DEEMAH CHAPTER 14 BY ZAHRATEEY
A yau su _Mama_ suka gama bidirin biki kuma suke shirin dawowa sai dai abin da zasu taras a gidan bana dadi bane makiyinsu harda mata da yara lailai akwai tashin hankali bama kamar ita _Hanifa_ da take kokarin kawarda _Jidda_ ga wata kuma ta 6ullo har ma da yaranta sannan ga yaran _Khadeemah_ da suka riga suka iso _Bauchi_ saura a kai su cikin dangin mahaifin su.
Sati guda _Jidda_ tayi a kwance kafin ta samu saukin jikinta, kuma a cikin sati guda da tayi duk _Bibalo_ keyin abinci tana aikata mata, kuma ita take kula da yaran da kuma babansu. Sosai _Hajja_ taji dadin yadda _Bibalo_ take kula da abokiyar zamanta, haka _Anty Aisha_ ma ta yaba mata sosai. Bayan ta samu sauki ta kar6i nata ayyukan inda suka raba kwana uku-uku kuma duk wacce bata da duty ita take kula da yaran, sannan wanda take da duty a 6angarenta ake had’uwa aci abincin safe dana rana da dare kuma ko wacce a 6angarenta take cin abincin ta. Me duty tare da me gidanta mara duty tare da yaran.
A yau suke saka ran ganin yaran _Sufyan_ na gurin _Khadeemah_. Ashe har sun dawo sun kwana biyu a gurinsu _Baba K_ yau za’a kawo su, kuma su _Mama_ ma yau suke hanyar dawowa. Family meeting aka had’a dan gabatar da _Bibalo_ da y’ay’anta da kuma yaran _Jidda_ dake gidan _Hajy Naja_ sai kuma yaran _Khadeemah_. Kuma an shirya hakan ne kafin isowarsu _Mama_.
Mutane da yawa sun zo ma’ana yaran gidan da sukayi aure da kuma jikoki duk sun hallara, babban falon gidan da akeyin ko wani taro a cikinsa na iyaye maza cike yake da mutane da yawa y’ay’a da jikoki dan Allah ya albarkace su da tarin y’ay’a da jikoki inda a cikin jikokinsu ne suke da y’ay’a maza masu yawa amma a y’ay’an su _Sufyan_ ne kawai d’a namiji da Allah ya azurta su da samu. Kuma Allah ya azurta su da tarin tagwaye daga y’ay’a har jikoki ko dan iyayensu sun kasance tagwaye ne haka zalika kakannin su suma duk tagwaye ne kuma zuria d’aya. D’akin su _Sufyan_ nema babu tagwaye a y’ay’a sai a jikoki.
_Daddy_ ne ya bud’e taro da addua sannan _Abba_ ya yi bayanin dalilin abin da ya tara su anan, inda aka gabatar musu da _Bibalo_ da y’ay’anta da kuma y’ay’an _Jidda_ da suke hannun kakanninsu da y’ay’an _Khadeemah_ wanda aka kawo su a yau tare da kakannin su maza da mata, da yan uwan mahaifiyarsu, duk mamakine ya cika su da al’ajabi, munafukan cikin su kuma tsoron Allah ne ya shigesu wanda yake iko akan komai kuma yake aikata abin da ya so a duk sanda ya so, ga shi duk yadda suka so kawar da shi sai Allah ya kara azurtashi da wasu y’ay’a mazan wanda zasu maye gurbinsa, lailai kainuwa dashen Allah sai dai ayi hakuri a kyaleshi domin babu ne iyawa dashi, duk suka zubda makamansu tare da neman yafiyar ubangiji akan citarsa da suka so yi amma kuma bai basu dama ba sai a _Mama_ ya bawa ikon cutarsa wanda kuma a halin yanzu ita ce a ruwa domin zai yi wuya ace _Daddy_ ya cigaba da zama da ita haka zalika kuma ta shafawa kanta bakin fenti wanda ba zai ta6a goguwa ba, gwara ita dama aure ne ya hada amma su jini daya suke idan da su aka kama da aikata haka tabbas sai sunji kunyar kansu da kansu.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan an gama gaisawa da juna an jajantawa juna abubuwan da suka faru aka kuma taya juna murnan samun karuwa a cikin zuria da murnan dawowan _Sufyan_ sai aka shiga hira kafin aka ci abinci, yan gidansu _Khadeemah_ suka koma tare da bawa _Jidda_ da _Bibalo_ amanar yaran, sannan sauran yan uwan su _Sufyan_ suma suka fara shirin tafiya gidajen su yayin da wasun su kuma sai washe gari zasu koma.
Tun da suka shiga cikin gidan suka ga motoci jikin su ya basu ba lafiya ba. Wasu motocin fita sukayi yayin da wasu kuma babu alamun a lokacin za’a fita dasu, ta so ta tambayi masu gadi amma kuma ta fasa, har cikin 6angarenta direban ta _Dauda_ ya kai musu kayansu. Basu bi ta kan kowa ba sai da sukaci abinci suka huta kafin suka shiga 6angaren d’akin taro wanda anan suka samu yan gidan har ma da wad’anda basu tafi ba. Babu wanda ya nuna musu wani alamu kamar yadda _Daddy_ ya bukata, yadda aka saba muamala dasu hakan aka cigaba dayi, bayan sun gaisa da mutanen cikin falon suka nemi sanin ko lafiya gidan ya cika harda baki? Anan ake nuna musu _Sufyan_ da _Bibalo_ da yaransa shida da suka karu acikin dangi maza uku mata uku. Tashin hankali wanda ba’a sa mishi rana wani irin jiri ne ya fara d’iban _Mama_ daker ta saita kanta ta nuna farin cikinta kamar da gaske haka abin yake a ranta, duk wanda ya ga yanayin yadda ta kar6i zancen sai ya kara gaskata abin da aka fad’a a kanta, basu kara dogon lokaci ba ita da maman _Hanifa_ suka koma 6angarenta cike da bakin ciki da tashin hankali. Yayinda uwar munafukai mai fuska biyu munafukar 6oye ta iya danne abin da yake ranta ta bayyana farin cikin ta me nuna cewa tun daga zuciyarta yake fitowa, kowa a gurin ya yarda da kyakyawan halayyarta wanda babu irinsa a tare da iyayenta, kowa yana tausaya mata data fito daga tsotson mutane marasa mutunci da imani irinsu _Mama_ sai dai basu san cewa ita ta wuce su _Mama_ tana zarce su a munafurci da iya had’a guri, ta fisu bakin zuciya da rashin imani duk wani mummunan halayyarsu ta damasu ta shanye.
Bayan _Hanifa_ ta gama nuna musu farin cikinta wanda suka yarda da ita dari bisa dari ba tare da tunanin meke cikin ranta ko zuciyarta ba, ta musu sallama tare da koma 6angarensu da sunan zataje ta huta saboda tafiyar mota sukayi bana jirgi ba. _Bibalo_ kuwa zuciyarta yaki aminta da yanayin _Hanifa_ sam sam a ranta batajin ta yarda da ita amma ganin yadda _Jidda_ ta nuna farin cikin ganinta ya sanyaya mata gwiwa duk da cewa ta fuskanci ita _Jidda_ macece me saurin yarda da mutum da saurin manta sharri tare da yiwa mutum kyakyawar zato wanda hakan shine yake cutar da ita a cikin rayuwarta. Sai dai ita kam ba zata bari a cuceta tanaji tana gani ba kuma zatayi iya kokarinta gurin yin taka tsantsan da _Hanifa_ dan tunda har taji bata mata ba bata kwanta mata a rai ba to tabbas akwai wani abu mara kyau a tare da ita.
A 6angaren su _Mama_ sai da tayi amfani da inhaler dinta saboda tashin hankalin da take ciki wanda ya janyo mata tsarkewan numfashi, sai da ta d’auki kusan awa guda kafin numfashinta ya dawo dai-dai. Kukan bakin ciki ta fashe dashi wanda ta kasa rikewa a duk yadda ta so sai da ya su6uce mata “me kenan zan gani ni _Laminde_ yanzu aikin da boka ya mana ya lalace kenan ko kuma menene? Babban tashin hankalina yaran da aka gabatar a matsayin y’ay’ansa (ni ko nace dan ma bata san da y’ay’an _Jidda_ da suke raye ba)” ajiyar zuciya _Mansura_ mahaifiyar _Hanifa_ tayi “wallahi _Lami_ ni duk na rasa ma abin cewa, inace boko ya tabbatar mana da cewa ba zai ta6a bari asirin jikinsa ya warware ba? Ni bana wannan ba na san tunda har _Hanifa_ ta gan shi to tabbas sai tayi iya yinta dan aurensu ya tabbata, kinsan cewa tana son shi tana kuma kaunarshi dan haka mu fara taka mata birki kafin ta aiwatar da wani kudirinta akansa”.
A 6angaren _Hanifa_ tana komawa 6angarensu ta nufi falon _Mama_ dake sama, dan tunda har bata gansu ana kasa ba t
a san suna na sama, tana zuwa kuwa kamar yadda tayi tsammani taji tattaunawar da sukeyi a kanta, sai da ta gama jin duk abin da suke fad’a sannan ta wuce d’akinta ta kira likitanta ” _Hanifa_ ta samu kenan? Dan na san sai idan ta samu kike kirana” tsaki taja da d’an karfi ” _Dr Nasir_ bana son rashin mutunci ka bari mana kaji dame nazo kafin ka fada abin da kake so din! Na samu mahaifina kuma tabbas da ganinsa zaka tabbatar ni jininsa ce kuma wani abin mamakin shine ba _Anty Mansura_ bace mahaifiyata _Mama_ ce mahaifiyata! Amma kuma ban nuna musu na san da zancen ba har sai na samu cikekken bayani akan yadda akayi hakan ya faru yadda _Mama_ ta haifeni alhali azahiri bata haihuwa kuma sannan meye dalilin mak’alawa _Anty Mansura_ kanwarta ni a matsayin uwar data haifeni. Zan zo office din ka zamu k’arasa hiran mu a chan dan tafi sirri kuma abu na gaba shine na kuma k’unso wani wanda yake bukatan bin rariya” murmushi ya yi yace “ai dama shege ke haifan shege, ki bincika tarihin iyayenki da kyau domin akwai abin da baki sani ba har yanzu, sai dai kin zo din kawai amma ya kamata ki waye haka ki daina d’auko ciki kina zubarwa domin kin kusa lalata mahaifarki da kan…” bata gama jinsa ba ta kashe wayar ta buga shi da k’asa.
Safa da marwa kawai takeyi acikin d’akin bayan sun gama waya da _Dr Nasir_ tana tunanin shin me kalamansa suke nufi? Da ita dasu _Mama_ duk shegu ne? Ta san dai _Mama_ yan _Bauchi_ ne kuma ta san gidan da yake gidansu _Mama_ duk da cewa iyayensu da suke ikirarin iyayensu ne duk sun rasu kuma su biyu kawai iyayen suka haifa. Family house ne gidan kowa da 6angaren sa kuma su ba masu kudi bane sai dai suna da rufin asiri. Gyalenta ta d’auka ta yafa ta fice daga gidan gaba d’aya adaidaita sahu ta tare ta shiga, tana zuwa gidan ta sauka sannan ta shiga, 6angaren kakanninta yanzu wasu samari biyu ne suke ciki kuma kannen a gurin _Mama_ yaran kawun su _Mama_, 6angaren _Nene_ ta shiga wata masifaffiyar tsohuwa me sanya ido akan lamarin kowa gata da iya gulma da kinibibi, tayi sa’a ita kad’ai ta samu, bayan sun gaisa ta ajiye nata kud’i dan ta san sune abokan tafiyar _Nene_ “ina son sanin gaskiya akan rayuwarsu _Mama_” d’aukan kud’in tayi ta kunshe a bakin zaninta sannan ta 6antari goron dake hannunta kafin ta fara mata bayanin cewa ai su _Mama_ shegu ne sai dai an rufe maganar ne saboda rufuwan asirin ahalinsu, iyayensu yan uwan juna ne sai dai zaman dadiro sukayi har aka haifesu sam-sam sunki yin aure dan shi kakansu yace ba zai auri wacce ya riga ya san bata da mutunciba, mahaifiyarsa kuma tace sai dai ya hakura da aure dan matukar ba kakar _Hanifa_ ya aura ba tunda ya gama lalatata to shi da aure har abada idan yayi kuma bata yafe mishi ba, bayan haihuwar _Mama_ ne duk hakan ya faru daganan suka raba hanya kafin wani lokaci kuma ta sake biye mishi saboda tana son shi ta sake samun ciki inda ta haifi _Mansura_ daganan kuma ta rasu bayan ta haihu shi kuma ya kamu da cutar shanyewar 6ari d’aya be kuma sake tashi ba har ya koma ga Allah, kuma babu wanda ya san wannan lamarin sai tsofin cikin gidan da manyan y’ay’an ma’ana manyan jikoki bayan su sai _Hanifa_ da take fadawa a yanzu. Yan anguwa kuma an nuna musu cewa auren sirri aka musu saboda wasu dalilai to tunda akaji cewan da aurensu sai aka share maganar ganin y’ay’an a tsakaninsu, kuma sanin cewa gidan gidan mutunci ne shiyasa ba’a tada zaune tsaye ba.
Tunda ta koma gida take jin wani irin rashin hankali, gaba daya ta rasa natsuwarta sake sa6an gelenta tayi bayan ta chanja kaya ta nufi gidan _Dr Nasir_ dan ta san cewa yanzu yana gida, ai kuwa taci sa’a yana gida kasancewar bata da shamaki da gidab shiyasa ta shiga kanta tsaye, anan ta same shi yana cin abinci cikin kwanciyar hankali “kinje kin bincika kenan tunda har na ganki a gidana yanzu?” Ya fad’a yana murmushi, zama tayi a kusa dashi tana kallon shi sosai yadda zata iya karantarsa idan yana fadin gaskiya ko karya “taya akayi ka san cewa su _Mama_ shegu ne _Dr Nasir_?” Ajiye cokalin yayi yace “saboda kakanki aminin mahaifina ne kafin ya rasu, wannan dalilin yasa ya fadawa mahaifina halin da yake ciki ni kuma a lokacin naje kai musu sako daga hannun mahaifiyata shine naji zancen nasu, ba wai ya fad’a mishi saboda wani abu bane kawai shawara yake nema, a nan ne ya bashi shawaran ya auri kakarki zaifi samun kwanciyar hankali, bayan ya koma gida da zummar idan ta haihu sai ya aure ta, to abinda da ya faru kuma shine a ranar data haihu sai ta rasu dalilin daya sa kenan ya yanki jiki ya fad’i shima bai sake tashi ba har ya koma ga Allah” bakin cikin wannan lamarin shine ya sata 6arin cikin jikinta a gidan _Dr Nasir_.
Bata farka daga doguwar suman da tayi ba, sai washe gari da safe inda takejin cewa cikin ya fita da kansa kuma ta samu matsala a mahaifarta, sosai tayi kukan bakin cikin abubuwan da suka had’e mata a lokaci guda masu tarwatsa zuciya, ga lalacewar mahaifa, ga rashin asali me kyau tun daga kan iyaye, ga uwa uba masoyinta daya yi aure har mata biyu ga yara maza a zuri’arsa, duk bakin ciki ya mata yawa tama rasa daga ina zata fara shin ta kan su _Mama_ ne ko kan lafiyar ta ko kuma ta kan auren ta da _Sufyan_.
+
Tsaban damuwar dasu _Mama_ suke ciki basu san ma _Hanifa_ bata gidan ba balle kuma su san cewa ta gama sanin sirrinsu harma da wanda yake sun jima da binne wa a tsakaninsu. Har zuwa safiya babu wanda yabi ta kanta balle a san bata kwana a cikin gidan ba haka suka cigaba da tunanin hanyar da zasu bi su samu biyan bukata, sanin cewa ita ma tana cikin tashin hankali kila shiyasa bata fito din ba sai suma suka share ta acewarsu idan ta gaji ai zata fito ko dan ta samu mafita akan auren burin ranta. Karshe ma suka tattara suka tafi gidan bokansu a sannan ne kuma _Hanifa_ ta dawo gida ta taras basa nan, bata wani damu ba dan ta san ko suna nan din ma ba wai zasu gane me yake tafiya a rayuwarta bane, kitchen ta shiga ta bawa me aiki umarnin dafa mata ferfesun kaza da tuwon semo da miyar kuka, sannan kuma tace idan ta tashi kawo mata ta had’a mata shayi me kauri, kafin nan ta wuce d’akinta tayi wanka ta gasa jikinta ta kwanta dan hutawa.
Har bayan azahar data tashi ta cika cikinta basu dawo ba, ta sake koma wa wani barcin, sai daf da magriba suka dawo tana tsaye a bakin taga tana kallonsu duk agajiye ga annuri dake tattare da fuskokinsu alamun sun samu nasara akan abin da ya fitar dasu, tsaki taja ta koma ta kwanta tana tunanin ta inda zata fara tunkarar matsalolin su. Data tuna wani abun kuma sai ta tashi cikin sauri ta fita, a falon dake sama ta same su suna hutawa ko wacce da kwalin juice a gabanta ” _Umma_ ina kukaje haka tun safe?” Wani kallon ki shiga hankalinki tayi mata kafin tace “inda kika aike mu, in banda rainin hankali ba ina ruwanki da inda mukaje da har zaki zo ki titsiye mu da tambayoyin banza” hararanta _Mama_ tayi kafin tace “rabu da yar banza kawai saboda ta ga munayin komai a gabanta ne shiyasa zata mai damu sa’anninta”. Bata ce musu komai ba ta tashi tayi wucewarta kitchen ta bada umarnin abin da za’a dafa mata sannan ta koma d’aki ta kira kawarta domin su tattauna lamarin.
________________________
Ina zaune a bakin hurhu ina kwashe tuwon da nayi, tuwon dawa miyan busasshen ku6ewa, yau _Ummulu_ bata nan tana makaranta _Asiya_ kuma ba’a sakata a lissafin girki. Ina gamawa na kaiwa _Mama_ nata a d’aki sannan na fita na kaiwa _Yaro_ na shi, na dawo na d’auki nawa dana _Ummulu_ na wuce d’aki, a bakin kofar d’akinta na ganta tana taunar chewgum irin dai yadda yan bariki irin ta suke yi, ban kulata ba nayi shigewata ina jinta tana cewa “mutum da gidansu amma bani isa a kawo mishi abincinsa ba sai dai yabi kitchen yaje ya dauka” aikin banza kenan in dai ni take jira in dafa in kai mata har uwar daki zata dade da yunwa kuwa dan bata isa ba kuma bata kai ba, mutuncin _Ummulu_ da _Malam_ shine ma yasa nake girki a gidan idan ba haka ba ai da ba zan ma girka ba, balle har ta samu taci har ta had’a da rainin hankalin cewa ban kai mata a d’aki ba.
STORY CONTINUES BELOW
Salla na farayi kafin naci abinci, ina gamawa na fita dan mike kafa, bayan na dawo n
a motsa jiki kamar yadda na saba sannan nayi wanka, ina fitowa _Ummulu_ tana dawowa “wai sannu hajiyar boko na san kin gaji da yawa” na fad’a ina dariya ” _Anty_ wallahi yau gajiyar dabanne dana kullun paper uku fa mukayi alhali kullun daya mukeyi” ta fada tana shiga dakin nima nabi bayanta, zama tayi ta jawo abincin ta faraci tana cewa ” _Anty_ nikam jiya naji _Mama_ suna hayaniya da _Malam_ abin da bai ta6a faruwa ba kuma inaga duk akan maganar aurena da _Ya Yaro_ ne, ni wallahi inaji kamar in fasa saboda bana son a sanadina a samu babban matsala tsakanin iyayena” shuru nayi ina kallonta nima dai abin baiyi mun dadi ba sam-sam musayar yawun nasu ya tsorata ni domin harda maganar saki a ciki “ni dai kawai sai dai ince miki ki cigaba da addua amma ki fitar da komai a ranki idan _Yaro_ mijinki ne babu tsumi babu dabara sai anyi auren nan ko tana so ko bata so, idan kuma ba mijinki bane sai muyi fatan Allah ya za6a miki mafi alkairi” amin tace sannan ta cigaba da cin abincin ta, ni kuma na saka kaya na tada salla.
Yau ma dai kamar jiyan ya kasance sosai _Mama_ da _Malam_ suka haura har sai da ya yi zancen saki sannan ta natsu ganin cewa tabbas zai iya sakinta saboda maganar auren yasa tayi shuru, “dole ki za6a d’aya ko auren _Ramlah_ da _Yusuf_ cikin kwanciyar hankali ko kuma igiyar aurenki ya tsinke kuma ba wai daya ko biyu ba duka nake nufi, dabara ya rage game shiga rijiya” yana gama fad’a ya yi ficewarsa alamun ransa ya 6aci sosai, bori da zage zage _Mama_ tayi ta mana a cikin gidan bayan fitarsa daker muka shawo kanta tayi shuru akan cewa ni zan hakura da auren _Alhaji me gwanjo_ in barwa _Asiya_ shi ta aura, in dai na amince shikenan zata yarda da kaddararren auren _Ummulu_ da _Yaro_ tunda sanadin haka igiyar aurenta ke lilo shiyasa tun fil azal ta tsani _Yaro_ ta kuma tsani zamansa a gidan.
Ba tare da 6ata lokaci ba nace mata na amince dama ni neman yadda zanyi dashi nakeyi dan ya isheni ya ishi rayuwata, cike da murna _Mama_ tace shikenan magana ta wuce tunda har zata had’a zuriarta da _Alhaji me gwanjo_ dama ita burinta shine had’a zuria da shi. _Ummulu_ tace mata anya _Asiya_ zata yarda da wannan hadin kuwa , tace dolenta ma ta yarda idan kuma taki ita tasan yadda hakan zai faru. Ko da muka koma d’aki _Ummulu_ ke cewa ta 6angaren _Alhaji ne gwanjo_ ba za’a samu matsala ba saboda ba zai ta6a yarda ya kashe kudi a banza ba, dan matarsa ta uku itama yayarta yaso bayan ta gama cinye mai kudi taki aurensa shine ya tada fitina aka bashi kanwar dan iyayen basu da kudin biyansa. Sosai na jinjina alamarin mutumin lailai shiyasa _Mama_ bata damu ba da zancen ko zai amince ko a’a saboda ta san halinsa. _Malam_ kuma bai dawo gida ba har muka kwanta, hakan ya tabbatar min da lailai ransa ya 6aci da yawa dan tunda nazo gidan gaskiya irin hakan bai ta6a faruwa ba.
Ashe sai tsakar dare _Malam_ ya dawo, _Mama_ kuwa barcinta tayi hankali kwance dan ta san ba zai ta6a kwana a waje ba, a yadda naji take fadawa _Asiya_ da safe. A ranar kuma ta kira _Alhaji me gwanjo_ ta sanar dashi ta musanya mishi ni da _Asiya_ duk da cewa bai so ba amma haka ya amince saboda ba zai bari kudinsa da aka ci ya tafi a banza ba ko ba komai zai rage zafi da auren _Asiyar_, ita kuma _Asiya_ bori tayi wa _Mama_ tace mata ita kam ba zata auri sauran wasu ba, nace daga baya kenan wai anyi sadaka da bazawara kuma tace ta fasa sai an biya sadaki baki sake muke kallonta ni da _Ummulu_ yo ba gwara _Alhaji me gwanjo_ ba auren sunna yakeyi ita kuwa rabawa gardawa jiki takeyi cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin me gobe zata haifar ba. Sosai sukayi musayar yawu ita da uwarta mu kam muna daga gefe karshe dai _Mama_ ta zari gyalenta tayi ficewarta ba tare data ce mana komai ba, muma muka kama bakin mu muka cigaba da harkar gaban mu.
Washe gari sai ga _Asiya_ har da kwalliya gurin tarban _Alhaji me gwanjo_ lailai _Ummulu_ tayi gaskiya dama tace da _Asiya_ ta kwantar da hankalinta anyi komai cikin natsuwa da bata jawa kanta aure a sanda hankalinta baya jikinta ba, ko da na nemi sanin ma’anar kalamanta sai take cewa ai fitan _Mama_ shine silar komai dan kuwa ta san gurin malaminsu zasu je ita da kawarta domin ayi aiki akan _Asiya_. Ashe kuwa da gaskiyarta abin da _Mama_ ta aikata kenan dan nayi mamakin sauyawar _Asiya_ a dare d’aya wai ta amince da auren sauran wasu.
Ko da _Malam_ ya dawo _Mama_ bata 6ata lokaci gurin sanar dashi abin da yake faruwa ba, duk da cewa bai so wannan had’in ba amma kuma burinsa shine _Asiya_ tayi aure ta rufawa kanta asiri, daga baya kuma ya tuna cewa ance mishi gurina _Alhaji me gwanjo_ yake zuwa shine ya kirani yake tambayar dalilin faruwan hakan ya akayi komai ya koma kan _Asiya_? nace mishi nice nace bana son shi shine ya nemi amincewar ita _Asiyan_, addua kawai ya yi akan Allah yasa hakan shine yafi alkairi na amsa da Amin.
Cikin kankanin lokaci akayi baikon _Asiya_ da _Alhaji me gwanjo_ sai kuma _Ummulu_ da _Yaro_, bikinsu kuma sai idan _Ummulu_ ta gama jarabawan fita daga sakandiri shine za’a saka. Sosai nayi farin cikin wannan lamarin ko ba komai _Ummulu_ da _Yaro_ zasu samu farin ciki duk da cewa zuciyarsa na gareni amma ni inaji ajikina da yardan Allah zai manta da zancen soyayyata ya rungumi matarsa.
Tunda akayi baikon su kullun _Ummulu_ cikin tunani da murmushi take ita kadai, ni abin ma dariya yake bani ita kuma _Asiya_ sai _Alhaji me gwanjo_ yazo take fara’a mara karewa amma da zaran ya tafi shikenan zata shiga kunci saboda har cikin ranta bata son shi amma aikin da akayi a kanta shine yake aiki, A nawa 6angaren kuma ina ta samun masoya amma sam soyayya baya raina ni burina biyu ne a yanzu tabbatuwar auren _Ummulu_ da kuma fatan Allah ya dawo min da tunanina dan nima in samu in koma cikin dangina.