DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 14 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Ya yi dariya, ya ce, “Lallai kina son shi, ko da yake so ba karya bane, nima Fadima sunan masoyiya ta ne, wacce sonta bai taba gushewa a zuciya ta ba, haka kullum tausayin ta karuwa yake a gare ni. Ina tsananin kaunar ganinta”.
Ta shaki kishi, ta ce, “Ko? To ai munyi anko, nima sunan Mubarak bana jin za’a samu wanda nake so irin sa”.
Ya ce, “Ban ga laifin ki ba, don nayi soyayya na san zakin ta na san dacin ta”.
Dariya yake, ya ce, “Zan sa miki Mubarak har dozin daya in kina so”.
Ta ce, “Uhm”.
Ta mike, ya ce, “Kin aureni ba ki sona saboda nai miki tsufa, ita ko an raba ni da ita tana kuka, ai ba darajar ku daya ba”.
Ta juyo tana kallon sa, amma bata ce masa komai ba.
Khalid ya shigo sanye da doguwar riga da hula tashi ka fiya naci, da Alkur’ani a hannun sa.
Ya dago ya ce, “Mal. Khalid, an dawo?” Ya ce, “An dawo Abba”.
Ya zaúna ya ce, “Abba, ina son in halarci kallon Musabaka na duniya, malaman mu sun ce duk wanda yake ganin iyayen sa za su iya daukar nauyin sa to an bayar, amma ni ban bayar ba sai naji ra’ayin ka”.
Ya ce, “Haba Khalid, ai ba zai gagara ba. Zanso ace shekara mai zuwa zaka je gurin a matsayin
dan takara ba dan kallo ba”.
Ya ce, “Amin Abba, kowa da iyayan sa za shi, kaima sai kaje, da Aunty Suhaila, sai kuyi Umra”. Ya sanya masa yatsa a bakin sa, ya ce, “Shshhh”.
Umma Halima a yanzu hankalin ta ya kwanta, sam ta daina damuwa, saboda ganin yadda abin ya
zama, kuma lauyarta ta ce kotu za ta kori shari’ar
Www.bankinhausanovels.com.ng
saboda Haj. Saratu bata da cikakken hankali, tunda mahaifiyar ta da mijinta sun fada. Kuma Weediyan ta sake kwantar mata da hankali, tana kaunar yarinyar nan sosai, saboda karamcin ta.
Ba su isa garin Kaltingo ba sai daf da magariba, ba asan da zuwan su ba. Kofar gida Mal. Sallau ne zaune suna alwala ya ga mota tayi parking, ya zubo ido yaga waye? Sai yaga ashe kanwar sa da iyalinta.ne
Hannu kawai ya dago yana, “Lale da zuwa
Su kuma suka shiga gidan, direba shi ne ya zo don bin jam’i, Inna Ladidi taga mun shigo ta washe baki.
“a’a, mutanen Kano ne? Sannun ku da zuwa,
lallai kun sha hanya”.
Duk suka aje kayan su, su ma sallah suka fara yi, sannan Umma ta bude katuwar kula ta zubawa direba abinci da lemo mai sanyi da’ robar ruwa, aka kai
waje. Dadi ya cika Inna ladidi, Allah Ya kawo bakon da zai ciyar da masu gida, don ka’idar su basu yin girki, ins ko sunyi sai dai kowa ya ci nasa, gaba daya surukanta babu mai ganin girmanta, kuma babu mai raga mata. A yanzu duk mugun halinta surukanta
Www.bankinhausanovels.com.ng
sun fita, don matar Sallau har dambe suke, shi yasa ba ta da tartibin mai kula da ita. Duk burinta na haihuwar ‘ya’ya mazan gashi dai ta haifi mazan amma mace ke neman rike gidan.
Dama akwai dakin da take sauka ta in tazo, duk zuwa sai ta sake gyara, don in ta tafi duk abinda ta bari a ciki sai an haura an dauke. Yanzu Inna Ladidi da rawar jiki ta soma shara, don ta gyara. Sahura matar Sadau na fadin, “Kwadayi
mabudin wahala, Allah wadaran kwadayayye”. Inna Ladidi ba ta tanka mata ba, ta share, ta shigar musu da kayan su. Umma ta ce, “Inna, mun same ku lafiya?”
Ta ce, “Lafiya lau, nima kwnaakin nan kina zuciya ta,na kasa zuwa amma ina son zuwa gurin ki’.
Ta ce, “Ke ko lafiya?” Ta ce, “Eh to, ai sai mun zauna”.
Ta kalli Izzatu ta ce, “Ke ina jikan nawa?”
Bata ji ba, bata kalle ta ba, don haka bata gane me take cewa ba.
Ta dubi Surayya ta ce, “Yan matan Kano, yaushe za ki kirani inzo inyi iniki zaman daki?”! Tayi murmushi ta ce, “Ai ni karatu nake, da saura”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta mike ta barsu don su huta, Umma ta ce.Inna, ga dafaffen abinci, sai ki diba”.
Da rawar jiki ta dauki katuwar kular abinci, don rabonta da abinci tun kokon safe, taje ta diba. Sai da ta ci ta koshi, ta aika da shi inda take so, sannan ta ce da sirikan nata su kawo kwanuka. Sahura ita ce tantiriyar cikin su, kai tsaye ta
fito ta ce. “Ai munyi zaton ba zaki bamu ba? Don gulma da son zuciya shi ne aka ba da abinci, sai da aka aika da shi makota don neman suna? To ki kiyaye mu, ni ban son rainin hankali”.
Harira ta ce, “Haba Sahura, gidan fa da baki”. Ta ce, “Su waye bakin? Ni bana nema agun kowa, saboda haka bana kwadayi’.
Sun san rigima take nema, suka yi mata banza. A lokacin Sallau ya shigo.
“Lafiya nake jin hayanita?”
Ta ce, “Ato, gata nan kinibibinta ne ya tashi, ta ga mutanen Kano sun zo”.
Ya ce, “Ke Inna wacce iri ce?” “Ai kai sai ka fada mata tunda ta haife ka”.
Gaje ta harare ta tare da yi mata tsaki, ya kwace abincin da kansa ya raba, yayi dakin da su Umma suke, ya daga labule ya ce. “Sannun ku da zuwa”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya shiga ciki ya samu guri ya zauna, ya ce..
“Halin Inna sai ita, sai take shiga sabgar yara”.
Umma ta daga masa hannu, ta ce. “Duk abinda ya faru a kunne na, saboda haka abinda kayi dai dai ne, ace mace ta fi uwa”.
Ita ko Izzatu sai hararar sa take, ya ce. “Ato, ke kanki kin san halin Inna, ba dadi ne
da ita ba. Wacce wahalar tace ba ki sha?” “Uhm, ai komai ya wuce”.
“Haka ne fa, Allah Ya bamu ya taki”. Ta ce, “Ko? Ai dole ka sake hali”.
Ya mike, “Ina zuwa, bari yanzu zan dawo”.
Ya fita, can ya aiko yaro da kunshin tsire, ya ce a kawo musu.
Umma ta karba ta ce, “An gode”. Washe gari duk yayunta da matan su sun shigo an gaisa, haka kowa ya aiko da abin karyawa,
kuma sun shigo sun gaisa.
Ta ce ta zo musu ta kwana biyu. Sun nuna murnar su, sunyi hirar su.
Inna Ladidi a gurinsu ta sha tea mai kauri, Umma ta raba musu tsaraba don kayan ta kwance da na ‘ya’yanta duk ta kawo musuz. Sun nuna murna, haka kayan mijinta kwance
Www.bankinhausanovels.com.ng
duk ta rabawa ‘yan uwanta, har sabbi ta bi kannen mahaifinta don kwata-kwata ba su zauna a gidan ba, yawo suka yi tayi gidajen ‘yan uwa da abokan arziki. Garin Kaltingo ya samu ci gaba sosai, komai nasu ya ci gaba.
Da daddare suna zaune Izzatu ta ce, “Umma, ban ji kinyi maganar zuwa gidan Sarki ba, zan je zan kai kaina fada”.
Ta ce, “Kiyi hakuri irin su manya ne, ganin su
sai an kai ka. Kiyi hakuri, ina ji a raina lokacin
bayyanar gaskiyar al’amari yana nan zuwa”.
A lokacin Inna ladidi ta shigo ta samu guri ta
zauna, ta dubi Umma ta ce.
“Yar nan, kiyis min aikin gafara, na gano gaskiya kamar yadda mijina ya so in gane. Wato zan sanar dake wani al’amari da ba ki sani ba.
Musbahu tsohon mijin ki baban Izzatu ya zo gidan nan neman ki da kuma neman ‘yarsa, a lokacin ina tsaka da mummunan hali na. Maganar gaskiya ni na aika na ce ace masa Izzatu ta mutu”.
Gaban Umma ya fadi, “Ta mutu kamar ya?” “Saboda n
a gano yana son karbe ta, saboda bana so kiji dadi, nafi so inga ba kya rayuwa, nafis so ki mutu kamar mahaifiyar ki in gaji gida, daga ni sai ‘ya’yana. Nafi so bakin ciki ya kashe ki”. Ta sa kuka, “Yanzu nayi nadama, kullum fada
Www.bankinhausanovels.com.ng
nake yi da Sallau da Sadau akan abinda suke yi, na gano hakkin ki ne. Shi kuma Sallau ban san cewa yana zuwa ya hana auren Izzatu ba sai daga baya, amma ki yafe min, wallahi duk hanyar da zan bi inga Musbahu in fada masa ‘yarsa tana nan na bi ganinsa ya gagara”.
Umma ta dubi Inna ido fal kwallah, ta ce. “Au, kin san Izzatu ‘yarsa ce?”
Ta ce, “Na sani, saboda yanayin rashin kwarin jikinta lokacin da aka haife ta, kawai bana so ace kin zama matar Sarki, to gashi nan kina cikin rufin asirin Allah, ni kuwa kullum ina cikin rigima da sirikai, su dake ni babu abinda ‘ya’yan nawa zasu yi. Ni dai fata na kiyi min gafara, ki yafe min, na zalunce ku ke da mahaifiyar ki, har da mahaifin ki”.
“Inna babu komai, ni na yafe miki, amma su ban da ikon yafe nasu, sai dai su. Yanzu ya za a yi inga Musbahu ko inga mabaifin sa?” “Sarki ai baya nan, ya je Umra”.
“Ba zan bar garin nan ba har sai na sada ta da dangin mahaifin ta”.
Alh. Abdulmajid a office dinsa dake birnin tarayya aka yi knoking kofa aka shigo, ya daga ido yayi dariya, ya ce.
“Yarima mai jiran gado”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya yi murmushi, suka yi musabiha, ya nuna masa gurin zama. Sun gaisa suka shiga hira akan kwangilar (furniture) da za a yiwa gwmanatin tarayya, shi aka bawa kwangila. Ya ce, “Yarima, ina son tambayar ka, bayan
kai Musbahu akwai wani ne a gurin ku?” Ya girgiza ya ce, “Wani yarona ne zai auri wata yarinya, da bincike yayi sai aka ce ba ta da
uba, to kuma sai aka ce min jikar Sarki ce, wai…..
Ya dakatar da shi, ya ce, “Ya sunan ta?” Ya ce, “Izzatu Musbahu Kaltingo”.
“A ina take?” Ya ce, “A kano”.
Ya ce, “Yata ce, ni na haife ta, ban taba rayuwa babu tunanin ta ba, ance min ta rasu, sai daga baya wani ya sanar min karya ne. Nayi duk yadda zan sadu da Fatima amma abin ya kai, wai me yasa Hausawa muke fama da matsalar matar uba ne? Ko abin haka yake a sauran yarerrika? Ko ko sai mu Hausawa?”
Sai ya sunkuyar da kai, numfashin sa ya ringa
sama-sama, sai da Alh. Abdulmajid ya mike ya dauko masa ruwan sanyi ya sha.
Ya kira number din Musty ya ce ya turo
number din Izzatu, ya ce.. “Ai ba ta daukar waya sai (text) kuma ta tafi
Www.bankinhausanovels.com.ng
Kaltingo”.Ya ce, “Okey”.
Ya dubi Yarima Musbahu ya ce, “Ai kaji Izzatu na Kaltingo, kuma ka san kurma ce”. Ya mike a razane, ya ce, “Kur me?”
Ya ce, “Kurma ce”.
“Oh my God! Na ji dadin ganin ka Alh. Abdulmajid, insha Allah gobe zan wuce Kaltingo”. Suhaila na falo ta ga shigowar maigidanta, ta
tare shi cikin fara’a kamar yadda ta ganshi, ta ce. “Ah, Sweet Derling, ince ko yau an hadu da
Fatima? Domin ban taba ganin fuskar ka na walwala kamar yau ba, haka ban taba ganin farin cikin ka kamar yau ba”.
Ya matso gare ta, ya sa hannu ya shafi cikinta, ya ce.
“Dana taya uban ka murna, yau ya kusa
haduwa da cikon farin cikin sa”.
Cikin farin ciki Suhaila ta ce, “Muna taya ka murna, Allah Yasa farin cikin naka shi ne alkhairin gidan ka. Khaleed, zo mu taya abban ka murna”.
Ya shigo yana fadin, “Me ke faruwa?” Ya ce, “Gobe za mu wuce kal
Kaitingo”. Khaleed ya ce, “Ashe zan hau doki”.
Cikin murna Suhaila ta ce, “Za muje Gombe
Www.bankinhausanovels.com.ng
gobe gobe?”Ya ce, “Insha Allah”.
Weesal ita da Mubarak sun tabbatar da kaunar su, don sun yiwa juna alkawarin aure. Hajiya Marka tayi murna kwarai, ita ko
Weediyan matar manya, ga soyayya na cin zuciyar ta ga shegen buri a ranta, don iyayen Abduljalal dara-dara sun zo tambaya amma tun bayan nan bai kuma zuwa gurinta ba, amma kullum account dinta cikin kudi yake, haka duk kasar da yake yakan turo mata da duk abin bukata.
Haj. Aisar mahaifiyar Jalil ta zo har Kano, ta yaba da kyan tsarin surukar tata. Ta ji dadin karbar da aka yi mata, tayi musu kyauta ta ban mamaki, don ta basu damar su kawo matasa mutum ashirin wadanda za a dauka aiki a kamfanin su.
Weediyan an samu abinda ake so, don ta *
zama uwar marayu ta kika, burinta ya cika. Alh. Fatawi shi ne mahaifin ta, dan asalin kasar Turkey ne, yana daya daga ma’aikatan kamfanin su Mustapha, dalilin auren sa da Haj. Marka wataran ya kawo wa Alh. Abdulmajid ziyara, ita kuma Haj. Marka ta kawowa yayarta ziyara, a lokacin mijinta na fari ya rasu, to anan Alh. Fatawi ya ganta ya nuna yana sonta, dama shi yana Nigeria
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG