DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 13 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Mun tsaya
ya za kiyi?” Ta ce, “To ba zan auri Bahaushe ba, zan auri
yaren baban mu”.
Ta ces, “Ashe Turkey za kije?” Ta ce, “Haka nake tunani”.
“Uh matar manya, amma fa ban yarda dakeba”.
Ta ce, “Kamar ya?”
Ta ce, “Kina son Mustapha kuma na dade da sanin ko kinyi aure ba zaki iya zama da wanda kika aura ba, saboda inda’ duk kake zaton zaman aure ya
shige nan”. Ta zumburi baki, ta ce, “To auren kika yi bare
ki san kansa?” Ta ce, “No, duk ‘yan group dinmu matan aure
ne, kuma wallahi ba abinda suke Boyewa duk na san
shika-shikan auren”.Weediyan tayi dariya, ta ce.
Wato ke zama da mijin ne kawai ba ki iya ba?”
Ta ce, “Wannan shi ne zahiri. Zan ba ki shawara, arziki na Allah ne, ki ajiye makaman ki, ki yarda da kina son Mustapha, kuyi auren ku ya fi miki alheri, amma duk wannan burin naki na banza ne”.
“Ni ba zan taba cewa ina son sa ba, sai dai sonsa ya kashe ni. Kuma na tsani wannan kurmar, tunda na kula abinda nake so take so, ke na bar mata. Ni fa sai me manyan kudade, mai manyan harkoki”.
A lokacin suka nufi cikin get din gidan su,
suka yi parking. Wasu shegun motoci masu numfashi suka gani, suka hada ido ba tare da sunyi magana ba, suka
yi cikin gida. A bakin famfo suka tarar da Momin su tana
“Ku ko ina kuka tsaya?”
alwala, ta dube su ta ce. “Ga bakin ki nan nan”. Weesal ta ce, “Ni Momie?”
Suka ce suna tare da Musty, ta ce.
Ta ce, “A’a, Weediyan mana”. Tayi kalar kuka, “Momie su waye?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Uhm, kin gane wadanda muka hadu
da su a Umra din nan da muka shiga siyayya?” Ta ce, “Ni? Ni na manta shi”.
Ta ce, “Ato, yanzu kin tuna shi, gashi can sai
ki shirya kije, an kai musu komai”.Ta ce, “To”.
Ta shiga ciki, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta isa falon da aka sauke su.
Kai, hakika Allah Ya yi halitta, don Weediyan ta iya kwalliya, mace ce mai diri, akwai body mai kyau.
Tana sallama ta kai duban ta garę su, ta gano shi, ta samu kujera ta zauna.
Da fara’ar sa ya ce, “Ranki ya dade yau gani a Kano”.
Tayi murmushi ta ce, “To ya aka yi ka gano gidan mu?”
Ya ce, “Kin manta kin bani card dinki?”
Ta ce, “Na manta”. Ta kalle shi, babu abinda za ta nuna masa
inda kyan sura ne. Ya ce, “Na fada miki ni haifaffen Lagos ne,
baba na Bayerabe ne, sai dai mahaifiya ta ‘yar kasar Misra ce. Ni kadai mahaifina ya haifa, ya rasu bani da wa bani da kani. Ni ina son ‘ya’ya sosai, saboda haka nayi alkawarin ‘yan biyu zan aura ko da za ta
Www.bankinhausanovels.com.ng
dinga bani bibbiyu”.Ta yi murmushi kawai, ya ce..
“Ga amini na Saifuilah, shi dan nan Kano
ne”.
Kai Weediyan akwai jan aji, ta kalle shi kawai ta basar.
Ya ce, “Da karfina na zo, domin mahaifiya ta tana son tayi min aure, ni kuma bani da burin ayi min auren dole ko na hadi, ko na zumunta Nafi so ace ni naga mace na ce ina so, da falan za ki karbeni.
Watanni shidda da haduwar mu dake, kullum bani da lokacin kaina, ba na samun zama, saboda yanayi na harkoki na. yanzu ma na zo da Saifullah don shi ne zai dinga zuwa, saboda gaskiya sai in shekara biyu, uka ban shigo Nigeria ba. Amma zai kawo Ummi dina ku gaisa, don ta ce tana so ta ganki”.Tayi shiru, ya ce.
“Na kula ba ki son yin magana”. Ta ce, “Ba haka bane, na jí daga zuwa daya
kana batun maganar aure, ba mu fahimci juna ba”. Ya ce, “Uhm, za mu fahimta ne, bani da lokacin kaina ne Weedyan, kada ki damu, ina son ki sosai. Wallahi na fi son ki da kudi, zan iya yi miki komai”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Kin gama karatu?”Ta ce, “Mun dai kusa”.
ya ce, “To zan wuce”. Ya mike yayi rubutu a cheque ya ajiya, ta
share.
“Ki bani number dinki, saboda idan ina burin jin muryar ki”.
Ta rubuta masa, sannan ya mike har mota ta raka shi. Wasu mutane ta gani sun taho, suka tsaya a bayan sa, wani kuma ya bude mota ya shiga baya, ya kalle ta.
“Weediyan, sai mun yi waya”.
Suka ja suka tafi, ko da ta koma falo ta daki cheque din, numfashin ta kusan daukewa ya yi, saboda ganin abinda aka rubuta. Ta nufi ciki da gudu, ta ce.
“Weesal, duba nawa aka rubuta?”
Ta zaro ido waje, ta ce, “Ko dai ya yi mantuwa ne?”
Momie ta ce, “Ko kadan, Abduljalil Dara Dara ne, waye bai san su a kasar nan ba?” Tayi zaune tayi turus.
Washe gari ta fidda kudin a banki, a cikin satin ba ta da lokacin kanta, ita ce gidan mahaukata, ita ce gidan gajiyayya, ita ce asibitoci. Titina take bi saboda taimakon almajirai. Matasan da ta bawa Adai.
Www.bankinhausanovels.com.ng
daita sahu kuwa suna da yawa, har wanda ta yiwa alkawari. Haj. Marka ita da Haj. Hadiza suna hira, ta ce.
“Oho, ni halin Weediyan har tsoro yake bani, ita fa ko nawa ne da ita yanzu ta rabar. Ai gashi Allah Ya cusa mata burin ta, gashi ta samu irin wanda take so”.”Shawara zan baki, ki kama shi kam”,
Ta ce, “Ai ni kin san ba na irin wannan huldar, komai na Allah ne. Ko lokacin da take shirmen ta ni kallon ta nake, saboda shi wannan ta taba zuwa hira da shi don kawai ta ganshi ya ce yana sonta”.
Suka sa dariya, Haj. Hadiza ta ce. “Ikon Allah, Suhaila ta zo tayi nin zance, ko
ba shi ne wanda suka je har Lagos gurin sa ba ya basu miliyan goma su takwas, mata biyar maza uku?”
Ta ce, “Shi ne mana, ko kin san ba a nan ya ganta ba? Ya ganta ne a Saudi, muka hadu”. Ta ce, “Gaskiya ta more, ai kudi shi ne rayuwa”.
Haj. Marka ta ce, “Kin san abinda yasa nake rabuwa da Weediyan? Saboda tana son taimako, sannan akwai nacin addu’a, shi yasa duk iyayinta
Www.bankinhausanovels.com.ng
nake rabuwa da ita. Amma da ace son kudin ne zallah, ai da tuni na gyara mata zama, saboda ba komai Allah Yake cika maka buri ba”. Ta ce, “Haka ne, amma ita ai ta samu cikar burinta”.
“Zuwan sa daya fa, kuma sai munyi bincike mun yarda da addinin sa sannan za mu bashi, mun gano asalin sa, amma ai ba sayar masa da ita zamu yi ba”.
Haj. Hadiza tayi tsaki ta ce, “Kai Allah Ya san manufar jaki da bai bashi kaho ba”. Haj. Marka ta ce, “Oh, wato da ke ce sai
shagali?”
Mustapha shi da dadin sa suna zaune a falo,ya ce.
“Daddy, ina son magana da kai”.
Ya ce, “Ina jinka my boy”.
Ya ce, “Batun Momi ne, don Allah Ka dawo da ita, domin ni kaina ina ji a zuciya ta ba ita ta haife ni ba, kuma na jima da wannan tunanin. Abinda yake damuna ya kuma shigar min zuciya, shi ne ni din DAN WAYE?”
Alh. Abdulmajid ya ce, “Kai dana ne, ko da an gano kai ba nawa bane ba zan taba son nawa din kamar ka ba, kai ne akan komai nawa. Ni ban dauki
Www.bankinhausanovels.com.ng
mahaifiyar ka a mutum mai hankali ba, domin kotu ba ta shari’a da mutumin da yake fama da aljanu”. “Daddy, ni dai ina neman alfarma, ka dawo
min
da ita gidan nan, don zaman ka haka babu dadi”. Ya ce, “Ba zan dawo da ita a yanzu ba, domin na san ba zan iya sakin ta ba, don munyi aure cikin aminci da kaunar juna. Amma da ace ba na waige lallai da ba zan zauna da ita ba”.
Ya ce, “Daddy, aí dama zama da mata sai hakuri, kuma ni na san kana da hakuri. Hakuri magani ne Daddy, ni kam na san in ka dawo da ita ka gama min komai”.
Na ji Mustapha, abinda nake so da kai komai ya samu bawa mukaddari ne, don haka bana so ka sanya damuwa. Ina so ka koma Mustaphan ka, dan gatan baban sa, kuma don Allah ko da na kasance ba mahaifinka ba lallai ka rike ni a matsayin uba. Idan na mutu kayi min addu’a”.
Hawaye ya zubowa Mustapha, ya ce. “Daddy, kai ma ka karaya kamar ni?”
Ya ce, “A’a, rayuwa ce ita kuma shari’a
sabanin hankali ce dana”. Ya kada kai, “Shi kenan Daddy, kai mahaifina ne, kuma zan iya karbar dukkan kaddara kamar yanda na rayu cikin tsana da tsangwamar uwa”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi ma ya ce, “To zan dawo da Saratu, amma sai bayan alkali ya gama da shari’ar”. Ya kada kai, daga nan suka shiga hira akan
kasuwanci har suka gangara kan batun auren Mustapha. Ya ce, “Daddy, ya kamata aje ayi maganar
saka rana”. Ya ce, “Na fada maka ba zan amince ba waye ubanta? Na fiso in nema maka auren ta hannun mahaifin saboda ita zina bin jini take my boy”.Ya ce, “Daddy, tana da uba, wallahi wani akasi aka samu…”. Ya warware masa komai, ya ce.
“To, to ni kuwa ina da aboki dan sarkin ne, don ko yanzu sarki ya mutu lallai shi ne mai jiran gado, zan je masa da wannan maganar, domin in gano gaskiyar al’amari.
Yau gaba dayán su za su nufi garin Kaltingo don kai ziyara, Umma ce da yaranta biyar, amma babu mai gidan. Sun shiga mota cike da farin ciki a zuciyar su, a lokacin motar Mustapha tayi parking shi da Alpha ne, ta gansu saboda haka ta fito ta tako har inda suke, tayi kyau kamar furen fulawa. Mustapha duk bacin ran da yake indai zai ga Izzat sai yaji dadi, a yanzu ji yake kamar ya dauke ta ya
Www.bankinhausanovels.com.ng
rungume.Ta karaso ta ce, “Ranka ya dade, tun jiya na sa ran ganin ka, ko dai ‘yar fashin miji ta kwace min kai?”
Ya yi dariya, ya ce, “Ai ni naki ne”. Alpha yayi murmushi ya ce, “Wa ce ‘yar fashin miji?”
Musty ya yi dariya, ya ce, “Wai Weediyan”. Ya gyada kai, ya ce, “Ai kanwar mu ce wannan”.
Mustapha ya ce, “Ina zuwa haka?”Ta ce, “Za mu garinmu Kaltingo”.
Ya ce, “A’a, sai kuma yaushe?” Ta ce, “Za mu kwana biyu in munje”.Ya ce, “Amma babu labari?”
Ta ce, “Jiya na zo ance ba ka nan”. Sai taji kunya har ta rufe ido, ya ce. “To sai kun dawo, ni ma gobe zan wuce”.
Ta ce, “To Allah Ya kiyaye”. Ya fidda kudi a aljihun sa, ya mika mata. “Gashi, kunyi tsaraba”.
Ta boye hannu, ta ce, “Ai Abba yayi mana”.
Ya tsare ta da ido, ya ce ta karba.
Ta ce, “To ai in na karba babu abinda zan yi da kudin”.
Ya ce, “In kunje Kaltingo in kin shiga gidan
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sarki kiyi ta bawa jama’a”.
Ta ji faduwar gaba, don yadda take ji a ranta lallai za ta je gidan Sarki. Sai taji jikinta yayi sanyi, don haka sai yayi shiru.
Ta ce, “Zan shige, sai munyi (charting) ko?” Ya mika mata, ta karba, ta ce, “Na gode”.
Suhaila an soma nauyi, don cikinta ya yi wata biyar, suna zaune ita da maigidan suna hira, ta ce. “Oh, yaushe za muje Gombe?”
Ya yi murmushi ya ce, “So nake sai kin haifa min Fadima”. Tayi murmushi ta ce, “Oh, ni da so nake in haifi Mubarak”.
Ya yi dariya, ya ce, “Lallai kina son shi, ko da yake so ba karya bane, nima Fadima sunan masoyiya ta ne, wacce sonta bai taba gushewa a zuciya ta ba, haka kullum tausayin ta karuwa yake a gare ni. Ina tsananin kaunar ganinta”.
Ta shaki kishi, ta ce, “Ko? To ai munyi anko, nima sunan Mubarak bana jin za’a samu wanda nake so irin sa”.
Ya ce, “Ban ga laifin ki ba, don nayi soyayya na san zakin ta na san dacin ta”.
Dariya yake, ya ce, “Zan sa miki Mubarak har dozin daya in kina so”.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG