DEEMAH CHAPTER 16 BY ZAHRATEEY
Www.bankinhausanovels.com.ng
_Mamitaaa_!!! “Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ya hayyu ya qayyum” kallon hagu da dama nayi inaso in gano inda nake, yar budurwan dake kusa dani na kalla ina mamakin wai duk wannan ihun da nayi bataji ba? Kaina na rike ina son tuno da yadda akayi na tsinci kaina a wannan gidan dan ban ga alamun fuskar wacce na sani a tare da yarinyar ba, d’akin na bi da kallo ko ina tsaf tsaf ne babu wani tarkace da yawa, zama nayi ina kallonta can kuma na tashi na fita daga d’akin. Ko ina shuru babu motsin mutane sai kukan karnuka da kuma tsuntsaye jefi jefi, zama nayi a wani dakali “mun baro gida nida kawunai na, mun shiga mota nayi barci na farka naga wasu maza biyu a zagaye dani mun fito na fahimci cewa 6arayi ne, sun sanya tsofi a mota dan amayar dasu _Bauchi_ mu kuma suka tafi damu daganan kuma na manta duk wani abin da ya faru ” wayyo Allah na ni kam na shiga uku daga wannan bala’in sai wancan, nan kuma ina ne a ina nake ya ilahi?” Rike kaina nayi saboda ciwon da yakemin, so nake sai na tuno da abubuwan da suka faru bayan mun bar garin _Abuja_ amma na kasa tuna komai, tashi nayi na koma d’akin na kwanta daker barci ya yi awun gaba dani.
Washe gari da safe na tashi da wani irin ciwon kai sai da aka dangana da asibiti inda sukayi min alluran barci na kwanaki uku wai saboda in samu saukin tunanin daya addabi kwakwalwata. Bayan kwanaki uku na farka, a hankali nake bude ido na da sukayi min nauyi, sosai naji dadin kan nawa dan ya rage min ciwo, wannan yarinyar na gani wacce muka kwana a daki daya duk hankalinta a tashe, tana juyowa muka had’a ido “Alhamdulillah _Anty_ kin tashi, wallahi har kin ban tsoro! wannan wani irin ciwo ne ya kamaki a dare d’aya, Amma dai yanzu kinji sauki ko? Bari inje in kira likita yazo ya dubaki” bata jira nace komai ba ta fita cike da zumud’i, ni duk mamaki ya kasheni a ina na zama _Antynta_? Ikon Allah kenan, murmushi nayi tunowa da yar uwata _Mamita_ lailai ina matukar son yar uwata tunda da ita na farka a raina kuma sunanta na fara ambata, itama _Anty_ take cemin kuma ita kad’ai ke kirana da _Anty_ ba tare data had’a da sunana ba sai kuma wannan baiwar Allahn da nagani.
Ina kwance suka dawo tare da likita, dubani ya yi tare da yimin tambayoyi ina amsa mishi, sai da ya gama sannan yace ta biyo shi office din shi, bayan kamar mintina goma ta dawo rike da wani fallen takarda guda biyu, “d’aya na sallama be d’aya na magungunan da za’a saya, ki jirani bari inje in sayo sai in taro mana me adaidaita” har na fara gyangyad’i naji bude kofa, da ita nayi tozali ta shigo rike da ledan magungunan, had’a mana kayan dake gurin tayi sannan ta taimakamin na sauka daga gadon dan har yanzu ina jin jiri, a hankali muke takawa har zuwa in da me adaidaitan yake, sai da na fara shiga kafin ta ajiye kayan ta can baya sannan ta shiga ita ma, _Anguwar Basa_ tace mishi, munyi tafiya me nisa kafin muka isa gidan bayan mun sauka ta ba shi kudinshi sannan muka shiga gida. A bakin famfo muka taras da wata mata tana zaune “sannunku da zuwa, wai yanzu nake son in gama kwashe abincin sai muje nida _Asiya_ mu duba jikin nata, sannu _Asma’u_ ya karfin jikin naki yanzu? Allah ya baki lafiya” ta fad’a tana gyara d’aurin zaninta ” _Ummulu_ maza kai mata ruwan dumi ta d’an watsa ni zan shiga gidan _Saude_ d’iyarta ta haihu d’an ba rai” da to kawai yarinyar ta bita sannan ta shiga kitchen ta d’auko bokiti ta juye ruwan ni kuma na shiga d’akin da muka kwana randa na dawo cikin tunani na, na lura na manta komai ne a baya yanzu kuma na tuna amma kuma na manta abubuwan da suka faru a rayuwar da nayi a wannan gidan da nake, bayan na cire kaya na d’auro zani da hijabi sannan na fito na shiga band’akin tare da yiwa _Ummulu_ godiya.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan na fito na saka kayan dana gani a saman katifan sannan na zauna ina tunanin rayuwa ” _Anty_ kici abincin ki sha magani kuma kinga _Likita_ yace ki rage yawan damuwa dan shine yasa miki ciwon kai me tsanani har fa jininki sai da ya hau” banyi musu ba na bude abincin _Shinkafa_ da _Wake_ da _Mai_ da _Yaji_ ne yasa _Salad_ da _Tumatir_. Sosai naci abincin dan _Yajin_ yamin dadi sosai, ina gamawa ta bani magani na sha sannan ta fita da kwanon. Bata dad’e ba ta dawo ta zauna kusa dani tana cewa ” _Anty_ ansa bikin mu da _Ya Yaro_ sati biyu idan na gama jarabawa, bikin _Asiya_ kuma a dakatar sai ta haihu za’ayi” kallonta nayi zanyi magana sai ga wata tsohuwa tsohuwa ta shigo “ke ina kika ajiyemin abinci na? Ai kin iya gayyar sod’i gayyar na ayya kin kawo mata nata amma ni me juna biyu kin barni da yunwa ko _Ummulu_ ya yi kyau ” tana gama fad’a ta juya ta wuce kamar zata tashi sama, _Ummulu_ ta mara mata baya ni kuma na kwanta dan naji kaina ya fara ciwo kad’an kad’an.
Ban tashi ba sai bayan magriba, ban damu ba saboda ina fashin salla, wanka na sakeyi na saka kaya sannan na fita waje inda suke zaune, ina zama wani mutumi ya shigo rike da leda a hannun sa, na gane shi dan tare dashi aka kaini asibiti, yaron dake biye dashi a baya ne ban gane ba, bayan ya zauna ya tambayi lafiyata na amsa mishi sannan nace “kuyi hakuri dan Allah amma ni duk ban gane ku ba” zaro ido _Ummulu_ tayi duk jikinta ya yi sanyi tace “har dani kenan _Anty_ nima kin manta dani?” Ta tambaya kamar zatayi kuka, tausayi ta bani nima banso hakan ba amma yaya zanyi na kasa tuna komai ” _Baba_ tunawan da nake kokarin yin shine yake sani ciwon kai me tsanani shiyasa na hakura kawai amma zanso inji yadda akayi nazo nan kuma kafin nan nima zan sanar daku koni wacece” labarina na basu harda auren dake kaina da kuma yarana dana haifa babu ragi ba k’ari sai da na fad’a musu komai da kuma iya abin da zan iya tunawa shine fita daga garin _Abuja_ da mukayi daganan na manta komai, mamaki ne ya kamasu wai ina da aure harda yara na, sosai sukayi ta al’ajabin irin rayuwar da nayi a baya sannan _Ummulu_ ta fara bani labarin zuwana gidan su da rayuwar da nayi a gidan, har dasu _Alhaji me gwanjo_ da abinci da muke kaiwa _Yaro_ a 6oye duk sai da ta fad’a sai a lokacin _Malam_ ya san cewa ga irin rayuwar da _Yaro_ yakeyi a gidan, sosai nima rayuwar da nayi a gidan su ya bani mamaki da al’ajabi kuma na kasa tuno da komai, ranar hira mukayi sosai kafin mukaci abinci muka kwanta, _Mama_ taji haushin _Ummulu_ data fad’awa _Malam_ abin da takeyi wa _Yaro_ shi kuma _Yaro_ tunanin cewa ashe ni matar aure ce shine ya addabe shi karshe dai ya sawa zuciyarsa salama ya kama yar uwarsa hannun bibbiyu tunda ya ga babu damar samuna.
_________________________
Sosai _Baba K_ ya tsure ya rasa madafa, kallonta kawai yakeyi yana tuna _Lami_ “wallahi uwarki ta cuceni ta cuci rayuwata, ashe da aurenta ta bari mukayi tarayya da juna? Sai bayan da cikin ki ya bayyana shine take sanar dani cewa ai da auren ta amma kuma bazata ta6a zubarwa ba dole ne ta haifeki amma ba a gidan ba” ya fad’a yana share zufa, _Dr Nasir_ ne yace ya rabawa yara abincin sai su tafi shi zai biyashi kudin idan yaso sai su samu guri me sirri suyi magana a can. Ba tare da musu ba ya amince duk jikinsa na rawa ya rabar da abincin kafin suka taya
shi kwashe kayan, bayan sun isa parking space suka saka kayan a booth sannan suka shiga mota suka wuce gidan _Dr Nasir_.
Bayan sun isa gidan suka shiga daga ciki, a falon suka zauna _Baba K_ duk ya rasa meke mishi dadi shikam son kudi ya janyo mishi bala’i ya kai shi ya baro shi, wannan abin kunyan dame ya yi kama ya ilahi “Yarinya me kike nema a gurina? Kin ganni nan bani da ko sisi nema nake kokarin yi domin in rufawa kaina asiri, ki rufa min asiri karki tonamin, ki kama gabanki ki cigaba da zama da uwarki, tabbas mun aikata kuskure dagani har _Lami_ amma ta fini laifi domin da aurenta ta aikata wannan danyen aikin” kallon shi _Hanifa_ takeyi tana mamakin me _Mama_ ta gani ajikin shi da har ya burgeta.
Ruwan da _Dr Nasir_ ya ajiye musu ne ta dauka ta kur6a sannan tace “ai aikin gama ya riga daya gama tunda har aka haifeni, dama burina in san waye mahaifina in kuma san waye ainihin mahaifiyata tunda sun 6oyemin amma tunda yau naji sunan mahaifiya ta a bakin ka shikenan na yarda na kuma fahimci ko wacece mahaifiyata a tsakanin mata biyun, kai kuma tunda na ganka na tabbatar da waye kai din shikenan banda abin da zanyi da kai sai dai idan bukatar hakan ta taso, da ace kana da wani abin tunkaho ne dana zamu gurin zama amma tunda fatara kakeyi babu gurin zama a gidan ka domin ban taso a talauci ba, ba kuma zan zauna a cikin talaucin ba” ajiyar zuciya ya yi da yaji cewa kawai sanin shi take son yi ba wai wani abin ba.
“Ina son sanin wacece _Mamana_ a gurinka, a ina kuka hadu har akayi cikina?” Kallonta ya yi sai zufa yakeyi kamar an sa shi a bakin wuta, alhali fanka da ac duk suna aiki a lokaci guda ” _Lami_ budurwata ce tun kafin inyi auren fari, kaddaran aurenta da mijinta shine ya raba mu, bayan wani lokaci me tsawo muka sake haduwa da ita, nayi mamakin irin daular da take ciki sai dai banyi tunanin tambayarta ba, ganin yanayina yasa ta bani adireshinta tacemin in sameta a gidanta dake kusa da _Jifatu_ banyi musu ba nace mata to zanzo, a lokacin matana hudu cif, kuma matata ta karshe haihuwarta na fari kenan karayar arziki ya sameni, bayan naje gurinta ta bani kud’ad’e masu yawa tace inyi amfani dasu amma sai na biya mata bukata zata dankamin kudaden, son kudi da sharrin shaidan yasa na amince tunda har a lokacin ina sonta kuma babu damar auren ta domin babu wacce zan iya saka a cikin mata na ko wacce tana da yara sannan bana bukatan ace saki ne ya raba sai dai mutuwa dan ba zan so matata ta fita ta auri wani ba, bayan komai ya faru a tsakanin mu ta bani kudin tayi min godiya na tafi, daganan bamu sake haduwa ba sai lokacin da cikin ki ya bayyana a jikinta kuma sanin kanta ne cewa bana mijinta bane, bayan ta fadamin na bata shawaran zubarwa shine tace ba zata zubar ba ni kuma nace babu ruwana karta sake nuna ta sanni ko da a hanya muka had’u, 6acin raina ma da ta fadamin cewa ashe da aurenta mukayi wannan aika aikan, dalilin cikin ki yasa tayi wani tafiyar karya ita da kanwarta zuwa kasar waje a lokacin cikin nata nada wata biyar kasancewarta mace me jiki sai yabi jikin ta babu wanda ya san tana da ciki, bayan zuwan su data haihu shine ta sanar dani cewa ta haihu amma baki zo da rai ba, sosai nayi farin ciki domin ni bana fatan haihuwar dan gaba da fatiya kuma ma da matar da take da aure a kanta”.
Kallonsa tayi cikin takaici “Ina so ka zama cikin shiri domin a ko da yaushe zan iya nemanka, sanin kan ka ne nasan gidan ka na kuma san gurin sana’arka, aurena zai iya zuwa cikin lokaci k’ank’ani dan haka ka zama cikin shiri dan akwai abin da nake shiryawa. Sannan kuma zan baka numbern _Mama_ ina son ka neme ta a waya ka tambayeta ajiyarka dake gurinta, kar kace min a’a domin idan ka fad’a kune a ruwa dan asirinku ne zai tonu, ni abin kunya gaba na bashi ba baya ba dan haka ko a k’olar rigata, ina son ka kirata yau da yamma gurin karfe biyar lokacin ina gida, idan kuma baka kira ba na riga dana fad’a maka abin da zan iya yi, na san dai yan gidanka basu san dani amatsayin yarka ba, idan kana son duk su sani sai ka tsallake magana ta” ta fad’a tare da d’aukan jakarta da mayafinta, jakar ta bud’e ta ciro yan dubu-dubu da wani fefa me d’auke da lambar _Mama_ ta watsa mishi sannan tayi gaba tana cewa _Dr Nasir_ sai sunyi waya.
Bayan tafiyarta ya d’auki kudin yasa a aljuhu tare da fefan sannan yace wa _Dr Nasir_ zai tafi “ka jira in sauke ka saboda nima fita zanyi” bayan ya canjo kaya ya d’auko key din motarsa sannan suka wuce “Kar kayi gigin kin yin abin da tace kayi tunanin ko barazana ne, tabbas ba barazana bane domin _Hanifa_ ta wuce tunaninka zata iya aikata komai, kamar yadda ta fad’a maka abin kunya gaba ta bashi ba baya ba haka abin yake, tsatson ta tun daga farko bame kyau bane, kuma baku kyauta mata ba daga kai har mahaifiyata, nan da kake ganinta ta zubar da ciki babu iyaka, tantiriyar yar duniya ce me fuska biyu, kayi tunanin abin da zata iya aikata maka idan bakayi yadda tace din ba” yana gama fad’a suka iso junction din gidan _Baba K_, anan ya saukeshi tare da ba shi kudin daya mishi alkawarin sannan ya yi tafiyarsa.
ta idan _Mama_ tayi mata wani abin shiyasa suke d’an d’asawa dashi dan haka yanzu ma ta san ba zai ki auren ta ba musanman idan _Jidda_ ce ta nemi wannan alfarman.
< div>