DEEMAH CHAPTER 11 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 11 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tafiya mukayi me nisa wanda ya sani barci, ina cikin mafarkin _Sufyan_ naji kamar hayaniya a cikin motar, a hankali nake bude idona wanda ya sauka akan wasu maza biyu suna tsaye suna zare ido, cikin sauri na bude idona da kyau sannan na kalli cikin motar amma banga kowa ba “wato tsaban jin dadi ana hayaniya amma ke barci kike harda minshari? Zaki sauka ne ko sai mun illataki?” Hararansu nayi a raina ina cewa “makaryatan banza kawai ni ban san ma yadda make minshari ba” cikin dakewar zuciya nace musu “ai sai ku dan matsa in sauka tunda dai  bata kanku zan haura ba” karfin halina ne ya basu mamaki, tsaki naja ina jira su bani hanya dan banga gurin kutsawa ba anan duk sun tare guri suna wani cewa in wuce to in wuce ta ina? Ta cikin jikinsu kenan kamar fatarwan film.

+

“Kai _Goga_ wai baza ku sa6ota a kafada bane ku fito da ita musan abin da zamuyi a gaba?” Kuji wani zancen banza wai a sa6oni a kafada kamar wata yar baby ko kayan shanya, aikin banza taran ruwa a abin tata, suma ai sun san cewa babu abin da zasu iya dan nauyin su su biyun shine nawa, gyara zama nayi ina jira su daukeni dan in gwada musu nawa haukan, sai dai kuma naga sun bani guri dan in wuce, tashi nayi na sauka inda naga an raba mutanen gida biyu, 6angare daya yan mata da samari sai daya kuma tsofi, tsofin baza su wuce biyar ba, da kawunai na biyu da wata tsohuwa sai wasu maza tsofi biyu, a 6angaren yan mata da samari kuma mutum shida dani mun zama bakwai.

Ogansu ne ya fito daga cikin mota yace a saka tsofin a motar da muka fito, bayan sun shiga ya sake cewa ina direban, shine aka nuna mishi daya daga cikin tsofin da suka shiga motan, kallon direban ya yi yace yaja mota ya koma inda ya fito, cikin sauri direban ya ja mota aka barmu mu kadai, “ku tashi tsaye” Ogan yace mana, cikin sauri muka tashi saboda ganin yanayinsa “no mercy” kallon mazan dake cikin mu su uku yayi sannan ya kalle mu mata mu hudu, yace a rarrabu maza gefe mata gefe, bayan haka yace mazan su za6i daya ko mutuwa ko shiga cikinsu, wa zai so mutuwa kuwa a cikin su sunaji da samartaka, cikin sauri suka za6i komawa 6arayin karfi da yaji, bayan sun koma cikinsu Ogan ya kalle mu yace “ku kuma abu uku zan baku za6i, mutuwa, ko zama a cikin mu, ko kuma kowa a cikin yara na ya dandana ku” zare ido muka farayi, ni kam da wannan danyen aiki biyun ai gwara mutawa ta kawai shi zai fi yimin sauki, mata biyu suka bada kai wa yaran Oga dan dama ba sabon abu bane a gurinsu dayar kuma ta amince da zama a cikinsu sai ni da nayi tsaye na rasa madafa babu abin da nakeyi sai adduar neman tsari daga dukkannin sharrinsu.

Wani irin kallo Ogan nasu ya min yana wani malkwasa wuya, duk da cewa a tsorace nake amma kuma karfin hali na yana nan babu inda ya tafi “na za6i mutuwata akan in aikata abin da kuke bukata, zan iya komai amma banda cin mutuncin aurena, ina da auren shine zan aikata wadannan abubuwan, Allah ya gani ba zan iya ba” matsowa Ogan ya farayi kusa dani ina matsawa baya, “wato kece baki da kunya ko? Ni kike fadawa zancen banza zancen wofi, to tunda har kika fada haka tabbas taki ta kare zamu kashe ki amma ba’a nan ba, sai mun isa inda za’a samu namun daji zamu kashe ki mu jefar dake su cinye gawarki” ya fada cikin 6acin rai tare da kifa min maruka kusan guda uku.

Kasancewar ba’a tafi da kayan mu ba kowa aka bata jakarta a hannunta sannan muka fara tafiya, mu mata motarmu daya mazan suma motarsu daya ko wanne akwai yaran Oga uku a cikin ta, muna cikin tafiya daya yarinyar da tace zata shiga cikinsu ta juyo ta kalleni “kinyi tunanin cewa ke kadai ce matar aure kuma ke kadai ke son kare martaban aurenki? Toh nima din matar aure ce da yarana hudu, mata biyu maza biyu, ina zaune a garin bauchi tare da miji na da yarana, yanzu haka tafiya ce ta kamani zuwa garin _Jos_ domin duba lafiyar mahaifiyata, amincewar da nayi da wannan za6in nasu ba wai har raina bane, idan na amince da bawa yaransa kaine shine ma cin mutuncin auren da zanyi bayan ina da za6in mutuwa, sai dai za6i na biyun shine yasa na cire mutuwa a cikin abin da zan za6a saboda ina da yakinin cewa Allah ba zai barni haka ba zai kwaceni daga hannun su, ko ba koma ba zasu min wani shashanci ba, kinga daga haka zan samu hanyar guduwa” ta fada tana share hawaye, jiki nane ya yi sanyi, ni banyi mata kallon matar aure bama saboda karamin jikinta, kuma harda yara hudu lailai jikinta ne kyau ne, tunanin abin da tace shi yasa na sake kallonta tabbas tayi tunanin dani banyi ba, sam-sam irin hakan bai shiga kaina ba balle har inyi tunani me kyau akai, hakuri na bata tare da cewa “Allah ya karemu baki daya”.

_________________________

Suna zaune a falo suna hira sukaji sallamarsu kawunai na, cike da mamaki suke kallonsu, amma ganin tashin hankalin dake fuskarsu yasa suma hankalinsu ya tashi musanman da basu ganni a tare dasu ba, _Ya Kolo_ ce tayi karfin halin tambayan inda nake kuma meyasa bamu tafi ba, anan suka zauna suka fara basu labarin abin da ya faru, tare da direban motar suke dan haka aka mishi izini ya shigo shima ya fada iya abin da ya sani, cewa muna tafiya har munyi nisa sosai shine muka hadu da motar 6arayi sun tare hanyar, daganan suka sa mukayi parking sannan suka ce duk mu fito, labarin komai daya faru ya fada musu ba ragi ba kari, salati kawai yan gidan mu sukeyi cike da tashin hankali, _Mama Qudi_ tsaban firgici sai da ta suma kusan sau uku tana farfadowa, _Inna Abu_ sai kuka akeyi yayinda _Baba K_ ya zuba tagumi, kowa ya rasa ma abin da ya dace ayi sun rasa ta ina zasu fara, karshe yayanmu ya sanar da yan sanda abin da ake ciki.

Bayan yan sanda sunzo gidan namu aka sake mayar musu da labarin abin da ya faru, anan suka shiga kwantar wa da mutanen gidan mu hankali akan zasu tsananta bincike in Allah ya yarda babu abin da zai faru, da ban baki da lallashi aka samu suka saduda. Daganan gidan mu ya koma kamar gidan zaman makomi, wannan ya shiga ya fita wannan ya shiga ya fita akayi ta kuka ana jajantawa. Yarana sunfi bawa kowa tausayi saboda yadda suma suka zauna shuru kamar sun san abin da ake ciki, sunki cin abinci sai ma kuka da suka tsiri yi ko wani lokaci karshe kuma suka koma kiran sunana anan ne kuma wasu suka fara sabon kuka kamar an sanar da mutuwata.

Sosai aka tsananta bincike amma ba’a samu wani abu ba, kuma a ranar motar mu kawai aka tsayar dan sauran direbobi sunce sun bi hanyar sai dai basu hadu da komai ba, wasu kuma da sukejin haushin direba suka koma cewa kila ma da hadin bakin shi komai ya faru, maganganu dai kala daban daban, da ire iren bayanan da ake ta samu daga makiyansa aka garkame shi a police station tare da kwace wayarsa da sunan idan ma akwai hadin baki a tsakaninsa da 6arayin ai dole zasu kira shi. Shi dai ya mika lamuransa ga ubangiji, iyalansa suma duk suna cikin tashin hankali, mutum tsofai tsofai da shi amma ace wai zai aikata irin haka, duk da cewa duniya abar tsoro ce kuma ba kowa bane abin yarda amma me tsoho dan shekara kusan sittin da zai yi da hada kai da miyagun mutane, wasu dai sun goyi bayan kamasa yayin da mutane da yawa suka fara zanga zanga akan lailai lailai a sake shi.

Yan gidan kam basu da abin
cewa dan suma suna ta kansu ne, su kawu har yanzu suna gidan mu sun kasa komawa, ga gidan ya musu kadan amma tashin hankali yasa basu gane hakan bama kullun suna zaune jugum jugum wasu a daki wasu a falo wasu a tsakar gida, babban tashin hankalinsu yaran da suka ki cin abinci da yawan kukan da suke musu, ga zazza6i har ya fara kama su dan jikinsu yayi zafi rad’au, dole suka kira mijin _Kisma_ suka sanar da shi ana bukatan ta a gida domin yaran, shima da yaji abin da yake faruwa duk hankalinsa ya tashi yace zai kawo ta idan yaso sai su koma da yaran _Sokoto_ kafin aga abin da Allah zai yi.Shuru motar ya yi babu wani me magana har muka fita daga _Jos_ karshe dai ganin mu mukayi a _Abuja_, daga nan kuma muka shiga _Lokoja_ inda a nan aka tsaya dan shan mai, a lokacin gari ya fara duhu sosai, ko sau daya ba’a tsaya salla ba ko da yake sun san ai guduwa zamuyi idan har akace za’ayi wani dogon tsayuwa da har zamu samu mu fita, abinci ne dai aka tsaya a _Abuja_ aka saya a wani restaurant, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya tsayar da mu akan hanya wato ina nufin jami’an tsaro abin kamar sidabaru.

+

Bayan mun fito daga cikin gidan mai muka fara tafiya, mun danyi nisa muka tsaya direban motar mu da abokan tafiyarsa sukayi fitsari, in da akace idan zamuyi mu fito, hamdala nayi tare da daukan jakata na runguma, sosai abin ya min dadi dan yanzu zan aiwatar da shirina dan na dade ina tunanin wannan abin da nake kokarin son aikatawa. Bayan mun fito fitsari akasa wadannan yan matan gadin mu a matsayinsu na sabbin 6arayi, muna cikin yin fitsarin na faki idonsu na farayin baya baya har na kai jikin wani karfe dake kan gadan, ruwan dake kwarara ta kasa gadan na kalla a lokacin kuma naji suna nema na suna haska tocila, “ke ina kike a ina kike tunanin 6oyewa a nan? To gwara ki fito yanzu yanzun nan” ni dai kawai inata jinsu ne amma hankalina baya kan su.

Jin alamun cewa suna daf da inda nake yasa kawai nayi shahada na fad’a cikin ruwan, tare da dauke numfashina duk da cewa ban san yaya abin zai kasancemin ba, bayan na fada na bude idona inda idona ya sauka akan wata mace kyakyawa ta zubamin ido, a raina ina tunanin ita kuma daga ina take amma kuma tsoro ne ke cina sosai domin tana daf dani sai karemin kallo takeyi, a hankali na bi jikinta da kallon Kawai naga jela, sake saurin dagowa nayi domin in tabbatar ita dince ai kuwa ba kizo abin yake min ba itace, mutum kuma kifi wato mermaid, ai ban san sanda numfashina ya gama daukewa ba dama ga ruwa dake shiga idona da hancina, daganan ban san kuma abin da ya faru ba.

A 6angarensu Oga kuwa suna isowa gurin ina wuntsulawa, mamaki ne ya kamasu ganin babu tsoro a tare dani kawai zan fada irin wannan ruwan da ban san inda zai iya kaini ba, dan da wuya in samu me ceto na a irin wannan gurin, tsaki kawai sukayi suka juya suka koma motarsu tare da kama hanyar da zai kaisu Lagos. _Amina_ matar da muka hadu da ita a mota sai jimamin abin takeyi sosai taga wautata akan shiga inda na san zai yi wuya in samu mafita, tabbas nayi kasada ba kad’an ba a yadda tayita ayyanawa a ranta, sannan ta fara tunanin ita ma ta yadda za’ayi ta ku6uta, tunda su wadancan karuwan abin ba damunsu ya yi ba, da sukaji cewa za’a cafki kudi a harkar kawai suma suka tsunduma suna amince da shiga cikin 6arayin.

STORY CONTINUES BELOW

A hanya suka kwana zuwa safiya suka shiga _Lagos_ sosai suka gaji hakan yasa suka wuce masaukinsu, daki daya aka bawa matan, mazan kuma daki biyu ko wani 6angare tare da ainihin 6arayin, _Amina_ kuwa duk da gajiyar dake tare da ita ta kasa barci sai tunanin yadda zata fita daga cikin wannan bala’i takeyi, tunda take ko cikin _Abuja_ bata ta6a zuwa ba sai ga shi an wayi gari 6arayi sunyi ram da ita har zuwa _Lagos_ sa’anta d’aya tana da yan kud’ad’enta ko da ace zata samu tserewa bata da damuwa ta fanni kud’i. A haka tayi kwana bakwai tare dasu, a dare na uku da suka fita operation ta samu ta tsere inda ta fad’a hannun na gari ta samu barin garin _Lagos_ cikin ikon Allah har zuwa _Abuja_ bata samu matsala ba, daga nan ta shiga motar _Jos_. Bayan ta isa ta ara wayar kanwarta ta kira mijinta ta sanar da shi abubuwan da suka faru, sosai ya jinjina lamarin tare da adduar Allah ya kara karewa, bayan sun gama wayar ta zauna tunanin inda nake da kuma yanayin da nake ciki wanda take fatan ace ina cikin koshin lafiya…

_________________________

” _Yaro_, kai _Yaro_ wai ni tunanin me kake tayi ne tun d’azu? Ka wani zuba tagumi kamar anyi maka mutuwa, haba dan Allah ka rage yawan tunanin da kakeyi inba haka ba zaka iya janyo wa kanka wani fitinar. Ni a gani na duk wani abin da _Iya Gaje_ take maka ya kamata a ce ka riga ka saba, to menene kuma abin da zai sa ka tsaya kayi ta tunani, dan Allah ka ajiye komai ka fuskanci rayuwarka”. Juyawa ya yi saitin inda muryan _Aminu_ yake fitowa kafin ya yi ajiyar zuciya yace “ni ba tunanin _Iya Gaje_ nakeyi ba sai dai tunanin rayuwa ta da kuma abin da zai iya faruwa a gaba, Allah ya gani ina son inyi aure amma kuma ya zanyi tunda abin yaki yiyuwa mata babu tausayi bare tsoron Allah, duk wani nakasasse sai ya sha wahala yake samun aboki ko abokiyar rayuwa, idan a 6angaren macece sai ta sha wahala idan kuma babanta me kudi ne ko kuma Itan tana da abin kudin wanda zai amfani me aurenta shikenan sai kaga auren jari ya kankama inba wani ikon Allah ba mazan kirki suna wahala a fannin auren mace me nak’asa, a 6angaren mu maza muma idan ba mu ko iyayen mu sun kasance wani abin ba wanda za’a mora zai yi wuya mace ta so mu, amma munfi mata nak’asassu saurin  samun abokan rayuwa na kwarai wanda zata so mu dan Allah macen kirki wacce ta yarda da kaddara kuma ta yarda da cewa muma haka jarabawa ne a garemu.

Kallonsa kawai _Aminu_ da _Hamza_ sukeyi suna masu tausayi mishi, su kansu da ba nak’asassu ba suna masu tausaya wa kansu balle kuma shi tabbas dole ya tausaya wa kansa kuma dole me imani ya tausaya mishi, cigaba ya yi da cewa “rayuwa kenan Allah yana jaraba bawansa ta ko wani fanni ba wai dan baya son sa ba sai dai ya gwada karfin imaninsa ko kuma ya gwada na wasu ta hanyarsa, duk wanda Allah ya jarabce shi ta wani hanya to ya godewa Allah kuma ya yi kokarin cin jarabawar, domin Allah yana son shi shiyasa ya jarabceshi domin ya gwada karfin imaninsa kuma yasa shi ya gyara kura-kurensa” dan jim ya yi kafin ya ci gaba “a wannan zamanin da masu kudi sai masu kudi talaka sai talaka nak’asassu kuma sai nak’asassu abin ba’a cewa komai sai godiyar ubangiji tare da adduar Allah ya yaye mana son zuciya, da yawan mutane sun dauki masu nak’asa a matsayin wani halitta ne na daban wanda basu da galihu, ni abin da wani lokaci yake bani mamaki shine a gidajen masu kudi ba’a gane suna da nak’asassun y’ay’a saboda yadda ake ji da su ake karramasu, amma a gidajen talaka ne kawai ake kyamatar masu nak’asa, idan dan me kudi nak’asasshe zai tunkari budurwa ba zata ta6a nuna mishi kyama ko kiyayya ba, wata ma da kanta take neman ya sota idan kuma macece wani da gudu zaije auren jari amma a gidajen talaka sai a maida masu nak’asa kamar wasu halittu na daban, a maida su mutane marasa galihu ni shiyasa nake matukar tsoron tunkaran ko wata irin mace, na gwammace in auri irina zaman sai ya fi yimin dadi, dan wata a irin nawa nak’asan sai tayi ta cin amanata, ku dai kawai Allah yasa mu dace, ku ta shi muje muyi sallah” ya fad’a yana laluban sandarsa kafin ya mik’e, suma duk suka tashi jiki a sanyaye.

_________________________

A bakin kofar kewayen ya ajiye bukar sannan ya fara takawa a hankali zuwa cikin falon, guri ya samu ya zauna sannan yace “har yanzu shuru jami’an tsaron basu sake cewa komai ba, Allah dai ya bayyana mana ita ya kuma kareta a duk inda take” kallonsa sukayi kafin suka ce amin, su mamaki ma ya basu, shi da bai san ya yiwa mutane addua ba sai idan mutuwa sukayi, addua ko sanya albarka wa y’ay’a baya daga cikin tsarinsa sai in ta kama ko kuma abu na kudi ya shiga tsakani. (Iyaye da yawa suna wannan kuskuren na rashin sanyawa yaro albarka amma a haka suna jiran miracle ya faru na gyaruwar lamarin y’ay’ansu, kuna raye idan bakuyi yaranku addua ba wa zai m
usu, wani yaron sai dai yaji iyayensa na gayyar sod’in sanyawa wasu albarka amma abu ne me wuya shi ya samu hakan daga garesu, wani ma sai dai ya gani a wani waje anayi amma ba’a cikin gidan su ba, babban kuskure na bama karami ba, domin yaron dake tare da albarkar iyayensa ba zai ta6a ta6ewa ba, ko da ya kuskure hanya da yardan ubangiji zai dawo dai-dai, dan Allah iyaye ayi kokari a yawaita sawa yara albarka, wasu ma suna neman ace a nasu yaran suke sawa albarka amma Allah bai azurta su da samu ba, kai ka samu amma sai ya yi maka wahalar fad’a gaskiya ya kamata a gyara, Allah yasa mu dace”.

Da sallama su _Kawu Sule_ da _Kawu Nafi’u_ suka shigo, bayan sun zauna an gaisa shine suke sanar dasu cewa daga ofishin yan sanda suke kuma har yanzu ba wani cigaba amma dai sun hakura sun bada belin direba, yanzu ma sai da suka tabbatar sun kai shi gurin iyalansa sannan suka dawo gida, hamdala suka shiga yi saboda dama burinsu suga cewan an sake shi ya koma gida, ai ko da ace akwai hannunsa mutumin ya tsufa ba zasu so ace sun barshi a ciki kejin yan sanda ba domin azabtar da shi kawai wasunsu zasuyi, kuma ai gaskiya baya buya komai daren dadewa sai ya bayyana, dan haka gwara a barshi ya koma gida ayi kuma adduar Allah ya kawo sauki a cikin lamarin.

_Kisma_ itama tazo sai kuka takeyi daker aka lallasheta, yaran ba laifi sun dan sake da suka ganta har sunci abinci amma sai da aka musu allura saboda zazza6in da yake jikinsa. Tare da mijinta suka zo, dan haka tare zasu koma saboda gurin aikinsa, shirya musu kayansu tayi a cikin baby bag dinsu me kyau dan tare dasu zata koma sai a mayar dasu makarantar su nada. Duk da cewa kakanninsu basu so hakan ba amma ya zasuyi hakanne kawai zai rage musu wani abin tunda sunfi sabawa da _Kisma_ ita kuma ba zai yiyu tazo ta zauna da sunan jiran mahaifiyarsu ba bayan tana da aure, auren ma da ko wata bai cika ba.

A hankali nake bud’e idona amma dishi dishi nake kallon ko ina, sake rufe idon nayi tare da bada ratan mintina biyu sannan na sake bud’ewa, kallon ko ina na shiga yi a cikin d’akin, wata mata ce tayi sallama ta shigo, kallonta nayi ina kokarin gano wani abu a tare da ita, cike da tsananin farin ciki take cewa “Ashe kin tashi? to bari _Malam_ ya dawo ya sake dubaki” ni dai kawai kallon mamaki nake binta da shi, ni ina son tuno da wani abun ne ma, meke faruwa ne dani, a ina nake, wacece ita? Duk shine tambayar da nakeyiwa kaina, sai dai na kasa fahimtar komai, abin da zai k’ara tarwatsa komai shine wacece ni? Daga ina nake? Me nakeyi anan? Daga ina nazo? Duk wadannan tambayoyin shine yake yawo a cikin kwakwalwata, ina son tuno abubuwa da yawa sai dai dana fara tunani zanji kaina ya yi nauyi daganan sai barci.

Yanzun ma hakance ta faru barci ya sake d’auke na, nayi kusan awa biyu ina barci sannan na farka, wata yarinyace ta shigo tana cewa “Sannu bakuwa, ya jikin naki, Da fatan kin danji sauki? Zaki iya tashi kiyi alwala ne?” Ta fada tana murmushi, ni dai kallonta nakeyi ina mamakin yawan tambayoyin data ke jefamin, wanne zan amsa mata toh? Samun kaina nayi da cewa “dan Allah wacece ni kuma a ina nake” cikin sauri ta kalloni, sai naji duk jikina ya yi sanyi, ko dai na fada ba dai-dai bane naga duk yanayinta ya sauya, na shiga uku menayi ne haka, tashi tayi ta fita suka dawo tare da wannan matar, zama tayi kusa dani kafin tace “baiwar Allah baki san wacece ke ba, ko kin kamu da cutar mantuwa ne, mun shiga uku bari _Malam_ ya dawo sai a san abin yi” ta fad’a cike da jimami ni dai kawai kallonta nakeyi na rasa fahimtar komai.

Zama nayi shuru chan dai nayi tunanin gwara in tashi inyi sallar ko Allah zai sa in samu tuno koni wacece, tashi nayi nasa hijabin dake kusa dani sannan na fita waje, a tsakar gidan na samu wannan matar tana jin radio yayinda yarinyar take tankad’e sai wata kuma daban tana zauna ta daura kafa d’aya kan d’aya, ” _Mama_ ko zan samu ruwan alwala dan Allah” d’ago kai tayi ta kalleni sannan tace “a’a yarinya har kin fito kenan, ” _Ummulu_ bata ruwa a buta tayi alwala” yarinyar dazu ne ta kawo mun tare da nuna min kewaye akan idan ina son shiga “nagode _Ummulu_” na fada ina son tabbatar da ko itace me wannan sunan, “ba komai Anty” ta fada tana murmushi wanda ba lura hakan dabi’ar ta ce, juyawa nayi zuwa inda ta nuna min a matsayin kewaye, komai tsaf-tsaf gwanin ban sha’awa hakan na nuna cewa mutane ne masu tsafta, bayan na gama uzurina na fito nayi alwala a wani gurin da suka ke6e dan yin alwala sannan na shiga d’aki na shimfida sallaya.

Bayan na idar na fito waje inda na samu duk suna zaune akan tabarma, har dayan yarinyar wanda na lura akwai girman kai a tare da ita, hira sukeyi tsakanin _Mama_ da _Ummulu_ wani lokaci su sakoni a ciki, abin da na sani inyi magana wanda ban sani ba inyi shuru ko in shiga duniyar tunani, lokaci zuwa lokaci _Ummulu_ na zuwa duba girkin data d’aura, bayan mintina talatin ta sauke tare da zubawa a babban tray ta kawo ta ajiye a gaban _Mama_ “sannu da aiki” _Mama_ tace kafin ta kalli daya yarinyar tace ” _Asiya_ matso muci abinci ko, tunda baki da aiki sai danna waya sai kuma kici ki kwanta” dan tura baki tayi sannan tace “a zubamin nawa daban amma dai bazanci da wannan abar ba” tsaki _Mama_ tayi sannan tace “sai kije ki diba tunda Allah ya baki kafa da hannu har da idanun da zaki ga komai da komai” tana gama fad’a tace ku matso muci, tana kai dubanta garemu ni da _Ummulu_ wanda na lura ranta ya 6aci da abin da _Asiya_ tace, ni dai bance komai ba naja jiki zuwa kusa da abincin sannan mukayi bismilla muka fara ci.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan mun gama ci na taya ta muka kwashe komai zuwa inda suka kewaye dan wanke wanke, cikin mintinan da basu fi biyar ba muka gama, duk da cewa tace in barshi zatayi amma naki, _Mama_ kuma ta shige d’aki shiyasa bata san abin da mukeyi ba dan cewa tayi inje in huta kafin _Malam_ ya dawo, ita kuma _Asiya_ har yanzu bata d’ibo abincin ba, da alama tana zaman jiran _Ummulu_ ta zuba mata shiyasa, ai kuwa hakanne ya kasance muna gamawa ta zuba mata ta bata sannan muka shige d’aki.

“Wannan din yayarki ce ko kuma kanwar _Mama_ ce, kallona tayi kafin ta fashe da dariya wanda ya mata kyau sosai sannan tace ” gaskiya kin cuce ta wai kanwar _Mama_ dan kinganta wani iri kamar ta tsufe? yayata ce kuma ita nake bi, a yadda take harkan karuwanci ba dole ki ganta haka ba ko wani tsami gaye ya mai da ita motar haye, kuma ni banga laifinta ba, laifin iyayen mu na gani da suka zuba mata ido tun tana yar karamarta dan kawai tsaban soyayyar da suke mata suka kasa kwa6arta, a yanzu ta kai shekaru ishirin da takwas kuma tun tana yar sha biyar ta fara rabawa maza kanta, kuma ba kowa bane sila sai _Mama_ saboda son kudi irin nata ta sata a harkar talla inda sai ta samo kud’i take barinta ta shigo gida hakan yasa ta za6i wancan hanyar ba tare da kowa ya sani ba sai data zubar da cikinta na uku shine aka san da abin da take aikatawa, ni dama _Baba_ yace babu tallar da zanyi tunda yana biya mana bukata dai-dai gwargwado dan haka karatu zanyi, ita kuma data biyewa _Mama_ shine ta fad’a cikin gararin rayuwa, duk da haka danasanin da _Mama_ tayi ba wani na kirki bane tunda ta barta ta cigaba da zuwa talla ana mata juye, yanzu dai bata talla amma kuma har yanzu tana bin maza kuma taki aure, yayan mu _Yaro_ yaso ya aureta amma taki wai saboda shi makaho ne kuma talaka, da farko yayar mu yaso aura Allah bai yi ba kuma suna son junansu, ita kuma ganin halin data jefa kanta yasa yaso auren ta amma taki kuma _Mama_ ta goya mata baya wai acewar su me na sama yaci balle ya bada na kasa, shine aka rufe maganar ko _Baba_ bai san da zancen ba,  to har yanzu jiya wa yau bata sauya zani ba tana ta fama ga shi duk ta tsufe kamar me cutar aids”.

Kallonta na tsayayi kawai ina harhad’a kalamanta, lailai _Asiya_ ta rika sosai ta wuce tunani na, kuma _Mama_ ta tafka kuskure wanda sai nan gaba zatayi nadama mara amfani, shima kuma _Baba_ bai kyauta ba daya biye musu ya barsu da son zuciyarsu, da tun farko ya hana kamar yadda ya hana _Ummulu_ da abin baiyi nisa ba, ga shi yanzu abin nata ya wuce misali ta bar t
allar ta koma karuwancin hankali kwance kuma an rasa yadda za’ayi da ita, ice tun yana dan karami ake tankwasa shi, nata kuwa ya wuce lokacin da za’a iya tankwasawa sai dai kuma wani ikon Allah, jiki magayi lokaci na zuwa da zata girbi abin da ta shuka “Allah ya kyauta ya rufa asiri amma gaskiya banji dadin labarin nan ba, kuma su _Mama_ suna da hannu a lalacewarta, Allah yasa ta gane gaskiya” murmushi tayi sannan tace “Amin yar uwa, kullun ina mata adduar shiriya nima amma abin nata kullun gaba yakeyi”.

Kwanciya nayi ina tunanin yadda rayuwar gidan yake, daga baya kuma na koma tunanin yadda za’ayi in tuno koni wacece, juyawa nayi na kalla _Ummulu_ sannan nace “naga alamun kuma baku sanni ba, kuma baku san daga inda nazo ba, shin a ina kuka sameni?” Barin karatun da takeyi tayi sannan tace min “a ruwa _Baba_ ya tsintoki, ruwan dake gudana daga farko gari, kuma babban ruwan da yake cikin garin lokoja, wanda ya shigo zuwa rafin dake cikin yankin mu, _Baba_ yaje tsinko ganyen magani da yake sayarwa bayan ya dawo daga aiki, shine ya same ki a cikin wannan ruwan ya kawo ki gida, sannan kinci sa’a sosai da kike a raye domin duk wanda ya shiga wannan ruwan sai wani ikon Allah yake fito da shi, da yawa da sukayi kasadar shiga basu fito a raye ba, sai masu sa’a irinku, kuma ina me tabbatar miki da cewa zai yi wuya ki tuno da ko ke wacece domin tabbas kin hadu da yan ruwa wanda suka goge miki komai daga cikin tunaninki dan karma ki iya tuno da suffar su”.

Shuru nayi ina ta kokarin hada maganganunta musanman na ruwan data min bayani ina son tuno da wani abin amma naji na kasa karshe na fara gani dishi dishi sai kuma wani irin sarawa da kaina yakemin hakan yasa na kwanta tare da barin tunanin dana fara, ganin haka yasa _Ummulu_ tayi shuru itama ta cigaba da karatun ta.

_Baba_ bai dawo gida ba sai bayan da muka gama cin abinci lokacin har anyi sallar isha’i, kamar yadda dazu mukaci ba _Asiya_ haka ya kasance yanzun, bayan mun gama mukaji sallamar _Baba_ gaishe shi mukayi, ya amsa tare da zama akan kujeran roba dake ajiye a gurin, “yaushe bakuwar ta tashi” ya fada yana kallon gefen _Mama_ “tun da azahar ta tashi kuma har taci abinci ma, matsalar daya ce kawai” shuru tayi na dan wasu sakanni kafin ta cigaba da cewa “ta manta ko ita wacece, dan tambayar mu takeyi ko ita wacece” kad’a kai ya yi sannan yace “dama nasan za’a rina, data samu ta fito a ruwan a raye ma sai ta godewa Allah, sauran abubuwan zasu zo da sauki in Allah ya yarda, akwai magungunan dana had’a mata sai ta cigaba da shan su, sannan batun suna kuma zamu rinka kiranta da Asma’u, ina fatan hakan ya miki ko y’ata?”.

Cikin jindadi na amsa da ” eh _Baba_ nagode Allah ya kara girma, Allah ya biyaka da gidan aljanna” sosai yaji dadin adduar dana mishi ya amsa da “Amin” magana suka cigaba dayi da _Mama_ kafin _Ummulu_ ta shiga kitchen dan dauko mishi abinci, muna zaune a gurin mukaji sallaman wani wanda ban san ko waye ba, kyakyawa ne amma kuma makaho, idan ka kalle shi baza kayi tunanin cewa baya gani ba sai kaga yana lalube ko kuma ka kalli sandar hannunsa shine zaka fahimci lailai baya gani, yana shigowa ya iso inda muke ya tsuguna tare da gaishe da _Baba_ da _Mama_ sannan muka gaishe shi nida _Ummulu_ ita kuma _Asiya_ sai taunar awara takeyi tana harare harare, ni dariya ma abin yaso bani, waya kulata da zata rinka harare harare kamar sabuwar kamu. Bayan sunci abinci da shi da _Malam_ ya d’an jima a zaune kafin ya mana sai da safe ya tafi, inda naga _Mama_ tabi bayan sa da harara, ina d’aga kai muka had’a ido da _Ummulu_ alama tamin akan mu tashi mu shige ciki, ba musu nabi bayan ta bayan munyiwa su _Baba_ sai da safe.

“Shine yayan mu _Yaro_ wanda yake zaune damu, iyayensa sun rasu tun yana karami shine _Baba_ ya dauko shi, kuma mahaifinsa yayan _Baba_ ne, su kad’ai iyayensu suka haifa, shi kuma shi kad’ai ne a gurin iyayensa, mu kuma mu uku ne a gurin iyayen mu, da yayarmu da tayi aure wacce da suka so juna da _Yaro_ sai kuma _Asiya_ sannan ni. Tunda aka haifeni na fahimci cewa _Mama_ bata kaunar _Yaro_ in takaice miki zance ta sha gwada kashe shi amma Allah bai yi zai mutu ba, tare da had’in kan kawarta da kuma _Asiya_ ake son a kashe shi amma dake ance zakaran da Allah ya nufa da cara, ko me za’ayi hakan za’a gan shi a barshi to hakane ya faru da _Yaro_ sun kasa cin galaba akansa”.

Mamaki ne ya rufeni, haka kawai suke son kashe bawan Allah, to meya tare musu haka, ita ba ita take ciyar dashi ba sai dai tace su suke dafawa amma shine zata saka shi a gaba irin haka, ni a iya sani na me kudi ko kuma wani da yake samun cigaba a lamuransa shine ake sawa ido har ayi kokarin salwantar da rayuwarsa, to wannan ga shi makaho bai tara komai ba,bai ajiye ba bai bawa wani ajiya ba, Allah ya kyauta yasa mufi karfin zukatan mu “Allah ya ganar da ita gaskiya” na fada ina tunanin ko nayi dai-dai ko banyi ba, sai dai naji tana cewa “Amin nima abin da nake yawan cewa kenan” hakan da tace shi yasa nayi ajiyar zuciya…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *