DAN WAYE? CHAPTER 6 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 6 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

mata. Sai dai zan so ace kin kasance mai yafiya
mai afuwa akan mutumin da kike ganin ya zalunce
ki Kin san Allah Yana son bayin sa masu yafiya
Izzat tayi jigum tana mamakin wannan
sako, tayi kamar ta goge sai ta barshi.
Da safe da ta idar da sallah tana cikin shafa
addu’a wayarta ta motsa, sai da ta shafa addu’a ta
dauko.
Salam Www.bankinhausanovels.com.ng
Hasken idaniyata, rayuwa ta. Kin hana
zuciya ta sakat, bana iya bacci, ba na iya cin
abinci, komai na wa ya tsaya, amincewar ki nake
nema. Da fatan kin tashi lafiya, kin sanya ni cikin
addu’a..
Izzat ta jima tana karanta sakon, waye
wannan?A ina ya santa? Wa ya bashi lambarta?
Ta goge sabon sakon har da na jiyan ma
tana fadin.
“Ba zan yi soyayya ba, nayi banji dadinta
ba”

Ta ci gaba da sha’anin ta, don bata sa abin a
ranta ba balle ya dame ta, haka bata sanar da
kanwarta ba, bata kuma gaya wa mahaifiyar ta ba.
Mustapha yana zaune yana jiran k0 za ta
aiko masa da amsa, anmma shiru tamkar ya shuka
dusa. Hakan ya sanya jikinsa yayi sanyi matuka,
bai hakura ba kullum zai aika mata da (text) sau
uku ko fiye da haka bata taba bashi amsa ba.
Haka zuciyar sa na raya masa yaje gabanta
tadi ya same ta, to amma ya san ba zata saurare shi
ba.Yau kimanin sati biyu, yau sam bai aika
mata da sako ba. Yau (weekend) baya jin dadi, ya
damu kwarai ya samu Izzat
Ya samu Momi cikin kwalliya, ta juyo ta
dan dube shi ta ce.
“Boy, lafiya?”
Ya ce,
“Ban jin dadi Momi, ina da
damuwa”.
Ta ce, “Ba za ka rasa kanka da damuwa ba.
Ni fita zanyi, zan kai Hajiya gidan wani mai
magani (wato babarta da bata da lafiya)”.
“Momi ba nace ayi hakuri da zuwa gidajen
magungunan nan ba?”

Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai ta ce, “Ai shi sauki na Allah ne, ba a san
a inda waraka take ba, mu dai fatanmu mu samu
nasara
Ya ce, “To Allah Ya sauwake, sai kun
dawo”
Ya kwanta, bai fi rabin awa ba sai yaji
wayar Mubarak, ya ce ya shigo cikin gida baya jin
dadi.
Ya ce da shi, a’a shi dai ya fito yayi masa
sannu.
Mustapha ya mike ya je ya sa shi ya shigo.
Bai taba shigowa gidan ba sai yau, ya ringa kalle-
kalle, sai ga Alh. Abdulmajid ya shigo.
Sun jima suna hira har Alhaji ya fita suna
falo.
Izzat tun dare bata ga (text) ya shigo ba, sai
taji ta damu, domin ta soma sabo da kalamai masu
dadi da faranta rai.
Da safe ma shiru har biyu, sai taji ta kasa
Jurewa, har Surayya na tambayar ta yau ko lafiya?
Ba ta dai tanka mata ba ta kwanta kan kujera, ta
dauki wayarta ta rubuta. Text
Salam!
Yau ko lafiya?
Mustapha ya sake dubawa ya ga sakon daga
Izzat yake, yaji dadi sosai. Ya dade yana ta
maimaitawa, ya yi kamnar ya bata amsa, sai yaki
Izzat taji shiru har lokacin bacci, sai taji ta
damu, taji inama tana da kunne lallai da ta buga
wayar sa taji lafiya. Anya Izzat ba ta kamu ba?
Ta rufa cikin bargo ta kasa bacci, a karo na
biyu ta sake daukar wayarta ta rubuta.
Salam! Www.bankinhausanovels.com.ng
Na damu da in san cewa kana lafya? Ina
Son in san kai waye? Ka taimaki zuciya ta in samu
sukuni don inyi bacci.
Mustapha ya karanta, ya kalmashe kafafun
sa yana murmushi, yaji sanyi cikin ranshi, ya
rubuta mata.
Salam! Ina cikin tsananin damuwa, domin
CIwo ne ya dameni, zuciya ta na cikin tururi.
Ba wani bane ni face masoyin ki, ina son ki
kwanta kiyi bacci mai dadi.
Sakon na samunta ta tashi ta zauna tsakiyar
gado tana mai da amsa.
Ba zan iya bacci ba, bansan sanda zuciyara
ta damu da kai ba, bana son inyi makauniyar
sOyayya, ka daure in san kai waye”
Ya yi dariya mai isar shi, ya sake tura mata.
Izzat, na jima bana bacci kamar yadda duk
dan Adam ke yi, son ki ya hanani yin walwala,
kullum ina cikin fargaba. Ni mai laifi ne a gurin
ki fatana kiyi min afuwa.
Ta karanta, ta mai da mashi.
Wanne laifi kake da shi a gurina? Fada min
Naji Gani bana ji da zan so inji kalaman
ka ko na samu sanyi cikin zuciya ta.
Mustapha kalmomi sun yi masa dadi
matuka, ya jima yana karanta su, ya rubuta mata.
Ki kwanta kiyi bacci kada ki makara gurin
sallar asuba.
Ta rubuta masa.
Na kasa, ina son in san waye kai?
Ya mai do mata. Dole ki san ka waye ni, domin nine baban
ya yan mu daza ki haifa mana
Nifa kurma ce, taya iyayen ka
ZaSu barka ka auri nakasasshiya?
Ya sake tura mata
Ina sonki haka, fatan zaki amsheni duk sanda kikai ido biyu dabj
Tashi surayyah  tayi ta kashe wuta,
hakan ya sanya Izzat kwanciya tare da kashe
Wayarta
Shi kuwa Mustapha da yaji shiru sai ya
kwanta yana hango nasara cikin soyayyar su, ko
zai yi? Muje zuwa.
Da safe har sha biyu ba ta bude waya ba
sakamakon aikin da suka tashi da shi na bakin da
suka yi daga Gombe, sai da yamma tayi
a lokacin bakin suka zo. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kanin mahaifinta ne ya zo shi da iyalansa, da yake
su a can suke da zama.
Tana bude wayarta  (text) ya rinka
shigowa, ta zauna tana ta aikin karanta su tana
dariya, hakan yasa Surayya ta tambaye ta wai
waye ke yi mata (text)?
Tayi murmushi tace Sarayya, wani ne
kuma kin san abin mamaki? Ina sonsa fa, ya zanyi
in shima ya kufce min?”
Sai taji tausayin ta, ta ce.
“Ba zai kufce miki ba, kin san dama ance
wani hanin ga Allah baiwa ne”,
Ita da Surayya suka fito da Kamal dan
kanin baban su, Izzat ita da Kamal suna hira,
Surayya na bayan su. Mustapha dake gefe yaji
wani abu ya zo ya tsaya masa a wuya, yana
mamakin waye wannan? Sai ya dauki waya ya
rubuta mata.
Waye wannan da kuke tafiya da shi? Nifa
mutum ne mai kishi.
Duk da a tafe suke sai da ta karanta
(massage) din, tayi saurin juyawa tana kalle-kalle,
sai ta ci gaba da lafiya har suka tafi inda za su.
Suhaila ce tsugune gaban wanta Ya Aminu,
Ya Aminu, ina cikin damuwa, na rasa ya
zanyi? Shi ne na yanke in same ka inji me zaka ce
Ta ci gaba, “Na rasa me Mubarak yayi
wanda Mami bata son sa, da tace bai da aiki, to
saboda Allah yanzu fa? Ka duba yanda Baba
Halima take son Mami da kaunar ta, amma ita
Mami ta fifita kawaye akan ta, uwa daya uba daya.
Ban da ma ita Baba Halima mai karfin zumunci ce
ai da tuni ba sa tare, wannan wacce irin rayuwa
ce? Shi kenan yanzu ina son Mubarak wai sai dai
in auri tsoho saboda yana da kudi?”
Amiu ya ce, “Kin san su iyaye sai dai a
bisu a hankali. Ki hakura ki bi umarninta”
Ta ce, “Ban ki ta taka ba, amma ni a tunani
na zaman aure zama ne na har abada ba wai zanma
ne n
a wucin gadi ba. Ina son in tambaye ka,
rayuwa za ta tafi (normal) da mutumin da ba ka
kauna?”
Ya yi shiru, ta ci gaba da cewa
“Ta ya zuciyata za ta kyautata wa mutumin
da ba ta kauna?
Ya yi shiru, ta sanya kuka, ta ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ka fada min ta hanyar da zan shiga
aljannah a haka? Wannan ita ce biyayyar da zan
Wa iyayena a matsayina na ya mace, idanna
mata yadda take so na kuma kuntata mijina ta ina
zan shiga aljanna?Naji Mami bata so in auri Mubarak, ina so
ta barni in zo da zabina”
Ya Aminu ya ce, “Suhaila, kin san halin
mahailiyar mu, kiyi hakuri kiyi ta addu’a Allah Ya
ganar da ita”.
Mustapha ne yayi (parking) motar sa gidan
su Suhaila, maigadi shi ya sanar da ita tana da
bako Bata so fitowa ba.
Mustapha na tsaye yana jiranta, Mami ta
dawo daga unguwa, yayin da ta ce.”Wajen wa ka zo kake tsaye kai kadai?” Ya ce, “Na zo gurin Suhaila”. Ne
Mami ta kalli shegiyar motar da ya zo da
ita, ta kalli shigar sa ta ce.
“To bari a turo ta”.
A zaune take, ta ce, “Ke, ba kiranki ake
ba?”Ta zumbura baki.
Ta ce,”Sai kije kiga wanda ya zo, matashi
ne, da gani ya fito gidan ni’ima. Da fatan ba za ki
watsa min kasa a ido ba”.
Ba don Suhaila  ta shirya ta fita,
ganin Mustapha yasa ta saki fuska, ta ce.
“Sannu da zuwa”.
Ya ce, “Ni da tunanin lafiya nake”.
Ta ce,”Aa Mustapha laifinka ne, sai kace
min kaine”.
Ya ce, “Ya gari?”
Ta ce, “A’a, muje ga guri ka zauna”.
Ta kaishi gurin da take sauke bakinta, ta
kawo masa ruwa da lemo, sannan ta zauna ta gaida
shi ta ce.
“Ina hasken idaniya ta ka taho kai kadai?”
Ya ce, “Ai jiya ya.zo maigadin ku ya hana
shi shigowa, ke kuma yanzu ba kya zuwa ki gai da
Mah”.
Ta ce, “To an kammala karatu ya zanyi?”
Ya dube ta ya ce, “To za mu turo don a san
ba da wasa muke ba”.
Taji sanyi a ranta.
In ta mahaifinta ne babu matsala, matsalar a
gurin mahaifiyar ta ne.
Ta ce, “Mustapha, Allah na rasa wannan
matsalar, zan yi shawara da yayana”
Ya ce, “Okey, Allah Yasa muji alheri”,
Sunyi hira sosai, daga karshe suka yi
sallama.
Mubarak ne zaune gaban mahaifiyar sa suna
tattauna maganar sa da Suhaila.
Mubarak ya ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Dama ni fa na hakura da batun auren
Suhaila, domin ba zan.auri macen da mahaifiyar ta
ba ta sona ba”.
Mah ta ce, “Hakan shi yafi
Ya ce, “Ai Mah ba zan sake zuwa gidan su
ba har abada, tunda an sa mai gadi ya hana ni
shiga…”.
Kamar an jehota ta shigo,
mahaifiyar
Suhaila ce, ta ce.
“Halima, Suhaila dai ‘yata ce, ba zan bawa
danki ba, domin ba zan sai da akuya ta dawo tana
ci min danga ba, ki fada masa ya rabu da ‘yata”.
Mah ta ce, “Haba Yaya, nayi zaton duk
daya ne”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *