DAN ADAM CHAPTER 21
a hadiyeshi don so. *** *** *** KANO Ranar litinin ya kama na tafiyar Adnan, ranar ne su Rahila da Aisha suka zo gidan. Suna zaune a dakin Mami su duka banda Adnan sai kuma Mamin dake labartamusu batun auren Ummi da Faruk. Salati su Rahila suka shiga yi. “Tabdi! Ni narasa ma yanda zan fassara wannan lamarin? Wallahi karki sake ki yarda a had’a darajarki da wata can wacce ba komai ba. Anya haka Ummi ta barsu?” Rahila ke maganar cikin 6acin rai. “Wallahi nima ina tunanin da walakin, goro a miya. Amma don Allah ku yi tunani, ta ya ya Yaya Faruk zai so Ummi har ma wai ace son aure ya ke mata? Na yarda yarinya ba laifi ta hadu saidai anya kuwa ba zaa bawa Hajiya Babba shawara akan dagewa da rok’on Allah ba? Nikam wallahi ina tantama idan bawan Allahn nan cikin hayyacinshi ya ke.” Ta k’arashe cikin jimami, Ihsan na jinsu saidai takaici ma ya sa ta kasa cewa komai. Mami ta ta6e baki. “Su suka sani, idan aure ne suyi ta yi, munanan sai ta auri wanda yafi Faruk din kud’i in sha Allah.” Haka sukayita tofa na bakinsu, ko kusa Mami bata sanarmusu da sa’insar da ta shiga tsakaninta da Hajiya Mama ba. Sai a ranar ma ta daure ta amsa wayar Hajiya Babba, ta kuma fadamata cewar Ihsan kam ta hakura da Faruk akwai wanda ke sonta. Hajiya Babba gaba daya ta fahimci Madina fushi ta yi, ta nunamata hakan ma karin dankon zumunci ne idan akayi. “Kenan za’a fasa da Ummi ya aureta ita kadai?” Hajiya Babba daga can ta dan yi shiru, ina ita ina yiwa Sadaukinta wannan gangancin? “A’a Madina, menene idan ya auresu duka? Ina ce shi ya ga zai iya?” Mami ta yamutse fuska ta ji haushin maganar sosai. “To Ihsan dai ta dawo kuma ta tabbatar min matukar ba ita kadai zai aura ba to bata son auren.” Hajiya Babba ranta ya 6aci, wannan son kai ne kawai. “Amma Madina kin ban mamaki, menene ciki…” “Don Allah Hajiya ke babba ce, ina ganinki da girma, na gayamaki raayin ‘yata tunda bazai samu ba hakan to don Allah ki samamin lafiya, aure kuma idan ana daurawa sau dari a daura na Faruk da Ummi.” Daga wannan ta kashemata waya. A daren Adnan ya tafi, koda suka hadu da su Rukayya a(airport) hankali kwance suka gaisa yanda suka saba don babu wanda yasan wani abun, sun yi hotuna har Adnan na hawaye suna tayashi, haka suka yi bankwana cike da jin kewar juna. Hajiya Mama na zaune a falonta tana kallo, yayinda Amina ke gefe daga kicin tana 6arar tafarnuwar girkin rana, yaran gaba daya sun wuce makaranta. Lokacin karfe sha daya na rana. Wayarta ta dauki kara, Hajiya Babba ce, gabanta ya fadi, to har yaushe ne za ta yi ta 6oyon wannan lamari ga yayartasu? Ta rage k’arar talabijin ta dauka. Bayan sun gaisa Hajiya Babba ta jefomata tambaya. “Sadiya ya za ki 6oyen gaskiyar yanda ku ka yi da Madina?” Hajiya Mama ta gyara zama, shikenan fa ranar da ta ke gudu ya zo don jin muryar Hajiya Babba ta yi duk a sanyaye. Kafin ta nemo abin fadi Hajiya Babba ta zayyane mata yanda suka yi da Madina ta waya. Ran Hajiya Mama ya 6aci. “Bata isa ba wallahi ta yi kadan, auren Faruk da Ummi saidai ikon Allah ne kadai zai sa a fasa shi, Madina ta raina mutane. Hajiya kada ki soma yarda da wannan banzan maganarnata, itace sama da mu ne?” Cikin damuwa Hajiya Babba ta ce. “Sadiya zumunci nake dubawa, da dai Madina za ta yarda da tsarina da nafi kowa jin dadi.” “To Hajiya tunda ta nuna mana iyakarmu ba sai mu fita hanyarta ba? Ko ita ce ta haifemu?” “Hannunka bai ru6ewa ka yanke ka yarr Sadiya. Bari dai zan duba na gani, idan na samu zuwa Kano a satinnan zan zo mu hadu a tattauna.” Hajiya Mama bata so hakan ba sai don dai Hajiya Babbar ta dage akan hakan ne, dole ta amince suka yi sallama akan hakan. Amina dake kicin mutuwar tsaye ta yi jin an ambaci wata kamar Ummi kuam wai da Yaya Faruk aure. Anya kumnuwanta sun jiyemata daidai? Sai kuma ta ji Hajiya Mama na faman surutai tana fadin. “Ai ba ita ta haifemu ba, a da Ummi ke yar aiki amma yanzu yarinya ta tashi anan, sai ta hada diyartata kishi da yayan masu da shi, shegantaka kawai.” Batasan lokacin da ta bar abinda ta ke ba tana salati, ta dafe kai don tsananin kaduwa, ji ta ke kamar ta saki fitsari anan, haka Ummi ta yi? Ina shawarar da ta bata? Shikenan ta kawo rarrabuwar kai acikin zuri’ar nan. Hawaye ta ji ya soma zubomata, inama tana da hanyar da zata bi ta samu Ummi koda ta waya ne su yi magana, anan kam babu abinda za ta ji sosai. ‘Ba ki yiwa kanki dabara ba Ummi, ba ki kyautawa rayuwarki ba.’ Ta fad’a a ranta cike da tausayin Ummin, kokisa bata son abinda zai ta6ata, ita mamakin ma karfin halinta ta ke yi na yanda ta iya bari suka kai ga haka da Faruk wai magana har kunnen iyaye? Sai kuma ta tuna abin na Allah ne, idan Ya yi babu mai iya hanawa. Ta sauke ajiyar zuciya. ‘Allah Ya kauda dukkan fitinu. Ya yi miki za6i na alheri a rayuwa.’ Daga nan ta cigaba da aikinta bayan ta je ta rage marar, yinin ranar cikin sanyin jiki ta yishi, tunaninta ko wane yanayi Ummin ke ciki a Abuja? Tasan dai ba kowa ne zai so aurennan ba. *** *** *** BAYAN SATI DAYA ABUJA+ Ummi an soma gogewa, fatarta fara ta kara haskawa sai sheki da wani sul6i da jikinta ke k’arawa, hakanan har wata ‘yar k’iba ta yi, Ikram kadai ce matsalarta sai kuwa Baraka da matar Babban Yaya(Fadila) da Jidda idan sun zo. Su dinma a fili suke nuna rashin goyon bayansu. Wannan abu na yi mata zafi saidai fad’an da ya fi karfinka….! Hajiya Babba ta bi jirgi zuwa Kano ita kadai tun ran alhamis, gidan ya rage daga Ikram sai kuwa su din. Ranar Asabar misalin biyar na yamma Ummi zaune acikin (garden) tana sauraron wakokin hausa a waya wadanda Binta ta aikamata su da yawa, sanye take cikin wata atamfa ruwan madara mai adon fulawoyi, fuskarta fayau sai hoda da kwalli da ta sanya, kadan-kadan ta ke motsa lilon ta kwantar da kanta saman lilon idanunta a lumshe tana mai jin dadin wakar da ta ke bi na Alan waka na (Ummina). A hankali kuma hawaye suka soma zuba saman fuskarta, ta k’ara gyara zaman (earpiece) din kunnenta. Daidai lokacin da Faruk ya shigo gidan, dawowarsa kenan daga nan makwaftansu wajen wani dan makocinnasu mai mutunci da bai ji dadin jikinsa ba, kasancewar sun saba haduwa duk weekend yawanci anan kofar gidan su gaisa yasa koda ya ji ba shi da lafiya ya yi yunkurin zuwa dubashi. Yana sanye da riga koriya da wandon jeans bak’i, kai tsaye hanyar cikin gidan ya yi saidai idanunsa ya hangomasa sanyin idaniyartasa zaune saman lilo, ya dan kuramata ido duk a zatonsa ma bacci ta ke yi a hakan ganin yanda ta lumshe ido, ya taka a sannu ya karasa gareta, sai lokacin ya lura da(earpiece) dake a kunnenta ga kuma hawaye da ta ke zubarwa. Zama ya yi gefenta kamshi na turarensa ya ankarar da ita zuwansa. Da sauri ta bude idanunta gami da sa hannu ta share hawayenta, duk yana kallo saidai baice komai ba hannu yasa ya ciro kunne daya yasa a kunnensa, ya yi shiru yana nazarin wak’ar kafin kuma ya cire daga kunnensa yana mai dubanta, ta maida hankali ga wayar don kashe wakar. “Kina tunawa da Ummarmu ne?” Ta kasa magana sai gyada kai. Ya sauke numfashi. “Hakan yana da kyau, saidai ba kukanki ne abin so awajenta ba, addua ya kamata ki yi mata idan har kina son ta yi farinciki da ke. Duk wanda ya mutu yafi bukatar adduarmu sama da komai.” Ta gyada kai. “Hakane.” “Allah Ya jikanta.” “Amin.” Shiru ya dan biyo baya. “Ni kuwa Ummi kin ta6a ganin hoton Ummanki?” Ta girgiza kai, wannan ma na daya daga cikin abinda ke sosa ranta muddin ta tuno. “Ko a hoto bansanta ba, nasan dai muna kama ta bakin matar babana shima sai tana zagina ta dunga hada yanayina da ita sai ko makwafta da zan ji suna fadin kamarmu da ita.” Ya jinjina kai. “Allah Sarki. Kenan babu wani nata da ki ka ta6a gani?” Ta amsa da eh. Shiru ya biyo baya kafin kuma ya ce. “Bayan wuya sai dadi in sha Allah, wataran za ki zama abin so da alfahari wajensu.” Ta yi murmushi don har cikin ranta ta ji dadin maganar. “Allah Yasa.” “Amin.” Sun jima suna yar hira tana amsawa a kunyace kafin su mike su shiga ciki. *** *** *** KANO Hajja ta dubi Fatima babbar diyartata da kulawa. “Ke kam menene haka mai muhimmanci da ya taso ki daga Abuja zuwa Kano, maimakon ki bari tunda sati na sama ne zaayi taron zuri’a (family meeting) ku taho gaba daya da yara?” Hajiya Babba ta murmusa, kwananta biyu kenan da zuwa amman kullum sai Hajja ta yi mata korafin zuwannata don gani ta ke yi kamar wata matsalar diyartata ta samu da maigidannata. “Ke kam Hajja ba wani abin bane ba fa, daga zuwa ganinku duk kin bi kin damu kanki da tunani.” “A’a to, gani na yi ba ki saba wannan zuwan haka ba.” “To ke tunda kinsan bata saba ba, ai kinsan banza bazai kawota ba, akwai wani abun, bari yan uwannata su zo ko menene sai mu ji.” Cewar Dattijo Modibbo mahaifinsu. STORY CONTINUES BELOW Jin haka Hajja ta rausaya kai. “Ai shikenan na bari.” A karshe ma suka shiga wata maganar inda Modibbo ke fadin ya dace ma su kai ziyara Adamawa don sun jima basu je ba, ya ce idan anyi zaman taro zai fad’a. Sai bayan Azhar Hajiya Mama ta iso ita daya sai autarta Mufida. Bayan an gaggaisa suka zauna hira da zaman jiran Mami, ba ita ta zo gidan ba sai yamma. Nan din ma ta zo ne tana daure-dauren fuska, ko kallon inda ta ke Hajiya Mama bata yi ballantana wata gaisuwa ta shiga tsakaninsu. Sai lokacin Hajja ta fahimci akwai matsala. Bayan sun zauna har mahaifinnasu, Hajiya Babba ta zayyane batun auren Faruk da Ummi da kuma maganar Ihsan kaf ta fadawa iyayen, sai kuma Hajiya Mama ta dora da yanda suka yi da Madina a gidanta. Shiru ya biyo bayan gama saurare, can kuma Modibbo ya yi maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raajiun har sau uku. “Hakika shaidan ya so shiga tsakaninku, ina nema muku tsarin Allah daga sharrinsa.” Ya dan yi shiru kafin ya dora. “Kin bani mamaki Auta, kinyi abinda ban ta6a zatonki da aikatawa ba, da ace wani bare ne ke sanarmin kin yi wannan gagarumin laifin da babu ta yadda zan amince da hakan. Karki manta cewar Aure shi kaddarar Ubangiji ne, idan Allah Ya kaddarowa shi Farukun da ita Ummi aure, to babu mahalukin da zai chanja yin Allah, hakazalika idan kaddararsa ce aurensu su biyu duka, nan ma duk wani tashin hankula da zaayi zai je ya dawo ne ba fa zaa fasa abinda Allah Ya shirya ba.” Shiru ya dan biyo baya, Mami ji ta ke yi ranta na zafi, wato iyayensu ba su ga hadin da ake so ayi na diyarta da yar aiki ba? To wai ma Faruk kadai ne namiji da har zaayita takurawa akansa? Modibbo ya cigaba da yi mata nasiha don ba shi da zafi sosai, ita kuwa Hajja shiru ta yi, wannan fadan da ake yiwa Madina yafi komai yi mata zafi, tana ji da yar autarta ta. Bayan Modibbo ya kai aya ta soma magana a fusace. “Nifa banga laifin Madina ba yarinyar nan da gaskiyarta. Ke banda rashin wayo da girman kwabo ki rasa da wacce za ki had’a dangantaka saida yarinyar da bakisan komai game da ita ba, ‘yar asali ce, shegiya ce, oho! Duk ba daya da ki ka sani,duka-duka ko wata uku bata cika ba inace tare da mu, kece kuma har da marin kanwarki saboda…” Tsawar da Modibbo ya dakamata ne yasa ta yin shiru tana kwafa, zuciyarta na tafarfasa kamar ta rufe Fatima da Sadiya da duka haka ta ke ji. “Ke meyasa baki da tunani ne? To ko fita idona tun ban sa6amiki ba wallahi! Kina ganin ana kokarin gyara lamari ke kuwa kina neman ki k’ara dagula shi? Ko an gayamaki shi Amadun ba shi da hankali da ba zai yi bincike ba kafin hada zuria da su? Haba!” Ya juya ga yarannasa kafin ya kai ga magana Mami ta soma. “Ka yi hakuri Baffa, amma don Ihsan ita ta hakura, mahaifinta ma ya yi mata miji bata sani ba.” Ta fadi hakan don ma kada ya ce lallai hakan zaayi, Modibbo ya so fahimtar kawai ta fada ne saidai ya yi tunanin barin mutum da halinsa, ya jinjina kai ransa baiyi mishi dadi game da wannan sa6ani da aka samu ba tsakanin yaransa wadanda ya ke alfahari da su wajen kokarin zumunci da hadin kai. Haka dai aka rabu ran kowa babu dadi. Hajiya Babba kuwa ji ta yi kamar ran lahadi ta bi mota ta bar garin Kano sakamakon Hajja da ke ta jifanta da bakaken maganganu marasa dadi, daman Hajja ta na da fada idan an ta6ota musamman idan aka ta6a autarta. Ranar litinin kuwa jirgin safe Hajiya Babba ta bi zuwa Abuja zuciyarta a cunkushe, saukinta ma ta samu goyon baya wajen mahaifinnasu inda ya ce kuma ta dage nemawa dannata za6in Allah, Allah ba Ya bacci, Shi Mai amsawa ne. Da wannan hankalinta ya dan kwanta, itama Hajiya Mama ta jaddadamata ta kwantar da hankalinta, karon kanta Mamin zata zo ta gano kuskurenta, wannan zamanin namiji mai rikon aure sai an auna, tana kyautata zato akan Faruk. Madina zata yi da na sani acewarta. *** *** *** RINGIM Salati Habiba ta shiga yi tana kallon Saude wacce ta shigo a rude ta zubar da Mariya akan kujera tana rusa ihun kuka sakamakon maganar da wata makwafciyarsu ta kawomata akan ta sanya ido akan yarinyarta don ta ganta sun shiga wani lungu da Dauda fitinannen d’a ga Zinaru itama makwafciyarsu, wannan dalilin yasa ta duba diyar ta tabbatar ana amfani da ita. “Kingani ko? Daman na sha kwa6arki akan sakacin da ki ke na barin yarinyar nan tare da wannan yaron, itace har shagon Usi mai kanti, yanzu ga irin ABIN DA AKE GUDU!” Ita dai Saude ba bakin magana, don cuta an gama cutarta diyarta kenan daya a duniya, tana ji da ita ta kuma ci buri akan aurenta idan ta girma don yanzu duka-duka shekarunta bakwai a duniya. “Ba kuka ya kamace ki ba, mu lalla6a mu kaita asibiti a aunata ko tana da cutar kanjamau, idan babu duk sauran mai sauki ne.” Suka dunguma zuwa asibiti, anci sa’a bata da cutar saidai ciwon sanyi da ya yi mata yawa a jiki, likitan ya tabbata musu ana amfani da yarinyar, abu ne da suka riga suka sani, ya nemi yardarsu a yi mata dinki suka k’i acewarsu sunsan yanda zasuyi. Daga asibiti suka wuce wajen bokanya nan ta hadamusu magunguna, anan kuma Habiba ta je da batun matsalar Dija da Raihana, Bokanya ta ce zata yi aiki akai. Haka suka wuce ran kowannensu ba dadi, Saude ta so zuwa gidan Zinaru ta zagesu tas saidai Habiba ta kwa6eta gami da nunamata wannan tonon silili ne don wanda bai sani ba ma zai iya sani. Basusan cewa ba, mutanen gari sunsha tarar Malam Balarabe akan ya saka ido akan diyarsa, anan kuma Saude idan ta ga ya hana diyar fita ta nunamishi bai isa ba. Daman yasan shi din ba shi da wani kata6us a gidan, yan uwansa ma an rabashi da su, ba wanda ke takowa Ringim da zummar ganinsa tun bayan rasuwar Yayar Malam Balaraben da ta rik’eshi, itama har ta mutu bata ta6a haihuwa ba. Daman iyayen na Malam Balarabe sun rasu da “Ke meyasa baki da tunani ne? To ko fita idona tun ban sa6amiki ba wallahi! Kina ganin ana kokarin gyara lamari ke kuwa kina neman ki k’ara dagula shi? Ko an gayamaki shi Amadun ba shi da hankali da ba zai yi bincike ba kafin hada zuria da su? Haba!” Ya juya ga yarannasa kafin ya kai ga magana Mami ta soma. “Ka yi hakuri Baffa, amma don Ihsan ita ta hakura, mahaifinta ma ya yi mata miji bata sani ba.” Ta fadi hakan don ma kada ya ce lallai hakan zaayi, Modibbo ya so fahimtar kawai ta fada ne saidai ya yi tunanin barin mutum da halinsa, ya jinjina kai ransa baiyi mishi dadi game da wannan sa6ani da aka samu ba tsakanin yaransa wadanda ya ke alfahari da su wajen kokarin zumunci da hadin kai. Haka dai aka rabu ran kowa babu dadi. Hajiya Babba kuwa ji ta yi kamar ran lahadi ta bi mota ta bar garin Kano sakamakon Hajja da ke ta jifanta da bakaken maganganu marasa dadi, daman Hajja ta na da fada idan an ta6ota musamman idan aka ta6a autarta. Ranar litinin kuwa jirgin safe Hajiya Babba ta bi zuwa Abuja zuciyarta a cunkushe, saukinta ma ta samu goyon baya wajen mahaifinnasu inda ya ce kuma ta dage nemawa dannata za6in Allah, Allah ba Ya bacci, Shi Mai amsawa ne. Da wannan hankalinta ya dan kwanta, itama Hajiya Mama ta jaddadamata ta kwantar da hankalinta, karon kanta Mamin zata zo ta gano kuskurenta, wannan zamanin namiji mai rikon aure sai an auna, tana kyautata zato akan Faruk. Madina zata yi da na sani acewarta. *** *** *** RINGIM Salati Habiba ta shiga yi tana kallon Saude wacce ta shigo a rude ta zubar da Mariya akan kujera tana rusa ihun kuka sakamakon maganar da wata makwafciyarsu ta kawomata akan ta sanya ido akan yarinyarta don ta ganta sun shiga wani lungu da Dauda fitinannen d’a ga Zinaru itama makwafciyarsu, wannan dalilin yasa ta duba diyar ta tabbatar ana amfani da ita. “Kingani ko? Daman na sha kwa6arki akan sakacin da ki ke na barin yarinyar nan tare da wannan yaron, itace har shagon Usi mai kanti, yanzu ga irin ABIN DA AKE GUDU!” Ita dai Saude ba bakin magana, don cuta an gama cutarta diyarta kenan daya a duniya, tana ji da ita ta kuma ci buri akan aurenta idan ta girma don yanzu duka-duka shekarunta bakwai a duniya. “Ba kuka ya kamace ki ba, mu lalla6a mu kaita asibiti a aunata ko tana da cutar kanjamau, idan babu duk sauran mai sauki ne.” Suka dunguma zuwa asibiti, anci sa’a bata da cutar saidai ciwon sanyi da ya yi mata yawa a jiki, likitan ya tabbata musu ana amfani da yarinyar, abu ne da suka riga suka sani, ya nemi yardarsu a yi mata dinki suka k’i acewarsu sunsan yanda zasuyi. Daga asibiti suka wuce wajen bokanya nan ta hadamusu magunguna, anan kuma Habiba ta je da batun matsalar Dija da Raihana, Bokanya ta ce zata yi aiki akai. Haka suka wuce ran kowannensu ba dadi, Saude ta so zuwa gidan Zinaru ta zagesu tas saidai Habiba ta kwa6eta gami da nunamata wannan tonon silili ne don wanda bai sani ba ma zai iya sani. Basusan cewa ba, mutanen gari sunsha tarar Malam Balarabe akan ya saka ido akan diyarsa, anan kuma Saude idan ta ga ya hana diyar fita ta nunamishi bai isa ba. Daman yasan shi din ba shi da wani kata6us a gidan, yan uwansa ma an rabashi da su, ba wanda ke takowa Ringim da zummar ganinsa tun bayan rasuwar Yayar Malam Balaraben da ta rik’eshi, itama har ta mutu bata ta6a haihuwa ba. Daman iyayen na Malam Balarabe sun rasu da jimawa. *** *** *** KADUNA… Lamura sun ca6ewa Dija tun ranar da Raihana ta yi mata waya akan tana nan zuwa, ta fahimci dukkan wani abu da su ke yi don a rabasu ya ci tura hakan bai samu ba, ranar da Deen ya koma dakin Munira a ranar Raihana ta zo. Da shirinta ta zo wajenta don kuwa wani shegen kwalli ta sanya a idanunta da yasa Dija kasa yi mata musu a dukkan abinda ta ce, ga wani dan iskan turare mai saukar da shaawa. A wannan ranar Raihana bata bar gidan Dija ba sai dare, Dija kuwa saidai ace Allah Ya kwatota don kuwa tuni ta fada tarkon shaidaniya Raihana. Tun daga ranar suka kara shak’uwa ta waya, har Raihana ta yi zuwa biyu gida, mutan gidan ba wanda ya ta6a kawo munin abu irin wannan a kansu saidai sun shaida Raihana ba ta yi kalar nutsastsun mata ba. *** *** *** KANO Ihsan ta yi tsai tana duban hoton saurayin da Maminta ta bata, babu laifi kyakkyawa ne kuma bak’i, yana da ‘yar kiba. Ta numfasa, ba wai ta ji sonsa a ranta ba, kawai dai ya kai yanda zaa iya auren huce haushi da shi. “Dan wani babban abokin Abbanku ne dake Adamawa, mahaifinsa babban Injiniya ne, Alhaji Kabir Jimeta.” Ihsan ta ajiye hoton a gefe. “Yana da d’a Abubakar?” Cikin dariyar mamaki Mami ta ce. “Ashe kin sanshi ma, ai shine wannan din.” Ta dan ta6e baki. “Yana da kirki, muna chatting da shi ai saidai ban sanshi a hoto ba, ya sha gwada yana sona saidai ni ce ban ba shi fuska ba.” “Ai kuwa ya zama dole ki so shi, kin kuwa san matakin arzikinsa yanzu a Adamawa? To ana sanyashi cikin goman farko na yara matasa masu kudin garin sannan kalleshi da kyau ba shi da makusa a halitta.” Ihsan ta danyi jim, kafin ta ce. “Yana da mata fa Mami.” Tsaki Mamin ta ja, ta soma fusata da lamari na diyartata kuma. “Shikenan sai ki zauna jiran aurenki da Faruk ki yi kishi da wacce bata kai ba, ni wallahi bansan irinki ba, ina ruwanki da matarsa? Matarsa gogaggiyar yar boko ce kuma bata ta6a haihuwa ba da shi, shi kuwa ba shi da burin da ya wuce na ganin ya haihu a duniya. Idan ki ka haihu da shi tabbas mun warke, kada ki bar wannan dama ta wuce mu. A zamanin nan samun matashin da ba shi da aure kuma mai rikon aure sai an tona, gwara ki auri wannan da kowa ya shaida kyawawan dabi’unsa.” Haka Mamin ta yi ta kod’a Abubakar a wajen ‘yarta, ita Ihsan har mamaki ta ke yanda uwar ta sanshi haka, sai kuma ta tuna sunan mahaifiyarsa da ta ambata, wato Hajiya Salma kusan tare suka tashi da Mamin a Kano, aure ya rabasu. Dole Ihsan ta amince da hakan, saidai abinda ta kasa sanar da Mamin shine, Abubakar ya sha janta da hirar da bata dace ba tana k’in ba shi fuska, hakan yasa ma dangantakarsu ta yi tsawo. Ai kuwa kamar jira Mamin ta ke, Abba na dawowa ta tare shi da zancen, ya ji dadi matuka don kuwa acewarsa daman Alhaji Kabirun ya ta6a neman tayin hakan tun akan Aisha saidai Allah baiyi rabon dannasa bace, yanzu kuwa yasan zai ji dadi idan ya kasance da Ihsan, daman burinsu a k’ulla zumunci. Kwana biyu da yin hakan Alhaji Muhammad ya yi magana da abokinnasa. “Kamar kuwa kasan ina kan ga6ar nemarwa dan nawa aure, ina burin ganin jikokina, fatana Allah Yasa idan anyi hakan mafarkina ya tabbata.” Nan suka sasanta magana inda Alhaji Kabiru ya tabbatar mishi cewar cikin(weekend) zai zo tare da dan nasa don su ga juna. Da wannan suka ajiye wayar ran kowa ya yi dadi. Bayan Abba ya ajiye ne ya dubi Mami. “Kinga cikin ikon Allah sai a had’a auren harda na Iklima, itama ta tsaida yaron nan dan gidan tsohon kansila, Mu’azzam. Itama Hussainar ba barinta zan yi ba, lokaci guda zan aurar da su idan Allah Ya yarda, da zarar sun kammala wannan ajin, ba don ma yaron ya ce sai ya gama gini ba, da sai a soma na Iklimar.” Mami ta gyada kai, ranta baiso ba, ta so ya zamana ba za’a hada auren diyarta ta da na kowa ba, ko don a fi ganin kalar bajintar da zata yi. Amman ta riga ta saba da binshi yanda yaso. “Hakan ma ya yi, Allah Yasa ayi muna raye.” Ya amsa da amin cikin jin dadin sha’ani na uwargidan tasa wanda ya sha bamban da Hajiya Binta, da ita ce sai sun kai ruwa rana, gwara-gwara Hajiya Luba, itama akan yi abin arziki da ita idan kishinta bai motsa ba.