DIYAM CHAPTER 14

DIYAM CHAPTER 14

Ina jinsu suka fita daga gidan, and some parts of me went with them.+ A juya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki na koma sama nayi alwala na gabatar da sallar isha sannan na kai kuka na gurin ubangiji na. Bayan na gama nayi shirin bacci na zauna akan gado ina jujjuya waya ta a hannuna, I wish zan iya sanin halin da Sadauki yake ciki, I can’t even begin to imagine in dai har son da yake yi min ya kai wanda nake ji a raina a game dashi to kuma tabbas da nice zuciyata bugawa zata yi in fadi in mutu. It hurts so much to meet him bayan shekaru da yawa and not be able to talk to him, to ina ga shi kuma da yake kallona a matsayin matar wani? Ina nan zaune naji shigowar Saghir, ya jima a kasa sannan ya hawo sama, nayi tsammanin dakinsa zai wuce kamar kullum amma sai naji ya turo kofar dakina ya shigo da tray a hannunsa ya ajiye akan side table ya zauna a kusa dani yana janyo table din gaban mu. “Sarkin yan tuwo gashi nan na debo miki, ko ba zaki ci ba?” Na zuba a plate ina cewa “Nagode” sai naga ya dauko chokali shima nace “au zakaci ne? Bayan baka cin tuwo?” Yace “albarka ta zan saka miki” murmushi kawai nayi zuciyata tana ayyana min abinda yake ransa. Sai da muka gama ci na kwashe kayan na mayar kasa na taho da ruwa da zuba masa a cup na mika masa ni kuma na zauna ina sha a robar ruwan. Sai dana gama na juya naga ya tsatstsare ni da ido kuma nasan irin wannan kallon but not today, I just can’t. Sai na mike zan bar gurin yasa hannu da yawo dani kan gadon, ya jawo ni jikinsa yana mammatsa min kafadu na amma sai nayi saurin ture hannunsa dan ji nake kamar wanda yake doramin garwashin wuta a jiki, kafin in matsa ya saka hannunsa biyu ya juyo dani ina facing dinsa ya jawo fuskata dai dai tasa yana kokarin hada bakin mu, nayi saurin juyar da kaina nace “Please stop, bana so” amma yaki hakura, na fara ture shi kuma yana jawo ni kamar dai yadda muka saba yi duk sanda yazo da bukatar sa, ganin yafi karfina yasa na fara kuka shabe shabe da hawaye ina rokonsa akan ya kyaleni amma yaki, can kuma sai ya sake ni da karfi ya hankada ni baya ya mike tsaye yana kallona da idonsa da fuskarsa da duk suka yi ja saboda bacin rai yace “nagaji, nagaji, nagaji Diyam nagaji. Yaushe ne wai zaki daina guduna? Yaushe ne zamu mori auren mu ni da ke? Tunda akayi auren nan shekara bakwai Diyam in na zauna zan iya lissafa miki adadin lokutan da kika bari na kusance ki suma kuma babu wanda kika kawo kanki kuma babu wanda kika karbe ni cikin son ranki. Ni fa mutum ne, inada jini da tsoka a jikina ina bukatar kulawar matata amma ke na fahimci da dutse akayi taki halittar. Kullum ina bawa kaina hakuri ina ganin kamar zaki dawo hayyacinki amma kin ki, ni Saghir ni da mata suke rubibi na a waje har kawo min kansu suke yi amma ni ne matata take guduna. Na gaji wallahi. Hakuri na ya kai bango” na sauko daga gadon ina goge hawaye na nace “then let me go, mu daina daukan alhakin juna haka nan, auren nan tun farko da aka yi shi ni da kai bama so, igiyar nan a hannunka take, ka saki igiyar ni da kai mu huta da kunan zuciya” sai ya tsaya yana kallo na yace “haka kika ce? To tsaya kiji, lokacin da akayi auren nan ni kaina banyi niyyar zama dake ba wallahi, after what happened on our first night I thought in na sake ki ban kyauta miki ba, nayi niyyar in rufa miki asiri in cigaba da zama dake a haka ina tunanin with time zaki soni. Amma har yanzu kinki sona, kina ganin kamar ban isa ba ko something like that, ni kuma nasan babu macen da ta isa tace bata sona, in na sake ki Diyam kamar kinyi winning a kaina kin nuna min ban isa ba, which is something I won’t agree to. Kin san me? Nasan maganin ki. Aure zanyi. I will let you watch as a lady wadda bata kaiki komai ba take away your husband ta marar dani dan lelenta nima in mayar da ita yar lelena a gaban ki, maybe wannan shi zai nuna miki worth dina ki dawo cikin sense dinki” na mike na rike rigarsa cikin rarraunar murya nace “Saghir, ni ban hana ka aure ba, ni ba zan ma damu dan kayi aure ba ka auri duk matar da kake so Saghir but please ni ma ka barni in koma gurin wanda nake so” yace “ohh, wai dama har yanzu baki hakura da yaron nan ba, dama a saboda shi ne kike tayi min wannan wulakancin? Yaron da aka ce min babu wanda yasan inda yake watakila ma ya zama dan shaye shaye ko dan fashi amma ke shi kike so when you already have me?” Nace “so guda daya ne Saghir, kuma Sadauki naje yi wa shi” ya warce rigarsa daga hannuna yace “then you will rot here. Ke da Sadauki sai a mafarki” ya juya ya fita ya barni. Na jingina kaina da jikin bango ina jujjuya kan, sai kuma na zame na kwanta a gurin akan dandaryar tiles. Ina ji hadari ya hado aka fara ruwan sama mai karfi, tiles din dana ke kai ya dauki sanyi amma na kasa tashi ballantana in koma gado in lulluba, ji nake jikin nawa bashi da wani amfani dan haka lullube shima bashi da amfani. Anan assuba ta same ni, sai da akayi assalatu sannan na tashi da jan kafa na shiga toilet na dauro alwala na gabatar da sallah ina kara kai kuka na a gurin ubangiji na dan nasan shi kadai ne zai iya yi min magani, nasan yana gani na yana kuma jina kuma nasan bai manta dani ba dan yafi kowa sona.2 STORY CONTINUES BELOW A ranar na tashi da mummunar mura da tari, kuma nasan hakan yana da dangantaka da kwanan da nayi akan tiles. Na shirya Subay’a da kyar, na sha magani na kwanta daga nan kuma sai zazzaɓi ya rufe ni. Daga nan sai ciwo, zazzaɓi ciwon kai mura da tari amma Saghir ko leko inda nake baiyi ba ballantana yaga halin da nake ciki duk kuwa da cewa na tura subay’a ta gaya masa yafi a kirga. A haka nayi ta ciwo na, da kansa yake shirya subay’a ya kaita school kuma ya dauko ta yasiyo musu abinci suci kayansu. Ni kuwa sai naji yunwa tana neman illata ni zan tashi insha tea in koma. Har na kwana biyar a haka. Ranar Thursday na kira Inna na roke ta ta turo min Asma’u tayi min weekend dan ta dan taya ni wasu abubuwan, na gaya mata bani da lafiya ne. Friday sai gasu sunzo har da Inna, wannan shine zuwan inna gidana na uku tunda nayi aure kuma duk duba ni take zuwa yi in bani da lafiya. A kasa muka zauna dan bata taba hawa sama in tazo, tana tayi min mitar yadda duk nabi na kara ramewa tana cewa me yasa banje asibiti ba? Ni kuma sai nayi shiru kawai dan ina ganin fada mata cewa Saghir ba zai kaini ba bashi da amfani tunda nasan ko tayi masa magana ba zai ji ba sai dai kawai ranta ya baci. Sai kuma nayi tunanin ko ingaya mata zancen Sadauki? Sai dai bani da tabbas din yanzu menene ra’ayinta akan Sadaukin bansan yadda zata dauki kasancewar sa a matsayin ogan Saghir ba. Na dai san tana nemansa akan gadon Ummah na gida dan haka dole zan gaya mata amma ba yanzu ba, sai na samu damar magana dashi tukunna first. Asma’u ce ta tashi ta gyara min gidana tsaf, har dasu turaren wuta, sannan ta shiga kitchen tayi mana girki muka hadu muka ci tare harda Subay’a. Sai naji dadi sosai, maybe ciwon nawa harda rashin wanda zanyi wa magana da kuma yunwa. Ana yin la’asar Inna tayi sallah sai ta tashi ta fara shirin tafiya. Na fara mita “Inna daga yin la’asar? Ki bari mana sai kamar karfe biyar haka sai ki tafi” tace “uhm uhm, wannan gari na damina yanzu sai kiji ruwa ya sauko. Bana son mijinki yazo ya same ni a gidan nan” muka yi tayi mata dariya ni da Asma’u dan mu a gurin mu kamar babu komai dan sun hadu, ita kuma al kunya ce irin ta fulani. Ai kuwa kamar ta fada da bakin mala’iku sai ga ruwan sama ya sauko, da yake muma daki babu wanda yasan ma da hadarin sai kawai zubar ruwa mukaji. Inna ta fara salati mu kuma muna dariya “yau kwana ya kama Inna a gidan Adda” inji Asma’u, Inna tace “kwana bai kama ni ba, ai komai dare ruwan nan in ya dauke sai na tafi gida, balle ma ba lallai ne ya kai daren ba”. Wasa wasa ruwa har magrib, har isha yin sa ake kamar da bakin kwarya, Inna ta shiga dakin kasa inda Asma’u ta gyara dan anan take zama duk sanda tazo gidan saboda basu fiya shiri da Saghir ba, anan tayi sallolinta duk muka zauna muna hira ita dai tana ta bacin rai. Nace “Inna ki bari idan Saghir ya dawo sai ya kai ki a mota tunda ba kya son kwana” ta girgiza kai “ni da bana son ma yasan nazo? Bazan shiga motarsa ba. Allah ya tashe mu lafiya sai in tafi da safen”. Na dauki Subay’a muka tafi sama saboda naji dadin jikina sosai, na tafi da niyyar inyi mata wanka nima inyi, Asma’u kuma ta tafi kitchen tana gyara abinda muka bata. A lokacin Saghir ya dawo, yaga motsin Asma’u a kitchen sai ya leka, yana ganin ta yace “ke! Yaushe kika zo gidan nan?” Ta dan tsorata saboda bata san shigowar sa ba tunda shi dama ba sallama yake yi ba, ta gaishe shi sannan tace “dazu muka zo duba Adda, ni da Inna” yace “ita Addan taki ce tace muku bata da lafiya? ina gwoggon take?” Ta nuna masa daki a ranta tana tunanin yau Inna zata sha kunya in suka hadu da Saghir. Ya tura kofar ya shiga, Inna tayi saurin tashi duk ta diririce saboda ganin sa haka a cikin dakin gashi tana kwance dan ma dai ba kaya ta cire ba, ya tsaya a tsaye yace “gwoggo Amina barka da zuwa, ashe waccan makaryaciyar cewa tayi bata da lafiya?” Inna tace “uhm uhm Saghir ba karya tayi ba, kowa yaga Diyam ai yasan bata da lafiya” ya daga kafada yace “to ai sai kuzo ku tafi tun kafin dare ya sake yin nisa kuma” Inna tace “mu tafi kuma?” Asma’u data shigo tace “dare ai ya riga yayi, ballantana daren damina? Anan zamu kwana da safe Inna zata tafi ni kuma zan zauna sai sunday” ya girgiza kansa “no, kuzo ku tafi yanzu. A Kano ai dare baya yi ko sha biyu kuka fita zaku samu abin hawa” ya ciri dari biyar ya ajiye a kusa da Inna “gashi ku hau adaidaita” ya juya ya fita.6 STORY CONTINUES BELOW Suka tsaya cirko cirko suna kallon juna, Asma’u tace “hamma Saghir bashi da mutunci Inna, bara inje in gayawa Adda tayi masa magana, yanzu ina zamu fita a wannan unguwa tasu duk kango? Ga shi har yanzu yayyafi ake yi” Inna ta girgiza kanta, “kar ki gaya mata. Dauko mayafin ki mu tafi. Allah yana nan ai shi zai kaimu gida lafiya” Asma’u bakin ciki ya ishe ta, Inna ma wani irin zafi zuciyarta take yi mata amma bata son gaya wa Diyam, shi da yayi din ai yasan ba dai dai bane kuma Diyam sai dai ta bata ranta kawai amma ba zata hana shi abinda yayi niyya ba, tasan ko bare Diyam ta aura ba zai musu wannan wulakancin ba ballantana ɗan yayanta, ɗan yayan mijinta. Ko Sadauki Diyam ta aura ba zai wulakanta Inna ba.3 Mayafan su kawai suka dauka, lokacin karfe goma har ta gota Asma’u dan bakin ciki ko kayanta bata dauka ba suka fita ni ina can ban sani ba, ga duhu ga yayyafi anayi ga uban sanyin da yake kadawa. A bakin gate suka yiwa maigadi sallama, yace “Hajiya tafiya a cikin ruwan nan? Ku bari mana sai da safe ko kuma ayiwa mai gidan magana ya kaiku a mota” Asma’u tace “maigidan ai shi ya kore mu kuma yafi kowa sanin yana da mota”.2 Hanya duk ruwa ya kwanta haka suka ringa haskawa da wayoyinsu suna tafiya karnuka suna tayi musu haushi, babu alamar mutum ballantana abin hawa har suka fita bakin titi. Suka tsaya suna ta karkarwar sanyi amma babu abin hawa babu alamun sa. Asma’u ta fara kuka “Inna mu koma mu gaya masa bamu samu ba. In baya son mu kwana a gidan sa ba sai ya kaimu gida a mota ba? Ai muma muna da gidan ba’a titi muke ba” Inna dai bata ce mata komai ba. Can bayan sun gaji da tsaiwa sai suka fara tafiya a kafa suna saka ran maybe in sunzo round din yan kaba zasu samu adaidaita a can, ko babur ne ma in suka samu hawa zasuyi in dai zai kaisu gida. A lokacin sha daya na dare har ta wuce. Suna cikin tafiya ne wata mota ta tsaya a bayansu, suka juyo suna tunanin ko taimako ne tazo musu amma sai ji suka yi anyi musu fito, daganan suka gane yan iska ne dan haka suka kara sauri. Aka sake biyo su a baya aka ce “yan mata ji mana” Inna ta kankame hannun Asma’u suna sauri kamar zasu tashi sama amma sai motar ta sha gabansu, aka haske musu fuska da fitila sai wani yace “ashe ma tsohuwa ce da yarinya. Kyakykyawar yarinya” Inna ta tura Asma’u bayanta a lokacin da maza biyu suka fito daga motar. “Haba baba, Menene na boye ta? Rage mata hanya kawai zamuyi fa” dayan yace “kema in kina so sai mu rage miki hanyar amma a boot” suka kwashe da dariya sannan suka yo kan su Inna a tare. Da gudu su Inna suka diba, Asma’u tana gaba inna tana binta a baya mazan suna binsu a baya, daya yace “kunga tsohuwa ita ma ta iya gudu? Lallai itama da sauranta ashe”. Basu yi wani nisa ba suka cimmasu suka kama su, Asma’u tana ta ihu, Inna tana ta rokon su su rabu dasu “me muka yi muku yaran nan? Ku sake ta dan Allah marainiya ce” daya yace “nima maraya ne, kinga mun dace kenan”.3 Sanda suke tisa keyar Asma’u cikin mota ne wata mota ta hawo ta bayan su a hankali, har ta gibta kuma sai tayi reverse da sauri ta tsaya. Asma’u ta fara kokawa dan ta samu karfin ganin taimako yazo mata wannan ya hana su tayar da motar har na cikin bakuwar motar ya fito da sauri ya taho gurinsu. Wanda yake rike da Asma’u ya fara zarowa daga motar yayi masa naushi biyu take sai ga jini a gaban rigarsa. Ba shiri ya sake ta ya shige motar, wanda yake seat din driver yayi saurin tayar da motar dan yana gudun karbar nasa rabon suka bar gurin a guje. Asma’u ta fadi a gurin tana mayar da numfashi cike da tsoro sannan ta juya tana kallon wanda ya taimaka mata, sai taga Inna ma shi take kallo amma maimakon tsoro mamaki ne kawai a rubuce a fuskarta. “Sadauki?” Ta fada da rawar murya “Sadauki!” Asma’u ma ta fada, tabbas, wannan fuskace da baza ta manta ba duk kuwa da cewa rabon data ganshi tun tana shekara tara a duniya yanzu kuwa shekarar ta goma sha shida. Sai ta mike da gudu ta tafi ta rungume shi. “Yar Asama” ya fada yana rabata da jikinsa, fuskarsa dauke da murmushi.1 Ni ina can ina yiwa Subay’a wanka naji shigowar motar Saghir, har na gama yi mata wankan na shirya ta nima na shiga nayi na fito na tarar har ta yi bacci na shimfida sallaya na tayar da sallah, sai dana idar sannan na sauka dan in tabbatar su inna basa bukatar komai kafin in kwanta, amma sai naga dakin ba kowa, kitchen ma haka. Wasa wasa na chaje gidan amma babu su babu alamun su, hankalina ya fara tashi na koma sama na dauko waya da niyyar kiransu amma naji ance min “your account is not sufficient to make this call” bank da kudi, da zan kira Inna jiya ma ranta nayi a network dina. Hankalina in ya kai dubu duk ya tashi a lokacin dole na tafi dakin Saghir da sauri na fara buga masa kofa. Ya bude ya tsaya yana kallona nace “su Inna, ban gansu ba, ka bani aron wayarka dan Allah in kira su” yace “sun tafi gida. Ni nace su tafi. Da iznin waye kika gayyato min mutane zuwa gidana?” Na fara girgiza kai na saboda mamaki nace “mutane? Su Inna da Asma’u ne mutane?” Yace “ohh, aljanu ne ba mutane ba?” Ban jira sauran maganar saba na shiga dakina da sauri na dauko hijab dina, nayi hanyar stairs, nima gidan zan bari tunda har zai iya ya kori uwata daga gidan nan toni zaman me zanyi a cikin sa? Da sauri naga yazo ya wuce ni ya riga ni sauka, ban fahimci me yake yi ba sai dana ganshi a bakin kofar fita daga pallon, ya saka key ya rufe kofar sannan ya juyo ya wuce ni hau stairs yana kallona yace “nasan in na ce miki in kika fita a bakin auren ki da sauri zaki fita tunda abinda kike so kenan”.2 Na bishi a guje ina ihu “ka bude min kofa Saghir, ka bude min kofa nace” sai ma ya shiga dakinsa ya rufe kofa ya rabu dani. Na dawo kasa da sauri ina neman hanyar fita amma babu, duk windows din gidan akwai burglers a jiki, kofar kitchen ta baya kuwa dama tun ina amarya data lalace har yau ba’a gyara taba mun dai a amfani da ita. Sai na kama kuka ni kadai kamar mahaukaciya ina zagaye gidan. Ji nake a raina gwara in kwana a titi a ranar akan in sake kwana a gidan Saghir. A haka har karfina ya kare na zauna na jingina kaina da jikin kujera ina ajjiyar zuciya. A raina ina aiyana abinda zanyi wa Saghir in wani abin ya samu su Inna. A lokacin ne waya ta tayi kara, nayi saurin dauka na duba naga sunan Inna da sauri na amsa nace “Inna me yasa zaku tafi a cikin daren nan? Kuna ina Inna?” A nutse naji muryar ta, hakan ya kwantar da hankali na sosai tace “ki daina kuka Diyam, muna gida mun iso lafiya” nayi ajjiyar zuciya nace “alhamdulillah. Inna hankali na ya tashi sosai” sayi shiru sai kuma tace “Diyam, Sadauki ne ya kawo mu gida. Ba dan Sadauki ba Diyam yau da bansan me zai same mu ba. Sadauki ne ya taimake ni Diyam a lokacin da Saghir ya wulakanta ni”.12 Sadauki?” Na maimaita cikin tsananin mamaki “a ina Sadaukin ya ganku?” Sai ta bani labarin abinda ya faru dasu bayan sun bar gidan. Wannan ya kara ruda tunani na, me Sadauki yake yi a wannan hanyar a wannan lokacin har ya gansu ya taimaka musu? Duk da bansan a wanne hotel yake zaune ba amma nasan babu hotel a kusa damu, sannan unguwar mu wajen gari ne ballantana inyi tunanin ko wani abu ya fito nema kuma ma ai mutane masu kudi irinsa ba zasu fito neman abu ba sai dai suyi order a kai musu har inda suke. Tabbas ina bukatar yin magana da Sadauki. Amma dai ko menene yake yi a gurin am greatful da taimaka musu da yayi saboda I can only imagine irin horror din abinda zai faru dasu da bai zo din ba, wannan kuma sai ya kara hura wutar kiyayya da nake yiwa Saghir saboda shine ya kusa jefa su cikin wannan halin. Naso in tambayi Inna a game da Sadauki amma sai tayi min sallama tace dare yayi sai gobe zamuyi magana. Anan palo na karasa kwana saboda saman gani nake kamar na kara kusa da Saghir.+ Sa safe Subay’a ce ta tashe ni tana neman abinci, da yake ban samu nayi bacci sosai ba shi yasa na makara. Na jata muka shiga dakin kasa mukayi sallah tare sannan muka shiga kitchen na dora mata noodles na soya mata kwai, ina cikin aikin Saghir ya shigo Subay’a ta tafi gurinsa da gudu ya dauke ta suka tsaya a bakin kofa yana kallona yace “me ake dafa mana ne?” Ko kallo bai ishe ni ba, shi har yana da karfin halin pretending kamar babu abinda ya faru? Subay’a ce ta bashi amsa, sai yace “Subay’a mommy fushi take yi da Daddy saboda yace zaiyi aure” na juyo na watsa masa harara, ni har na manta ma da yace zaiyi aure. Ina jin Subay’a tana tambayarsa menene aure, na bar musu kitchen din sai ya biyo ni yana cewa “wai duk kishin ne haka? Ni na taba ganin anyi kishin wanda ba’a so?” Har zan wuce kuma sai na dawo na karbi Subay’a daga hannunsa nace taje kitchen ta dauki abincinta taci sannan nace masa “Saghir ko matan duniya zaka aura ko a tafin kafar Halima. Ni din ce dai ba zaka samu zuciya ta ba wallahi. Kuma su Inna sunje gida lafiya babu abinda ya same su, sun samu wani bawan Allah wanda yasan mutunci da darajar mutane ya taimaka musu kuma ya kaisu har gida a mota, bawan Allahn da basu hada dangantaka ta jini dashi ba” yace “ohh there is that, ashe fushin biyu ne” wato shi a nufinsa har ya manta da abinda yayi. Yace “to yanzu wanene bai san darajar mutane ba? Ni mutum ne mai ka’idoji kin sani kuma, ni bana son a shiga rayuwata sam bana son ake kawo min mutane cikin gidana” nace “gida? Amma dai kasan muma muna da gida ko? Kasan ba’a titi muke ba ko?” yace “sai su zauna a gidan naku kar su zo min nawa gidan, as simple as that” na girgiza kaina nace “ni Saghir bani da sauran karfi, na zuciya da na jiki da zanyi fada da kai, ka fadi duk abinda kake son fada ka kuma yi duk abinda kake son yi. Duniya ce, akwai ranar kin dillanci kuma ina sanar maka da cewa tana daf da zuwa” ban jira abinda zai ce ba na haye sama. Ina jinsa ya bude kofar palo ya fita, na leka naga shi da Subay’a ne suka fita a mota, na sauko kasa da sauri na tura kofa naji a rufe, wato rufe ni yayi daga waje ya tafi da key din. Ina zama Inna tana kira na, dama tun dazu nake ta zuba idon ganin kiranta amma sai naji muryar Asma’u tace “Adda inna fa kuka take yi tun da muka dawo jiya da dare, tun da taga Sadauki take kuka na rasa dalili” na gyada kaina, ni nasan dalilin, nace “me Sadaukin yace sanda ya dauke ku?” Tace “baice komai ba fa, kawai tsokana ta yayi tayi har muka zo gida. Inna tace masa tana son ganin sa sai yace zai zo watarana” na tambayeta “ya tambaye ki ni?” Tace “a’a” na lumshe ido ina jin hawaye yana taho min. Idan ni ce na hadu da yaya ladi misali nasan abinda zan fara tambayarta shine Sadauki. Ko dai Sadauki ya daina so nane? Duk da dai Saghir yace min baiyi aure ba amma for all I know maybe yana da budurwa yanzu, maybe ma an kusa bikin. Maybe ma yaruwarsa zai aura a Maiduguri. Nace da Asma’u ta kira Mama ta gaya mata abinda ya faru, ni ba zan iya zuwa in lallashi Inna ba saboda Saghir ya rufe ni a gida. Na san kuma yanzu inna tana bukatar wanda zasuyi magana dashi, musamman wanda yasan abinda tayi wa Sadauki da shi kuma sakayyar da yayi mata. Ta barshi a titi a lokacin da yafi bukatar gida, shi kuma sai ya dauko ta daga titi ya kai ta gida a lokacin da tafi bukatar hakan. Washegari Sunday, Saghir ya fita sai gashi ya dawo yana washe baki, ko kula shi banyi ba dan ban damu da insan me ya saka shi farin ciki ba amma sai ya zauna yana cewa “subay’a daddyn ki zai tafi kasar waje, me kike so in siyo miki?” Ta mike da murna tana tsalle tana yi masa list din kaya, shi kuma yana ta dariya, sai ya kalle ni yace “ki hada min kaya, gobe zan tafi oga ya tura ni zanyi signing contract da wani company a can” na dauke kai kamar ban ji shi ba sai yace “dama nan da two months ne tafiyar nan tazo, da da amarya ta zan tafi. Ohh ban fada miki ba ko? Nan da wata biyu ne aure na fa” nace “to ka daga tafiyar mana sai anyi bikin? Ohh na manta, ashe bada kudinka zaka yi tafiyar ba da kudin oga ne kuma dole sai abinda oga yace sannan zakayi tunda kudin sa ne. Mtsww i pity you” da naga dai neman magana yake yi sai na tashi na bashi guri saboda ni bana son rigima dashi a gaban Subay’a, amma kuma sai na samu zuciya ta da jin haushin Sadauki na budawa Saghir da yake yi. STORY CONTINUES BELOW Shi ya hada kayan tafiyar sa da kansa, da safe ya turo Subay’a ta kira ni naje na tsaya a bakin kofa yace “rashin kunyar ki, da rashin biyayyar ki shi yasa har yanzu auren mu yaki daidaita, da ace kin kwantar da kai, kin bini yadda nake so da ba karamin jin dadi zakiyi tare da ni ba. Kinga wannan tafiyar ma oga mu biyu ya biya wa, ni dake, yace in tafi da matata saboda wata daya zanyi kar in zauna gwauro a can, kinga da sai muyi tafiyar mu ni da ke da Subay’a but I guess I will have to go alone” ya ajiye kudi a kan mirror “ga kudin cefane nan, kinsan ni ina tsoron Allah dan haka ina kokarin sauke hakkin ki da yake kaina. Ban yafe ba, in kika fita ko da kofar gida ne indai ba abinda ya shafi makarantar Subay’a bane ba, sai kuma rashin lafiya, Allah yana kallonki in kika ci amana ta in bana nan” nayi murmushin takaici kawai, akwai amsoshi da yawa a raina wanda nake so in bashi amma ganin Subay’a yasa nayi shiru har ya dauki jakarsa ya fita yana cewa “gwara mutum ma ya dan bar kasar ya sarara na kwana biyu”. Tafiyar Saghir da kwana biyu Alhaji Babba ya kira ni a waya, I can’t remember last sanda ya kira ni. Na dauka na gaishe shi sai naji muryarsa wani iri yace min “Diyam ki zo gida ina nemanki dan Allah” sai naji wani iri da yace min dan Allah, duk da dai Alhaji Babba yayi sanyi sosai tunda yanzu kusan hannu baka hannu kwarya suke zaune a gidan, bashi da komai sai yan abokai da suke taimaka masa da kuma kawu isa shima da yake dan bashi wani abu, duk sana’ar daya kama sai ta rushe, kullum muka je gidan yana ta cewa makiya ne suka sako shi a gaba ni kuwa deep down nasan inda matsalar dukiyar Alhaji Babba take, kudin mune da yaci, dukiyar marayu daya handame ya hada da tasa dukiyar da yasha wahala gurin nema dan haka sai yayi asarar har tasa dukiyar gabaki daya. Na tambayeshi ko lafiya? Sai yace inzo dai kawai yana nema na. Na shirya ni da Subay’a muka tafi. Bayan mun gaisa da mutanen gida ne muka tafi palonsa na ganshi daga shi sai riga yar shara wadda duk tayi datti. Na durkusa na gaishe shi sai ya dauko wasu takardu ya miko min. Na bude a nutse ina dubawa a dan ilimi na sai na fahimci takarda ce daga kotu ta sammaci, mai kara shine ‘Aliyu Usman Kollere” Wanda ake kara kuma “Alhaji Muhammadu Kollere” sai kuma sauran takardu da suka kunshi photocopy na takardar fili belonging to Aliyu Usman Kollere, da kuma takardar garage din Baffa, sannan anyi list na duk abinda yake ciki da kudinsa da kuma estimate na kudin business din gabaki daya, sai kuma akayi jimullar kudin wanda yawansu sai da yasa na kama baki na. Yanzu wannan ne dama kudin da Alhaji Babba yaci na mu? Wannan shine kudin da akace anyi min kayan daki dasu? Amma mai yasa alhajin yake nuna min a yanzu? Kamar amsar tambaya ta sai naji yace “Diyam kinga abinda tsohon saurayin ki zaiyi min ko? Yaron da Usuman ya rike kamar shi ya haifeshi kinga sakayyar da zaiyi mana ko? Wai ya kaini kara wai naci dukiyar marayu to dukiyar ta ubansa ce? Ina ruwansa? Kudin nan ba aure nayi miki dasu ba? Ai na gaya wa Amina tun a lokacin kuma ra amince. Takamarsa shine da kason uwarsa a ciki shine yake so yayi min tonon silili” ni dai na ajiye takardun ina kallonsa har ya gama fadan sa sannan kuma sai yace “an ce min in na saka kika yi masa magana zai iya ya janye wannan maganar” na gyada kai, so that’s it. Wannan shine dalilin da yasa aka shigar dani maganar. Nace “ni Alhaji bansan inda Sadauki yake ba ballantana inyi masa magana, kuma ma ba lallai ne ya saurare ni ba. Amma shi ne ya kawo takardun?” Yace “ina fa? Babu wanda yasan inda yake fa, lauyoyi ya dauka har guda uku, su suka shigar da karar alkali kuma ya aiko min da sammaci” ba gyada kaina, wato basu san waye Sadauki a yanzu ba. Nace “to ni Alhaji in zanyi masa ma maganar ai bansan inda zan same shi ba” yace “Amina ma tace bata san inda yake ba. Kuma ko number dinsa babu a jikin takardar sai ta lauyoyinsa” na dauki takardar ina kara dubawa sai naga numbobin, na dauki daya a waya ta nace “idan na same shi me zance masa?” Ya gyara zama yace “ki gaya masa ni ba matsiyaci bane ba, kaddara ce ta sauka a kaina da kuma makiya da suka sako ni a gaba wannan ne yasa a yanzu bani da kudin da zan bashi, amma kice masa yayi hakuri muyi aggrement zanke biyansa a hankali a tsakanin mu ba sai munje kotu ba” nace “shikenan Alhaji, zanyi kokarin ganin yadda za’ayi a fahimci juna” yayi ta saka min albarka sannan yace “ashe mijinki yayi tafiya? Sai da aka kawo takardar nan jiya na neme shi sannan naji ma wai baya kasar”. STORY CONTINUES BELOW Na fito ina ta mamakin halin Saghir. Sai kuma na koma lissafin wannan lamari. Me Sadauki yake after? Na tabbatar ba kudin yake so ba dan yafi karfin wannan kudin a yanzu. Sai kuma na fahimci wannan shine dalilinsa na tura Saghir kasar waje saboda baya so yayi blowing cover dinsa ta matsayin ogan Saghir, duk da dai yadda ya shirya kai karar ba lallai ne ma a ganshi ba dan lauyoyinsa sun isa su wakilce shi amma me yake bukata? Sai dana koma gida sannan na kira number din lawyer din. Ya dauka na gaishe shi ya amsa sama sama sai nace dan Allah ina son magana da client dinsa Aliyu Usman Kollere, yace “what for? Bana bada contact din client dina gaskiya” nace “na fahimta, but please ka gaya masa in ya tuna Halima Usman Kollere to tana son magana dashi” ya amsa zai fadi sakona sannan ya katse wayar. Jira jira har dare babu amsa, haka nayi ta duba waya ina karo volume wai dan kar a kira banji ba. Sai safe around ten sannan kiran ya shigo, lawyer din ne dai yace “yace menene? Ki gaya min sakon sai in gaya masa” na runtse idona ina jin duniyar ma duk tayi min zafi nace “shikenan. Tell him nace dashi nake son magana ba da kai ba in bashi da guts din da zai saurare ni shi kenan na rike magana ta” na kashe watar ina jin zafin Sadauki a raina. Wato bama yason magana dani, baya son gani ba, ya manta dani yake nufi ko me? Ya manta alakar mu? Ya manta alkawarin mu? He said he will love me forever yanzu har forever din tayi? Amma sai wata zuciyar take tuna min da matsayi na na matar wani, wata zuciyar tana so in yi wa Sadauki uzuri na kin saurata ta da yayi, na gudu na da yake yi. Around 12 wani kiran ya shigo wayata, saida zuciyata ta buga ganin sabuwar number, sai na samu kaina da rike wayar amma na kasa amsawa har ta kusa katsewa sannan na dauka a hankali na kai kunnena idona a rufe nayi sallama, shiru at first, sannan yace “kina son magana dani, ina jinki” muryar Sadauki, as clear as ever. Na hadiye abinda yaki tafiya a makogwaro na sannan nayi kokarin nima in yi irin nasa nace “maganar Alhaji Babba, yana son ayi negotiation. Can you do that?” Ya danyi shiru sannan yace “come to my office tomorrow morning, you know where it is” daga nan ya katse. Sai na zauna da waya a hannu ina mamakin wai da Sadauki nayi magana yanzu, but it sounded as if da wani stranger nayi maganar.1 Ranar bana jin nayi baccin awa daya. Da assuba na tashi nayi wanka nayi sallah sai kuma na zauna ina kallon agogo yana ta lakaki yaki yin sauri balle gari ya gama wayewa. Na tashi Subay’a na shirya ta sannan nima na shirya tana ta tambayata inda zanje, na bata breakfast nima na hada tea na kurba amma sai ya tsaya a makogwarona yakasa wucewa. A haka har lokacin kaita school yayi, na kaita sai kuma nayi tunanin is too early inje office din Sadauki dan haka na dawo gida na cigaba da kallon agogo har saida ten tayi sannan na fita. Ina gayawa mai adaidaita Abatcha Motors sai yace “okay companyn motocin nan ko?” Sai da muka isa gurin sannan na kare wa building din kallo, so all of this is owned by Sadauki, how? Na shiga trying not to act like yar kauye, shi kansa building din anyi shine da shape din mota, haka round about din da yake tsakiyar gurin shima siffar mota ce dashi. Sadauki and cars bansan wacce irin soyayya ce a tsakanin su ba. Ina shiga reception din sai na tuno da ranar da akayi party, nayi tunanin ko wasu zasu gane ni? Amma kuma ranar babu haske sosai dan haka ba lallai bane su gane fuskata. Naje desk din receptionist, kafin inyi magana tace “Halima?” Na amsa mata sai ta dauki waya tayi magana a ciki sannan ta nuna min bene tace in hau, na hau na tarar da wata tana jira na sai ta bude min wata kofa tace in shiga, na shiga na tarar da wata mata da name tunanin secretary ce, kyakykyawar gaske gata ta sha make up sai kamshi take zubawa, ta yi min murmushi sai kawai naji ina jin haushinta ba tare da ta yi min laifin komai ba, ta wuce gaba sai naga kamar tana sane take murguda min bombom ta bude min wata kofa da card din hannunta na shiga sannan ta rufe. Yana zaune a bayan katon table din gaban sa, as majestic as ever, bai ko dago kai ya kalle ni ba yaci gaba da rubutu a takardar gabansa ni kuma ina tsaye sai daya gama sannan ya dago fuskarsa blank yace “welcome Madam, have a seat please” naji kamar in juya in fita daga office din, nayi nadamar dana sani banzo ba amma ina bukatar amsa, ina bukatar ji daga bakinsa cewa ya manta da first twenty years of his life. Na zauna a kan cussion chairs din da suke jere a office din. Ya mike tsaye, sai naga ya kara cika min ido da kwarjini da girma baki daya ya zagayo ya zauna a kujerar gaban table dinsa sannan yace “kince Alhaji Muhammadu ya turo ki akan wani negotiation, ina jinki” naji wani sabon bacin rai, ni na ma manta abinda ya kawo ni kenan, sai kawai hawate ya fara bin fuskata. Nace “abinda zaka ce ma kenan? Irin karbar da zakayi min kenan? Sadauki nice fa Diyam, how can you even……call me Madam?” Sai ya mike tsaye ya juya bayansa ya saka hannu a aljihu yace “menene sakon da Alhaji yace ki fada min?” Sai na mike na nufi kofa da sauri ina goge hawayen fuskata, bai ce min komai ba har naje na kama kokawa da kofa amma taki budewa, na juyo ina kallonsa sannan yace “ba’a fita daga office dina sai nayi wa mutum izni” sai na dawo da baya da sauri na dauki wasu magazines na motoci na jefa masa, na debo tarkacen files din kan table dinsa suma na yi ta dukansa dasu har takardun suka tarwatse a gurin amma ko motsawa baiyi ba, na durkusa a tsakiyar gurin na kama kuka sai ya dawo ya zauna akan kujera yace “menene sakon da zaki gaya min?” Sai dana gama kukana sannan na tashi na zauna na goge fuskata nace “why? Sadauki why? Me yasa kame treating dina haka?” Yace “ya kike tsammanin zanyi treating mayar employee na?” Nace “shikenan? Matsayina kenan? Matar employee dinka? Me yasa ka dauke shi aiki ma? A ina ka sami wannan kudin kuma? I need answers Sadauki, I need to talk to Sadauki not this Mr Abatcha” yace “zaki samu answers dinki in due time. Now me Alhaji Babba yace?” Na goge hawayena nace “nasan kasan bashi da kudi yanzu, bashi da kudin biyanka ko da kuwa kotun koli zaka kaishi, dan haka I think you are just wasting your time” yace “really? To tunda bashi da kudin biya na fili na da gadona sai ya shirya zuwa prison for it. Kullum takamarsa kenan, kullum maganar sa itace zai saka a rufe ni, lokacin yana da kudi ni kuma bani dashi. Ki je kiyi masa albishir da cewa the table have turned, yanzu nine zan rufe shi” na bude ido ina kallonsa nace “you don’t really mean that, me zakayi da kudin? Me zakayi da filin Sadauki look at this” na fada ina nuna office din nasa “zaka iya siyan hundreds of wannan filin, kafi karfinsa yanzu” yace “Baffa ne ya siya min remember? I was suppose to build us a house a kan filin nan, gidan mu ni da ke da yayan mu remember?” Sai kuma ya mike ta sake juya bayansa yana kallon window. Mun jima a gaka sannan nace “kayi tunanin abinda Baffa zai so, Alhaji Babba yayansa ne uwa daya uba daya ba zai so ya ganku a court dakai dashi ba, ba zai so yaga ka rufe masa dan uwansa akan kudi ba” ya juyo yana kallona yace “kamar yadda ba zai so a cire ki daga makaranta exactly 40 days bayan rasuwar sa ayi miki aure ba, kamar yadda ba zai zo a siyar da abinda ya kwashe rayuwarsa yana building abar iyalinsa da hamma ba” sai yakuma juya wa sannan yace “kamar yadda ba zai so a raba mu ba” na runtse idona ina jin wound fin zuciyata yana dawowa sabo, kewar Baffa na tana lullube ni, mun jima haka sannan yace “tell Alhaji Babba nace yana da options guda biyu, na daya shine ya bar mana gidansa da yake ciki tunda shi kadai ne yanzu abinda ya rage masa, na biyu kuma shine ya tafi prison for the rest of abinda ya rage na rayuwarsa” Na mike tsaye, “Sadauki, ubangiji ma yana son rama sharri da alkhairi, kamar yadda kayi wa inna, dan Allah ka bar maganar nan, Allah ma daya halicce mu muna yi masa laifi kullum amma idan muka durkusa muka roke shi gafara sai ya yafe mana” ya juyo yana kallona, his eyes shining, yace “then tell him yana da third option, yazo ya durkusa ya roke ni gafara, ya saka gwuiyoyinsa a kasa ya roke ni in yafe masa kamar yadda na saka guiwowina a kasa na roke shi ya bani aurenki ya hana ni, ya durkusa kamar yadda na durkusa na roke shi kar ya aura miki that monster he calls a son amma duk da haka ya aura miki shi. Yes, I want him to cry and beg kamar yadda nayi in yaso in naki hakura duk da yayi haka sai yaji shima irin yadda naji”. Sadauki yayi tsauri da yawa ko?Raina ya kara baci, ina mamakin anya kuwa wannan Sadauki nane? Sadaukin da na sani will never do that amma kuma sai nayi wani tunani. Yes, Sadauki yana da kirki da kyawun hali sosai amma bashi da yafiya, musamman idan akan abinda ya shafe ni ne Sadauki bai taba daga kafa ba ko da kuwa waye ya taba nin indai ba Inna ko Baffa ba, na tuno ranar daya doka wa yaya Mukhtar ball aka a gaban Inna. Sadauki bashi da tsoro ko kadan tun a lokacin da bashi da komai ma, ballantana kuma yanzu da yake da masu garin.1 Nace “abinda kake so kenan? Abinda kake after kenan? Revenge?” Ya girgiza kai “this is not revenge, this is justice” nace “wanne justice din ne kuma wanda yafi wanda Allah ya riga yayi? Shin in kayi haka Sadauki ka gode wa Allah kenan? Kaga kuwa halin da Alhaji Babba yake ciki a yanzu? Ka kuma duba kaga halin da kai kake ciki a yanzu, kai kanka ka fada, the table have turned, menene kuma saura? Shin in ka yafe wa Alhaji Babba mai zai ragu daga jikin ka? Sai ma daraja da hakan zai kara maka a gurin ubangiji. Yanzu in ya siyar da gidansa ina zai kai iyalinsa?” ya bar inda yake tsaye ya zagawa gurin kujerar sa ya zauna yace “sai su dawo gidan ku ku zauna tare, ai naga kuna da bene, sai su zauna a sama ku kuma a kasa” na saki baki ina kallonsa sai ya danna wani button a jikin table din sai naga kofar dana shigo ta bude, ya kalle ni yace “goodbye, Diyam” na tsaya kawai ina kallonsa ina girgiza kai, I can’t believe Sadauki yayi tauri har haka, sai na je na tsaya a gaban table dinsa nace “I don’t like this Mr Abatcha da nake gani a gabana, I want my Sadauki back, I want my brother back” sai na juya da sauri na bar office din.4 Ina jin matar nan ta waje tana yi min magana amma ban ma fahimci abinda tace ba ni dai na gyada mata kai kawai na fita da sauri. Da saurin kuma na karasa wajen gate na tari abin hawa na shiga muka tafi. Sai da muka bar gurin sannan na saki kukan da nake rikewa, ma dauka hawaye ne kadai nake yi bansan ya fito fili ba sai da naji drivern yace “yammata kiyi hakuri, komai na duniya mai wucewa ne watarana sai kiga kamar ba’ayi ba” a goge hawaye na ina jinjina maganar sa, watarana zanga kamar ba’ayi ba? Yaushe? Sai dana je gida sannan nayi realizing wani abu guda daya, ni da na tafi gurin Sadauki da niyyar samun answers amma ban samu ko daya ba sai karin tambayoyi da na debo wa kaina. Na sani Alhaji Babba ya zalunce ni kuma ya zalunci Sadauki kuma har cikin raina ban damu ba in wani abin ya same shi a saboda abinda yayi, abinda na damu dashi shine Sadauki, I don’t like this person he as turned to bana son wannan hanyar da yake tafiya a kai. Ni da zai aje duk wannan kudin nasa ya koma former Sadaukin da na sani da sai nafi jin dadi. Na biya na dauko Subay’a sannan muka karasa gida. Muna zuwa na shiga daki na hada mana kayan mu ni da ita a akwati na chanza mata kaya muka fito. Mai gadi yace tafiya zakuyi ne haka Hajiya?” Nace “cikin gari zamu shiga baba iliya, sai Sunday zamu dawo” ya taro mana abin hawa ya saka mana kayan mu muka tafi Subay’a tana ta murna.3 Muna shiga gida naga Inna duk tayi wani jeme jeme da ita, bayan mun gaishe ta ta kalli akwatin kayan mu tace “da fatan ba yaji kika yo ba Diyam” na girgiza kaina nace “yayi tafiya ne Inna, shine muka zo gida muyi dan kwana biyu” ta gyada kai tace “duk da haka ina fatan da amincewarsa kika taho gidan. Nasan ba kya son Saghir, kin fada kin kara fada cewa ba kya son sa kuma har yau nasan ba kya son nasa din. Amma kuma rashin son nasa da ba kya yi ba zai cire shi daga matsayin mijinki ba. Ni nasan kiyayya Diyam nasan illolinta, tun zamanin yammatanci na na dora wa zuciyata kiyayyar Zainab kawai saboda baffanku yana sonta ni kuma ina sonsa. Kiyayyar ta karu lokacin da aka aura masa ni ina matsayin matarsa amma kullum sai ya tuna min cewa dole aka aura masa ni, sai ya gaya min cewa ga wadda zuciyarsa take so. Na kara kin ta kuma lokacin daya aure ta ya kawo ta gidan nan duk kuwa da cewa tayi aure ta fito amma bai rage soyayyar ta ba daga zuciyarsa. Sai ma ya dauki wani son daban ya dora akan agolan da tazo dashi har a gurina nake ganin kamar yafi sonsa akan ku yayan da na haifa masa. Sai ni kuma na tsani yaron ba tare daya yi min komai ba. Har yau ni bazan iya fadar wani abu na rashin kyautawa ko rashin kunya da Sadauki ya taba yi min ba. Na tsane shine kawai saboda na tsani uwarsa. A gaban Sadauki zan gaggayawa Zainab magana amma baya kulani saboda ta hana shi tace babu ruwansa da tsakanin mu. Amma haka na cigaba da rura wutan kiyayyar sa a zuciya ta yadda har mutuwar ita kanta wadda ta haife shi da wanda ya kawo su gidan bata wanke kinsa a raina ba a karshe ina ji ina gani na saka rayuwar yata ta cikina a wahala kawai saboda in bakanta masa” sai ta rufe fuskarta ta kama kuka “Diyam ki gafarta min abinda nayi miki,ni na haife ki amma na tauye miki hakkin ki na bawa azzalumai damar zaluntarki” sai na tashi daga gabanta na koma kusa da ita na dora kaina a kafadarta na fara kuka. Ta saka hannu tana shafa kaina tace “nayi nadama, nadama mai tsanani. Maganar baffanku ta tabbata, yan uwanmu sun watsar damu a titi Sadauki yazo ya dauke mu. Ohh duniya. Duk wanda bai godewa rahamar Allah ba to kuwa tabbas zai godewa azabtar sa. Diyam nayi nadama a lokacin da nadama bata da amfani. Wallahi da ace igiyar auren ki a hannuna take Diyam da tun haihuwar ki ta farko zan gutsire auren gwara ki dawo gida ki zauna a gaba na akan auren Saghir. Amma na kai ki na baro ki. Babu abinda zanyi sai dai in nemi gafarar ki” na rungume ta nace “Inna kinfi karfin haka ai, ni dama ban rike ki a zuciyata ba ballantana ki nemi gafara ta. Wanda zaki nemi gafara shine Sadauki. Shi kika fi zalunta ba ni ba” tace ” to ni Diyam ina zanga Sadauki? Tunda ya kawo mu nan ya ajiye mu bai dawo ba. A lokacin na gaya masa ina son magana dashi sai yace min zai dawo amma tun lokacin nake zuba idon ganin sa sai dai shiru babu shi babu labarin sa”.1 STORY CONTINUES BELOW Sai na bata labari. Na bata labarin asalin ko wanene Sadauki a yanzu sannan kuma na gaya mata yadda mukayi da Alhaji Babba da kuma irin amsar da Sadaukin ya bayar. Na karashe da “yanzu dai Sadauki yace Alhaji Babba yana da dama uku. Ko dai ya bamu gidan da yake ciki a maimakon kudin mu, ko yayi jail time, ko kuma yaje gaban Sadauki ya durkusa yana kuka ya roke shi gafara a bisa dukkan abinda yayi masa” Inna ta rike baki ta kasa magana. Nayi shiru ina kallon ta ina jiran ta inda zata fara jero tsinuwa ga Sadauki amma sai naji tace “to, kudin nan dai namu ne gabaki daya, ni dai abinda yake hakkina a cikin kudin nan na yafe wa Alhaji Babba tare da fatan Allah zai dubi niyya ta nima ya yafe min wasu daga cikin laifuffuka na. Amma a cikin ku ban tilastawa kowa ta yafe nata ba, duk wadda taga bata yafe ba sai ta bawa Sadauki goyon baya gurin karbo muku abin ku. Shima kuma Diyam kar ki kuma kokarin hanashi karbar hakkinsa, in ma zubarwa zaiyi ai nasa ne ko? Da basu san kina da amfani ba sai yanzu? Babu ruwan ki, ki fita daga harkar” na gyada kaina. Sai kuma ta tambaye mu in mun yafewa Alhaji Babba, nace “ni dama ai ni yace yayi wa kaya da kudin, to in ma ina da ciko na bar masa, wanda ya tara dukiyar ma ya tafi ya barta” Asma’u tace “ni kam in dai har hamma Sadauki zai iya karbar kudin nan to ina son kaso na. Shi da bai taimaka min da komai ba ni ba zan bar masa hakkina ba” na harare ta sai ta daga kafada tace “Inna tace kowa ya fadi ra’ayin sa”.1 Da daddare tare muka kwana gabaki daya a kan gado daya muna ta hira, Asma’u sai labarin motar Sadauki take yi min “wallahi ban taba ganin mota mai kyau da dadin wannan motar ba. Kai Adda ina ma dai shi kika aura da yanzu a wannan motar za’a ke kaiki unguwa kin huta da dan sahu. Nima in naje gidanki a irinta za’ake kawo ni gida” nayi juyi nace “Asma’u dan Allah ki rabu dani, bashi na aura ba chapter closed” sai kuma nace “motoci fa yake siyarwa. Dole ya hau mota me kyau”. Washegari na shirya, na bar Subay’a anan gidan na tafi gidan Alhaji Babba. Direct part dinsa na tafi tunda yanzu ba sai anyi wa mutum iso ba. Na same shi a zaune yana lazimi, sai da ya shafa sannan ya tambaye ni “Diyam kin same shi? Me yace? Jibi ne fa zamu fara zuwa court” nace “na same shi Alhaji” sai kuma na lissafa masa abinda yace. Ya kama salati, amma wannan yaro anyi asarar haihuwa, yanzu ni tsofai tsofai dani zaice in je in durkusa a gabansa? Sakayyar da zai yiwa rikon da Usman yayi masa kenan? Gwara da Allah yasa bamu bashi aurenki ba Diyam da yanzu da surikin mu zamu shiga Shari’a” ni dai nayi masa sallama na fita ina jinsa yana cigaba da maganganu shi kadai.3 A cikin gidan ne zuciyata ta karye. Hajiya Babba ita kanta a jigace take dan yan uwanta sun gaji da taimaka mata. Muka gaisa tace “Diyam baku kyauta mana ba ke da Saghir, yanzu ace tafiya ta same shi amma sai bayan da yayi ta zamuji labari?” Nace “Hajiya ni wallahi bansan be fada muku ba, na dauka duk kun sani” ta girgiza kai tace “ina fa, mu Saghir sai yayi sati ban saka shi a ido na ba sai dai in na kira shi nace ina nemansa. Yanzu idan kunyi waya dan Allah kice masa ya kira ni” nace “to”. Dana shiga dakin Hajiya Yalwati ne na tarar dasu abin tausayi. Aunty amarya dama ta kara mai ta bar yaranta guda uku duk suna gurin Hajiya Yalwati ga sauran yayan da ake bari a gidan duk mata, ga kuma nata yaran dam haka wajan yara goma ne a part dinta, dan abinda manyan ƴaƴanta suke taimakawa dashi da kyar yake ciyar dasu. Ga yara uku sun isa aure sun kuma samu mazaje amma babu halin yi musu auren. Muka gaisa itama tayi min mita “yanzu Diyam shi mijinki ko shinkafa ba zai ke siyowa yana kawowa gidan nan ba?” Ni dai bance komai ba saboda bazanyi alkawarin da nasan ba zan cika ba. Washegari Saghir ya kira wayata. Dama tunda ya tafi kullum sai ya kira sai in bawa Subay’a su gama maganganun su in kashe. Ranar sai yace ta bani zaiyi magana dani. Ina karba ya fara fada “da izinin waye kika fita kika je gidan Alhaji?” Nace “Alhajin ai shi yayi kirana ya hada ni da Allah da Annabi inje in taimaka masa” yace “ke kuma sai kika fita, saboda kina sauri za’a tura ki gurin saurayin ki ko? Ai Alhajin duk ya gaya min abinda yake faruwa, shegen yaro da bai san darajar manya ba wai har zaice zai kar Alhaji kara ya biya shi gadon uwarsa? Yanzu haka kudin wiwin da yake sha ne ya kare shi e yake neman refill” nace “amma Alhaji bai gaya maka lauyoyi ya dauka har guda uku ba? In kudin wiwi yake nema ya siya mana da kudin daya biya lawyers din dashi? In fitsari abinyi ne kaza tayi mana mu gani” yace “kar ki gaya min magana, kinsan dai dan bana gari ne da tuni zan biya shi kudin sa, ko Mr Abatcha na gayawa a take zai bani kudin in bashi” na girgiza kaina ina jinjinawa rashin sani da hausawa suka ce yafi dare duhu. Sai nace “to ko a daga shari’ar ne sai ka dawo sai ka karba a gurin Mr Abatcha ka bawa Sadauki?” Yace “to kudin ma ba Alhaji yace dasu akayi miki kayan daki ba? Ki gayawa Sadaukin haka in yaso in karar ce sai ya kai ki ke ki biya shi” sai na gaya nasa jimlar kudin, nace “ni nafi tunanin bayan kayan daki na har gidan da muke zaune a ciki da kudin aka siya, sannan aka kara jari da sauran. Dan haka dani da kai za’a gamai biyan kudi”.5 Da daddare lawyer din Sadauki ya kira ni, wai Sadauki yace kar muje court gobe. Inna tace ai dama babu inda zamuje. Washegari suka zauna a court. Sadauki ma baije ba kamar yadda nayi tsammani, lawyers dinsa ne kawai suka je a madadin sa. Suka gabatar da dukkan takardu da kuma dukkan shaidu da suka tabbatar da wanzuwar garejin da kuma filin, sannan suka kawo shaidun cewa an siyar, har wadanda aka siyarwa ne suka zo sukayi testifying da kansu suka kuma fadi kudin da suka siya. Alkali ya nemi Alhaji Babba daya fito da kudi shi kuma ya tabbatar cewa kudi dai babu su kuma bashi da hanyar samun su a yanzu, sai dai yana neman alfarmar a bashi lokaci yake biya a hankali har ya gama. A take lawyers din Sadauki suka gabatar wa court da shaidar cewa Alhaji Babba yana da gida mai number 43 a unguwar sharada, har da estimate na kudin gidan, dan haka suna so Alhaji Babba ya siyar da wannan gidan nasa ya biya wadannan kudade, a take alkali ya amince kuma ya bawa Alhaji Babba kayyadadden lokaci na siyar da gida shi kuma Alhaji Babba sai ya nuna cewa lokacin yayi kadan saboda sai ya samu mai siya, anyi ciniki anyi komai. A take lawyers suka ce Sadauki yace zai siya, ai kuwa alkali ya bada lokaci yace aje a daidaita a kan price.1 Ana fitowa daga court kawu isa ya kira Inna ga Alhaji Babba nan hawan jini ya tashi an kaishi asibiti. Haka Inna ta saka mu a gaba muka tafi dubiya ni dai ba’a son raina ba amma dana ganshi sai naji zuciyata ta tsinke. Yana ta kuka shabe shabe da hawaye. “Yanzu ya zanyi in siyar masa da gidana? Gidan dana gina tun auren fari da gumina. In na siyar da gidana a ina zan saka iyalina kuma?” Sai naji tausayinsa,ko babu komai yayan Baffa ne shi uwa daya uba daya. Sannan ga tausayin iyalinsa ina zasu je? They are innocent. Su zan iya rantsewa basu mori ko kwandala a kudin ba. Na fita na dauki waya ta nayi ta kiran number din Sadauki bata shiga. Ko kuma blocking dina yayi ne oho. Da daddare kawu Isa yazo gurin Inna, wannan shine zuwansa gidan mu na farko tun da su Inna suka dawo. Yace “kudi dai da za’a bawa yaron nan babu su. Dan ni kaina in nace zan fitar da kudin nan to kuwa tabbas zan kassara kasuwanci na. Gida kuma kamar yadda Alhaji ya fada in ya siyar ya kai iyalinsa ina? Dan haka third option shine a kira yaron nan a bashi hakuri, ku zakuyi mana jagora zuwa gurinsa a sasanta maganar nan as a family tunda shima ai kusan family din ne, shekarar sa ashirin a hannun dan uwan mu”.1 Ni aka saka in kira Sadauki. Na gaya musu ba dauka zaiyi ba amma suka ki dan haka a gabansu na kira kuma taki shiga din. Sai na tura masa text. “Third option. Kazo a baka hakurin da kake so” na tura masa. An jima kadan yayo reply “tomorrow evening. Gidan Baffa” na gayawa kawu Isa abinda yace sannan ya tafi da niyyar gobe zai zo tare da Alhaji Babba.1 Washegari. Inna har dayiwa Sadauki girki tana ta gyaran gida ni dai ina kallonta kawai. Su Alhaji Babba ne suka fara zuwa, sai a lokacin ma yasan akwai yan haya a gidan mu. Suka zauna nan palo aka bawa Alhaji pillow ya dan kashingida saboda babu lfy. Sai after 5 Sadauki ya shigo gidan. Shi kadai, babu wani abu a jikinsa da zai nuna cewa shi mai kudi ne dan shirt da wando ne kawai a jikinsa ko agogo babu a hannunsa. Sai naga ya koma min wancan Sadaukin da na sani ba wai Mr Abatcha ba, kuma ganinsa a cikin gidan mu sai yayi adding to that feeling. Yana shigowa palon muka hada ido sai ya dauke kai, fuskarsa babu walwala ko ta cikin cokali sai kawai naji gabana ya fadi. Ya gaishe da Inna ta amsa, the first time da naji Inna ta amsa gaisuwar Sadauki. Sai ya samu guri ya zauna yana kallon Alhaji Babba yace “ina jin ka,” kawu Isa yace “dama cewa mukayi a kira ka muyi magana. Ayi hakuri a bar maganar nan ta wuce” sai yace “ba kai zaka bada hakurin ba ai” Alhaji Babba ya tashi daga kwanciyar da yayi ya matso gaban Sadauki yace “ka duba darajar rikon da Usman yayi maka, da kuma darajar yanuwantakar da take tsakanin mu ka bar maganar nan. In na baka gidana iyalina kuma ina zan kaisu? Ka duba halin da nake ciki na karayar arziki data same ni ka yafe min kudin nan. Banyi dai dai ba na sani, na aikata maka laifuffuka na sani, amma na hada ka da Allah kayi hakuri ka bar maganar nan” sai naji zuciyata ta karye, hawaye ya fara bin fuskata amma dana kalli Sadauki sai naga kamar da dutse ake magana. Sai ya mike tsaye yana kallon Alhaji Babba yace “na yafe maka kudin gadon Ummah. Amma kudin fili na ban yafe ba dan haka zan aiko a yankar min wani part na gidan ka a maimakon fili na, dama ina da sha’awar yin kiwon kaji sai inyi a gurin”.5 Na mike da sauri ina kallonsa cikin mamaki. Can his heart really be this dry? Bai jira sauran magana ba yayi hanyar waje na bishi da sauri ma sha gabansa nace “this is not you Sadauki. Ba kai bane wannan. Kai kace minzaka yafe masa in ya durkusa a gabanka ya roke ka and he did just that” ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace “ni ba haka na ce miki ba. Cewa nayi in ya durkusa ya roke ni gafara in naki yi masa a lokacin ne zai fahimci irin yadda naji. So, nayi kokari ma ai, na yafe masa rabi saura rabi”. Na dafe kirjina nace “are you this heartless Sadauki?” Yana kallona with straight face yace “do you blame me? Yes, I am heartless because they took away my heart. You are my heart remember?” Sai ya juya ya fice ya barni a tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *