DIYAR FARI COMPLETE
Au bazakiyi shiru ba? Inji mama ana magana kina magana? Wallahi ranki zai b’aci idan bakiyi shiru ba
Matar Dake zaune a falon ce tace Hadiza wallahi ko kaffara babu kece dalilin lalacewar Raeesah, au anti salma haka zakice? Toh babu damuwa 😔 kwallace ta fara zubowa daga idanun Hadiza wacce kuka baya mata wahala
Chan sai anti salma tace Hadiza ba wai na fad’i haka bane domin na saka ki kuka amma gaskiya yarinyar nan tana so tafi karfin mutane! Sai anyi da gaske kafin a samo kanta inji anty salma ,
Hadiza tace Toh anty salma yaya zanyi da Raeesah wacce mahaifinta ya gama b’ata ta kuma gashi yanzu ta fara girma kuma abin babu sauqi sai na Allah . Idan na ce Raeesah tayi min abu batayi sai na dura mata zagi kafin take jin magana ta fada tareda nuna Raeesah wacce ta tsaresu da ido tana jin duk abin da suke fad’a
Hadiza ce tace Toh ki wuce ki tafi islamiyya idan ba haka ba sai na sab’a miki mara kunya kawai!
Raeesah: toh maman hauwa amma kinsan dai bani da tajweedi kuma kince zaki bani kud’i na siya
Hadiza: wai ba last week aka siya ba Toh bazan qara siyan waniba
Raeesah: maman hauw! Kafin ta qarasa Hadiza tace ya akayi kika b’atar da wanda aka siya last week? Raeesah tace: maman hauwa wallahi wata yarinya ce ta yagamin amma nima na yaga nata subhanallah inji Hadiza tana dafe kanta 😂
Raeesah! Ashe duk fad’an da nake miki ba kya ji ? Ashe bazaki shiryu ba? Ashe bazaki natsu kisan mai kikeyi ba? Toh Allahu ya shiryeki ya da ki zamu daga cikin shiryayyu inji Hadiza wato mahaifiyar hauwa (Raeesah). Sannan ya dauko N500 ta bata tana fadin kuma ki dawn min da chanji na sannan dan Allah Raeesah I’m advising you in advance please and please banda tsokana banda cin zali , Banda zagin malamai Dan Allah.
Anty salma ce tace Toh Hadiza idan kum gama dramar ke da yar ki toh ni na tafi sai gobe ,Toh anty salma a gaida yaran da maigidan muma munanan zuwa InshaAllah . Anty salma ta bud’e kofar falon ta fita cikin hanzari
A hanya kuwa fad’i take “haba yarinya babu natsuwa sai rashin kunya da rashin ganin girman na gaba da ita sai fitina ta addabi kowa gida da waje babu mutunci wallahi da za,a kawo min ita gidana tayi sati daya Toh data shiryu don wallahi sai na yi mata horo irin na yarabawa inji anti salma .
Toh fah 😂🤣
Pls show me some love and vote
Love ya oll 💗 also encourage me by commenting
Next page who is Raeesah?+Alhaji Abubakar Dan kwambo sunan sa, a garin lagos yake harkar kasuwancin sa amma shi haifafen kano ne, bai damu da karatu ba hakan ya sa ya fara kasuwanci domin ya tsirq da kansa da iyalensa yana da mata Guda biyu hajara da hauwa kuma Allah ya albarkace shi da yara guda uku hassan da hussaini ta bangaren hauwa sai Aminu ta bangaren hajara
Yaso ya d’ora yaran nasa a harkar kasuwancin sa amma sam Husseini yace shi makaranta zaiyi domin yanzu ilimi shine a gaba yacewa baban nasu Alhaji Abubakar. shi kuma hassan ya yarda da kasuwancin tareda dan autan su Aminu.
Wannan ahali sun taso cikin farinciki da tausayin na qasa da kuma girmama na gaba sannan matan Alhaji Abubakar basusan menene kishi ba kansu a hade yake kuma suna bawa junansu girma sannan ga taimakon juna .
A cikin lokaci qanqani hassan da aminu suka fara gane komai da baban su yake nuna musu ta b’angaren kasuwancin sa,
Shi kuwa Hussein yayi nisa a karatunsa gashi ma next year zaiyi graduating , ya kasance mutum ne mai fasaha ga koqari da kuma kwazo kuma ya taso yana son mahaifiyarsa hauwa da kuma kishiyar ta hajara.
~ ~ ~ ~ ~
A halin da ake ciki yanzu Alhaji Abubakar ya miqa dukkannin kasuwancin sa ga y’ay’ansa Hassan da Aminu domin ganin tsufa yazo masa bazai iya Ci gaba da juya dukiyar sa ba amma amfannin haihuwar kenan tunda yana da masu kula da dukiyar tasa.
Shi kuwa Husseini a yanzu ya zama graduate harma a yafara neman aiki kuma ciki ikon Allah ya samu aiki a kaduna Toh annan ne ya hadu da Hadiza Muhammad ya fara soyayya da ita . Saidai yana zuwa kano lokaci zuwa lokaci yana duba iyayen nasa da kuma y’an uwansa
Saidai hankalin mahaifinsa a tashe yake don ganin tsufa yazo masa gashi kuma babu wanda yayi aure daga cikin y’ay’an sa abin dake qona masa rai kenan idan ya tuna
~~~~~~~~~~~~
A lokacin da Husseini yaje ganin iyayensa ne babansu yayi musu magana akan kowa ya nemi mata ya aura domin yafiso yaga aurensu kafin ya bar duniya inji mahaifinsu Alhaji Abubakar
Toh fa babu wani b’ata lokaci aka aika kaduna domin neman auren Hadiza sannan hassan da aminu kowa ya nemi matar aure kuma an basu
Farin ciki ne ya cika Alhaji da godiya ga ubangiji Daya sa zaiga auren y’ay’ansa Hassan Husseini da Aminu, cikin qanqanin lokaci aka daura auren su aka kuma kaiwa kowa matarsa wanda dama shi Husseini a kaduna yake da zama saboda aiki . Hankali Alhaji ya kwanta saidai kash ya tsufa sosai ko fita baya iya yi saboda ciwon qafa dayake damunsa
~~~~~~~~~~~
Shekaru biyu kenan da auren y’a’y”an Alhaji Allah ya albarkace su da haihuwar y’ay’a hassan matarsa ta haifi y’an biyu basma da basman Aminu matarsa ta haifi namiji mai suna Ibrahim khaleel, Husseini ne dai haryanzu Hadiza matarsa bata haihuba amma tana nan da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe!
A yau Monday 8th August Allah ya sauki Hadiza ta haifi y’arta mace kyakyawa ga idanuwa ga kuma hanci duk da mutane suna cewa kamannin babantane amma dai Babyn tana da kyau.
Tirqashi…… a wannan safiya da Hadiza ta haihu ne hassan ya kira Husseini domin sanar mai da rasuwar mahaifinsu. INNALILLHI WA INNAILAIHIRAJIUN …. abin da yayi ta maimai tawa kenan yana mai zubar da kwalla yana cewa Allah ya gafarta maka mahaifina yasa ka huta. Gaban Hadiza ya fadi wacce ke riqe da jaririyarta tana fadin mai ya faru? , nan ne ya shaida mata cewar babane ya rasu kuma ya kamata ya tafi kano a yau domin janaizar babansa.
Abu dai biyi dadi ba duk da ita mutuwa dolece ga mai rai Toh babu yanda za,ayi . Husseini yayi wa jaririyar hud’uba da sunan mahaifiyar sa Hauwa , sai hadiza ta fad’a cewar za,a dinga cewa yarinya Raeesah .
+
Wannan shine asalin Raeesah D’iyar fari
Is your girl Zubaidahn Gaddafi
Show me some love by voting and comments also 😘 love you oll 💗~~~~~~~~~~~~~
Raeesah dai ta taso cikin jin dad’i da kulawa daga wajen uwa harma uba sai dai Husseini mahaifinta yafi sonta da shagwab’ata kasancewar ita kadai suka haifa kuma sunan mahaifiyarsa gareta
Sai dai wasu lokutan Hadiza batason yadda shi Husseinin yake b’ata Raeesah
Gashi yanzu bata jin maganar kowa kuma bata sauraron kowa sai rashin kunya da kuma wauta irin ta y’ay’an fari😉
Ahalin yanzu Raeesah ta kai kimanin shekaru 19 amma har yanzu batasan mai takeyi ba kuma batasan inda ta dosa ba domin ita daukar kanta take amatsayin qaramar yarinya saboda yanda babanta yake shagwab’ata kuma a kullum yake gayamata ita kyakyawace
Wannan shi ya sa take qara yiwa mutane wulaqanci da rashin mutunci da kuma nuna cewa ita ba ajinsu bace da rashi kunya da kuma sakarci irin nata na y’ar fari
Batajin storon kowa, haka a islamiyya ma takeyiwa malamai rashin kunya hatta ma d’alibai bata barsu ba duk wanda ya gayamata mutuwar uwarshi sai ta gayamasa na ubanshi (hausa proverb)😉
Gashi yanzu da taga ta kammala secondary school dinta koh islamiyyar ma bata zuwa
Amma ba da son mahaifiyar ta Hadiza ba domin tafison y’ar tata da ta samu ilimin addini kodan gaba da kuma lahira
Sai dai yanda rai yakeso ba haka yake samuba
Inji Hadiza
~~~~~~~~~~~
qarfe takwas na safe 8:00
Hadiza ce ke magana kamar haka: abban Raeesah ya kamata ka san abin da zakayi akan yarinyar nan domin koh islamiyya fah bata zuwa kuma gashi yanzu ta gama secondary school Toh mai zai hana ta ci gaba da karatu? Idan kuma ba haka ba toh gaskiya ayi mata aure tunda ta isa aure shekara goma sha Tara! Koh kuma a sakata a catering school ? Saboda Raeesah babu abin da ta iya ..
Hadiza ita kad’ai taketa maganar ta shi kuwa abban Raeesah yana ta kai laumar dankali ko kulata baiyi ba domin duk abin da take fada basu gamsar da shi ba ita kadai take ta surkullen ta 😂…..
Sai da ta fuskanci ba ta ita yake ba sannan tace wai abban Raeesah ba da kai nake ba?
Toh maman hauwa mai zance?
Au me zakace?
Shikenan tunda baka da abin da zakace mstwww.. ta ja tsaki sannan ta juya ta b’ata rai
Saida yaga alamun ranta ya b’aci matuqa kafin yace: maman Hauwa kiramin mamana
Sannan ta saki rai ta tashi ta nufi inda d’akin Raeesah
Kai tsaye ta shiga ta ga ashe koh tashi batayiba gashi yanzu 8:29
Yanzu da haka yarinyar nan koh sallah batayiba! inji Hadiza
Dagewa tayi ta kai mata duka a baya tana fad’in tashi dan ubanki wani daren za,a qara miki?
Bargo Raeesah taja tana fadin : haba maman hauwa yanzu fah aka kira sallah ki bari na d’an kwanta ….
Inji ubanki toh 8:29 yanzu wallahi koh ki tashi koh in watsa miki ruwan sanyi
A firgice ta tashi saboda taji an ambaci ruwan sanyi 😅 sanan maman hauwa tace idan kin gama abbanki yana jiranki a dining
Toh tace sannan ta fad’a toilet da kayan bacci tayi wanka sannan ta d’auro alwala tazo ta bud’e wardrobe dinta ta dauko wata baqar riga doguwa tayi sallah sannan ta shafa mai ta hau shafa hoda sannan ta sanya red lipgloss kafin ta fito .
Shigowar ta falon ne ya katse musu hirar da sukeyi
Zama tayi kusa da abban nata sanna tace abba ina kwana ya amsa da lafiya mamana kin tashi lafiya tace lafiya
Maman Hauwa ina kwana itama ta amsa da lafiya Raeesah ya bacci ya chatting?
Ran Husseini ne ya b’aci dayaji wannan sannan yace a,a maman Hauwa banason irin wannan tambayar da kikeyiwa yarinyar nan bai kamata ba . Toh dole in tambayeta ya chatting saboda wannan yarinyar idan ta fara chatting tun 8:00pm sai takai har 2:00am batayi bacci ba saboda Maita 🤔 inji Hadiza
Magana ya fara da cewa mamana na kiraki ki ne domin inji ta,ra,ayin ki wai shi makaranta kikeso kici gaba kokuwa aure kikeso? Kokuma kinaso a saka ki a catering school? Wanne kikeso daga ciki ?
Cikin muryar kuka ta fara magana abba aure kuma? Toh ni na isa aurene? Kumama ai idanma auren ne toh wa zan aura ? Ta qarasa maganar tana kuka .
Toh Toh… mamana dan Allah ki daina kukan nan banason gani ki daina! Shikenan yanzu idan kin karya zamu je a kaiki catering school inda zaki koyi girki da kuma abubuwa da dam ai kina so koh?
Eh! Abba d’an dama dama wannan..
~~~~~~~
Hmmmm inji maman Hauwa ana ganin abu anan , oh oh naga ta kaina ni dije 🤦🏻♀️.
~~~~~~~~~~~~~~~~~
Yau ranar Farko da zata fara zuwa lesson anci sa,a ta tashi da wuri
Tun 6:30 ta tashi ta fara shiri, ta sha doguwar riga domin yawancin kayanta gowns ne
Tayi kyau simple makeup tayi sannan tayi rolling pink gele ta dauko takalmi ta saka sannan ta fito falo
Abbanta ta tarar zaune kan doguwar kujera yana jiranta , sallama tayi tana fadin abba good morning: abba yace morning mamana
Hope you sleep well? Yana tambayarta
Ta amsa tareda cewa abba ina maman hauwa ?
Tana kitchen tana yi mana breakfast.
Allah sarki maman Hauwa akwai qoqari inji Raeesah 😊
Amma gaskiya abba ya kamata a samowa maman hauwa mai aiki ta dinga tayata aikin gida
Toh mamana ai ita ta qi tun lokacin da mukayi aure da maman ki naso a nemo mata mai aiki amma sam tace bataso ,
Sallamar Hadiza ce ta dakatar dasu daga hirar tasu. Maman hauwa ina kwana
Lafiya qalau Hauwan mama da fatan an tashi lafiya
Haka sukayi breakfast cikin jin dad’i da annashuwa har suka gama
Wayar abba ce ta fara Ringing ya amsa tareda sallama yana cewa d’an uwana da fatan ka tashi lafiya? Lafiya qalau inji Hassan
Abba yace toh ya yaran duk qalau? Lafiya qalau inji Hassan : ina Raeesah da mamanta duk suna lafiya abba ya amsa
Muryar Raeesah ce tana fadi uncle Hassan good morning ina sister basma da yaya basman ?suna lafiya inji Hassan sannan ya yanke wayar
~~~~~~~~~~~~~
Hikma catering school wanda yake badarawa kawo district kaduna Abba yayi parking sannan ya juya yana kallon Raeesah yana cewa: mamana pls and pls ki natsu ki san mai kikeyi dan Allah banda rashin kunya always do what you were ask to do Allah yayi miki albarka
Ameen tace sannan ta fita shi kuma ya wuce office.
Shiga tayi class din inda taga wata mata a tsaye tana jawabi
Toh ikon Allah harda maza a wajen koyan giki da snacks? Abin da ta fad’a kenan a zuciyar ta
Ni Zubaidah a ganina ina ruwanki? Banda neman magana 😂
Zama tayi tana kallon abin da matar takeyi fish roll ake had’awa a yau Toh dama abba ya siya mata duke wani abu da ake buqata a lesson din
Daga zuwanta har ta fara surutu da wasu y’an mata guda biyu Asmau da Ihsan sunata chatting a class suna dariya
Ikon Allah har sun saba gashi yanzu an gama lesson kowa ya nufi hanyar gidansu
Kash tace na manta gashi Asmau da Ihsan sun tafi amma ban karb’i numbern su ba Toh saidai gobe in Allah ya kaimu.
~~~~~~~~~~~~
A kwana a tashi Raeesah har tayi wata shida da fara catering kuma wannan shine watan qarshe za,a basu certificate dinsu na six months . Domin a halin yanzu Raeesah ta iya abinci kala kala snacks kuma babu wanda bata iyaba, kama daga kan abincin hausawa harma dana turawa duk ta iya
Yanzu ma bata barin maman hauwa ta shiga kitchen komai ta iya .
Raeesah ta fara hankali inji Hadiza tana gayawa yayarta anty salma wacce ke zaune a hayin malam Bello da tazo musu ziyara , anty salma tanada yara guda biyu Abdullahi da zee duk sun girmi Raeesah , mijinta kuma lecturer ne a kaduna state university (KASU).+
+~~~~~~~~~~~
qawance mai qarfi ne ya qullu tsakanin Raeesah, Ihsan da Asmau kamar wasu yan uwa na jini
Raeesah ta kan kai musu ziyara suma kuma suna kawo mata, suyi ta hira kamar kar su rabu
Da Asmau da Ihsan suna yawan bada labarin samarinsu Kowa ta fad’i abin da saurayinta yake mata amma banda Raeesah domin ita bata tab’a tsayawa da wani namiji ba da sunnan soyayya
Saidai tayi shiru tana jinsu kamar bata wajen
Kokuma tayi tsit kamar an ajiye dutse .
Wani lokaci ma Asmau ce mai yi mata ba’a tana ce mata : wai ke haryanzu babu ma shinshini ne? Kokuma meh! Dariya kawai Raeesah take sannan kuma ta d’auko wata hirar, domin ita sam bata so ayi mata maganar saurayi kokuma aure
Wani lokacinma a wautarta kira takeyi bazatayi aure ba 🤔
Ranar asabar misalin qarfe 2:00 na rana Raeesah na gida tana kwace a d’aki ita kad’i ta rasa abin da yake mata d’ad’i gashi daga ita sai maman hauwa a gidan babu wanda zatayi fira saboda maman hauwa bata ciki zama tayi fira da D’iyar tata ba, har gwara Abba yakan yi fira da ita harma ya bata labarin kakanin ta na kano da kuma irin gwagwar mayar da suka sha wajen kasuwanci da kuma neman halal d’insu.
Tashi tayi ta fad’a toilet tayi wanka sannan tafito ta shafe jikinta da mayika masu qamshi ta kuma shafa turaren jiki
Sannan ta bud’e wardrobe ta dauko wani brown lace da uncle Hassan ya bata lokacin birthday d’inta na shekara sha tara , mayafi ta dauko shima yayi daidai da kalar lace din. Kwalliya kad’an tayi ta dauko red lipgloss ta sa tayi kyau sosai kamar xata biki.+
~~~~~~~~~~~~
D’akin maman hauwa ta shiga ta tarar da ita tana waya da umma , Raeesah bakin ta ta kai kusa da wayar tana cewa tsohuwa mai farin gashi har yanzu baki aikomin da yajin kalwar ba! Toh wallhi zance kakana ya koraki gidanku
Dalla can inji maman hauwa banason wulaqanci mamana kike gayawa haka, ta kashe wayar ina zakije? Gidan su ihsan a dawo lafiya kuma karfe shida ki dawo, Toh maman hauwa InshaAllah zan dawo da wuri
Sannan ta sa kai ta tafi , mamaki ne ya cika hadiza tana fad’in: Wanda Allah ya shirya shine cikakken shiryayye wanda Allah ya B’atar babu mai iya shiyashi
Sab’anin da idan tayiwa Raeesah magana bata yi mata biyayya amma yanzu gashi tana jin magana harma tana taya ta aikin gida, gaskiya na yarda da yarinta ne yake damun Raeesah amma yanzu ta girma hankali ya fara zuwa mata kuma yanzu ta daina iya shege da sakarci irin na y’an fari.
Wayarta ta ciro daga cikin jaka! Lambar Asmau tayi dialing…..
hello…..
naam….
Babe how far? Kina gida ?eh! Toh dan Allah mu had’u a gidan su Ihsan !okay on my way .
Keke napep Raeesah ta tara ta hau ta nufi gidan su Ihsan,
D’akin Ihsan ta nufa kai tsaye, tana shiga ta cire mayafinta ta zauna a bakin gado, ba ayi minti biyu ba saiga ihsan ta shigo da 2plates na fried rice da coconut juice da cups
Mamaki ne ya cika ta tana fad’in:! Babe what’s the secret wai? Naga kwana biyu sai wani kyau kikeyi kina wani qara shining kamar za ayi miki aure…
Toh! Toh! Ya isa inji Raeesah babu wani aure da zanyi uban wa zan aura… Allah ya baki haquri my crazy bestie! Muci abinci
No! Raeesah tace mujira Asmau na kirata tana zuwa, okay inji ihsan
Ko minti biyar ba ayi ba saiga Asmau tayi sallama ta shigo, gaisawa sukayi sannan suka fara cin abinci! Tareda wasa da raha da dariya da kuma labarai kala kala har yamma tayi sannan Raeesah tayi musu sallama tace zata wuce itama Asmau tace yayanta zaizo ya d’auketa.~~~~~~~~~~~
Hadari ne ganga ganga ya had’u gashi babu masu keke napep gashi kuma wayar ta ta d’auke babu chaji, hankalin Raeesah ne ya tashi ta rasa yanda zatayi, a chan gidansu kuwa maman Hauwa ta kasa samun natsuwa saboda ganin anyi sallar magrib gashi Raeesah bata dawo gida ba kuma gashi wayarta a kashe , ta kasa zama waje d’aya tana tsoron kada Abba ya dawo Raeesah bata dawo ba.
Ya salam! Ya salam! Abin da Raeesah ke ta maimaitawa kenan a zuciyarta
Gashi an fara ruwa mai qarfin gaske yana dukanta , wayyo Abbana dan Allah Abba kazo ka d’aukeni ruwa yana dukana ! Da karfintq take fad’a saidai banyi tinanin wani zai ji ta ba saboda kowa yaje domin ya fake wa ruwan.
Haka ta tsaya a bakin hanyar nan tana ta rawar sanyi ko ina na jikin ta ya jiqe hatta wayar ta ma ruwa ya mata duka .
Umbrella taji an sanya a saman kanta! Cikin hanzari ta juya dan ganin koh waye
Wani namiji ne ta gani a tsaye yana riqe da umbrellar tana ta rawar sanyi kamar ba gobe
Ki riqe ni zan wuce… abin da mutumin yace kenan, hannu tasa ta karb’a tace: Allah ya biya ka! Dan Allah a ina zan samu mota in koma gida? Koh amsawa bai yi ba yasa kai y wuce,
Kuka ta fara yi tana fad’in Ya Alalh ka kawomin agaji in samu in tafi gida, domin na san idan abbana ya dawo bai ganni ba akan maman hauwa zai sauke, ni kuma banason b’acin ransu su biyun .
Tafiya ta a fara yi a hankali koh zata samu abin hawa amma ina titin nan kamar anyi shara
Hasken mota ta gani daga nesa kamar tasan mai motar: murmushin farin ciki ta fara yi
Abbanta ne a cikin motar ! Sauri tayi ta isa gurin motar ta shiga .
~~~~~~~~~~~~~~
Innalillahi wa innailaihirajiun bata ta’ba ganin abban ta da irin b’acin ran da ta gani ba yau ranshi ya b’aci matuqa fuskar sa ta chanza
Sunkuyar da kanta tayi ta fara magana cikin muryar kuka Abba Dan Allah kayi haquri ka yafemin ban samu abin hawa bane shi yasa ban dawo da wuri ba I’m sorry Abba 😭.
Babu komai mamana amma a kiyaye kin san duk duniya babu wacca nake so kamar ki kuma ke kad’ai nakeda a fad’i n duniyar nan saboda haka a kiyaye domin idan na rasa ki kamar na rasa wani sashe na jiki nane.
Alalh sarki Hadiza tana gida tana jimami ashe ya gama yi mata masifa kafin ya fito kuma yayi mata gargad’d’i idan wani abu ya samu mai sunan maman shi toh ta kuka da kanta.
Suna isa gida Raeesah ta nufi d’akin ta , kayan jikinta ta cire sannan ta fad’a toilet ta watsa ruwan zafi a jikinta sannan ta dauro alwala ta fito tayi sallah,
Kayan bacci ta sanya ta hau gado ta janyo blanket ta rufe jikinta tana rawar sanyi ….
Har sha biyun dare baccin yaqi zuwa gashi sanyi takeji matuqa .
Tashi tayi ta shiga kitchen ta had’a coffee ta dawo d’aki ta fara sha! Toh wanene shi? Daga ina yake? Amma yana da kirki! Toh a ina zan ganshi na mayar mai da umbrellar sa ? Kodai ba mutum bane? Allah kasa dai ba gamo nayi ba da namijin aljani…. ita kad’ai taketa saqe saqe a zuciyar ta .
Bayan ta gama Shan coffee din ne ta koma ta kwanta har bacci ya d’auke ta bata daina tunanin mutumin daya bata umbrella ba, tana ta fad’in Allah yasa ba gamo tayi ba.+~~~~~~~~~~~~~
Masoyiya ashe haka dama kike da sauqin kai?
Ashe bazan sha wahalar samunki ba? Ashe haka soyayya take da dad’i? A kullum burina shine a d’aura min aure da abin da nafi so a rayuwata, zan nuna miki soyayya irin wacce babu wani namiji daya tab’a gwadawa, zan so ki kamar yanda Romeo yake son Juliet, sannan zan haukace a kanki kamar majnoon Laila .
Maganganun sane suka rastsa cikin jikin ta a lokaci guda taji kamar ba,a duniyar take ba saboda d’ad’in kalaman nasa
Kanta ta d’ora a kan kafad’arsa tana fad’in da gaske? Eh da gaske ya amsa, Toh idan haka ne toh ashe tunanin mu iri guda ne nima haka nakeji a cikin jiki na
Amma nayi mamakin kaina da sonka ya shiga cikin zuciyata cikin lokaci qanqani domin ban tab’a zato ba,
Hannunta ya kamo yana murzawa a hankali masoyiyata ki yarda dani wallahi ina son ki, watermelon din dake cikin plate ya dauko ya sa mata a baki tareda kalamai masu dad’i
Nima ina son…..k…
A daidai wannan lokacin ne Raeesah ta farka a firgice daga baccin da take
Hankalin ta ya tashi, batayi tunanin yin addua ba ta fara kuka tana fad’in:wayyo Allah Abba…..maman hauwa kizo……
Wata irin azaba ban zafi takeji dukda air conditioner din dake d’akin amma sam ji take kamr babu
A lokacin ne ta samu bakin yi addua , duk adduar da tazo bakin ta yi take
Wayyo Allah! Ubangiji ka tsareni daga sharrin shed’anun Aljanu 😭 ai dama saida na fad’a wataqila ba mutum bane ya bani umbrella tunda gashi nan harda fitomin a mafarki.
Agogon bango ta kalla taga 3:42pm , tashi tayi a tsorce ta shiga toilet ta dauro alwala ta dawo d’aki ta d’aura xani ta hau sallah tana roqon ubangiji daya rabata da duk wani abun da zai cutar da ita , bayan ta idar da sallar ne bud’e side drower ta bud’e ta dauko Alqurani ta fara karantawa , don rabanta da Alqurani ma ta manta tun a islamiyya amma gashi yau ta tuna dashi ( kuma dama ance duk wanda ya bar Alqurani toh Alqurani zai barshi fiye da yanda ya barshi) .
A haka dai ta samu ta karanta wasu y’an ayoyi na neman tsari da neman kariya sannan ta rufe Alquranin ta tofa addua a jikinta da fuskarta
A kan abin sallar ta fara bacci har asubahi yayi kafin ta tashi tayi alwala tayi sallah .
Kasa komawa baccin tayi domin kamanin mutumin da ta gani a bacci sune suke mata yawo a cikin zuciyar ta da kuma idanun ta.
Tabbas shine! Shine mutumin daya bani umbrella jiya, Toh idan yasan shi mutum ne ba aljani ba toh mai yasa danayi masa tambaya bai bani amsaba ya wuce? Kuma mai yasa zai biyoni har ma yace yana sona a mafarki?
Ita kadai takeyi wa kanta way’anan tambayoyin da batasan amsarsu ba amma dai abin da zuciyar ta ke gayamata shine wannan mai umbrellar aljani ne! Wata zuciyar kuma tana gaya mata ba aljani bane tunda har ya iya taimakon ta ya bata umbrella .+
~~~~~~~~~~~~~
Har karfe 7:00 n safe batayi bacci ba domin a tsororace take amma ta yanke shawarar bazata gayawa kowa abinda ya sameta ba sai ihsan da Asmau koh Abba bazata gayawa ba balle ya tada hankalin shi
9:00am tayi wanka ta gyara gadonta sannan ta shiga kitchen ta had’a breakfast d’inta da kanta tana aiki tana saqe saqe a ranta kuma tana kallon fuskarsa a idanun ta da kuma muryar daya mata magana lokacin daya bata umbrella, bayan ta karya ne ta dauko wayar ta fara neman lambar qawayenta, conference call ta had’a musu su ukun sannan ta kwashe labarin ta kap ta gaya musu ,
Alhamdullilah at last my bestie is now a woman……
Asmau ce ta fad’i haka tana dariya tana tsokanar Raeesah, Taji haushi sosai yanzu abinda zaku ce kenan? Nida nayi tunanin zaku bani shawara ashe qara min haushi zakuyi? Toh ba damuwa sai anjima!
Haba hauwan mama…. haba hauwan Abba
Kiyi haquri kinsan halinmu ai idan ba muyi tsokana ba bamu jin dad’i,
Ihsan ce ta fara bata haquri tana kwantar mata da hankali sannan tace mata ta dinga yin addua idan zata kwanta , kuma ta dinga kwanciya da Alwala
Haka suka gama waya har kowa ya kashe wayarsa,
Raeesah kuwa tunani ya mata yawa haka ta wuni ranar koh palour bata fito ba.
Har lokacin da Abba ya dawo bata fito ba tana d’aki , zama yayi akan sofa Hadiza ta kawo masa mango juice har ya fara sha ya sauke kofin kan table ina wannan yarinyar ta shiga ne? da safe na fita ban ganta ba gashi yanzu na dawo ban ganta ba! Kirawomin ita… koh kin mata wani abune bayan nafita?
B’ata rai Hadiza tayi sannan tace: me kwa zan mata tsaki tayi sannan ta nufi d’akin Raeesah tace mata taxo Abba yana son ganinta.~~~~~~~~~~~
Yau tsahon sati biyu kenan kullum Raeesah sai tayi mafarkin mai umbrella wai yazo suna soyayya kuma suna nishad’i
Amma har yau bata yarda da abinda zuciyar ta ke gaya mata ba . Amma yanzu kam ta yarda cewa ba aljani bane mutum me kamar ita
Asmau da ihsan har sun gaji da jin labarin mafarkin Raeesah,kullum idan suna magana toh maganar Raeesah bata wuce ta mai umbrella har ta sa masa suna wai jameel
Koh da suka tambayeta sai tace musu wai abinda yasa ta bashi suna jameel saboda yana da kyau ,
Amma wallahi qawata kin fara bani haushi anya ba aljanu bane suka shafeki? Anya ba gamo kikayi da namijin aljani ba? Gashi yanzu har kinzo kina ce mana wai sunansa jameel, kuma yana da kyau, Toh wallahi sai naje na samu mama nace mata a nemo malami yayi miki ruqya dan wallahi kin fara tab’uwa
….. tsawa Raeesah ta daka mata tana huci Asmau bansan bakya sona ba sai yau, wato so kike Abbana ya san halin da nake ciki? Nifa ba wai soyayya na fara ba kawai dai nace yana da kyau kuma yana da kirki……ya isa Raeesah ni kikewa tsawa a kan wani wanda bai san kinayi ba a kan wani banza toh shikenan ni zan tafi gida kar ki qara nemana. Kuka Raeesah ta fara tana bata haquri amma dai ita batasan menene yake faruwa da ita ba kuma ita bata tab’a tinanin zata so wani namijin ba, kuma ita ba son sa take ba kawai dai tana ganinsa ne a zuciyar ta da kuma mafarkin ta,
A haka ta ba Asmau haquri har suka shirya sannan asmau tayi mata sallama ta tafi gida.
Bayan asmau ta fitane kiran Abba ya shigo wayar Raeesah yace tazo palo ya sameshi,
Toh tace sannan ta tashi ta fita zuwa kiran abban nata,
Zaune ta sameshi kan sofa yana karanta jaridar DAILY TRUST hadiza kuma na zaune kusa dashi , sallama tayi ta zauna kusa da abbanta
Yauwa mamana dama na kiraki me domin in sanar dake tafiyar da zanyi zuwa Turai ran Thursday in Allah ya kaimu saboda haka kiyimin list d’in Abubuwan da kike so na siyo miki ni kuma nayi miki Alqawarin in Allah ya yarda zan siyo miki,
Magana ta fara cikin shagab’a: Abba ai inaga ma ba sai na fad’a ba duk abinda kaga ya dace dani ka siyomin ni kuma xanyi farinciki dashi.
Allah sarki mamana Allah yayi miki Albarka Ameen tace tana dariya, ita kuwa manan hauwa ido ta zuba musu tana riqe baki ohoh uba da y’a kenan wani lokaci kuna bani mamaki , toh toh munji kodai kina baqin ciki ne? Dariya suka fara Dukkansu suna farinciki da annanshuwa.
~~~~~~~~~~~~
Yau kwana hud’u da tafiyar abba London ya fara siyayyar kayan tsarabar da zai taho da ita, ya siyawa maman hauwa kayayyaki na gani na fad’a sannan akwati guda ya siyo ta kayyayakin basma da basman Raeesah kuwa ba’a magana domin akwati biyu ya siyo mata kowanne cike take da kaya da takalma harda sarqoqi na azurfa ya siyo mata,
A ranar da zai dawo gida ne ya shirya da wuri ya tafi airport kuma dama morning flight yakeda, bayan ya shiga jirgi ne ya had’u da wani abokinsa wanda sukayi secondary school tare , yayi farin ciki matuqa daya ganshi harma suka fara hira irn wacca suka saba da , anan ne abokin nasa mai suna Alhaji Aliyu kundi ya bashi labarin iyalan sa harma ya sanar dashi y’ay’an da ya haifa guda uku mata biyu namiji d’aya Amma Allah yayiwa mace d’aya rasuwa yanzu saura mace d’aya wacce ke aure a ghana da kuma namiji d’aya da ya gama karatu harma ya fara aiki yanzu shine CEO a deen’s enterprises .
Abbane yayi murmushi yace Allah sarki abokina lallai an d’ad’e ba’a had’u ba yanzu ni zancen da nake dakai d’iyata d’aya tal daga ita Allah bai bani wata ba.
Ah toh ai fad’uwa tazo daidai da zama mai zai hana mu had’asu aure kawai saboda mu qara qarkin abotar mu? Eh…. kuma hakane amma saidai ita mai sunan mama gaskiya bansan ra,ayin taba saboda ba tason ma ayi mata maganar aure! Amma dai zanyi tunani in gani
Haka dai sukai ta hira har suka sauka a airport d’in kano sannan kowa ya nemi hanyar gidansa.
+Abba yayi farinciki sosai da jin wannan batu na Alhaji Aliyu amma yana tunanin amsar da Raeesah zata bashi da kuma yanda reaction d’inta zai kasance saboda bayason b’acin ranta kuma abinda takeso shi yake so
Bai iso kaduna da wuri ba sai qarfe 11:00 na dare Raeesah har ta gaji da jiransa ta shiga d’aki ta fara abinda ta saba as usual wato tunanin jameel wanda bata saniba he exists or not, ita dai abinda ta sani shine wata rana zasu qara had’uwa taga kyayyawar fuskarsa da kuma murmushinsa abin birgewa, wani lokacin ma har biro da takarda take qauka ta fara rubuta kalamai masu d’ad’i wai idan ta had’u dashi face to face zata fad’a masa kalaman.
Tana cikin wannan tinanin ne taji sallamar abba ya bud’e k’ofa da gudu ta fita ta rungume abban nata tana mai sannu da zuwa tana farinciki da ganinsa maman hauwa ce ta fito daga d’aki itama tana mai sannu da zuwa, amsasu yayi sannan yace wa Raeesah ta tafi d’aki tayi bacci da safe zasu had’u! Toh tace ta nufi d’aki sannan ta kwanta taci gaba da sana,ar da ta saba . D’akinsa ya nufa ya shiga toilet ya watsa ruwa , kafin ya fito kuma Hadiza ta gama shirya masa abinci da drinks kala kala, Bayan ya fito ne ya huta ya ci abinci sannan ya fara baiwa hadiza labarin abokinsa da suka dad’e basu had’u ba sai yau a jirgi, a nan ne ya sanr da ita cewa zasu had’a yaransu aure Toh ya take gani? Gaskiya naji d’ad’i sosai amma bansaniba koh Raeesah zata yarda a iya sanina dai nasan bata da wani saurayi da suka tab’a tsayawa inji Hadiza, toh Allah dai ya tabbatar mana da Alkhairi Ameen inji Hadiza.
~~~~~~~~~~~
Raeesah fah abu ya girma a cikin zuciyar ta har ta fara zance ita kadai kamar mai hauka duk ta sauya ta rame kamar ba ita ba, Abbane zaune kan sofa Raeesah ta zo zata shiga d’akin Hadiza, kiranta yayi sannan tazo ta zauna kusa dashi
Raeesah you look different! What’s wrong with you these days?
Abba nothing!
Mamana kar kiyi min qarya ba haka na sanki ba, amsawa tayi cikin natsuwa Abba da gaske nake babu komai ! Toh mamana babu komai shine duk kika rame kamar mara lafiya……..
shigowar Hadiza ne ya dakatar da shi daga magana, yauwa gwara ka tambayeta wata qila kai zata gayama ma abinda ke damunta domin ni taqi fad’a min
Juyowa abba yayi bangren Raeesah ki taimaka ki fad’a mana abinda ke damunki don Allah ba don halinmu ba… Amma sam Raeesah ta dage akan babu komai,
Kwana biyu shima abba ya shiga cikin tunanin irin halin da y’arsa zata shiga idan ya fito mata da maganar aure musamman ma auren wanda bata saniba, a haka dai ya yanke hukuncin sanar da ita koda ranta baya so saboda bayaso yaji kunya a wajen abokinsa Alhaji aliyu , Hadiza kuwa ranta fal yake tana farinciki da hakan .
A yanzu kam Tabbas Raeesah ta yarda da soyayya kuma ta yarda cewa son jameel take amma wani lokaci da kanta take ganin haukanta, yaya za,ayi na fara son guy din da na gani a dream bayan shi bai sanniba? Kuma toh ina xan ganshi na fad’a masa abinda ke zuciyata kohda baya sona? Ina zan ganshi ? Allah ka yayemin abinda ke damuna ! Adduar da takeyi kenan idan ta tuna da mai umbrella da ta sawa Suna Jameel .
A yau watan Abba d’aya da dawowa daga turai Alhaji Aliyu kuwa kullum yana faman kiran abba yana tambayarsa wacca shawara ya yanke gameda auren y’ay’ansu ….. amsardai guda d’ayace kullum ina kan shawara! Shine abinda abba yake fad’a masa domin baisan ta inda zai fara ba!
A yau Tuesday abba ya shirya sanar da Raeesah abinda ke faruwa…. Hadiza ya aika ta kiramai Raeesah a d’akinta! Toh tace ta tashi ta nufi d’akin Raeesah suka fito tare…
Bayan sun xauna ne abba ya kalli Raeesah cikin tausayi yana magana kamar haka: mamana ki saurareni da kunnen basira ki kasance mai yimin biyayya kar ki zama mai taurin kunne a gareni , Abbba ban fahimce kaba inji Raeesah! Magana yacigaba dayi Toh kamar yanda kika sani haqqinmu ne mu iyaye nu zab’awa yaranmu abokan zama na gari,
Toh shi yasa naga tunda kin isa aure in aurar dake kema ki zama mutum kamar kowa domin raya sunnar annabi, kuma na samar miki wanda xaki aura yanzu so nake inji daga gareki…..+Manyan idanuwanta ta d’ago wanda sun d’ad’e dayin ja , hankalinta ya tashi Zuciyar ta ta fara quna
Cikin kuka ta kalli abban nata tace! Nayi qoqarin hana zuciyata wani abu amma na gagara. Ban tab’a neman wani abu a wajenka na rasa ba abba, baka tab’a hanani wani abu ba amma abba ina tunanin a barni na zab’i wanda nake so……bata qarasa ba ya katseta toh baki isa ba tun muna mu uku da mahaifiyar ki ki yarda da buqatata shine kad’ai kwanciyar hankalin ki , so kike naji kunya? Koh so kike ki zubar min da mutunci? Toh wallahi sai kin auri zab’i na… Raeesah tayi mamakin abbanta cikin lokaci qanqani ya chanza mata toh wai meke faruwa da ita ne?
Idan har kika watsamin qasa a ido toh lallai xaki xama abin Allah wadai a gareni sannan duniya zata tsine miki Saboda kin sab’awa mahaifinki sannan kuma xan manta dake a rayuwata, yana gama fad’a ya tashi yayi waje
Kuka taci gaba dayi kamar ranta xai fita… matsowa tayi wajen hadiza maman hauwa ki taimaka ki roqi abba ya yafemin kar yayi fushi dani dan Allha maman hauwa , maman hauwa ta tausayawa yarta matuqa , haquri ta bata sannan tace taje d’aki ta kwanta zata yiwa abba magana, koh da ta shiga d’akin ta kasa yin baccin kuka kawai takeyi tareda tunanin jameel d’inta mai umbrella yaya zatayi da soyayyarsa da ta fara shiga zuciyar ta… ga wani irin zazzab’i da ya riqeta jikinta yayi zafi, tunanin mai umbrella kuwa ya dawo kmr sabo a zuciyar ta. A haka dai har gari ya waye batayi bacci ba kuka kawai tasa a ranta
Qarfe goma na safe Raeesah ya fito domin ta nemi gafarar abbanta, muryar Hadiza taji tana magana da qarfi a dakin abba, fasa shiga tayi ta lab’e a kofar d’akin dan jin abunda ke faruwa a d’akin, hankalinta ya tashi da faji iyayen nata suna cecekuce a tsakaninsu : muryar maman hauwa taji tana cewa: gaskiya ban yarda da hukuncin da ka yanke a kan yarinyar nan ba bazai yuwuba tunda tace bataso toh a kyaleta ta kawo zab’inta kar ka zama silar jefa y’arka cikin halaka kada ayi mata dole, ita kadai Allah ya bamu…… tsawa ya daka mata da qarfi ! Hatta Raeesah dake lab’e jikin qofa saida ta firgita, a guje Raeesah ta shiga d’akin ta zube a gaban iyayen nata tana basu haquri: Abba, don Allah kuyi haquri ku daina fad’a a tsakninku banaso Allah yayi fushi dani, banaso Duniya ta kalleni a matsayin wacce iyayenta ke fad’a dalilinta , Abba na yarda zan auri wanda kakeso
Bayan ta gama fad’in hakane ta tashi da gudu ta tafi d’aki ta ci gaba da kuka kamar ranta zai fita,
Tausayintane ya kama hadiza kamar tayi mata kuka .
~~~~~~~~~~~
A yanzu kam Raeesah ta amince da auren dan Abokin abbanta amma babu farinciki a ranta don gani take zata iya mutuwa! Amma babu yanda zatayi saboda batasan abbanta yayi fushi da ita .
Shikuwa abba yanzu ji yake kamr Raeesah ta biya masa kujerar maka domin ta dad’d’a masa rai , tsaye abba yake a garden d’in gidansa yana waya da abokinsa Alhaji Aliyu kundi harsun fara shawarar abinda zasuyiwa yaran nasu ta yanda bikn zai zamo ba,a tab’a yin irinsa a qasarnan ba domin sunsan cewa suna da kud’inda zasu yi komai dan ganin bikin yayi armashi , Toh Abokina ai sai a turo yaron domin yazo su had’u da y’ar tawa… Alhaji Aliyu yayi farinciki Sosai dajin haka …..kukan Hadiza ne ya dakatar da abba daga wayar da yakeyi, a guje ya taho hankalinta a tashe tana kiran abba: kazo ka taimaka min dan Allah , cikin hanzari ya tambayeta mai ya faru? Amsawa tayi: Raeesah ce !! Raeesah ka taimaka min kar in rasa y’ata
Toh mai ya sameta?
Nima ban saniba d’akinta na shiga naga bata motsi, kumfa na fitowa daga bakinta Idanuwanta a bud’e
Shima abba hankalinsa ya tashi da gudu suka tafi d’akin dan taimaka mata… wayyo Allah na! Mamana ki tashi dan Allah karki mutu kiyi haquri ki tashi, juyowa yayi ya kalli Hadiza yace d’auko mayafinki mu kaita Hospital kiyi sauri ni kuma barina dauko mota mu tafi, cikin kuka Hadiza tace toh kayi sauri dan Allah!
Bayan ya fita ne Raeesah ta tashi ta doki kirjinta …wayyo Maman hauwa !!ina jin tsoro kar asirinmu ya tonu kar a gano mu, aa karki damu babu wanda zai gane cewa plan muka had’a
Wayarta ta d’auko ta kira Doctor sule yaro ta fad’a masa yanda ta keso ayi.
Abbane ya shigo da sauri yace mata ta dauko ta su sata a mota a taimaki rayuwar Raeesah domin idan ya rasata kamar ya rasa wani b’angarene na jikinsa.+Dedicated to Raudatul Jannah,hauwa Adam, Asmau Adam & Sadiya Bello 🌸🌸🌹🌸much love .
~~~~~~~~
Tuqi Abbah yake cikin hanzari kamar zai tashi sama, yanayi yana kuka yana fad’in Mamana dan Allah kiyi haquri karki mutu kece rayuwata, kece farin cikina Kiyi haquri na fasa aura miki wanda bakyaso,
Maman hauwa dake rike da raeesah itama kukan take tana fad’in: dan Allah kayi sauri ka tuqa motarnan da sauri idan yarinyar nan ta rasu ka cuceni kuma bazan yafemaka ba, shi kuwa abba hankalinsa ya tashi kansa ya d’au zafi, zuciyarsa na quna gashi tuqin yake kamar zai tashi sama amma gani yake kamar baya yi.
Suna isa asibitin doctor sule yaro nurses guda hudu suka iso wajensu suka karb’i Raeesah suka shiga da ita , umarni aka basu da su tsaya a reception kar su shigo ,
Doctor sule da yake yasan komai baiyi kasa a guiwa ba don taimakawa Maman hauwa akan plan d’insu, bayan ya fito daga Emergency room ne ya tarar da abba da maman hauwa a reception suna zaune sunyi tagumi , zuwansa ne yasa suka tashi tsaye suna tambayarshi halin da d’iyarsu ke ciki.
Innalillahi wa innalillahi rajiuna abin da doctor sule ya fad’a kenan yana yi musu tsawa! Menene haka !!meyasa zaku bari yarinya kamar wannan ta shiga halin damuwa? Toh gashinan abinda kuka ja mata ai! Ku biyoni office d’ina
A gaskiya hankalin abba ya tashi maman hauwa ta tausaya masa sosai, bayan sun shiga office d’in Doctor ne ya basu dama su zauna, sannan ya basu advice akan abinda ya kamata suyi kuma ya gayamusu abinda ya kamata ta dinga ci, saidai bai basu maganiba yace suje an sallamesu sannan suka tafi gida.+
~~~~~~~~~~~
Kwana biyu Raeesah ta nuna alamar samun sauqi 😂 abba yaji d’ad’i sosai da yaga jiki ya ware.
Abbane zaune a garden yana hutawa , wayarsa ya d’auka ya kira lambar Raeesah,
Assalma Abba
Wslm mamana! Kizo Garden ki sameni inaso muyi magana
Kashe wayar yayi sannan ya ajiye wayar, koh minti biyu ba,ayiba saiga Raeesah tazo wajen Abban nata, zama tayi akan carpet d’in da aka shimfid’a a garden din wanda ya qarawa garden din kyau da tsari,
Magana Abba ya farayi kamar haka: mamana ya jiki da sauqi tace, Toh abinda yasa na kiraki shine dama na fad’a miki tunda bakyason aurenan toh na fasa miki, ki daina damuwa kinji mamana! Toh Abba saidai itama ta tausayawa abbanta kuma tayi tunani mai tsaho kar Allah ya hukuntata akan bijirewa babanta,
Abba na amince ka auramin wanda kakeso ni kuma InshaAllah zanyi biyayya !!
Abba ne ya d’ago kansa cike da mamaki! Mamana da gaske kin amince da auren zab’i na? Cikin shagwab’a tace eh abba na amince, na tsaya nayi tunani ne kar in sab’a maka Allah ya hukunta ni shiyasa nace nikuma zanyi biyayya. Na gode miki mamana ina Alfahari dake Allah yayi miki Albarka Allah ya sa ki gama da duniya lafiya mamana. Nan dai yayi ta sa mata albarka yana mata godiya. Bayan ta shiga cikin gidane ya dauki wayarsa ya kira Alhaji Aliyu yana k’ara jaddada masa auren na nan, kuma yanaso zuwa nanda sati d’aya a turo yaron domin su daidaita da Raeesah .
Bayan ta shiga gidane ta nufi d’akin maman hauwa , sannan ta sanar da ita abinda ke faruwa, lallai ma Raeesah yanzu ke kin yarda da auren? Karki manta fa da plan d’inmu ya tashi a banza kenan? Lallai na yarda baki da hankali yaronda koh ganinsa baki tab’ayiba shine zaki aura, ba damuwa bazan takura miki ba
Maman Hauwa kiyi haquri na tsaya nayi tunanine kar Allah yayi fushi dani akan mahaifina shiyasa kawai nace na yarda kuma na amince da auren d’an Alhaji aliyu kundi kuma zanyi biyayya dukda ban tab’a ganinsa ba.
Toh shikenan Allah yasa shi yafi alkhairi Allah yasa mu dace, Ameen Raeesah tace tana sunkuyar da kai,
Saidai batasan ya zatayi da tunanin jameel ba don Har yanzu bata dainaba kullum saita ganshi a mafarki .
Har an fara tsara abubuwan da za,ayi a bikin gashi maman hauwa ta fad’a wa anty ta nijar cewar zata kawo yarta ayi mata dilka da magungunan mata irin na y’an Nijar, ita kuwa Raeesah bataso don magungunan mata haushi suke bata koh kad’an ranta bayaso
Anty salma ce mai yi mata fad’a: ke baki da hankaline toh darajarki ake so a d’aga da kuma samar miki mutunci a wajen mijinki da kuma qauna .
Toh Anty salma mutumin da koh ganina bai tab’a yiba maybe ma baya sona tunda gashi kullum sai ance yazo ya ganni amma sai yace wai yana da aiki a office kamar shi kad’ai ne mai office,inji Raeesah.
Can you vote?
🦋🦋🦋🌹🦋~~~~~~~~~~
Gidan Alh Aliyu kundi
Kai da ganin gidan kasan gidane irin na yan boko wanda suka ci karatu suka koshi, yanayin ginin gidan da tsarin gidan kai ka san bana qananan mutane bane, saidai ahalin gidan basu da yawa mutane uku ne ke rayuwa a gidan sai masu aiki guda hudu sannan sai masu gadi , wani saurayi ne wanda bai wuci kimanin shekaru 26 ba ke zaune a kan sofa yana operating wayarsa ga yayi wani irin zama na taqama ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya
Alh Aliyu ne ya shigo inda yake sannan ya fara masa magana kmar haka : tun jiya nake magana amma baka bani amsaba Toh wai menene nufin ka? Don’t you want to see me happy? Na fad’a maka wannan yarinyar d’iyar abokinace bai kamata kace wai bazaka je ka ganta ba ya zama dole kayi canceling office kaje ka ganta ku daidaita
Kansa ya d’ago yace okay dad I will do as you say InshaAllah ! Hajiar gidance ta fito riqe da jaka a hannun ta alamar unguwa zataje, Toh Alhaji nidai na tafi gidan qawata zanje muyi magana akan yanda za,a tsara bikin yaron nan ! Toh yace mata sannan ta sa kai ta fita, Alh ne yaci gaba da magana Toh my son yaushe zaka je ka ganta domin in sanar da baban ta?
Gatsine fuska yayi sannan yace dad maybe Wednesday InshaAllah! Toh Allah ya kaimu my son , shidai kwata kwata ransa bai soba amma koma dai menene zab’in iyaye shine gaba.
Alhaji Aliyu ne ya kira abban Raeesah ya sanar dashi cewar d’ansa zaizo ranar Wednesday domin su had’u da y’arsa, yaji dad’i sosai kuma yayi farinciki dajin haka .
A b’angaren Raeesah kuwa ta rame ta fita a hayyacin ta duk ta qare saboda tunani da tasa a ranta na mutumin da baisan da ita ba , kullum babu walwala a tattare da ita kullum daga tunani sai tunani koh abincin kirki bata ci saboda tunani irin rayuwar da zata shiga a gidan mijin da bata saniba , maman hauwa ce ta shigo d’akin nata ta tarar da ita a zaune tayi tagumi! Toh sarkin tunani abbanki yace a gayamiki jibi yaron da zaki aura zaizo ya ganki ki tabbata kinyi kwalliya kuma kinsa kaya mai kyau kuma ki saki fuskarki idan yazo! Shiru Raeesah tayi batace komai ba! Tsawa maman hauwa ta daka mata koh baki ji ba!! Naji tace ,
Yauwa kuma an sanya aurenku nanda watanni uku, tana gama fad’a tayi waje+
~~~~~~~~~~~
Washe garin ranar da zaizo ne abba ya sa Raeesah da maman hauwa da su tabbata sunyi abinci na saukar bako kuma ba abinci kala d’aya ba duk wani abu da suka san baqo zai buqata toh su tabbata sunyi don shima yasan cewa yazo gidan karamci.
Ai kuwa a ranar da zaizo anyi abinci kala kala ba adadi snacks kuwa ba,a magana, Raeesah tayi wanka ta sha makeup ta sanya wata blue gown da abbanta ya siyo mata a London tayi kyau sosai fuskar ta sai sheqi take saidai ranta babu walwala, karfe uku na rana saiga baqon nan ya iso bayan tafiyar da yayi mai nisa tundaga Kano, Raeesah kuwa tana d’aki a xaune kirjinta na dukan uku uku, ya samu kulawa sosai a wajen Abba harma da maman hauwa, bayan wasu y’an mintuna ne Abba yace shi zai fita, ita kuma maman hauwa ta nufi d’akin Raeesah tace mata tayi maxa taje ta sameshi
Tashi tayi ta nufi inda yake ta tarar da shi xaune kan sofa ya juya qeya, sallama tayi sannan ta tsaya har wasu mintuna bai juyoba ita kuma bata qarasoba ta tsaya tana ganin irin xaman taqamar da yayi musu a palo , hmmm tace a ranta, ta tsaya tana shakar kamshin turarensa .
A hankali ta qaraso inda yake ta tsaya a kanasa
Kai ba musulmi bane! Nayi sallama baka amsaba koh baka iyaba? Har a lokacin bai juyo ba saida tayi magana har sau hudu kafin ya juyo ya cire Sunglasses d’in dake fuskarsa! Ke qaramar yarinya what are you felling like! Ni sa,ankine? Koh dan xan taimaka in aureki!
Har yanzu Raeesah bata yarda da abinda idanuwanta suka gane mataba, tun tana magana a zuciyar ta har ta fara fitowa fili: Allah kasa ba mafarki nake ba, Allah ka sa ba Aljanu ne suka shafeniba, idan har mafarki nake Toh da idan na tashi bazan qara komawa baccin nan ba , shidai kallonta kawai yake baice komai ba, nuna shi tayi da hannunta tana fad’in sunansa jameel! Jameel! Jameel ! Jameel kaine? Jameel! Jameel! . Kuka ta fara yi Allah ka nuna min ranar da zan daina mafarkin jameel, ni na sani cewa mafarki nake na riga na saba da irin wannan mafarkin! Ke menene haka? Kin wani tsaya a kaina kina min maganar mafarki toh ni ina ruwana da mafarkinki! Ci gaba tayi da kuka dan Allah ka rabu dani Kullum saika zomin a baccina kayi haquri dan Allah 🙏🏻
Ohoh my Goodness! Abinda yace kenan keh Wai meye daga zuwana gidanku zaki fara cemin Aljani kuma wai kina ganina a mafarki meye damuwarki? Idan xaki zauna ki zauna idan bazaki zauna ba toh ki tashi a kaina. Toh waima waye ya fad’a miki sunana?~~~~~~~~~~~~
qafafuwanta ne suka kasa d’aukarta, hankalinta ya tashi ga zufa data fara karyo mata
Zubewa tayi a qasa tana ajiyar zuciya shi kuma ya zuba mata ido ya riqe baki, magana Raeesah ta fara yi cikin sanyin murya dan Allah ka fad’a min waye kai! Ka fitar dani daga cikin dogon tunanin dana shiga ka fitar dani daga rud’ani , a iya sanina kaine mutumin da ka taimaka min da umbrella a ranar da na rasa mota zuwa gida,sannan tun daga ranar kullum na kwanta sai kazo min a mafarki ,na kamu da tunanin ka ina ganinka a cikin idanuna ka fad’a min kai wa…………bata qarasa ba ya katseta ! Idan kika natsu zaki ji komai yanzu , magana ya fara yi cikin salon ji da kai da kuma fasaha ! Gaskiya nayi mamaki da kika kira sunana daidai, Amma banyi mamakin ganinki a nan gidan ba kuma a matsayin wacce daddyna yace in aura ba, tun ranar da na fara ganinki a hikma catering school na fara bibiyarki, har zuwa ranar da na ganki a bakin hanya kin rasa mota na baki umbrella, naso na d’aukeki a mota na amma sai naga bai kamata ba sai na yanke hukuncin siyo umbrella in baki , daga nan ne na fara adduar Allah yasa kece mafi Alkhairi a rayuwata, dalili kuwa saboda ban tab’a tunanin zanyi soyayya a rayuwata ba
Kullum ina cikin tunanin ki kullum ina ganinki a idanuna amma sai na daina ganinki koh a hanya, bayan daddyna ya dawo daga London ne ya sanar min da maganar aurenmu, da fari banyi tunanin ke bace sai da daddyna ya nunamin hotonki ! Tabbas naji dad’i amma ban nuna a fili ba saboda tunanin kar qaramar yarinya tayi disgracing d’ina shi yasa kullum idan nace zanzo sai in fasa sai yau Allah yayi zuwana! Kallon Raeesah yayi wacce hankalinta ya gama fita daga jikinta ta bud’e manyan idanunta tana kallonsa kamar gunki, Toh yanmata koh zan iya sanin labarinki? Oh yes!! Yes …. ta fad’a bakinta na rawa! Daga nan ne ta kwashe labarinta gaba d’aya ta fad’a masa! Ya tausaya mata sosai ashe Haka Allah yake hukuncin sa ! Kuma haka Allah yake qulla soyayya tsakanin y’an adam!
Kanshi ya d’ago ya kalleta Hauwa! Naam tace ta maida kallonta zuwa qasa, tambayarta yayi: shin mainene burinki? A kullum burina shine Allah ya had’a fuskata da jameel wanda na dad’e ina mafarki! Sannan ya amshi soyayya ta ko da ta rana d’aya ce, sai gashi yau kazo min a matsayin wanda zan aura, sab’anin tunanina da mafarkina da yake fad’amin kai ba mutum bane sai gashi Allah ya nuna min kai a zahiri bayan daren da ka zo min da umbrella, idan har da gaske kaine wanda ka bani umbrella toh babu shakka kai mutumin kirki ne kuma bazanyi dana sani ba , hannunta ta d’aga sama tana yiwa Allah godiya daya had’ata da dream d’inta.
Keh …. wai meye haka daga tambaya guda d’aya amma kin kunce sai zuba kike toh waya fad’a miki ni ina sonki? Kawai dai zan aureki ne saboda in taimaka miki da kuma bin umarnin daddy, shiru tayi kamar bata wajen kirjinta na dukan uku uku, Kin tsorata koh ? 😎 Toh da wasa nake .
Murmushi dukkansu suka fara suna kallon juna cika da qauna.
Hira suka farayi kamar dama sun saba da juna shi kuwa jameel tsokanar ta kawai yakeyi… shiga ki d’auko min umbrella ta idan ba haka ba sai na….. hmm tace Toh mijina zan d’auko maka umbrellar amma sai ka biya ni mafarkina da tsoratarwa, dariya suka fara da jin shauqin soyayyar juna a tareda su,
Maman Hauwa ce ta fito cike da mamaki ikon Allah ya salam!! Toh lallai ma Raeesah ashe dama sunsan juna ta tsaya take raina mana hankali! qarasowa tayi inda suke , suna had’a ido da jameel sai taji kunya ta kama ta 😂 sai taji dama bata fito ba.
Emm… emmm.. tace cike da kunya d’an nan amma dai nan zaka kwana ba? Koh kafin yace komai Raeesah ta amsa! Eh anan yace zai kwana! A,a mama ba nan zan kwana ba yau zan koma gida saboda ina da meeting a office gobe ! Raeesah ce ta b’ata rai toh masu office baxaka koma yau ba abbana bazai yarda ka koma yau ba sai gobe. Maman hauwa dai abin duniya ya dameta! Raeesah ki kaishi guest room yayi wanka idan kin gama kizo d’akina.
Cikin sauri Raeesah tace toh ka tashi muje in muna maka d’akin! Maman hauwa kuwa baki ta riqe ta bisu da kallo ta nufi d’akinta .
+~~~~~~~~~~~
Da shigarsa wanka Raeesah ta shiga d’akin ta sanya turaren wuta mai qanshin gaske , bayan tasa ne ta nufi d’akin maman hauwa don amsa kiran da take mata , sallama tayi sannan ta zauna a bakin gado kusa da maman nata! Maman hauwa gani! Magana ta fara yi Raeesah …naam tace! Wai Raeesah mai yasa kike so ki yi mana wasa da hankali? Menene yake faruwa? Ki fad’a min nifa mahaifiyar kice kar ki b’oye min komai Raeesah… ki fad’a min wai dama kunsan juna ne dake da wannan yaron jameel? Mamaki ne ya cika Raeesah .. amma maman hauwa mai yasa kika min wannan tambayar? A,a saboda naga da k’yar kika amince da zancen auren nan amma sai gashi daga zuwansa har kun fara hira kamr kun saba da juna ! Amsawa Raeesah tayi maman hauwa gani nayi idan ma ban ban saki fuskata ba dole ne fah sai anyi auren nan kuma na riga nayiwa Abba Alqawarin zan zama mata ta gari ga miji na , kuma bana so na sab’a umarnin Abba kawai shi yasa na saki fuska ta na kuma karb’i soyayyar sa Hmmm… maman hauwa tace , eh kuma hakane kina da gaskiya domin aure kam babu fashi Allah yayi muku albarka, Ameen Raeesah tace sannan ta fita.
K’arfe 8 da rabi Abba ya dawo, maman hauwa ce ta tareshi da labarin da yake son ji lallai kam abu yayi daidai Allah ya nuna mana auren nan, za,ayi auren da aka dad’e ba,ayi irinsa ba a kaduna Allah mun gode maka.
A b’angaren Raeesah kuwa kitchen ta shiga tana had’awa jameel coffee , sallama tayi ta shiga d’akinsa ta miqa masa coffee d’in , bayan ta miqa masane ta juya zata koma ya riqo gefen hijabin ta 😉ki zo ki zauna domin na dinga kallon ki hauwa ta! Dawowa tayi ta zauna Toh gani… magana ta fara! yau gaba d’aya rayuwa ta ji nake kamr ina aljanna, daga zuwanka gidan nan naji gaba d’aya rayuwata ta koma sabuwa , haqiqa yau ne na farka daga baccin da nake yaune kuma mafarkina ya zamo gaskiya, nayi qoqarin yin bacci amma na kasa shiyasa na kowo maka coffee domin na qara sa ka a idanu na kafin safiya!
Idanun sa ya lumshe cike da shauqin soyayya yana mamkin yanda yarinya kamar Raeesah ta iya kalamu masu dad’i da kwantar da hankali, kusa da ita ya matso shima ya fara mata nasa kalaman yana nuna mata soyayya da qauna, bai barta ta koma d’aki ba sai 12am kafin ta koma d’aki ta kwanta a gajiye,
A b’angaren jameel kuwa kansa ya daga sama yana saqe saqe a zuciyar sa , a zahirin gaskiya jameel kyakyawa ne, dogon mutum ne mai d’an duhun fata, mutum ne mai son tara gashi , yanada fad’in kirji , kuma yasan ya kamata saidai baya son raini, shine babban abun da ya hana shi karba’ar soyayyar Class mate d’inshi Amira saboda baya d’auakr raini , sai gashi kuma lokaci guda yaji soyayyar Raeesah a zuciyar sa kamar da wasa .
+
~~~~~~~~~~
K’arfe 7 da rabi na safe Raeesah tayi kwalliya cikin wata koriyar riga mai daukar hankali, d’akin jameel ta nufa, tana shiga ta tarar dashi har ya shirya cikin manyan kaya yana shirin tafiya , good morning tace … amsawa yayi cike da qauna morning my Hauwa….. I’m ready, shagwab’a ta fara masa … haba dan Allah ai dai ka jira 12 yayi kafin ka tafi koh ! qarasowa kusa da ita yayi sannan ya kama hannunta ya fara shafawa a hankali Ki yi haquri I have no choice … meeting d’ina 2 Oclock ne kuma ya kamata inje kafin 2 d’in I know you will miss me and I will miss you more… a haka yayi ta bata baki da zafafan kalamai masu dad’i har ta haqura.
Driver ta kira domin ya kai jemeel airport, sallama yayi da maman hauwa da kuma Abbanta sannan suka fito tare yayi mata sallama ya shiga mota
Zubeefly 🦋….. love you oll 😉🌸~~~~~~~~~
Matsanan cin kuka takeyi mai ban tausayi tana share majina wallahi baxan yafewa zuciyata ba idan har ban auri jameel Aliyu bah, dan Allah qawata ki taimaka min ki ceto rayuwata pls
Wata matashiya ce ke fad’ain wannan maganar tana mai zubar da qwalla
qawarta Fatima itace mai bata haquri haba babe kina yarfa mata wallahi duk wannan kyawun da Allah yayi miki ga ilimi sannan gaki da dukiya ga isa , ga mulki da Allah yabawa babanki sannan gaki da sura mai kyau , bayan haka kinada abinda duk namiji xaiso ace kece a matsayin matarsa Toh menene naki na zubar da hawayenki a banza a kan wanda baisan kinayi ba!
A,a fatima duk dukiya ta Jameel ya fini, duk kyawuna jameel ya fini sannan shima yanada ilimi, nidai burina ace ni ce matarsa ta sunnah amma kash…. wata banza wacce batasan menene yake mata ciwo ba itace zai aura
Ba niba! Babban abinda ke damuna shine jameel baya sona baisan inayi ba ,
Kuka taci gaba da yi idanuwanta kuwa sunyi jazir
Fatima ce tace Amina karki damu akwai mafita
Cikin hanzari Amina ta juyo ta kalleta dan Allah ki fad’a min mecece mafitar
Matsowa fatima tayi kusa da ita my Friend relax… everything will be okay! But stop crying
Da sauri Amina ta share fuskarta I have stopped..
okay inji fatima! What we will do is kawai mu kawarda d’aya daga cikinsu… koh jameel koh kucakar da zai aura
OMG! Fatima are you in your senses?
Yes…. I I’m
Wannan shine kawai abinda zamuyi ! Idan kuma ba hakaba ki tsaya a banza kinaji kina gani zai auri wata ba keba, ke kuma sonsa ya kasheki daga nan kuma kin zama mara amfani , toh what do you think?!
Amina dai ranta bai soba domin ita gani take bazata iya kashe mutum ba ballantana ma ace wanda takeso perhaps dai tasan baya sonta amma bazata iyaba
Eh na yarda saidai bazan iya kashe jameel ba kuma bazanso ace ya mutu ba, saidai mu kashe wacce zai aura amma ba shiba
Okay fatima tace idan har kin yard zakiyi abinda na saki toh baza kiyi nadama ba kuma xaki samu jameel
Cikin farinciki Amina ta juyo are you sure fatima? Idan har hakan ya kasance toh nayi miki alqawarin zan baki 30 milliom naira
Hahahah fatima tayi wata irin dariyar mugunta… ni kaina nasan bani da mutunci kuma zan iya koh menene indai da gaske kike zaki bani 30 milllion toh ni kuma daga yau zan fara neman information akam yarinyar da zai aura
Za kiga aiki da cikawa kuma kukanki ya qare daga yau
Dariya suka fara suna raha da farinciki ita da Fatima+
~~~~~~~~~~
A b’angaren su Raeesah kuwa abin yayi nisa yau aure saura sati biyu
Komai da ake buqata a gani a gidan amarya abbanta yayi ordering daga abroad sannan anyi inviting manyan mutane zuwa wajen bikin , gida har ya fara cika su anty salma anyi kiran masu SPA na gargajiya da na zamani maman su basma itace ta d’auki nauyin kayan mata da dilke
Kai da ka ganta kasan ta sha gyara irin na amare fatarta sai shining take kamar ka taba jini ya fito kuskarta kuwa sai wani haske da take yi ,
Shi kuwa jameel baki yaqi rufuwa saboda farinciki, Hajiyar sa kuma ana ta hidima akai a kawo d’an autan ta zaiyi aure koh ina sai murna
Humaira yayar jameel wacce ke aure a Ghana har tazo itama da y’ay’anta anas da ummi
Gaba d’aya way’an nan families guda biyu kowa a b’angaren sa babu komai sai murna da farinciki.
Raeesah ce xaune akan doguwar kujera suna ta hira da baqi y’an uwa da abokan arziqi
Maman hauwa ce ta fito daga kitchen tayi kiran Raeesah! Ke baki da kunya ne mai yasa zakizo cikin mutane ki zauna ai sai ace baki da kunya ki wuce d’aki ki zauna karki qara fitowa cikin mutane
Kwanciya tayi akan gado ta dauki wayarta ta dokawa jameel d’inta kira
Sau d’aya wayar tayi qara ya d’auka
Hlo my heartbeat 💗
Darling inata missing d’inka yaushe zaka zo?
Hmmm ….. next tomorrow ! ya amsa
Why not tomorrow Tace
A,a baby idan nazo gobe ai sai ace na cika gaggawa, dariya dukansu suka fara
Toh !
zafafan kalaman sa ya zubu mata da kuma qauna!
A haka suka kashe wayar gaba d’ayansu Suna farinciki.
Bayan sun kashe wayar ne ta kira ihsan da asmau tare a conference call suna shawarar abinda ya kamata suyi
Fatima ce ke waya a d’akinta tana bada umarnin a nemo mata bayanai akan hauwa Husseini domin taga sunanta a invitation card sannan a nemo mata bayani akan hall din da za,ayi dinner d’in bikin
Ita dai fatima ji take kamar ta samu 30 million a hannunta
Gata y’ar talaka amma Allah yayi ta da son abin duniya don ita cikakkiyar yar bariki ce wacce idanunta suka bude da duniya.
Ita kuwa Amina kullum sai tunanin wanda baisan ma tanayi ba.
🦋🦋🦋Bayan gaisuwa da fatan Alkhairi masu karatu
Allah ya sadamu da alhairan dake cikin wannan rana, sannan ya bamu ikon gama rubutun wannan littafi mai suna D’iyar fari
Na zubaidan Gaddafi mrs fly ☺️
Allah yasa mu dace Ameen ya rabbal Alamein ‘
Masu karatu a baya mun tsaya a inda fatima qawar Amina ke kiraye kirayen waya tana neman details akan wacce Jameel Aliyu zai aura
Domin kwad’ayin abinda aminar zata bata.
Ita kuwa Amina zuciyarta cike da zullumi da soyayyar jameel Aliyu kundi
anan muka tsaya yanzu zamuci gaba.
~~~~~~~~~~~~~~~
Maman hauwa ce zaune akan sofa tana waya da su anty salma,
Way’anan families d’in guda biyu kowa da kowa ana shirye shirye ba kama hannun yaro .
Jameel kuwa da family d’insa kowa babu komai a zuciyarsa fiyeda farinciki,
Masu gyaran jikin amarya y’an Niger 🇳🇪 har sun iso an fara gyare gyaren jiki ,
Ayanzu haka Raeesah ce zaune akan wata kujerar qarfe a d’akinta
Masu gyaran jiki guda biyu ne a d’akin sunata mulke jikin Raeesah da sinadarai kala kala irin nasu na buzaye saidai ita Raeesah way’an nan abubuwan duk basa burgeta aganinta tunda anfi wata d’aya da farawa ai sai a barta haka, amma ina
Skin d’inta ta koma kamar ta jariri, jikinta na daukar qamashi yana sheqin Amarci .
Ana cikin gyaran jikin ne a shafa wannan a shafa wannan sai taji kira ya shigo wayarta
Abokin rayuwata abinda ta fara fad’a kenan
Amsawa yayi naam abokiyar rayuwa gani a bakin gate d’inku,
Rai ta b’ata
Dan Allah stop making me missing you 😞
Toh babyna na daina
Cikin sassanyar murya tace Abokin rayuwa mutanen nan zasu kasheni sai faman mulke mulke suke min na gaji da wannan abubuwan ,
Dariya ya saki mata hmm babyna ai Nafiso a gyara min ke
Cikin kuka tace shikenan tunda kafison na sha wahala ba damuwa !
Zafafan kalaman nan nasa da suke sanyaya zuciyarta ya fara zubo mata yana lallashin ta da kuma manna mata kisses a wayar domin hankalinta ya kwanata
A haka dai Sukai sallama ya ci gaba da aikin office d’insa wanda dama shi yakeyi kafin ya kira ta, ita kuma ta ajiye wayar a gefenta !
Ana cikin mulke jikin ne d’aya daga cikin masu gyaran jikin ta fara cewa a gaskiya anty kinyi sa,ar miji dukda cewa ban sanshi ba kuma ban tab’a ganinsa ba amma dai ance alamar karfi tana ga mai qiba, ina fatan Allah yasa har mutuwa keda shi,
Wani irin murmushin farinciki Raeesah ta saki Allah koh kedai baki da dama! Toh na gode da wannan adduar taki
Sallamar wata mata ne ya katsesu
Amsawa sukayi sannan aka mata izini ta shigo ,
Wata qwarya ce a hannunta cike da madara a ciki
Toh gashi idan kun gama a bata ta sha sannan a yi mata wanka da sauran madarar
Manyan idanuwanta ta zaro! Kai da madarar za,amin wanka tab! Gaskiya gwara ku bani kawai in shanye
Matarce ta b’ata rai kaji sha-sha-sha keda akeso ki sha kad’an
Shagwab’a ta fara yi mata Toh anty naji!
A,a ki daina min shagwab’a ki bari idan kinje chan gidan mijinki sai kiyi mai.+
~~~~~~~~~~~
Jameel ne cikin motarsa yana tuqi a hankali domin dama shi bai iya gudu a mota ba, sautin waqar Dj Ab soyayya ce ke tashi a motar!
Yana cikin hakane bai ankara ba, kwatsam sai jaga wata mota ta sha gabansa da alama mace ce a cikin motar
What !! Abinda yace kenan yana sauke glass d’in motarsa, wanne banzane wannan yakeso yasani accident?
Amina ce !! Ta fito daga cikin motar tata! Koh kafin jameel ya bude qofarsa ta iso inda yake tana faman hargagi! A hankali jameel ya bud’e kofar motarsa ya fito, kallonta ya fara daga sama har qasa! Gashi dama jameel akwai kallon raini 😂
Wai me kake nufi dani ne? Kana nufin duk shekarun dana b’ata ina fama da sonka a zuciyata nayi a banza kenan? Ka taimakawa zuciyata mana ka ceto ta daga halin sonka da ta shiga! Please!
Har a lokacin jameel bai ce komai ba, tafiya da baya ya fara a hankali yana mata kallo irin na wayayyun mazannan
Invitation CARD ya d’auko a bayan motarsa
Ya dawo inda take ya miqa mata , magana ya fara cikin murya mai sanyaya zuciyar mai karatu
Ban tab’a sonki ba, bazan tab’aba , kuma baxan tab’a gwadawa ba
Idan kinga dama you are invited! Koh bakizoba za,a daura
Da sauri jameel ya koma ya ja motarsa ya tafi.
Tsugunnawa tayi a wajen da take tsaye tana gurnanin kuka har ya b’ace mata da gani . Anan ne ta qudiri aniyar sai ta yiwa jameel abinda bai tab’a tunani ba,
Ransa a b’ace ya koma gida yana gurnani kamar wani zaki ran maza ya b’aci !!
Tun daga bakin qofa ya jefa brief case d’insa kan doguwar kujera, da sauri mummynsa ta taho gurinsa tana tambayar d’an nata,
Yau dai alamun shagwab’a yakeso yayiwa mummyn nasa!! Ita kuwa hajiyar tasa tambayarsa take tana nuna damuwa a kan al amarin nasa a haka harta lallashe sa!
A yau asabar aka daura Auren Hauwa Husseini Abubakar da Jameel Aliyu kundi
Alhamdullilah biki yayi albarka ya tara jama,a kala kala
Su basman manyan gayu an sha kaftan
Abban Raeesah kuwa farinciki kamr ya goya Raeesah da maman hauwa, yan uwa da abokan arziqi duk an hallara, Raeesah kuwa tunda taji ance an d’aura jikinta ya fara sauyawa, baki yaqi rufuwa,
A b’angaren jameel kuwa ansha fararen kaya shida abokansa ana takun girma,
Gida dai ya cika! Koh ina sai sha,ani ake
Yan uwa da abokan arziqi duk an had’u sai farinciki.
Vote
Zubeefly 🙏🏻~~~~~~~~~~~
(A wannan yammar bayan an daura auren jameel Aliyu kundi da hauwa Husseini Abubakar)
Kowa da kowa farinciki baya misaltuwa
Amarya kuwa da friends d’inta suna Luxury Hotel ana shirin tafiya wajen Dinner,
D’an qaramin towel ne a jikin Raeesah da shower cap a kanta , zaune take sai faman makeup ake a shafa wannan a shafa wancan
Da yake Tafeeda’s glamour aka d’auko domin yin kwalliyar tun daga kano .
Asmau ce ta shigo tana taku a hankali domin high hill d’in da tasa a qafarta . Wata qaramar nylon ta bud’e ta d’auko wasu blue nights wears y’an qanana ta jefawa Raeesah wacce ke zaune a gaban mirror
Wallahi ke dai asmee sai a hankali !! Inji Raeesah ,
Toh daga abin arziqi?
Toh bari kiji wannan shine wanda xakisa on your first night
Hmm Raeesah tace Toh nagode, asmau ce tayi wanni wawwan tsalle ta fad’a kan Raeesah tana kyalqata dariya , oh oh asmau ki d’agani dan Allah, koh tausayina bakiyi! Ki luguiguita ni kuma anjima in sha wani!
Hmm wannan batu na manya ne ! Inji ihsan
Harara Raeesah ta galla musu zaku sani ai shegu mugwaye!!
Dariya suka fashe da shi suna kallon Raeesah suna mata waqa! Tareda tsokan , Amarya a gidan jamilulu, ke kikace kinaso, xamu kaiki mu barki 🤪.
Qarfe 8:40 aka fara had’uwa a ceremonial canopies dake anguwar rimi kaduna ,
Babban hall ne wanda yake daya daga cikin top 5 greatest event center a kaduna, an kashe kud’i kamar yayi.
Maman hauwa da Abban Raeesah kaya kala d’aya suka sa,
Hmm su maman hauwa uwar Amarya 😉 ansha gwala gwalai a wuya da hannu sai sheqi ake, abban Raeesah kuwa a wannan ranar kyautar kud’i ya dinga yi domin aljihunsa kansa yayi nauyi ,
Abokan ango sunyi shigarsu cikin sky blue da hula , ango da Amarya sunsha kyau Amarya da friends d’inta guda biyu sai sister basma sunsha peach material, amarya kuwa b’a magana domin yau ranarta ce , hmm su Raeesah Amare 🤩+
1
Fara event d’in keda wuya ana ta hidima a yanzu haka amarya da ango sunyi cutting cake d’in aurensu wanda aka rubuta HML J&H
Hmm gayyar sod’i Amina ce ta shigo da tawagarta kamar ance suzo wajen su biyar har da ita, Fatima kuwa ta tandi makaman yaqi domin a yau take jin kanta zatayi betraying Amina domin jameel ya kwanta mata a rai, amma babu yadda zatayi saboda haka ba Raeesah zata kashe ba jameel zata kashe kowa ya rasa domin itama ta kamu da sonshi 😥 she can’t do without him jameel Aliyu kundi .
A daidai lokacin da Amarya da ango suka koma mazauninsu ne Amina ta dokawa Fatima kira,
Hlo yes mah lady! Inji Amina
Sannan taci gaba da magana, it’s time to do your work, make sure no one sees you, idan aka kamaki babu ruwana!
Toh shikenan ta kashe wayar,
A daidai wasu manyan chairs Fatima ta lab’e domin aiwatar da abinda ya kawota, a yau dai tayi alwashin kashe jameel domin kowa ya rasa,
Saboda ita kanta haushin Amina takeji, a hankali ta fitoda bindiga daga hand bag d’inta tana riqeta da kwarewa kamar ta saba,
You are under arrest taji ance mata! da sauri ta juya bayanta don ta firgita , batayi tunanin za,a ganta ba ! Yan sanda ta gani su hudu a bayanta kowanne da bindiga a kanta,
Fashewa tayi da kuka , don Allah kuyi haquri wallahi qawata ce ta sani, dan Allah ku barni in tafi gida, pls
Kuka takeyi kamr ba gobe ,
Amina ce ta tako tana clapping hands d’inta,
Oh oh poor girl, revenge is a dish best served cold,
Wannan kalma tayiwa fatima ciwo
Aminace ta kalli police d’in tace: officers you can go with her, okay ma! Sannan suka tafi da ita.
Ta Zaci zan barta ne batasan na fita iya cin amana ba,
Sauran mutane masu biki kuwa babu wanda yasan abinda ke faruwa har aka game dinner,
11:30 aka kai amarya dukda cewa yayi dare amma abba yace a kaita da haka, maman hauwa ce mai kukan rabuwa da Raeesah amma ita madam kuwa koh irin kukan amaren nan babu,🙃
Bayan an kai amarya ne su anty salma suka yi mata d’an fad’a wanda ba za,a rasaba sannan suka barta ita kad’ai sai angonta jameel abin qaunarta.
Alhamdullilah yau dai Allah ya nuna mana auren Raeesah da jameel saura naku masu karatu!🤪
Zubeefly 🦋
Vote pls 🥰~~~~~~~~~
Ga masu karatu
A zahirin gaskiya in miqa godiya ga yawan viewers d’in da nake samu, amma mai yasa bakwa yin comment ?
Ai yawan comments d’inku shine zai yi encouraging d’ina domin update a Kullum!
Amma a daddage a daure a cije a dinga comment da vote , hakan ne kad’ai zai nunamin kuna fahimtar littafin.
Taku zubeefly @ follow .😘🙏🏻🙏🏻
Much love 💕+
1
Amarya da angonta abin qaunarta jameel 💗
~~~~~~~~~~
Xaune Raeesah take a tsakiyar gado fuskarta a lullub’e da mayafi,
Kirjinta ne yake dukan uku uku, zuciyarta cike da zullumi da shiga sabuwar rayuwa ( wato rayuwar Aure) . Tana saqe-saqe iri iri a zuciyarta, da tunanin yanda rayuwarta zata kasance da masoyinta, abin begenta.
Jameel ne yayi sallama yana takowa a hankali
Amincin Allah ya tabbata a gareki yake wannan ma,abociya kyau!
Amsawa tayi cikin murya mai sanyaya zuciyar mai karatu, wa alaika, ( kaima haka) , tareda bude mayafin dake fuskarta!
Kallo d’aya jameel yayi mata Godiya da daukaka su qara tabbata ga sarkin da ya qagi wannan hallita , abinda yace kenan sannan ya maida kallonsa ga madaukakiyar fuskarta
Hannu jameel ya daga yana godiya ga ubangiji, da yayi masa wannan babbar Kyauta ,
Sannan ya sanya hannunsa a saman kanta ya aiwatar da sunnar da Annabi (s a w) ya koyar
Tambaya Raeesah ta jefa masa, wacce ta juya tunanin sa
Jameel why did you love me?
Idanu jameel ya qifta mata sannan ya bata amsa cikin kwarewa da ilimi saboda dama jameel akwai ilimin magana da fasaha: habibti there is no reason to love , if someone really love you no reason , if there is a reason what about the day when that the reason disappear that means I won’t love you , babe I love you with no reason, a Kullum burina shine na qare rayuwata dake masoyiyata, domin donki ya rufemin idanuna, kece uwar yarana, Ina roqon Allah yayi mana tsawancin kwana domin in nuna miki menene so, yaya so yake
Sann……. a daidai lokacin da jameel ya kai nan a maganarsa ne hawayen farinciki suka fara gudana a fuskar Raeesah ,
Jameel ina sonka, Allah yayiwa rayuwar aurenmu albarka, qanqameta yayi a jikinsa yana shaqar kamshin jikinta yana numfarfashi a hankali, mayafin dake kafad’arta ya yaye gefe ya fara shafa jikinta yana aika mata da saqonni kala kala.
A daren farko kenan, haka way’annan masoya suka yi daren aurensu cike da soyayya mai dumbun yawa,
Karfe 7 na safe , jameel ne a kitchen yana making musu breakfast
Raeesah kuwa anyi laushi domin ta sha wahala a gun jameel a wannan daren 🙃
Wayarta ce ta fara ringing, Asmau ce amma bata dauka ba, don tasan hali shegiyar yarinya tambaya zata yi mata about her first night kuma batason tambayar, 😂
Daidai lokacin da jameel ya shigo d’akin ne Raeesah ta shigar da kanta cikin blanket alamu dai kunyar had’a ido dashi take yi !
Good morning baby! Good morning watermelon!! Good morning sunshine,
Har a lokacin bata amsaba,
Look at me, idan ba hakaba xan….. sauri tayi ta bud’e fuskarta ,ehn da na miki duka…
😫 bayan wanda kayi min jiya?
Aa Toh sorry my Queen ! Kije kiyi wanka
Toh amma dai ka fita,
Amsawa yayi, gaskiya bazan fitaba I’m your husband. So I’m not going out,
Tashi tayi a hankali tana tafiya a daddafe har ta kai toilet sannan ta shiga cikin jacuzzi .
Ta kai tashon 1hour a toilet tana zuba ruwa a jikinta, alwala ta d’auro sannan ta fito da towel dai dai cinyarta, a gaban mirror ta zauna sannan ta fara shafe jikinta da mayuka masu qamshi da turare iri iri,
Black lace ta dauko daga wardrobe d’inta ta sanya sannan ta zauna ta zizara makeup ta kashe dauri, gold d’in da aka sanya mata a cikin kayan lefe ta d’auko ta sa a wuyanta, sarqar ta fitarda asalin kyawun Raeesah kamar baturiya, takalmi mara tsini ta sa sannan ta fara takawa a hankali kamar bazata taka qasa ba,
Dining area ta nufa domin tasan angon nata yana chan, cikin marai rai cewa ta isa wajen sa sannan yayi mata umarni da ta zauna a jikinsa , soyayya dai ba,a magana tsakanin wannan ma,aurata jameel da hauwa
A baki ya bata abincin har ta qoshi sannan shima yayi nasa breakfast d’in, bayan sun gama ne jameel ya dauketa suka fara zagayawa a cikin gidan domin ya nuna mata yanayin gidan,
A gaskiya darling gidan nan ya had’u Allah ya qara arziqi, Ameen yace sannan ya manna mata peck a chin d’inta .
A haka rayuwar jameel da hauwa ta kasance Kullum har baya son tafiya office ya b’arat a gida wani lokacin ma tareda ita yake zuwa office, saidai baya iya aiwatar da komai sai sha shanci da shirme domin soyayya hauwan sa tafi mai aikin office d’in,
Gashi a yau wata biyu kenan da aurensu.
Can you vote?
Okay let’s comment together 🤗 Dedicated to Abubakar ( boc🌺🌸
~~~~~~~~~~~~~
Kamar da wasa abindai sai ci gaba yake, gashi yau watan Raeesah hudu a gidan miji hmm Rayuwa ta chanza , al’amura duk sun chanza,
Hmm.. abindai ba’a magana 😋 ( koh ni zubeefly da naga Raeesah da qyar na gane ta) 🤪
Back to business 🤞🏻a yau Monday da safe Jameel na gaban mirror yana gyara tie d’insa, Raeesah ce ta zo ta bayansa ta sanya hannayenta ta zagaye wuyansa tana faman yin shagwab’a sunshine pls ka zauna a gida yau I need you by my side pls sai wani narkewa take a jikinsa watermelon you know I have an important meeting in my office koh , kiyi haquri dan Allah ki barni in je I promise you gobe zan zauna InshaAllah kinji my love 😍
Da qyar dai ya shawo kanta ya manna mata peck a goshi amma duk da haka Raeesah dai bata haqura ba , har bakin qofa ta bishi tana shagwab’a kamar yadda ta saba, roqonta ya fara yi dan Allah my love ki bani brif case na I will be late, Toh shikenan zan baka amma sai kace kana sona! Okay ina sonki my Raeesah A’a ni ba da hausa ba da larabci zaka fad’a idan ba haka ba you are not going anywhere!
😏hmm kedai kamar yarinya wallah… ehh mai kace? No nace ke kyakyawa ce 🤣 Raeesah tace: Toh naji kace kana sona da larabci idan ba haka ba bazan baka brief case naka ba 🤪
Gyaran murya jameel yayi sannan!!! Yace
Ana ahabbuki ya habeebti 😘
Ah toh koh nayi daidai oho 😂
A ransa yake fad’in wannan, duk da haka da qyar ta miqa masa ya wuce , yana shiga mota mai gadi ya bud’e masa gate ya fita , Raeesah kuwa bata koma ciki ba har saida mai gadi ya rufe gate, addu’a ta kwararowa mijin nata!! Ya
Allah ina roqon ka ka tsare min mijina ka kaishi lafiya ka dawo dashi lafiya sannan ka kareshi ka bashi abinda yaje nema, ya Allah ka nesanta shi da cin haram ka bashi halak d’insa da yaje nema.
Ciki ta koma ta nemi waje ta zauna sannan ta d’auki wayarta ta kira Asmau da Ihsan, conference call ne kamar yadda suka saba, hlo girls how fa: lafiya kalau ya kuke, fine ya mai gidan klu ! Nace idan kun samu dama koh zaku d’an shigo gidana? Wallahi nayi missing d’inku ! Toh inji ihsan bari muga ni dai yanzu ina yiwa mom aiki ne zuwa anjima zaki gammu, alright bye bye sannan sukayi ending call d’in .+
~~~~~~~~~~~~
Ba ayi minti ashirin da gama wayarsu ba Raeesah taji anyi knocking!! Yes come in ‘
Knock knock!! Aka qara knocking har sau hud’u! A’a waye idan bazaka shigoba Toh ka koma! Ance ka shigo kuma kana faman knocking Toh ba sai ka koma ba…
Da qarfi taji an bankad’o kofar an shigo 😳
Bak’uwar fuska ta gani tayi tsaye a kanta sai faman kalle kalle takeyi, Wow this is Amazing… fantastic 🌚lallai masoyina ka kashe kud’i a gidannan sai dai ba wannan ce matar da ta dace da shiga gidan ba , ni yakamata ace ina cikin wannan gidan!
Idanuwa Raeesah ta zazzaro tana mata kallon Rashin sani domin batasan wannan fuskar ba
Amina ce dai a cikin palon Raeesah a tsaye tana mata rashin arziqi,
Tsaye Raeesah ta tashi!! Ke kuma daga ina? Waye ya aiko ki? Kuma mai kikazo yi?
D’ai d’ai ta fara takawa tana zagaye Raeesah , sai dai Raeesah ta kasa jurewa, hannunta tasa ta bigi qirjin Amina da qarfi , har saida Amina taji zafi sosai
Dalla malama kyaleni, ke kin san koh wacece ni? Abinda Amina take fad’a kenan Toh bari in fad’a miki idan baki sani ba , nice Ex-girlfriend d’in jameel kuma ina dauke da cikin jameel a jikina, saboda haka nazo ne domin ganin uban babyna,
Shin yana ciki ne? Koh ya fita?
Raeesah dai was speechless domin abin ya d’aure mata kai
Hawayen dake k’okarin fitowa daga idanuwanta tayi k’ok’arin hana shi fitowa ta daddage ta shanye,
Ya salam! Ya salam, ya salam!!
Abinda Raeesah ta dinga maimai tawa kenan a ranta, domin kanta ya kulle gaba d’aya ta rasa madafa,
Daurewa tayi ta daka wa Amina tsawa!
You bitch get out of my house , kije ku hadu a inda kuka had’u yayi miki cikin,
Tsaki Amina ta ja what ever! Xan fita amma fa zan dawo !
Tana fita Raeesah taja qofa ta rufe tareda matsanancin kuka, sulalowa tayi tun daga sama har qasa ta zube sharaf a kasa tana faman kuka,
Ni Jameel zai yiwa haka? Meyasa banga mutuwata kafin ganin wannan tsinanniyar ba, Allah ya isa tsakanina da kai jameel bazan yafe maka ba,
Saidai wata zuciyar na yi mata fad’a kan yanke wannan hukuncin da wuri, alhalin tasan halin mijinta koh waye ba mutum ne mai son kula mata ba,
Wani ihu mai gigitarwa ta saki wanda ya jawo har mai gadi saida yaji ihun kamar ana yankata,
Ihsan da Asmau ne suka qaraso da gudu domin sanin abinda yake faruwa,
A kwance suka tarar da ita tana tsanin kuka ,
Raeesah! Raeesah! Mai ya faru ? Meye aka miki ina jameel, keda wa, babu tambayar da ta iya amsawa a cikin tambayoyin da su Asmau suke mata, saidai nuni da takeyi da d’an yatsan ta tana nuna bakin qofa da alama akwai wani koh wata daya fita ba da dad’ewa ba.
Asmau ce ta ta nufi gate da gudu,
Gurin mai gadi ta nufa,
Mai gadi mai gadi!!
Naam! Ya amsa ‘
Yauwa mai gadi kafin shigowar mu waye kaga ya fita daga gidan nan,
Amsa mai gadi ya bata
“Eh Toh da safe dai oga ne ya fita kuma hajia ce ma naga ta rakoshi har parkin space, bayan shi kuma sai wata matashiya data shigo da mota harma ta dinga zagina domin ban bud’e mAta gate da wuri ba, da ta shiga gidan sai naga ta fito kamar ranat a b’ace, daga ita dai babu wanda ya shigo sai ku
Okay nagode, Asmau ta koma ciki da sauri,
Ciccib’ar Raeesah suka yi suka kaita har d’akinta,
Bayan wasu mintuna ne Raeesah ta bud’e narkakkun idanuwnan ta wanda sukayi jazir don kuka,
Magana ta fara cikin muryar kuka,
Wata ce ta shigo ta ci mun mutunci harda cewa wai tana d’auke da babyn Jameel.
What! Are you serious! Who is she
Wani sabon kukan ta tasa tana faman yi ,
Hak’uri suka fara bata suna lallashin ta tareda kwantar mata da hankali,
Amma dai wannan abu da mamaki , inji Ihsan
Raeesah bazan ce wannan matar tayi gaskiya ba domin kin fimu sanin halin mijinki, amma abin dubawa shine toh ita d’in wacece,
Bugu da k’ari ma kin san halin mutane a duniya baka san maqiyinka ba, akwai mutane da dama wanda basa son ganinki da mijin ki a kullum burinsu suga bakwa tare , amma ki qara haquri, kuma kiyi bincike tareda tunani mai zurfi kafin ki yanke hukunci,
Asmau ce ta matso daidai fuskarta ta share mata hawayen ta da gefen mayafinta, Raeesah bana so kici gaba da wannan kukan kuma ban so ki nunwa jameel cewa wani abu ya faru, ki natsu kiyi bincike , ki zama mar’atu saliha, kiyiwa mijinki biyayya sai ki rabauta, kar ki sake maqiya su shiga sha’anin ku kinji Raeesah na! Yauwa
A haka sukai ta bata baki har ta haqura sannan suka tafi ,
qarfe hudu jameel ya dawo gida, yaga palon babu kowa kuma bai ga matar tashi ba, domin ya saba idan ya shigo yayi arangama da kyakyawar fuskarta,
Salam sunshine ! Sunshine! Where are you? Sunshine I’m back…
shiru kakeji, kofar d’akin Raeesah ya bankad’a ya shiga,
Sunshine, sunshine, meye yake damunki ? Hannu ta miqo mishi ya riqeta,
Tsorata yayi da jin yanda jikinta yayi zafi sosai,
Subhanallah! Meya ya same ki tashi muje asibiti ,
Cikin dashashiyar murya da tasha kuka ta amsa no I’m okay
Aa ki tashi muje asibiti ga jikin ki yayi zafi, kuka ta fara tana fad’in ni baxanje asibiti ba, na sha magani, okay my love barin samo miki abinda zaki ci, aa I’m not hungry, kiyi haquri , janyo ta yayi ya qanqameta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali har wani sabon baccin ya dauketa.Godiya mara misaltuwa ga masu karatu
Masoya kuma y’an uwa ❤️🍯💝
Zubeefly na qaunarku , tsofaffin masu karatu
Harma da sabbin masu karatu 🤗💝
Babu laifi idan kunyi tambaya a comment box, a shirye nake da na amsa bambayoyinku da karb’ar gudun mawar ku 💝
Love you oll 😍😍
Thank you for giving me Nd my precious little book a chance.
Even if you decide not to continue reading, thank you for taking the time to check the previous pages. Maybe the time isn’t right but it will always be here.
Always feel free to ask me any Question !Via
Comment box, DM, Twitter and Instagram everything is fine InshaAllah. 🤲🏻💝
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~,
Rana mai kamr ta yau laraba, Jameel bai fita aiki ba domin ya gaji sosai, kuma yana buqatar baiwa matarsa lokacin sa ,
A kwance suke a kan gado, tana maqale da shi, yana faman jan gashin kanta yana massaging d’in gashin ,
Sannan kuma ga wayarsa a hannun Raeesah tana faman dannawa , (are you thinking what I’m thinking🤔)
Sai faman shige-shige take, a wayar
Shi kuma gogan yana ta kwararo mata labarai kala kala , harama da labarin anty Humairan sa yadda suka taso cikin qaunar junan su, saidai abu kad’an yake had’asu fad’a, saboda yawan zolaya irin ta jameel tun yana yaro .+
Saidai fah ita Raeesah har yanzu bataga wani abu makamancin wannan bah don shi wayarsa ma babu lambobim y’an mata a ciki inba y’an office d’in sa ba,
Amma abin da yake qara d’aure mata kai shine Toh idan har jameel baya da alaqa da matar da tazo, Toh mai yasa zatace tana d’auke da babyn sa? Wannan shine abun tambaya!
A haka dai taji ma duk ta gaji da bincika wayarsa, inda ta waiga gefen fuskarsa taga da alamu bacci yayi gaba da jameel d’in nata , amma dai wannan mata sai kinci ubanki!
Tabbas kinyi da y’ar halak! Kuma mijina yafi qarfinki! Sannan zanyi maganin ki InshaAllah
Kinyi da Hauwa kulu…..
A ranta take fad’in wannan, (hmm yaya zata kasance?)
itama gyara kwanciya tayi a kan kirjinsa ta kwanta, basu tashi ba sai misalin qarfe hud’u na yamma .
~~~~~~~~~~~~~~~~~~
Washegari
Raeesah ce a cikin BMW tareda drivern Jameel wanda jameel yayiwa umarni da ya dinga kaita duk inda zataje,
A qofar gidan su Ihsan akayi parking ko minti biyar ba ayiba saiga Ihsan da Asmau sun shigo tare ( dama Asmau tana gidan su Ihsan tun tuni) ,
Tafiya suka fara gashi har sun kai kimanin mintuna Talarin suna tafiya a motar ,
Cikin mintuna arbain suka isa inda zasu , bayan tafiya mai tsaho da sukayi ,
Raeesah tace da su Asmau:
Ku jirani a moto,
Kar ku shigo, saidai idan nace ku shigo
Amma ku jira anan,
Toh suka ce da ita,
Ki dai yi a hankali , kuma harki yi mata da sauqi, ki nuna mata ke kin fita iya bariki, koh kadan kar ki raga mata, best of luck,
Abinda ihsan tace da Raeesah kenan, sannan ta fita a motar ta nufi cikin gidan da sukayi parkin a gate d’in,
Cikin isa da taqama Raeesah ta bud’e front door ta shiga cikin qwarjini , kai zaka zaci dama ta saba shiga gidan ne.
Sunglasses d’in dake fuskarta ta cire ta maida shi saman forehead d’inta,
Matar dake zaune a palon ce ta ragana don Ganin wacce ta shigo mata gida without permission ‘
Ke baiwar Allah ya zaki shigo min gida
Ba tareda izini ba?
Ai a ganina bai kamata in shigo da neman izini ba,
And by the way ! Ba wajenki nazo ba
Wajen Amina nazo,
Hummm idan tana nan inason ganinta ,
Waya hajia binta ta d’auka ta kira Amina !
Hlo daughter where are you,
Mommy I’m in my room
Okay come downstairs!
Alright mom.
Da sauri ta sauko don taga mai ke faruwa domin Tasan dai mommynta bazata mata irin wannan urgent kira ba,
Mommy gani:
Yauwa nemanki aka zo yi
Raeesah wacce ke gefe ta fara clapping hannunta,
99dayz for the thief one day for the owner,
Abinda tace da ita kenan
Kina mamakin yadda akayi nazo gidanku,
Toh bayan kince min kina d’auke da cikin na mijina a jikin ki, tun daga ranar na na fara neman details naki,
Humm… sai gani yau a gidanku,
Nazo ne domin in miki warning akan mijina kar in sake jin kin ce mijina yayi miki ciki, idan ba haka ba toh sai nayi miki abinda koh kare bazai ci ba, and by the way … ki shirya mu tafi asibiti domin ayi miki pregnancy test daga nan sai in raka ki court ki kai report,
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ,
Abin da hajia binta ke maimaitawa kenan, Amina ashe baki da hankali? Haka kawai kije ki samu mata kice mata kinada ciki kuma na mijinta?
Ince last month ma kinyi period, ?
Baiwar Allah kiyi haquri don Allah ki yafemata amma yanzu babu inda zaki da ita tunda babanta baya nan kiyi haquri wlh qarya take!
Amina kuwa dake zaune kan leather sofas hannu ta qame a kirjinta tayi shiru , tana mamakin yadda akayi Raeesah ta gano gidansu,
Da qyar dai Aka shawo kan Raeesah ta haqura Amma da tace sai Anje anyi Test zata kyalesu,
Fitowa tayi ta dawo cikin mota,
Babe yane?
An gama wannan sai dai kuma wani idan ta sake ,
Labarin yadda sukayi da maman Amina ta tsara musu, dariya suka tayi suna nishad’i
qawata shi yasa nace kibi abin a hankali saboda wannan shegiyar zata iya rabaki da mijinki, ki dai yi a hankali kuma ki ci gaba da bin mijinki ,
Taji dad’i sosai da irin shawarar Asmau , domin samun irin wannan qawayen da wuya,
Nagode dear Allah ya nuna min Auren ku
Ameen suka ce sannan kowacce ta koma gida, Raeesah kuwa special dinner ta fara shiryawa jameel d’inta bayan ta koma gida,
Saidai wani irin shawqin soyayyar sa da ke qara shiga ranta. Tamkar sabuwar soyayya.
A b’angaren Amina kuwa tasha fad’a a wajen mommynta duk da basa yi mata fad’a amma yau dai kam tayi mata don yanzuma ta hanata fita har na tsahon sati uku.
How was this page?😍
~~~~~~~~~~~~~
Sallar Asuba sukayi a jam’i , jameel ne ya ja musu sallar yana gaba tana bayansa
Bayan sunyi sallama ne, sukayi azkar, Jameel ya jawota kan cinyarsa ya cire mata hijabin dake wuyanta,
Good morning sunshine
Morning my love tace!
Inaso yau ki tashi ki fara shiri domin zamu je wani waje,
My love ina zamuje?
Ke dai kawai ki tashi,
Toh tace sannan ta tashi,
Toilet ta nufa, ta fara wanka, bayan mituna kad’an ta fito da dan towel d’inta,
Wardrobe ta nufa zata dauki kayan sawarta, da sauri jameel ya zo yayi tsaye a gaban wardrobe d’in,
Baby excuse ! Aa sunshine na dauko miki kaya,
Kuka ta fara no baby, ka matsa in dauko da kaina, haquri ya fara bata akan kar ta bud’e wardrobe din, amma sam taqi, tunani jameel ya fara akan yadda zai b’ullo mata kar ta bud’e wardrobe d’in saboda surprise d’in da yake so ya mata, tunani yayi dama Raeesah akwai ta da tsoron kyan-kyaso,+
Toh wallahi akwai kyan-kyaso a cikin wardrobe d’in nan shiyasa bana so ki bude,
Wani uban tsalle Raeesah ta daka ta qan qame shi tana kuka, wallahi na fasa bude wa!
Na fasa sam har abada! Zan saka wanda ka d’auko min,
Shed’anin murmushi ya saki, sannan ta fara shafe jikinta da mayukan qamshi, shima jameel wankan ya shiga , saidai ita Raeesah har yanzu jikinta bai bata ba domin har yanzu da sauran tsoro a ranta, bayan ta gama makeup ne ta duba wajen da kayan nata yake,
Wow, black top ta gani kan gadonta wacca akayi printing zanen sunanta da jameel A manyan baqi RAMJEEL,
Gaskiya rigar ta burgeta,
Hmm wato yau riga da wando zan sa kenan! A ranta take fad’ar haka,
Blue jeans ne shima, saidai da alamun jameel shima irin kayan zaisa, bayan ya fito daga toilet ne ya ya fara shiri shima,
Dukkan kayan da tasa irinshi Jameel yasa, trousers and top sai black face cap da jameel yasa mai Tambarin R ita kuma tayi rolling black mayafi a kanta, sai black shoes da suka sa iri daya, couples kenan sunyi kyau sosai kamar ka sace su.
Tafiya sukayi mai d’an tsaho Raeesah har ta fara bacci, qarfe 7:20 suka isa international airport ,
Babban abin mamakin Raeesah shine yadda jameel ya iya tsara abubuwa cikin dubara,
Akwati guda biyu taga driver ya fito dasu daga bayan mota ,
Baby wannan ai akwatin mu ne ina zasu kai mana kayanmu?
Cikin jirgi! Ya amsa,
Ina zamuje?
Mauritius ya amsa,
Kamar a mafarki Raeesah take jin kalaman nasa,
Ya salam! Tace a cikin ranta.
Babban abin mamaki abin farinciki abin burgewar da Raeesah ta gani a airport, Private jet d’in jameel wanda batasan da shi ba koh labarin sa, wanda aka rubuta a jiki kamr haka
RAMJET Airline.
Ai mutuniyar batasan lokacin da ta fad’a jikinsa tana kukan farinciki, ilove you so much my husband my everything,
8:30 suka tashi bayan sunyi breakfast da hamburger da coffee a airport, headphone guda biyu pilot ya kawo masa, guda daya jameel ya dauka ya kunna Qira’a ya sa mata a kunne, dai dai lokacin da akayi announcing saka seatbelt jameel yasa nasa headphone d’in.
Mauritius!!
Sir Seewoosagur Ramgoolam international Airport , anan jirgin nasu yayi landing , ba,ayi minti biyar ba aka turo musu da driver daga hotel domin ya dauko su saboda dama an san da zuwansu , kayansu drivern ya sa a bayan mota mai qirar BMW sannan ya bude musu suka shiga,
In a few minutes suka isa The Aravalli Spa, Mauritius Luxury , wanda yake babban birnin Mauritius ,
Suna shiga aka miqa musu receipt wanda aka tanadar musu , poòléur 4, Room 106 ,
Raeesah dai bata cewa komai ita dai kawai bin jameel take kamr raqumi da akala, d’akinsu suka shiga wanda kyawun decoration d’in ya kusa tayar mata da hankali har taso ta d’an yi qauyanci 😃
Shi kuwa jameel da yake yasan yadda wajen yake shiru kawai yayi yana faman yi mata dariyar mugunta
1
Da shigar su d’akin jameel ya baje a kan gado domin babu wanda bai gaji ba a cikin su, ita kuwa hanyar toilet ta nufa domin ta watsa ruwa, sai da ta gama wankan ne ta fito da pink towel a jikinta sannan ta Sa kayanta a laundry basket,
Babayna ka tashi kayi wanka!
Toh sunshine wlh I’m very very tired ne!
Sorry baby,
Bayan ya fito daga wanka ne ya dauki wayar sa yayi musu ordering Archard Relish of pickled vegetables da mustard Energy drink.
Cikin minti biyu waiter yayi knocking room 106 domin basu abincin, thanks yace bayan ya karbi tray din abincin,
Raeesah dai ta qosa Don ya gama sa kaya su fara cin abincin domin qamshin sa qara mata yunwa yake,
Sunshine I’m done can we eat now?
Yess tace cikin hanzari don rabonta da abinci tun a Nigeria Airport,
Bacci mai nauyin gaske ne ya dauke su bayan sunyi dinner mai nauyi,
WASHEGARI…
Shiri ma,auratan sukayi cikin fararen kaya,?Raeesah Gown tasa shi kuwa jameel riga da wando yasa suma farare domin zagaya gari, farinciki gun Raeesah ba,a fad’a,
Uber driver jameel yayi ordering domin bayaso ya fita da motar hotel .
Mon plaiśir Restaurant suka fara zuwa ,
Saidai ita Raeesah abun ya d’aure mata kai,
Baby ya naga restaurant d’in nan babu kowa?
Don’t worry about that sunshine na riga nayi bucking d’in wajen nan,
Hmm tace sannan ta saki dan murmushi ilove you hubby,
Love you more sunshine 🤗
Wheat pancakes stuffed with ground peas aka kawo musu a table d’in da suke ,
Su Raeesah sai selfie kamar baza,a dena ba, bayan sun gama ne ta kira waiter guda d’aya domin yayi musu pics,
Wonderful white and the island boost suka wuce , over 150km of beaches around the shoreline widely planted with sugar cane ,
Wajen yayi matuqar had’uwa Raeesah kuwa pics ba,a magana har phone storage ya kusa ya cika, don har mat suka shimfid’a sannan aka kawo musu fresh water prawns da hot sauce,
Sai qarfe 11 na dare suka dawo masukin su sannan suka kwanta, Asubar fari jameel ya tashe ta don sake wani shirin fitar,
Sai dai Ina… jikinta yayi zafi kamar wuta, ga headache mai tsanani,
Karfe 8 jameel ya kirawo female doctor daga dholl puri hospital domin ta duba masa Sunshine, duk ya rikice yabi ya damu,
Bayan ta gama ne ta sanar musu da Cewar Raeesah na Dauke da 4weeks pregnancy.
Farinciki mara misaltuwa a gun jameel ita kuwa Raeesah sai wani qara narkewa take kamar butter,
Jameel ba kunya ya kira mommynshi don sanar da ita abinda ke faruwa, saidai Raeesah bata so hakan ba gashi har ta fara missing maman hauwa da abbanta,
Kuma jameel yace bazasu koma ba sai sunyi three months.
Rauyuwa dai ta sauya wa way’annan masoya jameel da Raeesah,
Yau ma daga Rougaille yake a motar Hotel ya je, diamond Ring ya siyo wa Raeesah ya sa mata a hannayenta, godiya mara misali ta dinga kwararowa tana godiya ga Allah daya bata miji mai qaunarta, kuma tana roqon Allah yasa ta haifi mai kamarsa domin ya gado babansa, kuma Allah ya mayar dasu gida lafiya don taga maman hauwa da abbanta , ihsan da Asmau.
ALHAMDULLILAH Ala kulli halin
Nan ne na kawo muku qarshen wannan shahararren littafi mai suna d’iyar fari,