DAN ADAM CHAPTER 36
Meyafaru?” Ta fada cikin sanyin muryarta, ya dagamata gira yana mata murmushi. “Zo nan.” Ba musu ta ajiye robar furarta ta mike ta nufi inda ya ke gami da zama a gefensa, sanye take cikin riga iyaka gwuiwa da dogon wando(tight). Ya janyota jikinsa. “Gaba daya kin chanja, anya babu ajiyata anan?” Ya karashe yana mai kai hannu cikinta gami da shafa. Ta yi shiru, ita daman wata nada sati daya ta tare a gidan yanzu gashinan har watan ya cinye bata ga komai ba. Ya zungureta. “Answer me.” Ta shagwa6e fuska. “Nidai bani da komai.” Ya yi murmushi. “Anya kuwa? Ji fa yanda ki ka k’ara girma a komai.” Ta lumshe idanu jin yanda ya kasa tsayar da hannunsa wuri guda, da sauri ta zame ta koma gefe tana fadin. “Kai FAR HAS abinci fa ka ke ci.” Ya yi mata duban rashin fahimta. “Af, kinga na manta ko? Inason tambayarki ma’anar wannan FAR HAS din na manta.” Dariya ta yi wacce ke burgeshi, bai iya 6oyewa ba saida ya furta, don Faruk sam bai iya 6oye abinda ya yi mishi, ko girki ta yi sai ya yaba balle idan idan ta ci ado, hakazalika duk sadda ya shigo gidan sai ya yaba da gyaranta, wannan ba karamin kara mata sonsa ya ke ba, babu macen da batason a yabawa kokarinta, wasu mazan nasu tunanin su kadai zasuyi ana yabawa, su ba zasu yaba naka ba, basusan cewa yabo na kara soyayya tsakanin maaurata ba, koda ta yi ba daidai ba idan ka fada bazata ji haushinka ba saboda tasan ka yabawa kokarinta kafin haka. “Har kullum bana gajiya da ganin dariyarki.” Ta rage dariyar tana murmushin jin dadin kalamansa. “Nagode FAR HAS.” Ta fada cike da zolaya, ya basar gami da maida kansa ga faranti yana murmushi. Bai kara magana ba hakanan itama kowanne na bawa cikinsa, ita kuwa saida ta shanye robar fura tas. Lokacin shima ya kammala cin abincin ta dauke kwanukan sannan ta dawo ta zauna kusa da shi kamar yanda ya nunamata yafi bukata idan suna zaune. Ya ja yatsun hannunta. “Fadamin ma’anar FAR HAS.” Ta saki k’ara kad’an kafin ta turo baki. “A kyauta?” Ya na murmushi ya girgiza kai. “Fad’i bukatarki.” Ta kanne ido daya. “Gobe a karomin fura.” Ya janyota ta yi filo da cinyarsa. “Mai sauki kenan daga abinda za ki samu, just tell me.” Ta lumshe ido tana murmushi. “Faruk da Hasiya nake nufi.” Sai lokacin ya dan tsaya nazari kafin ya dubeta da mamaki ya na murmushi. “Sunan ya burgeni ya kuma ban mamaki ta yanda har ki ka yi tunanin hadawa.” Ta rufe ido da hannu tana murmushi. Ya sunkuyo da fuskarsa zuwa nata….! *** *** *** KANO Kwance ta ke tana duban hotunan da suka shigo wayarta ta (whatsapp) don bisa al’adarta duk dare idan ta gama komai sai ta bibiya ta ga ko akwai wadanda basu dace ba ta goge, kamar abinda ya shafi gawarwaki da hatsari. Karaf, idanunta suka kai ga wani hoto wanda yasa ta mikewa zaune babu shiri. Hoton Abubakar ne tare da wata ‘yar ajinsu Rukayya Tsigai, ai ba shiri ta hau online ganin wacce ta aiko, Zahida Taskira ce daya daga cikin yan ajinsu wacce suka sanyamata sunan sanadin surutunta da tone-tone don ba a sirri da ita. Inda ta yi mata bayani kamar haka. “Aslm, Ihsan please ba batun gulma ko hada husuma ba, inace wannan shi ki ka ta6a nunamin matsayin wanda zai aureki? Magana ta gaskiya guy dinnan na sanshi tare da Tsigai, saidai ban gayamaki ba time din kada ki ji haushi, idan har dagaske shi ki ka za6a matsayin mijin aure zan baki shawara ki chanja tunani saboda wallahi guy din yana da son mata, Rukayya ba wajen Partyn wata cousin dinta sukayi hoton nan kuma na tabbatar suna chatting.” Kan Ihsan ya yi dum, ta rasa meke mata dadi a duniya, batasan lokacin da ta soma hawaye ba tana ambaton Allah, saidai me? Ko kankani bata ji soyayyar Abubakar ta ragu ba sai kishi mai zafi da ya turnuketa, ba don tana sonshi ba babu abinda zai hana a yau ta rabu da shi. Bata maidawa Zahida amsa ba don tasan zai iya komawa kunnen Rukayya Tsigai, kawai sai ta kira Abubakar ta ce ya hau online zata mishi magana. Badiyya na kallonsa yana waya yana tambayar ko lafiya duk ya rikice saidai bata ce uffan ba, banda murmushi, idan da sabo ai ta saba da halin Abubakar na hira da yanmata balle kuma ta tabbatar cewa wannan Ihsan ce don duk cikin yanmatansa tana da yakinin ita ya ke yiwa so na aure tunda har ankai da sanya rana. Mikewa ta yi ta bar falonnasa shi dinma bai tsaidata ba don hankalinsa ya tashi jin muryar Ihsan din ba’a hayyaci ba. Nan ta aikamishi hoton, duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, shakka babu wannan hoton ya jima, yanzun ma ba ya tare da Rukayya sun rabu akan zafin kishin Rukayyar kan yanmatansa, shi kam kullum adduarsa bai wuce na Allah Ya yaye mishi wannan mugun hali ba. Ranar kam Ihsan ta yi kwanan bakin ciki, dakyar bacci ya saceta don idanunta saida suka kumbura. Washegari da ciwon kai ta tashi, koda Mami ta tambayeta sai ta ji bakinta ya yi nauyi ta kasa fadamata, tsoronta kada a fasa auramata Abubakar don Allah shaida tana sonsa yanzun musamman yanda ya ke kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a rai wanda ta tabbatar da shi ya ke yaudarar yanmata sai kuwa kudi. Ikram kadai ta sanarwa, Ikram da ranar ta tashi da farincikin jin Hafsa matar Gidado ta haihu da kuma dan kishinta a kasan rai duk sai ta ji nata 6acin ran ba komai bane idan an hada da na Ihsan. Ta hau salati, tasan tabbas Abubakar yana da kula yanmata don tasan wata kawarta wacce tasan shi saidai batasan har zuwa wannan lokacin ba, nan ta shiga bata baki da nunamata ta cigaba da adduar neman za6in Allah, katse wayar kawai ta yi. Abubakar ranar ya kira yafi sau biyar saidai ta k’i dagawa, ya bita whatsapp hakanan ya yi mata text saidai ko kusa bata maida amsa ba. A ranar dai suka shirya don kuwa bata iya dogon fushi da shi, abin mamaki Zahida ba ta daddara ba ta turo wani, ai kuwa ta sha zagi kafin a karshe ta rufeta yanda babu damar da zata k’ara shiga sabgarta. *** *** *** A KWANA A TASHI….! Tun Ummi na zuba idon ganin 6atan watanta, har dai ta ji shiru, wannan ya daga hankalinta, ga wani haske da ta kara hakanan komai nata ya k’aru, watarana suna kwance da Faruk ya dubeta. “Ummina ban yarda ba, anya babu ajiyata a wannan cikin naki? Kwadayinki ya yi yawa, yau kice magwaro, gobe ki ce bakyason kamshin turarukana.” Ta kwanta jikinsa tana mai turo baki. “Nifa bani da komai.” Ya ja karan hancinta. “Zamu tantance yanzu. Taso muje.” Ta mike zaune idanu a waje ta ke dubansa. “Ina?” “Asibiti mana.” Ta yi narai-narai da fuska. Ya yi saurin toshe bakinta da hannu. “Shii..karki soma rok’ona don kuwa sai munje.” Ta langa6ar da kai tana sosa idanu. “To ai..ai yau babu aiki.” Cikin muryar rarrashi ya ce. “Wajen Dakta zamu je, bamu jima da waya ba ya cemin yana asibiti.” Ta turo baki. “Please FAR HAS, allura fa zasu yi min.” Ya matso da ita yana ji kamar ya hadiyeta. Saitin kunnenta ya yi magana. “Ba wanda zan bari ya soka maki karfe a jiki, tashi ki chanja kaya kinji?” Ba musu ta mike, daman sanye ta ke da riga wacce ko k’ugu bata karasa ba sai kuwa wando shima da bai kai gwuiwa ba, ta kai kofa ya kira sunanta. Ta juyo fuska a turnu6e. “I love you.” Furucinsa yasa ta murmusawa gami da lumshe ido ta budesu akansa. “Love you too.” Ta furta a hankali ya sanya yatsunsa cikin sumar kansa yana murmushi gami da sauke ajiyar zuciya, wasu kance soyayya na raguwa bayan aure, shi kam ya rasa dalilin da yasa koyaushe soyayyarta gaba ta ke k’ara yi a zuciyarsa, Allah Ya sani kauna fisabilillahi ya ke yi gareta, tun dora idanunsa da ya yi akanta, bai ta6a hutawa daga tunaninta ba har saida ya mallaketa. Mikewa ya yi shima ya fad’a bandaki don kimtsawa. Lokacin karfe hudu ta kusa, Ummi ta kammala shirinta cikin wani koren leshi dinkin riga da siket, ta yafa farin mayafi ta sanya takalmi flat mai kalar fari da baki. Saida sukayi sallar la’asar kafin su fito kasancewar ranar bata da lesson don daga litinin zuwa juma’a sukeyi, kwarai Malamar na yabawa da kokarin Ummi don har mamakin kaifin basirarta ta ke, ko wata basuyi da somawa ba, ta iya abubuwa da dama. Gogan kananun kaya ya sanya, wandon 3quarter ne fari k’al, sai kuwa t-shirt dinta mai layi-layi fari da bak’i. Idan ka gansu dole ka k’ara daga ido ka kallesu don kuwa sunyi matukar dacewa da juna. Saida ya budemata 6angarenta ta shiga ta zauna kafin shima ya shiga, maigadi ya budemusu gate suka fita. A asibitin suka iske Dakta Ridwan, yana duba wasu kasancewar yawanci ranakun hutu, manya yafi gani, saida ya sallami wasu kafin suka shiga. “Ango na Amaryarsa.” Ya fada yana dubansu fuska dauke da murmushi. Suma murmushin sukayi Ummi na sunne kanta, Faruk ya kara matse hannunta cikin nasa. “Ya son ranka?” Sukayi dariya don tsakaninsu babu wani zancen raini, sun dauki junansu tamkar abokai musamman su ukun nan idan an cire Babban Yaya wanda ba koyaushe ya ke biyewa shiriritarsu ba. Ummi ta gaisheshi ya amsa tana tambayar su Muhsin. “Suna nan lafiya.” “Ai ba’a kyauta ba, ya dace a kawo mana su koda ran Friday ne.” Cewar Faruk. Dakta ya yi dariya. “Karku damu, duka yaranku zasu zo hutu, ai (second term) din ya kusa k’arewa.” “Wai me? Noo, kar a kawosu duka, ba zasu takura min Bebina ba.” Dariya Dakta ya yi. “Oh, har ka tabbatar da ka samu bebin? Toh ai sai ku tashi ku je Allah Ya raba lafiya.” Ya karashe yana mai daure fuska da wasa. Faruk na murmushi yana mai dafe goshi. “Please ka yi hakuri, dubamin ita yau wata biyu kenan bata ga period dinta ba.” Saida gaban Ummi ya fadi ta dan dubeshi, ya dagamata gira yana murmushi. “Eh ko?” Ta kauda kanta a kunyace. Dakta murmushi ya yi ya ce. “Lil kenan.” Daga haka ya janyo takarda ya yi rubuce-rubuce bayan gama yiwa Ummi tambayoyi daga haka ya mikawa Faruk takardar. “Sai ka je a auna fitsarinta.” Ba musu ya kar6a suka fita, bayan fitarsu ta dubeshi. “Kai FAR HAS, ko kunyar Dakta ba ka ji ba ka ke magana haka?” Ya daga kafada kadan yana yamutse fuska. “Don bakisan ma waye Dakta ba shiyasa ki ke fadin haka, sa’ar da na ci yana jin kunyar idanunki da sai na koma ni ke jin kunyarsa.” Dariya kadan ta yi kawai batare da ta ce uffan ba. Bayan angama auna fitsari an basu sakamako suka koma ga Dakta. Ya bude takarda ya karanta yana murmushi kafin ya dubesu kadan, Faruk ji ya ke kamar ya warce takardar, cikin zakuwa da son sanin meke faruwa ya ce. “Wai don Allah ka yi magana mana.” Dariya Ridwan ya yi. “Bani goron albishir.” Ya fada yana mai mikamasa hannu. Faruk ya wawuro na’urar auna jini (Sphygmometer) ya dora saman hannunsa. Har Ummi saida ya bata dariya, shi kansa dariyar ya yi. “Toh nagode dai na tausayamaka tunda naga ka damu.” Ya dubi Ummi fuskarsa a sake.2 STORY CONTINUES BELOW “Congratulations, you are two months pregnant.” Sunkuyar da kanta ta yi, ta fahimci me ya ke nufi, wato dai tana da ciki wata biyu. Faruk mikewa ya yi ya karasa ya rungume Yayansa suna dariya. “Congratulations my lil, Hajiyarmu zata yi farinciki da jin hakan.” Sukayi dariya. Tunda Ummi ta sauke kanta bata k’ara dagoshi ba har zuwa sadda Faruk ya dawo ya zauna gami da lalubo hannunta yasa cikin nasa, idanu ta lumshe ta saci dubansa, shima ita ya ke kallo. A hankali bakinsa ya motsa. “I love you.” Ta fahimci hakan ya fada, ta kauda kanta tana murmushi gami da damke hannunsa alamun ta amsa. Hankalin Ridwan ba ya kansu, ya gama rubuta magunguna kafin ya mikowa Faruk. “Sai a kula banda yawan aikace-aikace. Yau za ka shiga Gida ne?” “Ai can na nufa ma.” Sukayi dariya, Ummi hankalinta ya tashi, kamar ta ce mishi kar su je, tasan kawai kunya zai sanyata gaban su Hajiya. Ai kuwa suna fita ta hau rok’onsa akan kada su je, baice uffan ba banda murmushi. Saida suka je din, Ikram ta tarbesu kamar ta hadiyesu don yanzu bil hakki tana kaunar Ummi, soyayyar Gidado ya shafeta. Hajiya ta yi murnar jin cewar Ummi na dauke da juna biyu, don Faruk da bakinsa ya fadamata, ta hau yi mata gargadi akan ta kula za’a samo mata mai tayata hidima, ta nuna a barshi saidai Hajiya ta dage sai anyi hakan. Faruk bai ce uffan ba don da ta raayinsa shi kansa bazai so ba saidai yana tuna maganar Dakta da ya ce ta dunga hutawa ya amince. Da Magriba tana dakin Ikram sunyi sallah suka yi zaman hira, anan Ikram ke labartamata yanda sosai yanzu Gidado ke damuwa da ita har idan ya ji shiru bata hau online ba zai damu ya kirata a waya. “Ikon Allah.” Shine kawai abinda Ummi ta ce, duk kuwa da cewar ta yi mata murnar hakan saidai kasan ranta tana tsoron abinda zai je ya dawo idan Hafsa ta samu labari. Ko da wane ido za ta dubeta? A hakikanin gaskiya ko a baya idan Gidado bai jin wani abu game da Ikram to a yanzun yana ji, don ita kanta Ummin ta fahimta ta yanda duk sadda sukayi waya sai ya yi maganar Ikram, wataran ya ce suna hira wataran ya dunga yabon halin kirkinta . A bakinsa ne ma ta ji cewar suna chatting Abubakar ne ya bashi lambarta. Ko Abubakar din da kullum suke waya bai sanarmata ba. “Ya karatun? Kina ganewa sosai ko?” Ikram ta fada gami da katse shirun. Murmushi Ummi ta yi. “Ina fahimta.” “Allah Ya taimaka, ga Azumi ma ance nan da sati biyu ko?” Ta gyada kai. “Hakane, abin ba wuya, kamar yau ne muke lissafi da Anti Amina ta ke cemin bayan Azumi bikinta, yanzu har ga azumin ya zo.” Dariya Ikram ta yi. “Kina ban dariya idan kina ce mata Anti, sa”arki ce fa.” Dariya itama Ummin ta yi kadan. “Ta cancanta, ita ta mayemin gurbin uwa kuma Yaya a gurina alokacin da bani da kowa cikin DAN ADAM dake son ya ra6eni, alokacin da kowa ya gujeni. Ita ke cemin na yi wancan mai kyau ne, kada na yi wannan babu kyau, ta zama Malama agareni tun ban kai ga soma zama a aji ba. Kinga kuwa ta cancanta na kirata da Antina.” Ikram ta gyada kai, ita kam yanzu Ummi na burgeta, mutum ba zai san tana da shiga rai ba sai ya zauna da ita, daman bata tsaneta ba tun a baya sai sadda Faruk ya ce zai aureta har ya mareta akanta ga kuma taya Ihsan kishi. “Lallai ta cancanta har ta wuce cancantar ma. Ni kuma nan gaba ina fatan zama yayarki.” Ta karashe da gwalo, Ummi ta gane, wato ta zama matar Gidado. Sukayi dariya lokaci guda. “Dagaske nake, kinsan kuwa Hajiya da Daddy sunce saidai nima na karasa jami’a a gidan mijina, da zarar mun gama jarabawarnan ta karshe sai aure.” Ta jinjina maganar. “Kice tare za mu sha bikinku da su Ihsan.” Dariya Ikram ta yi sai kuma ta maida fuskarta kalar damuwa. “Allah Yasa mu auri wanda yafi alheri garemu.” “Amin.” Sai bayan isha’i sannan suka bar gidan zuwa gidansu. Nan kuwa aka shiga rainon ciki babu wasa, yarinya karama aka kawomata, batafi shekaru goma sha hudu ba. Farkon kawota Ummi idanu ta zubamata tana kallonta cike da tausayawa sannan ta dubi wacce ke tare da ita wacce aka kira da mahaifiyarta da ko kusa bata ga kama ba. “Yanzu Baba wannan aiki zata dunga yi?” “Eh, aiki kowanne da ki ke so ki sanyata, babu wanda ba zata iya yi gareki ba.” Ta k’ara duban yarinyar wacce ta yi wani firi-firi da idanu. Tausayinta ya kamata. “Shikenan.” Jin haka matar ta hau washe baki tana gyara mayafi zata mike. “To bari na koma tunda naga gidan, ke kuma Batula ki kula, kada inji kar in soma gani kin sa6awa uwar dakinki kinji ko? Hajiya don Allah ki dunga kula yarinyar akwai shegen munafunci.” Ummi da ke jin kamar ta makureta ta ce. “Wane irin munafunci kuma?” “Um, kada ta dunga yi miki la6e wai, to shikenan ai, sai anjima, Allah Ya kara arziki.” Ta karashe cikin basar da wancan maganar. Ummi ta bata dubu biyu ta hau mota. Nan ta hau zuba godiya ta fice. Ta maida hankali ga yarinyar da aka kira da Batula. “Sannu Batula, inaso ki saki jiki da ni, ki rikeni tamkar yayarki, ni bazan cutar da ke ba, zan kuma rikeki bisa amana kinji ko?” Cikin mamaki mai tsanani da rashin gaskatawa ta gyada kai don gani ta ke kamar wani salo ne na cutarwa, gida na uku kenan da aka kawota, wadancan biyun duk guduwa ta yi saboda matsi da takura. “Fadamin gaskiya Batul, mene alak’arki da wannan matar? Dagaske itace ta haifeki?” Ta girgiza kai cikin raunin zuciya kiris take jira ta fashe da kuka. “A’a, kanwar mamana ce uwa daya uba daya da ta rasu.” Runtse idanu Ummi ta yi ranta na suya. “Meyasa ta ke kawo ki aikatau?” “Babana ne ya aureta bayan rasuwar Mamana, ba da son ransa ta ke kawoni gidan aiki ba, ko yau da zamu taho da kuka muka rabu da shi. Kullum saita dakeni, komai ni nake yi mata.” Hawaye Ummi ta shiga fitarwa, DAN ADAM kenan, ace ‘yar yayarki ki ke yiwa rikon sakainar kashi? Duniya abin tsoro. Ummi ta tabbatar mata zata riketa bisa amana, ta bata kyakkyawan muhalli ta sanyata a makaranta. Ita da kanta ta wankemata kanta bayan ta tsefemata kitso, suna yi suna hira Batul na kara bata labarin kauyensu Maraba. Cikin kayanta ta dauko wanda ya yi mata kadan ta bata ta sanya kasancewar yarinyar akwai tsawo nan suka zauna das a jikinta. Koda Faruk ya dawo, ya yi mamaki, bai gane ko wacece ba ganin tana zaune a kasa suna hira da Ummi suna dariya. Batul ta gaisheshi ta yi ciki, ya zauna yana duban Ummi wacce ta tashi ta tarbeshi. “Ummina wacece wannan?” Da murmushi ta amsa. “Itace wacce Hajiya ta turo zata tayani aikace-aikace.” Ya jinjina kai. “Naga kamar wata kanwarki kunata hira ai.” Murmushin ta kara yi. “Kanwartawa ce ma. Tausayi take ban.” Nan ta labarta mishi labarinta, shi kansa ya yi mamaki. “Allah kenan, DAN ADAM babu mai iya masa sai Allahn da Ya halicceshi, Allah Ya datar da mu.” “Amin.” Tun daga wannan ranar Ummi ta riki Batul bisa amana, har makaranta an sanyata na Arabi. Haka har azumi ya zo, nan ma komai tare sukeyi, cikin azumin ne kuma Intisar ta haihu diyarta mace. Kowa ya yi murna da hakan, ranar suna aka sanya sunan Hajiya Mama, wato Sadiya. Hajiya Mama ta ji dadin wannan karar da sukayi gareta. Anci suna an kare lafiya kowa na yaba yanda Faruk ke nan nan da Ummi ko gaban mutane ne ba ya iya 6oye son da ya ke mata. A ranar sunan ma ganin yanda Ummi ke yiwa Batul saida su Jidda suka tofa. “Wai wannan inace ‘yar aikinki ce ki ke mata haka?” Murmushi ta yi. “Ni ina mata kallon mutum mai daraja.” “Don kema a baya yar aikin ce ko?” Cewar Fadila. Abin ya ta6a zuciyar Intisar da su Ikram, Ummi kuwa ko a jikinta ta soma bata amsa. Ko bayan wannan, yan aiki mutane ne kamar kowa, hakazalika suma suna da nasu daraja da k’imar, da yawa cikinsu kan fito aiki bisa kaddara ba da son zukatansu ba, wasu anfi karfinsu ne wasu kuwa halin rayuwa ce. Ni Ummi bana fatan ranar da zata zo na wulakanta wani DAN ADAM a duniya, da yawa suna kuskure, sukan dauki kansu wasu har su dunga wulakanta masu tayasu hidima don kawai tak’amarsu biyansu su ke yi, sai yaronki karami ya budi baki ya zagi dattijuwar da ko ke ta haifa amman ba zaki kwa6eshi ba kasancewar kina mata kallon yar aikinki, sai ya zagi direba ko maigadinki duk ba za ki ji ko darr ba, asalima har ya kai ga kin shigarwa danki don kawai kina yi musu kallon kaskantu, watakil kuma sun fiki matsayi a wajen Allah. Ba ma akan masu aiki ba, kowaye kada ka wulakantashi don shakka babu bakasan mai yi maka rana ba, ko ya ya, bana mance halacci.” Fadila da Jidda suka k’ulu da maganganun Ummi, musamman Jidda wacce ke ji kamar da ita ta ke, basu kadai ba har da wasu cikin gayyar sunan wadanda sun kasance suma sukan dauki yan aiki ba komai ba face kaskantu maganar Ummi ta shigesu, nan kuma wasu suka hau fadin ai yan aikin ma suna suka tara akwai mugaye. Ita kuwa Fadila bata kara cewa uffan ba don ta cika da mamakin yanda har Ummi ta yi kaurin wuyar mayarmata da martani. “Ku bar ganinta haka, yar aiki ce a baya shiyasa ta fiye wannan zakalkalewar, ai duk inda mutum wanda bai saba da arziki ba ya ke to fa sai kun gani ko a jikinsa ko furucinsa.” Cewar Jidda a fusace. Ummi ta dubeta, kamar ta ce wani abu sai kuma ta hadiye kawai tana murmushi. “Kai don Allah Anti Jidda.” Cewar Intisar kenan, Jidda ta watsamata mugun kallo. “Na ambaci sunanki?” Ta rausaya kai. “Ko ba don wani abu, ku yi duba fa da cewar cikin azumi ake…” “Please ya isheni, wani abin nace?” Jin haka Intisar ta ja bakinta kawai. Wata hamshakiyar mace da ta hade cikin wani tsadadden leshi ta tofa. “Kwarai Jidda suna haka, don wallahi wata yar aiki da kawata Mariya Sadik ta ta6a yi, ai kinsanta, yarinyar a dakin mijin ta kamata. Ai babu butulu kamar dan aiki saidai mata mu kiyaye.” Nan kuma babin ya koma hirar yan aiki, Ummi ganin abin nasu kamar da biyu ne, yasa ta mikewa ta bar dakin zuwa falo, Intisar da Baraka suka biyo bayanta har Ikram don abin ya 6ata ransu suma. Ta nunamusu ba komai ganin yanda suka damu. Ita kuwa damuwarsu akai ma kadai ta sanya komai gogewa a zuciyarta. Sai Magriba Faruk ya zo daukarta, anan ya sha ruwa da su Haidar hakanan suma nan ciki suka sha ruwa sannan ya shigo ya ga bebi, anan ne Fadila da Jidda suka kai mishi k’arar Ummi akan ya ja mata kunne. Ya cigaba da danne wayarsa yana yiwa yarinya hoto, gefensa Haidar ne zaune sai Ridwan wanda shima bai jima da zuwa ba. “Wai muna magana ka maidamu wasu shashashai.” Cewar Jidda mai saurin fusata. “Wai meyafaru? Me Ummin ta yi muku?” Cewar Dakta yana duban Jidda. Jidda ta yi kwafa. “Mene idan ba rashin kunya ba har tana kiranmu masu raina mutane. Yaushe kan mage ya waye da har raini zai shiga tsakaninmu?” Faruk ya bar abinda ya ke ya dubi Jidda ransa a 6ace kamar ya yi magana saidai shigowar Ummi da Intisar falon Haidar ya katseshi, sanye ta ke cikin wani leshi bak’i mai adon orange flowers, sai mayafinta (orange) da ta yafa, hakanan jakarta da takalminta marar tudu. Idanunta akansa suka soma sauka. Wani sassanyar murmushi suka sakarwa juna kafin ta karaso ciki ta gaida Angon karni da Dakta. Faruk ya mik’awa Dakta bebin. “Bari mu wuce.” “Ai daman fuskar da ta samu wajenka ne yasa ta ke…” “Ya isa! Haba!” Cewar Ridwan ga Jidda wacce ke zak’alk’alewa. “A’a Dakta, babu batun ya isa fa, magana ta gaskiya.” Cewar Fadila tana taunar cingam da kallon banza. “Ummi me ya hadaki da yan uwanki?” Cewar Dakta kenan, Faruk na tsaye hannuwa ciki aljihu kawai yana kallonsu. Ta dan murmusa don ita bata ga abin daukar zafi ba. “Ba abinda ya hadamu.” “Karya ki ke yi uwar kissa.” Cewar Fadila. “Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?” Cewar Dakta. Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana. “Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!” Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin magana, ko babu komai yana da kwarjini. Haidar ya dubeshi. “Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma’aruf, kune masu laifi ba Ummi ba, sai ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku.” Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad’a, Ummi dai ganin mijinta ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa. A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida ta mishi magana. “Don Allah ka rage gudu.” Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru. Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire dan kunne da sark’a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido. Murmushi ta sakarmishi a kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a runtse. “I’m sorry.” Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta. Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato. “Haba FAR HAS, don Allah ka daina inajin wani iri wallahi.” Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na farinciki. “Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba, DAN ADAM ajizi ne.” Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska. “Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?” Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya. “Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?” Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a. “Kai don Allah.” Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi. Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata daure musu fuska. Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon banza ba. Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki. Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda yanzu suke zaman aminci. Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda ta iya ne. Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka waya a handsfree tana amsawa. Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla. “Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka.” Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan lokaci. “Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar…” “Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata.” Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya. Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka zata dunga fama da shi? Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa. ‘Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.’ Ta fadi a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama.