DAN ADAM CHAPTER 20

DAN ADAM CHAPTER 20

  KANO Da yamma suka isa, direba na fakin, ta sauko daga motar a hargitse, tana rataye da jakarta ta hannu. Sukayi kici6us da Iklima wacce ke shirin fita zuwa makwafta, daga ita sai doguwar riga(fitet gown) da mayafi karami kalar kayan. Ta watsamata kallon tara saura. “Akwadaita an dawo?” Ihsan ko kallonta bata yi ba ta gifta ta wuce. Iklima ta bita da kallo gami da sakin dariya, batasan meyasa yanzu gaba daya ta tsani Faruk ba, wani mugun so ta ke yiwa dan wata k’awar Hajiya Binta, Mu’azzam, shima sonta ya ke yi tamkar ya mutu. Ihsan bata zarce ko’ina sai sashensu, tuni Fahad ya isar da zuwanta ga Mami wacce ke kicin tare da Ramma suna aiki, saidai duk fuskarta babu digon walwala. Jin zuwa Ihsan yasa ta fito, Ihsan na shiga itama uwar ta hau kwalawa kira. Suna yin kici6us ta fad’a jikinta gami da ruk’unk’umeta ta soma hawaye. Mami ta lumshe ido tana mai rungumeta, ta riga tasan meke damunta. “Aa lale da manyan gari.” Maganar Ramma ya katse tunaninsu, jin hakan Mami sakinta. “Shiga ciki ina zuwa.” Bata ko amsa sannu da zuwan Ramma ba, ta yi gaba abinta, wannan ya bawa Ramma tabbacin akwai matsala kenan. Mamin tasa Ramma mik’amata kayan sama. Tana jin Ramma na fadin. “To ita kuma Ummin tana ina?” Saidai babu mai amsamata, koda ta shiga dakin Ihsan harara ta samu da ta kulata. Ramma ta kama baki. ‘O’o, ko ta yi gamo ne a hanya?’ Ta tambayi zuciyarta don tasan ba mai amsamata. Ta fice tana jimamin wannan lamari na sauyin da aka samu daga uwar har d’iyar, tana nan Hajiya Mama tazo saidai kafin ta je gida ta dawo ta tarar batanan. Sai bayan Magriba, Mami ta yi wanka ta shirya tsaf da nufin zuwa turaka, alokacin ne ta shiga dakin diyarta ta inda ta tarar da ita tana goge jikinta alamun wanka ta yi. Ganin Mami yasa ta zama gefen gado, itama zaman ta yi. “Mami kin ji…” “Kar ki ma 6ata bakinki, nasan komai.” Cike da mamaki ta ce. “Au Mami har daman zasuyi mana wannan cin fuskar su iya kiranki su sanarmiki?” Ranta ya dan sosu da jin kalma ta cin fuska da ‘yarta ta jefi Hajiya Babba da shi, zata so ita ta kirata da komai amma bataso yaranta su rainasu. “Kar ki k’ara fad’ar haka tunda ba ke ta ciwa fuska ba, ni ta yiwa. Kuma idan har muna raye zasu ga sakayya.” Ihsan ta yi kwafa tana mai jin zafi a zuciyarta. “Wallahi Mami ni na hakura da Yaya Faruk, na ji na tsaneshi ma. Wai akansa aka ci zarafina, banda cin zarafi ta ya ya za’a had’ani kishi da ‘yar aiki, wallahi nafi karfinnan.” Ta ji dadin kalaman Ihsan din, daman ita ta ke ganin zata bata matsala sai kuma ta bata mamaki. Cikin murmushi ta dafa kanta. “Kin burgeni matuk’a, barni da su suna gani sai kin auri mijin da yafi Faruk komai da komai, sai sunyi mamakin mijinki Ihsan. In sha Allah kuma sai kin riga d’anta aure. Ita kuwa Ummi su jik’ata su shanye, mu ba’a koyamana yawan malamai ba, idan ita ta bisu don kawo mana rashin jituwa a zuri’armu to ta cigaba idan zaiyi tasiri.” Ihsan ta dan ji wani iri, so daban ya ke, anya zata so wani nan gaba irin son da ta yiwa Faruk? Tana ji Mami ta gama maganganunta kafin ta mike bayan ta ce idan ta kammala ta zo ta gaida Abbanta, daga nan ta fice, Ihsan ta bita da kallo. Sai kuma ta dan ja guntun tsaki gami da cije le6e. Ummi kadai ce matsalarta fa, da babu ita, babu abinda zai hanata auren Faruk. Amma kuma Mami na da gaskiya, watakil fa ba banza ta bar su ba, ta yi kwafa. “Babu abinda yafi karfin addua, za ki gane kurenki.” Ta yi furucin a fili. Saida ta kammala shiri cikin doguwar jallabiya ta fito, bayan kammala cin abinci da Fahad ta ja hannunsa zuwa ga Abbansu, Adnan tun maganar da sukayi da Mami ya bar gidan. Abba ya yi farinciki da zuwanta, ita kuwa dadin sake ganin dariyar Abbanta ne ya cika zuciyarta, gani ta ke yi kamar a mafarki. Sun jima suna hira kafin Mami ta umarceta da shiga sashen matan gidan a gaisa. Haka ta soma da zuwa sashen Hajiya Binta, babu kyakkyawar tarba daga gareta harma yaranta, itama ganin haka ta nuna yar zamani ce ta fito batare da ta k’ara kallonta daga gaisuwa daya. Kai tsaye wajen Anti Amarya ta nufa, ta sakarmata fuska fiye da baya don ita bata da matsala a hakan, hakanan su hussaina yaranta, har Anti Amarya tayita janta da hira tana fadamata ta yi k’iba. Ihsan ta ji dadin zuwa sashenta kafin su yi sallama. Haka halayen Anti Amarya ya ke saika rantse dagaske so na tsakani da Allah ta ke maka, takan yi iyakar kokarin boye ainahin sirrin zuciyarta agabanka. (DAN ADAM MAI WUYAR GANE HALI KENAN…!) Hajiya Mama ranta duk a 6ace, Amina da yaran Hajiya Maman, Rukayya, Maryam, Na’im da autarsu mai shekaru goma, Mufida. Intisar ce babbat diyarta don Hajiya Mama bata samu haihuwa da wuri ba. “Lafiya kuwa yau?” Cewar Rukayya tana duban yan uwanta. Amina wacce suka zama kamar yan uwa ta jinjina kai. “Nifa na lura tun dawowar Hajiya Mama daga gidan Mami bata cikin hayyacinta, Allah Yasa ba wani abun ne ya faru ba.” “Amin, ni duk jikina ya yi sanyi ma wallahi, bakuga wainar fulawar nan ta dazu ba gaba daya fita daga raina ta yi wallahi.” Rukayya ke maganar tana yamutse fuska cike da damuwa, duk da ita ce ma karfin cewa suyi wainar fulawa har ana rabon aiki, wannan ce zatayi suya a farko idan ta gaji waccan ta yi, wancan mai daka yaji. “Allah Ya jishshemu alheri.” Fadin Amina kenan. Suka amsa da amin, ita kam Amina ko aka bata ta6a kawowa wani batun Ummi ne ya tashi da Faruk ba? To wa zai kawo hakan ma? Suna nan zaune Adnan ya shigo da sallamarsa. Suka amsa, Maryam ta saki baki tana dariya. “Ikon Allah, kodai mafarki nakeyi, ku mintsileni mugani.” Ai kuwa Amina da Rukayya harma da Mufida suka hau rige-rige, ganin dagaske suke ta yi tsalle ta ja baya suka sanya dariya gaba daya. Adnan ma cikin dariyar ya zauna, hankalinsa ya dan kwanta da yanda suka tarbeshi, ko babu komai ya ji dadin ganin Hajiya Mama bata sanarwa yaranta ba. Bayan an gaisa yake sanarmusu batun tafiyarsa gobe, Rukayya harda ihun murna, Maryam ta zaro ido. “Dagaske?” Adnan ya jefeta da kallon kauna don kuwa sun had’a kansu saidai a 6oye suke soyewa ta kafar sadarwa harda yiwa juna alkwarin rikon amana. “Kamar baki sani ba?” Sai kuma ta yi murmushi. Maryam ta ta6e baki. “Ato, ai munsan komai saidai mu yi shiru.” Ya yi dariya da mamaki kafin ya dubeta. “Ke kika sani malama, ina uwata?” “Au, daman baku hadu ba? Daga gidanku fa take.” “Eh, ni na dan fita ne.” “Ayya, bari ayi mata magana.” “Kamar ba gidanmu ba?” Ya fad’a yana hararar Rukayyar, sukayi dariya kafin ya wuce. Sallama ya yi, Hajiya Mama ta amsa don ta ji maganarsu da yaranta. Fuska a sake tana mai kokarin danne damuwarta ta ce. “Aa Adnan? Karaso mana.” Ya karasa jiki a sanyaye ga kuma kunyar abinda Maminsa ta aikata gareta ya russuna ya gaisheta. Ta amsa. Shiru ya biyo baya kafin ya soma bata hakuri kan abinda ya faru. “Kayya, dama baka shiga ciki ba don kuwa wannan tsakaninmu ne. Karka damu, ka yiwa mahaifiyarka uzuri kasan ance mai d’a wawa, watakil son nata ne ya rufemata ido har haka. Amma nasan Madina ba lallai har zuciyarta hakan bane.” Ta fad’a ne kawai ba don har zuciyarta tana ganin hakan bane, saidai bata kaunar yaransu su shigo cikin maganar wanda dai da kamar wuya. Bazata so ya shafi zumunci yaransu ba da mazajensu. Adnan shi kansa yasan Hajiya Mama ta fad’a ne kawai. Ta share maganar. “Ashe kuma gobe zaka wuce ko?” “Eh.” Ya fada yana mai shafar sumarsa. Ta shiga yi mishi nasiha tamkar dan cikinta, da nunamishi sanya Allah a rai da kuma gujewa mugayen dabi’u da abokan huld’a. Adnan ya ji dadi matuk’a na shawarwarinta, ya ji dukkan damuwarsa ta warware daman ya dauka shikenan Hajiya Mama ta barsu kenan, sai ya ga ba haka ba. Koda ya ce zai wuce, dakatar da shi ta yi don saida ya ci abincin dare sannan ta kaishi har wajen Alhaji Haruna mahaifin su Intisar suka gaisa shima ya bishi da kyawawan nasihu da kuma addu’o’i kafin suyi sallama ya tafi bayan su Maryam sun tabbatar mishi zasu zo rakiyarsa zuwa(Airport) goben. *** *** *** ABUJA Faruk kuwa yanda sukayi da Haidar ya yi, ya shirya ya wuce gidan Dakta. Bai iskeshi ba sai Jidda da ta hau shi da tsiya akan ta ji da auren wacce kuma ya 6ige. “Amman wallahi ka bamu kunya.” Ya watsamata wani kallo yaso ya tanka sai kuma ya tuna maganganun Haidar, bazai so kam zumunci ya 6aci ba. Ya yi kwafa. “Kin fa ci darajar yarana, da a yau za ki koma Ghana.” Ta yi dariyar k’ular da shi. “Dad’in abun ba kauye na tashi ba ballantana na tsoraci komawa.” Bai ko k’ara kallonta ba ya fice yana murmushin kinyi kad’an. Kai tsaye asibitin da Dakta Ridwan ya ke ya isa. Duk da ba ranar aiki ba ya shiga don duba wata mai nak’uda da ta samu ‘yar tangard’a, ya yi nasarar ciro bebin lafiya yana cikin dinketa ne, ya hango kaninnasa daga jikin windo kasancewar windon gilas ne, ya dubi nos dake gefensa cikin fad’a. “Ba ki da hankali ne? Ta ya ya za’a barmin windo bud’e ina aiki?” “I’m sorry Sir.” Daga haka ta karasa cikin sauri ta saki labulen, murmushi Faruk ya yi ya zura hannuwa a aljihu kafin ya wuce kai tsaye ofishin Dakta. Zama ya yi akan kujerarsa yana kalle-kalle kafin ya ta6e baki. “Wani aikin sai likita, duk wani jagwal suna gani.” Ya k’arashe kafin idanunsa ya kai ga dan karamin frame din dake saman teburin, su hud’u ne a hoton wanda akayi musu ran bikin Ridwan din. Idanun Faruk a rufe don lokacin ma bai zama cikakken matashi ba, su kuwa sun dubeshi suna dariya aka yi hoton. Murmushi ya yi, shi kam haka Allah Ya yishi bai fiyeson hoto ba. Duk da dai yayyunnasa sun ce bikinsa ne da baizo ba, muddin ya tashi aure watakil ma da kansa zai dunga kiran mai hoton ya dauka. Yakan yi dariya don yana ganin lamarin wasa kawai. Baifi mintuna goma ba sai ga Dakta ya shigo. Yana ganinsa ya tsaya ya daure fuska. “Get out of my office.” Ya fada yana mishi nuni da k’ofa. Faruk ya mike tsaye ya na dubansa fuskarsa dauke da damuwa. Ganin ba shi da niyya yasa Dakta soma tattara abin amfaninsa zai wuce gida don daman abinda ya shigo da shi kenan, da sauri ya sha gabansa ya rungumeshi. “Please forgive me brother, kayimin dukkan hukuncin da kaga ya dace da ni.” Ya dago jikinsa yana dubansa da idanunsa wadanda suke nuni da gaskiyar abinda ya ke fad’a. “Amma kada ka hukuntani ta hanyar dauke fara’arka daga gareni da kuma fita harkata.” Jikin Ridwan ya yi sanyi, daman dauriya kawai ya ke yi don tun bayan barinsa gidan Daddy, ya ji babu dadi, yasan kaninnasu mai son farincikinsu ne, ta ya ya shi ya kasa kar6ar abinda yazo musu da shi da hannu bibbiyu ko don faranta ransa? Ya dafa kafadarsa. “Kamin laifi Lil, saidai na yi maka uzuri tunda baka ta6a yimin makamancinsa ba. Karka damu ya wuce.” Ran Faruk ya yi sanyi, tare suka jera suna tafiya, Ridwan na k’ara nunamishi dalilin da yasa ya nuna rashin goyon bayansa. “Gani nake kamar ka wuce ajin yarinyar ne, na kuma yi tunanin kodai wani asirin ta yi maka? Amman ka yo hakuri.” Faruk ya yi murmushi. “Babu abinda ta yimin, ka manta muna dagewa awajen adduar neman tsari? Duk da dai akwai kaddara, amma bama fatanta. Wannan kauna ce daga Allah nake jinta game da ita.” Suka dubi juna sukayi dariya, ya bugi kafadarsa. “Lil ne da soyayya? Kamar ranar nan ba zata zo ba.” Faruk ya shafi sumarsa yana shagwa6e fuska. Hanashi wucewa ya yi suka nufi gidan Ridwan din da niyyar zuwa yamma su wuce gidan gaba daya. Ta (whatsapp) ya sanarwa da Haidar cewar sun shirya. Ya aikomishi da rawa na mace har abin ya sanyashi dariya. Jidda ganinsu yasa ta hau cakar Faruk akan batun Ummi, shi kuma ya ce ta yi ta gama aure ne babu fashi sai idan Allah baiyiba. Shi kam Dakta na jinsu saidai baisa baki ba, saida ya kula da Jiddar na neman korar mishi k’ani yasa shi tsawatarmata dole ta saki hirar ta yi shigewarta daki da alama dai ‘yar bayan Ihsan ce. ABUJA Hajiya Babba ce zaune a falonta tare da yaranta maza ana ‘yar hira. Ta dubesu cike da farincikin ganin yanda Ridwan ya sakarwa Faruk fuska kamar yanda suka saba, fatanta Allah Ya cigaba da had’a kan yarannata haka. Suna zaune a saman kafet ga katuwar leda agabansu an shimfid’a sai kulolin abinci duk Ikram ta zuzzubamusu. Haidar ya sanyo batun auren Faruk da irin kyauta ta musamman da ya tanadar mishi. “Mata biyu lokaci guda? Ai wannan ni kadai nasan tanadin da na yi ma.” Ya fada saitin kunnen Faruk , ya yi kamar bai ji ba ya cigaba da cin abincinsa. Babban Yaya na jin haka ya ajiye cokali gami da dan kora ruwa sakamakon kwarewar da ya so yi babu shiri. “Wai wa zai auri mata biyu?” “Oh, baka da labari fa ashe Dan uwa.” Cewar Dakta. “Abincin za ku ci ne ko hira zaayi?” Suka tsinci muryar Daddy wanda ya katse hanzarin Haidar da Dakta masu zuci-zucin bawa Babban Yaya labari kamar wasu yara. Ya karaso fuska a sake ya zauna. “Ke kuma na lura duk ranar da ‘ya’yanki ke gidannan kina mantawa da lamurana, ina ga dai na kusa hanaku irin wannan zuwan.” Ya karashe yana kallonsu, suka yi dariya har Faruk. “Kai amma da na ji dadi Daddy.” Ya fad’a yana kanne ido daya. Suka watsamishi hararar wasa banda Babban Yaya da ya ke dariya. “Kwana nawa ne kaima?” Fadin Haidar kenan. Daddy ya dakatar da su da hannu. “Ya isa hakanan, a ci abinci a nutse. Idan kun kammala ina nemanku.” Daga haka ya tashi Hajiya ta bi bayansa. Bayan sun kammala suka hadu sashen Daddy har Ikram. Ya soma da fadin. “Ku amanar Allah ce awajena, ya kuma zama dole na dunga nusar da ku akan lamura na rayuwa.” Ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ya sanyo batun auren Faruk da Ummi. “Idan Allah Ya shiryo hakan babu wanda zai hana, hakazalika kowa da kaddararsa a rayuwa.” A karshe dai ya kara nusar da su batu na hadin kai, akan ko bayan ransa yana fatan su rike zumunci. Sun jima anan, Babban Yaya bai nuna wata alama ta k’in sha’anin ba, Ikram dai har lokacin zuciyar bata lafa ba, koda ta yi yunkurin hakan da zarar ta tuno da wacce zaa aurar sai ranta ya yi bak’i. Ko yar uwarta Baraka lamarin baiyi mata dadi ba, Intisar ma ta nuna rashin yardarta ga Hajiya Mama nan ta ci karo da fushinta, dole ta ja bakinta ta yi shiru ba don ranta naso ba, ga mijinta shima da ya goyi bayan dan uwansa. Haka taro ya tashi zuciyar kowa a sake har Ikram don ta samu dama Faruk ya sakarmata fuska. Bayan fitarsu Daddy ya sanarwa Hajiya cewar lokaci ya yi na dauke Ummi daga sashen yan aiki, itama daman ta yi tunanin hakan saidai tunanin da ya yi mata yawa akan k’in daga wayarta da Madina ta k’i yi duk kuwa da cewar ta samu magana da Hajiya Mama ta nunamata komai lafiya amma sam hankalinta bai kwanta ba. Sunyi waya da Adnan ya sanarmata gobe zai wuce, ta bishi da kyakkyawar addua da kuma nasiha. *** *** *** RINGIM Habiba da Saude suna komowa Ringim kai tsaye wajen bokanyarsu suka zarce. Suna isa bayan anmusu iso suka shiga gami da zubewa agaban Uwar Biyu mai bori. Habiba ta zayyanemata dukkan yanda ya faru a mafarki. Ta mike ta soma jijjige jiggigenta da kad’e-kad’e kafin ta zauna fuska a murtuke sai kuma ta kyakyace da dariya wanda ya razanasu ya kada yan hanjin cikinsu. Maganarta ta katse tunaninsu. “Karki damu kanki! Wannan ba komai bane sai shaida na cewar diyarta na nan tafe da wata gagarumar nasara a rayuwa wanda zai iya janyo tonon silili kala-kala ciki harda mutuwar auren daya a cikinku! Abubuwa da yawa a rufe su ke nakasa fahimta amman ina mai tabbatarmuku ba mai kyau bane gareku! Wannan duk ba damuwa bane idan ni Ade Mai Bori na raye to ba bazai afku ba ko kadan!” Cikinsu ya k’ulle tsabar rud’u, Saude har fitsari ta soma a wando, Habiba da ta soma had’a gumi ga jiki da ya dauki rawa ta daure ta soma magana cike da dauriya. “Mudai yanzu bokanya da ke muka dogara, ki taimakemu ki fiddamu wannan hatsari.” (Waiyazubillah) Dariya na hauka Ade Mai Bori ta yi kafin ta yiwa kanta kirari cikin karaji sannan ta dubesu fuska murtuke. “Zan yi muku aiki fiye da yanda na rufemuku bakin shegu a baya! Me ku ke bukata?” Saude ta riga Habiba magana. “Idan da hali a kashe Ummi!” Ta tsaya ta gama tsaface-tsafacenta kafin ta dubesu idanuwa a zazzare. “A’a! Na duba wannan bazai yiwu ba!” Saude da hawaye ya tahomata ta kasa magana sai rawar jiki, Habiba ta cafe. “Bokanya nidai a haukatar da ita yanda bazata yi amfani ba koda ta zo.” Ta gama tabbatarwa da ba mai yiwuwa bane ba a hanyar tsafinta, saidai bata son ko kusa ta nuna gazawarta har karo na biyu hakan yasa ta kyakyacewa da dariya. “Angama!!! Ko garinnan ba zata ta6a waiwaye ba!!!” Ransu ya danyi sanyi, suka had’a duk kudaden dake jikinsu wanda ya kai dubu ashirin suka ajiyemata. Haka suka baro wajen hankali tashi, Saude suna fita ta ke6e bayan gini ta rage mararta, tana ji cikinta na kad’a saidai ta danne har su isa gida ta kasaye. A hanya babu wanda ya iya magana kowanne tunaninsa ya ke yi, duk tunaninsu ya basu cewar karshensu fa ya kusanto. Babu babban abinda ya k’ara hargitsasu sai mutuwar auren dayansu da Bokanya ta ambata. Ko kan wa zai fad’a??? Koda suka isa a gidan Saude suka yada zango, saida Saude ta rage cikinta sannan ta samu zama don su tattauna, alokacin kuma Mariya ta shigo gidan daga gidan makwafciyarsu acan ta kwana. “Habiba, kinji kuma sabuwar masifa ko?” Habiba ta numfasa. “Hum, bari kawai Saude, wallahi don ba ki ji yanda kwakwalwata ta dauki chaji ba, kai wannan jarabar da me ta yi kama? Da nasan akwai wannan ranar tafe wallahi da sadda na gama da shegiya lokacin zan gama da ita itama. Ni na yi zaton shikenan ta zama hanyar arziki ashe akwai sauran rina a kaba?” Saude ta share gumi da mayafinta. “Wallahi dadin da naji daya ne, na cewa da Bokanya ta yi zata haukata mana ita, kinga shikenan sai daga nan ta k’ara gaba, idan ma ta samu motar da ta kad’eta, mun huta.” Habiba ta saki fuska. “Allah Yasa hakan.” “Ameen dai.” Nan suka cigaba da maganar, hankalin Saude ya kai ga diyarta Mariya da ta zura hannu a wando ta yi shiru tana kallonsu. Cikin tsawa ta ce. “Ke ciremin hannu daga nan tun ban bubbugeki ba!” Habiba ta mik’e gwuiwa a sake. “Atoh, ki ka sani ko k’aik’ayi ne?” “Ai ina zaton haka, mantawa na yi ma ina son kar6omata maganin sanyi wajen Bokanya, wannan yawan soshe-soshen ya isheni.” “Yafi dai kam idan ba so ki ke ta diyarki ta 6aci tun yanzu ba. Bari na je na huta gajiyar bikinnan tunda hankali ya kwanta.” Saude ta taka mata har kofar gida kafin su yi sallama itama ta koma ga harkokin gabanta batare da ta k’ara maida hankali ga yarinyar ba….! KADUNA+ Amarya Dija an dirji amarci, Deen kamar ya haukacemata tsabar rud’ashin da ta yi, ita kanta tasan ta yi aure ta samu miji na nunawa sa’a. Munira baiwar Allah, a wannan daren ta ci kuka har ta gode Allah, tana yiwa ranar kallon bak’ar rana agareta, wai mijinta da yar uwarta da ta dauketa tamkar wadda suka fito ciki daya, sune tare a makwanci guda. Dakyar ta iya saita kanta don a daren ba wani bacci da ta yi. Da safiyar litinin ta daure ta rigasu fitowa ta hada karin kumallo na gaba dayansu. Kamar ta je ta . kwankwasa musu sai kuma ta tuno cewar ko sallama a daren jiya Deen fa baizo ya mata ba, koda a waya bai nemeta ba sai ita da ta mishi sakon taya murnar aure nan ma bai amsa ba. Anya yanzu ba bada kai bane ta je kwankwasa musu? Ai ta daure ma da ta yi girkin. Juyawa ta yi ta koma suka karya da yaranta ta shiryasu ta fice kaisu makaranta. Su kuwa masoyan basu tashi ba sai bayan takwas, suka shiga wanka bayan sun gama suka shirya. Dija ta hade cikin wani leshi kore dinkin da ya kama jikinta, shi kuwa kananun kaya ya ci don ya samu hutu wajen aikinsu na amarci. Koda Munira ta shigo, dariyarsu ce ta bata shaidar sun tashi, ta daure ta hadiye abinda ta ke jin ya tasomata a zuciya ta shige dakinta. Su kuwa karya kumallo sukeyi hankali kwance, Deen na so ya je ganin Munira saidai yana gudun 6acin ran Dija. Bayan sun kammala suka koma daki, wayarta ta dauki k’ara, ganin mai kiran yasa duk ta dan diririce ta wayance da katsewa gami da saurin sanya wayar a(silent), ta jefa wayar k’asan filo tana murmshin yak’e. “Mutane ayita takura mutum.” Ya yi murmushi yana mai janyota jikinsa. “Madam ko za kimin rakiya mu gaisa da yarana?” Ta daure fuska. “Kodai kace za ka ga matarka?” Ya ja karan hancinta. “Ta ci albarkacin yaranki mana.” Zata k’i sai kuma ta tunano da kiran da Raihana ke mata, ta yamutse fuska. “Jeka kai daya, ni babu inda zanje.” Ya yi murmushi. “Shikenan.” Ya mike ya fita saida ta tabbatar ya tafi din sannan ta ciro wayarta a k’asan filo. Mayyar lokacin m wayar kiranta ne ke kara shigowa. Takaici ya isheta, ita fa yanzu duk ta ficemata aka, idan ma abinda ya shafi bukatarta ne to yanzun ta samu mai daukemata, duk wannan haukan ya fice daga kwanyarta daman ba ta6a aikatawar ta yi ba a fili. Ta daure ta kai zuciyarta nesa ta daga wayar. Daga can kuwa Raihana har wani gwauron numfashi ta saki wanda Dija ta ji shi har ta ji kamar ta shiga wayar ta mak”urota. Ta daure “Kin kira ban kusa.” “Eh kina can kina amarci ai, ni na dauka ma ko wani laifin nayi miki.” Ta cije le66anta. ‘Laifin uwaki.’ Ta fad’a a ranta, a fili kuwa ta dan yi murmushi mai sauti. “Haba ni ina na yi wannan isar da za ta ce haka gareki? Ko kusa.” “To ya ango? Dijat kada fa ki k’i cika alkawarin da ki ka dauka, ki yi hankali, idan har ki ka ce za ki juyamin baya zan iya daukar kowane mataki.” Hankalin Dija ya tashi, yau ta shiga uku, hankalinta ina ya tafi da ta mance da batun bokanyar uwarta har ta amince da Raihana akan ta sama mata mafita? Kodayake lokacin ji ta ke ko menene ma zata iya aikatawa matukar zata samu ta auri Deen. “Kinyi shiru.” Ta dan gyara murya. “Ina na isa na mance da hakan? Karki damu ina sane.” Raihana ta yi dariya. “Ina Kaduna, da zarar kin gama satin amarci, zamu soma namu.” Ai saita mike tsaye tsabar kaduwa. Kasa magana ta yi ta kashe wayar gaba daya, ta koma ta zauna gefen gado. Babu wata mafita face na kiran Babarta, dole ta bar yin rufa-rufa gareta yanzu, idan yaso ta je mata wajen Bokanya ta gayamata duk halin da ake ciki. Acan kuwa, Deen ya shiga dakin Munira, tana zaune gaban madubi daga ita sau daurin kirji ta yi wanka. Ganinsa ba sai ta juyo ba, sallamar ma a ciki ta amsa. Zama ya yi gefen gadon yana dan satar kallonta tana shiryawa, tunaninsa bai wuce tsakanin matannasa biyu ba wace ta fi k’ira? Yana lura da abubuwa da dama wanda Munira ta mallaka, Dija bata mallakesu ba saidai ya dan lura da ramarta, ya kasa jurewa ya mike ya isa gareta gami da rungumota ta baya. “Wai ba gaisuwa?” Ta tureshi kadan sannan ta gaisheshi, ya amsa. Cikin gatse ta tambayi amarya, ya shafi kansa ya amsa a dan kunyace. “Idan na kammala abinda nake na je mu gaisa.” “Am ina yaran nan?” Ya fada cikin basar da wancan maganar, ta watsamishi wani kallon da bata shirya ba. “Ka manta yau litinin?” Ya jinjina kai yana dan kame-kame. “Oh hakane fa.” Daga haka bata k’ara ce mishi uffan ba, har ta kammala shirinta ta hau gyara, ganin haka yasa shi ficewa sum-sum. Ta bishi da kallon tausayawa kanta. Kamar ba Deen din da ta sani ba, gabadaya ya chanja, ta soma tunano kyakkyawar rayuwar da suke gudanarwa kafin zuwan Dija, yanzu kam babu shi. Hawaye ya zubomata, ta kasa cigaba da aikin don daman kanta ciwo ya ke, kwanciya kawai ta yi bayan ta sha magani, cikin taimakon Ubangiji kuwa bacci ya yi awon gaba da ita. *** *** *** ABUJA Ta rude iyakar rudewa jin da ta yi wai yau zata koma gefen dakin da Ikram ta ke wato dakin Baraka harma da batun da Binta ta zo mata da shi na cewar ayau dinne sabbin yan aiki biyu zasu zo. Binta ta zunguri kafadarta. “Wai kina daukar hakan wasa? Wallahi dagaske nake, Hajiya na ji tana sanarwa Ikram kar kiso kiga yanda yarinyar nan ta hada fuska, karshe ta kwalamin kira ina daga kicin akan na zo na kiraki.” Ummi ta jinjina kai, wato shikenan ta tashi daga matsayin ‘yar aiki? Allah kenan mai yanda ya so. Jiki a sa6ule ta bi bayan Binta, ai kuwa kamar yanda Binta ta fad’i haka dinne ya tabbata wato dai za’a chanja mata muhalli, ita kuwa Binta ta samu k’arin albashi wanda yafi ba baya tsoka. Wannan abu ba karamin dadi ya yi mata ba. Ita ta taimakawa Ummi suka gyare dakin tsaf, dakin sak irin na Ikram ne, saidai bambanci and kala, na Baraka komai adon ruwan hoda akayi, ita kuwa Ikram (sky blue)da fari. Binta cewa ta ke.. “Ki godewa Allah Ummi, Allah Ya daukaka ki lokaci guda ke kam alherin Allah ne ya kiraki Kano ki ka hadu da Yalla6ai har ga shi sanadinsa kin samu matsayin dab an ta6a ganin wata ‘yar aiki ta samu ba. Ummi kam murmushi kawai ta ke, gaskiyar maganar kenan da Binta ta fad’a. A ranta godiya kawai ta ke ga Allah, saidai a gefe guda tana jimamin haduwarsu da Antinta Amina, anya lamarinnan zaiyimata dadi? Bayan sun kammala ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana kallon Binta wacce ta dage sai an jera kaya a sif, ita kuwa sam bata so hakan ba, gani ta ke kamar za’a maidata sashenta. Ta daga kai ta dubi(Ac) da Binta ta kunna sai aiki ya ke yi, acewarta gwara ta dinga shan ra6a itama ta murje. Aka banko kofar aka shigo babu ko sallama Ikram ce, ta rike k”ugu tana bin dakin da kallo kafin ta yi musu duba na raini. Sai kuma ta kyalkyale da dariya. “Abinka da wanda bai saba ba kenan.” Ta dauki(remote) ta kashe Ac, sannan ta dubi Ummi tana yamutsa fuska. “To sarauniya dangin matsafa ki zo Hajiya na kiranki.” Daga haka ta fice bayan ta yi wurgi da remote din har yana dukan k’afar Ummi. Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da nuna damuwa ba ta dubi Binta. “Ina zuwa.” Binta ta yi kwafa. “Wallahi da ni ce ke Ummi sai na gayawa yar banza bak’ar magana, bansan sadda Ikram ta 6aci haka ba. Wallahi ki daina ragamata, ya dace ki dunga kwatarwa kanki ‘yanci, ko babu komai yayanta za ki aura.” Ummi da har lokacin bata bar murmushi ba ta ce. “Meye duniya? Wataran don kanta za ta gaji ta bari.” Binta ta ja tsaki. “Ai ke daman hakurinki kusan ma ince ya yi yawa, ba fa komai za ki zuba ido ayimiki ba wannan raini ne.” Ummi ta yi hanyar fita tana fadin. “Gwara dai na tafi kada na yi laifi.” “Je ki dawo ranki ya dade!” Ta karashe cikin zolaya, itama Ummin tana jinta bata tanka ba bayan dariya da ta danyi. A falon sama ta tarar da Hajiya, agefenta wasu atamfofi ne da leshi. Sai wata mace wacce daga gani ba bahaushiya bace zaune a can gefe. Bayan ta gaishesu ne, Hajiya ta bata umarnin zuwa ga matarnan. “Hafsa aunata.” Wacce aka kira Hafsa ta amsa da gur6atacciyar hausarta sannan ta shiga auna Ummi bayan tasa ta cire hijabin jikinta. Saida ta gama sannan Hajiya ta bata umarnin tafiya, haka ta koma daki jiki duk a sanyaye, wato har dinkuna zaayi mata. A kwanaki uku kuwa sai ga Hafsa da dinkuna kala goma kala-kala. Atanfa biyar leshi biyu sai wasu yadi guda biyu. Ta rasa bakin godiya tsabar murna, Hajiya kam ta sha addua har saida ta dakatar da ita da fadin”Yiwa Kai ne.” A ranar kuma ta hadata da. Ikram don ta zuwa siyo kayan undies da na shafa. Jin da Ikram ne Faruk ya kira wayar Ikram ya yi mata gargadi da babbar murya don tun a daren da Hajiya ta sanarmata ta ke faman cika da batsewa, ya tabbatar mata ya lura da hakan. Hakan da ya yi sai ya samawa Ummi lafiya, Ikram na dawowa daga makaranta suka wuce. Har gaba ta ke yi wai don kada su jera da Ummin don ta lura sai wani d’ar-d’ar Ummin ta ke na rashin sabo da shiga ire-iren wajen da sai dan wane ko wance. Don mugunta babu abinda ta za6ar mata saita barta da za6in wannan yasa Ummi ta d’ibi undies kala bibbiyu, a 6angaren shafa ma ta rasa kalar da ya dace kawai sai ta dauki wani(Cream) da batasan ko na menene ba, hoda ma ta dauki daya sai janbaki da jagira, daganan Ikram ta fiddo kudi masu yawa ta ciri adadin abinda Ummin ta dauka ta biya suka tafi babu mai yiwa wani magana. Ummi gaba daya sai ta ji tausayin kanta, wane irin rayuwa ne haka za ta yi cikin mutanen da suka fi ta? ‘Allah Ka dafamini.” Ta fad’i a ranta.1 Yana kwance yasa filo tsakaninsa da mahaifiyartasa sannan ya dora kansa saman filon suna ‘yar hira akan ginin gidansa wanda ya yanzun ya yi nisa sosai. A haka suka yi sallama suka shigo, ya lumshe ido jin muryar abar kaunarsa kafin ya bude ya kai idanunsa gareta. Bata ko kalleshi ba saboda idon Hajiya dake kansu, ya mike zaune gami da rungume filon kujerar a kirji. “Wash! Sannunku da gida.” Cewar Ikram, itama Ummi ta gaishesu. Sannan ta mike don zuwa gabatar da Magriba don a hanya ta yi musu. Kasancewar Ikram na fashin sallah, ta dakata gami da budewa Hajiya ledar kayayyakin kamar yanda ta buk’ata. Tun ganin kayan Faruk ya daure fuska, ya yi shiru yana jiran abinda zai fito daga bakin Hajiya. Ita dinma fuska ba walwala ta dubi Ikram. “Menene wannan ki ka kwaso kuma? Wannan cream din nasa haske fa?” Ta girgiza kai. “Ita fa ta za6i abinta wallahi, bari na yi ta za6i abinda ranta ke so.” Suna hada ido da Faruk ya watsamata wani mugun kallo da ya yi sanadin kadawar yan hanjin cikinta, ta daure ta kauda kai. Baice komai ba, yana ji Hajiya ta hauta da fad’a sosai akan wannan ba daidan ba da ta yi mata. “Haka na sanyaki? Bance ki za6omata ba? Ko don kinsani ita din bawani za6e zata yi ba?” Gogan waya ya hau dannawa abinsa yana mai nazari, amma kwarai Ikram ta rainashi, wannan ba Ummi ta raina ba, shi ta raina. “Ai dole sai kin koma gobe…” “Is ok Hajiyata, ki yi hakuri.” Ya katse Hajiya da ke faman sababi, ta mike ta wuce sashen Daddy daman yana nafilfilu shiyasa ta zauna nan. Bayan fitarta ya dubi Ikram. “Tashi muje.” Ta kasa motsi ta hau ba shi hakuri, ya dakamata tsawa. “Na ce ki tashi!” Ba shiri ta mike shima ya mike tsaye ya nufi dakin Ummi, tana zaune saman darduma mai taushi ta idar da salla tana addua, saida ya jira ta kammala sannan ya bata umarnin ta taso. Ba tambaya ta bi bayansa sanye da hijab ajikinta. Tare suka fice bayan ya sanarwa Hajiya ta waya, gudu kawai ya ke shararawa a saman kwalta, har suka isa wani katafaren boutique wanda duk Abuja babu irinsa indai a fannin saida kayan amfanin mace ne. Haka ya shiga ya lodowa Ummi kayayyaki masu matukar kyau da tsada wanda Ikram zata iya rantsewa ita kam bata ta6a amfani da irinsu ba, saidai ta yi ta burin ta siya. Jikinta ya yi sanyi tana kallo takalma kala-kala da kananun kaya masu kyau da tsada amma babu halin ta ce ya siyamata. Ta k’ulu matuka, wato don ya ramawa Ummi ya yi mata haka kamar ba kanwarsa ba, saida ya gama jidar son ransa har da abaya kala uku da kayan shafe-shafe masu kyau da gyara fata sannan ya biya ta hanyar Atmcard dinsa. Haka aka loda kayan a boot wasu a gefen Ikram da ke zaune bayan mota sannan suka tafi, a hanya ma sai jan Ummi da hirar soyayya ya ke tana kakkaucewa, wani abin kuma ya sanyata dariya. Wannan ya k’ular da ikram matuka. Hajiya ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da Faruk ya siyo saidai tasan don an 6ata mishi ne, yasa Ikram ta shigar mata da su daki, kamar ta yi kukan wannan abu haka ta yita kwasa tana shigarwa. Ya shigo har dakin ya tsaya bayan komawar Hajiya sashen Daddy, ya umarceta da ta jeramata na shafar a gaban madubi, tana hawaye tana yi, Ummi na zaune bata so hakan ba saidai ya hanata motsi, asalima zama ya yi gefenta ya soma nunamata wasu hotunanta a wayarsa da ya dauka batare da saninta ba, soyayya dadi, nan ta mance da wata Ikram, saida ta juyo ta ganta ne yasa ta dan janye daga hirar. Bayan ta kammala yasa ta jera takalman harda su abayoyin da sauran kananun kayan na shigar mutunci a kwaba. Faruk bai bar dakinnan ba saida ta shirya komai tsaf sannan ya dubeta. “Get out now.” Ya fada gami da maida dubansa ga abar kaunarsa, ta dubesu suna hada ido da Ummi ta watsamata harara sannan ta fice tana goge fuskarta. “Da ka barshi wallahi zanyi Yaya Faruk, ba ka gudun janyomin bak’in jini?” Ya daga kafada. “Sun jima basu yi ba, karki damu kanki ai kin wuce haka a wajensu, kannenmu ne fa.” Ta yi murmushi kawai can kasan ranta damuwa ce fal, ta lura shi ko a jikinsa, dakyar ta korashi kada Hajiya ta ganshi. Ya fice yana dariya ta bishi da kallo tamkar ta hadiyeshi don so. *** *** *** KANO

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *