DOCTOR EYSHA CHAPTER 3 BY FANAN_A.A
“*Luxury* me 😳” ta fada tana miƙewa tsaye .
“bakiji abinda Na fada bane haka nace *Luxury ward* ko bazaki iya bane ” ya faɗa yana juyi akan kujerar sa .
“kaima kasan halin dad bazai taba yadda da wannan Batum ba, Na Waare ɓangaren Masu kudi a hospital dinsa ba ,kasan matsayi ɗaya ya ɗauki mutane gaba ɗaya ,kasan dai bazan iya ba try to understand please” takai ƙarshen zancen murya a sanyaye .
” yayi kyau doctor zahra nagode sosai kina iya tafiya” ya fada yana nuna Mata hanyar fita.
“kayi hakuri Zan faɗa masa kuma inshaallahu zai amince ” ta faɗa jiki a sanyaye yayin da take haɗa files ɗin gabanta.
*Dr Aryan*
Zaune yake a ɗakin sa yana hada duk wani abinda yake buƙata A Wajen aiki, Dan gobe ne zai koma bakin aiki , white coat dinsa CE ya ɗauko daga drawer, Abu ne ya faɗo daga cikin aljihun rigar , duƙawa yayi da niyar ya ɗauko abinda ya faɗo,
Ƙwasham abin daure gashin *doctor eysha* ya gani murmushi yayi Wanda ya bayyana fararren haƙuransa “Eysha rigima yaushe kuma abin ɗaure gashin ta Wanda tafi so yazo nan ” tunawa yayi ɗazu da suka haɗu a Wajen wannan accident ɗin anan ne abin ɗaure gashin ya shiga nan “Turkashi ! ,Yau komin dare nasan sai tazo Neman sa ,Dan kuwa bata Wasa dashi , saboda Shi kadai ne abinda take gani tana Tina iyayenta.
(Kada Ku manta fans gaba daya a Kashmir hospital Babu Wanda yasan asalin Eysha sai doctor Ibrahim da kuma doctor Aryan kasancewar sa shine babban abokin ta kuma halin su tazo ɗaya, sai kuma doctor kaseem Wanda Shi Dan Jin ƙwaƙwaf ne da bin diddigin mutane ).
*Doctor zahra*
Tunda ta fito daga office din Dr kaseem Babu inda ta nufa sai office din Dr Ibrahim, tayi sa’a kuwa Babu kuwa a office ɗin,bata jira aka bata iKON shigowa ba kawai ta faɗa .
” daddy Na Wajen ka nazo ” .
“Nasan waje Na kika zo mana tunda Ni kaɗai ne a office din , Zahra wai yaushe ne zakiyi hankali ne ki ƙoyi sallama ” ya faɗa Rai aɓace .
” daddy look Naga fa Babu kuwa a office din, kaga Ni shiyasa Na shigo kuma ai nan din office din daddy nane ba sai Na jira an man izinin shugowaba” ta fada tana murguda baki wai ita Dole haushi take ji “kuma Aida Dr maryam CE Na tabbbata ita bata yin laifi a Wajen ka nasan ai baza kayi Mata ihu akai ba .
Shuru yayi yana mamakin Hali irin Na diyar tasa ,Dan yanzu Al’amarin ta ya fara bashi tsoro abu kullum sai lalacewa yake , Indai gatan daya nuna Mata shine yasaka ta koma haka Allah wadaran gata a duniya ,”yanzu ba wannan ba menene ya kawu ki Dan nasan banza kawu banza kasuwa “.
“daddy dama wani abu ne ya kawu Ni dama so nake a bude Luxury ward a Kashmir hospital” ta fada cike da ƙarfin gwiyewa .
” What! Me kika CE , impossible Dan kuwa badai a Asibiti Na ba Dan bazan taba yadda da wannan haukan ba ” ya fada Rai abace .
“okay ,well that’s good yayi kyau daddy yau ka nuna man matsayi Na a Wajen ka ,yanzu ka nuna man ba ka ƙyauna ko kadan , tohm yau ina so ka kwana da sanin Dole ka zaɓi daya tsakanina da Dr maryam, ka zaɓi daya ɗiyar ka ko budurwar ka” ta faɗa yayin da take tashi tsaye .
Tun lokacin da Dr zahra ta shigo office din Dr Ibrahim, Dr maryam take Wajen a tsaye saboda bata so ta shigo office din ran Dr zahra ya ɓaci Dan tasan Dr zahra bata ƙyaunar ta ko kaɗan , ganin yanzu zata fito daga office din yasa Dr maryam saurin barin Wajen amma hakan baiyu ba Dan har ta fito,
Wata muguwar harara Dr zahra ta watsa Mata ,ita kuma sai ta mayar Mata da murmushi .
Dr maryam ƙoƙarin barin Wajen tayi Dan yadda taga ran Dr Ibrahim yake a ɓace ba kula ta zaiyiba, Babu ɓata lokaci kuwa ta juya zata tafi , bazata taji murya Na fito wa daga office din Dr Ibrahim ” ina zaki je ne ki dawo Dan Na ganki……..
Fanan_A.A❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️