DIJAH QAYA COMPLETE

 DIJAH QAYA COMPLETE

Likita! Likita!! Likita!!!
Wani dattijon Bafulatani ke fadi, sanye yake da Riga da wando "yar Shara light green irin wanda mazan fulani ke sawa  da hulansa malfa wanda akasaka da kaba bakin takalmine kwafta na roba akafanshi yana rataye da Goran ruwansa a wuyansa da sandansa ahanunsa farine shi kal har yana Kore Kore kyakykyawa dashi, kallo daya zaka masa ka fahimci tsananin damuwan da yake ciki

gudu gudu yakaraso jerin dakunan ganin likita yana kokarin kutsa kansa sai dai cincirindon mutanen da ke zaman bin Layin ganin likitan ne yasa shi yin turus awajen yana kalle kalle

Daga dan gefe ya hango wani daki guda daya bai da layin mutane sosai ahanzarce ya nufi dakin baiyi wata wataba ya murda handle din ya shiga, wani matashi ne zaune akan kujera yana sanye da jeans  blue da shirt light pink da lapcoat asamanta da fari kal din glass manne a idonsa matashin dan kimanin shekaru 27 fari ne shi amma ba kalba yana da kyau sosai, Rubutu yakeyi, gefenshi wata nurse ce tana shirya files
agabansa,

yakaraso gabanshi yana fadin
Likita likita "yata zata mutu don ALLAH kataimaka min kazo ka dubata,


Dasauri likitan yadago kai yana kallonshi ganin yanda jikin sa yake barine yasashi yatashi ahanzarce yana kokarin fita daga cikin kujeran zamanshi yace " ina take? Da yatsa ya nuna masa hanyan waje tana can jikin mota Doctor, Don Allah ka taimakeni kar in rasa ta bata ko iya tsayuwa,

Doctorn ya dubi nurse din da take shirya folder yace " sister jeki shigo da ita, cikin girmamawa tace " Ranka ya Dade ba nan ya kamata yakawo taba G O P D zai kaita in suka duba suka ga case din yafi karfinsu sai suturosu nan,  "no problem sister shigo da ita kawai ya fada yana kokarin zama,

ta karasa ta dauki well chair tafita gudu gudu dattijon yake binta har suka isa inda yarinyan  take kwance agalaibaice take batasan inda take ba,

Shi yadagata yasata aciki nurse din ta turo har office din,

nan ya umurcesu dasu kwantar da ita akan gadon da yake office din,
Ya jawo kwalin hand glovs yazari guda biyu yasa ahanunsa sannan ya karaso gadon yafara dubata kusan minti biyar yana dubata sannan yaja jininta yazuba a "yar  kwalba ya mika ma nurse din yace" sister akai aje amana test yanzu mukeson answer tadan rusuna ta karba tafice, ya dauko srinji yaja ruwan Allura yamata yazare glovs din yazuba a dosbin sannan yakarasa wajen fanfo ya wanke hanunsa yagoge sannan yadawo yazauna sai lokacin yadubi dattijon

yace"  bismillah Baba zauna anan yanunamasa wurin zama, yazauna yana ajiyan zuciya, sabon file yadauko ya bude yayi dan Rubuta sannan ya kalleshi,
Baba meye sunan Mara lafiyan? Yace sunanta Dija Bukar, Doctor yayi dan murmushi

yace Baba Dija ba suna bane, kafadamin asalin sunanta,

haka  muke kiranta yaro, Doctor yakara dan murmusawa  Yace Baba na Asalin sunan ai KHADIJA ne, ko?

Eh hakane asalin sunanta khadija Abubakar, "yauwa Baba adinga cikamata sunanta yafi, "hakane dannan  amma tafi gane Dijan yayi murmushi yace" Meyasa metane Baba? Wlh ciwon cikine yake damunta sannan wani lokaci da daddare sai  jikinta yayi zafi kamar wuta kuma tana yawan kukan ciwon kai ga amai komi taci sai tayi amai, yadanyi rubutu sannan yadago ya kalleshi yace "tun yaushe ta fara Baba?,

"kusan wata kenan tana fama, "wata? Likitan ya fada yana zaro ido "haba Baba wata guda tana ciwo anma ba kukaita asibitiba? " mun kaita wani asibiti can gaba da ruganmu sati d'aya suka sallamemu muka koma gida ba sauki shine muka sake komamusu shine suka turo munan,
DOWNLOAD HERE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *