DR BOBBY CHAPTER 1 BY AISHA RANO

Dogon building ne mai matukar kyau da tsaruwa…sannan yanada girman da baka isa kace ga iya inda ya tsaya ba…daga ciki akwai makeken surrounding mai daukeda shukoki iri daban daban da sukayi matukar qawata wajen…ga wani tafkeken titi da ban samu ganin iya inda ya tsaya ba a shimfide hadda roundabout kamar dai normal hanya…kallo daya zakayima makarantan kasan bana ‘ya’yan kananun masu kudi bane domin tun daga yanayin gini da yanda akayi tsarinta ko university albarka…a takaice dai kallo daya zakayima FCNM kasan makaranta ne daya amsa sunanshi makaranta…kuma makaranta ne da duk wanda ka gani a ciki zakasan iyayenshi manya manyan attajirai ne…ko ina yayi tsit sai few students dake kaiwa da kawowa kasancewan duk students suna classes dinsu sai securities da masu gadi da kowa ke various post dinshi…ana wangale gate wata Hadaddiyar Range Rover ta shigo ciki baqa wulik daidai da glasses dinta baqin tint ne a jiki hakan yasa baa iya ganin wanda yake ciki…ta karasa parking lot da aka rabashi biyu tareda indicating staff and students parking area…kai tsaye staff parking area motan ta nufa tayi parking cikin wani babban car park da yafi duk sauran na wurin girma…securities da some of staff da sukaga shigowan motan sukayo inda tayi parking da sauri kamar yanda suka saba duk proprietor yazo har rige rigen zuwa tarbanshi sukeyi snn su take bayanshi har zuwa office dinshi…driver na gama parking ya bude ya fito saidai kafin ya zagaya ya bude motan wadan nan mutanen sun rigashi nan take mutumin dake cikin motan ya bayyana…legs dinshi yafara saukowa waje kafin shima ya fito a hankali yana kallon mutanen…matashi ne da ak’alla bazai wuce 31 to 32 years ba…dogo ne sosae don cikin maza goma da kyar zaa samu guda daya wanda tsayinsu zaizo daidai dashi duk da cewa yanada dan jiki kai tsaye bazaa kirashi da siriri ko kuma mai qiba ba…komai tsawon namiji duk ya jera dashi sai yaga ya zama gajere kusa dashi…sannan yanada wani irin haske mai daukan ido wanda kallo daya zaka mishi ka gane ba full blood bahaushe bane…ko hannunshi ya daga zakaga tarr sbd tsabar farinshi…sanye yake cikin three piece suit dark blue dayayi matching da jikinshi sosae…tun daga gashin kanshi har zuwa sajenshi sun kwanta luf gashi sai shinning suke as a result of gyara da sukesha…yanada round face mai daukeda dogon hanci da matsakaicin baki…sai eyes dinshi da duk ya ware maka su a kanka saika tsorata sbd tsabar girmansu and su kansu eyeballs dinshi abun kallo ne..fararene tas sai wajen bakin kuma nashi ya kasance golden brown…sune irin idanun dake ladabtar da mutum komai rashin mutuncinshi…sune kuma irin idanun da suke sanya mata kware mishi domin kallo daya zakayi musu ka gane ba kowane irin ordinary eyes bane…they are kind of special kaman yanda mamallakinsu shima ya kasance special…hannu yaketa faman mikawa staff din nashi suna gaisawa domin bai son durkuson da suke mai sam…yafi gane suyi musabiha kmr yanda addinin musulunci ya tanadar…bayan sun gama gaisawa suka shiga binshi a baya har zuwa office dinshi as always driver na rikeda brief case dinshi…secretary na ganinsu ta mike da sauri ta bude office din suka shiga…bayan ya zauna ya dauko kudi ya basu suka fita suna zabga mishi godia as always…Obi driver ya ajiye mishi briefcase shima ya fita…Ngozi(his secretary) ta shigo itama ta gaisheshi snn ta mika mashi schedule dinshi tareda wasu files kmr yanda ta saba…bayan ya karba tasake mika mashi wani envelope tana fadin”Sir you have a message from Kinana Hospital”…baice komai ba ya sake karban envelope din ya ajiye…ganin har yanxu tana tsaye yace”is there anything else?..”da sauri tace”Ss..Sir its Doctor Bukar…he said..”bata karasa baya katseta da fadin”hold it… how many times do i have to tell i dont want to hear about him?..”kai a kasa tace”Sorry Sir”…yace”this should be your very last warning…if you dare repeat this mistake again you are fired”…jikinta har ya fara rawa tace”am very sorry sir… i will never do that again”…ba tareda ya sake kallonta ba yace”you can go”…yana rufe baki ta juya ta fita daga office din…shi kuma ya dauki files data shigo dasu ya fara dubawa…yayi signing inda ake bukatan signing dinshi snn ya shiga duba schedules din…ba wasu schedules bane masu yawa kawai staff meeting zasu fara 9 zuwa 10:30…by 11 zai shiga Area Hostel ya duba construction na new apartments da ake a both male and Female hostel sai kuma ya shiga College Clinic by 2…tsaki yaja yana ajiye file din shi bai cika son shiga college clinic ba shiyasa yayi employing Dr Bukar sbd ana samun cases din da sukafi karfin nurses…dukda iya students ake dubawa ciki shidai bai cika son shiga ba sam…yanxu gashi dole saiya shiga tunda Dr Bukar din was fired…ya jingina da kujera yana shafa lallausan gashin kanshi…ya zama dole ya sake employing wani Dr dan bazai iya hada duk aiyukanshi da shiga college clinic ba tunda ba ko yaushe yake shigowa college din ba sai Thursdays da Fridays…sauran ranakun yana hospital dinshi mai suna FREEDOM SPECIALIST HOSPITAL… duba agogon hannunshi yayi yaga yanada sauran time kafin 9 dan haka ya janyo computer dinshi ya fara aiki a ciki…sai yanxu na samu daman karema office din nashi kallo and i was like”Wow wow wow”…my people its one huge office you know…tunda nake ban taba ganin office mai kyau da tsaruwanshi ba…daidai da funitures dake cikin office din abun  kallo ne hadda su dinning ko office din governor sai haka lol😂…a jikin wall din office din wani katon picture dinshi ne yana sanye da white suit daya matukar yi mishi kyau sosai…ya sunkuyar da kanshi yana rubutu aka dauki picture din da gani bai san an dauka ba amma fadan kyawun da yayi is a waste of saliva…a kasan pic din an rubuta Dr.BOBBY ATTAHIR WAZIRI…sai kuma in bracket aka rubuta CEO FREEDOM GROUP OF SCHOOLS AND HOSPITALS…Landline dake ajiye kan table dinshi ne ya fara ringing…yana dauka secretary dinshi tace”The Provost wants to see you sir”…a takaice yace da ita”ohk”snn ya ajiye wayar…ko two minutes baayi ba wani matashi ya turo kofa ya shigo…yana sanye cikin white shirt long sleeve da black trouser yayi tuck in shirt din…dogo ne shima mai haske saidai kallo daya zakayi mishi ka gane ba bahaushe bane…ya karasa ciki ya zauna yana kallonshi with a smile yace”the Proprietor Sir”…dan dagowa yayi ya watsa mashi wani kallo snn yacigaba da abinda yake…daya guy din ya bata rai yana cewa”nidai ka dena hararana da wnn big golden eyes din naka pls…haka nan kasa na fara having nightmares”…dena operating computer yayi yajuya yana facing dinshi sosae…cikin husky voice dinshi yace”Nuruddeen”…da sauri ya amsa da”yes Bobby”…yace”just go straight to the point nasan tunda kazo office dina akwai abunda ya kawoka…say what you want to say”…kmr jira yake kuwa ya gyara zamanshi before yace”its about Dr Bukar..dont you think he deserve a second chance?..”tsaki Bobby yaja tareda fadin”i don’t want to talk about him”…da sauri Nuru yace”but you have to Bobby…give him a second chance…we are all bound to make mistakes so forgive him tunda har yayi nadama…please!”…girgiza kai Bobby yake voice dinshi na nuna tsantsan bacin ran da yake ciki yace”i will never forgive that bastard..never”..dafe goshi Nuru yayi ya rasa ta yanda zai bullo mishi…can yace”Bobby me kakeyi ne haka?…this is unlike you?..”yana rufe baki yace”bazan taba yafema wnn mutumin ba…i trusted him amma yaci amanata…this is the problem with Hausa Fulani people…kwata kwata basu san alkhairi ba snn basu da imani basuda rikon ama..”Nuru bai bari ya karasa ba yace”enough please!…zaka fara kou?…you are always looking for a way to insult Hausawa ko Fulani sai kace kai ba bahaushen bane”…da karfi Bobby ya buga table dake gabanshi cikin karaji yace”stop calling me bahaushe niba bahaushe bane…infact babu abinda ya hadani da hausawa so mind your tongue”…murmushi sosai Nuru ya saki yana kallon yanda yake ihu sai kace cewa yayi shiba musulmi bane…har kullum baya dena mamakin kalar kiyayyan da Bobby kema Hausa Fulani…ya tsanes
u to the core shiyasa ko cikin staff da securities dinshi yawanci ba hausawa bane infact a duk Company dinshi da kyar zaa samu hausawa goma da suke aiki…ko a wurin aiki baison hada hanya da hausa fulani ya rasa gane kan wnn kiyayya…and the funny part of abun is shi kanshi Bobbyn jinin hausa fulani ne…his father was Fulani from Gombe state and his Mother Igbo from Enugu state shiyasa always yake considering kanshi as igbo sbd Mom dinshi is one…wnn dalilin yasa ko cikakken hausa bai iyaba sbd bayi yakeba idan yana mgn da hausa zakaji kaman he is learning cox yanda yake pronouncing words din kadai zaisa ka fahimci ya hada jini da qabilu and a gidansu ma kuma sunfi magana da english ko igbo din at times ko da hausa akayi mashi mgn sai ya amsawa mutum da English ko igbo…yasan idan yaci gaba da jan mgnr ransu ne zaizo yana 6aci dan haka ya mike hands dinshi a aljihu yace”See you at the meeting”snn ya fita daga office din…Bobby ya bishi da kallo cikeda takaici…wlh ba don alaqar dake tsakaninshi da Nuru ba yau saiya ci mutuncinshi for calling him bahaushe…he hates everything that has to do with hausa fulani…he hates them with passion…Nuruddeen abokinshi ne tun a University…tare sukayi karatu a America saidai shi Bobby yayi specializing ta bangarori da dama shi kuma Nuru baiyi ba…Dr.Nuruddeen Ugochuku Dominic shine cikakken sunanshi and he is also a muslim igbo from imo state zama ya kawoshi kano har ya hadu da Bobby a America…bayan sun kammala karatu sun dawo yayi mishi provost din FCNM sbd abotan dake tsakaninsu…shima kuma ya rike mishi amana dan tsahon shekaru basu taba samun matsala ba.

10:30 sharp suka fito daga meeting…direct Bobby office dinshi ya koma har yanxun ranshi bai dena baci kan abunda Nuru yayi mishi ba…yana shiga ya wuce ya hadama kanshi coffee snn ya zauna kan one of luxury sofas dake cikin office din yana sipping coffee din a hankali yana sauke numfashi…dama duk yake cikin bacin rai baida abun sha daya wuce coffee shiyasa ko a gida yanada coffee machine a flat dinshi duk yaji yana son sha hadawa kawai zaiyi…saida ya shanye coffeen yana kokarin komawa seat dinshi wayanshi dake aljihunshi ya fara ringing… yana daukowa yaga My Mummy rubuce kan screen with all sort of heart emojis…murmushi kyakykyawa ya saki kafin yayi picking call din wanda har hakan ya bani mamaki sbd yanda naga lokaci daya duk wann sadness dake kan face dinshi ya bace…hakan alama ne na tsanstan kaunar dake tsakaninshi da Mom dinshi…yana dauka cikin igbo yace mata”Mummy nah”…itama da igbo din tace”Bobby nah”…yana sake sakin smile yace”Mummy how are you?..”tace”ina lafia Bobby..yanxun wani employee dinka yazo ya sameni”…shiru yayi yana tunanin waye?..lokaci daya kuma zuciyarshi tace mishi Dr Bukar ne…jin baiyi mgn Mummy tace”are you there?..”yace”yes am listening Mummy”…tacigaba da fadin”he said his name is Dr Bukar…he told me all that happened between you two kuma ya fadamin yayi nadama dan haka ina ganin you should get him back to his job inshaAllah bazai sake faruwa ba”…Bobby yayi shiru yana sauraronta kmr ruwa ya cinyeshi…yasan wnn duk plan din Nur ne…shine nan zai tura Dr Bukar wurin Mummy sbd yasan bazai taba iya tsallake umarninta ba…wani bacin rai yaji yazo mishi amma bazai iya nunawa Mummy ba kmr yanda bazai iya tsallake umarninta ba…tunda yake Mummy bata taba sashi yin abu yakiyi ba and bazai so ya fara yanxun ba especially not because of that bastard dan haka yayi lowering voice dinshi sosai yanda bazata gane he’s angry ba yace mata”it’s ohk Mummy inshaAllah zan maidoshi…i will talk to Nur sai ya kirashi ya fada mishi”…yana iya jiyo farin cikin da Mummy ta shiga kafin tace”nagode sosai Bobby Allah ya maka albarka…Allah kuma ya baka kids da zasu maka biyayya kmr yanda kakemin”…murmushi kawai yayi without saying anything… itama bata damu da cewarshi ba don tasan dama bazaice din ba tunda duk tayi mishi zancen aure ko yara haka yake behaving…kwata kwata ta kasa gane kan Bobby akan wnn alamari…tace”you send Obi by 1 yazo ya daukan muka abinci”…saida ya wani marairaice muryanshi yace”Mummy yau ba sai an kawo ba pls…am not hungry”..tun kafin ya karasa Mummy tace”No i insist..yanxun zan barka kacigaba da aikinka and make sure you take care of yourself”…yana wani lumshe eyes dinshi yace”i will Mummy..bye”…itama tace mishi”bye”..snn sukayi sallama…mikewa yayi a fusace ya fice daga office din zuwa office din provost wato Nur…secretary dinshi na ganinshi ta mike sauri tana wani sandarewa kaman taga soldier tace”good day sir”…ko kulata baiyi ba ya banka cikin office din…Nur na zaune da wata lecturer a gabanshi tana mishi bayanin wasu abubuwa kawai sukaga mutumi a gabansu…baidai ce komai ba sai huci da yake like an angry lion…Nur na ganin haka yasan sunyi mgn da Mummy dan haka ya mikama malamar file dinta yace”am sorry miss Fatima kije zuwa gobe ki dawo mu karasa”…ba musu ta mike da sauri ta fita daga office din dan Allah ya gani tsoron Bobby takeji…bama ita kadai ba almost all of his staff tsoronshi sukeji sbd yanda face dinshi kullum a daure kuma mistake karami sai yaceya kori mutum…saida yaga ta fita snn ya juyo yana kallon Nuru da angry eyes dinshi yace”why did you do that?..”Nuru ya koma seat dinshi ya zauna yana daga shoulders dinshi yace”because i have no choice”…a fusace Bobby ya sake fadin”but how dare you…who gave you that right…haka nan sai ka ringa tura kowane jick and jerk yana mgn da mahaifiyata…are you sick or something?..”dagowa Nur yayi ganin yanda yake ihu kawai sai yasa daria…Bobby ya sake kulewa dashi yaji kaman ya watsa mashi mari…”so i have become a mad person right?..”da sauri yace”No..kawai wnn hakilon da kake yake bani daria…kan dan karamin abu kaman wnn kake bacin rai haka…haba mana…you need to stop this pls”..wani malolo Bobby ya sakeji yazo ya tokareshi…bai sake yunkurin cewa komai ba kawai ya juya ya fita daga office din…kai tsaye nashi office din ya koma yana cizon dan yatsa…agogon office din ne ya buga 11 dan haka ya sake ficewa zuwa inda motarshi yake…Mr.Obi na ganinshi yazo ya bude mishi motar ya shiga snn shima ya shiga suka nufi hanyar hostel…ta mirror ya hango motar Nur na binsu a baya don tare dashi zasu shiga hostel din…shi kanshi hostel din  tafiya ce mai dan nisa tsakaninshi da inda classes dinsu suke…a fisrt gate suka fara tsayawa inda Male Hostel yake suka shiga suka duba aiyukan snn suka wuce next gate inda anan Female Hostel yake…basuyi wasting time ba nan ma suna gamawa kowa ya shiga office dinshi suka koma cikin school…har yanzun Bobby bai denajin haushin abunda Nur yayi mishi ba domin baiyi niyyar dawoda Dr Bukar ba sam dukda dama can sbd Nur din ya daukeshi aiki amma da bazai dauki bahaushe ya ajiye clinic dinshi ba…kowa office dinshi ya wuce..

Basu sake fitowa ba sai lokacin sallah…da yake staff masjid daban yake dan haka Nuru baiyi wahalar hango abokin nashi ba…yana kokarin zuwa ya sameshi kawai yaga ya mike ya fita shi kuma sai ya saki daria yana girgiza kai…yasan halin kayanshi tsaf duk wnn fushin babu inda zaije dole haka zaiyi hakuri ya barshi ko bayaso…shi kuwa Bobby ko office bai komaba ya nufi Clinic dake ta bayan office dinshi…Clinical instructor na ganisnhi ya mike tareda gaisheshi..

Bobby ya amsa a takaice snn ya bukaci sanin if there is any complicated case ko kuma emergency da yake bukatan doctor’s attention… da sauri Mutumin da ya dauko wani file guda daya ya fara mishi bayanin patient din da yanayin ciwon nashi kawai sukaji wani hadadden kara daga cikin Clinic din…Bobby ya kalli mutumin yana kokarin yin mgn ya sakejin wani karan this time around hadda magana amma bai gane me ake cewa ba…ranshi ne yaji ya sake baci ya kalli mutumin tareda ware masa idanuwansa yace”what the hell is happening here?..where is this sound coming from?..”da sauri mutumin yace”pls sorry sir…i think its..”Bobby bai bari ya karasa ba ya juya ya kama hanyan ciki inda yake jiyo sound din da sauri mutumin ya bishi a baya…so yake ya mishi bayanin ba wani serious abu bane amma he won’t dare sbd yanda yaga ranshi ke baci ba abunda bazai iya aikatawa ba…suna kara kusantowa karan da sukeji na kara karfi…saida sukazo daidai injection room snn ya tsaya…yana tura kofan daidai lokacin ta sake sakin wani karan tana fadin”aunty Meena dan Allah Nooo…wlh idan kika bani magani zansha amma banason injection pls pls plssss”…wani kullutun bakin ciki yaji ya sake tokare mai makoshi…yanxu dama duk wnn ihun akan common allura akeyinshi?..a fusace ya tura kofa ya shiga ciki aikuwa gaba daya mutanen dake ciki suka juyo suna kallonshi…shima kallonsu yakeyi daya bayan daya fuskanshi daure yanda kasan bai taba daria ba…Nurse Meena ce tsaye rikeda injection da swab a hannunta sai kuma wata student sanye da uniform dinta farare sol da ratsin pink a hannun riga alaman midwifery take karanta knn…dayar kuma tana tsaye ta kankame wadda ke sanyeda uniform din jikinta har shivering yakeyi sbd tsabar tsoro…dogon hijab ne a jikinta daya haura guiwarta da kadan sai skinny trouser dake jikinta red…almost rabin gashin kanta is out sbd batasa dankwali ba kuma hijab dinta ya dan zame kadan…gaba dayansu ba wanda hantar cikinshi bai duri ruwaba sbd wanda suka gani tsaye a wurin…da sauri Meena ta risina tana fadin”good afternoon sir”…ba tareda ya saki face dinshi ba yace”afternoon… what’s going on here?..”da sauri Meena tayi pointing yarinyar dake sanye da hijab tace”Sir batada lafia ne shine doctor yace a bata wnn injection din to ita kuma batason injection shine take kuka”…wani haushi Bobby ya sakeji ya juya yana kallon yarinyar da idanunta ke runtse sai sauke ajiyar zuciya take…murya a kausashe ya kalli wadda take rikeda ita yace”let go of her right now”…da sauri ta matsa daka jikinta tana sunkuyar da kai gabanta nata aikin faduwa…itadai ko Allah yasan bakaramin tsoron Proprietor dinsu takeba…shi kuma ya tsayar da idonshi kan yarinyar da har yanxu bata bude idanu ba dukda cewa tasan shine a wurin kuma jikinta bai bar shaking ba sbd tsabar tsorata da tayi..duk iskancinta tana tsoronshi sbd tasan bashida mutunci ko kadan…saida ya sake daure face dinshi snn yace”C’mon open those eyes before i slap you”..da sauri ta bude idanun nata ta dora a kanshi..sai kuma tayi kasa dasu da sauri sakamakon kadawar da hantar cikinta yayi…ya mikama Nurse hannu ba musu ta mika mashi injection din snn ta sake dauko another swab da hand glove shima ta mika mashi…yana karba  ya ware idanunshi masu ladabtar da fitinannu a kanta murya cunkushe yace”come over here”…tana dago kanta taga injection a hannunshi sai ta fara yarfa hannu tana fadin”dan girman Allah Sir…”bata samu courage din karasawa ba sbd idanunshi da suka ladabtar da ita…ta juya tana kallon friend dinta data rakota clinic din wai ko zata taimaka mata amma sai taga kanta a kasa…ta kalli nurse da clinical instructor suma duk taga alaman a tsorace suke sai ta shafama kanta salama ta shiga takawa a hankali sbd ciwo da kafanta ke mata har zuwa inda yake…hawayen dake zuba a idonta kuwa ko pump albarka…Bobby na tsaye da injection a hannu yasa glove a both hands dinshi har saida ta karaso snn ya sake murtukewa yace”turn your back”..batayi musu ba ta juya bayanta jikinta nata rawa…kallo daya yayiwa Meena ta gane me yake nufi dan haka ta karaso inda suke tareda kama hijab din jikinta ta daga bayan tayi covering dinsu da screen…ta sauke wandon jikinta a hankali nan take fair bombom dinta ya bayyana iya daidai inda zaayi injection din…Bobby ya dauke kanshi gefe tareda dan risinawa ya zura injection din a jikinta aikuwa ta saki wani irin ihu tana kokarin kwace kanta Meena tayi mata kyakyawan rikon da bazata iya kwacewa ba…saida ya gama injection din snn yayi disposing syringe a safety box ya cire glove dake hannunshi itama yayi disposing snn ya juya ya fita daga injection room din clinical instructor ya bi bayanshi…ita kuwa wadda akaiwa injection sai yanxun ta samu daman saki kukanta…tana kokarin dukushewa a wurin friend dinta tai saurin kamata suka zauna kan bed tanata kokarin mulmula mata wurin amma sai kaucewa take wai bataso a taba…zaunawa tayi kusada ita saida ta gama gursheken kukanta snn ta kamata suka fito daga dakin tana takawa da kyar sbd rikewan da kafan nata ya sakeyi…every month haka take fama duk zatayi period sai yasa mata ciwon kafa ko ciwon baya haka za’ayita tata6urza da ita kan allura sai kace small baby…har sukazo wucewa ta bayan office din Bobby bata dena kuka ba…saida suka fita ta samu daya daga cemet shairs dake wajen admin block ta zaunar da ita akai snn tayi dialing number da tayi saving da Lamido’s Bestie a wayarta…tana fara ringing ya dauka yana fadin”are you done?..”a hankali tace”yes muna ta wajen admin and kayi sauri kazo dan ta isheni da kuka”bata jira ko zaice wani abu ba ta kashe wayarta…ba bata lokaci kuwa sai gashi yazo inda suke…saurayi ne da akalla zaikai 25 years..baqi ne dogo kuma kyakyawa dashi yana sanye cikin uniform dinshi complete white yayi tuck in shirt dinshi…da sauri ya zauna kusa dasu yana duban mai sanyeda uniform yace”Billy kin tabbata ta samu sauki kuwa?..duba fa yanda take kuka?..”harara me kyau Billy ta watsa mishi tace”kajika da wani magana sai kace bakasan halin bestyn naka ba…allura fa akayi mata shine take wnn abun kamar an yankata”…bata rufe baki ba wadda akama alluran ta dago tana dubanta fuska shabe shabe da hawaye tace”ni wlh gara a yankani akan dai ayimin allura…sbd tsabar mugunta inata ce miki kizo mu gudu amma kika ki har saida wnn azzalumin yazo”..rai a bace Billy ta mike tana kokarin barin wurin tace”ba laifinki bane Lamido laifina ne da nake damun kaina a kanki…next time dama kina fara rashin lafiyarki saidai bestyn naki yazo ya kawoki Clinic amma bani Bilkisu ba…kuma wlh saina kira Ammi na bata labarin duk iskancin da kikayi”…tana gama fadin haka tayi wucewarta ta barsu a wurin…Lamido ta sake fashewa da matsanancin kuka shi kuma bestyn nata ya danyi kasa da murya yace”besty dont mind Billy kinji..yanxu ki daure ki tashi in maidaki hostel sai ki samu ki huta sosai”…yana rufe baki ta hau girgiza tana hawaye tace”i dont think i can walk besty..gaba daya leges dina sun sake rikewa”..ya sake fadin”daurewa zakiyi besty just try it zaki iya”…ba musu ta dafa kujeran da take zaune tareda mikewa da kyar…shima mikewan yayi ya nufi inda motarshi yake ya bude snn ya dawo ya taimaka mata suka karasa wurin..tana shiga shima ya zaga ya shiga snn tayar da ita suka nufi gate din hostel.

A bangaren Bobby yana komawa office yayi sanitizing hands dinshi with a hand sanitizer snn ya fada kan sofa ya zauna yana jin haushin abunda ya faru…gaba daya bacin ranshi sai ya karu fiyeda wanda yake ciki already…tunda yake bai ta6a ganin sangartacciyar yarinya kamn wnn yarinyar ba…allura kawai takema wnn abun…kawai yau ta sashi yin abunda ya manta yaushe rabonshi dayi koda a gidane kuwa..ya manta when last yayima wani injection ko yan gidansu akwai Nurse dake musu injection shi Mummy kadai yake yiwa amma yau wnn spoiled brat din saida ta tilastashi yayi mata…yana zaune lokacin da sukazo wucewa yaji wani gursheken kuka da takeyi kamar wadda akama operation…haka nan

yaji kaman ya dauki bindiga ya harbeta har saita dena wnn kukan…For Gods sake injection kadai take yima wnn ta6aran?..wnn wace irin lalatacciyar yarinya ce?..wai meyasa wasu iyayen if sunga sunada kudi sai suyita spoiling yaransu haka?..meyasa yaran masu kudi yawancinsu sangartattu ne?…koda yake ba duka masu kudi suka taru suka zama daya ba dan shidai yasan a gidansu ko Miemie ce tayi wnn iskancin ba abunda zai hanashi lakada mata dan iskan duka…sai faman sakin tsaki yake feeling extraordinary hot inside…yana cikin shan coffee Mr.Obi ya shigo da abinci daga gida…ya karaso ya ajiye kan table snn ya mishi sallama ya fita…shi kuma Bobby ya maida kanshi ya lafe jikin kujera tareda lumshe ido…kaman daga sama yaji voice din Nur akanshi…bai bude idon ba sai cewa yayi”waya baka izinin shigowa office dina?..”Nur ya dauki basket din abinci ya nufi dinning dashi kafin yace”har saina wani jira an bani izini?..ko dazu ma kawai nace bari in dana ne?..”bai sake cewa komai ba saida ya mike ya isa dinning din ya zauna snn yace”why are you doing this?..meyasa zaka tura mutumin nan wajen Mummy?..”a nuste Nur yace”because you are not willing to listen to me…kai kanka kasan da kayi abunda nakeso tun farko bazai kaimu ga hakaba…kuma mutumin nan yanada kirki Bobby kaddarane kawai ya fada mishi snn yanada iyali kuma duk ta karkashinka suke samun abinci yanxu kanaso kayi musu cutting hanyar samun abincinsu sbd small mistake daya aikata?..”a hankali Bobby ya sauke ajiyar zuciya before yace”amma daga small mistakes ake zuwa har manyan mistakes ka sani…kan wane dalili zaka turashi wurin Mummy”Nur yace”nayi maka alkawari inshaAllah bazai sake ba…to be honest banajin dadin yanda kake kasa hakuri da workers dinka…sbd suna aiki a karkashinka ba yana nufin su slaves dinka bane…suma mutane ne kamar kowa and suna bukatan a ringa yi musu uzuri akan wasu abubuwan…banajin dadin wasu maganganun da suke fada a kanka shiyasa nakeso ka gyara”…tunda ya fara mgn Bobby yayi shiru yana sauraronshi yasan gaskia yake fada mishi yana kuma jin dadin yanda abokin nashi ke zaune dashi tsakani da Allah shiyasa komai dacin gaskia yake fada mishi ita…ganin yayi shiru yana tunani Nur dake kokarin kai loma baki yace”so yau azumi kakeyi knn?..”baice mishi komai ba yayi serving abincin shima ya shigaci a hankali…suna cikin cin abincin yace mishi”kasan me na gani a clinic yau?..”a hankali Nur ya girgiza kai alaman aah…saida ya sake sakin wani tsaki cikeda takaici yace”a spoiled brat..wata yarinya ce mai shegen shagwa6an tsiya…can u imagine yarinyan dake high institution ta tsaya tana kukan injection?.. wlh if u see how she was crying zakayi tunanin surgery akai mata..she was crying out loud kaman mara hankali..gaba daya ta karasa spoiling mood dina for the rest of the day..i feel like strangling her”…saida ya gama Nur ya shiga murmushi gamida girgiza kanshi yace”i think it was Lamido”..da sauri Bobby ya kalleshi yace”how do you know that?..besides mace kaji nace maka ba namiji ba..”Nur ya saki wani murmushi yana sake kai loma bakinshi yace”ai bama ni ba kaf FCNM bana tunanin akwai wanda baisan who is Lamido ba…jikar Lamidon Gombe ce…and duk college din nan Ita kadai na san tanama allura wnn kukan…she is allergic to injections”…Bobby na tabe bakinshi yace”ba wani allergy tsabar iskanci ne kawai da kuma sangarta”..Nur na girgiza kai yace”bazaka gane bane Bob…tunda nake ban taba ganin mace kaman yarinyar nan ba…she is so different from other girls…komai nata special komai nata unique…kaga na farko she is beautiful kai she is more than beauty itself… Snn she is intelligent…wlh ban taba ganin yarinya mai brain dinta ba..she is a genius tunda ta shigo makarantan nan take overalling kaf department dinsu…gata very young snn gata da goog heart…gata kum…”bai kai ga karaswa ba Bobby ya katseshi da fadin”malam hold it plss…this one you are saying as if you are taking about your girlfriend”..da sauri Nur yace”she really is an angel Bob you will never understand”..still bai bari ya karasa ba yace”naji enough talking about her now and ka sake cemin Bob you’ll see the other side of me”…sake kai loma Nur yayi yana murmushi yace”wnn other side of you din ai koda yaushe cikin ganinshi nake..har devil side of you ma duk na gani so am not afraid”tsaki kawai Bobby ya saki baice mishi komai ba duk ya sake spoiling mood dinshi…suna gama cin abincin ya kira Mr.Obi yazo ya tafi da ragowar…sai a lokacin Bobby ya samu damar ce mishi ya kira Dr.Bukar yace mishi ya dawo bakin aikinshi..Nur yasaki kyakyawan smile kafin yace”i’ve already done that ai..tunda mgn yaje wurin Mummy nasan dole zai dawo ai”…harara Bobby ya maka mashi yace”wato u did it on purpose koh?..”Ugo ya daga shoulder dinshi tareda fadin”yes”.

Karfe 4 ya fara shirin barin College bayan ya dawo daga masjid…kafin ya fita office wayanshi ya fara ringing yana dubawa yaga Sister akan screen…baiyi wasting time ba ya dauka yana cewa”Aunty Sumy how far”…daga daya bangaren sis dinshi tace”Bobby kanajina?…wata qawata ce ta kirani wai yarinyanta ba lafia sun kaita hospital dinka shine tace i should please ask u kaje ka duba musu ita plss”…saida ya gama sauraran abunda ta fada snn yace”but Aunty Sumy akwai many doctors a hospital din fa?..kinsan ni yau ba ranan shiga hospital bane yanxu haka ina cikin college”…Aunty Sumy ta sake yin kasa da murya tace”haba dan qanina…kirana fa tayi sbd tasan na isa insaka kaje…yanxu kawai sai in kirata incemata kace bakaza samu daman zuwa ba…kana ganin ya dace hakan?..kanaso ka nuna mata ban isa da qanina ba knn?..”dan daure face yayi yana turo baki yace”Aunty Sumy are you emotionally blackmailing me now?..this is not fair”..da sauri Aunty Sumy tace”ba wani emotional blackmail am just telling you the fact..dan Allah ka taimaka kaje ka duba musu ita Please otherwise zasuyi tunanin ban isa da qanina ba”…yayi shiru kamar bazaice komai ba sai can yace”i will go”…Aunty Sumy ta washe hakora tana fadin”yauwa my Lil bro Allah ya maka albarka kaji…Allah baka mace ta gari”…yana tabe baki ya kashe wayarshi yana kunkuni…cikin ranshi yace”tunda kin gama dani ai dole kice haka”…bai sake wasting time ba ya fita daga office…kafin ya karaso Mr.Obi ya bude mishi mota dan haka yana zuwa ya shiga ciki shima driver ya shiga suka fita daga makarantan…kai tsaye yacema Mr.Obi”Hospital zaka kaini”.

FCNM Female Hostel,Apartment C Room 2a.

Zaune take tsakiyar gado ta zuba tagumi da duk hannayenta…gaba daya hankalinta naga Macbook dinta dake ajiye gabanta suna video call da yan gidansu…kana ganin yanda ta daure fuska take faman turo baki zaka fahimci fada akeyi mata…fara ce sosai kamar ka tabata jini ya fito kuma kallo daya zakayi mata ka gane Fulani blood ke running a cikin veins dinta dan she is full blood Fulani of Gombe state…face dinta daukeda siririn pointed nose da cute red lips masu masifar kyau sai kuma sexy idanunta da suke nan farare tas dasu kaman na larabawa…gashin kanta nada tsawo sosai tayi parking dinshi a tsakiya ta saki jelan nata yawo a gadon bayanta…red jessy ne a jikinta mai daukeda tambarin Manchester United a kirji sai black trouser dinta three quarter…daidai da bedsheets da pillow case dake shimfide kan bed dinta Red ne mai daukeda tambarin Manchester United ko ta ina…wnn alama ne na she is a die heart fan of MUFC…babu dankwali ko hula a kanta hakan kuma ya bayyanar da silky black hair dinta da yake nan a barbaje…ganin yanda ta bada hankalinta kacokam ga vidoe call datake yasa nima na karasa dan inga da wanda take magana…wata mace ce da kallo daya zakayi mata ka gane mahaifiyarta ce sbd tsananin kama da sukeyi da ita…hatta dimples dinsu da yake lostawa duk sukayi motsi da cheeks dinsu iri daya ne…dukda ba a zahiri nake ganinta ba dimples din are so visible da kana dora idanu a kanta zaka gansu…cikin fushi takeyi mata fada snn ta karkare da fadin”kuma wlh duk na sake jin ance kinyi irin wnn rashin hankalin sai ranki yayi mummunan baci tunda ke har yanxu bazakiyi hankali ba…kece babba amma kullum rashin hankalinki karuwa yake…na tabbata ko Yusra da take karama bazatayi wnn iskancin da kikeyi ba kawai sbd zaayi maki allura sai kiyita zubama mutane ihu kina musu kuka sai kace karamar yarinya?..dont worry daddynku yana dawowa dama zan fada masa ga abunda kikeyi a makaranta”…tunda Mom dinta ta fara fada batace wani abu ba sai yanxu…hankali a tashe murya tamkar zata fashe da kuka tace”Ammi dan girman Allah karki fadama daddy kinji wlh bazan karaba…Ammi kinsan yanda allura yakemin shiyasa nayi kuka wlh amma i promise bazan kara ba pls pls plssss”..ta karasa mgnr hawaye na wanke mata fuska…tasan muddin mgnr nan yaje kunnen daddy ta gama yawo…ta sanshi sarai mutum ne shi mai zafi shiyasa baya daukan nonsense kuma ta tabbata idan yaji mgnr nan yana iya zuwa har Kano yayi maganinta tunda tun tasowarta ake wnn rikicin da ita akan allura…tun tana yarinya dama duk zaayi mata allura saidai ya tsaya a gabanta rikeda bulala snn zata yadda…har zuwa yanxun kuma ta kasa sabawa dashi…tana rufe baki Ammi tace”to wlh na sakejin mgn makamancin haka sai kinci ubanki kuma itama Bilkisun zan fada mata duk kika fara period sai su barki da abunki tunda ke har yanxu bakisan annabi ya faku ba”…da sauri ta sake cewa”am sorry ban karawa”..Ammi bata sake cewa komai ba sai tsaki data saki tareda mikama sisters dinta dake zaune tun dazu suna jira suyi mgn da ita Macbook din hannunta kafin ta fita daga parlorn…da sauri ta goge hawayenta dan bataso su gani…immediate sister dinta mai suna Husna ta shiga duban screen din fuskanta da wani murmushi tace”hajia Adda mai kukan allura”..da sauri ta dago idanunta tana watsa mata harara tace”so na zama abokiyar wasanki ko Husna?..raini ya fara shiga tsakanina dake ba?”…Husna ta shiga girgiza kai tace”kai Adda dan Allah nidai bance haka ba…kawai dan nace mai kukan allurr”..bata karasa ba ta daka mata wani hadadden tsawa tace”Husna kina hauka?..ni kike fadama mgn haka koh?..”Husna tayi shiru tana duban yar uwar tata baki a tsuke tace”Allah ya baki hakuri..laifina ne ma dana dage sai nayi mgn dake..sai anjima”..daga haka ta mike da sauri ta ajiye Macbook din ta tafi dakinsu abunta…Yusra  ta matso da fara’arta sosai tace”Adda don’t mind her kinji?..she is not a good girl”..lokaci daya murmushi ya maye gurbin face dinta tace”of course she is not habibty..how are you?..”Yusra tace”ina lafia Adda..ya karatu”…saida ta dan bata rai snn tace”karatu ba dadi habibty kuma ina missing dinku sosai”..tace”muma muna missing dinki Adda amma Hammanmu  yace duk zai sake zuwa wurinki damu zaizo”…tace”to shikenan habibty i can’t wait to see you…yanxu ki bama Hamma Macbook muyi mgn dashi”..ba musu ta mike zuwa inda Hamman nasu ke zaune yana sararonsu ta mika mashi MacBook din…yana amsa yaja cheeks dinta tareda mikewa ya fada dakinsa…saida ya zauna akan bed snn ya daidaita screen din yana dubanta da kyau yace”so you are done”…tana wani tale baki tace”Hamma Ammi kaman zata cinyeni sbd fada…hadda cewa saita fadama daddy nidai dan Allah kace mata kada ta hadani dashi kaji”…murmushi ya saki yana cigaba da kallonta yace”ai ke dince Maama bakya jin mgn…na rasa gane wane irin tsoro kikema injection da duk akazo yi miki sai kin tarama kanki jama’a sai kace ba health personnel ba”…tana sake turo bakinta tace”Hamma dan ina health personnel dole sai naso allura ne?..”yace”ya kamata kiso ta mana tunda kina yiwa mutane”..ta rungume hannunta a kirji tana girgiza kai tace”nidai aah wlh..dan inayi bashi yake nufin dole nima sai anyi min ba…yanxun yaushe zakazo ka ganni kaga fa yau almost 6 weeks knn baka zo ka ganni ba”..yana murmushi yace”i will come inshaAllah nima ba karamin missing dinki nakeba…aiyuka ne kawai sukamin yawa suka hanani zuwa ganin qanwata”…nan da nan ta saki smile daya bayyanar da dimples dinta tace”to yaushe zakazo Hamma?..”yace”zanzo Maama amma ba yanxu ba…kinga wnn week din daddy zai dawo amma inshaAllah yana tafiya zamuzo har su Husna”..tace”to shikenan Hammana thank you”..shima yace”thank you cutie pie amma yanxu qafan ya warke koh?..”tana gyada mishi kai tace”ya warke wlh…kuma ko injection din ma bayamin ciwo kaman yanda yakeyi da…kilan proprietor dinmu bashida zafin hannu”…murmushi kawai Hamman nata yayi kafin yace”ohk ki samu ki kara hutawa yanxu and kice ina gaishe da Billy da kyau”..da sauri tace”zataji inshaAllh…besty fa?..”saida ya danyi jim snn yace”shima ina gaisheshi”…ta sake amsawa da zaiji snn sukayi sallama…ta ajiye Macbook dinta a gefe tana sauke ajiyar zuciya tace”Finally”…tana kokarin kwanciya Billy ta fito daga kitchen hannunta rikeda bowl data dama custard a ciki…tana karasowa ta janyo table ta dora mata akai snn tace”ga custard din nan idan zakisha”…Aysha ta dan daga ido ta kalleta sai taga fuskanta daure tace”haba mana Billy…haba my besty..fushin bai kare bane har yanxu?..”harara Billy watsa mata tace”kije ki nemi inda bestynki yake dai amma ba a nan ba…kawai dazu kikasa mutumin nan yayita watsa mana wadan nan shegun idanun nashi masu kama da na aljanu…saura kadan na saki fitsari wlh sbd tsabar tsoro”…Aysha na kokarin fashewa da daria tace”haba Billy fitsari kuma sai kace wanda taga mala’ika”…Billy tace”ba gara mala’ika ba Lamido shi yanada imani snn aikin Allah yakeyi…amma Proprietor fa kullum fuskanshi a haka yake sai kace namijin saniya”…wnn karon daria Aysha ta saki sosai sai kace ba itane me kukan allura ba dazu…saida tayi me isarta tace”wlh ni kaina bansan sanda na shiga hankalina ba…gaskia idanun mutumin nan basuyi ba a rayuwa…kawai kuna hada ido da mutum kiji kmr yayi miki asiri”…Billy ta sauke ajiyar zuciya tace”shiyasa ni ko hanya bana son hadawa dashi ballantana mu hada ido hantar cikina tazo tana kadawa”…kafin Aysha tayi mgn wayanta ya dauki ringing…ta dan tsayar da dariyanta snn tayi picking tareda fadin”my bsty”..a daya bangaren yace”besty ya jikin naki?..”tace”na samu sauki sosai besty”…yace”to Alhamdulillah wajen injection dinfa?..”saida ta kalli Billy taga yanda take ta wani tabe baki snn tace”shima da sauki sosai…Billy tace wai ita bazaka tambayi yanda take ba”…da sauri Billy tace”Allah ya kiyaye yaushe na fada miki haka?..me ma akai akayi wani Sa’eed da har zan damu dan bai tambayeni ba…ya dade baiki tambayata ba wnn matsalarku ce ba nawa ba”…Aysha najin Billy ta fara mgn tayi putting nata on speaker tace”besty kanajin mutumiyar taka koh”…yace”inaji rabu da ita besty duk wnn maganganun da take fada basu kai zuci ba…i know
she is boiling inside sbd mai girma Sa’eed bai tambayi ya Bilkisu take ba”…tun kafin ya rufe baki Billy ta sake fadin”nikam Allah yayi min tsari da ganin wnn rana…kudai kuje can kuyita abunku amma bada Bilkisu ba”..Aysha dai na zaune gefe tana sauraronsu tanata yi musu daria…ta kasa gane wnn ‘yar tsama dake tsakanin Billy da Sa’eed tun tale tale…tun farkon haduwarsu basa jituwa sam suna haduwa zasu fara tsokanar juna sai kace mage da bera…Friendship dinsu kuma ba karamin sake karfi yakeyi ba…dukda kasancewar kowa state dinshi daban karatu ne kawai ya hadasu a kano ba karamin shakuwa sukayi da junansu ba…shi Sa’eed dan kaduna ne sunanshi Sa’eed Mukhtar Makarfi…shekarunshi 25 yana karantar basic Nursing a FCNM dukda cewa saida ya kammala Bsc dinshi kawai sbd sha’awan Nursing profession yayi joining FCNM kuma sai Allah ya hadashi dasu…yanxu haka yana final year…Billy kuma asalinta jihar Bauchi…Bilkisu Ibrahim Muqaddas shine cikakken sunanta…she is a 2nd year student of Basic Midiwifery…class dinsu daya da Lamido likewise hostel dinsu..ita kuma Aysha Ahmad Lamido shine complete sunanta…suna kiranta Lamido kasancewar almost kowa a school abunda yake kiranta dashi knn…mahaifinta bafulatani ne Alhaji Ahmad Adnan Lamido shine present deputy controller general na Nigerian Custom Service snn shine ‘da na biyar cikin jerin ‘ya’yan Lamidon Gombe Alhaji Muhammad Adnan Lamido…mahaifiyarta kuma Maimunatu itama asalin bafulatanar Gombe ce…yara uku garesu Aysha itace babba sai Asma’u da suke kira Husna sai kuma Yusra data kasance ‘yar auta…shi Kuma Hamma Najeeb cousin brother dinsu ne da mahaifinsu ya rike tun kafin a haifi Aysha shiyasa suka saba dashi sosai dan idan ba fada akayi ba bazaka taba tunanin Cousin dinsu bane.

Wnn knn…

Bobby bai samu dawowa gida ba sai after magrib…haka kuwa ya shigo gidan rai a hade sbd tsabar gajia da yayi…driver na shigowa ya samu wuri yayi parking snn ya bude motan ya fito saidai tun kafin ya zagaya ya bude mishi kofa mai gadi yazo ya bude yanata faman mishi kirari sai kace wani sarki…Bobby bai iya ce mishi komai ba sai hannu daya daga mishi kafin ya nufi entrance…tun daga compound din gidan zaka gane mamallakinshi ba karamin mai kudi bane duba da girma da kuma tsagwaron kyau da kuma tsaruwar gidan…katoton Mansion ne daya amsa sunan Mansion saidai abu daya daya bani mamaki is yanda naga gidan shi kadai ne kaf girman layin nasu..ko makota basu dashi dan sai kayi tafiya mai nisa daga nan kafin ka fara hango gidajen mutane…cikin raina nace kilan mutanen gidan basu son zama cikin mutane…ga uban motoci zube cikin compound din bila adadin sai kace ba kudi ake sawa ake siya ba…hatta plate number dake jikin motocin nashi duk sunanshi ne a jiki tunda daga Dr.Bobby 1,2,3 har zuwa ba adadi dan ban samu damar irga adadin yawan motocin ba…ajiyar zuciya na sauke ina jinjina baiwar kudi da Allah yayi masa at such young age snn nabi bayanshi zuwa cikin gidan…bai samu kowa a central parlour ba sai tv dake aiki sai kuma sanyin ac da qamshin freshener da suka hadu suka bada wani sassanyan qamshi a dakin…shi kanshi palorn abun kallo ne…bai tsaya wasting time ba naga ya nufi wani corridor suit dinshi rataye a shoulder dinshi…another parlour naga ya shiga wnn karon dai da akwai mutane a ciki…ya karasa ya zauna kusada wadda kallo daya nayi mata na gane Mom dinshi ce…if you see yanda yayi da face dinshi zai baka daria sosai…ya lumshe eyes dinshi tareda dora kanshi shoulder dinta voice dinshi can kasa cikin igbo yace”Mummy am home”…Mummy na shafa kanshi fuskanta daukeda wide smile itama da igbo din tace”welcome back son..akwai gajiyan aiki koh”…ya danyi pouting lips dinshi before saying”gajia sosae Mummy…kawai Aunty Sumy tace lallai sai naje na duba yarinyan friend dinta a hospital”..Mummy na cigaba da shafa kanshi ta maida dubanta kan Aunty Sumy dake zaune gefe tana aiki cikin system dinta tace”gaskia Sumayya baki kyauta min ba..haka nan kin wahalar min da yaro”..aunty sumy daria tasa sosai kafin tace”Mummy dan yaga kina biye mishi nefa yake wnn abun…ko Sabeer da yake dan auta baya wnn shagwaban da yakeyi..you better grow up wlh wnn shagwa6an babu inda zai kaika”…ta karasa mgn referring to him.