai, abin mamaki har zuwa ta ke ta zauna a hau wasa da dariya da ita har ma su dinga wareta cikin hirartasu saidai ta yi shiru tana sauraronsu. Dija da kanta ta bawa Deen shawara akan lokacin komawarta gida ya yi idan har da gaske ya ke sai ya turo magabatansa. Alokacin ne kuma ya yi dumm, ya dubeta. “Kina ganin hakan bazai janyomin matsala da Munira ba?” Ta ji haushin furucinsa, ta fahimci koda asiri ya ci shi akanta, tofa baisa ya mance da matarsa ba. Ta nunamishi idan ba zai iya aurenta saboda matarsa ba, shikenan. Anan kuma ya hau bata hakuri suka ajiye maganar yanda za’a 6ullowa lamarin. Kwanaki biyu da yin maganarsu ta tattara ta koma Ringim, Munira ta ji dadin tafiyarta don Allah shaida ta soma tunanin akwai wata alak’a tsakaninta da maigidanta wanda bata fatan zatonta ya kasance gaskiya. Ta rik’i Dija yar uwa haka kuma da zuciya daya ta ke zaune da ita. Koda zasu rabu, tayi mata kyauta ta sutura da abin hannu, idan kuma zaa hada da wanda Deen ya yi mata, to fa ba komai bane. *** *** *** RINGIM “Lale da ‘yan Kaduna. To, saukar yamma ce?” Baba Habiba ta fada tana mai dan tafa hannuwa kamar kawata Bingel a fagen nanaye (LOL). Dija ta sakarmata jakar kayanta ta kar6a da gaggawa tana mai k’arewa diyartata kallo da dumbin mamakin yanda akayi ta chanja, wani k’iba ta k’ara da kyau. Sai da dare bayan sun zauna ne suna ‘yar hirarrakinsu, wayar Dija ta k’ara daukar k’ara a karo na biyar tun shigowarta gidan. Baba baki bude ta ke dubanta, ta rasa inda zata tsoma ranta don tsananin murna, ga dukkan alamu dai diyarta ta samu saurayi dan birni, lallai ba zasu yi sake ba. Bayan Dija ta ajiye wayar ne ta dubeta. “Ya sunansa?” Dariya ma tambayar ta bawa Dija, bayan ta gama kyakyatawa ta ce “Wa kenan?” Baba ta girgiza kai. “Ke bafa za muyi sake ba, fadamin sunansa mu k’ara kamashi a hannu yanda bazai ta6a iya su6uce mana ba kafin zuwa lokacin da za’a tashi aurenku muyi shiri na musamman.” Wani murmushi Dija ta saki. “Zahraddeen sunansa.” Baba ta zaro ido waje. “Wanne kenan?” Babu ko d’arr ta amsa. “Zahraddeen dai da kika sani, mijin Munira, shi nake so kuma ya ke sona.” Baba ta yi tsit, Dija tiryan-tiryan ta labartamata ire-iren hidimar da yake mata har da kyautar kudi dubu talatin da ya yi mata da za ta taho ya kuma siyamata sabuwar waya tana nan cikin kayanta. Har ma da yanda suka ajiye magana da shi akan zai zo neman aure. Bayan ta kammala bayanin ta fiddo kudaden ta damk’a a hannun Babarta, ta zaro kwalin wayar shima daga jakarta tana mai nunamata. Baba Habiba ta zurawa kudin ido da wayar kafin ta washe baki. “Ke Dije! Wadannan yanzu duk mallakinki ne? Shakka babu daman bokanya ta tabbatar min idan mijin aurenki ya zo za muyi mamaki gashinan tun ma ba’a je ko’ina ba na soma. Abun yi yanzu, gobe zan koma gidan bori na ji yanda zamuyi ayi komai cikin salama batare da ansamu matsala ba, don ta ubanki mai sauki ne, sai yanda nace.” Wani ihun dadi Dija ta saki gami da rungume mahaifiyarta. “Shiyasa nake bala’in sonki wallahi Baba.” Suka yi dariya, nan suka soma shawara kan irin k’ulle-k’ullen da zasu sanya ayi bayan auren. Ko kusa Dija bata sanarmata komai akan Raihana ba gudun yanda zata yiwa kallon abin. *** *** *** KANO Mami ta yi mamakin chanje-chanjen da ta gani wajen Mijinnata. Abin mamakin bai wuce yanda ya dage akan lallai su bata girkinta ba. A ranar kuwa suna isa ita ce ta shiga fadarsa. Saboda Fahad, Ramma ta kwana a gidan kasancewar yaranta suna kauye ziyarar dangin ubansu. Ta sha rok’o a wajensa akan ta yafemishi har ta gaji domin duk da nunamishin da ta yi komai ya wuce, bai iya sakin jiki ba. Ranar kam komai ya yi lafiya, ya sanarmata haka kawai ya soma tsintar kansa cikin halin tunani da kuma tsananin kewarta. Tsakanin mata da miji dai sai Allah, a wannan daren suka dinke har ma ya nemi kiran d’ansa don ya dawo ya soma shirin tafiya karatunsa. ‘Babu abinda ya fi karfin Allah.’ Shine abinda Mami ta fad’a a zuciyarta cikin murmushi lokacin da ta saci kallon fuskar mijinta ta ga annurinsa ya dawo ba kamar da ba.1 *** *** *** ABUJA Misalin karfe shida a gaggauce ya kammala shirinsa ya fice zuwa aiki ko karyawa bai tsaya yi ba. Ummi tun misalin takwas suka soma ayyukansu, ta yi gyararrakinta tsaf, Binta itama ta kama nata. Hajiya Babba ta yaba kwarai da gyaran Ummi. Koda ta shigo ta iske falon kyal-kyal tana(mopping) ta kalli wajen kafin ta amsa gaisuwarta da murmushi dauke saman fuskarta. “Eh lallai, dole Madina ta so zamanki wajenta, ashe haka kika iya gyara? Lallai kam na yaba miki Ummi.” Wani murmushi ta yi har kumatunta saida suka lotsa, kwarai ta ji dadin wannan yabo da ta samu. Hajiya Babba ta yi dakinta, nan ma an kyalkyaleshi tamkar ba’a ta6a kwana cikinsa ba. Komai tsaf, hakanan ta ga bambancin aikinta da na Sa’a kwarai. Ummi duk jikinta babu dadi, duk da cewar tana son gujewa Adnan, rashin had’uwarsu a kwana biyunnan yana damunta, batasan dalilin son sanyashi a kwayar idanunta da ta ke yi ba. Hankalinta ya kai ga tafkekan hoton matasan yaran Hajiya Babba. Dukkansu sanye suke da shadda ruwan k’asa tazarce, ta sha surfani mai tsada. Hularsu mai surkin ruwan k’asa mai duhu da marar duhu, a tsaye sukayi hoton a farfajiyar wani (hall), daga hotunan bayansu za ka tabbatar cewar a wajen wata walima ne. Ta kauda idanunta gami da sauke ajiyar zuciya, duk cikinsu babu wanda yafi haskakawa a idanunta kamar Faruk, ko don shi zuciyarta ke so ne? Har Ummi ta yi kwana biyu a gidan, Faruk ba shi da masaniya don gaba daya aiyuka sun mishi ca a ofis. Ba shi ya samu kansa ba sai ranar Asabar. Ranar kam ya sha bacci, bai farka ba sai sha daya. Kai tsaye wanka ya fad’a, bayan fitowarsa ya shirya cikin t-shirt fara tas da wando na (Adidas), bak’i mai surkin fari kadan sannan ya zura silifas ya nufi sashen mahaifiyarsa. Tafe take a hanyarta ta zuwa wajen(garden) don dauraye tsummokaran da ta kammala gyaran dakunan Hajiya da su. Kallon benen da zata yi ta ganshi yana saukowa shima a daidai lokacin ya bar duban wayarsa ya maida ga hanya alokaci daya kuma yana kokarin sanya wayar aljihun wando. Karaf idanunsa cikin nata, yanda ta tsaya bata motsa ba, shima ya tsinci kansa da mutuwar tsaye. Abu biyu ke yawo a kwakwalwarsa. Buri na son kasantuwar abinda ya ke gani yanzu tamkar mafarki da kuma tambayar daman tana gidan? Dakyar ya yi jarumtar k’arasawa har gabanta, alokacin ita kuwa ta sunkuyar da kanta cike da matsanancin fargabar abinda zai k’ara ce mata. Saida ya kai dab da ita har suna jin numfashin juna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya matsa, ya tabbata ita din ce ba gizo ta ke mishi ba. A hankali ya matsa baya, cikin rawar murya ta gaisheshi bayan ta durkusa. Ya amsa cikin jin wani irin nishadi a ransa, ta mik’e tsaye, tana shirin barin wajen maganarsa ta dakatar da ita. “Daman ba ki tafi ba?” Ta dan saci kallonsa, murmushi ta gani dauke saman fuskarsa wanda ya kara fiddo kyawunsa. “Eh.” “Saboda ni?” Ya fada a tausashe bayan ya dan rankwafo da kansa yana kallon fuskarta. Ta k’ara satar kallonsa, shi dinma bai kauda nasa idanun daga kanta ba. Ta ji wani iri a jikinta, wai saboda shi. Maganar ma nauyi ta yi mata, ta kauda idanunta. “Mami ta ce na zauna zuwa wani lokaci.” Ya ji dadin maganar, ba zai iya misalta farin cikin da ya shiga sanadin hakan ba. Ya dubi hanya babu wani ko wata da ke tahowa sannan ya dubeta. “Ummi, yau kenan za ki tayani hira?” Ta zaro ido batare da ta dubeshi ba, cikin sauri ta girgiza kai. “Kayi haku…” “Shiit.” Ya dakatar da ita ta hanyar dora yatsansa a saman le66ansa. “No please, karki hana zuciyarki abinda ta ke so mana Ummi. Ko kina so wani abu ya faru da mu sanadin hana zukatanmu farin cikinsu?” Ba amsa sai idanunta da suka kawo ruwa, ya mik’e da rankwafawar da ya yi. “Shikenan, ki tafi, mu had’u wajen pool.” Daga haka shiru ya biyo baya, karshe ma ya juya ya cigaba da tafiya. Da ido ta bishi, ta tabbatar shi babu abinda ya ke tsoratashi, kamar yanda babu matsalolin da ya ke hangomusu, ita kadai ta damu da duk wadannan. Koda zai shige saida ya juyo domin ganin yanayin da ta shiga, suna hada ido ta juya da sauri ta soma tafiya. Murmushi ya saki kafin ya karasa cike zuciyarsa cike da tsantsar farinciki. Daidai da Ikram da Ihsan sun ga chanji yau wajen yayannasu, don kuwa biyemusu ya yi akayita hira da dariya. Ihsan ji ta ke tamkar ta buga tsalle don murna da farinciki, yau ita Faruk ya dage hira da ita? Tabbas shawo kansa zai zo mata da sauki muddin ya d’ore a haka. A yan kwanakin da ta yi tsaf Hajiya Babba ta fahimci inda ta dosa, a farko bata gaskata Ikram ba da ta sanarmata cewar Ihsan na son Faruk ba, saida ta lura da kanta. Abin ya yi mata dadi, zata so hakan ta kasance, saidai d’annata ne batasan abinda ke ransa ba. A ganinta da wuya ya kaunaci yarinya mai rawar kai irinta, hakanan Ihsan sam bata da hakuri, ga saurin fushi. A raayin Hajiya Babba, bata kaunar abinda zai damu ‘ya’yanta, kusan halinsu daya da Mami na son ‘ya’ya.+ Acan kuwa Ummi tana isa ta zauna saman kujera gami da zubawa famfo ido, hankalinta gaba daya ba a wajen ya ke ba, ya tafi gaba daya ga tunanin Faruk. ‘Dagaske fa ya ke.’ Shine abinda ta fad’a a ranta, tabbas Faruk dagaske ya ke, asalima babu wani alama na tsoro ko fargaban abinda zai biyo baya. Yanzu ya zata yi? Bai bata damar cewa ba zata zo ba, ya riga ya yanke cewa lallai kawai ta zo ta sameshi. Ta riga tasan duk ranar da wani a gidan ya gano to fa tashin hankalin da zata shiga ba k’adan bane. Tagumi ta zuba tana tunano da Antinta, yau ne rana ta farko da ta soma jin bukatar waya a rayuwarta, ayau inda ace tana da waya, tuni zata yi kiranta ta bata shawarar da ta dace. Ta ja guntun tsaki sannan dakyar ta mike ta soma aikin da ya kawota, saida ta kammala ta shanya sannan ta koma ciki. Misalin biyar na yamma tana zaune a k’asan bishiyar mangwaro tana wasa da ganyen, hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin Faruk, banda murmushi da wani annuri, baka ganin komai saman fuskarta. Ita tasan tana sonsa, bata ta6a son wani d’a namiji ba sai shi, saidai kawai bambancin dake tsakaninsu, shi kadai zai hanasu aure. Ta jima kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga inda ta ji sautin dariyarsu. Ihsan ce da Ikram dukkansu sanye da kananun kaya, riga da siket, sun nad’e kansu da karamin dankwali. Hira sukeyi abinsu da dariya har suka iso wajen motar da tun zuwansu Abuja, Faruk tasan yana hawanta. Suna hada ido da Ihsan ta maka mata harara, Ummi ta kauda fuskarta. ‘Kanki ake ji.’ Shine abinda ta fad’i a ranta. “Har kun fito?” Tattausar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ta so ta jure kada ta kalleshi, saidai hakan ya k”i yiwuwa, ji ta yi tamkar bazata nutsu ba idan bata ga tasa shigar ba. ‘SubhanAllah!’ Shine abinda ta fad’i a ranta. Riga tshirt ce yasa kalar(golden, long sleev) mai mannuwa a jiki, sai (blue jeans) ya sanya gilas dark brown, agogonsa na k’a’ida yana daure a hannunsa sai zobunansa da baya rabo da su. Ji ta yi tamkar numfashinta zai dauke tsabar kyawun da ta ga ya yi mata a idanu. To ba Ummi kadai ba, Ihsan kanta baki ta bud’e tana kallonsa, ji takeyi tamkar ta dora hannu a ka ta ce wayyo Allah, kamar ta matsa bakin Faruk ya furta yana sonta. “Wow Yaya Faruk, kayi kyau wallahi.” Muryar Ikram ya katse Ummi da Ihsan daga tunanin da zukatansu suka lula. Ya dan rankwashi kanta yana dan murmushi. “Ko?” Ta yi dariya. “Allah kuwa.” Ya jinjina kai sannan ya zagaya zuwa mazaunin direba ya bude motar, Ihsan da sauri ta bude gidan gaba ta shiga, hakan bai wani dameshi ba, don shi bai dauketa wata aba ba face k’anwa. Ya bud’e motar kenan yana shirin shiga idanunsa ya kai gareta. Ita dinma har lokacin shi ta ke kallo, batasan tana da kishi ba sai a yanzun, Faruk ne da Ihsan wacce ta riga tasan tana tsananin sonshi, babu walwala a fuskarta hakanan bata daureshi ba, ta mik’e da sauri ta bar wajen ta nufi ciki. Ya dan dubesu. “Ina zuwa. Zo ki tayar da motar kafin na zo.” Ya karashe zancensa da duban Ikram. Ba musu ta kar6i muk’ullin, basu kawo komai ba don babu wands zai yi tunanin wai Faruk zai dauki Ummi wata aba. Shi kuwa da sauri ya nufi hanyar da ta yi da zummar komawa sashensa saidai ya zarce kai tsaye wajen dakunansu da zummar kwankwasa mata. Hawaye ta ke fitarwa da batasan dalilinsa ba, tasan dai tana jin zafi ne cikin zuciyarta na ganin Ihsan a gaban motar Faruk. (Ji karfin hali!) Tana shirin lek’ensu ta windo, ta ji bugun kofarsa yana kiran sunanta. A rude ta saurara ta ji, tabbas shi dinne, ta share fuskarta da sauri sannan ta bud’e k’ofar. Ya fidda gilashinsa yana dubanta, bata yarda ta kalleshi ba. “Kar kiji shiru Ummina, zan kai yaran nan siyayya amma bazan jima ba kinji?” Kai kawai ta gyada cike da jin haushi, da tana da iko da ta ce ya fadawa Ihsan ta koma baya saidai yin hakan wani nuna karfin hali ne wai 6arawo da sallama. Ita da ke cin arziki? “Ko za kije?” Ta girgiza kai a tsorace. “Sai kun dawo.” Ya daga kafada yana mai wani shagwa6e fuska kamar wani yaro. “Allah kuwa idan kina so ki zo muje.” “Don Allah kayi hakuri.” Itama tayi maganar cikin marairaice murya don gaba daya tsoro ya cikamata ciki, bata so wani ya zo ya gansu tare. “Shikenan, me kikeso na siyomiki?” Hankalinta ya tashi ga shi ya tsare bakin hanya babu damar ta duba hanyar ta gani ko wani ya taho. Ta dubeshi gaba daya a rude ta ke. “Ko menene.” Ya fahimci duk a rude ta ke, murmushi ya saki yana mai juyawa. “Bari na tayaki duban hanyar.” Ya dan kalla sannan ya dubeta har lokacin bai bar murmushin ba, kafada ya daga gami da daga gira kadan. “Karki damu, idan don Binta ce, tana tare da Hajiya, can na barota. Bazan tafi ba sai kin gayamin abinda kike so na kawo miki.” “Na shiga uku.” Ta yi furucin da bata shirya fitowarsa fili ba, ga mamakinta sai ta ga yana dariya har yana dan jijjiga kafada. Ta yi sakato tana kallonshi, bai ta6a yi mata dariya har haka ba, sai taga ya k’ara yi mata kyau matuk’a. Hon din da suka ji ya katse su, tasan su Ihsan ne. Ta dubi windo kafin ta juyo ta dubeshi. Ya dan daga gira. “Kina 6atamusu lokaci.” Ta rasa ya zatayi. “Ka siyomin alawa.” Ta fada kamar zata fashe da kuka. Ya kwaikwayi muryarta. “Guda nawa?” Ta yi mishi nunin biyu da yatsa. Ya murmusa. “Bye, sai na dawo.” Kanta kawai ta gyada, ya juya ya tafi. Ta lek’o ta na kallonsa har ya maida gilashinsa, murmushi ta saki gami da juyawa ciki ta rufe kofar. Wajen windo ta k’arasa da saurinta tana lek’ensa, tana ganin yanda ya had’e musu gira tamkar ba shine ya gama yi mata murmushi harda dariya ba yanzun. Akan idanunta ya bude motar ya shiga, daga haka ta daina ganinsu sakamakon gilashin motarsa mai duhu ne. Sauke ajiyar zuciya ta yi gami da rike kirji tana dariya marar sauti idanunta a lumshe, dariyar Faruk kawai ta ke gani ta ke jin sanyi, yanda ya nunamata tsantsar kulawa har mamaki abin ya bata, ashe ire-irensu sukan ji dadin duniya? Da ace wannan farincikin zai dore da ta fi kowa sa’a a rayuwa. Ta numfasa gami da bin lafiyar kafet ta kwanta. Sauranta jiran dawowarsa da ganin da wacce ya zo, duk kuwa da tsantsar fargaba da ke cin kasan ranta. Bata so wani ya san alaka’ar da ke tsakaninsu…