DEEMAH CHAPTER 5 BY ZAHRATEEY
Sosai yan gidan mu suka shiga tashin hankali ba dare ba rana suna aikin nema na, har report suka kai a police station amma babu wani ci gaba da aka samu, _Baba K_ kuma har zuwa yanzu babu abin da yace musu, ko da ya bani labarin halin da suke ciki sosai na shiga damuwa amma kuma naji dadi da suka nuja damuwarsu a kaina, ashe dai suna sona sosai kuma sun damu dani, babban abin farin cikin shine yau zasu gan ni zuciyarsu ya samu sukuni nima nawa ya samu tare kuma da kyakyawar labari wanda na san zai sanyaya zukatansu.
+
Muna isa garin _Bauchi_ naji wani irin natsuwa da kwanciyar hankali a tare dani, duk da cewa akwai wani yar damuwa dake makale da zuciya ta, “ina zan ganshi?” Nayi wa kai na tambayar da bani da amsa, saurin goge ruwan hawayen daya zubomin nayi sannan na mayar da kaina jikin window har muka isa tasha, bayan mun sauka na biya mana kudin motar sannan muka tari napep zuwa gida.
Anguwar shuru kamar ko yaushe ba kamar wanda muka bari ba a da, dan wancan anguwar cike yake da yan sa ido da yan zaman kashe wando, sa6anin wannan da zai yi wahala kagansu a waje sun buga taro kamar gurin zaman makoki. mikawa me napep din kudinsa nayi sannan muka taka zuwa kofar gida, _Baba K_ ne ya fara shiga sannan nabi shi a baya, suna zazzaune a tsakar gidan wasu sun zabga tagumi wasu kuma suna d’an hira jefi jefi, ” _Yaya Khadeemah_!” _Kisma_ ta fad’a daga bakin kofar falon kayan abinci data dauko suka zube a gurin baki daya, sake da baki kowa yake kallon mu, ita kuma ta rugo da gudu ta rungume ni tana kuka.
Kasa daurewa nayi nima na fashe da kuka, bama mu kadai ba kanne na da yayyina mata duk sai da sukayi kukan farin ciki, sai da komai ya lafa sannan _Baba K_ ya sanar dasu duk abin da ya faru, a lokacin ne har mazan sai da sukayi kwallar tausayina, basu ta6a tunanin zan aikata hakan ba, nan fa kowa ya shiga tarairaya ta da nuna min kauna, mutane sai zuwa sukeyi taya yan gidan mu murna, yan uwa da abokan arziki duk sun zo, wadanda suka san kan maganar su aka sanar da dalilin 6atan nawa, wanda kuma basu sani ba aka barsu da cewa yan garkuwa da mutane ne suka sace ni, dayawa sunyi farin cikin dawowa ta, yayin da wasu suke bakin cikin dawowar tawa har suka kasa 6oyewa, _Inna Abu_ ko da taji na dawo bata zo ba sai bayan kusan wata guda sannan ta shigo mana.
Ina zaune a kujeran roba a tsakar gida na gama yiwa _Kisma_ kitso kenan zan tashi naji wani irin jiri kaman zan kife a k’asa, da sauri na koma na zauna ina rike kaina, a yan kwana kinnan idan nayi zama sosai ko nayi tafiya me nisa ko aiki me yawa sai in farajin jiri yana d’iba na, ga kuma yawan barci da yake damuna ko da a wajen aiki ne kawai dai dauriya nakeyi na rasa menene matsalar tawa.
Sallamar _Inna Abu_ ne yasa na d’aga kai na kalli k’ofar zauren, tana shigowa taja tsaki a lokacin matan gidan mu duk suka fito “an dawo daga yawon ta zubar din kenan? Sai dai ki raina wa iyayenki amma banda ni _Zainabu_ kin tafi yawon gantali za’a fake da kinje kawo karshen mugaye! Har me zaki iya da zaki tunkare su? Naji wannan, shi kuma haske da cikan da naga kinayi menene ya faru ko kin chanja mai ne ko kuma anyi miki 6arin madara a inda kika je din? Ai dama ba zaki samu amsar bani ba, yar iska, yar gaba da fatiya kede anyi asaran haihuwa anan” wani irin zuciya ne ya ciyoni nayi kan _Inna Abu_ ban sani ba ko me ya faru amma dai ganina nayi a d’akin asibiti an jona min alluran drip, _Inna Abu_ kuma a d’aya gadon ta sha bandeji a fuska irin goggoron _Baba K_ na rannan, duk jikinta ya kunkunbura ta ko ina, ga kafarta d’aya da hannu duk a d’aure alamun karaya, kenan duka na mata na musanman? Lailai nayi aika-aika.
Satin mu guda a cikin asibitin ana kulawa da mu, abu d’aya ne ya d’auremin kai, yadda naga wasu nayi min kallon banza, hatta _Mama Qudi_ sai dai ta zo ta duba _Inna Abu_ wacce babu bakin magana sai ido, ni kuma _Inna Suwaiba_ ce kawai da _Kisma_ suke bani kulawa sosai da kuma kannena na gurin uwa, sauran duk sun maidani ba abakin komai ba, ko kallona na lura basa son yi, idan _Inna Suwaiba_ ta tsawatar nema ake min sannu.
A yau aka sallame mu, muna isa gida muka samu duk yan gidan mu a tsakar gida sunyi cirko-cirko, ga kayana a zube a k’asa duk an had’e min a akwati da Ghana must go, da gani dai an san komai nawa aka had’a, kallonsu nayi d’aya bayan d’aya _Inna Abu_ ce kawai bata gurin an shiga da ita cikin gida “ga kayanki nan sai ki nemi gurin zuwa domin ba za’a haifamin d’an gaba da fatiya a cikin gida na ba” _Baba K_ ya fad’a yana muzurai, ni duk bangane me hakan yake nufi ba duk da cewa hausa ya yi min, kawai kunnena ya kasa d’aukar maganar ne, sai da _Mama Qudi_ tace “Allah ya isa tsakanina dake _Khadeemah_ kin cuceni kin cuci zuri’a ta, kin shafa mana bakin fenti, kin tozarta mu, kin yaye mana rigar mutunci, yanzu abin da zaki saka min dashi kenan, ki yo ciki a waje, Cikin shege _Khadeemah_? Ashe gaskiyar _Inna Abu_ da take cewa gantali kike zuwa tunda kika ki aure, kije na cireki a cikin yarana ki nemi wata uwar” tana gama fad’a tayi gaba kamar zata tashi sama dan bacin rai, kallon kowa na cigaba dayi, wasu namin kallon tsana yayin da wasu kemin kallon tausayi.
Kasa ta6uka komai nayi kawai na sulale a k’asa, ciki wani irin ciki kuma ana zaune kalau, ni sam na manta abin da ya faru tsakanina da wannan bawan Allah na gidan Felicia, gaba daya kaina ya d’aure, zancen _Mama Qudi_ yafi komai warwaremin lissafi, _Baba K_ kuwa tunda ya gama furta nashi kalaman yayi waje kuma ya jaddada musu cewa duk wacce ta barni na zauna a gidan a bakin auren ta, yan uwana kuma duk wanda ya tanka min ya cire shi a cikin y’ay’ansa kuma ba zai yafe mishi ba, sosai kalaman suka girgiza su shiyasa babu wanda yayi gigin ta6ani sai _Kisma_.
Ina zaune a gurin ta shiga d’aki ta had’o kayanta tace min in tashi mu tafi koma ina ne mu bar musu gidan su dafa su cinye, ai batasan duk basu da imani da tausayi ba sai yau, ashe duk basu yarda da kaddara ba, yanzu basa tunanin kila a gurin ceto nasu rayuwar ne nawa ya fada halaka? Kawai zasu yanke hukuncin korata, haka tayi ta masifa ina binta da idanu, karshe bayan ta taro me napep ta kwashe mana kayan mu ta kai ciki sannan tazo ta taimakamin na tashi, muna fita wasu suka fashe da kuka musanman matan da suke da rauni domin tabbas maganar _Kisma_ ya ta6a zukatan su har sunji cewa basu kyauta min ba, kalaman _Baba K_ ne ya lalata komai duk ya tsorata su.
Muna shiga napep sai ga _Inna Suwaiba_ itama da kayanta, ta saka kayan a gefe sannan ta shiga duk da cewa bata san inda zamuje ba, tasha _Kisma_ tace ya kaimu, muna zuwa tace motar _Kano_ babu 6ata lokaci muka samu muka shiga kowa da abin da yake sakawa a ransa, ni sai a lokacin na tuna da waye uban abin da yake cikina, tabbas Felicia ta cuce ni cuta mafi muni, kuma duk ta sanadin kar a cutar da mahaifiyata da mahaifina na yarda amma sai ga shi sune sukayi watsi dani suka juya min baya, anya zan ta6a yafe musu kuwa? Na tambayi kaina ina share hawaye.
Muna isa kano ta sake cewa motar sokoto mu dai kawai da ido muke bin ta babu wanda yace mata
wani abun, kafin mu shiga mota haka nayi ta amai saboda tashin zuciya, na rasa ma inda zansa rayuwa ta, na dade ina yi kafin ya lafa, _Inna Suwaiba_ nata jeromin sannu, sai da na gama ta bani ruwa na wanke baki na sannan _Kisma_ ta rufe gurin da k’asa, mota muka shiga nida _Inna Suwaiba_ ita kuma _Kisma_ ta tsaya ta sayo doya da kwai wanda ta lura tun zuwan mu idona na kai, bayan ta dawo ta bawa _Inna Suwaiba_ leda d’aya da maltina a cikin da tsire sai ta ajiye mana d’aya muka fara ci nida ita, ni duk doyan yafi komai armashi a gurina.
a murmushi tace “abin da yake raina kenan kuma abin da _Alaja_ tace take so kiyi kenan jiya bayan mun fita”.
_Alaja Tahira_ muna ta hiran abubuwan da yaran suka samu, inda _Inna Suwaiba_ tace a sayar da filayen da suka samu a had’a musu da kud’insu a barshi a cikin account din, sosai _Alaja Tahira_ ta amince ta shawaran kuma tace zata yiwa mijinta magana duk yadda yace zata sanar mana. Wayarta ne yayi ringing, yanda naga fuskarta ya sauya daga farin ciki zuwa ak’asinsa yasa nima na damu, har wayar ya tsinke bata d’auka ba, sai da aka kira kusan sau uku sannan ta d’auka ta kuma saka a speaker.