DIYAM CHAPTER 16
Jin yayi shiru kuma bai fita ba yasa na bude idona, na ganshi still a tsaye yana kallona, muna hada ido yace “me nayi miki me zafi haka Diyam? Still akan wannan dan iskan yaron ne ko? Saboda kina sonsa ne yasa kika tsane ni irin haka ko?” Na yaye abin rufar nace “don’t bring Sadauki into this, babu ruwan Sadauki da tsakanin mu” yace “saboda an miki auren dole ne dani? It that it? Nima in kika tuna ba son auren nake yi ba lokacin da aka yishi” na girgiza kaina nace “ba dan an tilasta min aurenka bane ba Saghir. Su kansu wadanda suka tilasta min auren naka Inna da Alhaji ai ban rike su a zuciyata ba, babu komai a yanzu tsakanin mu sai kyautatawa da tausayi” yace “ni kuma fa Diyam? Menene nawa a ciki? Nasan ba kya sona but me yasa ba zaki bani dama ba?”+ Na mike tsaye ina jin zuciyata tana karyewa nace “you……raped……me” sai jikinsa yayi sanyi, nace “in ka manta da dakin nan yana magana zai tuna maka, na nuna gado na nace “here, anan ka dasa irin kiyayyar ka a zuciyata. I was only 14 years then, ranar baffana kwanansa 47 a kasa and you raped me”.1 Hawayene kawai suke bin fuskata, ya diririce “Diyam na baki hakuri ai, I was drunk, I wasn’t…..” Nace “shine excuse dinka? Giya ce excuse dinka? Bayan kuma har yau shanta kake yi? How can you raped me and then expect me to enjoy sexual relationships da kai? Tun ranar gini ai tun ranar zane. Ka dasa tsiron ƙinka a raina sannan kazo ka zuba masa taki when you killed my babies” sai kuka ya kwace min “you killed my babies and you left me to die a asibiti”. Sai ya taho da sauri ya jawo ni ya rungume ni, na fara ture shi amma yaki sakina har na hakura nayi ta kuka na a jikinsa. Yayi kissing forehead dina yace “Diyam ba zan iya dawo da baya ba, amma nayi alkawarin gyara gaba. Kome kike so zan yi miki Diyam in dai zan goge baya, banda saki because I can’t. I love you”. Knocking kofa akayi “Darling?” Fauziyya ta fada daga waje, na ture shi na hau kan gado na lulluba har kaina. Ina jinsa ya hawo yayi kissing Subay’a sannan ya fita gun darling din tasa. Da safe tun dan tashi da assuba ban koma ba, fuskata duk ta kumbura tayi min nauyi saboda kukan da nasha jiya da dare na tausayin kaina da rayuwata. Yaushe zanji dadin aure ne ni? Na gabatar da adduoi na kamar kullum, ina rokon Allah ya bani ikon cin wannan jarabawar da nake ciki ta auren Saghir, idan har zama da Saghir shine mafi alkhairi abu a rayuwata Allah ya rage min kiyayyar sa daga zuciyata. Sannan kuma nayi addu’ar Allah ya bamu zaman lafiya da amarya. Dalilin da yasa na yarda da auren Saghir shine, ina ganin yin auren nasa wata hanya ce ta rage wa ksina tarin zunubin da nake dauka na gudunsa da nake yi, at least in da wata matar nasan wannan responsibility din ya ragu daga kaina.3 Ina gamawa na sauka kitchen na fara fere dankali, sai ga murja nan ta shigo mu ka gaisa ta dauka ta fara tayani muna hirar mu, har muka gama na fara soyawa ita kuma tana soya kwai sai ga Saghir nan ya shigo, har yayi wanka yayi kwalliya, murja ta gaishe shi ta fita sai ya jawo stool ya zauna yana kallona “barka da assuba” nace ina kallon sa, yayi murmushi “good morning. Ina jin yunwa a bani abinci” nace “wai da so nake in hada muku kai da Fa’iza sai akai muku sama” yace “Fauziyya ba Fa’iza ba” na dafe kai “sorry. Fauziyya” ya girgiza kai “bacci take, ni kuma yinwa nake ji. Zubo min inci anan kawai” na zuba masa a plate na dora fork na mika masa, ya karba yace “naga Subay’a yau bacci take tayi” na hado masa tea na kawo masa na koma na cigaba da aikina shi kuma yana ci. Sai daya gama ya mike yazo bayana ya rungume ni yana shanshana gashina yace “am sorry Diyam kinji? I promise insha Allah zan saka ki murmushi more than yadda na saka ki kuka” ya juyo dani yace “da ace ina da dama da sai na bude nan” ya dora hannunsa a kirjina “na saka soyayya ta a ciki na rufe da kwado” na ture hannunsa ganin yana neman wuce gona da iri nace “stop it. Amarya tana sama tana jiranka” sai yayi murmushi kawai yace “zan fita. Sai na dawo”. Tare da murja muka gama aiyukan mu kamar kullum, sannan naje nayi wanka nayi wa Subay’a muka sauko muka fara cin abinci sai ga amarya ta sauko. Tana ta wani yayyatsina fuska, sai kawai na tsaya ina kallonta. Babu makeup din jiya, wannan ya sake fito da kamanninta sosai, sai nayi realizing ai na santa ma, tana daya daga cikin matan da suke zuwa har gida neman Saghir shi kuma yana ce min abokan aikin sa ne. Tazo ta zauna murja ta gaishe ta sai naga tana kallona irin kamar tana jira in gaisheta din nan tunda tana ganin ta girme ni. Nace “Subay’a ki gaishe da auntyn ki. Fa’iza ga Subay’a, koda yake nasan kin santa ma ai tun sanda kike zuwa” sai ta bini da kallo kawai. Na tashi na barta a dining nace “ga abinci nan Bismillah”3 STORY CONTINUES BELOW Na koma sama ina mamakin wannan rayuwar. Ni in nice Saghir ya zanyi in auri saura na, ai sabuwa zanso wadda ban taba testing ba, no wonder yazo yana shashshafa ni da sassafe.2 Rayuwa ta cigaba da tafiya, har Fauziyya tayi sati a gidan. A ranar ne kuma Saghir ya tubure. “Babu wata shekara, ban yarda na. Eh an baku dama kuyi kyautar kwana amma sai da amincewar mijin ni kuma nace ban amince ba” na daga gira ina kallonsa a raina ina cewa ‘zakayi saki reshe kama ganye kuwa’ a dole na na hakura na karbi kwana na. Dokin da yake sai daya sa naji tausayin Fauziyya. Ni kuma kamar an saukar min da bacin rai haka naji nayi zamana a dakina amma sai gashi ya taho. Ina game a waya ya karba ya ajiye yace “me kike so inyi miki ne Diyam? Kuka zanyi ne ko tsallen kwado?” Na juya masa baya nace “duk wanda ranka yafi so” sai ya hawo gadon ya fara yi min tausa. Yace “da gaske fa nake. Say it, anything, yanzu zaki ga anyi miki” na tashi na zauna yace “kudi kike so?” Sai ya dauko bandir din 500 notes ya ajiye min akan cinyata yace “ki shirya gobe in kaiki shopping ki sayi kayayyakin ku na mata, kayan kwalliya, jaka, takalmi anything” na mayar masa da kudin sa nace “ka sayi kayan abinci ka kai gidan Alhaji” ya dawo min da kudin yace “angama. Can we please go to my room? Kinga Subay’a tana nan”. Washegari kuwa ya fita dani, yayi ta lodo min kaya komai ya gani na mata sai ya dauka, “wannan zaiyi miki kyau, wannan ma yana da kyau, wannan zai dace dake” haka dai yayi ta fama. Muna dawowa gida muka tarar babu abinci, bata yi ba tunda girkina ne dan haka na shiga kitchen na dora da yake weekend ne Subay’a tana sama tare da Saghir suna kallo. Riga da wando ne a jikina kaina babu dankwali na daga gashina sama ina ta aiki na ina jin kida a waya ta sai naji kawai wani strange kamshi da ban sani ba, ina juyo wa sai naga wani mutum a tsaye a palo yana kallona muna hada ido sai cewa yayi “Fauziyya tana nan?” Ni kuwa na zunduma ihu ina kiran Saghir, sai kuwa gashi nan a guje ya sauko kafin mutumin ya fita. Ya damko shi yana tambayarsa lfy sai cewa yayi wai shi gurin Fauziyya yazo shi dan uwanta ne kuma ita tace mishi ya shigo. Ranar naga bala’i a gurin Saghir, daga Fauziyyan har bakon nata ya haɗa ya balbale su da fada daga baya ma ya haɗa har da maigadi wanda yayi ta faman rantsuwa a kan cewa shi bai san mutumin ya shigo ba. Ni dai na dauki yata muka koma sama nace ku kare kalau. Sai da daddare kuma Saghir yayi ta bani hakuri. Nace “duk wanda ya sayi rariya dama ai yasan zata zubar da ruwa. Tun da har ka auri yarinyar daka gama nema a waje ai kasan dole zata kawo maka maxa gida kaima. Duk abinda kayi ai kaima dole za’ayi maka. Haka rayuwa take” ya fahimci magana nake fada masa sai yace “kin san ai dalilin da yasa nayi auren nan ko? So nake kike kula dani yadda ya kamata sai nayi tunanin idan nayi aure kika ga wata tana kula dani kema zaki koya. Wannan shi yasa na auri Fauziyya saboda bana son in auri wata wadda itama bata iya din ba” a raina nace “oh, ita wannan ta iya din kenan” Rayuwa ta cigaba da tafiya. Saghir har mamaki yake bani yadda yake yi min, gabadayansa ya chanja kuma duk abinda nace to kuwa zaiyi shi sai dai in bance din ba. Na saka shi ya ke kai kayan abinci gidan su, sannan kuma na daina jin warin giya a tare dashi duk da ban tabbatar ko ya daina sha ba. Fauziyya bata da problem, tana dai da daga kai da nuna irin ta fini dinnan amma tunda ta fahimci yadda Saghir yake ji dani sai ta ja baya. Bamu fiya zama muyi hira ba kowa harkar gabansa yake yi. In ranar girkin tane tayi ta iyayi da rawar kai ni kuma in ranar girkina ne Saghir yayi ta rawar kafa, duk da dai ba koda yaushe yake samun abinda yake so din ba dan wani lokacin rufe kofa ta nake in kashe waya, watarana kuma in naje in bata rai har sai ya hakura ya rabu dani. A lokacin ne kuma bikin Rumaisa ya tashi, za’a hada ayi tare dana yaya Mukhtar. Lokacin muna 22 years, tana kuma final year dinta a jami’a.1 Bikin yana matsowa na tambayi Saghir sati biyu. Ya rike baki “sati biyu kuma Diyam? Kwana nawa za’ayi ana bikin da har zakiyi sati biyu?” Nace “nice fa babbar kawar amarya. In ina nan ta yaya zanyi shirye shirye?” Babu yadda zaiyi yace “shikenan” amma ina kira Mama na gaya mata zan taho tace “baki da hankali dama? Babu wani sati biyu da zaki zo kiyi, sati daya zakiyi shima kuma dan kina da abokiyar zama ne da ba zan barki ki taho ki barshi shi kadai ba” ranar har kuka nayi, I just needed a break from the house and from Saghir. Sai satin bikin sannan Saghir ya kaini gidan Mama. Ya kuma buga min warning “saura kuma ki shiga cikin yammata kuyi ta shiririta. Kinsan dai ke mai aure ce ko?” Nace “uhm” a raina ina mamakin wai yau Saghir ne yake kishi na. Ko yaushe zan fara nasa ni? Munsha bikin mu lafiya mun gama lafiya. Da muka je dinner naga yadda Rumaisa take nishadi da mijinta sai naji wani longing a zuciyata. I missed all this, ni banyi yammatanci ba kuma babu abinda zan adar na bikina. Ranar Lahadi muka kai amarya dakin ta. Litinin kuma na biyo su Inna muka dawo gida tunda satin da aka bani bai kare ba sai nan da kwana biyu. Muna zuwa naji Maman Iman tana soya wainar fulawa sai na aika Asma’u ta karbo min na zauna ina ci. Ina tsaka da ci sai kawai jin sallamar Sadauki mukayi wai ashe duk mondays yake zuwa ya gaishe da Inna. Na sunkuyar da kaina ina jin wainar ta fita daga raina har ya shigo ya gaishe da Inna da Mama sannan na dago na gaishe shi. Ya amsa yace “ya family?” Sai na kasa reply. Ya mike zai tafi Mama tace “oh Sadauki kaki aure har yanzu? Ko so kake ayi maka kidan tuzuru ne?” Ta tsaya yana shafa kansa, muka hada ido yace “an kusa ai mama insha Allah” Inna tace “alhamdulillah, ai gwara ayi din, aure ai shine cikar kamala da kimar mutum. An sami matar kenan” yace “eh, a can gida ne. A Maiduguri ne” sai naji wainar dana ci duk ta tattaro ta dawo makogwaro na, da sauri na mike na shiga toilet sai da na amayo duk wainar da naci. Sai dana gama sannan na zauna akan toilet seat na dafe kaina, ina jin jiri yana juyani duk da cewa a zaune nake. Nayi iyakacin kokari na gurin ganin cewa ban yi tunanin maganar da Sadauki ya fada a palo ba sannan na mike na wanke bakina da fuskata na fita, ina tunanin ya riga ya tafi amma ina fita sai na ganshi a tsaye yana kallona yace “ba kya jin dadi ashe? Allah ya sawake” na sunkuyar da kaina ciki ciki nace “ameen” sannan na wuce shi zan shiga cikin daki Inna tace “ba kiji Sadauki yana miki sannu ba? Shine kika wuce ba zaki amsa shi ba?” Na juyo nace “Inna nace masa ameen, ameen, ameen summa ameen,me kuma yake so ince masa” sai kawai yayi murmushi ya juya ya fita, inna kuma ta rufe ni da fada Mama tana taya ta, na zauna kawai nayi tagumi da hannu bibbiyu ina jinsu har suka gama sannan na zame na kwanta a gurin ina jin jikina kamar mai zazzaɓi har Mama tayi mana sallama ta tafi.4 Kwana biyun haka na kare su babu lafiya sosai, na so inki komawa saboda bana jin dadi amma Inna ta matsa Saghir ma kuma yace in ma zan zauna sai dai ya dauki Subay’a saboda makaranta ni kuma bana jin zan iya barin ta tare da Fauziyya dan nasan ba kunya ce ta ishe ta ba. Dan haka dole na shirya Saghir yazo muka tafi. A hanya ya kalleni yace “kin kara kiba, baki da lafiya amma kinyi kiba kin kara fari. What’s the secret?” Na bata rai nace “what secret kuma?” Yayi murmushi “wai cewa nayi ko Subay’a ce zata yi kani? It is about time, tayi girma da yawa” na juya kai ina kallon titi” I missed my period wannan watan, a lokacin bikin nan ya kamata inyi kuma banyi ba but that doesn’t mean anything tunda dama ina missing sometimes. Ina ganinsa yayi packing a bakery suka shiga shida Subay’a suka lodo kayan ciye ciye sannan muka tafi. A toilet da zan shiga wanka na tsaya ina kallon kaina a mirror, da gaske nayi girma na ciko ta koina musamman hips, abinda da bani dasu sai yanzu suke zuwa kuma. A raina nace “sai yanzu makerin budurci ya tuna dani” after I lost mine long time ago.5 Na fito daga wanka kenan ina shiryawa text ya shigo wayata. Na daga sai naga number din Sadauki, a raina nace “really? Ko dai batan kai yayi?” Sai kawai na ajiye wayar nayi shiryawa ta. Saghir ya shigo da magunguna a leda ya bani yana taba wuyana yace “gobe asibiti ya kamata muje in zazzabin nan bai tafi ba, test nake so ayi miki ma dan ni jikina yana bani ciki ne” nace “no fa ba wani ciki” amma a raina sai naji ina son ma ace cikin ne, I was really in need of love, kuma ina ganin haihuwa zata taimaka min sosai” na kwanta na dauki wayata yace “za’a fara karatun ko? Bana hana ba?” Nace “to me zanyi? Babu wani abin yi sai dai mutum yayi bacci ya tashi ya gyara gida yayi girki ya kuma komawa tayi bacci” ya danyi shiru yana kallona kamar mai tunani sai yace “kina son komawa school?” Nayi saurin kallonsa, ban taba tambaya ba saboda banyi tunanin zai bari ba amma raina yana so, ina son in zama abinda baffana ya ke kwadayi, nace “da gaske?” Ya daga kafada yace “why not? In dai zai faranta miki that’s what I will do” sai na kama tsalle ina murna shi kuma yana dariya sannan ya jawo ni yace “so? Me zaki karanta?” Nayi shiru ina tunani. Na tuna wani visiting da Sadauk yaje min school shida wani abokinsa and we talked about carrier, a lokaci nace musu bani da choice sai Sadauki yace later in life zan fahimci role din daya kamata inyi playing a rayuwa, but yet still, bani da choice a raina. Nace “me kake ganin ya kamata?” Yace “anything. Nasan ku mata da son harkar health, zaki iya yin nursing ko midwifery. In ma kuma medicine din kike so sai inyi wa Mr Abatcha magana ya hada ni da wani a samo miki admission” na ture shi ina jin raina ya baci nace “forget Mr Abatcha din nan” yace “why? Shi ya bani wannan shawarar ma fa, ya tambaye ni kina makaranta nace a’a sai yace ya kamata in saka ki. Kinga ai he will be willing to help” na girgiza kaina nace “na fasa karatun” sai kawai ya tsaya yana kallona da mamaki. Sai da zan kwanta na bude message din Sadauki “ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen” nayi tsaki na ajiye wayar na kwanta, sai kuma na tashi na sake karantawa sai kawai na kashe wayar na jawo drawer na saka ta nayi kwanciya ta.2 Da safe muna breakfast gabaki dayan mu har Fauziyya, ya ajiye ledar drugs din daya siyo min jiya yace “kina gama cin abinci zaki sha magani, dan naga ashe jiya baki sha ba kwata kwata” nace ” in tambaye ka mana Please” ya ajiye spoon din hannunsa yace “ina jin ki” nace “ya sunan ogan ku na office” ya bata rai yace “Mr Abatcha mana” na girgiza kai nace “sunan shi na gaskiya nake nufi. Like sunan da yake rubuta wa in an bukaci sunansa” ya danyi tunani yace “Engineer Aliyu Umar Abatcha” na gyada kai nace “ohh okay” yace “me yasa kika tambaya?” Nace “a bikin nan ne naji ana zancen wani, I tot shine ashe bashi bane ba” yayi murmushi ya fara praising Mr Abatcha “yana da kirki sosai, na girme shi amma mi gaskiya he is my role model. He is very smart and intelligent. Kuma yana sona. Kunga yadda yake korar mutane kuwa duk wanda yaga wasa yake yi ba aiki ba yanzu zai tura maka quiry amma ni ko sau daya bai taba bani ba. Diyam kin tuna sanda ya tura ni Germany? Sai da naje na fahimci ya tura ni ne kawai dan in huta ashe already ya riga yayi sighing contract din. Sai dan workshop dana ringa zuwa kawai” na girgiza kaina a raina nace ‘ya tura ka ne dan ya samu damar zuba kaji a gidan ku’.14 Munje asibiti anyi min pt and it came back positive. Sai naji dadi, maybe wannan haihuwar ta zamo min silar gyaruwar lamura na. Saghir kam doki har a gaban Fauziyya, ya bawa Subay’a labarin zata yi sister ko brother ita ma tayi ta murna. And yana fita sai gashi da sabuwar waya, yace “wannan tsohuwar wayar taki dai ya kamata ki ajiye ta haka” na karba nayi masa godiya sai kuma ya tambaye ni in akwai abinda nake so. Na zauna kusa dashi nace “so nake kayi wa su Murja aure” ya bata rai, nace “Please, auren suke so wallahi kuma Alhaji bashi da halin yi musu to waye zaiyi musu in ba kai ba? Su ba karatu ba, su ba aure ba me kake tunanin xasu yi?” Yana kallona yace “sai in kinyi min alkawarin kema zaki koma school” nace “sai in kayi min alkawarin zaka daina shan giya” ya daga kafada “na daina fa” na tsare shi da ido sai yace “na kusa dainawa. Seriously na kwana biyu rabo na da ita” nace “mata fa?” Yace “na daina wannan tunda na kara aure ai” sai kuma ya jawo ni yace “tell me, kishi kike yi?” Nace “Saghir ko bana sonka, kai mijina ne, kuma uban yayana, ba zan so kuma yayana su tashi suga babansu da wadannan halayyar ba”. Yayi murmushi yace “am getting there”.1 And two days after that. Ina ta aiyukan gyaran gidana, da yake ni ban damu ba ko aikina ne ko na Fauziyya ni in dai na tashi zan gyara gida saboda bana son kazanta, it irritates me, ina mopping kasa Saghir ya leko ta stairs yace min “ina tsohuwar wayar kine? Naga har yau baki kunna sabuwar ba” nace “tana bedside drawer ta” na cigaba da aikina. Na gama naje na wanke mop, na dawo ina saka turaren wuta Fauziyya ta sauko ta kunna tv ta kwanta tana kallo. Sai Saghir ya sauko da wayata a hannunsa, I looked at his face and I felt something knot in my stomach. Ya nuna min wayar “waye wannan?” Fauziyya ta mike zaune tana kallon mu. Message na gani a jikin wayar “ya jikin? Allah ya kara afuwa ameen” na girgiza kaina nace “duba ni ake yi, what’s there?” Sai yayi scrolling sama, tun message din farko. “Third option. Kazo a baka hakurin da kake so” “tomorrow evening. Gidan Baffa” “ina yiwa Asma’u godiyar kyautar da aka yi mata. Allah ya kara arziki mai albarka” “You are welcome”. Na daga kafada, ni banga abin tayar da hankali a cikin maganganun mu ba. Ya sake cewa “waye wannan Diyam? Sadauki ne ko? Amana ta kike ci ko Diyam? Wato abinda yasa kike guduna saboda kina samu a wani wajen ko? I always tot, yarinyar nan sai kace dutse, ashe kina da tap din da kike karbar rabonki a gurinsa”.1 Na zaro ido “wanne irin magana kake yi? How can You even accuse me of that. Menene a cikin messages din nan da zasu saka har ka fadi haka? Yes, munyi magana sanda suke case da Alhaji Babba kuma yayi wa Asma’u kyauta na yi mata godiya. Menene a ciki?” Yace “to uban wanene ya gaya masa baki da lafiya har yake duba ki?” Nace “a gida ya same ni yaje gaida Inna yaga bani da lafiya. I don’t even know me yasa nake defending kaina. Dan kana yin abu sai ka dauka kowa ma yi yake yi?”. A girgiza kai idonsa jawur yace “am going to trace him. Am going to enter his number into my phone and call him. In na gano inda yake kuma wallahi sai na daure shi. Sai yasan matata ya taba” ya juya da sauri zai koma sama sai nayi saurin rike rigarsa “Saghir ka tsaya ka saurare ni. Wallahi ba abinda kake tunani bane ba” ya juyo a fusace ya sauke min mari a fuskata, kafin inyi wani abu ya sake sauke min wani a same side. Na rine fuskata ina jin jini yana bin hancina, ganina yayi dusu dusu. Amma still na rike rigarsa i a girgiza masa kaina, ta gefen idona na hango Fauziyya tana dariya, sai ya warce rigarsa ya hankada ni da karfi na fadi, unluckily sai cikina ya bugu da kafar bene, na mirgina gefe ina rike marata da hannun bibbiyu shi kuma yayi sama da sauri ba tare daya kalli inda nake ba.2 Na sake kokarin mikewa amma marata ta rike kam sai da kyar na daddafa stairs na mike, tunani na daya shine in Saghir yayi dialing number din Sadauki a wayarsa zaiga Mr Abatcha. And that can destroy Sadauki’s reputation a gurin aikinsa. Na juya na kalli Fauziyya da take zaune tana kallo na da murmushi a fuskarta nace “get up from my chair. Munafuka” Sai na kama bene ina tafiya a hankali nabi Saghir a baya. Ina hawa sama yana fitowa daga dakinsa hannayensa da waya ta da kuma tashi. Nace “ka saurare ni Saghir” bai ce komai ba ya fara daddanna wayar sa. A lokacin mara ta tayi wata irin murdawar da sai da na kai kan guiwowina na runtse idona, sai ji nayi yace “Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?”Bature yace “when the going gets tough, only the tough gets going” hakane? It is either you get tough ko kuma kana ji kana gani a tafi a barka. “Mr Abatcha? Menene hadin Sadauki da Mr Abatcha?” Na dafa bango na mike ina kallonsa kawai. Babu abinda zance masa a yanzu, dama kokari na shine inyi preventing dinsa from finding out kuma ya riga yayi. So magana ta kare kuma.+ Ya zuba min ido, “magana nake miki Diyam? Sadauki kike texting ko Mr Abatcha” kallon da nake masa yasa ya tsaya shima yana kallona and then the realization hits him. I saw lokacin da yanayin fuskarsa gaba-daya ya chanza, ya saki wayoyin duk guda biyun suka zube a kasa. His whole world came crashing down on him. “Mr Abatcha? Mr Abatcha shine Sadauki? When? How?” Ya saka hannayensa duk biyun acikin kansa ya fara zagaya palon da sauri har wani gumi ne yake karyo masa. Idonsa ya ciko da kwalla. Ya taho da sauri ya tsaya a gaba na “you? You were playing me all these years? All these years kina tare dashi dama? My God!” Ya sake dora hannu aka jikinsa har rawa yake sai ya dafa kujera yana mayar da numfashi. Ya jima a haka sannan ya juyo yana kallona sannan yace “ke kika saka shi ya bani aiki ko? I remember ke kika ce inje in nemi aiki. Ke kika saka ya dauke ni without even looking at my credentials saboda ku kasance tare ko? Saboda kuyi controlling dina ko? Is that it?” Na girgiza kai kawai amma kafin inyi magana yace “kar kice min komai, ko inzo in babballaki anan. My God, wannan wanne irin cin amana ne, hatta sunan da zan sakawa yata shi ya zaba min” sai ya fara dukan kansa da hannunsa yana cewa “wawa, dolo, soko, dakiki”.3 Sai kuma ya zauna akan kujera ya dafe kansa da hannayensa yana girgiza kai. Yace “wato tare kukayi planning din abinda aka yiwa Alhaji ko? Shi yasa ya tura ni tafiya a lokacin. Da aka gayamin sharadan daya saka sai da nayi tunanin me yasa a ciki bai ce in sake ki ya aura ba, ashe baya bukatar wannan tunda already yana tare da ke”. Kamar wuka haka maganganun Saghir suke huda ni. Wannan accusations din yana daya daga cikin abinda na kasa mantawa har yau. Komai zan gaya masa ba zai fahimta ba, amma duk da haka zan gaya masa ruwansa ne kuma in ya dauka in kuma bai dauka ba matsalar sa. I was beyond caring a lokacin. Nace “sanda Sadauki ya dauke ka aiki bansan shi bane ba, bai taba contacting dina ba, I had no idea yana ina ma har sai ranar da kuka shirya masa party, a ranar nasan shine oganka. Bansan dalilin sa na daukan ka aiki ba, zata iya yiwuwa ya dauke kane kamar kowa, wannan shi yasa ban gaya maka ba tunda ina ganin fadin bashi da amfani. Bamu taba magana ni da Sadauki ba in banda sanda Alhaji ya tura ni gurinsa, a lokacin ma yayi shutting dina out dan haka babu maganar da muka yi sai wadda takaini. Bamu taba waya da Sadauki ba. Texts din da ka gani sune a tsakanin mu. Wannan shine gaskiyar magana” na juya zan bar gurin naji kafafuwana sun rike tun daga cinyoyi na zuwa marata suna min wata irin suka. Nace “Saghir?” Bai amsa ba sai cewa yayi “karki gaya min karyar banza. Wallahi bai isa ba. Baku isa ba daga ke har shi kuyi min wannan cin mutuncin. Sai na nuna masa dukiyar sa ta banza ce wallahi sai ya raina kansa. I will destroy him ko zan rasa raina wallahi.” Sai ya shiga daki ya dauko key din mota, zai wuce ni na rike rigarsa nace “Saghir bani da lafiya” ya kwace rigarsa yace “zaki warke ne ma, munafuka” ya fice ya barni without another look at my side. Na daga rigata naga jini yana bin kafata a dai dai lokacin dana ji tashin motarsa. And I realized something, na rasa cikin jikina kamar yadda na rasa twins dina. And there and then na yanke shawara, na gama auren Saghir. Nayi kokarin motsawa daga gurin na kasa. Ina so in taimaki kaina kuma ina son in warning Sadauki dan ban san me Saghir zaiyi ba daya fita amma na kasa zuwa ina waya ta take yashe a kofar dakin Saghir. Kafafuwana tamkar sun daina aiki haka nake jinsu sai jini ne yake biyo su zuwa kan tiles. Option dina daya, Fauziyya. Na fara kiranta da dan abinda ya sauwaka daga murya ta. “Fauziyya, Fauziyya” amma shiru, ban tabbatar ta jini ba ko a’a saboda nasan kallo takeyi. Na jima a haka sannan na jiyo hawowarta sama. Tana shigowa palon ta tsaya tana kallo na yadda na hada gumi ga busashshen jini a hancina ga kuma jinin da yake kwance a kasa na sai ta saki purse din hannunta ta taho da sauri “Halima? Me ya same ki haka?” Cikina kawai na iya na nuna mata, ta kama ni ta kwantar a gurin sannan ta koma ta dauko jakarta data yar ta dauko wayarta ta fara kira. Jikina ya bani Saghir take kira sai kuwa mukaji wayar tasa tana kara a kusa da tawa. Ta ajiye wayar tace min “ina ya tafi?” Kaina kawai na girgiza mata, sai tace “ko miscarriage kike yi ne? Ko asibiti zamu je?” Na gyada mata kai sai ta kama ni zuwa toilet dina, ta taimaka min na wanke jiki na amma fa jini zuba yake dan pad ma ba zata rike shiba sai face towel ta bani na saka muka tafi. She half carried my down the stairs sannan ta saka mai gadi ya samo mana abin hawa muka tafi asibiti. Wannan yasa ba zan taba mantawa da Fauziyya ba.1 STORY CONTINUES BELOW Bayan fitar Saghir daga gidansa ya shiga motarsa ransa a mugun bace, bai taba jin bacin rai irin na ranar ba danji yake kamar ya hada ni da Sadauki ya saka mana wuta mu kone. Sai kawai ya bude aljihun motarsa ya dauko wata tsohuwar ajjiyar sa da kullum in ya dauko zai sha sai ya tuna yayi wa Diyam alkawarin ya daina sha. But yau Diyam din ce da kanta ta bata masa dan haka with vengeance ya shanye kwalbar gabaki dayan ta sannan ya kunna motar ya fita daga gidan ya tunkari kamfanin Abatcha Motors. Sadauki yana cikin meeting da ma’aikatan sa, meeting din da ba’a ko gayyaci Saghir ba sai assistant dinsa. Sadauki yana tsaka da yin bayanin sababbin dokokin da yake kafawa saboda ma’aikatan da suke incompetent da irin hukuncin da za’a ke dauka akan duk mai karya doka sai ga Saghir ya banko kofa ya shigo, duk suka juya suna kallonsa ya taho yana tangadi ya nuna Sadauki yace “munafiki. Allah ya tona asirin ka yau” gaba-daya gurin suka mike, wasu daga ciki suka mike suka yo kan Saghir amma sai Sadauki ya dakatar dasu da hannu yace “ku rabu dashi” ya gyara zama ya kalli Saghir yace “menene yake tafe da kai?” Saghir ya nuna Sadauki yana kallon mutanen gurin yace “wannan da kuke gani is not who he is saying he is. Ba sunan shi Abatcha ba sunan shi Sadauki kuma Sadauki shine Mr Abatcha kuma shine saurayin Diyam kuma Diyam kullum sai ta fadi sunan Sadauki ashe shine Mr Abatcha. Shine kuma ya bani aiki sannan ya saka wa yata suna ya siya mata ragon suna. Yazo kuma ya kai Alhaji kara ya karbi rabin gidan sa yayi gidan gona. Sai yau na ga message din sa a wayarta sannan na gane ashe shine” Wani a gurin yace “do you understand cewa baka making sense kwata kwata?” Sauran mutanen suka kwashe da dariya. Sadauki yayi ajjiyar zuciya ya nuna Saghir yace “Ladies and gentlemen, this is an example of one of the effects of shaye shaye” sai ya kalli security yace “get him out of my sight”.1 A asibiti akayi confirming fitar cikina. Amma suka ce bai gama fita ba. Sai suka bani wani tablet suka ce zai fitar da sauran. Muna can lokacin tashin su Subay’a daga school yayi, Fauziyya ta koma gida ta dauko ta ta kai makotan mu sannan ta dawo gurina.2 Har muka koma gida gurin magrib Saghir bai dawo ba. Na sha tablet din sannan na kwanta, Subay’a tana ta jera min sannu. Na sake trying number din Sadauki bata shiga, duk da dai nasan koma menene zai faru ya riga ya faru. Na kwanta ina ta jiran shigowar Saghir amma shiru har bacci ya dauke ni banji ya shigo gidan ba. Cikin dare wani azababben ciwon mara ya tashe ni, ji nayi kamar raina zai fita gashi daga ni sai Subay’a a daki. Jini guda guda haka ya rinka fita daga jikina. Ban yi bacci ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah. Cikin bacci naji Fauziyya ta shigo dakin tana tashin Subay’a, sai kuma tace min “Daddy fa bai kwana gidan nan ba. Ga wayarsa kuma tana nan. Na kira Kabiru kuma yace basa tare. Ko zaki kira gidan Alhaji kiji ko yana can?” Nace mata to kawai, amma ba wanda na kira. Ita ta shirya Subay’a ta mika ta school sannan ta dawo ta kawo min tea. Zuwa 12 na dan warware, sai dai weakness sannan kana kallona zaka ga nayi pale saboda ba karamin jini na zubar ba. Na tashi nayi wanka, na fito na shirya sai na tsaya ina kallon kaina a mirror. Na dora hannuna akan marata ina tabbatar wa kaina cewa it is gone. It is dead before it even begins living. It is going to be the last thing da zanyi loosing a sanadiyar auren Saghir. Ina saka kaya na sai na jawo akwati na fara zuba kayana dana Subay’a. Ina cikin zubawa Fauziyya ta shigo, yanayin ta kamar a rude tace “Halima, kizo inji Kabiru” ta fita na saka hijab dina na bita a baya. Yana tsaye a bakin kofa ya kalle mu yace “Saghir yana station tun jiya. Bansan me ya faru ba amma ance security din gurin aikinsa ne suka kama shi suka damka shi a hannun police. Ban san menene charges din ba. Nayi kokarin yin bail dinsa sun hana ni, sunce order ce direct from the commissioner of police cewa kar a bayar da bail dinsa”. Fauziyya ta zame ta zauna. Ni kuma sai na juya nayi hanyar sama. Kabir yace “Diyam ki kira gida ki fada. Maybe Alhaji yana da wani a sama wanda zai saka a fito dashi” na gyada masa kai kawai na wuce. Ina zuwa daki na karasa hada kayana na fito na wuce Fauziyya a palo ta zabga tagumi na je na dauko Subay’a na dawo na sake wuceta. Na shirya Subay’a sannan muka sauko tare da akwatin kayan mu. Fauziyya ta tashi tsaye tana kallon mu tace “ina zuwa haka?” Nace “gida” bata kuma cewa komai ba har muka fita. Mai gadi yayi min sannu da jiki sannan ya taya mu da kaya muka tari abin hawa muka tafi. Inna tana ganina da akwati tace “lafiya” na ajiye kayan hannu na sannan na gaishe ta, bata amsa ba tace “lfy nace? Lafiya na ganki da tsakar ranar nan da akwati?” Na sunkuyar da kaina nace “Inna na gama auren Saghir” ta saka salati, “shi Saghir din ne ya turo ki gida ko kuma ke kika yi ra’ayin kin gama aurensa kika taho gida? Dama igiyar auren a hannun ki take?” Na girgiza kai nace “Inna Saghir fa….” Tace “Saghir me? Saghir din yanzu ai bana da bane ba. Kika zauna da wancan Saghir din ma ballantana wannan da kowa ya tabbatar ya chanja. Dama tun randa Sadauki yazo nan da maganar aurensa naga yadda kikayi nasan in ba sa’a akayi ba sai kin fito da wata maganar kuma” naji hawaye ya fara bin fuskata, nace “Inna ba a kan Sadauki na taho gida ba, tsakani na da Saghir ne, ni ba zan koma gidan sa ba Inna. Dan Allah karki mayar dani” tace “ina Saghir din?” Na share hawaye na nace “yana police station” ta sake wani salatin “me ya faru? Me yake yi a can?” Nace “Sadauki ne ya rufe shi.” Ta mike tace “kuma kika ce ba’a kan Sadauki bane ba. kira min Sadauki yanzu yanzun nan” nace “na baro wayata a can gidan. Kuma ma ba daukan wayata yake yi ba” ta kwalla kiran Asma’u. Tana zuwa tace mata “kira min Sadauki da wayarki” Asma’u tana kallo na da alamar tambaya ta dauko wayarta ta danna kira ta saka a speaker. Har ta gama ringing bai dauka ba sannan ta sake kira shima shiru. Sai kuma gashi ya kira. Ta dauka tasa a speaker naji muryar sa yace “Yar Asama ya akayi?” Tace “Inna ce tace in kira ka. Gata” Inna tace “Sadauki me ya hada ka da mijin Diyam har ka rufe shi?” Yayi shiru, ni kaina sai da nayi mamakin karfin halin Inna. Sai ta ce “tazo gida yanzu tace wai ka kama Saghir ka rufe shi” ya sake yin shiru sannan yace “ita Diyam din ce ta kawo kara ta akan na rufe mata miji?” Nayi saurin girgiza kai zanyi magana Inna ta harare ni tace “eh fa, shine nayi mamaki nace me ya hada ku?” Yace “a ce wa Diyam tayi hakuri, za’a fito mata da mijinta gobe in Allah ya kai mu” sai ya katse wayar. Na saka sabon kuka “Inna yanzu haushi na fa zaiji yace na kawo kararsa” Inna tace “na sani ai. Haka nake so saboda ki fita harkarsa ki barshi yayi aurensa kema ki zauna ki rike naki auren”.Inna taga ta kanta a gurin jama’a shekaran jiya. Duk inda na shiga kowa kokawa yake yi da abinda Inna tayi. But to me, laifin Inna a yanzu guda daya ne, rashin sauraron Diyam kafin ta yanke hukunci bawai hada Diyam da tayi da Sadauki ba. Wannan kuma shine halin kusan 70% na northern mothers. Kullum su dai burinsu shine yarsu ta zauna a gidan mijinta kar ta kashe auren ta dawo gida ta zauna a gabansu. But what if the marriage is not working? What if she is buying her ticket to hell fire instead of paradise a cikin auren?10 And Saghir, Saghir yayi laifuffuka da dama a baya but a yanzu laifinsa shine dukan Diyam. Nothing, nothing gives a husband the right to hit his wife. Duk kuma namijin da yake dukan matarsa to ba mijin aure bane ba, ballantana mata mai ciki? Hmmm5 Then Sadauki. Na lura Sadauki ya zama shafaffe da mai a gurin readers, sam basa ganin laifinsa komai yayi daidai ne dan ina jin few mutane ne naga sunyi comment akan laifin Sadauki. Sadauki is rather rude and very authoritative. Ba shi da right din da zai sa a rufe Saghir, yes Saghir yazo gurin aiki drunk kuma ya fadi maganganu wadanda babu wanda ya gane in banda shi Sadauki da ake magana a kansa. Abinda ya kamata Sadauki yayi shine yasa ka security su fitar dashi waje, in ya ga dama ya hada masa da takardar kora daga aiki. But bashi da right din kaishi station a rufe shi kuma wai without bail, saboda yana da kudi?15 Let’s continue Na rufe fuskata ina girgiza kaina da sauri. “Inna kar kiyi min haka dan Allah. Inna ki tsaya ki saurare ni ki fahimce ni kar ki mayar dani gidan Saghir in na koma wallahi mutuwa zanyi” tace “da baki mutu ba shekara da shekaru sai yanzu da Sadauki zaiyi aure shine zaki mutu?” Sai ta mike zata shige daki nima na mike da sauri na rike hannunta da hannu na daya dayan kuma na daga mara ta da shi nace “Inna nayi bari jiya” sai ta juyo tana kallo na ido a bude, ta taba fuskata da hannunta tace “bari Diyam? Ya akayi kika san bari ne kinje asibiti?” Na gyada kaina nace “naje Inna, su suka tabbatar min da cikin jikina ya fita Inna. Saghir ya fitar min dashi” ta dan bata rai cikin rashin fahimta tace “Saghir? Ta yaya Saghir zai fitar miki da ciki?” Nace “dukana yayi Inna, dukana Saghir yayi ya buga ni da jikin bene ya kashe min baby na, kamar yadda shaye shayensa ya jawo mutuwar yan biyu”. Sai ta kama hannuna muka zauna tace “Diyam, kin tabbatar abinda kike gaya min gaskiya ne? Me ya hada ki da Saghir har ya dake ki haka?” Na shafa fuskata sai itama ta saka hannu ta taba fuskar tawa, side din da Saghir ya mare ni, na dan yamutsa fuska alamar zafi sai naga idonta ya kawo kwalla amma sai tayi sauri ta mayar da ita. Tace “me ya haɗa ku nace” sai na bata labarin messages din Sadauki. Tana girgiza kai tace “me yasa? Me yasa zaki ajiye sakon Sadauki a wayar ki har mijinki ya gani bayan kuma kinsan yasan tsakanin ki da Sadaukin” nace “inna na fada miki menene a cikin sakon nan, babu wata kalma ko daya data kauce hanya a ciki kuma in na goge su ai kamar bani da gaskiya kenan. Ina son Sadauki na sani, amma Allah ne shaidata cewa ko sau daya ban taba tunanin yin sabon Allah da Sadauki ba. Kuma ke kece shaida, Sadaukin nan tamkar dodanniya haka nake a gurinsa, ko kallon inda nake baya yi. Shi dai ya zarge ni ne saboda shi din yasan shi mai laifi ne, abinda yake cikin tasa wayar idanuwa ma ba zasu iya gani ballantana hankali ya dauka” Inna tace “akan wannan maganar ne Sadauki ya sa aka kama shi?” Nace “ni ban sani ba, amma ina jin akanta din ne. Ya dai fita a fusace yace sai ya wulakanta Sadauki, tun daga nan kuma bai dawo ba sai da safe Kabiru abokinsa yazo yace mana yana hannun yan sanda” Inna tayi shiru tana tunani sannan tace “yace za’a sake shi gobe, Allah ya kaimu goben, ya fito sai yazo yayi bayanin dalilin da yasa ya dake ki. Kar ki goge messages din ki barsu saboda shaida a gani cewa babu abin duka a cikin su”.5 Sai naji raina yayi min wani irin dadi, babu abinda yafi dadi irin a fahimce ka babu kuma abinda yafi ciwo irin ace kana da gaskiya amma a hana ka tsarawa ballantana a fahimce ka. Ina ma dai iyaye zasu ke bawa yayansu wannan damar? A fahimci kowa sai a hada both parties ayi wa kowa fada dai dai da laifinsa? Ba wai ace da mace ki komaki cigaba da hakuri ba tare da ko murya an daga wa shi namijin da yake maltreating dinta ba, wannan tamkar ana ce masa ka cigaba da maltreating dinta ne.1 STORY CONTINUES BELOW Amma dana fara tunanin abinda zai iya faruwa gobe sai naji duk hankali na ya kuma tashi. Nasan halin Saghir sosai nasan zai iya jujjuya maganar gabaki daya ta koma laifina kuma na tabbatar iyayen mu musamman mazan bayansa zasu bi, musamman in nayi la’akari da irin kiyayyar su ga Sadauki, da kuma soyayyar da suka san ina yiwa Sadauki, tabbas komai Saghir ya gaya musu yarda zasuyi. Ni kuma ba yardar su ko rashin yardar su ce problem dina ba a’a tirsasani in koma gidan Saghir shine problem dina. Na gama auren Saghir, ba zan koma gidan Saghir ba. Wannan is my decision. Ni a yanzu auren Sadauki ko rashin auren Sadauki ko shi kansa Sadaukin basa gabana. Abinda yake gabana shine rabuwa da Saghir.1 Inna tace inje in kwanta in huta a daki. Na tashi na shiga ina jin Asma’u tane cewa “Inna amma ba za’a mayar da Adda gidan can ba ko?” Inna tayi shiru bata ce komai ba. Na kwanta kawai sai hawaye ya fara zubo min ina lissafin abin da zanyi in akace sai na koma. A ciki har da guduwa na lissafa amma inna gudu inje ina? Yan uwan uwata dai sune yan uwan ubana sune kuma yan uwan mijina. Sai kawai na yanke shawarar in aka matsa min akan in koma gidan Saghir to zan gudu gurin Sadauki, inje in tuna masa da amanar da Baffa ya bar masa ta kula damu, sannan in tuna masa cewa ni ma fa yar Baffa ce ba wai Asma’u ce kadai yarsa ba. In kuma roke shi daya shige min gaba in kai karar Saghir court alkali ya raba auren mu. Yes, wannan shine abinda zanyi.3 Ina kwance Subay’a ta shigo ta kwanta a kusa dani. Sai naji tana sheshshekar kuka, na jiyo nace “Subay’a? Lafiya kike kuka? Wani gurin ne yake yi miki ciwo?” Sai tace “Mommy ki daina kuka kema” na jawo ta jikina nace “ba kuka nake ba Subay’a ido nane yake min ciwo” tace “kuka kike yi ai na sani, naji kuma aunty Fauziyya dazu da tana shirya ni zan tafi school tana waya tana cewa kunyi faɗa da Daddy shine ya dake ki kike kuka, kuma naji dazu kina fada wa Inna Daddy ya dake ki” sai na kasa ce mata komai, lallai yara duk abinda ake yi a gabansu suna sane. Ta goge min fuskata tace “kiyi hakuri Mommy, in Daddy ya dawo zance masa kar ya kara dukan ki”.5 Sai na dage da addu’a sosai ina rokon Allah ya shiga lamari na ya kawo min agaji. Dan nasan in na koma gidan Saghir to ba rayuwata ta duniya ba har ta lahirar ma tangadi take yi, two zero kenan. Saboda ni dai nasan a rayuwar auren da nayi da Saghir a baya ba karamin zunubi na lodar wa kaina ba ballantana in na koma nasan bazan iya yi masa koda rabin biyayyar da nayi masa ada ba. In kuma haka ta faru to nice a ruwa dan Ubangiji babu ruwansa, laifina daban a gurinsa laifin Saghir shima daban. Kowa littafin sa daban. Dan haka sai na kwana ina kaiwa Allah kuka na.1 Washegari tun safe nake saka ran wani abu ya faru amma shiru, ko ya naji anyi motsi sai in tsorata in dauka Saghir ne zai shigo gidan. In naji wayar Inna tayi kara kuwa dai inji kamar zan saki fitsari a wando saboda tsoron ko kira ne a kaina amma shiru. Da safe Inna tayi min farfesun hanta mai romo tace in cinye, na cuccusa da kyar naci dan bani da appetite sam, sai kuma ta fita da kanta taje kasuwa sai naga tayo cefanen green vegetables kala-kala tazo ta hada min miyar ganye mai naman rago ta sani naci da tuwon shinkafa tace zai kara min jini. Daga ni har ita babu wanda yayi zancen Saghir amma dai nasan duk maganar tana ran mu. Shiru shiru har dare. Har gayi ya waye wani daren ya sake yi. Har aka kwana biyu sannan aka kwana uku, hudu biyar, sati ya zagayo shiru. A ranar ne Inna tace “to ni ko Alhaji Babba zan kira ne akan maganar Saghir din nan ne? Kar dai ba’a sake shi ba har yau. Ni kuma bana son in sake kiran Sadauki kar yaga kamar ina damunsa akan sirikina yaji babu dadi” Asma’u tace “dan Allah Inna ki rabu dasu, yayi ta zama mana a cell din wa ya damu ne wai? Itama yanzu ba gashi ta samu kina kulawa da ita ba da yana nan kuwa ba vari zaiyi kije gidan ki kula da ita ba kuma ba lallai bane ya barta tazo nan” Inna tace “Asma’u kenan, ke yarinya ce ba zaki gane ba. Maganar nan fa tana kara jimawa ne tana kara karfi. Dole ya kamata in bincika inji halin da ake ciki” sai ta dauko waya ta kira Hajiya Yalwati, suka gaisa sai take tamayarta ko taga Saghir kuwa? Nan take Hajiya Yalwati tace “dama yanzu nake niyyar in saka kati in kira ki. Me ya hada Saghir da Diyam da tsohon saurayin ta kuma? Tun jiya naji ana ta maganar a gidan nan ni dai ba’a yi min cikakken bayani ba amma na fahimci kamar ko sunyi rigima ne harda su yan sanda” inna tace “Saghir din yazo gidan kenan” Hajiya Yalwati tace “yazo gidan fa, jiya nan ya kusan wuni sai dare ya tafi”. Tunda suka gama wayar Inna ta zauna ta zabga tagumi, sai ajima tayi ajjiyar zuciya ta sake wani ragumin duk tabi ta damu kanta. Nima kuma na damu din amma ba kamar inna ba, ni damuwata shine bansan zurfin sharrin da Saghir yake shirya min ba. Muna zaune kuwa, Asma’u ta kawo mana lunch kenan sai gasu sunyi sallama. Na ajiye spoon din abincin kawai na fara ambaton Allah dan ji nayi zuciyata kamar ta dawo wuyana. Daya bayan daya suka shigo palo, Alhaji Babba, Kawu Isa, sai kuma Saghir. Inna ta tashi tana musu sannu da zuwa babu wanda ya amsa ta suka zauna. Ta gaishe su babu wanda ya amsa mata, dan haka sai naja bakina naji shiru ban gaishe su ba kaina a kasa. Kawu Isa ne yayi magana “gamu munzo Amina, mun sauke girman mu mu da muke manya munzo mun same ki tunda haka kike so. Kin bamu kunya Amina, Allah yaji kan hardo da inno, Allah yaso ba zasu ga wannan rana ba ba zasu ga wannan bakin ciki ba na abinda suka raina suka rike kamar abinda suka haifa kuma yazo yana yi musu bita da kulli. Amina yanzu ke wato duniya ta bude miki ido ko? Yanzu wato kudi sunfi miki yan uwanki ko?” Nace “Kawu….” Inna ta daga min hannu tace “kar ki sake inji bakin ki” sai ta juya tace “hamma kudi ba komai bane ba akan zumunci da halacci. Amma yanzu ni me nayi da har kake cewa na zabi kudi?” Alhaji Babba yace “me kika yi?” Ya nuna ni yace “wannan bata gaya miki abinda ya faru ba?” Inna tace “ta gaya min, ta gaya min komai har dukan da Saghir yayi mata da barin da tayi ta gaya min” Kawu yace “kuma ta gaya miki labarin cin amanar Saghir din da take yi tare da wannan tsinannen yaron? Ko kuma dama kin riga kinsan wannan labarin?” Inna ta girgiza kai tace “shi Saghir din ne yace Diyam tana cin amanar sa da Sadauki? Zai iya rantsewa da Allah cewa ya gansu suna cin amanar sa? Ko kuma zai iya rantsewa cewa sakon daya gani a wayarta ya nuna wata alama na cewa suna cin amanar sa” Alhaji Babba ya dubi Kawu Isa yace “kaji ba? Na gaya maka dama ta sani sarai. Da hadin bakinta ne akeyi komai. Ba dai yaron yayi kudi ba? Ni kuma na talauce” Inna tace “in kuka ce haka baku kyauta min ba. Yaron nan, duk cikin ku babu wanda ya kuntata rayuwarsa kamar ni. Tun yana cikin zanin goyonsa bana binsa da komai sai harara da muguwar magana amma me? Shine ya dauke ni a lokacin da Saghir ya watsar dani. Ya baku labari? Naje gidansa duba Diyam ya kore mu ni da Asma’u cikin dare ana ruwan sama. Badan Allah ya bude mu ba badan Allah ya kawo mana Sadauki ya taimake mu ba da yanzu babu Asma’u a duniya. Sadauki ne ya taimaka mana. Tun daga ranar kuma nayi nadama mai tsanani na kuma yi alkawarin yin rikonsa tamkar yadda zanyi rikon dana. Wannan ne yasa tun ranar da Diyam tazo min da maganar na kira shi nace ya sa a saki Saghir, sannan kuma na zauna ina jiran shi Saghir din yazo yayi min nasa bayanin inji” Kawu Isa yace “to mu yaje yayi mana bayani, ya gaya mana komai har yadda shekara da shekaru Diyam take tare da tsohon saurayinta, ta saka ya bashi aiki dan suji dadin cin amanar sa, yanzu kuma mun kuma tabbatar cewa duk abinda ake yi da sanin ki Amina. Wato ke naki salon sakayyar kenan a bisa dukkan alkhairan mu a gareki ke da yayanki. To gasu nan mun bar miki su, gaki nan ga duniyar nan ga kuma Sadauki nan. Ba dai kudi ba? Kamar yadda nawa ya kare haka nasa shima zasu kare sai kuma muga wanne sarkin za’a bi. Saghir dai kam ya gama auren Diyam. Dama tursashi muka yi ya aure ta ba’ason ransa ba saboda muna son mu karfafa zumunci da iyalin dan uwanmu kuma muna so mu rufa muku asiri. Taje ta auri Sadaukin mu gani, ba dai mune masu daurin auren ba?”11 Na dago kai na kalli Saghir wanda tunda suka shigo yake tsaye a bakin kofa ya rungume hannayensa ya zuba min ido, ina jin idonsa a kaina amma ban kalle shi ba har saida Alhaji ya gama maganar sa sannan na kalle shi. Sai ya tako yazo gabana ya durkusa yana kallon cikin idona yace “tunda nake a rayuwa ta ba’a taba yi min wulakanci irin wanda akayi min akan ki ba Diyam. Zan rabu dake, amma ba wai dan na hakura na yafewa Sadauki abinda yayi min ba sai dan wadanda suka ce in aure ki sun ce in sake ki. Na sake ki saki daya.”11 Sai ya dauke idonsa daga cikin nawa ya mike da sauri. Har yakai bakin kofa kuma sai ya dawo yasa hannu ya dauke Subay’a da take kwance kan kujera tana bacci ya dora a kafadarsa ya yi waje. Na mike da sauri kamar wadda aka mintsina nace “Saghir ka bani yata” ya juyo yace “in da ita kika je gidan ba sai ki karbeta ba in gani?” Na bi bayansa da sauri. “Ka bani yata Saghir, Subay’a! Subay’a!” Sai ta farka firgigit a hannunsa ta sauke idonta a kaina. Ganin ina kuka yasa itama ta saka kuka tana miko min hannu “Mommy! Mommy” yana fita waje ya saka ta a mota ya rufe ya shiga da sauri yaja ya bar gidan tun kafin su Alhaji su karasa fitowa”.Assalamu alaikum my dear fans. Baki ba zai iya bayyana muku irin godiya ta a gare ku ba a bisa karbuwar da littafi na ya samu a zukatan ku. Nagode Nagode sosai kuma nima ina sonku a duk inda kuke.1 A duk lokacin da marubuciya ta dauki biron ta dan rubutu, to tabbas da akwai wani topic a rants da take son yin rubutu a kansa. Dan haka duk abinda zata rubuta will be akan wannan topic din. Sanda nayi niyya kuma na fara rubuta Diyam abinda yake raina guda biyu ne, na farko shine illolin auren dole na biyu kuma karfin soyayya ta gaskiya. Dan haka duk abinda nake rubutawa akan wadannan abubuwan ne.+ So aim din bawai na koyawa mata yanda zasu gyara aurensu bane ba, aim din na nunawa iyaye da sauran al’umma illar auren dole ne.15 A kodayaushe rubutu na is open for corrections, criticism and suggestions. Duk abinda ka gani wanda kake ganin ba dai dai bane ba zaka iya tuntubata ka nuna min ko kayi dropping comment yadda zamu hadu mu tattauna har a samu fahimta. Amma kuma, ita fahimta hausawa sunce fuska ce kowa da irin tasa. Godiya ga wata baiwar Allah data yi min wani gyara a last episode, akan maganar da nayi ta cewa “nothing gives a man the right to hit his wife” what I should have said a gurin shine “nothing gives a man the right to hit his wife the way Saghir did” saboda munsan cewa an bawa maza damar horon disobedient wife da bakin sutturar su, shima kuma sai akace kar su taba fuska. Nagode baiwar Allah duk da bansan sunan ki ba. Lol Kar in cika ku da surutu, ga Diyam……….. Na tsaya a gurin tamkar wadda aka dasa ni, ina kallon bayan motarsa, ina nan tsaye su Alhaji Babba suka fito suka shiga motar Kawu Isa suka tafi ba tare da sun ko kalli inda nake tsaye ina kukan rabani da yata ba. Asma’u ta fito da tazo ta kamani “Adda kiyi hakuri kizomu koma gida, ki rabu dashi yayi ta tafiya da ita din, Allah zai baki wadansu kuma ita din ma da kafafuwanta zata dawo gurinki” ta kama ni muka shiga ciki. Muka tarar da Inna ta zabga ragumi idonta yayi ja, Asma’u tace “dan Allah Inna kar ki wani tayar da hankalin ki, ance musu in babu su ba zamu iya rayuwa ba ne ba? Ai mu kwallon mangwaro muka yar muka huta da kuda wallahi. Da auren Saghir ba gwara babu ba?” Inna tace “hmmm. Asma’u ke yarinya ce. Ba zaki gane ba”. Ni dai sai na wuce su na shiga daki na zauna a bakin gado. All I have ever wanted tun da aka daura aurena da Saghir shine inji sanda zai furta da bakinsa yace ya sake ni. To gashi na samu amma kuma yanayin da sakin yazo min sai yasa naji sam banji dadinsa yadda nayi tunanin zanji ba. Hakan kuma yana da dangantaka da abubuwa da dama. Na farko zargin da Saghir ya sake ni saboda shi, wanda kuma ba gaskiya bane ba, na biyu zumunci daya karasa lalacewa tsakanin mu da yan uwanmu, na uku Subay’a I can’t even imagine yadda rayuwar Subay’a zata zamo a gidan Saghir ba tare dani ba. In banda mutuwa menene yake raba uwa da yar karamar yarta? Amma ni gani a raye amma an raba ni da tawa yar. And I asked myself then, shin Saghir yana da wannan damar? Ranar haka na karasa wuni raina babu dadi. Da nazo sallah kuwa ina dora goshina a kasa sai kuka, zuciyata ta cunkushe gabaki daya, na idar na daga hannuna da niyyar yin addu’a amma sai na rasa me zan roka kuma. Sai kawai na roki Allah daya dubi zuciyata tunda ya fini ni kaina sanin abinda yake cikin ta, na roke shi ya daidaita min lamurana zuwa ga abinda yake shine dai-dai bawai abinda ita zuciyar tawa take so ba, ya saka rabuwar nan da mukayi da Saghir ta zamanto mafi alkhairi a gare mu baki daya, sannan ya bayyana gaskiya ya goge zargi ya kawo daidaito tsakanin mu da yan uwan mu. Na kuma roke shi daya kasance tare da Subay’a a duk inda take. My life had been full of challenges so far, na fuskanci kaddarori iri iri wadansu naji dadin yadda na dauke su wasu kuma I have made a total mess of them. Amma a cikin regrets dina babu rabuwa da Saghir, na daiyi regretting irin zaman da mukayi amma banyi regretting kuma bana jin zanyi regretting zama na dashi. For more than eight years muna tare dashi amma dai dai da rana daya ban taba jin zuciyata tana sonshi ba, ko da kuwa a cikin ranakun da yake kyautata min ne sai dai inni kiyayyar sa ta dan kwanta min amma ba dai ta tafi ba ballantana sonsa ya shiga. Nayi addu’ar kuma kullum, kullum nayi sallah sai nayi addu’ar idan zamana da Saghir ne mafi alkhairi Allah ya rage min kiyayyar sa a zuciya ta. Dan haka da akayi rabuwar sai nayi taking that as shine zabin Allah kuma ma roke shi ya cigaba da zaba mini. STORY CONTINUES BELOW Na fara zaman iddah a nan gaban inna, ba inda nake zuwa sai kewayen maman iman sometimes inyi kallo musamman in Asma’u ta tafi makaranta, sometimes kuma in zauna anan dakin Inna inyi ta karatu wanda shine yake kara nitsar min da zuciyata ina jina ina zama at ease. Inna ta gayawa Mama abinda ya faru, kuma tazo har gida ta ganni ta kuma yi min nasihohi sosai akan karbar kaddara da kuma shirin facing rayuwar da zata zo min. Tace “in kin gama iddah Diyam makaranta zaki koma. Kar ma kiyi tunanin aure gwara kiyi karatu ki huta kema jini ya dawo jikinki sosai. Sannan ki samu exposure. Kuma ki koma islamiyya ki karasa saukar ki dama kin kusa ko?” Na daga mata kai, tace “sai ki karasa kuma ki fara hadda, ki cigaba da bin sauran littattafan addini suma kina kara buda kwakwalwar ki” nace “insha Allah Mama”. Washegari sai ga Rumaisa amarya tazo gurina. Muka wuni tare muna ta hirarrakin mu sai naji hankalina ya kwanta sosai. Monday Sadauki yazo kamar yadda ya saba zuwa. Last Monday bai zoba ya kira Inna yace wani issue ne ya rike shi a Maiduguri amma tayi hakuri. Wannan Monday din kuwa tun safe naga tana ta haɗa masa kunun aya wai taga yana so, ta dama masa fura itama ta saka a fridge ni dai ina ta kallonta. Yamma tana yi, dama nasan da yamma yake zuwa sai na saka hijab dina na tafi gurin Maman iman muka kafa hirar mu. Bana son ganinsa yanzu kuma nasan kona zauna a cikin daki in yazo sai Inna tace in fito in gaishe shi. Amma muna zaune kawai sai ga baban iman da baki sunzo, dan haka dole nayi musu sallama na fita na koma gurin Inna. Ina shiga naga takalmin namiji a kofar palo, sai na jawo farar kujera na zauna a tsakar gida amma ina zama inna ta kira ni, na bata rai kamar zanyi kuka na tashi na shiga. Yana zaune a kasa, Asma’u kusa dashi da wata takarda a hannun ta tana nuna masa wani abu suna magana a nutse. Ga kunun ayansa nan a cup a hannunsa yana sha. Na zauna a gaban Inna nace “sannu da zuwa” ya dago ya min kallo daya ya mayar da kansa yace “sannu maman Subay’a” sai ya cigaba da yiwa Asma’u bayanin wanda na fahimci kamar takardar jamb ce take kokarin cikewa. Na mike na shiga daki nayi kwanciya ta. Sai naji Inna tace masa “Diyam fa sun rabu da Saghir” naji yace “rabuwa Inna” cikin mamaki, Inna tace “rabuwa fa, ya sake ta” yayi dan shiru sannan yace “ya Salam. Subhanallah. Abu baiyi kyau ba. Allah yasa hakan shi ya fi musu alkhairi” Inna tace “ameen” Asma’u tace “ai rabuwar ma itace alkhairi hamma, wannan auren na Adda ai dashi gwara babu” Inna tace “rufe min baki sarkin magana. Waye ya tambaye ki? Tashi ki fita” ta tashi ta fita. Sadauki yace “na dauka ai ko ganin ku tazo yi” Inna tace “uhm uhm, ai satinta biyu kenan anan. Tun sanda nayi maka wayar nan ai bata koma ba dama. Nan yazo har gabana ya sake ta yasa hannu ya dauki yarsa” yace “Subay’a? Ita ta bashi ita ko kuma shine kawai ya dauke ta?” Inna tace “ina kuwa zata bashi ita? Gata nan tunda ya dauki yarinyar nan kullum sai na ganta tana kuka kuma nasan kukan yarta take yi amma ya zanyi?” Yace “a’a in dai ba ita ta bashi ita ba to zata iya karbar yarta. Ai both islamically da constitutionally bashi da right din daukar yarinyar” Inna tace “to ta yaya za’a karbo ta kenan?” Yace “ba wahala ai. Ko hisba akaje akayi reporting zasu karbo yarinyar a hannunsa su kawo mata” Inna ta jinjina kai tace “mutanen nan sunyi mana ba dai dai ba daga ni har yaran nan, amma yanuwan mune. Bana son cigaba da rigima dasu so nakeyi a samu fahimta a tsakanin mu. Amma zabin Diyam ne” sai ta saka baki ta kira ni. Na gyara hijab dina na fita, sai na ganshi a zaune yana daddanna waya kamar ba shine yanzu suke magana rai rai da Inna ba, na zauna a gabanta nace gani, tace “Sadauki yace za’a iya karbar Subay’a a hannun Saghir in aka gayawa hisba. Kina so a karbo miki ita?” Na juya na kalle shi busy with his phone, at least a matsayin da yake dashi na yayana da muka tashi tare kuma Inna ta bashi wannan labarin ai ya kamata ko magana mai dadi ce yayi min, sai na dauke kaina nace “ina son karbar Subay’a Inna, kuma zan karbo ta insha Allah amma bana bukatar taimakon sa. I can do it on my own” sai naga yayi sauri ya dago kai yana kallona. Yace “how?” Nace “ba kace hisba ba? Ai nasan hanyar hisba din kuma ina da bakin da zanyi musu bayani in naje” Na daga kafada na mike na komawa ta daki.2 Daga nan babu wanda ya sake maganar karbar Subay’a ni kuma kullum yarinyar tana raina, kullum zan kwanta bacci sai nayi tunanin ko tayi bacci? In ina cin abinci sai na tunanin ko taci in na tashi da safe sai nayi tunanin ko an tashe ta an shirya ta zuwa makaranta? Kullum kuma a kowacce Sallah sai nayi mata addu’a amma kuma kamar yadda Inna ta fada bana son cigaba da rigima dasu Alhaji Babba, so nake a samu daidaito. Amma daidaiton da baiyi involving komawa ta gidan Saghir ba. STORY CONTINUES BELOW Lokaci ya cigaba da tafiya, har nayi wata biyu a gida. Duk sati ranar Monday sai Sadauki yazo gidan da yamma, in kuma ba zai samu zuwa ba to zai kira Asma’u ko Inna yace musu ba zai zo ba amma ni ko zuwa yayi gaisuwa ce kawai a tsakanin mu, sai sometimes ya kan tambayeni ko da abinda nake so to which I always reply “babu komai. Nagode”. Su Alhaji basu sake kallon inda muke ba ballantana Saghir. Ni kuma sosai na kwantar da hankali na babu abinda yake damuna sai kewar Subay’a. Har yar kiba ta nayi na kara haske. Ranar nan na hada kayan Subay’a da muka taho dasu gidan, nima kuma ina bukatar kayan amfani dan wadanda nazo dasu sunyi min kadan ga kuma har phone dita tana gidan Saghir. Amma sam bana son zuwa gidan Saghir, duk kuwa da cewa ina son ganin Subay’a amma bana jin zan iya taka gidan dan haka sai na bawa Asma’u ta kai mata sannan na lissafa mata abubuwan da zata dauko min kafin a debo kayana. Tunda akayi sakin inna take cewa za’a debo kaya amma jin su maman iman suna shirin tashi saboda sun kammala ginin su yasa Inna tace a bari sai sun tashi tukunna saboda a samu gurin ajiye kayan. Asma’u ta shirya taje ta dauko min duk kayan da nake bukata, amma sai tace min Subay’a bata gidan, daga alama gurin Hajiya Babba ya kaita. Sai na fara tunanin to chanza mata school yayi ko kuma dai tana gida kawai? Sai kuma tace min Fauziyya tace in na kunna waya ta zata kirani. Kuma ta bani labarin cewa “kinga gidan nan kuwa Adda? Gaba ki daya ya lalace har wani karni yake marar dadi. Kayanki kuwa in ba’a je an debo su ba to kuwa sai dai a wuce dasu bola. Na tarar da Saghir a gidan ma, yana kwance a palo ni ko kallon sa banyi ba na shiga na dauko abinda zan dauko na fito”. Da yamma nayi charging wayata da daddare kuma na kunna. Fauziyya ta kirani few minutes after na kunna. Muka gaisa tace “Halima yanzu wai da gaske ba zaki dawo ba?” Nayi dariya nace “my fight is over Fauziyya. Na gama. Bai gaya miki ya sake ni ba?” tace “ya gaya min amma ai saki daya ne dan haka akwai chance na zaki dawo din. Ya gaya min komai bayan kin tafi, kuma ni zanji dadi in kika dawo gidan nan. He loves you da gaske, in ma da baya sonki yanzu gaskiya yana sonki. Ya gaya min dalilin da yasa ya aure ni. Ni kuma na aure shine saboda ina son inyi settling down sai yazo da maganar aure ni kuma na karba. But a yanzu halin da yake ciki bayan tafiyarki I don’t think Saghir is the right person to settle down with. Sun daura abota shi da shaye shaye. Most of the time ma baya kwana gida, kullum masifa kullum zage zage. Shi ne na kira in gaya miki, for the sake of your only daughter ki dawo maybe zai dawo hankalinsa in kina nan”. Nace “kiyi hakuri Fauziyya, but kamar yadda na fada miki. Na gama. For more than eight years nake tare da Saghir amma babu abinda muka tsinta a ciki auren mu daga ni har shi in banda wahala. Rabuwar insha Allah itace alkhairi. And kar kice baya sonki, tunda har ya zabeki a cikin sauran mata ya aure ki to kuwa tabbas yana sonki. Ki ci gaba da kokarin ki, it will be okay with you insha Allah”. And then one day, lokacin har nayi period biyu ina jiran daya. Monday, ranar da Sadauki yake zuwa sai Rufaida tayi rashin lafiya dan haka Mama ta tafi dubata ta barmu gida ni da Asma’u. Ni nama manta ranar Sadauki yake zuwa dan haka ina zaune a palo ina kallon wani film din hausa da na aro a gurin maman iman kawai sai jin sallamar sa nayi. Na tashi zaune sosai na gyara hijab dina sai gasu sun shigo shida Asma’u tana ta zuba masa surutu shi kuma yana mata dariya. Ya zauna ta gaishe shi ya tambaye ta ina Inna ta gaya masa bata nan. Sai ya dafe kai “kash, yau kice bani da kunun aya kenan” Asma’u tace “lah, sai da tayi maka ai kafin ta fita” sai ta tashi ta dauko masa ta zuba masa yana sha sannan na gaishe shi “sannu da zuwa. Ya office?” Ya kalle ni yace “yauwa. Lafiya lau” and that was all. Naji wani makokon takaici ya tokare ni. It really does hurt to be ignored, especially by someone da kuka saba sosai. Sai kawai na kara volume din kallo na a raina ina fatan karar zata dame shi ya tashi ya fita amma sai ma naga sun dauko takardu shida Asma’u suna dubawa suna ta magana, kallo nake amma hankali na yana kansu sai na fahimci maganar ssce suke yi tana cewa “ni dai dan Allah hamma ka cire ni daga makarantar mu ka saka ni a government school in yi exams dina a can, wallahi government anfi ci, private basa bayarda da amsa” yarike baki “au kenan amsa kike so a baki? Maimakon kiyi karatu kici da kanki?” Tace “chaf, wadanda ma suka fini kokari basa ci ballantana ni? Yanzu kuma kaga in banci ssce din nan ba jamb dina ta tashi a banza kenan fa sai na sake wata” yayi dariya yace “kinsan kuwa sau nawa na zana jamb? Kuma a karshen karshe dai ban samu admission din dana ke nema ba” sai ta juyo ta kalle ni tace “Adda kema da kin sani kin cike form din jamb din. Kinga sai muyi tare in ba haka ba sai next year kuma” nayi kamar ban jita ba sai naji yace “in kina so sai a kawo miki gobe” na juyo na kalle shi naga yana kallona sai na kalli sides dina kamar me neman wani abu sannan na nuna kaina nace “are you talking to me?” Sai yayi kamar zaiyi dariya amma ya wani maxe ya dauke kai yace “kina so ko ba kya so?” Nace “ina so, amma karka wahalar da kanka gurin kawo min, zan kira yaya Mukhtar ince ya siyo ya kawo min” ya daga kafada yace “duk daya. Tunda kinci waec dinki ba sai kin sake ba” sai na kalle shi da mamaki, I don’t remember telling him cewa nayi waec ballantana zancen naci, nace “ya akayi kasan naci waec?”. Sai kawai ya zauna yana kallona. And then all of a sudden sai ganin Saghir mukayi ya shigo palon hannunsa rike da Subay’a. He looked at me then at Sadauki and then at me again. Subay’a ta saki hannunsa ta taho gurina da gudu na bude hannuna na rungume ta ina jin dadi har cikin raina. Saghir yace “what the f…..” Sai nayi sauri na mike nace “Asma’u dauki Subay’a ku fita” dan nasan halin Saghir zai iya fadin komai ko yin komai a gaban Subay’a shi babu ruwansa. Ai kuwa tun kafin su fita ya fara “wato na matsa na baku dama ko? Shine wato zaku cigaba daga inda kuka tsaya? Ba kwajin kunyar duniya ba kuma kwajin ta Allah ko?” Sai Sadauki ya gyara zamansa ya dora kafa daya akan daya yayi folding hannunsa yana kallon Saghir. Ni kuma sai na mike, gabaki dayan su basa gabana dan haka baxan tsaya su bata min raina a banza ba. Nazo zan wuce Saghir ya kamo hannuna “ina zaki je? Munafuka kina wani saka hijabi kamar mumina” nayi kokarin kwace hannuna nace “don’t touch me” ya maimaita “don’t touch me, don’t touch me kullum don’t touch me.” Sai ya juya yana kallon Sadauki yace “but I did touched her. Dan haka gwanjo nace. Duk inda zaka shiga babu inda ban shiga na fita ba and I left my foot print there” raina ya kai kololuwar baci, ban ma san me zance ba sai ji nayi Sadauki ya danyi dariya yace “are you sure about that?” Na kama kokawar kwace hannuna daga rikon Saghir zuciyata tana tafasa, zan so ace na fisu karfi in hada su duk su biyun inyi ta duka, how dare they talked about me like that. Saghir yace “of cause am sure kasan a ledarta na bare ta. Sabuwa fil aka kawo min ita and I took her virginity” I froze. What? Ba zan ma iya kallon side din da Sadauki yake ba amma sai naji yace “ita nake so, not her virginity so….” Na kwace hannuna da sauri nayi bakin kofa hawaye yana bin fuskata, kafin in fita Saghir ya finciko hijab dina ya dawo dani cikin palon, ya hada ni da jikinsa muna facing Sadauki, Sadauki ya mike tsaye, Saghir yace “me yasa zaki gudu ne? Dan ke fa ake wannan taron ai ya kamata ki tsaya ki saurara kema ki tofa albarkacin bakinki a ciki. For example, tell him about our first night, tunda yace bai damu ba tell him how I did it maybe zai damu” na fara girgiza kaina da sauri. It is either Saghir is drunk ko kuma kwakwalwar sa ta fara tabuwa. And he said it. “I raped her” and then I saw a flash of fire a idon Sadauki. Saghir ya sake maimaita wa “I raped her the first night da aka kai min ita gida na. That was how she got pregnant for me har ta haifa min twins”. Sadauki took one step sai nayi saurin kwace jikina daga Saghir na tari gaban Sadauki na daga masa hannu “don’t. Kar kace wani abu kar kayi wani abu just go” Saghir yace “yeah. Just go. But before you go, listen to this. Na mayar da ita dakinta.” Na juyo da sauri ina kallonsa zuciyata tana bugawa kamar zata bar kirjina nace “no, no” yace “yes. Na mayar dake tunda dama saki daya nayi miki kuma shima bada son raina ba. Na mayar dake saboda ina son ki sannan kuma saboda I want him to think of you every night of every day when laying on his empty bed har zuwa ranar da zaki bar duniya ko kuma shi zai bar duniya. Sai inga karshen soyayya”.16 Inna ce ta shigo dakin da sauri, daga alama taga motocinsu a waje kuma tayi sensing something is wrong. Tana zuwa bata ce komai ba sai ta kama hannun Sadauki ta ja shi da sauri ta fitar dashi daga palon. Kafin su fita ya juyo ya kalleni and I saw a look on his face similar to wanda na gani ranar da zamu rabu a gidan Alhaji Babba. Na juya da gudu na shige bedroom din Inna na rufe kofa.