DAWUUD
CHAPTER 2
Suna Isa gida jass yayi parking a babbar harabar gidan dukkaninsu suka fito kusan kowannensu agajiye yake Dan haka Kai tsaye suka nufi apartment ‘dinsu sufyaan ne agaba sbd ‘dan saurin daya ha’da dashi sbd dama amatse yake daya dawo ya duba yanda yabarta duk da yasan yayi Mata allurar bacci sbd ta huta sosai kafin yadawo.
Wani banxan kallo dawood yabisa dashi Yana yamutsa fuska coz sumtimes Yana mamakin yanda maza kewa Mata rawar jiki ko lallashi its irritating him.
Murmushi jass yayi ganin kallonda dawood yabi bayan sufyaan dashi Yana ‘dauke gira ‘daya yace,
Cool man…karkaga laifinsa you don’t know meyakewa rawar jiki and…..
Shigewa parlour yayi batareda yatsaya Jin sauran abinda jass ‘din zai fadaba…
‘dauke kansa yayi Yana shiga parlon sbd ganin Wainda ke zaune apalon.
Zaune take kan sofa tayi crossing dogayen legs ‘dinta dake sanye cikin blue parrazo trouser da milk loose shirt sai gashinta datayi coiling Shima a ‘daure tsakiyar kanta,
Cup ne a hannunta da gani coffee ne takesha sbd ‘dan tiririn dake fitowa daga cup ‘din,
Kyakkyawace ba laifi saidai gayunta da hutu tareda maqidan kudin datake kashewa gurin gyaran fatarta yasa kyawunta da burgewarta fitowa fili.
Cup ‘din hannunta ta aje ahankali tareda kallon maska dasuke Shan coffee ‘din tare suna fira tace,
My man is hia so…..
Yana kallon yanda dawood ya ‘daure fuska yayi hanyar bedroom ‘dinsa Yana dariya yace,
No no carry on sweetheart go.
Dariya tayi tareda nufar bedroom ‘din cikin tafiyarta ta ‘daukar hankali.
Yana shiga bedroom ‘din ya jefa wayoyinsa kan couch ya tu6e direct ya fada lafiyayyan babban toilet dinsa yashiga cikin bathtub ya kwanta tareda lumshe fararen oily eyes dinsa ‘dumin ruwan na rage masa gajiyar jikinsa.
Tana shigowa taga baya cikin room ‘din ta kalli qofar toilet tareda ‘dan yamutsa fuska ahankali tace,
I don’t feel like yin wani wanka yanxu but duk da haka lemme help.
Toilet ‘din ta nufa ta bude qofar tashiga tareda rufowa ta jingina jikin qofar ta qura Masa idanuwanta,
Dawood you’re my love and also my weakness,
I love you morethan anything,
You’re the only man I intend to spend my life with,
I can do anything to keep you for my self,wen I said anything I mean anything Dan Babu wata Rai dabazan iya kashewaba akanka shiyasa nake fatan ko yanxu ko gaba karkayi kuskuren Fara son wata coz I won’t think twice or hesitate to move anybody out of my way including poor Mrs assiddeeq Damien…
Sbd ko ita data haifeka bazata iya rabani dakaiba you’re only meant for me alone….. 1
Ahankali ya bude idanuwansa dasukai taushi ya ‘dorasu akanta fuska a ‘daure yace,
You need something??? 1
Murmushi tasaki harsaida dimple ‘dinta suka lotsa ahankali ta qaraso gurinsa ta ‘duqa ahankali tayi kissing lips ‘dinsa tace,
No I was just looking at the man who stole away my heart,,
Lumshe ido yayi sbd qamshinta daya ha’du Dana shower creams ‘dinsa ya cika toilet ‘din Yana kallon tsakiyar idanuwanta yace,
And who was that man?
Wani shu’umin murmushin tasaki tareda zura hannunta cikin ruwan dayake cikin ta shafosa tana cewa,
Are you sure you want to know him?
Jawota yayi cikin ruwa Yana cewa,
0 percent sure.
Dariya ta qyalqyale dashi tana sbd cakulkulin daya Fara yimata Nan suka Fara wasa cikin ruwan suna ta6e ta6ensu tuni ya manta da wata gajiya suka cigaba da sha’aninsu harsuka gama sukayo wankan tare suka fito.Shine namiji Amma fatarsa ma tafi Tata glowing duk kuwa da itama qarshe gurin kashewa jikinta kudi da bawa kanta hutu.
Cikin qananan Kaya marasa nauyi suka fito
Shi black trouser da white transparent shirt sai designer slippers ‘din channel dake qafafunsa farare qal kamar Bai ta6a taka qasaba.
Ita kuwa wata loose half gown tasaka Dan dama Bata rasa Kaya room ‘dinsa..
Tana Maqale a gefensa suka fito suna tana dariyar yanda idanuwansa sukai laushi sbd yunwa dayakeji.
Sufyaan ne kawai a palon gurin dining area yanata faman ha’da tea.
Kallonsu yayi tareda barin abinda yakeyi cikin farin ciki yace,
Thank God you are hia guys yunwa is killing someone hia.
Kallon dawood tayi tana cewa,
Yeah baby Let’s go somewhere and have dinner that silly idiot yau batayi aiki ba wai she’s not feeling well..
Maska ne yafito room dinsa ya qaraso Yana cewa,
Muje nima yunwar nakeji.
‘daki sufyaan yakoma ya ‘doro black shirt kan farar singlet dinsa yafito.
A Lamborghini car din maska suka fita dukkaninsu
Wani babban restaurant sukaje kowa yabada order abinda zaici suna gamawa suka dawo gida bayan maska yayi order sabbin tsadaddun kwalaben wine ‘dinsa sbd shikadai ne cikinsu baya neman Mata saidai shi alcoholic ne kowa yayi hanyar room ‘dinsa itama dai kamar lokuta da dama ranar agurinsa ta kwana batareda takoma apartment dinta dake gefen nasu ba.
1
*******
Tunda tazauna qofar ‘dakin tasake kwantarda kanta kan gwiwowinta tayi shiru tana kallon sama yanda gagarumin hadari ya ha’du iska na kadawa. 1
Kamar daga sama Salim yaron dasuke bara tareda Bilal ya rugo yazo gabanta Yana haki cikin tashin hankali yace,
NUR Bilal mota ta takesa Kuma……
Bai qarasaba ta miqe tsaye tareda Kama hannunsa ta matsar dashi daga qofar ‘dakin sbd kar baabaa yaji cikin sanyin murya tace,
Mekake cewa?
Duk da Yana yaro kuma yake cikin tsananin tashin hankali Saida yayi mamakin ganin yanayinta sam Babu razana ko firgici saidai idanuwanta dasuka ka’da lokaci ‘daya bawai Dan Bata shiga firgici ko tashin hankalinba ita haka Allah yayita baya bayyana saidai zuciyarta tayita ‘dawainiya da dakon wahalar tashin hankalin da firgicin. 1
Da saurinta fice gidan hartana hadawa da gudu ta qarasa gurinda ta tararda anyi cincirindo ansa Bilal din agaba anata masa fita sbd Wanda ya ka’desa ya gudu.
Rungumosa tayi jikinta da sauri hawayen idanuwanta suka sauko ta ‘dago kanta ta kalli mutanen gurin murya na rawa tace,
Dan Allah ku taimakeni ku kaimu asibiti…..
Watsewa taga mutanen sunfarayi sbd maganar taimako data ambata
Jikinta ne ya’dau rawa tasake rungume Bilal ‘din hawaye naci gaba da tsinke Mata.
Maigadin companin dasuke ne yaqaraso da sauri Yana salati akidime yace,
NUR maza kamosa mukaisa chemist tunda ba qarfin zuwa asibiti.To,,,tace tana miqewa jiki na rawa ta kamasa ganin takasa iya ‘daukarsa yasa ya kar6esa sukai hanyar chemist ‘din dake gefen titin da sauri daidai lokacin ruwa Masu qarfin gaske da iska Mai qarfi suka taso Nan jamaa suka Fara gudu kowa na neman mafaka Musamman ganin yanayin qarfin iskan. 1
Gabanta ne yayi mummunan fa’duwa tunawa tayida duk ana iska da ruwa irin haka fitowa suke daga ginin harsai angama ruwan sbd gujewa faduwar ginin Dan tuni dama want gefe yafara rugujewa.
Kallon Bilal da’akewa allurori ana dressing inda yaji ciwuwuka tayi tareda miqewa jikinta na rawa tayi hanyar fita
Damqo hannunta dahiru Mai gadi yayi cikin fada yace,
Bakida hankaline Zaki fita cikin wannan ruwa da iskan Masu qarfi ya kukaji da neman na abincima bare na ciwon mahaifinki gana bilalu yanzu sannan kina qoqarin samawa kanki wani… 1
Qwacewa tayi hawayen idanuwanta na qara gudu tace,
Baabaa nacan nasan cikin gidan Nan Babu Mai fiddasa zuwa zanyi na fito dashi.
Ke dalla yiwa mutane shiru idanma kin fiddosa wani gurin gareki na kaisa yanzu cikin wainnan ruwan Kuma…….
Zuwan Raheenatu hankali tashe tana ihun kukan daya mugun ka’da kayan cikinta tayi gurinta jikinta na wani irin mazari ko magana takasa yi sbd tashin hankali da hannu ta tambayi Raheenatun jikinta na tsananta rawa.
Cikin tsananin kuka tana nuna hanyar waje tace,
Gini ya Fado Kuma….Kuma…. 4
Wani wawan turi tayi Mata cikin tsananin tashin hankali ta fice da mugun gudu
Hankali tashe dahiru da sauran jamaar chemist din sukabi bayanta dahiru nakiran sunanta..
Sam ko gani sosai batayi sbd tsananin qarfin ruwan Amma Sam ko ruwan bataji duk inda tasamu jefa qafarta takeyi..Tana Isa Bata tsaya tunanin komaiba tafara qoqarin kutsawa ciki mutanen dake gurin suka rirriqeta suna cewa Batada hankaline tana ganin gini na zubewa zatashiga…
Qwacewa tayi cikin tsananin kuka tana Kiran baabanta jikinta ba inda baya rawa..
Cikin zafin nama dahiru ya damqota tareda riqeta da qarfi
Ihu take da kuka sosai tanason qwacewa Amma ba qaramin riqo yayi mataba Dan kuwa ayanda take ba cikin hayyacinta ba idan aka saketa zata iya shiga ginin Wanda tuni ya qarasa rugujewa….
Ihu tasaki Mai qarfi ganin yanda gaba daya ya qarasa rugujewa kamar ba’ataba dogon giniba agurin.,,
Arikice dahiru ya girgixata Yana Kiran sunanta cikin tsoro da tashin hankali sbd ganin kamar Bata numfashin..
Layla… Layla..ke tashi karki mutu ahannuna..innalillahi
Arikice Raheenatu tafara jijjigata tana Kiran sunanta cikin tsananin kuka Amma Sam ba alamar tanada sauran numfashi…
Cicci6arta sukayi suka koma gefe sbd ruwan saman ya ‘dauke mutane sun qara taruwa agurin ana kallon yanda ginin ya zube…
Kallon Raheenatu yayi cikin tsoro yace,
Ke kamata muje chemist idan Bata tashiba to tafiyata zanyi wlh ba ruwana.
Cikin tsananin kuka ta Mike suka kamata suna Isa chemist din hamisu Mai chemist na ganinta yace,
Aa wannan tafi qarfin chemist asibitin zakuje Dan da alama kamar bugawar zuciya ne kamarma ta Dade da mutuwa..
Ehhh,,, dahiru yafada cikin tsananin tashin hankali da tsoro Yana zaro jajayen idanuwansa
Nan Take jikinsa yadau rawa ya kalli Raheenatu Yana cewa,
Nayi iya yina saiki ‘dora Kuma wlh ka sunana yafito ciki.
Ficewa yayi jiki na rawa Yana sharce gumi duk da sanyin ruwan da aka gama.
Kallon Nur din tayi cikin sabon kuka tace,
Kiyi hakuri Layla nima bansan ya zanyi Miki ba Dan banida wata taimako Kuma.
Miqewa tayi ta fice batareda tabari hamisu Mai chemist ya luraba.
Wani mugun ashar ya sako lokacinda yagama sallamar wani yaga sun gudu sun bar Masa gawa
Ai nantake ‘yan hanjinsa suka ka’da Bai tsaya wata wata ba jiki na rawa ya zagayo yasa qarfi ya cicci6eta ya lalla6a yakaita gefen gininsu daya zube sbd duhun magrib yariga yagabato yadawo ya cicci6i Bilal yakai gefenta ya aje yadawowarsa ya rufe chemist dinsa yayi gida.
Babu Wanda yakuma kawosu arai sai tsakar dare guraren qarfe uku suka farfado kusan atare sbd sanyin asuba daya sawo Kai dakuma sanyin ruwan da’akayi.
Daqyar ta iya lalabawa ta tashi zaune ta bude idanuwanta da sauri ta rufe sbd ganin a inda suke yashe kan hanya kusada bola.
Da hannu ta lalabo Bilal dake kukan azabar ciwo ahankali ta rungumesa tareda sakin qaramin kuka ahankali tana kiran sunan mahaifinsu, 3
Sun zama marayu basuda uwa basuda uba basuda kowa dazasu gani ko sukira nasu
Tun adaren da mahaifinsu ya rasu sun Fara shiga garari tunda gasu da kwana gefen bola.
Jin kukan azabar da Bilal keyi yasata bude ido ta sake qanqamesa tana basa haquri Dan kuwa raunika ne sosai a jikinsa duk saiya qara ‘daga Mata hankali ta birkice.,
Daqyar taga lokacin sallar asuba yayi anyi gari ya ‘dan Fara haske takamasa daqyar suka ‘dan matsa daga kusada bolar ta samo wani jikakken kwali ta shimfida Masa ta kwantar dashi.Rawar sanyi yakeyi sosai ta rasa ya zatayi cikin hawaye ta kalli lifayarta data gama tsufa da faffashewa tasa hannu ya farketa biyu ta lullu6esa sauran ta ‘dan budeta ta rufe jikinta Wanda Bata rufe dukaba saima taqara fitowa datayi a sadaka yallah dinta.Koda gari yayi haske sosai jama’a kowa nata harkokin gabansa Babu Wanda ko kallo suka ishesa gashi har lokacin Bilal sosai yake cikin azabar ciwukan jikinsa ga zazzafan zazza6in dake cinta. +
Daqyar ta miqe ta kamasa suka qara matsawa daidai bakin ginin ta kwantar dashi duk da daqyar take iya daukarsa.
Zama tayi kusadashi tareda cusa Kai cikin qafafunta tanason tayi kukan Amma yaqi zuwa ga mutane suna ‘dan taruwa sake kallon ginin dakyau cikin haske.
Ahankali taga su Raheenatu da iyayensu suna zuwa suna zaunawa kusadasu kan kace me gurin ya ‘dan cika da mutane mabarata da musakai.
Raheenatu ce cikin Jin nauyi da tausayinta ta matso murya a sanyaye tace,
Ya jikin Bilal?
Kallonta kawai tayi da jajayen idanuwanta sbd ko magana batajin zata iya.
Allah yajiqan baabaa,,,tasake cewa tana kallon ginin.
Sake rintse ido laylar tayi Jin abinda Raheenatun tafafa ko Amin din takasa cewa.
Kaf gurin Raheenatu ce kawai ta iya yimusu mgn ta miqe takoma gurin Yan uwanta.
Shiru tayi jikinta na ‘dan rawar zazza6in dake tsananin cinta.
Ido dahiru yayita warewa harya hangota raku6e gefe kunya yadanji ya Sosa Kai tareda fuskewa ya nufi gurin tareda ‘dan yaqe Baki yace,
Layla ya jikinki Dana bilalun?
Sake cusa kanta tayi tsakiyar qafafunta batareda tace komaiba.
Kingane ki kwantarda hankalinki insha Allah zaku samu mafita wannan taruwar dakikaga wainnan munafukan sunyi na zuwan Alhaji Mai companin ne sbd zaizo yayi ta’aziyar abinda yafaru yakuma taimakawa wainda suke zaune suje su nemi wani gurin Kinga ke zakufi kowa kaso Mai tsoka tunda ke mahaifinku ya rasa ransa qila abin Nan zai biya…um um mema ake cewa sunan abun idan za’a biya….ummm yauwa diyya..Kinga daganan saina taimaka muku nasamo muku gurin zama da…..
Manyan jeeb jeeb dinda suka doso gurin yasashi miqewa da sauri Yana gyara fuskarsa zuwa kalar tausayi ya nufesu jiki na rawa haryana tuntube
Sauran mutanen dake cikin gurin kuwa tuni suka Fara fuskar kalar tausayi wasu harda kuka wasu kuwa kwantawa sukayi ana musu fifita da sannu.
Motocin na tsayawa tuni Yan press yo caaa suka rufesa da tambaya daidai lokacinda drivernsa yabude Masa ya fito motar.
Tambayoyi sukai tayi Masa Yana amsasu cikin nuna jimami da tausayawarsa ga alamarin.
Ahankali take kallon mutanen cikin tausayawa ta cikin glass din motar batareda tafitoba,
Rintse idanuwanta tayi sbd yanda gabanta ke tsanan faduwa duk lokacinda idanuwanta suka sauka kan ‘daya daga cikin mutanen…
Qura Mata ido tayi zuciyarta na ingizata ga zuwa gurinta..
Saurin ‘dauke Kai tayi numfashinta na fita da sauri.
Tunda yazo dukkaninsu suka Fara rawar jiki har lokacin Bata ‘dogo kantaba saima qarfi da zazza6inta yaqara.
Ahankali yafara binsu ‘daya bayan ‘daya Yana Basu kudi Masu yawan gaske suna wucewa haryazo kanta.
Kallonsu yayi cikeda tausayawa itada qanin nata ganin qarancin shekarunsu sosai.
Cikin jimami dahiru dake gefe ya matso daga gefen securities din Alhajin yace,
Alhaji wainnan sune marayun ‘yayan Wanda yarasa ransa.
Sanyi jikinsa yayi yasake kallonsu kafin yakalli PA dinsa yace,
Aminu ayi gaggawar Ciro gawarsa.
Ok sir,,,yace tareda Ciro wayarsa Yana danna Kira tareda komawa gefe.
Kallonsu yasakeyi cikin taushin murya yace,
Layla kamar yanda dahiru yafada sunanta.Kasa ‘dagowa tayi saima sake cusa kanta datayi cikin qafafunta tana kuka ahankali Jin gawar baabaansu daza’a Ciro sbd tana kwatanta irin azabar dayasha kafin ransa yafita lokacinda ginin yafado Masa.
Cikin qanqanin lokaci motocin aiki sukazo aka Ciro gawar saidai duk Wanda ke gurin Saida imani da sanyin jiki suka kamasa sbd ganin yanayin gawar abin babu kyawun gani saidai adduar Allah yaji qansa.
Kukanta yaqara tsananta sanyin jikinsu musamman qananun shekarunta daga ita har qaninta.
Basubar gurinba harsaida akayi jana’izarsa Nan Alhajin yaciro dubu ‘dari yabawa dahiru yace yakula dasu sbd cewa dayayi zai kaisu gurin innarsa ta riqe.
Suna barin gurin ya miqo Mata kudin cikin farin ciki da zumudi yace,
Ungo riqemin zuwa anjima idan zani gida zan kar6a sbd karna fita dasu yanxu a yankemin aljihu.
Kar6a tayi batareda ta ‘dagoba ta tura qarqashin kwalinda Bilal ke kwance Allah ya taimakesu ba Rana.
Agurin suka yini sai magriba Bilal ya farfado ta zaunar dashi jikinta na rawa
Kallo ‘daya tayi Masa taji jikinta yaqarayin sanyi sbd ciwo da yunwa data hango qarara nacinsa.
Ita kanta ciwo da yunwar na cinta Amma Batada yanda zatayi.
Kuka yasake daqyar yabude Baki yace,
Yunwa nakeji Kuma inajin ciwo Layla kisamomin magani da abinci kona cikin bolane Ni zanci.
Kukansa yayi tsanani daga Mata hankali rashin sanin abinyi yasa itama tasa kuka tana rarrashinsa amma kamar tana qara Masa ciwone Dan har wani irin rawa jikinsa keyi.
Tunawa tayi da kudin da’aka basu ta ‘daga kwalin taciro kudin ta zari ‘daya ta mayar tareda miqewa tace,
Zan dawo yanxu kaji.
Da sauri ta juya ta nufi Mai abincin kusada chemist din hamisu tasiyo Masa shinkafa da ruwa ta kar6o Masa magani gurin hamisu ta dawo da gudu.
Cak ta tsaya cikin tsananin tashin hankali jikinta na daukar rawa ganin Bilal cikin jini kwance kamar matacce.
Watsi tayi da abincin tayo kansa da gudu tana jijjigasa tareda kiran sunansa..
Bilal meya sameka?..meye yayi maka haka wannan jinin…..
Daqyar Yana kuka yace,
Kudin dakika aje sukamin duka suka ‘dauke duka sun gudu.
Wani irin kuka da ajiyar zuciyane sukazo mata lokaci ‘daya kafin tayi magana dahiru yaqaraso da saurinsa yace,
Yauwa Layla bani kudinnan Kuma kutashi muje..
Sunkuyar dakai tayi cikin kuka tace,
An dauke duka.
Harara ya watsa Mata tareda gyara tsayuwa yace,
Kinga banason baqin ciki nida zan taimaka muku banmuku baqin cikiba sai ‘dan kudinda zan qaru dasu shine zakumin baqin ciki Amma wlh bakida imani Layla…
‘daga kwalin yayi ya zazzage baiga komaiba.
‘dagowa tayi ahankali takallesa tace,
Wlh ansace sunema aukaiwa Bilal haka….
Ke dalla yimin shiru muguwa kawai Amma wlh kin cuceni Dan har bashi naci yanzu Koda uwarwa kukeson nabiya,
To wlh kanku kukayiwa Dan saiku nemi gurin zuwa wlh ba inda zan kaiku tunda bakida Jin qai da tausayi.Juyawa yayi afusace kamar zai rusa kuka ya wuce Yana masifa.
Bayansa tabi da kallo harya 6acewa ganinsu ta Sunkuyar dakai hawayenta na qaruwa takalli Bilal cikin hawaye tasake miqewa tareda komawa tasake siyo Masa abinci da sauran canjin hannunta da ruwa tadawo ta ‘dauki maganin dazu data siyo. 1
Tuni jikinsa ya rikice da zazza6i takamasa daqyar sbd itama qarfinta yayi qasa sosai ta tayar dashi zaune ta basa abincin kadan yaci yasha magani ta ‘daure sauran a Leda ta aje gefe tasake lullu6esa tana Masa sannu ahankali. 2
Dare nafarayi zazza6insa yayi tsanani ga mage mage dasuka dinga Bata tsoro Dan wani irin kuka sukeyi Mara dadi ta kalli bolar Nan tsoro yaqara rufeta ta miqe jiki na rawa ta tattarosa daqyar ta Goya nauyinsa na rinjayarta haka tabar gurin tana tunananin gurin fakewa kafin safiya. 2
Saidatayi nisa sosai da anguwar kafin taga wani qonannen shago bakin titi daga gani gobara yayi ta qarasa ahankali ta saukesa tareda zubewa gefe tana fidda numfashi daqyar sbd yunwa gajiya da zazza6in dake cinta. 1
A wahalce bacci ya daukesu su duka Bata farkaba sai da gari yayi haske tana bude ido taga Bilal zaune Yana kallon waje.
Tashi tayi ahankali ta dawo kusadashi murya Bata fita sosai tace,
Kaji sauqi Bilal?
Eh yace Yana qoqarin bawa kansa qarfin jiki Dan haka bazatai musu ba Dole zasu Fara bara danshi Sam bayada jimirin yunwa ko kadan.
Layla muje bara Kinga Ni yunwa nakeji wlh Kuma Kinga baabaa tuntini Yana cewa mu iya nema da kanmu kintuna.
Kallonsa tayi da idanuwanta dasukai jajir sukai mugun nauyi sbd kuka taga yanda duk ya kumbura fuskarsa da sauran jikinsa sbd kadewar da mota tai Masa dakuma dukan da akai Masa ga raunikansa sunanan saima quda dake qoqarin hawa ta girgixa Kai zuciyarta na qara karyewa tace,
Bazaka iya fita baraba kabari ga saurin naira ‘dari biyu a hannuna zamuci wani abu da ita.
Miqewa tayi ta fita tana dudduba inda zata samo abinda zasuci.
Duk Wanda tabi ta gefensa saitaga ana kaucewa sbd kallo mahaukaciya da ake Mata.
Qosai taga wata Mata nayi gefen wani shago ta qarasa tun kafin tafadi qosai tazo siya matar ta taso Mata cikin masifa tace,
Matsa daga can karki zubomin dau’da Kinga kima tafi bana bada sadaka nima nema nake.
Matsawa baya tayi murya asanyaye ta miqo kudinta tace,
Siya zanyi harda koko.
Wani mugun kallo ta watsa Mata kafin ta fizgi kudin ta zuba Mata kosan ‘dari kokon ‘dari a Leda baqa.
Kar6a tayi tareda tsayawa jiran canji.
Harara ta watso Mata tace,
Meye Kuma?
Canji zakiba…..
Canjin me Kuma ai kosan ‘dari ne kokon’dari jeki Kisha saikin ture.
Girgixa Kai tayi tace,
Banason na duka.
Rufe Ido Mai kosan tayi ta koreta cikin rashin mutunci kafin taci gaba da aikinta tana masifa ita kadai.
Komawa tayi takaiwa Bilal sosai yasha itakuma kadan Tasha Dan karya qare anjima su rasa ta ‘daure sauran a Leda. +
Ranar haka suka wuni cikin gurin Saida yamma tabasa sauran Kokon ya shanye tareda sauran paracetamol din daya rage musu ita saidai ta kwana hakanan.
Washe gari tunda safe saiga Mai shagon yayi musu korar wulaqanci kamar zai dakesu sbd kai Masa labari da’akayi sadaka yallah zasu mayar da shagonsa gida.
STORY CONTINUES BELOW
Suna fitowa suka hau titi suna gararanba harsuka Kai wani gurin siyayya sukaga mabarata da musakai zazzaune suna jiran duk Wanda ya fito ya Basu sadaka.
Ba 6ata lokaci Bilal yaja hannunta Bata musaba sukaje sukabi sahu Dan dama ko ruwa Babu acikinsu Bilal yayi kukan harya gaji yasawa kansa dauriya.
Tunda suka zauna ko acikin mabaratan sun fita daban sbd tsananin bushewar dasukayi ga dau’da da mataccin kaya hakadai suka zauna jiran tsammani.
Tunda suka zauna kusan so hu’du ana bada sadakar kudi sai mutanen su rabe abinsu ko kallo Basu ishesu.
Hawaye ta sharce tareda cewa Bilal yatashi sutafi wani gurin.
Qin tashi yayi saima matsawa daya qarayi kusa da qofar super market din daidai kuwa fitowar wani saurayi tareda yarinya kimanin shekarun Layla.
Da sauri Bilal ya matsa gurinsa yace,
Munajin yunwa nida yayata Dan Allah kabamu abinda zamuci tun jiya muke jinta.
Kallon Bilal din yayi ganin yanda bakinsa ke bushe yasa ya yarda da zancensa yaciro ‘dari biyar yabashi.
Saboda murya ko godiya baiyiba yayi gurin Layla da gudu yace,
Nur tashi muje munsamu.
Girgixa Kai saurayin yayi ita kuwa Layla ta qurawa Ido tanajin wani irin so da qaunar Layla na shigarta..
Tun ranar farko data Fara ‘dora idonta akan Layla ranar dasukaje gurin faduwar ginin da abbanta takejin wannan connection,
Tun ranar takasa cireta cikin ranta.
Harsuka shiga mota sukabar gurin Bata daina kallontaba harsaida suka 6ace.
Sukuwa barin gurin sukayi cikin farin ciki Dan kuwa ko ita Layla yau saidata nuna farin cikin samun kudin.
Shinkafa da wake da manja suka siya ta ‘dari biyu sukaci suka qoshi daga Nan suka cigaba da bulayinsu har dare yayi suka la6e gefen wata islamiya suka kwanta da zazza6i dukkansu suka kwana Amma gari na wayewa suka bazama bara bawai don sundaina jinsaba saidan ba amfanin kwanciyar Dan korarsu ma akayi tun Basu tashiba.
Koko suka siya da qosai sukasha daganan suka koma super market din jiya suka zauna.
Ranar Kam ba sa’a har Isha Basu samu komaiba jiki ba qwari suka koma inda suka kwana jiya suka kwanta bayan sun siya alalar hamsin sun raba sunci.
Tsawon sati uku da rasuwar baabansu Babu wani sauyi ko taimako saima ta6ar6arewa da rayuwarsu tayi Dan zuwa yanxu duk inda suka samu kwana sukeyi hartakai idan sunga kangon gida murya sukeyi dare yayi su kwanta gari ya waye suyi gurin bara..
Tsawon lokacin Basu ta6a ko wanka ba kayansu tuni suka qarasa yayyagewa Nan take suka zama kamar wasu aljanu,
Yawon dasuke yini sunayi ko mashin ne saiyaso hutu bare ‘dan Adam gashi bamai takalmi acikinsu daga bayane Bilal ya tsinto musu wasu fasashi a bola idan yasa yau gobe ita tasa.,
Duk wahalarsu ba kullum suke samuba ko sunyi barar.Tafe suke Bilal na Bata labarin yanda suke bara dah kafin baabaa ya rasu ta kallesa tace,
Bilal to meyasa yanxu bama samun sadaka.
Ko dacan fa gidaje muke zuwa muyi bara ko mu zubar musu da shara kafin abamu koya kwana munaci.
Qarasawa bakin wani babban mall sukayi tana cewa,
Yaudai Allah yasa musamu da wuri muje mu nemi gurin kwana karmuyi irin na jiya duhu yayi bamu samu gurin kwanciyaba Dole muka kwana gefen bola nidai tsoron bola nakeji banaso muna kwana anan.
Zama sukayi Bilal ya aje matacciyar robar daya samo musu ta bara dacin abinci.
Har kusan magriba Basu samu komaiba sai wani guntun biscuit da wata yarinya ta jefar gurin rigima ta fito gurin da uwayenta.
Kallonsa tayi cikin sanyin murya tace,
Bilal muje ko gurin kwanciya mu nema kar duhu yayi.
Sabon garari suka soma na neman gurin kwanan yau Amma duk inda suka Fara qoqarin zama da gudu ake korosu gashi yau akwai hadari sosai daga ita harshi tsoron walqiya da tsawa suke shiyasa duk jikinsu yayi sanyi.
Basu ankaraba aka Fara yayyagi saikuwa ruwa Mai qarfi da gudu suka raku6e qarqashin wata bishiya duk da ba wani ruwa take karewa ba Amma haka suka fake tareda qanqame juna.
Ruwa Mai qarfi akayi sosai sai tsakiyar dare ya tsagaita daqyar taja Bilal suka ra6e gefen shagunan gurin sbd rawar sanyin dayakeyi ko motsi yakasa.
Suna raku6ewa gurin itama ta dunqule jikinta na jijjiga sosai.
Ana fitowa sallar asuba gari na Fara haske takalli Bilal dake baccin wahala tace,
Bilal tashi muje karsuxo su dakemu kaga sunce duk suka sake ganinmu Nan saisun Mana duka.
Da qyar yatashi zaune takamashi suka miqe sukabar gurin tana riqeda hannunsa.
Doguwar tafiya sukayi ya sulale qasa ya zaune gefen wata babbar makaranta ya lashi busasshen makinsa daqyar yace,
Nagaji mu huta nan.
Zama tayi kusadashi tareda qurawa makarantar Ido.
Baccin wahala ne yasake daukar Bilal ta qura Masa Ido sai kawai ta fashe da kuka tana tunanin badai haka zasuyita rayuwaba harsu girma su mutu.,,
Ahankali tace gwara mota ta ka’demu tare mu mutu tare mu huta.
Suna gurin har qarfe biyu hayaniyar tashin ‘yan makarantar ne yatadashi ya tashi zaune yana kallon gate din makarantar yace,
Nur zanje na roqesu abinci idan sun rage.
Bai rufe bakiba wasu ‘yan Mata uku suka fito suna dariya da manyan school bags dinsu goye.
Cikin sauri yace,
Dan Allah ku bamu sadaka muci abinci..
Wani mugun kallo suka watsa mishi atare Layla na ganin haka ta taso ta riqo hannunsa batareda ta kallesuba.
Harsun juya ‘dayar taciro nera goma tace,
Kar6i.Da sauri Bilal ya juyo gurin kar6a ya ta6a hannunta wani wawan Mari ta sharara Masa cikin tsananin Jin zafi ya tureta harsaidata fadi yace,
Allah ya isa muguwa..
Zaro Ido sukayi dukkaninsu cikin hasala ta miqe tareda rufesa da shuri da sauri Layla ta rungumesa ta Kare
Qara quluwa tayi tasa qafa takaiwa laylar mugu bugu a goshi Nan take goshin ya fashe hannu ta qara dagawa zata Kai Mata Mari aka riqe hannunta.
Aleeya””””””tafada tana kallon cikin idon wadda ta riqe Mata hannu sbd batasaran ganintaba gurin zuwa daukarta.
Sake Mata hannu aleeyar tayi tareda juyowa ta kalli Layla dasuke kuka antaru anata kallonsu.
Hannu ta miqawa laylar.
Miqewa tayi tareda riqo Bilal suka juya zasu wucewarsu aleeya tayi saurin riqeta murya na rawa tace,
Zan taimakeku.
Atare itada Bilal suka qurawa aleeyar Ido sbd yaushe Rana ta farko da wani yace zai taimakesu duk kuwa gwagwarmaya da gararin dasukayi.