DANGIN JUNA BOOK 1 CHAPTER 5 BY SA,ADATU WAZIRI GOMBE
A hankali Faruk ya soma scanning, kaf cikinta bai ga komai ba. A hankali ya gangaro. mararta. Abin da ya gani ba karamin razana shi ya yi ba, kawai sai ya kashe komai ya fita.
Umma Aysha ta ce, “Ya Faruk ya za ka yi haka? Ba za ka gaya mana moke damun ta ba?” Murmushin dole ya yi amma ya kasa cewa komi.
Umma ce ta ce, “Barshi Aysha ya tafi ni na san ciwon nata”. Da sauri Faruk din ya fita.
Ya yin da Maryam ko kwance kan gado ta kura musu ido. Umma Aysha ta tambayi Umma, me ke damun ta Yaya? “Uhm! Aysha karuwa muka samu, Maryam ciki gare ta”
“Allah Yaya?”Tabbas”
Maryam dake kwance kan gado ta yi saurin juya kanta don kunya. Ciki ya hana
Maryam sakat, gobe lafiya jibi ciwo, wannan yasa su Abba suka yanke shawarar ta koma gida har sai ta haihu. Ya yin da shi kuma Faruk ya tafi Lagos, in yaso yana zuwa. Weekend end. A gaskiya Faruk ya Kara shiga damuwar da tafi tada, wai Maryam na da ciki kuma cikinsa, to in ba nasa ba a ruwa ta sha. Shi kenan ya dada tabbatarwa da ya rasa Fati. Hawaye masu dumi suka zubo mai, yanzu shi haka zai ci gaba da rayuwa da macen da baya so. Umma ce ta shigo falon nashi, ganin hawaye a fuskarsa bai ba ta mamaki ba, don ta saba ganin haka.
“Yanzu kai Faruk ba za ka hakura ba don
Maryam na da ciki sai me? Zina kuka yi ne? Ina mai tabbatar maka Fati za ta fi kowa murna. Ina so ka sani rabon da ke jikin Maryam shi yasa ka rasa Fati. Allah ya riga da yasa dole Maryam za ka aura har a sami rabo tsakani. To meye na damuwa, na gaya maka ka yawaita karatun Alkur’ani da addu’o’i za ka samu nutsuwa.
Amma kai kullum cikin bacin rai ka daina walwala duk ka wani sake wai kai wani iri ne?
Me yasa ba za ka saki rai ka yi ta aikinka kamar yadda ita ta saki rai take karatu ba? To Allah kiyaye ya ba da sa’a”. Ta fice. Cikin sa’a Faruk ya isa Lagos ya kama aikinsa. Ya yin da suka ba shi gida cikin asibiti, sai dai yaqi karba saboda Abbansa ya saya mashi tangamemen gida a nan cikin Victoria Island.
BAWAN WATA TARA
Na san za ku yi mamaki in na ce muku sai yau bakon America ya sauka gida Nigeria, qila ma ace na manta da shi. Al-ameen Abuja ya wuce ya kai musu duk wani takardun da ake bukata da duk wani aiki da ya yi. tura shi, cikakken Navy Officer.
Address din Habib ya nema, gidansu kawai ya je a Abuja. Mamaki tasa Habib rike baki, ba wai mamakin gain Al-amin din yake ba, a’a, sai mamakin yadda gaba daya ya canza ya dawo Baturen asali ba, kyawun shi tamkar an ninka mai. Habib ya ce,Lallai yanzu Fati za tace
ma Bature da tushe Murmushi ya yi wanda ya kara mai kyau,Haba yaya Habib, ban da zuga mu da muka je mu kai ta wahalar aiki”Haka ne, amma ka san weather”Nan dai suka yi ta hira har Habib ya ba shi labarin auren Faruk, sai dai bai gaya mashi wai Faruk bai son Maryam ba.
Amin ya ce, “Wato kuka yi auren ku bana
nan”To kai ne ka je ka zauna, ina fatan ba a samo mana Baturiya can ba”Haba, ni ai Baturiyata tana nan gida”Allah mutumin?”
冰水
米米
Habib da Al’amin da Abinda suka taho
Bauchi. A gaskiya iyayensa sun yi murna da ganinsa sosai, tun ba Sulaiman ba da suka shaku sosai.Al’ amin ba karamin bakin ciki ya yi ba da ya ji fati ba ta nan. Sai dai dama ya sawa ransa sai ya bita. Dukkansu suna gidan Baffa Ibrahim, ya yin da Maryam ke ta kaiwa da kawowa tana kawo musu abubuwan ci da sha.
Nan Abida ta karbe ta saboda ganin yadda take tafiya da kyar. Wayar Maryam ta yi Kara, da kyar ta samu ta dauka, sunan Fati da ta gani cikin sauri da zumudi ta dauka, ba ta bari sun gaisa ba ta soma mata albishir. Amma. Yaya Amin ya zare mata ido alamar baya so Fati ta sani yana so ya mata bazata. Nan ta yi shiru. Yadda Fatin ta matsa mata da son jin meye albishir din ta ce mata, “Na kusa haihuwa ne yau ko gobe”.
Ihun da Fati tasa ta wayar yasa Maryam cire wayar a kunnen ta da wuri ta ce, “My sistor za ki fa sa min kunne, don kina murna sai kisa in zama kurma. Kin san waye da waye a nan? Ga Habib, Abida kowa da kowa sai kece bakya nan.
A’a, ki yi hakuri kar kizo su…
Ta kasa isar da abin da ta yi niyyar fada saboda wani azababben ciwon da take ji, kan ka ce kwabo su Abida sun yi kanta sai asibiti. Al’amarin Fati ko jin ihun Maryam a waya ya rudata, ya yin da aka barta da tambayar yaya Maryam, ina ba wanda ya kula da inda waya take bare a saurare ta. Habib ne ya tsaya kan Maryam, a gaskiya ta ci wuya, tun safe take abu daya har zuwa bayan isha tukun ta haifi sambalelen da namiji mai kama da ubanshi. Gida ya cika da murna ganin maijego ta sauka lafiya ba masala. Habib ya yiwa Faruk waya yai mishi albishir biyu, zuwan dansa da
- kuma dawowar Al’amin.
Bayan guri ya nutsu Maryam ta koma - gida. Fati ta buga waya nan Umma ta ba ta tabbacin Maryam ta haihu lafiya da namiji, nan ta shiga ba ta labarin kamanninsa da Faruk. Fati ta ce,
“To Umma tunda ya yi kama da
Yaya Faruk sai asa mai Faruk Junior’
Umma ta yi dariya, “Fati kenan, ke dai har yanzu yarinta bai bar jikinki ba”.
“Allah Umma ina so inzo in ga baby ga shi muna exam”To kinga dole ki hakura”. Umma ganin Fati ba zata kyale ta ba yasa ta katse layin.
Saura kwana uku suna Faruk yazo fuskarsa ba yabo ba fallasa, don Faruk shi dai mai son yara ne, don abun yazo mai a haka ne.
An hadu a falo ana ta hira, Al’amin ya ce sai “A min mai suna tunda baby ya ki fitowa har sai da na zo’ Habib ya ce, “Ni dai za a sawa da na sha harbe-harbe” Umma tace, “Ku dai kun cika shirme,haka Fatima ta ce wai asa sunan Faruk tunda sunyi kama”.Tunda suka soma magana sai yanzu ya daga kai da sauri, “Umma Fatin tazo ne?”A’a, waya ta yi”.Girgiza kai kawai ya yi, ya kalli su Habib dake musu ya ce, “Ku bar musu sunan yaro Faruk” Dukkansu suka kalle shi, “Amma dai yaya ka cika son kai”. In ji Amin.
“A’a, ba son kai bane, ina da babban dalili” Al’amin ya raba tsaraba kaca-kaca, ya yin da ya ajiye na Fati sai ta dawo. Maijogo ma ta sha kaya tamkar ‘yar gwal, a gaskiya Maryam ta san iyayenta na sonta, don kuwa abin da Umma Aysha ke mata yaya babba ba ta mata, haka nan
Umma Aysha ba ta ma Fati abin da take mata.
Matsalarta daya Faruk, sai dai dama ita ta san Faruk miskilin gaske ne. Sai dai duk da haka ya kan shigo ya duba Faruk Junior kafin ya koma in yazo weekend end.
Wani zuwan da Faruk ya yi karshen sati suka hadu da Amin suna hirar da suka dade basu yi ba. Nan suka gangaro kan maganar Fati.
Al’amin ke cewa, “Gaskiya ya kamata a shirya duka gida aje gun Fati”Murmushi Faruk ya yi, yace, “Wallahi ya kamata. Sai dai ni ina fushi da Fati ta tafi karatu waje ba shawarata Amin ya ce,
“Gaskiya nima na yi mamakin tafiyarta karatu waje, don dai dama na san Fati ba ta ra’ayin tafiya waje karatu”.
Murmushin da bai kai lebe ba Faruk ya yi, ya san dai dan shi Fati ta tafi karatu waje. Ya kalli
Amin ya Ce, Wato Al’amin bayan
tafiyarka abu da yawa sun faru, kuma abubuwa da yawa sun canza. Don kuwa munzo muna shiri da Fati sosai Faruk ya yi niyyar ba shi labari sai ya tsinci kansa da kasa gayawa Amin cewa baya son kanwarsa, don haka sai ya fasa.
Amin ya katse shi, “Ina jinka”Yace, “Bayan munzo muna shiri sosai, sai ta nemi tafiya karatu waje, ni kuma na hanata shi ne ta je ta samu su Abba, ban san lokacin da da suka nema mata har ta tafi ba. Sai labari na ji wai tabar kasar nan ta tafi karatu Abrod”. Al’amin ya ce, Lallai ta yiwa babban
yaya laifi za ta amsa kwarai”Faruk ya ce, “Wannan yasa na yi fushi da ita”
Amin ya ce, “Ka yi hakuri ka huce muje gunta kafin na yi reporting aiki” Girgiza kai kawai ya yi yace “Duk yadda na yi ba zan iya fushi da Fati ba, because she means life to me