DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 5 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

kwakwalwa za a kai Haj. Saratu? Ko ya lallaba ta su wuce kasashen waje a gwada masa kwakwalwar ta?
Ji yayi wayar sa tana neman agaji, ya dauka, dansa ne Mustapha, ya ce.Ya aka yi Boy?”
Mustapha yayi murmushi, “Barka da yiniDaddy”.
Ya ce, “Sai yau ka tuna dani?” Ya ce, “Na isa Daddy? Wane ni? Ko kamanta dazu ma munyi waya?” Ya ce, “Haka ne, tsokanar ka nake yi”.
Ya ce, “Daddy, dama dazu mantawa nayi, ya kamata aje gidan iyayen Izzat ko? Na fada

maka ‘yar Alh. Habi Salga ce”.Ya ce, “Na ganshi rannan sun zo office dina shi da ‘yan office dinsu, har na ce ashe dana ‘yarka yake so? ya yi ta dariya, ya ce ai ya baka”.
Dadi ya cika Mustapha, “Kada ka damu, za a yi bikin ka da ita, sai in sako maka ita a jirgi ko?”
“Daddy na Allah Ya biya maka, kamar ka
san na bar Nigeria har abada”.
“Kai kadai nake da shi Mustapha, kana nufin za ka rabu dani da dangina? Nafi so ka huce, zan kawo maka ziyara mu zanta”.
Ya yi murmushi, ya ce, “Daddy, ina kewar ka, ina son ganin ka, don dama da son ka na rayu”. Suka yi sallama suka aje wayar.
Izzatu rayuwar ta tayi kunci saboda rashin abin sonta a kusa, don ma Surayya na kwantar mata da hankali, kuma sukan raba dare suna (charting) suna soyayya, suna samun ci gaba kwarai.


Yau ma kamar kullum tana (online) ta ganshi, ta ce.
“Ya kake?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Ni kin ganni nayi aiki na gaji,  amma ke na san yanzu kina kwance”.
Murmushi tayi ta ce, “Ya aka yi ka sani?” Ya rubuta mata, “Jiki na ya bani”,
Ta turo masa, “Ko kasan ‘yan gidan ku sun
turo ranar Lahadi za su zo?” “Amma naji dadi, na kuma yi murna”.
Ta ce, “Uhm, ance can Gombe za su”.
Ya ce, “Ai kina da babban matsayi, ko
birnin Sin ne za a je neman auren ki”.
Ta murmusa, ta ce, “Wai ko kana damuwa da rashi na?” Ya ce, “Sosai ma, amma da jin dadin
kalaman ki da kullum za ki fada min”.
Ta tura masa hoton hawaye, “Inama ina da
kunne inji muryar ka, don na san zata yi dadi”. Ya tura mata, “Ki daina hawaye, duk wata
cuta a duniya tana da magani, kada ki damu”.
Ta ce, “Babu komai, ko haka Allah Ya barni na gode Masa. Musty kada ka guje ni, ina son ka, son da ban taba yiwa wani ba, kada ka guje ko da kaji ajalina. Nayi alkawari zan gayawa duk wanda zai aure ni gaskiyar lamari, saboda gudun tijara a zamantakewar aure”.
“Kada ki damu, ko ya kike ina son in tabbatar miki ni da ke mun dace”.” Ta ce, “Haka ne, batiri na yayi (low), sai gobe”.
Ya ce, “Shi kenan mata ta”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Iyalan Haj. Hadiza sun taru don su kwantarwa Mah hankali, amma hankalin su ya yi masifar tashi da suka ji matar Alh. Abdulmajid ce, domin yana daga cikin manyan attajiran kasar nan, kuma babu ruwan sa da girman kai. To amma abin nufu, komai na yanzu duk abinda zaka yi muddin kai talaka ne to kai ne a kasa.
Sun shirya yadda za su samu lauya kafin lokacin shiga kotu, a wannan lokacin ne Baba Halima ta ce Haj. Hadiza ta taba damuwa da damuwar ta.
Shi kam Mal. Bala ya je duk ya sanar da ‘yan uwansa, sun yiwa lamarin addu’a, domin sun san duk da nasu ne, to ya ma ża a yi su dauki Mubarak su ba da? Yaro na gari, kai ai abin akwai mamaki.
Baba Halima, wato Mah sam ta kasa kwantar da hankalin ta, ta hana kanta sukuni, duk  ta damu. ‘Yan uwa da dangi da mijin ta duk suna ta
bata hakuri amma sai ta ce. “Shari’a sabanin hankali ce, ku rabu dani, ni kadai nasan irin tunane-tunanen da zuciya ta takeyi”.
Har rubutu Mal. Bala yasa aka yi mata don
zuciyarta ta samu nutsuwa.
Mubarak ya same ta zaune kan sallaya, hannun ta rike da Alkur’ani mai girma, ta ajiye, ta juyo gare shi.
Ya ce, “Mah, zan tafi gurin aiki”.
Ta çe, “Ka san gobe ne shiga kotu?” Ya ce, “Na sani”.
Hawaye ya zubo mata, “Mubarak ni ce uwar
ka, bani da wani da a duniya da ya fi ka”. “Ni ma bani da iyayen da suka kai ku, ki daina damun kan ki, asa ayi bincike. Ko karfin kudi ya sa an basu ni ba zan so su ba, ke kece uwa ta, wacce ta sha wuya. Hakika ba zan taba hada kaunar ku ke da Baba da wani ba, saboda haka ki kwantar da hankalin ki”. Muje zuwa.
Suhaila ta zo gidan Mah cike da kayan arzikin da, less da shadda, da atamfa, da (plat shoe) ta kawo mata. Yini suka yi tana kwantar mata da hankali, da za ta tafi ta bata kudi dubu goma. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi godiya, ta kuma bata dubu biyar, ta ce. “Ki ajiyewa Baba”.
Ta ce, “Na gode Suhaila, Allah Ya zaunar dake lafiya. Kin same ni hankali na ba a kwance ba, da na daka miki yaji nayi miki garin awara”.
Ta ce, “Kuma ina so, ki bari sai wani zuwan, kafin inzo zan aiko kiyi min”.
Sai magariba ta tafi, tayi ta jan lokaci don su hadu da Mubarak, amma sam ba su hadu ba.
Iyayen Mustapha sun je maganar auren Izzat, kai tsaye Gombe aka nufa da su, don neman auren. Za su kai kudin zance da gaisuwar iyaye. Sun isa wani gari wai shi Katingo, wai don
ma da motoci masu numfashi suka je. An karbe su
hannu biyu, don an nuna musu karamci.
Sun kai dubu dari biyar, iyayen Izzat sun nuna ba za su karbi kudi da yawa ba, sun fi son albarka, su kuma sun nuna a karba babu komai, sun san ai gidan manya aka je neman aure. Sun yi sallama da su sun nufo hanyar Kano cike da ganin irin karramawar da aka yi musu.
A yau kotu a cike take da jama’a ana ta shari’a, Mah kanta a kasa tana yiwa Haj. Saratu Allah Ya isa, don tunda take ko ta hanyar kotu bata taba bi ba, balle ta shiga ciki, yau gashi ana karar ta.
Ji tayi me gabatar da kara ya ce.
“Ina Mal. Bala da matar sa Halima?” Suka fito cikin shiga dai dai, sannan aka nemi-Haj. Saratu itama ta fito aka gabatar da shari’a.
“Haj. Saratu tana karar Mal. Bala da mai dakin sa Malama Halima akan tana zargin dansu
Mubarak danta ne da ta haifa da cikin ta”. Alkali ya ce, “Malama Halima, kinji zargin da ake miki”. Ta ce, “Ni ce mahaifiyar Mubarak, dana ne
da nake da shi kwalli daya”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai idanun ta suka kawo kwallah, ta ce.
“Dana ne, bana tantama ni na haife shi, na raine shi har zuwa yanzu da suka hadu da danta, shi ne tana ganin sa ta ce danta ne”. Alkali ya tambayi Haj. Saratu.
“Ko kina da shaidar cewa yaron nan naki Ta ce, “Tunda na haifi dana Mustapha zuciyata ta cika da kokwanto ko dana ne? Dalili da yasa ban taba jin son sa ko sau daya ba, hasali ma komai nake masa dauriya nake, kullum cike nake da tunani gami da addu’ar Allah Ya bayyana min gaskiya, kwatsam sai ga Mustapha da Mubarak sun zo. To a wannan lokacin da nayi ido biyu da shi na tabbatar dana ne, shi yasa na kawo abin
kotu, don hukuma ta karbar min yaro na ta bani”. “To yanzu shi mijin ki ya san da wannan maganar?”
“Ya sani, sai dai bai amince in zo kotu ba, don shi ya ce bashi da dan da ya fi Mustapha, nima kuma inaji a jikina Mustapha ba dana bane”.
Alk
ali ya yi rubuce-rubuce, ya ce ya daga
sauraron karar zuwa 21 ga watan uku, wato watanni biyu kenan. Jama’a da dama sun soma mamaki, don abin
ya girgiza duk wanda yake kotun, don ana mamakin wannan murdadden lamari.
Hankalin Alh. Abdulmajid ya tashi, don bai dauka zancen ta da gaske bane, sai da abokan sa suka ringa tambayar sa wai Mustapha ba dansa bane?
Ya ce, “Ni ne na haife shi, kawai hudubarshaidan ce yayi mata, kuma kanta ta yiwa, to sai me?”
Abokan sa suka dinga sanar da shi wannan lamarin, ranar bai runtsa ba. A yau ya tabbatar Mamie so take ta wulakanta shi a idon duniya, lallai zai nemi hirji tsakanin ta da shi, yana kuma rokon Ubangiji ya bayyana masa gaskiya, kuma Allah Ya sada shi da iyayen sa indai ba sune suka haife shi ba.
A babban filin saukar jirage na kasar Turkey jirgi ne ya sauka, mutane na fitowa. Alh. Abdulmajid sanye yake da manyan kaya na kasar Hausa, jama’ar da suke fitowa a jirgin duk yawanci ‘yan kasar ne, kana ganin sa ka san cikakken dan Nigeria ne, kuma Hausa Fulani. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya fito ne ya tsaya, mota ta zo ta dauke shi zuwa garin Istanbul, yana ji a ransa zai ba wa Mustapha mamaki, don ya san zai ji dadin ganin sa. Yana son ya nunawa Mustapha kauna da soyayyar sa, don ya san shi ne dan da ake so.
Mustapha na zaune yana cin abinci, gefen sa Juice ne, daya gefen sa babban aminin sa ne Ahmed, su haka suke kiran Ahmad.
Ahmad ya dubi Mustapha, ya ce, “Mert (haka Turawa suke kiran Mustapha) kana nufin ba zaka ba? A gaskiya ba ka kyauta ba, zai girmama mu ka ce ba zaka ba?” Da yake wani abokin su ne ya shirya musu shan shayi, don su wannna ba karamar karramawa
bace, mutum ya gaiyace ka shan (tea).
Ya ce, “Kawai yau jikina ne babu dadi”. Ahmad ya ce, “Na kula da kai kana son sanya damuwa ne a rayuwar ka, kai kamar ba malami ba?”Suna cikin maganar suka ji ruwan sama, da (knorking), suka ba da damar shigowa.
Kamar a mafarki ya ga mahaifin sa, ya mike
da gudu ya rungume shi, ya ce. “Daddy na, baka ce min ka taho ba? Ai da naje na dauko ka”. Ya ce, “Ai dama so anke ka ganni
kwatsam”.Wayyo dadi! Daddy barkan ku da isowa”. Ahmet ya taso ya rungume Daddy suka dangwara kai suka hada kai, dama wannan ita ce gaisuwar mutanen kasar Turkiyya.
Ya zauna suka gaisa, ya kira yaran gidan sa Miraty ya shigo da sauri, yana ganin Alhaji yayi masa gaisuwa irin ta ‘yan kasar su, sannan ya yiciki da sauri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhaji ya shiga dakin sa yayi wanka, ya sanya kananan kaya ya fito, ya tarar Miret ya fito shi ma yana jera kayan abinci, Alhaji ya yi murmushi ya ce.Sannu da aiki, har ka gama?” Ya zauna yana ci Mustapha na gefen sa, Alhaji ya ce.
Ina Ahmet?”Ya ce, “Ya fita. Amma Daddy na ji dadi da zuwan ka sosai, saboda ka zo a lokacin da nake bukatar ka”.
Ya yi murmushi ya ci yayi hani’an, sannan suka fita tamkar abokai, don gaskiya shigar kananan kaya suka yi.
Ya je gurin Jasnen family, su da yake duk
‘yan kasar kowa da sunan family dinsa a karshen
sunan sa. Babban family ne, kuma tare suke
kasuwanci shi da mahaifin Ahmet, wato Ahmet Jasnen.
Hakika mutanen Turkey mutane ne masu karamci da nuna soyayya, haka nan mutane ne masu masifar son ‘ya’ya, shi yasa da Mutsapha ya sanar da Ahmet matsalar sa abin ya girmama, don sam kwakwalwar sa ta kasa daukar zancen.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *