DIYAM CHAPTER 20

DIYAM CHAPTER 20

Diyam ta ajiye wayar tana tunani, sati biyu da suka wuce Inna tace anyi relocating gidan gonar, sati biyu da suka wuce lokacin Sadauki bai ma yi winning bet dinsu ba. This means yayi abinda yayi ne on his own account ba wai dan yayi winning bet din ba. Shin hakan yana nufin Saghir yana da hope? Washegari Sadauki ya koma Nigeria. A airport Diyam ta marairaice masa kamar zatayi kuka shi kuma ya rikice. “Ki taho mu tafi. Sai ki dawo next week” tace “school kuma fa?” Yace “share school din nan, ai baku fara exams ba” sai ta tuna sanda yake hanata zuwa islamiyya, tace “so kake ayi min bulalar fashi ko?” Yace “waye zaiyi miki bulalar? Gaya min shi in fara yi masa tun kafin yayi miki” tayi dariya kawai tana tuno jibgar da ta sha a gurin Saghir, sai tace “ni yanzu mai duka na ai sai dai ruwan sama, ruwan saman ma sai na tsaya” yayi kasa da murya yace “in kin tsaya din ma I will shield you from it, like an umbrella” sai ta tuno sanda Inna ta kama su suna saukowa daga sama tazo zata dake su ya kare ta shi akayi ta dukan sa. He had been shielding her all his life. Ya katse mata tunanin ta ta hanyar langwabe kai yace “Please kizo mu tafi” ta makale kafada tace “naki, sai dai ka zauna anan” yace “ai kinsan maganar da zata mayar dani Nigeria. So nake fa ayi lokacin hutun ku sai mu dawo tare” ta rufe fuskarta da hannunta tana murmushi, sai kuma tace “Inna ta gaya min zancen Alhaji Babba. An gode madallah Allah ya kara arziki” yace “ameen” sai kuma ya dauke kansa gefe kamar yana tunani yace “ina yammatan gidan? Su Murja kawarki wadanda kika yi min maganar su rannan akan har yanzu basuyi aure ba?” Diyam tace “suna nan. Muna waya da Murja ma. Wani abin ne?” Yace “ya maganar auren nasu” tace “suna jira dai. Last wayar da muka yi tace min zata tura saurayinta gurin Baba Sa’idu (mijin anty Fatima)” yace “idan kun sake waya kice mata zakiyi musu kayan daki, ita da sisters dinta” ta bude baki tana kallon sa yace “ke ba yayarsu bace ba, ke zakiyi musu kayan daki ai” ya dauke kai yace “in place of their brother”.+ A kano bayan Sadauki yaje gurin Mama yaje ya gaya mata sun daidaita da Diyam, sai kuma ya nemi shawarar ta akan abinda ya dace yayi next. Sai ta nuna jin dadin ta sosai tace “ko ku fa, ai hakan yafi muku akan wannan zaman jiran da da kuka ce zaku yi” ya shafa kai yana murmushi. Tace “to yanzu abinda za’ayi shine zanje ni da kaina in samu Alhaji Babba, in yaso sai ya fadi ranar da za’a je a same su kai kuma sai ka fada a can gida sai su zo” yace “da nayi tunanin ko Kawu Isa, saboda kar a samu matsala da Alhaji Babba” Mama ta girgiza kai tace “babu matsala insha Allah. Shine Babba dan haka dole a bashi girman sa in ya karba shikenan in bai karba ba in yaso sai a je wani gurin a nema” suna cikin maganar sai Mukhtar yazo, suka yi hannu da Sadauki, Sadauki yace “ka yar dani Mukhtar, ko nema na bakayi” Mukhtar yayi dariya yace “ai ka zama yallabai ne yanzu, ka zama hukuma sai da lallashi” Sadauki yayi murmushi yace “sharri zaka yi min kenan ko? Zan samu time zaka ganni har gidanka”. A Oxford da Diyam taje school sai taji babu dadi saboda ganin seat din Bassam empty. But sai taji dadi dan hakan yana nufin ya tafi gida kenan, ya tafi yaje ya gyara tsakanin sa da family dinsa. She just hope ba zai dade sosai ba saboda kar karatunsa ya samu matsala. Kamar yadda Mama tayi alkawari, washegarin da Sadauki yaje ya same ta sai ta tafi gidan Alhaji Babba. As usual, bata ji dadin yadda ta samu gidan ba duk da dai a yanzu matan gidan sun fara yan sana’o’i, Hajiya Babba tana siyar da ruwan sanyi, lemo da kankara. Hajiya Yalwati kuma tana yin snacks, da wannan sana’ar suke kokarin ciyar da kansu da yayansu dan Alhaji Babba har yanzu kusan dashi da babu duk daya a gidan sai ma jigilar asibiti da suke tayi dashi, shi bai mutu ba shi kuma bai cigaba da rayuwa normal ba. Taje suka gaisa da matan gidan sannan ta tafi dakin Alhaji. Yana nan har yanzu a dakin da Inna ta zauna bai koma part dinsa ba duk kuwa da cewa Sadauki ya saka an gyara part din tas batan an kwashe kajin. Ta gaishe shi ya tashi daga kwancen da yake ya amsa mata yana tambayarta lafiyar family dinta, kafin ta gabatar masa da abinda ya kawo ta sai cewa yayi “Hafsa ina Diyam, har yanzu bata zo gari ba?” Mama tace “bata zo ba. Basu samu hutu ba ai” ya mayar da kansa ya kwantar yace “Diyam yarinyar kirki ce mai son zumunci. Fatima ta gaya min abinda tayi wai taki auren shi wannan yaron da take ta nacin so tace lallai sai ya fito da Saghir tukunna zara aure shi. Banyi tsammanin haka ba, na dauka in ta juya bayanta ta bar Saghir a prison ba zata sake waigen inda yake ba, na dauka in ta samu cigaba a rayuwa ba zata sake tunanin halin da muke ciki ba. Ina so inga Diyam Hafsa, ina son in roki gafarar ta tun kafin lokaci na ya kare a duniya. Ina kuma son in roki gafarar Saghir. Ko ma menene Saghir ya zama ko ma menene Saghir yayi ko ake zargin yayi to laifi nane, nine na lalata rayuwar dana mafi soyuwa a zuciyata duk a tunanin soyayya ce nake nuna masa. Ina sane, ina sane da duk abinda Saghir yake yi nasan yana yi din amma sai in rufe idona in nuna tamkar ba zaiyi dinba saboda ina so in gaya wa kaina cewa ba zaiyi din ba. Banyi nadama a bisa tarbiyyar da nayi wa Saghir ba sai da na je gidan yari na ganshi tukunna” yayi shiru yana kokarin saisaita muryarsa saboda kukan da yaji yana neman ya kwace masa. Mama ta fara bashi hakuri “sai hakuri Alhaji, komai mukaddari ne komai rubutacce ne” yace “haka ne, amma komai yana da sila. Silar lalacewar Saghir kuma shine rashin tarbiyyar dani da mahaifiyar sa muka gaza bashi. Ba kuma mu tashi ganin sakamakon abin ba sai da ya zama babu abinda zamu iya yi akai. Bani da yadda zanyi in fito da Saghir daga inda yake, bani da kudi ko hanyar samun kudin da zan biya yaron nan kudinsa sannan bani da karfi na jiki dana aljihu da zan samo wannan yaron daya lika masa wadannan kwayoyi” STORY CONTINUES BELOW Yayi shiru yana tunani sannan yace “Hafsa, idan kunyi waya da Diyam ki nemar min gafararta dan ban tabbatar da zanyi tsahon ran ganin ta in roke ta da kaina ba, sannan kuma ki ce ina rokon alfarmarta akan ta janye waccan maganar ta kin cikawa kanta burin zuciyarta na auren Sadauki, ta aure shi indai tana sonsa, shi kuma ruwansa ne ya yafe wa Saghir ko kuma yaki yafe masa wannan zabin sa ne”. Sai Mama taji dadi, dan haka sai ta rufe maganar sasantawar da aka samu tsakanin Sadauki da Diyam dan tana son alhajin ya ji dadi a ransa ya dauka tamkar shi ya sasanta su din, dan haka ta ki shigar masa da maganar auren da niyyar sai bayan kwana biyu sai ta dawo ta sake shigar masa da maganar. Ta kuma yi masa alkawarin kiran Diyam ta gaya mata sakonsa. Sai dai tana mike wa sai ga Kawu Isa ya shigo dakin hannunsa rike da jariri. Ya wuce ta yaje chinyar Alhaji Babba ya ajiye masa yace “ga sakon Saghir nan. Nayi masa huduba da sunanka dan haka ina yi maka murna ka samu takwara” ya juya da sauri ya wuce Mama ba tare da ya kula mai take cewa ba ya fita. Ta juyo ta dawo gaban Alhaji tana kallon jaririn da take kwance kan cinyarsa yana ta jujjuya kai da alama abincinsa yake nema. Ko ba’a yi mata bayani ba ra fahimci cewa Suwaiba ce ta haihu kuma wannan shine dan gaba da fatihar data haifawa Saghir. Ta saka hannu ta shafi kan yaron tana kallon fuskarsa mai kama data Subay’a. Tace “Allah yayi maka albarka” Alhaji ya dago kansa daga kallon yaron shima yace “ameen. Ki kira min Hajiya Saratu a ciki”. Ga dai jika nan namiji Alhaji da Hajiya sun samu amma kuma shege. Kafin Mama ta baro gidan sai data yi ta zarya zuwa gidan Kawu Isa akan ayi hakuri a mayar da yaron nan hannun uwarsa amma Kawu Isa yace sam bai san wannan maganar ba “ba zata shayar dashi ba” ya fada ya kuma maimaita wa. Ko samun ganin Suwaiba Mama bata yi ba, daga baya ma ta tabbatar bata gidan dan haka ta hakura amma tace “yaron dai jikan mune gabaki daya, kuma shi bashi ne yayi laifi ba dan haka bai kamata a hukunta shi akan laifin dashi bai san ma sanda aka aikata shi ba. Rashin shayar dashi ba zai goge cewa Suwaiba ce ta haife shi ba”. Sai taje ta siyo baby formula da feeder ta dawo ta kawo wa Hajiya Babba. Ta tarar da ita ta goya dan jaririn da ya rare baki yana ta kwarara kuka. Ta mika mata tayi mata barka sannan ta koma tayi wa Alhaji sallama, sai yace “ki turo min Amina dan Allah” daga haka sukayi sallama. Bata koma gida ba kuwa sai da ta je gurin Inna, ta fada mata duk yadda sukayi da Sadauki da kuma yadda suka yi da Alhaji da kuma abinda ya faru a gidan alhajin. Inna duk ta tayar da hankalinta nan take washegari ta dauki kudi ta shirya ita da Asma’u da Subay’a taje tayo siyayyar kayan babies sukaje gidan Alhaji Babba, ta kaiwa Hajiya Babba ta kuma yi mata barka ta dauki yaron da yasha madarar sa yana ta baccinsa tayi masa addu’a sannan taje gurin Alhaji. Bayan sun gaisa yace mata “Amina idan kun yarda ke da yayanki ina so za’a zo a raba gadon usuman” Inna ta kalle shi da mamaki tace “wanne irin rabon gado kuma Alhaji?” Yace “an raba ne? Ai har yau ba’a raba ba. Kuma taba kudin da nayi ne ya haddasa min duk masifun da suka same ni. Tun da na shigo kano na fara neman kudi nake samun sa’a da nasara a rayuwata ban taba cin karo asara ba sai dana bi son zuciyata na taba kudin gadon nan. Kuma har yau ban biya ba, wannan shi yasa duk abinda nake dashi bashi da albarka, duk harkar neman kudi bana tarar da komai a ciki sai asara. Wannan kuma a duniya ne kadai, idan har ban biya ba to azaba tana can tana jirana a lahira. Na sani sarai, ina sane da duk abinda nakeyi son zuciyata kawai nake bi shi yasa na kasa gyarawa amma yanzu alhamdulillah rayuwa ta bani wata sabuwar damar gyara kurakurai na guda biyu. Zan fitar da hakkin usuman da yake kaina sannan kuma zan gyara kuskure na na tarbiyyar Saghir akan wannan yaron da aka haifa masa”. Inna tace “mu ai Alhaji mun riga mun yafe maka rabon mu ni da yara da yake cikin abinda ka dauka, shima kuma Sadauki yace ya yafe kason mahaifiyarsa, sannan kuma ai kaima da sauran yan’uwa kuma da rabo a ciki sannan…..” Yace “muna dashi, hardo yana dashi, hatta yaya ladi mahaifiyar Zainab tana dashi. Yanzu bayan mutuwar hardo matar daya aura kafin rasuwarsa tana dashi. Mutanen da suke da hakki suna da yawa, wannan yafiyar ba zata sauke min nauyin nan ba”. Tayi shiru tana lissafa maganar sa, sai yace “ina so azo ayi rabon gadon a bisa ka’ida. Zan bayar da complete kudin dana dauka, sai ayi wa gidan da kuke ciki kudi sannan a raba a bisa tsarin da addini ya tsara a bawa kowa rabonsa ko zan samu rayuwa ta dan sassauta min kafin in bar duniya kuma in samu sassauci a lahira” tayi tagumi tace “to a ina zaka samu kudin nan Alhaji?” Yayi murmushi yace “nan gidan da muke ciki shine kadai abinda ya rage min a duniya. Shi zan siyar. Kollere zan koma in cigaba da rikon sarautar da hardo ya mutu ya bari muka ki karba. Sauran abinda yayi min saura kuma sai in samu sana’ar yi a can wadda zata rike min iyalina a can din”. Inna ta girgiza kai tace “ba zai kai ga haka bama Alhaji, insha Allah ba zai kai ga haka ba”. Wasa wasa abu ya tabbata. Inna ta kira Diyam da Sadauki ta gaya musu abinda duk ake ciki, farko Diyam ta nuna rashin yardarta amma sai inna ta gaya mata cewa hakan shine dai dai “shima marigayin wannan wani sauke nauyi ne akayi masa”. Aka yiwa gidan Baffa kudi, a take Sadauki ya siya. Aka kuma yiwa gidan Alhaji Babba kudi aka siyar, ana siyarwa Diyam ta aiko da kudi tace a kama musu ko rent ne su zauna kafin komai ya zama settled. Sannan Alhaji Babba ya ware kudin garejin Baffa daya siyar aka hada da kudin gidan Baffa aka raba kudin cash, kowa aka danka masa nasa a hannunsa hatta amaryar da hardo yayi kafin rasuwarsa sai da aka fitar mata da nata a cikin kason Hardo aka aika mata dashi har Kollere. Babu yadda Alhaji Babba baiyi ba akan son komawa Kollere amma yaya da yan uwa suka saka shi a gaba akan lallai ba zai koma ba. Dole ya zauna a gidan da Diyam ta aiko da kudi aka kama masa haya a unguwar Jaeen, suka koma gabaki daya shida iyalinsa. A lokacin ne kuma Diyam daga can ta aiko da kudurinta na son yiwa kannen Saghir su hudu wadanda suka isa aure kayan daki. Sai Alhaji Babba yace “ku gaya mata tazo sai a hada auren tare da nata”. A bangaren Sadauki, yana ta son ya tunawa Mama da maganar da suka yi amma kunyar ta yakeji, sai yayi ta cewa Diyam wai ita ta kira Mama ta tuna mata, tayi dariya tace “wato nice marar kunya ko? To babu ruwana, tunda kaji tayi shiru tana da dalilinta”. Save the Date Yace “eh nasan tana da dalilin ta shi yasa ni kuma na kasa zuwa in tuna mata. Am just scared Diyam, tsoro nake yi kar a sake hana min ke a karo na biyu. Bansan me zanyi ba wannan karon” tace “babu wanda zai hana mu juna Aliyu. In har kaga ba’ayi ba to kuwa tabbas Allah bai rubuta za’ayi ba. Waliyai na ne su amma basu kadai bane waliyai na in sunki zamu iya zuwa Kollere mu……” Yace “no, no Diyam. Ba su kadai ne waliyan ki ba amma sune shakikan Baffa, kamar yadda kika fada haka ne Baffa zaiji dadi idan muka sasanta tsakanin mu da su. Kuma ni ba zanzo in zama sanadiyyar rabuwarki da yanuwanki ba but am not going to give you up, not now not ever. Dan haka zamu jira in ta kai ga cewa ni zan kuma durkusawa Alhaji Babba zan durkusa din” sai ya dan yi dariya yace “the table have been turning so past yanzu kuma na dawo ni nake nema a gurinsa” ta taya shi dariyar sannan tace “in lokacin durkusawar yazo, call me sai mu durkusa tare ni da kai because we are in this together”. Washegari sai ga wayar Mama. Ta gayawa Diyam duk abinda sukayi da Alhaji Babba tace “na bashi wannan damar ne saboda naga yadda yayi nadamar abinda yayi, so nake ya nemi Sadauki da kansa ya gyara kuskuren da yayi da kansa. Yanzu yace yana so kizo gari dan yana son neman yafiyarki, sannan kuma yace kice da Sadauki ya turo, in yaso sai a hada dana su Murja ayi gabadaya” Diyam ta lumshe idonta tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa a zuciyarta wanda har sai daya saka hawaye ya taru a idon ta. Mama tace “kinyi shiru kuma, me zance masa?” Ta dan goge hawayen idonta tana jin zuciyarta fari kal kamar takarda, rabon data ji wannan feeling din tun Baffa yana da rai, tun tana carefree teenager, tun lokacin da Sadauki yake zuwa gurinta a school suyi ta bayyana wa junansu abinda yake zukatan su.+ Amma sai taji kunyar Mama tace “mun kusa fara exams yanzu Mama, ba zan iya tahowa gida ba amma muna yin hutu zan taho sai in samu alhajin, duk da dai ni na riga na yafe masa tuntuni” Mama tace “to Allah ya bada sa’a. Maganar Sadaukin fa?” Diyam tace “duk yadda akayi Mama” Mama tace “ki gaya masa ya tura gurin Alhaji Babba, sai asa rana tare daba su murjan. Yaushe kuke so a saka?” Diyam ta sake yin shiru sai da Mama ta maimaita sannan tace “duk sanda aka ce dai dai ne” Mama tace “in aka saka lokacin hutun ku ai yayi ko?” Diyam ta sake yin shiru tana murmushi amma a ranta tana lissafa kwana nawa ya rage ayi hutun.Mama tace “shikenan tunda ba zakiyi magana ba, shi bara in kira shi in tambayeshi” s Suna yin sallama Diyam tayi saurin kiran Sadauki ta gaya masa yadda sukayi da Mama, yace “tare dana su Murja kika ce?” Tace “eh, haka tace min” ya girgiza kai yace “I don’t like that. Nafi son ranar bikinki ya kasance all about you not you and someone else, nafi son in an ganki ace ‘ga amaryar can’ kar ace ‘ga daya daga cikin amaren nan’ nafi son ki samu cikakkiyar kulawa daga kowa ba wai ki samu divided attention ba. Dan haka zan gaya mata ayi nasu first, later in an huta sai ayi namu”2 Tun da ya fara magana take murmushi har sai daya gama sannan tace “I don’t need attention din mutane, attention dinka nake so, in nayi kwalliya ban damu da a yaba ko ayi comparing dina da wasu ba as long as kai ka yaba as long as a gurinka babu wadda ta kai ni. Besides, ni ba biki zanyi ba, daurin aure kawai za’a hada da nasu, ni a gida zanyi zamana kawai sai wanda ya shigo aka gaisa kawai shikenan. Ban damu da having a big wedding ba as long as kaine angon that’s all that matters, tunda nasan a gurinka zan samu more than abinda na samu a wancan auren” a can kasan makogwaron sa yace “more of what?” Tace “everything” yace “like?” Tace “caring” yace “and?” Tace “tunda nace everything ai ina nufin everything ko? Sai na lissafa maka?” Yayi dariya yace “so nake ki fada da bakin ki, yadda in lokacin yayi zan tuna miki cewa ke nema da kanki” ta bata rai tace “abinda kake nufi fa ni ba shi nake nufi ba, we are not talking about the same thing” yace “zaki sha kwana ko? To gaya min ni abinda nake nufi” tace “ni ban san me kake nufi ba fa” yace “to in baki sani ba ya akayi kika san ba abu daya muke nufi ni da ke ba?” Tayi rolling eyes dinta tace “good night Aliyu” yace “ashe tsoro na kike ji tunda zaki gudu, ki tsaya mana” tace “ba tsoro nake ji ba bacci nake ji, ina da school gobe” yace “hmmm okay, Allah ya tashe mu lafiya, but I will still demand to know that ‘everything’ da kika fada, ko ba gobe ba ko watarana I will get the words out of you”. STORY CONTINUES BELOW Suna gama wayar Sadauki ya ajiye phone din yana kallonta, sai kuma yayi murmushi sannan ya lumshe idonsa ya kwantar da kansa a bayan kujerar office dinsa yana dan jujjuya wa a hankali. Sai kuma ya mike zaune sosai ya jawo system dinsa yana duba calendar, yasan ranar dasu Diyam zasu fara exams ya kuma san ranar da zasu gama sannan yasan ranar da zasu koma school, sai ya duba dates din da suke tsakanin hutunsu da komawar su school yana neman weekend mai perfect date for their wedding, sai idonsa ya sauka akan date din, his birthday. Ya dafe kansa yana fadada murmushin sa. He is going to have a perfect birthday gift for his 30th birthday.1 Mama ta kira shi kamar yadda tace zatayi, ta kuma maimaita masa abinda already Diyam ta gaya masa sai ta tambaye shi shima akan date, sai ya maimaita mata abinda Diyam tace mata “duk sanda aka saka dai-dai ne Mama” ta tabe baki tace “ai shikenan, idan manyan sunzo ayi magana dasu”. Washegari ya hau jirgi daga kano zuwa Maiduguri ya samu Alhaji Babagana wanda yake kani ne a gurin Papa kuma shine dai wanda shekaru goma da suka wuce yazo ya nema masa auren Diyam aka hana shi. Yanzu ma shi zai sake dawowa tare da Alhaji Bukar su karasa abinda suka fara. Nan take shi kuma ya kira Papa ya gaya masa sannan ya bashi izinin ya dauki sauran yan’uwa suje su hadu da Alhaji Bukar suyi duk abinda ya dace. Sai da suka gama wayar sannan Sadauki ya gaya masa date din da ya keso a saka. Sai shi kuma ya tambaye shi “kana ganin ba za’a samu matsala ba? Kar azo ayi irin ta wancan karon” Sadauki yace “babu matsala in sha Allah, tunda wannan karon ai sune da kansu suka nemi azo din”. Daga Maiduguri sai yayi branching a Yobe yaje damagun gurin yaya ladi wadda take zaune a gidan cousin dinta da Sadauki ya gyara musu shi tas ya zuba musu kayayyakin more rayuwa kuma ya daukar musu yan aikin da zasu ke kula dasu. Bayan sun gaisa ta gama loda masa tuwo da fura sai ya sanar mata da duk abinda ake ciki, yana maganar yana murmushi. Sai ta rike baki tace “Diyam din dai Aliyu?” Ya dago kai yana kallon ta yace “Diyam din dai. Ko kina kishi ne?” Ta tabe baki tace “ni dai daka hakura da Diyam din nan da nafi jin dadi, kazo ga yammata nan birjik ka zaba ka darje in ma hudu kake so a tsakanin yau da gobe sai a samo maka su amma kai ka nace sai yarinyar da yan’uwanta suka wulakanta ka, suka wulakanta mahaifiyar ka, suka wulakanta ni kakarka?” Ya daga kafada yace “ita nake so, ita ma kuma tana sona kuma in anyi auren da ita zan zauna bada yan’uwanta ba” Hajiya Dije, cousin din Yaya Ladi tace “amma duk da haka Aliyu, ko bayan anyi auren ne ya kamata ka samu budurwa ka kara da ita” sai ya mike tsaye yana daukan hularsa a hannu fuskarsa da murmushi yace “kar ku damu, bayan anyi auren da sayi daya zan dawo nan sai in aure ku duk ku biyun a rana daya” yaya ladi ta tabe baki dan tasan shirishitar da maganar yake yi, tace “to ai shikenan, uwarka ma haka nayi ta fama har sai dana hakura” ya durkusa a gabanta yace “kisa mana albarka kawai ke dai. Kiyi mana fatan alheri” ta dafa kansa tace “Allah ya sanya alkhairi a ciki, Allah ya baku zaman lafiya ya kuma kade duk wata fitina da zata taso sannan ya baku zuri’a mai albarka” yayi kyakykyawan murmushi yace “yanzu kika yi magana. Karki manta, ke ce uwargida ran gida a gurina, ita kuma amarya ta sannan kuma zuciyata”. A gidan Baffa aka sauki bakin da suka zo daga Maiduguri, aka bude musu part din Baffa inda Inna ta zauna da, Mama tazo da yammatan ta suka hadu suka shirya musu abinci mai rai da lafiya wanda duk da kasancewar su masu hannu da shuni amma sun tabbatar cewa an karrama su. Sannan Alhaji Babba yazo, Kawu Isa ma yazo sannan abban su Rumaisa shima yazo suka zauna suna ta hira ta wasan fulani da barebari suna ta dariya kamar sun saba. Sai a lokacin ne su Alhaji Babba suka san asalin waye mahaifin Sadauki, jin hakan ba karamin girgiza su yayi ba, ba kuma karamin nadama ya saka musu ba. Lallai rashin sani yafi dare duhu, wanne irin gorin arziki ne basu yi wa Sadauki ba? Wanne irin wulakanci ne basu yi masa ba shida mahaifiyar sa? Sai da suka nutsa sannan Alhaji Bukar ya gabatar musu da dalilin zuwan su cewa suna nemawa dansu Aliyu Umar Abatcha auren yarsu Halima Usman Kollere, sai Kawu Isa ya gyara masa yace “dan mu dai. Sadauki ai dan mu ne kamar yadda Halima take yar mu. Ku kawai zuwa kuka yi dan ku tunatar damu akan abinda ya kamata muyi tuntuni amma kuma son zuciya da kuma rabo ya hanamu aikatawa sai yanzu da Allah ya sake dawo mana da damar” Alhaji Babba yace “mun bawa Aliyu auren Halima. Duk sanda kuka shirya sai ku dawo a saka rana” Alhaji Babagana ya jawo yar jakar daya shigo da ita ya ajiye a gaban Alhaji Babba yace “a shirye muka zo. Kuma munzo da ranar mu amincewar ku kawai muke nema” sai ya fadi ranar da Sadauki ya gaya masa, yace “lokacin yarinyar tana hutu” babu musu kowa ya amince da hakan, sannan suka sake gaisawa yanzu kuma a matsayin surukai. Sai kuma Alhaji Babba ya roki gafarar su a bisa abinda yayi musu wancan zuwan. Su kuma suka yafe cikin sigar tsokana dan mayar da abin wasa. Bayan tafiyar bakin ne aka kirawo Inna da Mama da suke cikin gida suka zo akayi musu bayanin abinda ya faru da kuma ranar da aka tsayar. Alhaji Babba ya mikawa Mama jakar da aka bashi yace “ga abinda suka kawo” Mama ta bude sai ta dago kai tana girgiza wa tace “wannan kudin sunyi yawa, albarkar aure ake bukata ai bawai yawan kudi ba” Kawu Isa yace “nima dai naso ince haka, amma sai naga tunda bani suka mikawa ba gwara inyi shiru” Inna tace “ai duk daya ne babu bambanci, suma kuma nasan sun mika masa ne saboda shine Babba” Abban Rumaisa ya kalli Alhaji Babba yaga yadda yayi da fuskar abin tausayi kamar wanda yayi laifi sai yace “tunda an riga an karba ai ina ganin shikenan. Albarka kuma sai muyi ta saka musu ita mu kuma tayi musu addu’a shikenan”. Sai Kawu Isa ya tashi yayi musu sallama tare da fatan alkhairi sannan ya tafi. Ana isar da sako gurin Sadauki ya turawa Diyam message “save the date. 25th August”1 Ta lumshe idonta tare da jingina kanta da jikin kujerar da take zaune akai tana murmushi mai sauti wanda yafi kama da dariya. Murjanatu da take zaune kusa da ita tana cin abinci ta dakata da abinda takeyi tana kallon Diyam sai ta bude ido tace “what? Menene ya faru kike dariya ke kadai?” Diyam ta daina dariyar da take yi amma bata ce komai ba sai Murjanatu ta warce wayar daga hannunta ta karanta message din nan take ta mike tana tsalle tana kiran Judith, Judith tana fitowa tayi mata bayanin cewa auren Diyam za’ayi sai itama ta kama murna suna rawa a tsakiyar palon, Diyam tana zaune tana kallon su a ranta tana jin kamar ta tashi suyi rawar tare amma sai ta hana kanta. Sai da suka gama tsallen murnar su sannan Murjanatu ta zauna tana haki ta jawo phone dinta, Diyam ta bude ido tace “hey, me zakiyi?” Murjanatu tace “su Adama zan gaya wa” Diyam tace “ai za’a gaya musu a can, ki barsu kawai saji a can” Murjanatu tace “yanzu su Adaman ma kunyarsu kike ji? To Papa zan gayawa ma, in ce masa gaki nan kin saka waya a gaba kina ta dariya kin kasa rufe baki kina murna zaki auri dansa” nan da nan Diyam ta mike ta murde hannun Murjanatu ta karbe wayarta ta tafi daki tana cewa “nayi seizing phone dinki, bazan baki ba sai anyi hutu”.+ Tana shiga dakin Murjanatu ta dauki tata phone din ta kira Sa’adatu wadda a lokacin suna tare da Falmata sai suka kira Adama da taje school a lokacin suka hada conference call sannan Murjanatu ta basu labarin abinda yake faruwa. Duk sunyi murna sosai musamman da yake wannan shine biki na farko da za’ayi a gidan su. Sa’adatu tace “oh su yaya Aliyu za’ayi aure, I wonder ta yaya suke magana da Diyam din da wannan turbunanniyar fuskar tasa” Murjanatu tayi dariya tace “wallahi in kunga dariyar da yakeyi mata ko, zaku dauka chanja shi akayi gaba ki dayan sa” sun jima suna hirarrakin su sannan suka lissafa kwanakin da ya rage kafin bikin sai kuma suka fara tsare-tsaren events din da zasu shirya. Sai da suka gama Murjanatu tace “Allah yasa ya yarda, zamu iya gama shirya komai yace shi ba za’a yi wa matarsa kwalliya a shiga da ita cikin mutane ba, kishi ne dashi kamar me”. Sai da suka gama Murjanatu ta dauki wayar ta kai wa Diyam har daki ta mika mata tace “thank you for letting me use your phone” sai ta ajiye ta fita da sauri tana dariya. Diyam ta dauki phone din ta duba numbers din da Murjanatu ta kira, sai tayi murmushi tana mamakin zumunci irin na wadannan mutanen, sam basa nunawa Aliyu yan ubanci ko dan akwai wayewa sosai a tare da su? Daga gida ma Mama ta kira Diyam ta yi mata bayanin duk halin da ake ciki, sai kuma ta umarce ta data kira Rumaisa suyi shirye shiryen abinda zasu yi kafin tazo gidan. Sanda sukayi waya da Sadauki kuma sai yace mata “guess what? Na sayi fili zan yi gini” tayi dariya tana rike baki yace “au, dariya ma na baki ko?” Tace “I tot zaka sayi gida ne kawai, ko kuma ma ka riga ka siya” yace “hmmm, nima na dauka zan siya gidan ne, but then an opportunity presents itself to me, na saka a nemo min gida sai dillalin ya gaya min akwai wani fili ma in ina so, sai na bincika na gano ashe fili na ne, filin mune Diyam da Baffa ya siya mana zamu gina gidan mu, all these years ba’a gina shiba har sai daya dawo hannun mu. And now I hired wani construction company da aka bani labarin sa a Abuja ‘Moon Construction Company’ sunce zasu gama komai within a month. Ina ganin ai yayi ko? Tunda muna da kusan watanni biyu nan gaba”4 Diyam taji dadi a ranta tana jinjina hikima irin ta ubangiji. Tace “yayi sosai ma” yace “zasu turo min samples na building plans dinsu, sai mu zaba ni dake sannan sai su fara” sun jima suna hirarrakin su sannan suka yi sallama suka ajiye wayar. Sai ya cigaba da zama hannunsa rike da phone din yana kallon hotonsu shi da ita da yake kan screen din wayar, a Oxford suka dauka sanda yaje, selfie ne yayi musu suna tsaye a gaban motarta shi yana murmushi ita kuma ta turo baki tana hararar sa. Yayi murmushi saboda ya manta me yayi mata a lokacin take hararar sa kuma yasan itama kanta in da zai tambayeta ta manta. Ya saka babban dan yatsansa a hankali ya shafa fuskarta a jikin hoton sai kuma yayi sliding din hoton sama ya nemo number din one of his lawyers ya kira “barrister akwai maganar da nake so zamu yi Please, lets meet in my office in an jima. Okay, thank you”. STORY CONTINUES BELOW Diyam har ta fara sabawa da rashin Bassam a school, duk da dai kullum in ta kalli empty kujerar kusa da ita sai taji babu dadi. Sai a lokacin tayi nadamar rashin exchange din numbers da basu yi ba at least da yanzu ta kira shi tasan halin da yake ciki. And then one day, suna gab da fara exams din su sai gashi ya shigo ana tsakiyar lecture. Yayi ignoring lecturer din da yake masa kallon yazo late yana distracting din class sai ya wuce empty seat din kusa da ita ya zauna ya juyo yayi mata murmushi sannan suka mayar da hankalinsu kan lecture din da ake yi. Sai da aka gama lecturer din ya fita sannan Diyam tace masa “welcome back prince Sadiq” ya juyo yana kallon ta da mamaki dan shi dai ba zai iya tuna sanda ya gaya mata daga inda yake ba, yace “Prince? Yaushe na gaya miki haka?” Tace “ba ka gaya min ba, Aliyu told me” yace “shi din ya akayi ya sani?” Tace “okay, ba direct ya gaya min ba, kace ka taba ganinsa a gurin daurin auren yayanka a abuja last year, shi kuma yace daurin auren da yaje abuja last year na jikan sarkin Abuja ne, so, in yayanka ya kasance jikan sarki to kuwa kaima jikan sarkin ne, ko ba haka ne ba?” Ya dauke kai yace “an baki A1 a fannin bincike” tayi dariya tace “tell me everything. Dame da me ya faru? I hope komai ya warware yanzu and you are back to your old self again”1 Yace “well, bayan mun rabu naje gurin aunty Hafsat but she refused to see me. Nayi iyakacin kokari na amma abin yaci tura but sai na ci sa’a uncle Zayed ya dawo, dama yayi tafiya ne lokacin da muka samu sabani dan haka bai ma san abinda ya faru ba, I explained everything to him kuma na dauki laifina sai ya saka ni a gaba muka tafi Nigeria tare” ya danyi dariya yace “ba karamin taimako na Allah yayi ba da muka je tare dashi, da maybe in Daddy ya fara jibgata sai na kwanta a asibiti” Diyam tayi dariya tace “anya kuwa bakayi girma da duka ba?” Yace “not to my Daddy, ba ruwansa da girma na wallahi dukan tsiya zaiyi min Mami kuma ba zata hana shi ba. But Allah ya taimake ni Uncle Zayed ya shiga maganar, and my grandparents too, sai komai yazo da sauki musamman tunda na karbi laifina kuma na bada hakuri. And now Ya Ameen ne ya dawo dani tare da wife dinsa Humairah itama zata fara karatu. She is an artist, yana so ne ta samu qualifications din kawai” suka yi shiru Diyam tana tunanin ina ma dai itama nata family din zasu zama irin haka in ɗa yayi wa wani family member laifi sai iyayensa su danne son da suke yi masa su hukunta shi har ya zamanto su ake bawa hakuri ma. Bassam ya cigaba da cewa “Mommy, my grandma, tace wai in zabi budurwa a cikin cousins dina in place of khausar, but nace mata ta barsu duk na gode, saboda duk wadda na zaba din za’a iya forcing dinta dan a faranta min and I don’t want to end up like Saghir dinki, in zauna da matar da bata so na, so I decided zan jira, rayuwar ai yanzu ta fara ko? Zan jira har Allah ya hada ni soulmate dina da zata soni kamar yadda kike son Aliyun ki” ya karashe da sigar tsokana. Ita kuma tayi murmushi tace “ka lallaba ni in baka kanwata” yace “wacce kanwar?” tace “Murjanatu” ya daga hannu yace “no, no, no. Thank you so much but no. Wannan yarinyar samarinta sun kai cikin container”.2 Suna tare har aka tashi. A lokacin ne ta bashi labarin itama cigaban da aka samu a nata bangaren, ya taya ta murna sosai da sosai sannan shima ya tambaye ta game da shirye-shiryen da take yi. Ta daga kafada tace “ba fa abinda zanyi ni, ina naga friends din ma da zan shiryawa event. Nasan dai Inna zata yi taron yan uwa da abokan arziki and that will be all” Bassam yayi shiru yana kallon ta sannan yace “kinsan wani abu? Matar yayana dana gaya miki mun taho tare zata fara school itama, zan hada ki da ita ina tunanin you two will like each other. Zaku iya zama friends” Diyam tace “no, ni bana son friendship da yayan masu kudi” yayi murmushi yace “babanta ba mai kudi bane ba, mai rufin asiri ne. Kuma bafulatana ce irin ki” tace “in babanta ba mai kudi bane ba ai mijinta mai kudi ne” Bassam yace “that makes the two of you” sai ta sunkuyar da kanta tana murmushi, the mare thought of Sadauki as her husband yana saka ta murmusawa. Suna rabuwa da Bassam ta kira Sadauki ta bashi labarin dawowar Bassam. Wannan shine dai dai saboda boye boye shi yake kawo zargi in a relationship. STORY CONTINUES BELOW Kamar wasa sai ga Bassam ya kawo wa Diyam Humairah har gida. Sai Diyam taga cewa ashe duk abinda take tunani a game da Humairah ba haka bane ba, na farko she is young, dan Diyam tana ganinta ta san cewa ta girme ta. Ko kuma dan tana da baby face ne? Da suka zauna suka fara hira sai ta fahimci tana da saukin kai sosai da kuma addini. Ta karbi babyn da yake hannun Humairah tana yaba kyawunsa tace “masha Allah, ya sunansa?” Humairah tace “Abubakar, Ayman ake ce masa” Diyam tayi murmushi tana tuna mitar da Bassam ya taba yi akan cycling suna daya within a family. Amma ai honor ne ko? Kowa yana burin ya haihu yayi wa iyayensa takwara. Nan da nan Diyam ta dauko zani ta goya Ayman, tana tuna sanda Subay’a take jaririya. Wannan yasa Humairah ta kara sakin jikinta saboda hausawa sunce mai ɗa wawa ne. Sun jima suna hira, suka yi hirar similarities dinsu sannan suka yi hirar differences dinsu, a take kowacce a cikin su ta fahimci cewa tayi kawa. Tare suka shirya abinci sannan suka zauna suka ci a plate daya, suna cikin ci Murjanatu ta shigo tayi joining dinsu itama. A nan ne take bawa Humairah labarin cewa an kusa auren Diyam da yayanta, sai kuma hirar ta koma kan hidindimun aure da kuma zamantakewa ta aure har sai da Murjanatu ta mike tace “wannan hirar tafi karfina kar kuje ku kona ni tun kafin in tafasa”. Komai ya tafi normal har Diyam ta kammala exams dinta, a cikin lokacin sau biyu Sadauki yana zuwa Oxford Diyam tana koro shi Nigeria saboda tace karatu yake hanata yi in dai yana can din. A dole ya hakura ya dawo Nigeria amma da sharadin cewa kullum zasuyi video call sau biyu. Ranar da zata dawo Nigeria Sadauki ne yace zaije ya dauko ta, amma sai ya gaya wa Asma’u ta shirya Subay’a su tafi tare. Subay’a kam murna take tayi ta kasa rufe bakinta saboda farin cikin zata ga mommyn ta, dan haka bata damu bama da wate zasu tafi tare dashi. Shi ya fito da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga sannan ya zagaya ya zauna yana tsokanar ta “Subis yanzu duk wannan kwalliyar ta mommy ce? Dama ashe kin iya kwalliya haka shine ni ba kya yi min sai mommy ko?” Ta sunkuyar da kanta tace “bani nayi ba ai, aunty Asma’u ce tayi min” yace “to gaya min, me kika tanadarwa mommy?” Ta bude hannu tace “babu komai, ai ni bani da kudi” yace “to me kike so ki siya mata” tayi shiru sannan tace “sweets” yayi murmushi “wato kin san ta da shan sweet ko?” Sai tayi shiru bata ce komai ba. Yace “kina so in kai ki ki siyo mata?” Ta gyada kai kawai, sai yace “a’a, in dai kina so to sai kinyi magana da baki ba da kai ba. In kuma baki yi ba bazan siya miki ba” tace “ina so” yace “to sai kin fadi sunana tukunna. Ya sunana” a hankali tace “uncle Aliyu” yayi murmushi ya shafa kanta yace “good girl”. Suka biya ta mall suka ciko leda da kayan zaki sannan suka karasa airport. A airport din sai yaga duk walwalar data fara dazu ta ragu, tayi shiru kamar mai shirin yin kuka, sai ya durkusa a gabanta yace “menene kuma? Ba kya murnar ganin Mommy? Ko in kira ta a waya ince mata ta koma ba kya son zuwanta?” Sai tayi sauri ta girgiza kai, yace “to me kike so?” Tace “rannan da muka zo nan da mommy, sai police suka zo suka tafi da Daddy na kuma har yanzu basu dawo min dashi ba” sai hawaye suka zubo daga idonta ta dago tana kallonsa kamar yadda shima yake kallonta ta sake cewa “mommy tace zaka fito min dashi ko?” Ya saka hannu ya share mata hawayen fuskarta yace “daddyn ki zai fito little girl. I promise you” sai kuma yayi murmushi yace “amma sai kinyi min wani alkawari, promise me daga yau mun zama friends” ya fada yana mika mata dan karamin finger dinsa, ta goge hawayen fuskarta ta saka nata karamin finger din a ciki sannan ta gyada kai tana murmushi. Ya daga ta masa ya dora ta akan kafadarsa yace “now, let’s wait for your mommy”. Diyam tana fitowa ta hango su, and seeing them smiling together ya saka taji wani irin joy a zuciyarta marar misaltuwa, tana kallonsa ya sauke Subay’a kasa ita kuma ta taho da gudu gurinta sai ta durkusa ta bude mata hannayenta ta shige zuwa kirjinta ta rungume ta taba ajjiyar zuciyar dadi, ta dago fuskarta tayi kissing goshinta tace “I miss you so much little girl” Subay’a tace “I miss you too mommy”. Ya karaso ya tsaya a kansu yace “na gane matsayi na” ta mike tana kokarin daukan Subay’a yace “ke! Careful kar kisa a daga min biki” ta harare shi tace “wato bikinka ne a gaban ka ko?” Yace “a yanzu, yes” Subay’a tace “uncle bikinka za’ayi?” Ta fara tsalle, “zanje gidan ka inga amaryarka” ya daga ta sama yace “karki damu, kece yar zaman daki”. Daga airport basu yi cikin gari ba sai suka dauki wata hanya daban. Diyam tace “ina zamu je?” Bai kalleta ba yace “kawunan ku zanje in siyar” tayi dariya “ni kaina yafi karfin babarbare ya siyar” ya kalleta yace “siya na nawa kuma? Sai ya kalli Subay’a ta mirror yace “kinci sa’a we have company” ta murguda masa baki, yace “ki cigaba, ba dai rashin kunya ba, akwai ranar kin dillanci”. Titin bypass suka hau sannan suka shiga unguwa uku, suka sauka daga babban titi suka shiga wani layi sannan yayi packing a gaban wani gida yace “Mrs Abatcha, welcome to your home” ta bude vaki tana kallon gidan sa yake gabanta sannan tace “wow” yayi murmushi yace “shall we?” Kafin ta bada amsa Subay’a ta bude motar ta fita da sauri tana cewa “uncle gidanka ne wannan?” Ya fito yana cewa “gidan mu ne princess, ni da mommyn ki da ke” sai ta kwasa a guje ta kama gate din tana cewa “Mommy ki kira inna kice ta aiko min da kayana” Diyam da Sadauki suka yi dariya a tare. Malam iliyasu ya fito yana bude musu gate. Diyam ta kalleshi sannan ta kalli Sadauki shi kuma ya daga mata kafada yana murmushi. Sai ta juya tana amsa gaisuwar da malam iliyasu yake yi mata amma bata ce masa komai ba sannan suka taka da kafa suka shiga gidan. Tsayawa bayyana tsari da kyawun gidan zai tsawaita labarin mu amma dai tabbas Moon construction company sun kure adakar su a wannan gidan. Daki daki suka bi a nutse Sadauki yana yi mata bayanin komai kuma tana neman gyaranta in akwai amma ita bata jin akwai wani gyara da za’ayi a wannan tsararren gidan. Bayan sun gama sun fito ne suka zagaya baya gurin wani dan karamin gurin shakatawa mai lullube da grass carpet da kuma madaidaicin swimming pool mai dan karen kyau wanda ganinsa kawai ya isa ya saka mutum yaji yana son yin wanka. Suka zauna a wasu daga kuherun gurin ita kuma Subay’a ta bazama tana zagaya gurin a kuje. Diyam tace “amma gidan nan yayi kyau, irin sosai din nan fa” yayi murmushi yace “am glad you like it. It will be our Kano home insha Allah. Zamu yi wani a Maiduguri saboda muke sauka in munje, and for Oxford we have to get a bigger apartment dan wanda kuke ciki yanzu yayi mana kadan”. Sai ta dauko wasu takardu ya mika mata sannan ya gyara zama yana kallonta. Ta karanta ta kuma karantawa, ta fahimci cewa wata yarjejeniya ce signed by Aliyu Umar Abatcha cewa ya yafewa Saghir Muhammad Kollere kudaden sa daya satar masa. Akwai saka hannun lawyers dinsa, akwai saka hannun alkalin da yayi waccan shari’ar sannan akwai saka hannun Saghir. A kasan inda Saghir ya saka hannun ya rubuta “thank you”.2 Ta dago da sauri tana kallon Sadauki, sai kuma ta kasa magana. Yaushe Sadauki yayi wannan shawarar? Shin hakan yana nufin Saghir ya fito ko kuwa bai fito ba? Jin bata ce komai ba yasa yace “lokacin da Saghir ya fada min wannan maganar a kanki ba rufe shi nayi niyyar yi ba, zuciyata abinda take gaya min shine in kama shi inyi ta dukansa har sai ya daina numfashi sannan in kaishi daji in ajiye shi dabbobi su cinye shi da rai” ya danyi dariya ganin kallon da take yi masa yace “babu irin imagination din da bana yi that’s why I decided to set a trap for him and luck him up, a hakan zaiyi paying for what he did and he will be out of my reach yadda bazan yi masa lahanin da duk zamuyi dana sani ba. I didn’t know his friend will set him up for drugs. Niyyata shine a lokacin da naji zuciyata tayi sauki a kansa sai in yafe masa ya fito but as fate have it ba wannan ne kadai case dinsa ba, so, har yanzu yana can kamar yadda alkali ya fada har sai an samu nasarar kama abokin nasa kuma sai abokin ya karbi laifin shi ya bashi ajjiyar drugs din” Diyam ta gyada kanta tana kallon Subay’a da take wasa a can nesa dasu sannan take murya can kasa “thank you. Mun gode Allah ya kara arziki” baice komai ba shima yana kallon Subay’a sai zuwa can yace “zanyi kokarin ganin ya fito, dan Subay’a taji dadi. But bazan bashi aiki ba kamar yadda kika bukata daga farko, ruwansa ne yayi hankali ruwansa ne kuma yayi akasin hakan. Na riga nayi magana da Ahmad, duk da dai kamar baya goyon bayan fito da Saghir din but yace zai taimaka min, matsalar shine su iyayen Kabir din sunki vada goyon baya su fadi inda dan nasu yake” ya juyo yana kallonta yace “naso ya fito kafin auren mu, naso yazo ayi dashi dan anan ne zan tabbatar da nadamarsa ko akasin hakan. But it is beyond me dan haka sai bayan biki”.. The Wedding The chance of you dying with COVID-19 is 1% while the chance of you dying anywhere anytime by any means by Allah’s wish is 100%. Wanne ya kamata muji tsoro? Corona virus ko Allah? Then why the panic bayan mun yadda da kaddara munsan komai rubutacce ne?10 Mafita kawai shine mu koma ga Allah mu rungumi Alqur’ani da Azkar, mu yawaita istigfari sannan kuma mu bi dokokin da ma’aikatan lafiya suka kafa.7 Idan Allah ya riga ya rubuta cewa Corona virus itace sanadin mu muna rokon Allah ya karbi shahadar mu (mutuwar annoba shahada ce), idan kuma ba ita bace ba Allah ya bamu rayuwa mai albarka ya dawwamar damu cikin imani Ameen. Allah kuma ya kyautata karshen mu.28 Diyam…………… Diyam taji dadi sosai a ranta. Tabbas ko da Sadauki bai fito da Saghir ba to kuwa yafe masa ma da yayi ya nuna cewa his stone hard heart is now soft. Yanzu ya yi part dinsa ya rage nasa kuma ya taimaka wa Saghir ko yaki duk ganin damarsa ne, taimakon yana da kyau sosai musamman saboda xuri’ar da aka riga aka hada, amma kuma ba wajibi bane ba. Dan haka ba zata sake yi masa magana ko kokarin tursasa shi zuwa haka ba dan in yayi din ya zamanto niyyarsa ta kyautata.3 Tayi masa kyakykyawan murmushi tace “hakan ma mun gode sosai, Allah ya bar zumunci” yace “Ameen, Mrs Abatcha” ta harare shi, “bana so” yace “okay, madam kike so?” Ta mike tsaye kamar zata yi kuka “bana so wallahi” ya mike shima yana mata dariya “gaya min to, me yasa ba kya so?” Tace “sai in ji na zama kamar wata katuwar ƙedara, wai Madam” yayi dariya sosai yana matsowa kusa da ita yace “to me kike so ince miki?” Ta juya ido tace “Diyam” yace “Sadiyam” tayi masa gwalo tace “sholoki” sai ta bar gurin da sauri ta tafi gurin Subay’a tana waigensa. Ya daga murya yace “zan kama ki ne ai, not now but on the 25th” bata waigo ta kalleshi ba but she blushed. Wayarsa tayi kara ya duba sannan ya taho gurinsu yana cewa “time off, Inna ta gaji da jira tasa yar asama ta kira mu” Diyam ta mike straight tana cewa “Allah sarki inna ta, nima nayi missing dinta sosai” ta mika masa takardun hannunta suka tafi Subay’a tana ta fushi wai ita ta dauka sunzo kenan. A kofar gida ya ajiye su yace bazai shiga ba. Subay’a ta fita da gudu tana ta dokin bawa Asma’u labarin sabon gidan da suka je. Diyam ta yi masa sallama zata fita kenan sai ya miko mata wani card ta karba tana dubawa taga credit card ne sai yace “ki dauki kudin da zaki bukata a ciki, ki kuma dauki na su Murja da kika yiwa alkawari” kafin tayi masa godiya sai yace “birth year din ki shine pin din” ta gyada kai tana murmushi, ta sake bude baki zata yi godiya yace “bana son ji. Ko ki fita ko kuma in tafi dake kuma bazan dawo dake ba sai dai a biyo ki da kayan ki”. Bata san tayi missing inna har haka ba sai da ta ganta tukunna, ta tafi da sauri ta rungume ta tana dariya, itama innar dariyar take yi amma sai ta ture ta tana cewa “kar ki karya ni” Asma’u ma ta kankame ta tana cewa “nayi missing dinki, sosai Adda ta” Diyam ta kalleta tace “oh, Asma’u kin kara girma fa. Inna wannan ai itama kamata yayi a hada bikinta da nasu Murja” Asma’u ta fara buga kafa tana cewa “shikenan zaki kunto min ruwa, dama inna kiris take jira ta dawo kaina” ta karashe maganar tana tafiya daki. Inna ta bita da kallo tana cewa “yayanki ne ya daure miki gindi ai, daga ke har shi kun tsaya kuna ruwan ido amma ace yarinya kamar ki har yanzu bata da saurayi?” Diyam dai tana tayi musu dariya saboda ta fahimci wanne yayan ake nufi, shi har yanzu kallon Asma’u yake kamar wata jaririya. Diyam ta lura da chanji a gidan su, an bude part din Ummah an kwashe kayan ciki sannan an gyara shi amma ba’a zuba komai a ciki ba. Ta shiga daki tayi wanka ta shirya tayi sallah sannan ta dawo palo suka zauna cin abinci da Inna, Asma’u da Subay’a da take ta zuba mata hira tana kokarin bata labarin duk abinda akayi a gidan sanda bata nan. Sai Diyam taji tamkar gidan yafi ko ina dadin zama. STORY CONTINUES BELOW Bayan ta kwana biyu ta huta sai shirya da niyyar zagaya gidajen yan uwa ta gaishe su. Inna tace “sai kiyi musu sallama kuma dan ba lallai ne ki sake samun zuwa gurin su ba”. Tare da Asma’u suka fita, gidan Alhaji Babba suka fara zuwa, wannan shine zuwan Diyam gidan na farko kuma taji dadin yadda taga gidan, ba kamar dai nasu nada ba amma kuma basa cikin kuntata. Babban abinda ya kara mata jin dadi shine ganin Alhaji Babba ya chanja sosai ya samu nutsuwa fuskarsa ta saki ta rage nuna damuwa. At last ya daina blaming makiya da sauran al’umma for his misfortune. Da fara’a sosai ya amsa gaisuwar tata har da tsokanar ta da cewa “munji ki shiru har ina tunanin ko sai dai kawai mu daura auren anan in yaso angon ya biki can?” Ta rufe fuskarta tana jin kunyarsa. Sai kuma yayi mata godiyar kudin haya data biya masa sannan ya dora da bayanin neman yafiya a bisa abubuwan rashin adalcin da yayi mata. Ta katse shi da sauri “Alhaji ni na yafe ai, tuntuni na yafe muku tun ma kafin mu rabu da Saghir. Komai ya wuce sai fatan Allah ya kara gyara mana zumuncin mu” yace “ameen” ya dora da “ina son kuma ki sake yi min godiya gurin yaron nan Aliyu. Satin daya wuce naje na gano Saghir kuma ya gaya min abinda yayi masa, ya gaya min ya yafe masa kudaden daya daukar masa” ya fada yana dauke hawaye da babban yatsan sa. “Kudade masu yawa amma yace ya bar masa su. Kuma yace min ya hada shi da lauyoyinsa zasu taimaka masa akan maganar kwayoyin nan. Allah ya saka masa da alkhairi, Allah yaji kan mahaifiyarsa, matar da har ta mutu Allah bai bamu ikon neman yafiyarta ba”. Ta shiga dakin Hajiya ta dauki Muhammad, kyakykyawan yaro har ya warware yana ta shan madarar sa. Sai kuma ta shiga dakin Hajiya yalwati inda acan ne tafi dadewa suna ta hira da Murja da sauran yammatan, suna ta competition gurin farantawa Diyam. A gidan Kawu Isa shima ya karbe ta sosai shi da iyalinsa. Sun jima suna hira yana tayi mata nasiha a game da aure, sai taga kamar wani chance ne ta samu na kokarin gyara tsakanin su da Alhaji Babba. Tace “Kawu, mu kuwa zamu ji dadi idan komai ya wuce tsakanin ka da Alhaji, kune iyayen mu, ta yaya zamuyi zumunci idan ku ba kwa yi?” Sai ya girgiza kansa yace “uwata shi zumunci yi min ne inyi maka, shi Alhaji Babba son kansa da son dansa ne ya jawo igiyar zumuncin sa da mutane duk ta gutsire. Ni fa wai kyautata wa ce na yiwa yaron nan na dauki yarinyar nan nace na bashi ita a daura musu aure saboda in gyara zumuncin da nayi tunanin kamar ya samu baraka, amma kinga sakayyar da ya saka min dashi. Dana je gurin uban na gaya masa ga abinda dansa yayi maimakon ya nuna alhinin sa kuma ya kira yaron nan ya nuna masa laifinsa sai ya shafawa idonsa toka yace shi ba dansa ne yayi ba, ko tambayar yaron ma fa baiyi ba. Yanzu gashi nan ya ga sakayya ai. Ni kuma gashi an barni da yarinya, ni ina ganin na kaita Kollere ta haihu a can ina tunanin kamar na rufe maganar ashe duk jama’a kowa ya sani. Jiya jiyan nan na fito daga masallacin unguwa naji ana maganar. Yanzu waye zai aureta da wannan tambarin? Menene makomar rayuwarta dana zuri’ar da zasu fito daga gareta?” Diyam tayi shiru tana tunani sai tace “Yanzu Kawu zaka hakura idan Saghir ya fito ya auri Suwaiba? Suka bude sabuwar rayuwa suka kuma rike dansu? Zaka yafe masa ka dawo da zumuncin ka da Alhaji?” Yayi shiru yana dan jujjuya kafa sai yace “yaushe Saghir din zai fito?” Diyam tace “very soon, insha Allah” sai yace “Allah ya fito dashi lafiya, abinda zasu yi shida mahaifinsa idan ya fito din shine zai zama tubalin cigaban alaka a tsakanin mu”. A cikin gidan sai Diyam taga bata ji dadin ganin Suwaiba ba duk ta rame, duk da cewa ita mai kiba ce amma yanzu duk ta sirance, farin ma ya ragu amma sai Diyam ta danganta hakan da haihuwar da tayi. Sai da Diyam tazo tafiya sannan Suwaiba ta biyo ta da niyyar rakata sai tace “Diyam kinga Jawad a gidan Alhaji?” Diyam ta gyada kai tana kallon ta, sai tayi murmushi kawai, anan Diyam ta fahimci problem din Suwaiba, kewar jaririnta take yi, sai tace “Diyam naga abban mu ya sakar miki fuska, dan Allah ko zakiyi masa magana ya karbo min Jawad” Diyam tayi shiru bata ce mata komai ba saboda ita dai ba zata iya wannan rashin kunyar ba. Sai dai kuma ta tausayawa Suwaiba saboda tasan zafin rabuwa da ɗa musamman ma wannan da yake dan jaririn da ko nono ba’a barta ta bashi ba. But hausawa sunce idan bera da sata to kuwa daddawa ma tabbas da warinta. Tabbas Saghir yayi laifi amma kuma itama Suwaiba da akwai nata laifin da har ta bari dadin bakinsa da kyawun fuskarsa suka rude ta ta bude masa kafafuwanta yayi mata ciki. Abinda ta shuka ne itama take girba. STORY CONTINUES BELOW Sai Diyam tayi tunani akan lalacewar zumuncin zamani. Babban dalili a fahimtarta shine son kan mu da muke dashi da kuma nuna son yayan mu a fili. Yes, an sani kowa yana son dansa amma hausawa sunce kaso naka ne duniya ta kishi ka kuma ki naka duniya ta so shi. Duba misalin uwa in ta kama danta tana duka idan yayi laifi, sai kuga mutane sun tafi da gudu sun karbe shi a hannunta suna bata hakuri suna kuma lallashinsa. Amma idan da ace zaiyi laifin ta goyi bayansa ta nuna cewa ba laifi yayi ba sai kuga mutane suna yi musu tsinuwa daga ita har shi. Daga nan kuma zasu fara ja baya dasu, zasu yanke zumunci dasu, in yayi laifin ma babu mai kwabar sa babu mai hana shi. Wannan tsarin na daga ni sai yayana shine tsarin daya tarwatsa zumunci. A gidan Mama suka kai har dare. Diyam ta tambayeta shawara akan kayan dakin da zata yiwa su Murja, shin ta siya musu kayan ne ko kuma ta basu kudi kowa ya siya da kansa? Sai Mama tace “ina ganin ki sai musu furnitures, sai kuma ki basu kudin da zasu sai sauran kayayyakin anfaninsu tunda kowa da irin taste din ta” nan suka yanke shawarar irin kayan da za’a siya da kuma adadin kudin da za’a basu. Sannan Mama tace “to ke kuma fa? Menene naki shirin?” Diyam ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannayenta. Mama tace “ba kunya zaki tsaya ji ba fa, magana zaki yi sosai. Dan ba kya gari ne da tuntuni ya kamata a fara yi miki gyaran jiki da sauran abubuwa. Amma tunda kin dawo yanzu zamu fara insha Allah. Kinga akwai tsumin Maman Fareeda shine gatan da ake yiwa ko wacce amaryar da za’ayi aurenta a yanzu, ko matan auren ma zasu iya amfani dashi, very pure and natural babu algus. Ga number dinta nan zan baki ki kirata kiyi order zata kawo miki har gida kiyi ta sha kuma sai ki ajiye number din daga baya ma kya cigaba da karba” ta karantowa Diyam number din kamar haka “07033742833”.2 Sai kuma ta nemi Diyam ta sanarwa da Sadauki cewa zasu zo ganin gida ita da Aunty Fatima dan su san yawan kayan da za’a siyo. Amma da daddare da Diyam tana waya da Sadauki ta gaya masa sai yayi dariya yace “wanne kayan za’a siyo? Ki ce musu suyi hakuri nayi musu shigar sauri har na bayar da order kayan gida gabaki daya, za’a sa komai da komai, sai dai in an gama sakawa sai suzo su gani in akwai gyara suyi mana” da Diyam ta gayawa inna sai ta kama fada “wannan wanne irin abu ne? To wannan kudin da suka kawo a cikin jaka kuma me zamuyi dashi?” Rumaisa tazo har gida suna maganar gyaran jiki da Diyam. Tace “akwai Hajiya Hannatu Sokoto, mutuniyar Sokoto ce amma ta zauna a sudan dan haka ta iya gyaran jiki sosai kuma duk kayan ta ma daga sudan take zuwa da abinta, nima wata matar abokin abban Najma (babynta) ce take bani labarin ta, aikinta akwai tsada dan matan manyan mutane kadai suke iya hiring dinta amma kuma fa akwai kyau dan saita mayar dake tamkar jaririya, Sadauki kuwa in ya shigo hannun ki to kuwa ya kade har ganyensa” ta karashe maganar tana dariya. Diyam ta dungure ta, sai kuma tace “to kisa a hada ni da ita mana” Rumaisa ta harare ta tace “au, na dauka ai ba kya so”. Tunda aka hada Diyam da Hannatu Sokoto shikenan komai ya chanja mata, matar ta karbi kudade da yawa a gurin Diyam amma fa tana fara aiki akanta, Diyam tasan cewa she is worth it. Kullum sai tazo kuma kullum da kalar gyaran da take yi wa Diyam. Tun daga kan gashin kanta zuwa faratan yan yatsun hannayenta da kafafuwanta babu abinda gyaran bai shafa ba. Yau a shafe ta da wancan a wanke da wannan gobe a saka ta tsugunna akan wancan turaren jibi kuma a bata wannan ace ta liƙa ta kuma yi tsarki da wancan. Gata kuma a jika ta gabaki dayanta a wanke ta. Har bakin Diyam sai da akayi masa gyara na musamman yadda zai bada wani sihirtaccen kamshi. Ga kuma tsumin maman fareeda (07033742833) da Diyam ta kira aka kawo mata shi har gida, wanda tana sha sau daya ta tabbatar wannan bana wasa bane ba dan haka tayi wa number din kyakykyawan ajiya dan gaba.1 A gefe guda kuma tayi dinkuna na fitar biki. Duk da dai ita har yanzu tana nan akan bakanta na cewa ba zata yi taro ba, wanda inna zata yi kawai ya wadatar. Sadauki kuma a nasa bangaren baya samun zama sam. Kullum yana cikin zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Kano. Family dinsa duk sun taho daga Canada suna Maiduguri suna nasu shirin. Kamar yadda Murjanatu ta fada, lokacin da suka gabatar masa da jerin events din da suke son yi na biki sai yace “no, kuyi parties dinku ku kadai amma ni ba za’a fitar min da mata ana tallata ta a duniya ba” duk suka juya suna kallon Murjanatu ita kuma ta daga kafada tace “I told you so”. Abinda kawai Sadauki ya yarda za’ayi shine wushe-wushe, wanda yake bikin al’ada na kanuri. Sai mother’s eve da Mama zata yi washegarin kai amarya dan a nuna wa yan uwa amarya itama kuma ta san su. STORY CONTINUES BELOW On impulse Diyam ta kira Humairah, matar yayan Bassam ta tuna mata zancen bikinta. “Ban sani ba ko zaki samu zuwa?” Humairah tace “what are you talking about? Zan zo mana, ai ina lissafe da lokacin dama already na tambaya har an barni ma. Insha Allah kwana ma zanyi tare dani za’a kai ki gidan Mr Abatcha” sun jima suna hira sannan suka yi sallama. Ana bugo kati Diyam ta sake tura mata, sannan kuma ta tura mata na daurin aure tace “ki nunawa Bassam ko zai samu damar zuwa”. Satin biki yazo, su Mama sunje sunga gidan Diyam kuma babu abinda suka gyara saboda babu abin gyarawar, sai dawowa da sukayi suna rike baki suna bada labarin aljannar duniyar da suka gani. Mama tace “har Subay’a anyi mata dakinta, da set din gadonta da komai na bukatar ta”. Ranar talata Diyam tayi baki, Sa’adatu, Falmata, Fanna da Adama gabaki dayan su da akwatinan su “tunda yaki yarda muyi dinner da luncheon da bridal shower da cocktail party gwara mu dawo gidan su amaryar mu zauna muyi ta kallonta” inji Murjanatu tana turo baki. Diyam tayi murmushi tana taryen su with open arms, da alama shi kansa yayan nasu bai san da zuwan su ba tunda bai gaya mata ba. A ranar ne sauran sisters din Sadauki suka fara ganin Diyam a zahiri, gashi kuma dama tasha gyara sai abun yayi musu duka biyu. Adama tace “gaskiya pictures basa yi miki adalci Diyam, you are much more beautiful in person” Murjanatu ta kama hannunta tana shafawa tace “what’s the secret? So kike ki kashe min yaya na ko?”. Part din Ummah Inna tasa aka shirya musu aka yi musu shimfidu aka saka musu duk abubuwan bukata sannan aka kai musu kayansu can suka sauka. Sai Diyam itama ta koma can tare da Subay’a da Asma’u suka barwa Inna da yan uwanta da suka fara zuwa daga Kollere part dinta. Wasa wasa sai ga gida yana kara cika. Kusan duk wanda yazo daga Kollere sai yace a nan zai sauka, da Asma’u ta tambayi wata mai yasa basa tafiya gidan Alhaji Babba shi da yake auren yaya hudu? sai tace “haba yar nan, kowa ai yana son dan maiko maiko ko?” Jin haka yasa Inna ta aikawa da Hajiya yalwati kudi da kayan abinci tace saboda baki. Kamun amare (su Murja) an saka shi ranar Alhamis, juma’a kuma angwaye sun shirya dinner su da amaren su da kawayen amare. Assabar za’ayi daurin aure, wanda shine za’a hada dana Diyam, Alhaji Babba ya bawa Kawu Isa waliccin yaran duk su hudun shi kuma zaiyi waliccin Diyam. Ranar assabar din ne kuma za’ayi yini sannan da daddare akai amare. A bangaren Diyam kuma babu kamu, babu dinner, sai wushe-wushe ranar friday sai daurin aure assabar da safe sannan inna tayi yinin ta anan gida da daddare kuma akai amarya. But, ranar laraba sai ga mutane daga Maiduguri wai sunzo kawo kudin cin-cin, aka tarye su sosai aka kuma karrama su amma kuma akayi ta mamakin wannan al’ada ta cin cin. Mama tace “to yanzu cin cin din zamu zo mu soya ko kuma me?”. Alhamis da safe Hannatu Sokoto tayi wa Diyam kunshi ja da baki mai dan karen kyau, sannan kuma tayi mata kitso shuku kanana kanana, duk a cikin aikinta ne. Da yamma Diyam ta shirya tayi simple kwalliyarta cikin atamfa riga da plain zani ta dauki in-laws dinta suka tafi gidan aunty Fatima inda a can ne za’ayi kamun wadancan amaren. Amma Diyam tana zuwa sai kallo ya koma sama, kowa ya kalle ta sai ya sake waigo wa “wai Diyam ce wannan?” “Diyam ke ce kuwa?” Har sai data gaji dan haka kafin a gama ma ta gudo ta dawo gida. Tun a daren Sadauki ya gaya mata zasuyi baki washegari. Washegari Friday, da wuri Humairah tazo gidan, hakan ba karamin faranta ran Diyam yayi ba. Suka hadu da Rumaisa, Rufaida, su Murjanatu da kuma Asma’u. A ranar Kasusu (yan uwan ango) suka zo gari, gidan Alhaji Bukar suka sauka, daga nan kuma suka taho gidan su Diyam kawo kayan gaisuwar uwar amarya. Set guda akayo wa Inna na kaya tamkar wanda aka hado mata lefe, sai kuma kayan kunshi iri iri wadansu ma ko sunan su su Inna basu taba ji ba. Su kuma anan gidan suka hada musu goma sha tara ta arziki na nau ikan kayan ciye ciye, fura da nono kam ba’a maganar ta saboda tambarin su na fulani, sai gurasa ita kuma shedar su kanawa ne, sai kuma sauran abinciccika da kala kalar nama da drinks har sai da suka ci suka bari suka kuma yi takeaway. Da zasu tafi suke tsokanar su Sa’adatu “wato dan kunyi yaya shine kuka tare anan? To sai ku bita har gidan mijin kuyi mata zaman daki” Asma’u tayi saurin cewa “nice yar zaman daki ai”. STORY CONTINUES BELOW Daga nan kuma sai aka fara shirye-shiryen wushe-wushe (bangajiya). A gurin taro na Meena event center anyi decorating gurin da traditional costume na barebari. Falmata, wadda take registered beautician ita ce ta zauna ta tsarawa Diyam kwalliya sannan suka nannade ta da flowery laffaya mai kalolin red and blue. Su kuma yammatan duk sunyi kwalliyar blue shadda da akayiwa dinkin riga three quarters da skirt, sai kuma suka yafa jan mayafi. Duk abinda suke yi Diyam tana jin sune kawai, amma ita hankalinta yafi tafiya ne akan murnar yau zata ga Sadauki, dan rabonta da ganin sa tun ranar Monday daya tafi Maiduguri zai taya Papa shirye shiryen saukar bakinsa da zasu zo daurin aure.2 Bayan magrib motoci suka zo akayi ta diban mutane ana kai su, kowa cewa yake yi zaije saboda kowa yana son yaga wannan al’ada ta barebari sannan kuma kowa yana son cin dadi. Lol3 Sai da aka gama kwasar mutane saura Diyam da yammatan ta sannan Sadauki yazo daukan ta. Aka kawo kuma wata motar da zata dauki kawayenta. Ya kira ta yace ta fito su tafi, ai kuwa duk su fanna suka taho rakiya da kuma tsegumi. Suka hango motar daya zo da ita, tun daga motar suka fahimci cewa yau a shiryen sa yake, Al- Mustapha ne a seat din driver, kuma dama yana daga cikin samarin Murjanatu dan haka ta bude seat din kusa dashi ta zauna. Diyam kuma aka bude mata baya inda Sadauki yake zaune ta shiga ta zauna kusa dashi aka rufe kofar. Adama ta zagaya side din da yake tayi knocking window, ya sauke glass yana kallon ta yace “ya akayi?” Tace “yaya Aliyu dan Allah in shigo? In zauna a tsakiyar ku kaga waccan motar kamar ba zata ishe mu ba” ta karashe maganar tana kokarin yin dariya, bai ce mata komai ba sai tayi winding up glass din yana murmushi yace “yaran nan so suke su mayar dani kakan……” Sai kuma maganar ta makale ya kasa kammalawa saboda juyo wa da yayi suka hada ido da Diyam da take kallon sa saboda kyawun da yayi mata ko kuma maybe dan bata saba ganin sa da manyan kaya bane ba?. Bakin sa ya motsa a hankali amma Diyam bata ji mai yace ba, sai ta tambayeshi. Yace “tasbihi nake yi ga Allah, mahaliccin kyawawan surori” ta sunkuyar da kanta tana wasa da hannunta sai yabi hannun da kallo, idanunsa suka sauka akan tsararren kunshin da yake kwance akan farar fatarta. Yace “wadda tayi kunshin nan ko nawa aka biya ta taci kudinta” Diyam tayi masa fari da ido tace “harda kitso tayi min” yace “may I see it?” Ta makale kafada tace “not today” yace “gobe ne dai kadai ta rage min. Amma ban sani ba ko zan kai goben? Dan wannan abin da kike min da ido bana jin zai barni in yi bacci yau” dariya suka ji Murjanatu tayi daga gaba, Sadauki ya kalle ta yace “ko kiyi shiru ko kuma a sauke ki ki hau napep” Al-mustapha ya dan waigo yace “amarya, ni ko gaisawa ma ba’a bari munyi dake ba” Sadauki yace “hey! Juya ka kalli gabanka, don’t go about looking at something that is not yours” Murjanatu tace “an fara, yau zanga yadda za’ayi wannan taron” Sadauki yace “kinyi shiru ne ko kuma ayi packing ki fita?” Al-Mustapha yace “in ka sauke ta sai dai ka zagayo ka ja motar ka da kanka” Diyam dai tana jinsu tana ta murmushi. Ita kanta tasan tayi kyau kuma tasan yau za’ayi rigima da Sadauki duk kuwa da cewa komai nata a rufe yake fuskarta da hannayenta ne kawai a bude.3 Suna packing ya miko mata hannu yana murmushi, ta makale kafada sai ya langwabe kai yace “Please” sai ta saka hannunta a cikin nasa, ya juya hannun sannan ya saka fingers dinsa a tsakankanin nata yana kallon yadda hannayen nasu suka yi kyau sosai together, perfect match for each other, kamar dama a haka aka halicce su. Suka fita suka jera a tare suka tafi gurin da aka tanada saboda su, Diyam idanuwanta a kasa tana jin tsananin kunyar mutanen gurin. Tun daga bakin mota ake turara su da turaren wuta iri iri masu kamshi kala kala har suka je suka zauna sannan aka sake zagaye su da turarukan wuta. Nan take aka fara gabatar da shagali wanda ita Diyam ba fahimta take yi sosai ba saboda hannun da yake rike da nata kuma tayi dabarar kwacewa ta kasa. Ga kuma idanuwa guda biyu a kanta suna kallon duk wani motsi nata. Ta dan kalle shi tace “hey…….stop looking at me like that” ya daga gira yace “ko? Saboda me? Baki san ni maye bane ba? Ko baki da labari?” tayi murmushi tace “kar ka bari Inna taji ka” yace “am serious fa, kin dauka wasa nake yi ko? Ina tausaya miki ranar da zaki fahimci a inda tawa maitar take” ta sake kokarin karbar hannunta ta kasa. Yace “wannan hannun tunda kika bani shi kuma ya zama nawa, sai sanda nayi niyya zan baki aron sa” ta sake cewa “ni ka daina kallo na” ya bata rai yace “ba fa ke nake kallo ba, lips dinki nake kalla wondering what they taste like” taji kamar zata nutse a gurin, tace “wayyo Ummah”.1 Anyi rawa sosai, rawar barebari, yan’uwa da abokan Sadauki ne suka fara yi sai kuma na Diyam sukayi joining dinsu suna koya, sai kuma suka koya musu suma irin tasu rawar ta fulani. Amma Diyam ko motawa daga seat dinta Sadauki bai bari tayi ba ballantana ta saka ran yin rawa. Duk wanda yazo gurin su daukan hoto kuwa indai namiji ne to Sadauki zai ce masa “zagayo ta side dina” sai suyi dariya gaba daya. And Diyam wondered, anya kuwa Sadauki zai barta ta koma school?2 Sai after 11 suka tashi, shima dan dare yayi ne ba wai dan sun gaji ba. Da kyar Sadauki ya bar Diyam ta shiga gida, shi ji yake kamar su yi ta zama a mota har gari ya waye, gani yake kamar gobe ba zata yi ba. A ranar duk su biyun babu wanda yayi bacci. Kwanciya suka yi da wayoyinsu a kunnuwansu suna bitar rayuwar su, yarintarsu, rabuwarsu, da kuma sake haduwarsu. Diyam ta bashi labarin sanda take lekensa ta window lokacin da Saghir ya kawo shi gidan su. Yace “ohhhh, ashe shi yasa naji kamar zan fadi, ashe idanuwa ne suka yi min yawa”. Sai da dare ya raba sannan suka yi shawarar gabatar da salloli da addu’ar neman alkhairi a cikin sabuwar rayuwar da zasu shiga gobe. A kan sallayinsu suka karasa kwana. Sai da suka yi sallar asuba sannan Diyam ta kwanta, amma kuma ba wai bacci tayi ba likimo kawai tayi tana jin su Humairah dasu Murjanatu suna ta hirarrakin su suna dariya har gari ya waye. Bata tashi ba sai da Hannatu Sokoto ta zo ta tashe ta tana cewa “gwara da kikayi baccin ai, shi bacci yana kara fito da kyawun mutum” sai ta ajiye mata special dahuwar kazar da tayo mata daga gida, ta zauna ta cinye tas sannan ta kora da tsumin maman fareeda (07033742833), tana ci suna hirar su da Humairah suna kuma jiyo hayaniya a tsakar gida maza suna ta shirye-shiryen tafiya daurin aure. A lokacin Bassam ya kira Humairah ya gaya mata ya shigo gari amma ya zarce venue din daurin auren, Alfurqan Mosque.2 Kafin ta gama Hannatu Sokoto ta shirya mata ruwan wanka dan haka ta shiga tayi wanka tafito, tana zama a gaban mirror message din Sadauki ya shigo wayarta.5 Dear Mrs Abatcha Alhamdulillah I’m now yours and you’re mine Sighned mrs abacha Ai mun gama ko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *