DEEMAH CHAPTER 17 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 17 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Addua kawai aka dukufa yi akan lamarin rayuwan _Khadeemah_ domin duk komai na rayuwarta a juye yake. Kasancewar abubuwa da yawa na sihirin jikinta sun karye sai asiri ya tonu, a cikin hakan aka samu wacce tayi mata magani tun farkon haihuwarta kuma matar ta kasance yar uwar _Inna Abu_. kuma wai tayi mata sihirinne saboda kar tafi d’iyarta haskawa a duniya, a yadda tayi bayani wai a lokacin tana da ciki sai kafin ta haihu taje gurin boka inda ta nemi ya yi mata aiki wanda zai sa a duk cikin zuri’ar su babu wacce zata kama kafar d’iyarta a samun nasara, bayan ya buga ya buga sai ya sanar da ita cewa d’iyarta bata da wannan hasken sai dai akwai wacce take dashi wato yarinyar dake cikin matar d’an yar uwarta, sosai hankalinta ya tashi da jin hakan shine ta bukaci ya yi wani abu a kan hakan ko nawane ita zata bashi, shine yace mata karta damu da an haifi yarinyar zai tura mata aljanu wanda zasu rinka sata tana abubuwa da zasu sa mutane k’ita su kuma tsorata da ita sannan kuma zasu hana ta aure domin aure shine abin da zai karya komai, hakan akayi suka shiga jikinta suna juyata yadda suka ga dama sannan suka hanata aure tare da kashe duk wani manemin ta yadda wasu masu son ta zasu tsorata da lamarinta su hakura da ita, hakan kuwa ya kasance mata sai da Allah ya yi ikon sa a kanta har ta hadu da _Sufyan_ sukayi aure har da zuria a tsakani a lokacinne sihirin dake jikinta ya fara warwarewa domin an lalata aiki.

+

A wannan lokacin boka ya sanar da ita cewan da zaran an bari sihirin jikin nata ya karye to abin zai koma kan d’iyar _Goggo Sahura_ ne kuma haka ta yarda da sharad’in kuma ta sanya ido a kan shige da ficen _Khadeemah_ ta kuma cigaba da lalata mata suna a gidajen manemanta, sai gashi duk iya kokarinta ya tashi  banza, tunda _Sufyan_ ya kusanci _Khadeemah_ d’iyarta suka fara samun matsala da mijinta a halin yanzu dai satinta ya yi har saki biyu kuma yace ba zai maidata ba, ko da taje gurin boka ya sanar da ita cewa akwai yiyuwar komawar d’iyarta amma sai taje gurin iyayen _Khadeeemah_ ta sanar dasu gaskiyar lamari shine abin da zai karya sihirin jikin mijinta har a samu ya mayar da ita d’akinta. Sosai _Inna Abu_ taji bakin ciki a kan abin da yar uwarta tayi mata dan kawai son duniya ta so lalata rayuwar jikarta. Kowa sai da ya yi Allah wadai da wannan mummunar halin nata karshe dai mijin yarinyar ya mayar da ita d’akinta ita kuma _Goggo Sahura_ aka barta da kunya da dana sani.

Bincike sosai aka kara tsaurarawa akan lamarin 6atan _Khadeemah_ sai dai har yanzu babu wani labari me dadi da zai sanya natsuwa a zuciyar mutane. 6angaren su _Ummulu_ sai da _Jidda_ tayi magana da ita tare da nasiha me ratsa jiki sannan ta fuskanci jarabawanta da kyau dan har ta fara karaya bata me da hankali saboda kaunar da takeyi wa _Khadeemah_ domin sunyi zama na fahimtar juna wanda ya dace ace tsakaninta da _Asiya_ ne aka samu irin wannan zamantakewar amma sai ga shi da bare tayi irin wannan zaman. Kullun adduarta shine Allah ya bayyanarda _Antynta_ dan ita yanzu tace a dage aurensu da _Yaro_ sai _Khadeemah_ ta bayyana kafin ayi, sosai _Malam_ da _Mama_ suka jinjinawa girman soyayyarta ga _Khadeemah_.

STORY CONTINUES BELOW

_________________________

A 6angaren su _Malam_ da mukarrabansa bayan sun bar _Bama_ suka koma _Chibok_ anan yasa aka kira mishi abokan harkallarsa suka zo suka za6i na za6a ciki har da d’iyar matar da suka shiga mota daya da _Khadeemah_ sosai matar tayi kuka har ta gode Allah domin a matsayin karuwa aka sayar mata da diyarta, bayan kowa ya kwasa adadin da yake so aka barwa _Malam_ mutane biyar da wasu mata uku da kuma _Khadeemah_ da matarnan wanda har zuwa lokacin tana jinyar zuciyar ta saboda rabata da diyarta da akayi.

Bayan an watse jirgin su ya d’aga zuwa _Abuja_ inda 6oyayyen gidan _Malam_ yake wanda mutane kalilanne daga cikin ma’aikatarsa suka san da gidan, kuma yana tafiya da matanne a matsayin masu taya matarsa aiki alhalin amfanin kansa yakeyi dasu idan matar shi batanan, babban malami ne agarin _Abuja_ me fada aji a cikin yan siyasa amma ba me wa’azi ba, mutum ne wanda a gurin shi yan siyasa maza da mata suke kar6an taimako akan mulki, kuma a gurin shi manyan mata ke kar6an taimako gurin samun kan mazajensu, abin takaici matar aure taje tayi watsewarta da _Malam_ kuma wai duk a cikin aiki ne.

Bayan sun yada zango a _Abuja_ aka gabatar dasu a gurin matar gida a matsayin masu aikin _Malam_ kuma masu aikin ta a yanzu kafin _Malam_ ya sake tafiya wani aikin. A walakance ta kar6e su tare da basu gurin zama kamar yadda aka saba. Kasancewar bata dade da dawowa daga tafiya ba shiyasa har sukayi wata guda babu inda taje tana gida, sosai _Malam_ ya shiga damuwa domin babu damar amfani dasu, ga shi tunda ya kyella ido a kan _Khadeemah_ yaji duk duniya babu abin da yake so kamarta kuma yaji a ransa matukar be samu biyan bukata da ita ba, ba zai ta6a samun kwanciyar hankali ba, shiyasa yake ta Allah Allah matarsa tayi wani tafiyan domin tana shiga hakkinsa a fadarsa, yanzu haka yana jira zuwa wata me zuwa idan batayi tafiya ba shi zai shirya tafiya domin ya samu biyan bukata.

Ita dai _Khadeemah_ babban damuwarta shine yaranta, kullun dasu take kwana take tashi tana tunanin a wani hali suke. yanzu abubuwa da yawa ne a cikin kwakwalwarta, kasadar da zatayi shine guduwa wanda take fatan Allah yasa kar su kamata ko kuma ta samu damar sace waya ko aron waya ta kira gida ta sanar musu inda take, sanin cewa suna _Abuja_ yasa hankalinta kwanciya domin idan guduwa zatayi ma zai zo mata da sauki ta san inda zata nufa. Tunani kala kala takeyi tare da kara nazarin gidan dan ta samu saukin yin abin da tayi niyya. Da yardan Allah ita zata zama silar tonuwar asirin _Malam_ wannan shine fatan ta a kullun kuma burinta.

_________________________

Bayan watanni uku

Suna zaune a garden din gidan dukansu, yaran suna wasa ta d’aya 6angaren. ” _Anty Jidda_ ciki ne dake ko?” kallon _Bibalon_ tayi sannan ta kalli _Sufyan_ daya zuba nata ido yana jira yaji ko zata sake musawa “ai mijin naki ne sai a hankali ni sai da nace na bar muku ni hutu nake bukata amma yaki ji” dariya ta sasu saboda yadda tayi maganar da hakikanin gaskiyarta “in banda ke _Anty Jidda_ ai y’ay’a rahama ne mu kam muna maraba dasu ko _Abby_?” yace “kwarai ma kuwa tunda muna da halin tarbiyantar dasu da kuma ciyarwa da tufatarwa, dama ai na dade da sanin cewa ciki ne da ita amma sai wani wainani takeyi kamar waina” hararansa tayi ta d’auke kai ta cigaba da cin gyadarta.

Su kuma suka cigaba da hiransu, _Hanifa_ ce ta doso inda suke tana wani karairaya, nan da nan _Bibalo_ ta 6ata rai, ita kam Allah ya gani ta tsani yarinyar sam-sam jininsu bai zo daya ba ko kadan, hararanta tayi sannan ta dauki _Amir_ tace bari taje ta daura girki saboda ranar girkinta ne, _Jidda_ kam har ta fara barci a saman kujeran. Zama tayi suka gaisa da _Sufyan_ kafin tace lafiya kuwa _Jidda_ take barci ya warhaka, sarkin zumudi da be san dawar garin ba yace ai cikin jikinta ne yake sata barci sosai kwanakin nan,
wani irin bugawa kirjin _Hanifa_ ya yi nan take annurin fuskarta ya dauke gaba daya ta rasa natsuwarta, sa’anta daya hankalin shi baya kanta hakan yasa tayi karfin halin cewa “Allah ya raba lafiya” sannan ta tafi.

Daker _Hanifa_ ta iya kai kanta 6angarensu, tana zuwa cikin falo ta fadi a gurin ta hau kuka kamar ance mata _Mama_ ta mutu. Cike da tashin hankali su _Mama_ suka nufo ta suka cinci6eta daga kasan tiles din suka mayar da ita saman rug. “Ke lafiyarki kalau kuwa? Meke faruwa ne haka?” _Anty Mansura_ ta tambaya “wallahi ku san yadda zakuyi da cikin jikin _Jidda_ idan ba haka ba mutuwa zanyi” ta fada tana kara sautin kukanta, wani irin dokawa kirjinsu ya yi, meke nan _Jidda_ da wani cikin “ke me kike fada ne haka wacece tayi cikin ko kuma ince wata _Jidda_ kike nufi wai ma tukunna”  _Mama_ ta fada tana zama dabas a kasa tana so ace mata ba gaskiya bane “shi kam wannan yaro akwai dan banza, wani irin haihuwa matansa suke yi kamar awakai, kuma ke waya fada miki ciki gareta? Ta ya akayi kika san tana da cikin ma ke har wani abu kika sani game da ciki?” _Anty Mansura_ ta fada tana fifita da dankwalinta wani irin harara _Hanifa_ tayi mata tare da dauke kai, wai har ita za’a yiwa wannan tambayar to karewar ciki ta san maza kala kala bama yadda ake gane cikin kawai ba.

Tashi tayi ta basu guri domin suna kara 6ata mata rai da kalamansu, ita yanzu burinta kawai cikin jikin _Jidda_ ya 6are, ga shi har yanzu zancen aurensu da abin kaunarta ya kasa yiyuwa, da ace anyi da tayi me gaba daya wato kawar da _Jidda_ daga doron kasa da ita da cikin jikinta, sannan sai ta dawo kan wannan karamar mara kunyar wato _Bibalo_ domin tana shiga mata hanci ta lura yarinyar bata da mutunci ita ma, safa da marwa ta hau yi a cikin dakin tana tunanin shin wani hukunci zata dauka a kansu, ita dai ta san bata isa ta tunkari _Sufyan_ da zance soyayya ba a halin yanzu domin zancen 6atan matarsa shine a ransa, kuma ko da ace taje tayi wa _Hajja_ magana ba zai yiyu ayi wani shagali ba saboda damuwar da ake ciki sai dai ko ayi daurin aure babu wani shagali, ita kuma ba zai yiyu tayi biki kamar bikin binne gawa ba, biki zatayi gangariya, na nunawa duniya kuma na kece raini, dole tayi wani abu da sauri domin ta samu biyan bukata nan kusa.

Su _Mama_ kuma zancen cikin _Jidda_ shi yafi komai tsaya musu a rai, haka suka dinga saka da warwara suna tunanin mafita guda daya da zasu bi domin samun natsuwa a cikin ransu, ga aikin _K³_ da aka ce musu ba zai yiyu ba saboda akwai kariya a jikin shi, ga kuma auren _Hanifa_ da suke so ayi da _Sufyan_ dan biyan bukatarsu, ga cikin _Jidda_ daya kunno kai, ga zancen _Khadeemah_ da boka yace aikin yaki yiyuwa a kanta itama kuma ta kusa bayyana nan da kankanin lokaci, su kam duk abubuwa da yawa sun shige musu gaba kuma duk ayyukan su na neman lalacewa yanzu tunanin su ma shine canja boka kila za’a dace idan sukayi hakan.Suna zaune a bakin famfo sunayi wa matar gida wanki, sukaji karan jiniyar yan sanda, kafin wani lokaci motocin jami’an tsaro ya cika ko ina a gida an zagaye babu hanyar tserewa. Cikin sauri suka koma can 6angaren su na masu aiki cike da farin cikin yau ranar ku6utar su ne ya yi, ko wacce ta fara had’a kayanta cike da jin dadi suna cewa gaskiya tunanin _Khadeemah_ ya taimake su. Matar nan da aka d’aukesu tare ne tace “d’iyata ya naga ke kinyi shuru baki fara hada naki kayan ba?” Sai a lokacin ta dawo hayyacinta, ta murmusa kawai sannan ta fara hada nata, abin da ya sata a comma shine ganin wani a cikin motar kamar _Sufyan_ dinta, har Allah Allah takeyi su fita ta sake dubawa ko shine da gaske.

+

Bayan sun gama hadawa suka fito kowa da jakarta a rataye. Mamaki sosai jami’an tsaron sukayi ganin su dayawa dan a kalla zasu kai su talatin, jerin sauran maza masu aikin suka shiga suka tsatsaya, ana cikin haka aka taso kyeyar matar _Malam_ aka sakata a mota can sai ga _Malam_ shima an taso kyeyarsa sai 6oye fuska yakeyi dan yan jaridar da sukayi mishi caaa a kai, wasu daga cikin matan aka kira domin suyi bayanin abin da suke yi a gidan, a nan wasu sukace su din ma’aikatan gidanne da gaske ya yin da wasu kuma sato su akayi kamar dai yadda aka sato su _Khadeemah_, sannan shekaru bibbiyu suke yi a gidan kafin a sayar dasu a wasu mutane na daban a kuma sake sato wasu irin su, wadanda suke cikin shekarun su na biyu a gidan sune suke wannan bayanin.

Bayan an gama dauka ake sake tambayarsu yadda akayi suka samu daman samun wayan da suka sanar da halin da suke ciki.har kuma aka kawo musu dauki tunda a bayaninsu since baa basu waya kuma basu da damar amfani da ita. A nan suke cewa ai shawaran _Khadeemah_ ne akan su samu su sace wayan daya daga cikin amintattun ma’aikatan gidan, bayan sun samu shine ita tayi amfani dashi tayi kira har aka samu samar sanin inda suke, kuma cikin ikon Allah har suka sace wayar sukayi amfani dashi suka matar babu wanda ya sani domin cikin takatsantsan sukayi komai ba tare da barin wani shaida da zai sa a zarge su ba.

Tambayoyi da dama aka musu suna bada amso shi masu gamsarwa wanda da shi za’ayi amfani gurin gurfanar da _Malam_ a kotu. Ko wacce a cikin matan aka hadata da jami’an tsaro biyu zuwa garinsu tare da kudi masu tsoka, ita kuma _Khadeemah_ motar yan sanda aka sakata wanda hakan ya tsinka mata zuciya duk tunaninta wani abin ne zai sake samunta. Shi kuma _Malam_ ofishin yan sanda aka wuce da shi inda aka fara gana mishi azaba bayan yaki bude baki ya yi bayanin inda abokan huldarsa suke, sai da yaji jiki sosai ganin dai zasu kashe shi a banza sannan ya sanar musu da sunayen sauran abokan huldarsa da kuma inda za’a samesu.

Cikin kankanin lokaci aka bazama nemansu bisa ga bayanan _Malam_ kuma cikin ikon Allah duk a cafkesu sannan aka kwashi matan da suke tare dasu ko wacce aka hadata da yan sanda kamar yadda akayiwa na gidan _Malam_. Cikin yaran harda diyar matan nan abin bakin ciki har da ciki a jikinta, sosai mahaifiyarta tayi kuka harta gode Allah, abin dai gwanin ban tausayi ko wacce aka sadata da ahalinta sannan aka tasa kyeyar abokan harkallan _Malam_ zuwa _Abuja_ inda za’a aika su kotu washe gari tare da shaidu masu karfi wanda zasu sa a musu hukunci me tsanani.

STORY CONTINUES BELOW

A 6angaren _Khadeemah_ airport suka wuce da ita, inda _Sufyan_ yake jiranta ashe dazun da gaske shi ta gani sai dai kafin ta sake ganin shi ya tafi yi musu bookings flight zuwa _Bauchi_, shuru tayi a motar tana tunanin me kuma zai sake faruwa da ita a cikin kundin kaddararta. Suna zuwa filin jirgin sukace mata ta fito, cikin sanyin jiki ta fito tana binsu a baya kamar wanda kwai ya fashewa a ciki, ganin sun tsaya yasa itama ta tsaya, jin shurun ya yi yawa su ba magana ba su ba tafiya ba yasa ta daga idan ta a hankali karaf sai a cikin na _Sufyan_ sake bude ido tayi da kyau da ga dai shi dinne, rufe idon tayi ta juya ta kalli wani gefe daban sai ta ga ba kowa sai ta juyo inda ta ganshi dazu still shi dinne, marin kanta tayi ta sake kallon inda yake ta ga bafa gizo bane abin, murmushi ya yi mata tare da bude hannayensa a lamun tazo, ganin dai da gaske yake yasa ta fara takawa a hankali duk jikinta rawa yakeyi kamar tayiwa sarki karya, tana isa gaban shi ta fada jikin shi tare da sakin wani irin kuka me ta6a zuciya, kukan dadi kukan abin yazo mata a bazata kukan wahalhalun data sha, sosai kukan nata yake ta6a mishi zuciya rintse ido ya yi yana so yace ta bar kukan haka amma ya kasa itama taki ta bar kukan, ” _Deemah_” ya fada a hankali “kiyi hakuri kinji, kukan ya isa haka kar kanki ya yi ciwo” a hankali ta fara rage sautin kukan ta koma ajiyar zuciya.

Godiya ya yiwa jami’an tsaron wanda suke kallon su cike da sha’awa sannan ya kar6i jakanta suka wuce. Bayan sun shiga jirgin ya dauko iPad dinsa ya bude mata hotunan yaranta daya musu vedio suna wasa ya bata, kar6a tayi tana kallo tana murmushi tare da hawayen farin ciki, sosai ta bashi tausayi hakan yasa ya yi ta mata hiran yaran da irin wayon da suke dashi, kasa hakuri tayi ta tambayeshi abubuwan da su
ka faru bayan batanan wato yadda akayi ya hadu da yaran, labarin rayuwarsa ya fara bata har zuwa haduwar su da kuma rabuwarsu da ita har aurensa da _Bibalo_, babu abin da ta rage ko ya kara komai sai da ya sanar da ita dalla dalla har kar6an yaran da _Jidda_ tayi. Kirjinta ne ya dinga bugawa tunda taji wai bayan _Jidda_ da ita har wani auren ya kara, sai dai jarumtar _Jidda_ shi yafi komai birgeta har take jin itama zata iya kwatantawa zatayi kokarin 6oye abin da yake ranta itama ta samawa mijinta farin ciki, ba zata so ace duk cikin su itace ta zama mishi matsala ba, tunda daga _Jiddan_ har _Bibalon_ a yadda taji labarinsu mutanen kirki ne kuma k’asaitattun mata da suka san abin da sukeyi. Kwanciya tayi a jikin shi bayan ta gama kallon hotunan har barci ya kwasheta.

Har suka isa tana barci, tashinta ya yi lokacin har mutane sun fara sauka, a motarsa daya bari suka tafi, gidan _Anty Aisha_ ya fara zuwa da ita, sai da tayi wanka taci abinci sannan suka wuce gidan su _Khadeemah_ tare. Ko da suka isa gidan shuru suka samu anguwar duk an tafi masallaci saboda yau juma’a, _Anty Aisha_ ce a gaba sai _Sufyan_ da _Khadeemah_ a baya, matan gidan duk suna zaune a tsakar gida suna hira jefi-jefi, sallamar _Anty Aisha_ yasa suka maida hankali kanta tare da amsa sallamar _Inna Suwaiba_ ce ta fara ganin _Khadeemah_ cikin sauri ta tashi har zaninta na neman kuncewa da gudu itama _Khadeemah_ ta isa gurinta ta rumgumeta, kuka suka fashe da shi a tare gwanin ban tausayi, duk matan gidan sai da sukayi kuka har _Anty Aisha_. Daya bayan daya _Khadeemah_ ta rungume su, sai da kukan nasu ya lafa sannan ta shiga basu labarin komai tun daga tafiyar da suka yi da kawunanta har zuwa yanzu da aka sameta. Sosai abin ya sake komawa sabo a gurin su sai da _Sufyan_ yasa baki gurin rarrashin su sannan sukayi shuru. Basu wani dade ba suka musu sallama suka tafi bayan ya mata alkawarin dawowa washe gari tare da bata wayarsa daya.

Ko da ya koma gida gurin _Daddy_ ya fara zuwa in da ya samu duka uncles dinsa a gurin, nan ya sanar musu da komai tun daga kiran da _Khadeemah_ tayi wa _Anty Aisha_ har ita kuma _Anty Aisha_ ta kira shi ta fada mishi abin da ake ciki shi kuma ya samu jami’an tsaro ba tare da jinkiri ba sukayi amfani da bin diddigin layin data kira dashi har suka samu gida, sosai su _Daddy_ sukayi ta mamakin abin tare da tsinewa _Malam_ da ahalinshi. Daganan ya musu sallama ya shiga gurin _Hajja_ itama ya mata bayani kamar yadda ya yi wasu _Daddy_.

A falo ya same su dukan su _Jidda_ na shan kunu suna hira da _Bibalo_ gaisheshi sukayi tare da tambayar ko an dace, a nan suma ya basu labari _Jidda_ uwar tausayi nan da nan ta fara kuka itama _Bibalo_ har da kwallarta, bayan sun gama jimamin _Jidda_ take tambayarsa ko sai yaushe zata dawo cikin su, yace shima bai sani ba tukunna amma dai a kalla zai bari ta huta cikin yan uwanta tukunna kafin ta dawo din. Yau a 6angaren _Bibalo_ yake shiyasa sai da ya biyo gurin _Jidda_ kafin ya wuce, a falo ya zauna ya kira _Khadeemah_ dan jin lafiyarta sannan ya mata sallama ya haura sama inda d’akin _Bibalo_ yake.

A 6angaren _Khadeemah_ kuwa gidan cike yake da jama’a duk yan uwanta sun zo harda _Kisma_ data kasa hakuri sai da ta biyo jirgi ita da mijinta suka zo, dangi ko ta ina sun cika gidan gwanin ban sha’awa, masu murnan dawowarta nayi masu bakin ciki nayi. _Sufyan_ shima yazo kamar yadda ya mata alkawari, sosai taji dadin ganin shi musanman da yazo tare da yaranta har da yaransu _Jidda_, duk ganin komai takeyi tamkar a mafarki wai yau ga _Sufyan_ dinta da yaranta duk a tare da ita kuma da alama shima ya amince da kasancewarta matarsa, sosai hakan ya sanyata farin ciki. Bayan tafiyarsa su _Jidda_ suma suka zo tare da _Anty Aisha_, ganin yanayin zamansu da _Bibalo_ sai abin ya bata sha’awa kamar ba kishiyoyi ba sun hade kai suna zaman lafiya, itama taji tana Allah Allah ta shiga cikinsu. Basu suka wuce ba sai yamma amma sun bar mata yaran duka dan duk sun ce ba zasu koma ba sai tare da _Triple_ hakan da _Khadeemah_ ta gani ya sake tabbatar mata da ana kyakyawar zama ne da alaka me kyau a gidan _Sufyan_. Da dare ma sai da ya dawo ya duba su da ita da yaransa, kuma bai zo hannu babu ba sai da ya sayo musu kayan ciye ciye kala kala. A nan yake tambayarta ko sai yaushe take son tarewa, tace mishi idan ta cika sati biyu a gida in sha Allahu sai ta tare. Bayan ya koma gida ya sanar dasu _Bibalo_ yadda akayi suma kuma sunji dadin hakan kafinnan sun gama gyara mata 6angarenta kamar yadda sukayi shawara dazu.

Cikin sati guda da nayi a gida kullun sai _Sufyan_ yazo kuma sai ya kawo min yaran, sosai naji dadin yadda yake bani kulawa wanda ada banyi tsammanin samun irin hakan ba. Yan uwa da abokan arziki duk sunzo taya su _Mama Qudi_ murnan dawowa ta, ni yanzu damuwa daya ne a raina yadda naga _Baba K_ kamar yana cikin matsala, dan kullun sai ka ganshi ya zauna shuru shi kadai ya zuba tagumi, ko da na tambaye shi meye ne matsalar kawai cewa yakeyi ba komai ni kuma na kasa yarda da zancen ba komai.

A 6angarensu _Jidda_ har sun gama gyara mata 6angarenta saura tarewa ne kawai, inda _Daddy_ ya shirya walima na musanman a ranar da zata tare din kamar dai yadda akayiwa _Bibalo_. Duk wannan bidirin _Sufyan_ bai san anayi ba dan tsayar dashi takeyi a office idan sunje aiki dan kar su dawo da wuri su samu masu aiki basu tafi ba, haka tayi ta mishi har sai da aka gama gyaran sannan ta daina.

Su _Mama_ suna nan bakin ciki ya musu yawa sun rasa mafita domin boka ya margaya jiya da dare dan haka dole suyi gaggawan nemo wani sabon bokan ko kuma duka aikinsu ya lalace. _Hanifa_ har zazza6i ne ya kamata da taji wai an samo matarsa kuma wai har zuwa gurin ta yakeyi kullun a yadda taji _Anty Mansura_ na bawa _Mama_ labari.

A cikin wannan satin zata tare dan haka kamar yadda ya yi wa _Bibalo_ sabbin akwati haka itama ya mata seti biyu masu kyau, sannan ya yi wa _Jidda_ itama na musanman ya aika gidan _Anty Aisha_ yace a kawo mata daga can dan ya san idan shi ya kai mata direct ba zata kar6a ba zata iya 6ata rai ma akan hakan, ko da _Anty Aisha_ ta ga kayan sai da ta kara jinjinawa soyayyarsa ga _Jidda_.

Dawowata kenan daga raka su _Anty Jidda_ wai sun biyo ta hanyar gidan shine suka tsaya sannan tace kar muyi tunanin yin komai domin sun riga da sun gama shiryamin nawa 6angaren, banyi mamaki ba saboda itama _Bibalo_ a labarin da _Sufyan_ ya bani yace _Anty Jidda_ ce tayi komai, godiya nayi musu tare da fatan alkairi. Ina shiga gida _Anty Aisha_ ta kirani tace zasu kawo lefe zuwa anjima nace mata Allah ya kaimu, sannan na fadawa su _Inna Suwaiba_ yadda mukayi dasu _Anty Jidda_ da kuma _Anty Aisha_, fatan alkairi suka mana tare da adduar Allah yasa mu dore a hakan.

An kawo lefe an watse cikin aminci, _Anty Aisha_ da wasu mata uku ne suka kawo, kowa sai son barka yakeyi domin kayan sunyi ba karya komai a wadace aka saka, masu murnan gaskiya nayi masu bakin ciki a zuciya duk sunayi, _Kisma_ harda dan taka rawa saboda farin ciki, mijinta har ya koma akan sai bayan na tare zai zo ya d’auke ta dan taki yarda ta bishi, shima dai da hakuri yake saboda halin _Kisma_ sai a hankali, soyayyiyar kaji, snacks da lemon kwali kala biyar aka had’a musu aka musu packaging me kyau sai godiya sukeyi.

Bayan sun bar gidansu _Khadeemah_ suka wuce gidansu dan kai kayan _Jidda_, yan uwan _Anty Aisha_ ne yaransu _Abba_, gidan shuru kamar ko yaushe yaran suna 6angaren _Bibalo_ saboda _Jidda_ ce da girki kuma yamma ya yi shiyasa suka koma can, tana zaune a kan rug tana cin taliyar hausa da manja taji sallamarsu, bayan ta amsa suka fara shigowa da tsadaddun akwatuna har guda shida, basu bi ta kanta ba suka haura mata dashi dakinta na sama kamar yadda _Anty Aisha_ tace suyi, bayan sun kai sun dawo sai a sannan suka gaisa da ita tare da mata ya jiki, jiki a sanyaye ta amsa tana son tayi magana amma tana shakkar yanayin fuskar _Anty Aisha_ shiyasa taja bakinta tayi shuru “ga kayanki can _Sufyan_ ya kai min gida yace a kawo saboda idan shi zai kawo da kanshi ba
zaki amsa ba, ke dai kawai kiyi godiya ga Allah daya baki mini kamar _Sufyan_ wanda yake matukar kaunarki kuma bai had’a soyayyarki dana kowa ba dan haka kar kice komai Allah ne ya kashe ya baki kuma kyakyawar halinki shine ya kara saya miki mutunci nima kuma na yaba miki sosai, abokiyar zamanku tace akara muku godiya dan har kun gama gyara mata 6angarenta, hakan ya yi kyau Allah ya kauda idon makiya a kanku ya kuma baku zaman lafiya” duk suka ansa da amin suka kara mata nasiha tare da yabawa kokarinta na son zaman lafiya dan kwanciyar hankalin mijinta. 6angaren _Bibalo_ sukaje itama suka mata godiya bisa jajircewan da takeyi dan ganin abin da _Jidda_ ta faro be watse ba, nasiha suka mata itama sannan suka mata sallama suka wuce.

Da dare bayan _Sufyan_ ya dawo cikin sand’a ya shiga 6angarenta, tana kallon shi tana gimtse dariyarta domin ta san saboda akwatin daya sa akawo yake haka, sai da ta bari ya haura sama sannan itama tabi bayan shi a hankali, tana shiga dakin ta kunna wutan, da sauri ya juyo yana raba idanu “6oye 6oyen me kakeyi kai da gidanka?” Kallon akwatunan tayi sabbin fitowa ne ma, design din sunyi kyau sosai kuma be cika ado ba hakan yasa ya kara haskawa “akwatunan sunyi kyau na gode Allah ya kara budi” ajiyar zuciya ya yi ita kuma ta fashe da dariya “ni yau naga matsoraci ai sai kasa ace maka mijin _Hajiya_, kai da kawai zaka bada umurni kace ga shi a dauka kuma ayi amfani dashi shine kake wani kwana kwana har sai da kasa _Anty Aisha_ ta baro gidanta tazo kawo akwati?” Dariya shima ya yi sannan yace “ni da na san halinki kamar yunwan cikina ai dole in biyo miki ta bayan gida, Allah dai ya taimaka banji naushi ba” sukayi dariya a tare sannan ya bude mata akwatin yana fitowa da kayan ita kuma tana yabawa.

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya, a yau zan tare a gidan masoyina kuma mijina uban y’ay’ana, tun safe gidan mu yake a cike kamar sabon biki za’ayi, _Ummulu_ da _Mama_ ma sunzo dan kasa hakuri tayi wai sai tazo ta ga ko da gaske ne na dawo din. Karfe uku motocin da zasu kaimu suka iso, kuma kowa sai da ya samu shiga saboda waliman da za’ayi. Ko da muka isa park din mun samu a cike da mutane, a babban hall din da za’ayi waliman mukayi parking sannan aka budemin mota na sauka. Babu wani 6ata lokaci aka gabatar dani sannan malamar ta fara wa’azi da babban murya inda take jan hankalin mata masu abokan zama da suyi koyi da kyakyawan halayyar matan fiyayyen halitta da sauran mata magabata, sannan tayi kwatance da _Jidda_ a matsayin abar koyi, nasiha tayi me ratsa jiki da zuciya sannan tayi mana adduar fatan alkairi, bayan anci an sha aka watse cikin aminci, nida _Jidda_ da _Bibalo_ muka shiga mota daya.

Masu gulma sunzo kallon gida kuma masha Allah sai dai kushewar me hassada, bayan an watse _Sufyan_ da abokan shi suka zo inda suma suka tofa nasu albarkacin bakin, nasiha da jan hankali dai yau munshata, daganan suka mana adduar fatan alkairi suka tafi, bayan tafiyarsu _Sufyan_ ya dawo ya fara dayiwa Allah godiya daya azurta shi da mata kamarmu, sannan ya mana nashi nasihar tare dayiwa su _Anty Jidda_ godiya bisa kokarin da sukayi dan sai a cikin satin bikin ya san cewa sun gyaramin nawa 6angaren a lokacin yana shirin kirawo masu gyara. Bayan ya gama _Anty Jidda_ tace ta bamu sati guda itama _Bibalo_ tace ta kara mana ya zama sati biyu kenan, godiya ya yi musu tare da sanya musu albarka, ni kam na rasa ma wani irin mutane masu kyakyawan zuciya Allah ya hadani dasu, tabbas mahakurci mawadaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *