EL-MUSTAPHA CHAPTER 12

EL-MUSTAPHA




CHAPTER 12




A gurguje😏

‘Washe gari su hajiya suka soma shirye shiryen tafiya, uwani harda kuka tana roqon su, su barta a gidan kakan ta ita ma taji dadi. +

Idan tana cewa kakan ta abin dariya yake bawa abba, ya qara yarda uwani bata da hankali,

Sanda suka fito, sarki ne kawai bai fito masu rakiya ba, amma su jiddah da uncle b duk sun fito, rumaisa da sauran yaran gidan ma, afiya ce ma bata fito ba.

Uwani tayi tsaye baxata shiga motar ba lallai sai an barta inda kakan ta, suna mata baqin ciki da ta xamo jinin sarauta shiyasa basa son ta xauna a gidan.

Rumaisa dai bata ce komai ba sai kallonta take sam yarinyar bata birge ta bata da nutsuwa kuma bata respecting iyayen ta a yanda ta lura,

Jiddah ma batayi magana ba sai su hajiya ne ke ta fada akan ta shiga motar.

Suna haka afiya ta fito harabar gidan, tayi kyau sosai cikin farar alkyabba, fuskar nan tata babu annuri amma hakan bai boye kyawun fuskar ta ba, da alama fushin na rumaisa ne daga yanda take xuba mata harara tun da ta doso gurin.

Kallo daya uwani ta mata ta rikice a tunaninta itace take harara, ba shiri uwani ta soma qoqarin shiga motar ta qofar glass a rude,

Miye haka? Afiya ta tambaya sanda ta doso gurin tana kallon su.

Jiddah tace uwani ce tun daxu ake ta fama akan ta shiga motar taqi wai sai dai a barta nan,

Uwani ta fashe da kuka, yaushe nace haka, kada kimin sharri, ta soma kuka sosai har ga Allah tsoron afiya take.

Afiya ta tabe baki tana kallonta, bude motar ki shiga tun daxu kin batawa mutane lokaci, kenan duk gurinnan ke kadai ake jira kuma acikin su an rasa wanda xai baki mari biyu masu kyau da tuni kin dade da shiga motar.

Uwani na jin haka ta balle murfin motar ta shiga, da qarfi ta rufe gam, ta maida glass da sauri ta rufe tana maida numfashi cikin tsoro.

Yaran dake gurin suka dauki dariya, su abba suka yi godiya suka shiga motar suka fice.

Afiya tace tun daxu nake jiranki, mrng flight xamu bi kinsa ni amma dubi ko wanka baki yi ba, ta fada tana kallon rumaisa.

Rumaisa ta soma tafiya tana fadin sarkin rawar jiki ina sane kuma akwai time ai.

Afiya tace ki bata mana lokaci Allah tafiya xamuyi mu barki,

Sai me, ni bansan hanya bane, tayi shigewarta.

Jiddah tace wai yau xaku tafi gabaki d’aya.

Afiya tace eh mana mun bar yara acan, kinga ba wanda yaxo da yaro ko d’aya, dama two days muka xo muyi yau xamu koma.

Jiddah tace Allah ya kaiku lafiya, ni kam naso ki bani labarin ki da nabila bayan tafiyar ki, uncle merah bai bani wannan labarin ba.

Afiya ta dube ta tana fadin, not now jiddah kuma baa nan ba, amma nabila
. sai kuma tayi shiru ganin fitowar Merah da fadawa a bayansa.

*

Barci uwani keyi sosai a cikin motar, sanda suka iso gida aka tayar da ita, budar bakin ta sai cewa tayi.

Hajiya kinsan me, wallahi wannan sarkin ya hana min sukuni a barci sai bibiya ta yake, duk na rufe idanuna shi nake gani, ina gani fa ya kamu da soyayyata ne shiyasa naga yana ta kallo na jiya fa da kuna magana.

STORY CONTINUES BELOW


Hajiya tace iskancin naki har ya kai acan, tsohon mutum ma baki bari ba, me xaiyi da ke.

Aa hajiya kinsan fa ance idan kana mafarkin mutum tabbas son ka yakeyi, karki yi mamaki a yanxu yana can yana baqin cikin tafiya ta, ni nasan yana sona hajiya, kada kumin baqin ciki da gidan sarauta, ina ji a jikina ya’yana xasu xo cikin jinin sarauta suna alfahari dani, nima na xama kakar jiddah saboda ina sons
. Dukan da taji a bayanta ya saka ta yin shiru,

Wayyo abba kayi haquri,

Yace shiga mota, ba musu ta shiga da sauri tana fadin qila can xai maidata inda sarki.

Yace hajiya shiga cikin gida, xamu dawo bada jimawa ba.

‘Abba yaja motar, inda wani babban malami ya nufa da ita inda yayi masa bayanin uwani sosai.

Malamin yace shedanun aljannu mu suna haka, sukan juya kwakwalwar yaro yayi ta yin abinda bai dace ba, yanxu xamuyi mata ruqiya insha Allah duk abinda ke kanta xai bayyana insha Allah.

‘Abba yayi addua sosai, yana fatan ta sami lafiya ya fita waje ya bar uwani xaune cikin tashin hankali.

Malamin ya kira almajiran sa suka soma yiwa uwani ruqiya.

Ana ta karatu, idanunta wiqi wiqi sai kallon su take tana tunxure baki.

Malamin ya tashi da xungureriyar bulala a hannunsa yana fadin, aljannun dake kan wannan yarinyar da alama kangararru ne, 1

Uwani ta bude idanu tana kallon malamin da bulala kafin tayi wani yunquri ya aika mata ita iya qarfinsa,

Ta saki wata qara cikin gigicewa, ta fadi gurin ta tashi tana tsalle, wayyo abba.

‘Abba tun da yaji ihunta hankalinsa ya tashi ya qara yarda lallai jinnu ne acikinta tun da suke da wani bata taba qara irin wannan ba, ya cigaba da karatun qur’ani a wayarsa yana nema mata sauqi.

Ku nawa ne acikin ta, su waye ku? Malamin ya tambaya cikin xare ido yana kallonta.

Uwani bata gane abinda yake magana akai ba, ga bayanta sai radadin ciwo yake,

Ganin taqi magana malamin ya qara kai mata wata bulalar, a gigice ta nemi hanyar ficewa, almajirai suka yi cikinta suka riqo ta,

Wayyo abba, wayyo hajiya xasu kashe ni, wallahi baxan qara ba, ko magana xan daina yi, dan Allah kayi haquri. 3

Malamin yace ku musulmai ne,

Da sauri uwani ta gyada kai, sau biyar nake sallah kullum, kuma ina xuwa islamiya ka tambayi abbana. 1

Malamin ya gyara hannun rigarsa yana fadin har yanxu jinnun basu tako ba, suna so su nuna min taurin kai, ni kuma xan wahalar da ku, kuna so ku batawa yarinya rayuwa.

Yasa wani almajirinsa ya riqa hannayen uwani ta baya aka banqare ta, aka daure qafafunta da igiya, ya riqe tsakiyar kanta ya daga murya sosai yana karanto mata qur’ani,

Ya jima yana yi sosai ya qara kallonta, su waye ku?

Uwani tayi wiqi wiqi da ido, hawaye da majina duk sun hade a fuska saboda tsananin axaba,

Tace wallahi nice uwani, sunana Aisha, ni jikanyar sarki ce, bani da aljannu, dan Allah kuyi haquri. 1

Daga inda abba yake xaune yana jin muryarta, tausayin yar sa ya mamaye xuciyarsa, Allah ya bawa uwani lfy, ya tashi a hankali ya nufi inda suke.

Ganin yanda aka banqare uwani hankalinsa ya tashi sosai ya shigo dakin da sauri,

Malam menene haka, meyasa kake dukan ta da wanna bulalar.

Uwani na ganin sa ta taso a wahalce ta rungumesa sosai.

‘Abba karkaje ka barni kashe ni xasuyi, ni bani da aljannu, abba baxan qara ba na tuba, ka gayamasu baxan sake ba.

Ya dubi bayanta duk shatin bulala ne gurin yayi ja sosai abinka da farar fata,

Yace na kawo tane ka duba min ita idan akwai amma bance ka dake ta haka ba, mutum ce ba dabba ba, baa taba mata duka irin wannan ba. 1

Yace amma alhaji m
. Abba ya katse sa,

Shikenan ai ka riga ka aiwatar, yaja hannun uwani suka fita sai kuka take jikinta na rawa, da kansa ya bude mata motar ta shiga kafin ya shiga ya tayar.

Cikin kuka tace abba ina da hankali baxan qara ba, kada ka qara kaini wani gun a dake ni, ni bansan ina yin komai ba.

Abba ya tausaya mata yace ba inda xan qara kaiki uwani, xan haqura dake haka na cigaba da xama dake, inaji haka Allah ya tsaro maki taki rayuwar amma duk da haka uwani ki rage wasu abubuwa a kullum ina gayamaki hakan kuma xan cigaba da maki addua kinji.

Ta gyada kai da sauri tana fadin abba kada ka qara kaini a dakeni, baxan qara ba, na daina yin magana.

Yace idan kika qara ma nan xan dawo dake malamin nan ya qara dukan ki, kinga Malam guzuma ya huta da dukan ki.

Ta fashe da kuka har tana riqo hannunsa dake kan sitiyari, abba wallahi baxan qara ba kayi haquri.

Kafin su iso gida har tayi barcin wahala sai ajiyar xuciya take.

*

Cikin kwana biyu aka xagaya da jiddah taga dangi haka dangi sun ganta,

Daga baya suka dawo gida tare da kuyangu da sarki ya bata guda uku,

d’aya sunanta Xuwaira, sai Nafee Anka sai ta qarshen Lailah, masu hankali da nutsuwa.
1

Jiddah ta qara samun matsayi a xuciyar el’mustapha sai nan nan yake da ita cikin nuna mata wutar soyayyarta dake adabar xuciyarsa.

Jiddana mai iyaye da yawa, jiddana jinin sarauta ya fada lokacin da yake qoqarin xama a kusa da ita.

Iyayen nan xan raba su biyu na bawa el’mustapha rabi, iyayena ai iyayen ka ne.

Kefa yar gata ce jiddah, ni yanxu nafiki xama abin tausayi.

Ba uwa ba uba, ni maraya ne jiddah ki kula da ni da yarana shine farin cikin rayuwa ta.

Ta rungume sa tana fadin komai runtsi komai wuya, komai dadi a duniyar nan baxan manta da musty na da ya’yana ba, sune jibin rayuwata, farin cikina, ina matuqar son su baxan iya rayuwa batare da su ba, el’mustapha ya kwantar da hankalinsa, jiddah tashi ce kuma har yanxu da baxar sa take taka rawa.

Ya kwantar da ita a hankali hade da hada bakinsu guri d’aya.

*

Yusuf kayan menene haka, akwati nake gani kusan shidda kamar kayan aure. 2

Yace eh surry xo ki xauna muyi magana ta fahimta, akwai naki kaya akwati kusan uku hannun anty ikram na fadar kishiya.

Fadar kishiya ta fada cikin firgici tana kallonsa yayin da xuciyarta ta tsananta bugawa tamkar xata fado daga qirjinta.Aure xaka yi yusuf? Wacece xaka aura, ina so na santa dan Allah ka gayamin. +

Ya riqo hannunta yana qoqarin xaunar da ita, ta fisge da qarfi tana kallonsa,

Tambayar ka nake, just answer me, bana son dadin bakin ka wacece xaka aura, who is she yusuf, ta fada hade da riqo gaban rigarsa tana kallonsa idanunta taf da hawaye.

Am sorry surry, uwani ce, amma wallahi u
. Shut up ta katse sa cikin tsawa, idanunta sun juye sunyi jawur.

Uwani kuma yusuf, ashe baka barta ba, menayi ma, what did I do to deserve this? Menene bana yi ma, dame na gaxaka da shi a gidannan na kyautatawar aure, me uwani ta fini dashi,

Wallahi babu komai surayya babu abinda uwani ta fiki da shi sai hauka, haka kawai nake son na aure ta badan kin gaza ni da komai.

Idan aure xaka qara meyasa dole sai uwani, mata nawa ne a gari, kasan bata da hankali kake neman hadani xama da ita, You are not serious, nagane me kake nufi a yanxu, xaka auri uwani ku xauna ku wulaqantani saboda tun farko ba nice kake so ba, na amince na aure ka saboda tausayin abinda uwani tayi maka a baya, na xauna da kai da xuciya d’aya, na koyawa kaina soyayyar ka amma yanxu kake son nuna min halin ku na maxa, tabbas na yarda namiji ba dan goyo bane, kaje gaka ga uwani, ta juya a fusacce. 3

Hankalinsa ya tashi yabi bayanta yana bata haquri sam abinda take tunani bashi bane a xuciyar sa, idan har surry xata barshi tabbas xai haqura da auren uwani sadakin da ya bada ma xai yafe.

Kayanta ta soma hadawa tana kuka, duk rarrashi da ban baki da yake bata bai sa ta saurare sa ba, ko ta kan yar’ta Mimi bata bi ta soma qoqarin fita daga dakin, ya riqota da qarfi suka soma kokawa a dakin, qarfi ba daya ba dole ta saduda ta fashe da kuka.

Tsura mata idanu yayi yana kallonta, idan yace baya son surry yayi qarya, macece da kowane namiji xaiyi alfahari samun irin ta, tun daga kan nutsuwarta haqurin ta da biyayyarta, kuma ya sani duk duniya ba macen da xai so kamarta har uwani kuwa domin son da yake mata baima uwani shi ba kuma yasani ko a mafarki uwani baxata masa biyayyar da surayya ke masa ba. 1

Idan bai manta ba shi uwani xatayiwa laifi amma shi xaije yana bata haquri, idan kuma shi yayi laifin duk shi xaije yana bata haquri, bai taba sanin dadin rarrashin mace ba sai akan surry da ta soma yi masa, baya manta har ganin uwani yake a mafarki ta tsare sa da fada yana bata haquri, to me akayi? 2

Ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu tabbas idan auren uwani matsala ne a rayuwarsa da matarsa ya haqura dashi.

Yayi juyin duniya da surry ta kula shi taqi, yana fita massalaci ta dauki yar’ta da kayanta ta fice daga gidan.

Sanda ya dawo ya sami batanan kuma babu kayanta da ta diba daxu hankalinsa ya tashi sosai, kai tsaye gidan jiddah ya nufa, kallo daya tayi masa ta gane baya cikin nutsuwa.

Meke damun yusuf?ta tambaya lokacin da take qoqarin sakawa airah pampers.

Surayya ta guje ni anty jiddah, bansan ya xanyi ba, she left my house.

Saboda me?

Saboda aure na da uwani, ya xanyi?

Tace ka haqura da auren uwani, dole ne?

Yace aa, amma ita ma ina son ta, kuma kinga iyaye sun shigo maganar me xance dasu.

Kace masu ka fasa, ina maka sha’awar xama da surayya fiye da xama da uwani, banga laifin surry dan ta guji uwani ba saboda tasan abin da tamin, babu mai son kishi da uwani kai tsaye xata ga bayansa.

STORY CONTINUES BELOW


Yace hakane nasani wallahi, uwani tausayi take bani anty jiddah, bayan wannan ma bafa a gida daya xasu xauna ba, kowacce da gidan ta kuma na baiwa surayya xabi akan duk gidan da take so acan xata xauna, auren nan fa ba haramun bane ya halatta, hudu akace muyi ko. 2

Tace hakane amma baa ce kuyi hudun haka kawai ba, sai aka qara da cewa idan xaku iya adalci tsakanin su.

Insha Allah, Allah baxai kamani da laifin rashin adalci a tsakanin su ba, ki taimakeni anty jiddah nasan ke kadai ce mai sauqin kai da xata duba min anty ikram bata son auren nan ko kadan kinsani, ki shige min gaba muje mu rarrashi surry wlhy ina son ta.

Jiddah ta kira el’mustapha ta sanar da shi xata fita da dalilin fitar, yayi mata ixini kafin su tafi ita da yusuf.

Surayya sai kuka take a gaban mahaifiyarta tana gayamata komai da kuma halin uwani.

Addua xakiyi, abinda yafi xama alkhairi Allah ya tabbatar amma kada ki daga hankalinki dana mijinki ki sakawa xuciyarki damuwa surayya, maganar yusuf ya sake ki bana son ji kuma kada ki kuskura ki furta masa wannan kalmar.

Kiyi haquri dama aure ya gadi hakan, xama na tare dole sai ana haquri duk yanda kake da mijinka baxaka taba cewa baxai maka kishiya ba, wata Ma sai ta tsufa a gidanta da yaranta mijin xai auro mata yarinya sharkaf warin yar cikinta, illah kawai kayi addua Allah ya hada ka da ta gari.

Wallahi mama uwani ba ta gari bace, kinsan halin ta fa kinsan lokacin da take xuwa gidannan har ke da kanki kike min magana akan ta bata da nutsuwa da kamun kai, kuma kinji abinda tayi wa yar uwarta.

Duk nasani surayya, shiyasa nace kiyi addua mafi alkhairi nima xan tayaki, kuma abinda tayi wa yar uwarta a baya ba lallai bane ke ta maki shi karkiyi mamakin ta sauya daga yanda kika santa sai kuxo kuna xama na amana da ita.

‘Surry ta share hawaye tana yatsine fuska, kowa yaqi ya duba mata duk wanda ta tunkara da maganar sai haquri yake bata, xata xubawa sarautar Allah ido ta kuma gwada yin haqurin tagani idan haqurin xai kaita ga riba.

Har su jiddah suka xo duk maganar da suke da mahaifiyarta tana ji komai bata ce ba har suka gama, da kyar tabi yusuf suka koma gida sai kuka take kamar ranta har wani haushinsa take ji.

Ya bata xabi akan gidan da take, sabo wanda ya gina ko kuwa wanda take ciki, kai tsaye tace sabo saboda tana ganin ai dan ita ya gina tun farko ba dan wata ba,

Yusuf sai godiya yake mata, burinsa yaga ta kwantar da hankalinta baya son damuwar ta ko kadan,

Ya canxa mata sabbin furniture ya saka a sabon gidan da xata tare, ko godiya ta kasa masa cos tana ganin yana yin komai ne duk don saboda xai qara aure har wani rawar kai yake a yanda take gani kenan.

Kayan fadar kishiya da ya qara tunkarar ta dasu cikin tsananin fushi tace bata so idan ya tilasta mata da karba xata qona su duka bata damu da abinda ya kashe ba.

Haka ya dauki kayan ya fita dasu jiki a sanyaye, ya nufi dakin sa dasu yasan watarana xata sauko har ta nemi kayan.

Suka tattara suka koma sabon gidansu, kana ya soma gyaran tsohon gidan.

Koda yaje mata da albishir ya biya masu hajji xasu je su biyu bata wani nuna murna ba saboda haushin sa da take ji, kuma shi kansa bai damu ba cikin murna ma yake sanar da ita anty ikram ta gayamasa ai harda jiddah da el’mustapha duk xasu je, da wannan mai aikin jiddah da tayi aure banan duk xasu je, el’mustapha ya biyawa banan din.

Allah ya saka da alkhairi shine kawai abinda ta fada.

Baqin ciki xai ma uwani yawa, kowa xaije makka a barta, a shiga shirgi ba da ita bađŸ€Ș. 2

STORY CONTINUES BELOW


Bayan sati biyu akaje kai lefen uwani, ba laifi yusuf yayi qoqari sosai.

Tunda uwani taji labarin xaa kawo mata lefe taje tana fitar da tsofin kayanta tana rabawa yan unguwa, takalma da jaka duk bata bari ba, sai labari take badawa a unguwa sabbin kaya xaa kawo mata, ai auren ta na farko baqin ciki ake mata dashi shiyasa mijin ko atampha bai dinka mata ba, yanxu kuma Allah ya bata wanda baya mata baqin ciki mai son ta. 1

Duk abinnan da ake abba da hajiya basu da labari, akwatunan ta ma ko daya bata bari duk ta rabawa qawaye da masu aure wadanda basu da arxiki sai godia ake mata ana saka mata albarka tana washe haqora.

Wani abin mamaki uwani na bakin gate xaune tana jiran yan kawo lefe, ga yan uwa can acikin gida sun cika sai hidimar kayan tarbon lefen suke.

Tana ganin motoci sun tunkaro gidan ta tashi xumbur ta hangame masu gate tun kafin su kawo, 3

Qanwar abba ce ta fito ta ganta tsaye riqe da qofar gate ta jawo ta da qarfi tana mata fada,

Tace aa to miye abin fada anan gwaggo, na bude masu ne kada suyi batan kai suje sukai wani gida, idan ba baqin ciki ake min ba ai ba wanda ya fito waje ya tayani xama na jira xuwan su.

Gwaggo ta bige mata baki iya qarfinta, bata wasa sam da uwani, ta riqo hannunta duka biyu ta riqe tana neman abin dukan ta, uwani na ganin haka ido ya raina fata ta soma bata haquri tana roqonta, baxata qara ba ta yafe mata.

Gwaggo taja ta, ta saka ta a daki ta rufe ta, ta barta anan ciki tana fadin inga kin fito a dakin batare da an nemi ki ba.

Sanda suka shigo anyi masu tarba mai kyau kuma duk cikin su ba idon sani dangin yusuf ne kawai.

Har xasu tafi daya daga cikin su cikin wasa tace, bamu ga amaryar tamu ba da yake ba wanda ya santa a cikin mu, ko boyon ta kuke yi ne.

Gwaggo tace baxaku ganta a yanxu ba har sai ankai maku ita, xaku gaji da ganin ta k
. Gwaggo bata rufe baki ba, uwani dake cikin daki a rufe tana jin abinda ake fada ta kunno kai ta window tana fadin gani nice amarya Uwanitilyusuf jikanyar sarki merah.

Duk falon aka juya ana kallonta, ta kuwa xuba masu ido dan bata san su ba, nan fa suke mata kallon mamaki, anya wannan tana da kunya kuwa duk da take kyakkyawa sam bata birgesu ba.

Bayan tafiyar su gwaggo tayi mata duka sosai kuma ba wanda ya hanata saboda ransu yayi matuqar baci da abinda tayi.

Dukan bai bata mata rai ba ta dauki hakan a matsayin baqin ciki ake mata da kada dangin miji sun san ta, bayan ta gama kuka ta share hawayen ta matso ana kallon kayan da ita.

Wani dadi da farin ciki take ji idan ta tuna duk kayan nata ne, lallai ta yarda auren ta da el’mustapha ba alkhairi bane sai talauci da baqin ciki, ta xame jiki tayi dakin ta, tana jin wata nutsuwa na shigo mata, to ko dai yusuf yafi el’mustapha kudi ne, amma ta tuna sanda xai auri jiddah kayan da ya kawo mata ma sunfi wadannan, kenan baya son ta.

Ta dauki marker tabi dakin nata duka da xanen *Uwanitilyusuf* cikin heart, daga qarshe tayi wani rubutu da manyan haruffa wanda ke nuna har cikin xuciyarta she mean it iya gaskiyarta, *I LUV U EL’MUSTAPHA, STILL CAN’T FORGET YOU IN MY HEART*, ta xauna gurin tana kuka sosai,
1

Bayan kwana biyu uwani ta soma saka kayanta na lefe tana fita, koda hajiya ta lura tayi mata magana anan take sanar da ita ai tuni ta kyautar da kayanta bata da na sakawa a yanxu sai sabbin.

Sosai abba ransa ya baci koda ya duba har akwai kayan da basu dade da dinkawa ba kuma masu tsada duk ta kyautar,

Tunda uwani taji abba na maganar xai maidata inda malami, hankalinta ya tashi taje da gudu ta cire kayan ta nufi dakin hajiya tana da wasu kaya acan ta saka ta fito tana kuka.

‘Abba kayi haquri sharrin shaidan ne da sharrin xuciya, baxan qara ba, dan Allah ka yafe min abba kada ka kaini gurin sa kashe ni xaiyi.

Ganin abba da gaske yake ta soma kururuwa tana kuka iya qarfinta, yana riqo hannunta ya saka ta mota ta xube gurin a sume, bata manta waccan wahalar ba.

Ga bacin rai ga dariya sune suka saka abba a gaba, hajiya ta xuba mata ruwa a jiki.

Bayan wasu awanni suna xaune a dining suna cin abinci uwani ta dube sa tana fadin.

‘Abba ina fa sane da cewa baka bani sadaki na ba, nasan ana baiwa mace sadakinta, ko anti jiddah ta bani nawa da el’mustapha ya bada.

Suka yi shiru suna kallonta, ta cigaba da fadin ai maigadi ne ya fada min daxu, ina so nayi jari da kudin na tallafi kaina da ya’yana masu xuwa.

Hajiya tace wane kudin xakiyi jari dashi, duka sadakin naki nawa ne?

Ina da wayo hajiya, baxaa min wayo a cinye min kudi ba, ko anti jiddah ma ta bani kuma na tuna sanda aka bata sadakin ta a hannunta kuka bata abunta.

Amma ai da aka bata maidawa tayi, hankalin ku ba daya ba.

Hajiya a bani nima nayi hankali ai, itama dan tana da kudi ne ta baku ni kuma kowa yasan talakace bani da kudi, abani a buna kada nayi wani laifi ace xaa hadani da Malam.

‘Abba ya tashi ya fita bai jima da shiga dakin sa ba ya fito dauke da kudi a hannunsa, ya bawa hajiya yana fadin kirga min kiji nawa ne.

Hajiya ta qirga kudin tana fadin dubu hamsin ne, ya karba ya miqawa uwani yana fadin ga sadakin ki.

Ta karba tana murna harda godia, ta tashi ta dauki kudin dake hannunta duka ta hada ta fita tana fadin ni yanxu bana qaunar mota a rayuwata, ina da wadda el’mustapha ya bani xanje na dauko ta.

Ta jima sosai da fita sai gata ta dawo da wani mutum ya goyo ta akan babur.

Da gudu ta shiga cikin gida ta kira iyayen nata suxo suga ta siye sabon mashin vespa wanda ake yayi đŸ›”,

Ai abba ni xan riqa hawa abina duk inda xanje akan sa xanje, yanxu haka ana kan koya min tuqin sa, har masallaci idan xakaje ni xan riqa kaika ka huta da xuwa da qafafu tunda baka xuwa da mota. 2

Gobe da asuba ka tadani barci xan kaika masallaci, hajiya idan xakije maqota ki gayamin duk xan kaiki bana so kiyi ciwon qafafu ki tsufa da wuri, ai na gayamaku ni bana maku baqin ciki da na samu kamar kun samu ne, tayi cikin gida da gudu. 2

Halin da mahaifan nata suke ciki Allah kadai yasani, washe gari abba baiyi qasa a gwiwa ba ya sake daukarta ya nufi gurin wani malami da ita tsoronsa kada tayi aure tana wannan abin auren nata yaxo ya mutu ba kowane mutum xai iya xama da ita a hakan ba.

Malamin magani ya bata, dana turare dana sha suka dawo gida.

Cikin ikon Allah aka soma mata amfani da su

.A gurguje
.

Bikin uwani da yusuf sai matsowa yake yayin da iyayen ke iya bakin qoqarin su na ganin ta nutsu, kuma alhamdulillah abin yana ragewa kadan kadan. +

Surayya tun tana damuwa tana kuka har ta daina ta xubawa sarautar Allah ido, tana so taga yanda xamanta xai kasance da uwani duk da ba gida daya bane.

Hajiya sai faman gyaran amarya take, uwani na faman washe baki, ashe hajiya na sonta take boye mata, lallai jiddah tayi mata baqin ciki domin bata mata wannan gyaran ba shiyasa akace kishiya abin tsoro da gudu ce, wai uwani ke cewa kishiya abin gudu ceđŸ€”

Duk ranar da hajiya ta manta ba ta bata ta sha ba ita da kanta take tuna mata, hajiya bata mamakin rashin kunya irin na uwani tunda tasan ko wacece ita.

Ba suyi wani dogon biki ba kasancewar kowa yasan uwani baxawara ceđŸ€Ș, duk bikin da ake jiddah ta halarta kuma sosai ta bada gudumuwar ta, banan ma taje da jiddah ta gayamata,

Ta bawa uwani gudumuwar hadaddiyar cooler mai kyau da tsada, amma uwani ta rena.

An gaya maki abbana bai siyamin inda xan sakawa mijina abinci ne, qila ma kin xubo kayan mallakar miji aciki na xuba abinci na basa ki mallake min shi.

Banan tace subhanallah anty uwani, kin manta ina da aure bayan wannan ma ni ban taba bin boka ko malami ba a rayuwata, ashe har yanxu baki canxa hali ba.

Uwani ta tashi tana fadin, me kike nufi kina nufin ina da wani mugun hali ne, waye ma ya gayyace kixo min biki, banda baqin ciki ki rasa abin bani sai wannan cooler ni kayan mata nake so na gyara kaina kar na xamo bora a gaban miji. 1

Banan girgixa kanta kawai tayi sauqin ta ba kowa a dakin sai su biyu kawai da ta kunyata a yau, banda anty jiddah me ma xai saka taxo bikin uwani, jiddah ta shigo da sallama tana fadin hayaniya nake ji me ya faru?

Uwani tayi caraf tana fadin, anty jiddah wai banan fa mai aikin mu ta waye har tayi arxikin da xata kawo min gudumuwa dubi fa.

Jiddah tace laifine dan ta kawo maki? Ita da ta tashi yin nata nawa kika bata, ba dan ni ba kina tunanin ma xaki qara ganin banan, meyasa kike haka, meyasa har yanxu kin kasa nutsuwa kisan me kike?

Kina goyon bayanta kenan, ni xan dauka haka ba dan halin ta ba albarkacin kine, ni duk mai min baqin ciki na gano sa Allah bana iya xama dashi.

Jiddah tayi caraf ta kwace cooler tana fadin baki isa ba, ta miqawa banan, koma da ita gida baxaki bata ba, idan kinyi niyar kyautarwa ne kibawa hajiya.

Banan ta karba tana fadin shikenan anty jiddah, uwani ta bita da kallo cikin mamaki da haushi dan tama rasa wane irin baqin ciki ne jiddah take mata haka, amma xasu hadu


An daura auren yusuf da uwani, kuma a ranar xaa wuce da amarya.

Tun da aka xo daukar amarya ake ta daru taqi ta shiga mota ita lallai sai akan sabon vespa din ta xaa kaita gidan mijin ta. 4

Wai wace irin mata ce yusuf ya aura haka?cewar daya daga cikin mutanen da suka xo daukar amarya. 2

Dayar tace magana ne kawai banyi ba, amma tun ranar da muka xo kawo lefen ta na gane bata da kunya da nutsuwa, banda iskanci ina aka taba daukar amarya daga kaduna har abuja akan vespa?

Tsohuwar tace lallai da sake, wallahi da nasan tun farko matar da yusuf yake nema kenan da baxai aure ta ba, yanxu ma bata baci ba xai iya sakin ta.

STORY CONTINUES BELOW


Aa Inna dan Allah kiyi haquri, inaji yarinyar dama tun farko bata da nutsuwa anty ikram ta gayamana komai akanta shiyasa kika ga bata goyon bayan auren komai ma bata saka hannunta a ciki ba.

Inna tace amma meyasa tun farko baku sanar dani hakan ba, da ba abinda xai saka a daura wannan auren, ita ikram din ai bata taba gayamin ba.

Inna ai anty ikram xatayi maganin ta, tana tsoronta sosai, ki xuba idanu kawai kiyi kallo kada ki sakawa xuciyarki bacin rai. 1

Inna ta shige mota tana taunar goro cikin jin haushin uwani.

Lamarin uwani kuwa sai da aka kira abba kafin ta shiga mota amma sai da aka saka mata vespa a bayan motar tukunna, cewar baxataje ta barshi ba.

Jiddah bata tsaya daukar amarya ba tana can tare da masu gyaran gidan na uwani suna jiran isowar su.

Kuyanga Qaumi ce ta shigo dauke da airah tana kuka sosai, 3

‘Anty jiddah, airah ta tashi daga barci sai kuka take taqi ta karbi abincinta.

Jiddah ta karbe ta tana fadin, kada kije nesa yanxu xan kira ki karbeta da tasha, saboda sun kusa isowa, ina sauran abokan xaman naki,

Ranki ya dade muna tare da su a waje,

‘Yauwa, kije xan neme ki, ta fita,

Banan tace wai anty jiddah ni bansan wadannan kuyangun ba hala an canxa maki su ne.

Eh tuni sarki ya canxa min wadancan basa son aiki, shine ya bani Maryam, Hajja, Saina da Mom sadeeq.

Banan tace cab kice duk yan kayan baqin ciki ne aka hada ki dasu.

Jiddah murmushi kawai tayi.

Bayan wani lokaci sai ga motocin amarya sun iso, ana fitowa da uwani a mota ta cire mayafi tana kallon gidan da aka kawo ta, ba wanda ya lura da halin da take ciki sai da suka ji tana fadin,

Shiyasa nake son yusuf kwata kwata a rayuwarsa bashi da baqin ciki, duk wannan gidan nawa ne.

Wasu suka dauki salallami, wasu kuwa suka tabe baki tunawa da suka je da ita yanxu ta gaida iyayen yusuf sai da tayi makamancin irin wannan.

Sai aka rasa waye amarya aciki tun da suka shigo, jiddah tamkar ta nutse gurin saboda kunya, ta jawo uwani ta gyarta hade da kai mata rankwashi mai xafi a tsakiyar kai tana fadin uban waye ya gaya maki amarya na fito da fuskarta.

To baxan kalli gidan bane, gidana ko naki, banda baqin ciki miye n
. Jiddah ta qara bige mata baki.

‘Na qara jin muryarki anan wlhy abba xan kira na gayamasa kinsan yanda kukayi kafin axo dake,

Akaje da amarya bakin gado aka xaunar da ita, wasu suka fita suna fadin bari muje muga gidannan kamar ba wanda muka sani ba an gyara sosai gashi an qayata gidan da kaya masu tsada, iyayen ta sunyi matuqar qoqari gsky.

Uwani najin haka ta miqe kar abarta baya gwanda taje ganin gidan ta tsare abinta kada wata tayi mata sata ta wuce da kayan kitchen din ta taji yanxu haka ake yi.

Jiddah ta maida ta da qarfin gaske ta xauna,

Wai baki da hankali uwani, ina xakije, kawaicin ma baxakiyi ba har su tafi.

‘Anty jiddah xanje na tsare kitchen dina ne kada amin sata, abba ya siya min kaya masu tsada, baki ga gas dina yafi wanda kika siyawa banan ba idan aka dauke fa.

Cikin takaici jiddah tace to sai me dan an dauke, wallahi kika bata min rai dukan ki xanyi a gidannan.

Uwani tayi shiru tana tunxuro baki, sai ga hawaye suna bin kuncinta, jiddah tayi mata banxa, yau gata ita ke tsaron uwani ita bata taba ganin ana tsaron amarya ba, ta dubi uwani tana fadin,

Wai ke baki da qawaye ne, duk ina suke ko daya ban gani ba.

Cikin takaici tace bani dasu menene.

Jiddah tace au hakane fa, sam na manta da uwani nake magana wadda ke rayuwarta ita kadai.

Uwani ta tabe baki tana fadin ban gayyaci kowa ba duk yan baqin ciki ne, ashe na manta har ta kusa dani ma tana min baqin ciki saboda an kawo ni gidan mijina, kada ayi min snatching ace xaa auri mijina dan na auri mijin wata.

Jiddah ta tabe baki tana fadin, ai rijiya ba gurin wasan yaro bane, mijin wata da kika ga kin aura ai yafi qarfin ki shiyasa har kika kasa xaman aure dashi, wanda kika aura a yanxu ma ai sai da aka bisa da roqo da rarrashi akan has rufa asiri banda haka ai da kin tsinci hoton ki a gidan masallaci ana cigiyar mai so a kyauta.

Takaici ya hana uwani magana ta tashi ta leqa ta window dakin tana kallon harabar gidan kafin tace,

‘Yauwa har yanxu vespa dina yana nan kafin yan baqin ciki suyi gaba dashi, na lura yana tsonewa mutane ido sosai


Gidan yayi tsit yan kawo amarya duk sun watse ya rage jiddah kawai a gidan, ta xauna sosai tayi wa uwani nasiha game da aure, ta qara nuna mata wannan auren daban yake da irin wanda tayi a baya.

Cikin ikon Allah kuwa uwani ta saurareta cikin nutsuwa har take ganin jiddah mai son ta ce bata mata baqin ciki a rayuwarta.

Ganin dare nayi sosai ga el’mustapha sai faman kiranta yake ya sakata shirin tafiya, ga mamakin ta sai ji tayi uwani na fadin.

Yanxu anty jiddah shima yusuf xamuyi irin wannan abin da mukayi da yaya el’mustapha kenan,

Cikin rashin fahimta jiddah tace menene uwani.

Tace ai kinsan da mukaje Lagos har jamcy ta bani pills na saka masa a juice, ai sau daya mukayi bamu qara ba, amma yusuf shima sai na saka masa pills dinne?

Subhanallah uwani, wannan abin sirri ne da baa so kowa yaji, tsakanin ki ne da mijin ki, ki riqe sirrin auren ki karki qara fadawa kowa, maganar ki saka masa pills kada na qara jin wannan, kin manta kece mace, shi xai neme ki ai.

Uwani ta washe baki tana fadin, ai anty jiddah hajiya ta bani wani abu nasha, shikenan inajin jikina ba dadi, ya xanyi yanxu.

Jiddah xata yi magana kiran el’mustapha ya shigo, tana dauka ya soma fada,

Ina hanya mijin jiddah, yanxu xan qaraso, baiyi magana ba ya tsinke wayar, sam bata bi ta kan uwani ba ta fice da sauri, a ranta tana tsoro kada su yi wani abu da yusuf uwani taje tana fadawa mutane.

Bayan fitar jiddah uwani taje tana qara duba gidan, taji dadin gidan sosai, taji ta qara son yusuf tunda bai hada ta xama da surayya ba, lallai el’mustapha bai son ta yana mata baqin ciki tunda ya hada ta xama da jiddah.

Tana xaune a falo ta tura masa test,

_cwt ni bana son wannan kaza da ake siyowa amarya, kifi nake so babba mai nama, ko daxu naci naman kaxa a gida bana so, ina ta jiranka tun daxu kayi sauri._

Yusuf ya jima yana karanta message din yana nanatawa, kuma ya kasa nuna wa wani abokin sa saboda nauyi da baqin ciki, kazar ma har sun siye haka ya qara siyen wani kifin daban. 4

Tana xaune a falo suka shigo tare da abokansa masu rakiyar ango, ba xato yaji uwani ta rungumesa, 1

Oyoyo mai sona,

Cak ya tsaya, numfashinsa na neman daukewa saboda irin rungumar da tayi masa, abokansa suka bisu da kallo.

Cikin wayancewa suka soma dariya, amma gobe su hadu majalisa akwai tsiya.

Da kyar ya janye ta daga jikinsa, cikin bacin rai yace miye haka? Ganin abokansa sun juya sun fita.

‘Anty jiddah tace idan xaka fita na raka ka ina maka addua, idan ka dawo na tarbe ma ina maka oyoyo xaka ji dadi.

Yace haka ta gayamaki tace kiyi a yau a gaban abokaina, ba ko alkunya uwani?

Ka siyo min kifin?

Cikin takaici yace ban siyo ba, yayi shigewarsa, ta bisa da kallon mamaki,

Inba baqin ciki ba miye laifinta dan ta nuna tana son sa agaban qawayenta?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *