DAN ADAM CHAPTER 9

DAN ADAM CHAPTER 9

Ta kawo falon, tana kokarin ajiye suka had’a ido da ihsan ta samu tsarabar harara kuwa. Ta ajiye a gaban Faruk, wani daddad’an kamshi na turare ya bugi hancinta. “Thank you.”+ Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi bayanta da kallo kafin ya numfasa muryar Ihsan ta doki kunnuwansa. “Let me serve you.” Ya dubeta ya dan murmusa gami da gyada kai, cikin siririyar muryarsa ya amsa. “Kar ki cika, ban tare da yunwa.” Suna ci suna hira, jefi-jefi yakan dubi hanyar da ta bi, Mami ke faman jan shi da hira yana bata amsa. Ihsan gaba d’aya ta gama tafiya a kallonsa, sai yanzu take tabbatar da hakikanin gaskiyar abinda take ji game da yayannata. Ummi a d’aki zaune ta yi zugum tana tunani. A karshe ta d’aga rigarta ta shinshina gami da lumshe ido. Ita kam tana son kamshi a rayuwarta don dai babu yanda zatayi ne ta samu. Musamman wannan turaren da ta ji awajen Faruk, sai ta ji ya doke duk wadanda ta saba shak’a wajen masu gidan. ‘Komai na Yaya Faruk ba irin na kowa bane, komai nasa daban. Ya ji dad’in rayuwa.’ Cewar wani sashe na zuciyarta. ‘Kada ki kai kanki inda Allah bai kaiki ba Hasiya, babban goro fa sai magogin karfe, a komai na rayuwa Faruk ya d’ara ki, babu gatan da Allah bai ba shi ba. Yafi karfinki nesa ba kusa ba.’ Wannan tunanin yasa ta numfasawa, wani hawaye ya taho mata wanda bata iya hanashi kwaranyowa ba, shikenan su yan aiki basu da gata? A daren dakyar ta iya kokawa da zuciyarta har ta samu ta runtsa domin kuwa bata k’ara fita falon ba, asalima batasan sadda Faruk ya bar gidan ba, ta dai ji maganar Ihsan na fad’in Babban Yaya wanda ya nuna shima yazo daga baya.2 Tunanin duniya ya ishi Ihsan, ta gama tabbatarwa lallai tana kaunar Yaya Faruk, a wannan daren yini ta yi kallon hotonsa wani dad’add’e da sukayi da Adnan da Haidar. Karshe dai ta kirashi a waya, bayan sun gaisa ya nemi sanin wace don bil hakki ba shi da lambarta. “Ihsan ce.” Ya yamutsa fuska cike da mamaki sa’ilin da yake goge fuskarsa da tawul daga shi sai gajeran wando ya fito wanka. “Oh, kanwar Adnan?” Ta ji haushin kanta, wato ko lambarta babu a wayarsa? Da tasan da haka da bata bayar da kai wajen kiransa ba. Kamar zata yi kuka ta amsa da eh. “Ok, fatan lafiya?” Ta daure ta had’iye 6acin ranta. “Daman na kira na ji ya kuka isa gida?” Ya dan saki fuska. “Alhamdulillah. Nagode.” “You are welcome.” Ya dan murmusa gami da jinjina kai. “Good night.”. Daga haka ya ajiye wayar batare da ya katse kiran ba ya cigaba da abinda yake yi. Babban Yaya na gefen gado zaune yana tura sak’o email a laptop dinsa. Takaici da bakin ciki suka tararwa Ihsan, ta katse kiran don kanta. Duk da ta ji haushinsa, hakan baisa ta ji zuciyarta ta bar magagin kaunarsa ba. Inama zai aureta? Ta ayyana a ranta, wani tsalle tayi a saman gadonta gami da kwakwume filo tana murmushi, a haka har bacci ya soma fisgarta ta yi addu’a ta kwanta.2 Faruk yana kwance, ya zurfafa cikin tunani, a gefe yana dan tsintar hirar Babban Yaya da matarsa tamkar wasu sababbin aure, ya lumshe ido yana mai fatan bacci ya yi awon gaba da shi ko don ya daina ganin abinda ya ke gani a kwayar idanunsa, hakanan yabar jin sautin muryar da ta k’i gushewa a dodon kunnensa ba don komai ba sai don tsoron kada tunaninsa ya tabbatar da hakan, bayaso yanayin ya sauya zuwa ga abinda ya ke tsananin gudu. Haka bacci ya sureshi cike da tunani da mafarkai masu dadi da ban mamaki. Washegari da wuri suka tashi, bayan sun kammala shiri suka dunguma zuwa daurin auren da Daddy ya turasu, sosai kuwa Alhaji Labaran ya ji dadin zuwansu, a karshe sukayi sallama suka nufi gidan Hajiya Mama. Basu jima ba suka wuce don a ranar zasu juya zuwa Abuja. Suna komawa gida kuwa suka tattara suka bar garin Kano…! *** *** *** Ya gama buge-bugensa akan k’asa kafin ya yi wata arniyar dariya ya dubesu. “Shakka babu kun hadu da yarinya mai basira da har ta yi muku dabara batare da ta shiga matsalarku ba.” Hajiya Binta ta dubi kawarta Luba sannan suka maida hankalinsu ga bokansu. “Kamar ya ranka shi dad’e?” Cewar Hajiya Binta kenan cikin rawar murya. Ya girgiza kai. “Babu wani k’ulli da ta sanya a k’asan gadon abokiyar zamanki, asalima acan kwatami ta yarr.” Wani bakin ciki ya turnuk’e zuciyar Hajiya Binta, ta ji wata muguwar tsanar Ummi ya turnuk’eta, maganar Luba ta katse tunaninta. “Yanzu ranka shi dad’e ya za’ayi? Tabbas munyi kuskuren saka wata, kada dai ta tona asirinmu?” Ya girgiza kai yana dariya. “A’a, yarinyar ba haka ta ke ba, kada ku ji ko d’arr, yanzu me kukeso ayi?” “A maimaita mana irin wancan.” Fad’in Hajiya Binta kenan tana dubansa da jajayen idanunta wadanda 6acin rai ya kad’a. Nan take bokan ya turnuk’e fuska yana watsamata kallon banza na baki isa ba. Hakan ya kad’amusu ‘yan hanji. Ya cigaba da magana da kakkausar murya. Kafin na baku na gayamaku wuyar k’ara samun aiki irinsa, domin a shekara, sau daya Aljani Tsingil ya bani damar tambayarsa buk’ata, saidai ko kuyi hakuri har wata shekarar.” Hajiya Binta ta narke tana rok’onsa ko akwai wani abu da za’a iya yi? Ya jinjina kai. “Tabbas, abu mai sauki, zamu sanyamata warin ja6a, ta yacce ko ta ra6i mijin zai ji gaba d’aya ya tsaneta, amma hakan bazai sa soyayyarta ta fice a ransa ba, za dai ya kaurace mata kamar yanda kukeso, itama zata shiga tashin hankali. Ke kuma ga wannan (ya mik’a mata wani k’ulli) Ki dunga shafa kwallinnan aduk sadda za ki turaka, hakanan ki dunga shafe fuskarki da turaren nan, ina mai tabbatar miki za ki samu kulawar da ya saba bata, hakanan kuma ba dai kije da buk’ata ba, ya k’i aminta. Idan hakan ya yi muku…”+ Hajiya Binta da Luba suka amsa da eh har suna rige-rige. Yayi murmushi mai k’ara fiddo muninsa. “Ku tafi, ku saurareni nan da kwana uku, zakuga aiki da cikawa.” Suka mik’e suka bar wajen da sauri gaba daya a tsorace. A mota suna tafe Hajiya Binta na faman surfawa Ummi ashar tamkar tana gabanta. Luba ta dakatar da ita. “Laifin fa duk namu ne Binta, munyi wawancin sanya wata ta yi alhalin bamu gama fahintar halayenta ba. Wannan bata da son abin duniya kamar Zinaru tsohuwar ‘yar aikin Hajiya Madina. Ya dace ko nan gaba mu kiyaye.” Ta saki huci. “Naji, yanzu me kike ganin zamuyi mata?” Luba ta murmusa. “Me kike ci na baka na zuba ne? Wannan k’aramar alhaki ce muddin kika zama uwargidan Alhaji Muhammad Modibbo.” Jin haka yasa Hajiya Binta kyalkyalewa da dariya itama aminiyar shaid’ancin nata na tayata. Ta jinjina kai. “Tabbas zasu san basu da wayo.” Alokacin da suka iso kofar gidan, Ummi na kokarin shigewa ciki, dawowarta kenan daga islamiyya, gabanta ya fad’i ganinsu, suka bita da mugun kallo har ta shige lokacin da maigadi ke wangale musu k’ofa. Ummi wani zargi ya d’arsu a ranta, ta tabbata mutanennan da wuya idan sun kyaleta, tana kuma jiyewa uwar dakinta tsoronsu, ta tabbatar basu hakura ba, dole akwai abinda suke shirin k’ullawa. Ta sauke ajiyar zuciya sadda isa kofar sashensu. Da ace ita din tana da dama, da ta shawarci Hajiya akan ta dage da addu’a don ta fuskanci Umma akwai mugun abun da ta taka. *** *** *** ABUJA Zaune yake saman kujera (resting chair) a ‘yar barandarsa, ya sanya (sketch board) a gaba wanda aka kafa ajikin katako ya tsaya kyam, hannunsa alkalamin zane ne, daga shi sai singilet da gajeran wando, dawowarsa kenan daga aiki ya yi wanka, hannunsa na hagu rik’e da kofin (coffee) yana sha, ya dukufa sosai wajen kokarin zana abinda ke ransa, yana yi yana shan(coffee), saida ya kammala ya dubi zanensa yaga babu abinda ya manta sannan ya saki murmushi mai burgewa. Komawa yayi ya kwanta jikin kujerar bayan ya tara kansa da hannunsa na hagu yana mai cigaba da shan (coffee) dinsa da dama, ido ya zuba k’irr yana k’arewa zanen kallo alokaci guda kuma zanen na k’ara shiga ransa. “So beautiful.” Ya fad’a a bayyane, ya jima sosai yana kallon zanen kafin daga bisani ya mik’e ya dauko laptop dinsa ya yi aikin gabansa. A karshe ya nemi makwancinsa cike da dumbin tunani, abinda bai taba yi ba kenan duk tsawon rayuwarsa, kwana da tunanin abinda ya ke yiwa kallon 6ata lokaci a baya. *** *** *** KADUNA Mutan Kaduna sun isa lafiya lau, Dija cikin garin ya zamemata bak’o don bata ta6a zuwa ko’ina ba banda Katsina kauyen k’urfi inda nan ne asalin mahaifinta Yahuza. Ta yi mamakin ganin k’erarren gidan da Munira ke rayuwa cikinsa a unguwar Malali, ta sauke ajiyar zuciya har ta kasa 6oye mamakinta ta fito da shi fili. “Gidanki mai kyau.” Munira ta murmusa. “Nagode ‘yar uwa.” Bayan shigarsu ciki ne ta gane wajen ba komai bane, domin sakin baki tayi tana karewa falon kallo wanda ya yi bala’in had’uwa. Zata iya cewa tunda take bata ta6a zuwa gida makamancin wannan ba. Haka Munira ta rakata har dakin bak’i a sannan ta koma ga yaranta Tasleem da Haris. Ita dai Dija k’arewa komai kallo takeyi, tsaf, kamar ansan da zuwanta. Gado ne sai aka shimfida kafet a k’asa, a gefe sif ne maidaidaici na kaya, sai bandaki. Ina zata samu wannan a kauyensu kuma gidansu? Tunda dai akwai masu ginin zamanin, amma bata ta6a kwana ba. Tayi tsalle saman gado don dadi saikace wata ‘yar shekara goma. Munira ta dawo ta ajiyemata sabulu da soso a bandaki, ta umarceta da tayi wanka. Bayan ta kammala ta shirya tsaf sannan ta fito suka ci abinci saman tebur abin sai ya yiwa Dija banbarakwai, hatta yaran and saida sukayi mata dariyar yanda ta dunga nuna kauyenci saman tebur. A karshe suka tashi sukayi magriba mai aiki ta kwashe komai. Suna zaune a falon ita da yaran suna kallo, Munira kuwa na kicin tana shiryawa maigidanta abinci, suka ji sallamar maigidan. Gaba daya yaran suka mike suna ihun murna, hakan yasa Dina kallonsa. Sakin baki ta yi yayinda gabanta ya hau dukan tara-tara, haka mijin Munira ya had’u? Sanye yake cikin farar shadda, bak’i ne kuma dogo, yana da kyau babu laifi. Ya rungume yaransa yana mai farincikin ganinsu, zuwan Munira da sauri ne yasa shi bud’emata hannu ta karaso ta shiga ya hadasu ya rungume gami da lumshe ido, a hankali ya yiwa matarsa rad’a ta dubeshi tana murmushi ta sakarmishi hararar wasa shima ya kashemata ido yana murmushin. “Sannu da zuwa.” Maganar Dija ta maidosu hayyacinsu, sukayi saurin sakin juna, ita kuwa tuni ta tafi a kaunar mijin Munira. Munira ta matsa da sauri shi kuwa ya dake ya amsa yana mai tambayarta mutanen kauye. “Duk suna lafiya, sunce a gaisheku.” Ya amsa fuska a sake sannan ya maida hankalinsa ga Tasleem da Haris. “To, a jira nayi wanka na fiddo muku tsaraba ko?” Suka hau tsalle da ihun murna. Ya jinjina kai. “Kuma ku nemomin tsarabar da ku ka kawomin idan ba haka ba nima zan fasa baku.” Nan ya yi gaba yana dariya Munira da Dija na tayashi. Yaran kuwa kansu ya dauki chaji don basu yowa babannasu tsarabar komai ba. Haka sukayita tunani lokacin har Munira ta bi bayan mijinta, hakan yasa suka koma ga Dija don ta nemomusu mafita. Munira na shiga mijinta Deen (Zahraddeen) ya d’agata cak yana juyi da ita gami da fadin. “Oyoyo sweetna.” Sukayi dariya, dakyar ta zame daga rik’on da ya yi mata ta dan daki kirjinsa. Cikin muryar shagwa6a tace. “Kaidai wallahi ba ka rabo da abin dariya.” Ya k’ara janyota yana murmushi da nok’e kai. “Eh mana, musamman ma idan agaban sweetna nake.” Tayi dariya ta kwace jikinta gami da fad’awa bandaki don had’amishi ruwan wanka. Acan kuwa Dija ta kasa sukuni, hankalinta gaba daya baya wajen Tasleem da Haris masu tambayarta tsarabar da zasu bawa babansu. Mik’ewa ta yi. “Kuje kicin ku nemi wani abun da mamanku ta kawo.”. Da gudu suka wuce, dakinta ta koma ta zauna tana tunani, tunda take bata ta6a susucewa akan kowane d’a namiji ba kamar wannan, ta yi murmushi gami da k’udurta mugun abu a ranta.1 *** *** *** Da sallama ta shiga turakar mijinta, ya amsa yana mai dubanta fuska a sake, ta ci ado har ta gaji sai kamshi ke tashi ajikinta. Ya yi ta dubanta itama idanunta akansa ta karaso ta zauna. “Barka da…” Maganarta ta katse ganin irin razanar da Alhajinnata ya yi gami da mik’ewa yana mai saurin toshe hanci. A tsorace Mami ke dubansa da mamaki. “Lafiya Abban Adnan?” Ya girgiza kai. “Wane irin turare ne kika fesa haka Madina?” Mami ta dubi jikinta kafin ta dubeshi cikin rashin fahimta. “Bangane ba?” Ya kauda kai gami da k’ara ja baya. “Don Allah ki shinshina jikinki, wallahi turaren naki sam babu dadin shak’a, ki tashi don Allah ki je kiyi wanka kinji?”. Ya karashe da muryar rarrashi da kwantar da kai. Mami ta jinjina kai ranta na soyuwa, ba don Muhammad bane ayau da ta gasa mishi magana, saidai girma da darajarsa a idanunta yafi gaban haka, ga kuma soyayya tsantsa a gefe. Mik’ewa ta yi bayan shigewarsa daki da sauri da sauri, ta fice ta koma zuwa sashenta. Ummi dake zaune su kadai a falon ita da Fahad suna kallon (Harry porter) sai ji sukayi ana kwankwasawa, Ummi ta bude, kallo daya ta yiwa Mamin ta fahimci akwai damuwa shimfide saman fuskarta, itama Mamin zubamata ido ta yi domin ta ga ko zata nuna wata alama na cewa ta ji wari ajikinta, sai ma ta ga duk hakan bata kasance ba. Wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta giftata, ga mamakin Ummi, Mami har waiwayenta ta yi, ko me take son hangowa? Oho. Fahad ya mike zaune. “Lah Mami, ya kika dawo?” Ta yi yak’e. “Mantuwa nayi ne.” Daga haka ta shige zuwa dakinta da sauri-sauri. Suka cigaba da kallonsu, can kuma da jimawa, har Fahad bacci ya daukeshi saman kujera, Ummi kuwa na jiran Mami ta fita ta k’ulle k’ofar, sai ga Mamin ta fito tana zuba wani tsadaddan k’amshi na ban mamaki. Ummi dai tun kafin Mamin ta karasa fitowa kamshin ya ratsa kofofin hancinta. Tana mamaki kodai Mami 6arin turaren ta yi. Ta fito sanye cikin doguwar rigar abaya wanda daga k’asa kayan bacci ne,ta dora hijabi saman doguwar rigar. “A’a, bacci ya yi?” Ummi ta amsa a ladabce. “Eh.” Ta jinjina kai fuskarta na nuna alamun bata so hakan ba. Ta dubi Ummi jiki a sanyaye. “Ki kaishi makwancinsa.” “Toh.” “Saida safe.” “Allah Ya tashemu lafiya.” Cewar Ummi tana kokarin cika umarnint. Har Mami ta kusa k’ofa sai kuma ta juyo alokacin Ummi na susar hancinta dake k’aik’ayi. Gaban Ummi ya fad’i ganin ta dawo. Mami ta dubeta lokacin da take matsowa gabanta. “Kinji wari ajikina Ummi?” Da sauri Ummi ta girgiza kai a tsorace. “Wallahi a’a, asalima kamshi kikeyi sosai Mami.” Mami ta dubeta na dan lokaci kafin ta saki ajiyar zuciya. “Amma naga kin toshe hanci.” Ummi mai saurin kuka tuni murya ta raunana. “Aa wallahi k’aik’ayi yakemin shine na sosa.” Mami ta numfasa. “Saida safe.” Ta furta a hankali sannan ta yi gaba tabar Ummi na binta da kallon mamaki. Ga dukkan alamu dai akwai abinda ke damun uwar dakinnata. Ta yi shiru, duk tunaninta bata gano komai ba hakan yasa ta basar da zancen ta tashi Fahad ta kaishi makwancinsa sannan ta rufe k’ofar. A hankali bacci ya soma fisgarta ta ji ana kwankwasa k’ofa sannu-sannu. Mik’ewa ta yi a tsorace ta fito falo, agogo ya nunamata sha biyu harda mintuna. Ta karasa ta bud’e ta fita don bude kofar sashen. Shima Adnan lokacin ya mike ya fito don jin k’arar bugun don bai riga ya yi bacci ba yana karatun jarabawa. Ya dubi Ummi da mamaki. “Waye haka?” “Adnan ku bud’e ni ce.” Suka firgita jin muryar Mami, da sauri Adnan ya bud’e k’ofar. Ta shigo,ta dubesu da jajayen idanunta kafin ta wuce a sanyaye bayan ta umarci Adnan da rufe kofar. Ummi ta tsaya a falo cikin tsananin firgici, Adnan ya bi bayan mahaifiyarsa, can ba jimawa ya fito rai babu dad’i. “Rufe kofar Ummi.” Ya fada batare da ya kalleta ba hankalinsa na kan hanya da alama Mamin bata ba shi fuskar sanin damuwarta ba. Itama ta rufe jiki babu kwari ta koma dakinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *