DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
“Kaine Mubarak?”Ya ce, “Eh”.”Ina ne gidan ku?”
Ya yi mata bayani, ta kalle shi a tsanake,ta ce.
“Mubarak, kai dana ne, ni ce uwarka, ni na haife ka. Wallahi babu wanda ya isa ya raba ni da kai, sai kuma na karbe ka, don kai dana ne na cikina, ni na haife ka”.
Gaba daya suka zabura, anya kanta daya?
Mustapha ya ce, “To ni kuma DAN WAYE? Ki fada min ni din DAN WAYE? To fa, muje zuwa.
Yadda Mustapha ke daga murya yasa Alh. Abdulmajid ya fito, ya ce. “Lafiya? Me ke faruwa?”
Shi kam Mubarak yana tsugune tsuru yana mamaki, hakika wannan matar akwai motsowa a cikin lamarin ta. Ficewa yayi ba tare da ya bi ta kan batun ta ba.
Ita ko Hajiya Saratu ta kafe kai da fata tana
fadin.
“Yau Allah Ya cika min buri na, Ya nuna min abinda na dade ina nema, ruwa ko kaka, mutum ko aljan ba su isa su raba ni da dana ba”.
Alhaji ya daka mata tsawa, ya ce. “Wai ke mahaukaciyar ina ce? Haihuwar ki nawa? Ko kin haihu ba tare da sani na ba? Don a sani na dan ki daya, kuma gashi, shi ne Mustapha wanda Allah Ya azurta mu da shi, tun daga kansa ba mu sake haihuwa ba.
Wai ke wacce irin mace ce wacce kullum sai ta fidda sabon salon rayuwar ta? Dan daya da Allah Ya baki shi ne za ki min haka? To ki sani, duk abinda kika ga dama kiyi, amma ni ba zan shiga wannan shirmen naki ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya kalli Mustapha dake tsugune ya ce.
“Kai dana, baka da wanda ya fini, kada ka sake shirmen wannan mashiririciyar ya dame ka”.Cikin fushi Hajiya Saratu ta ce.
“Ko ka yarda ko kar ka yarda Mubarak dana ne wanda na haifa a cikina, wannan ya nuna Mustapha ba ni na haife shi ba. Na jima da wannan takaicin gami da bakin ciki, na rasa wanda zan fadawa bare ya saurare ni ko a gane abinda ya dame ni. Ka shiga magana ko kar ka shiga ni zan karbo dana, wallahi duk bala’i sai an bani dana”.
Mustapha wanda idanunsa suka rine da bakin ciki da fargaba, ya ce. “Na yarda ni ba danki bane, kin jima kina
nuna min rashin kauna, to amma sai ki sanar dani
ta inda ki ka same ni ki ka raba ni da iyaye na, kike wahalar da rayuwa ta”.
Ta ce, “Oho, ni dai komai za ayi Mubarak dana ne”.
Alhaji ya ce, “Na ce ka rabu da ita ko?”
Cikin tsananin kuka ya ce, “Momi, kin rasani har abada, ko Mubarak danki ne ko ba danki bane ni na haramtawa kaina ke, saboda kinacewa ni ba danki bane”.
Yana fadar haka ta yanke jiki ta fadi tana wasu sambatu wanda dole duk rashin tausayinka
ka tausaya mata, dole aka shiga yi mata addu’a. Aka sanar da Hajiya Lami, cikin kankanin lokaci ta iso da turaren ta, ta shiga yi wa ‘yartata turare, amma kamar turu, maguza ta ake, abin ko sauki babu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk iya hikimomin su abu yaki ci, in anyi mata addu’a abin ya sauka, sai ya dawo, kwana aka yi cikin wannan bala’in.
Mubarak ya shiga gida cikin tsananin rudewa, Mah na zaune gefen daki tana cin gyada marau ya shigo tamkar an jeho shi. Ya matsa jikinta ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya.
Ta ce, “Mubarak lafiya? Yaron maman sa?” Sai taga kwalla cikin idon sa, ya ce.Mah, akwai matsala”.Ta ce, “Kamar ya?”
Ya ce, “Na shiga uku Mah”. Ta ce, “Meye? Ka fada min”..
Ye co, “Daga gidan su Mustapha nake, wai mahaifiyar sa ce ta ce wai ni danta ne, ita ta haife ni, ko ruwa ko iska, ko mutum ko aljan babu mai raba ta dani, sai ta kwato ni”.
Tayar da gyedar hannunta, ta ce. “Anya kuwa kalau take?”
Ya ce, “Nima abinda nake funani kenan, ko tana da tabin kwakwalwa? in ba haka ba ya za a yi ta fadi haka?”
“To me Alhajin ya ce?”
“Yana ta fada, dama irin iyayen nan ne da ba su damu da ‘ya’yan su ba”.
“To ya Mustaphan?” Ya çe, “Oho, ni na taho na barshi”.
Ta ce, “Maza kira min shi, domin duk inda
yake yana cikin damuwa, kira shi in lallashe shi”. “Mah, ni kunyar sa nake ji, tsoro ma nake
Ta ce, “Kira shi, ni na damu da damuwar sa,
hakika ba zan barshi cikin damuwa ba”.
Ya kira wayar sa amma ba a dauka ba, ya kira har babu adadi, ya hakura.Mah ta rude iya rudewa, ta ce.
“Kaini gidan su, kaini in ganshi”. “Mah, me zai sake kai kafa ta gidan
ni da gidan su sai dai in shige shi”.su? Ai
Ta ce, “Sake kiran shi”. Cikin ikon Allah sai ya dauka, cikin muryar ban tausayi ya ce.
“Mubarak, na janyo ka inuwa gashi ni za ka sani cikin rana, ina ga za ka raba ni da farin ciki na. In kai dan Momi ne nisu weye iyaye na? Ni DAN WAYE?”
Ya kasa amsa masa illa ya mikawa Mah wayar, tayi sallama tace
“Dana na kaina, kana ina?” Ya ce, “Gani a gida, Momi na bata da lafiya”.Ta ce, “Zan iya ganin ka yanzu?”Ya ce, “Mah lafiya?”
Ta ce, “Ai kai ma kasan maganarYa ce, “Gani nan”.
Zaune suke akan tabarma shi da Mah, gefe Mubarak ne, ta ce.
“Kada ka damu Mustapha, kaddara ce Allah Ya dora maka, amma Mubarak ni na haifi dana, ta yaya za ta ce nata ne? Amma kayi min aikin gafara, bata da wani ciwo me kama da na masu tabin kwakwalwa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “A’a, sai dai tun ina yaro na san mahaifiyata ta tsane ni, ba ta sona, kuma kuma tana fama da matsalar jinnu, shi yasa duk abinda take yi min nake mata uzuri. kinga har yanzo tana ta buguwa, dazu ma naje Rano gurin wanda yake bata magani, da data sha komai yake sauyawa, amma yanzu shiru”. Mah ta mike ta dauko wani turare, ta ce.
“jeka a turara mata, gobe mayi magana.
Ubangiji Allah Ya bata lafiya, amma bana so ka
sanya damuwa inda za ta shafi lafiyar ka”.
Ya ce, “To Mah, na gode”. Mubarak ya biyo shi, ya ce.
Abokina”.Ya juyo ya dube shi, ya ce.
“Ina jinka”.Ya ce, “A rayuwa ka taimake ni, bana so ace ka samu damuwa a dalili na. Ni dan talakawa ne, dan asalin kauye. Ka yiwa Allah ka sanar da Momi ni ba danta bane, kaine danta. Ni bani da hadi da masu kudi, dangina kaf talakawa ne, kai ka tsamo mu daga babu, ta ya zan zama danta? Kada ka zarge ni abokina”.
Mustapha ya ce, “Ina jin wani abu a zuciya ta, nayi bakin cikin haduwa da kai, inama ban hadu da kai ba, ina ma ban sanka ba. Mubarak ka zamar min tauraro mai wutsiya, hakika haduwa ta da kai babu wani alheri a ciki”. Yasa kai ya fice.
Hajiya Lami duk abin duniya ya ishe ta, ita da ‘yarta Hajiya marka da Alhaji Sadi duk suna gidan, Mustapha ya shigo kamar wanda yayi amai da gudawa, duk ya rame, ga baki a bushe.
Alhaji Abdulmajid ya ce.”My Boy, daga ina?”
Ya ce, “Ga wani maganin a turara mata ko za a dace”. Ai ko ana turarawa ta ringa jera atishawa, ai
bacci mai nauyi ya dauke ta. Hajiya Lami ta ce, “Ni dai abin nan ya ruda ni, kaga duk aljanun da take maganar su daya Mubarak danta ne, me zai hana muyi bincike?”
Ya ce, “Ni ba dana bane, Mustapha shi ne nawa. ki dubi yadda yake ta fadi tashi akan ta, har sai da ya nemo magani. Wallahi ba zan yi magana akan Mubarak ba, don ni ba dana bane, sai taje can tayi shirmen ta, kada ku sake sa ni cikin wannan shirgin”.
Da safe Hajiya Saratu ta tashi cikin nutsuwa da hankalin ta, a dakin
sa ta same shi, wato Alhaji Abdulmajid. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Ya jikin?” Ta ce, “Da sauki”.Ta zauna gefen sa, ta ce.
“Alhaji, na zo muyi magana ta nutsuwa, ka saurare ni kaji uzuri na. Ina cikin hankali na da nutsuwa ta, ni ba mahaukaciya bace”.
Ya kalle ta ya ce, “Ina jin ki, ki fadi abinda kike so ki fada”.
Hawaye masu zafi suka ziraro mata, tace.
“Na jima ina tausayin Mustapha, don ba dana bane, sai dai na rasa ta yadda ya zo hannu na, Kullum bakin cikina ina dana yake? Ta ya na rabu da shi? A ina zan ganshi? Sai gashi yau na ganshi. Wallahi, Tallahi Mubarak dana ne, danmu ne ni da kai”.
Ya ce, “Ko? To ya aka yi muka rasa shi? Ya aka yi muka samu Mustapha?” Ta ce, “Wannan ne na rasa, amma ka
taimake ni ka dawo min da dana. Kana da kudin
da za ka karbo min dana, kana da kudin da za ka
karbo min farin ciki na. Wallahi Mubarak dankane”.
Ya ce, “Uhm, saboda ina da kudi sai in zama azzalumin attajiri? Ba na zalunci da dukiya ta, na tara dukiya da halal. To misali, yanzu asa mun karbi Mubarak, ya kike so ayi da Mustapha?”
“Duk sai mu hada mu rike”. Ya ce, “Mun zama azzalumai, mu karbi
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG