FARA YAR SHEHU CHAPTER B
A hankali na ja kafafuna cikin hostel, duk jikina Yayi sanyi Dan ko sallamar Arziki bamui nida Adda Sa’ada ba. Meye kuma Inna Ade take nufi da rayuwata zatace Ayimin aure, idan na tuna agreement din da mukai da Abba, har Yanzun akwai more than a year zuwa lokacin da ya yarda na kawo mishi mijin aure, but see what this old woman is talking about.+
Koda na koma daki, rasa inda zan saka raina nayi naji dadi, gaba daya se nakeji Tsoro yana addabar zuciyata. Alwala naje nayi na gabatar da Sallar Maghrib sannan na dauki wayata na kira Yaya Suleiman. Ringing biyu ya dauka yana fadin
“Ajhumma!”
Se naji na kasa ce masa Ajhussi Kamar yadda muka saba, nace
“Yaya Suleiman, kana ina? “
“Akwai wani abu ne? Ina gida “
Kaina na gyada Banji dadi ba, saboda it’s bothersome nace yazo Ya kaini Unguwa.
“Shikenan kawai”
Kanshi Ya girgiza yace
“Nasan dole akwai wani abu, ko daga muryarki ma, tell me do I have to come over? “
Kaina na gyada inajin bacin rai na yana dan sauka kadan kadan nace
“Gidan Anty Bintu zaka kaini Dan Allah “
Dariya yayi yace
” You don’t have to plead princess, on my way “
Ko godiyar dake bakina banyi ba, ya kashe wayar. Haka na janyo Hisnul Muslim dina Dan nayi azkar. Ina kammalawa yayi min waya na fito, Seda naje zan shiga front seat sannan na fahimci shida wani abokinshi ne, zagayawa nayi na koma baya. Seda ya Fara driving kafin na gaida abokin yana ta Murmushi yana fadin
“A’a dole mutumina, wannan kyakywar yarinya Haka, dole komai kace Asma’u “
Duka Yaya Suleiman Ya kai masa a kafada yana dan dariya kasakasa yayinda naji wani sassanyan farin ciki ya lullubeni. Kenan har Abokanshi sunsan Asma’u, kenan yana labarina cikin friends dinsa? Se na saki Ajiyar zuciya. Hisham sunan abokin, so shima Intern ne a AKTH sede shi ba Doctors bane, physiotherapist ne.
“Asma’u, Kinsan yadda kike kuwa a gurin Yayanki, a asibiti babu Wanda baisan sunanki ba…… “
Steeree Yaya Suleiman Ya buga da hannunshi, hakan yasa Hisham kallonshi kuma Yayi Shiru, Nima daga idanuna nayi Ina kallonshi ta rear mirror, se naga kamar ranshi ya baci ba Kamar zuwanshi ba. To me yasa? Ko baya son na sani ne? Kaina na sunkuyar na cigaba da danne danne a wayata amma badan ina fahimtar abinda nakeyi ba, Gabaki daya hankalina da kwakwalwar Kaina suna wajen Maganar da Hisham yayi, idan kuwa Hakane kuma da gaske ne, babu tantama soyayya ce.
A kalle kalle na, abinda na fahimci soyayya ba se an furta ba, Caring, showing concern, protection shi ne soyayya. Wanene Yaya Suleiman baiyi exhibiting ba, babu shi, so Far zan iya cewa shima yana jin abinda Zuciyar Asma’u takeji.
Anty Bintu last born dinsu Ummaah ce, kuma itace favourite Aunt dina, dukkan wani abu da ya sameni bayan Adda Sa’ada, to ita ce ta biyu da take sani. Tana sona sosae kuma ban taba kaimata kuka na ba, bata lallasheni ba.
Koda naje tana tsakar gida, ta gama kada miyar dare akan murhu, Tana jin sallama ta, Ya’yanta su uku suka yo Kaina, suna murna. Tabarmar da aka shimfida a tsakar gida na samawa Kaina matsuguni munata hira da Yaran. A Haka ta karaso muka gaisa aka zubamin tuwo.
“Wannan zuan Daren nasan dole akwai abinda ya faru da bazai fadi a waya ba Ko? “
Kaina na gyada ina gyara zamana nace
“Anty Inna Ade ce! “
Kawai se naga hawaye ya gangaro min, cikin sauri nasa hannuna na dauke shi amma hakan bai samu ba, Dan take Wasu suka Fara gangarowa, it’s sure unlike me kuka cikin mutane, ni ban yadda wani ya fahimci weakness dina ba, hakan yasa duk halinda nake ciki nafi so nayi kuka ni daya a toilet, amma see this useless tears!
STORY CONTINUES BELOW

“Kanki Inna Ade ta dawo kuma?”
Kaina na gyada nace “Tace Wai Ayimin aure, gaba daya ta dagawa su Ummaah hankali, kuma ni babu Wanda ya taba cewa yana sona, kowa sede yace Inada kyau! “
Kanta ta gyada, wannan Maganar repetition ce, ta rigada taji ta bakin Ummaah da Adda Sa’ada.
“Share hawayenki kijini. Yaushe zaku je bikin nabila”
Hawayen na share Kamar yadda tace, nace
“Kashen satunnan zamu tafi”
Kanta ta gyada tace
“Then zakije Kiyiwa Inna Ade magana, saboda a Yanzun mafitar da kike da ita kenan. “
Nima naji hakan ne ya dace, idan kuma ba Haka ba to tabbas abun ba Zaiyi dadi ba. Mun jima da ita Har nayi Sallar ishai sannan Yaya Suleiman Ya dawo na fita ya maidani makaranta shi kuma ya wuce.
Karshen sati muka tafi Fotuskum, inda anan ake rikon Nabila, kuma saboda karar da iyayenta sakaiwa marikan, aka yanke acan zaayi biki da komai. Da yamma likis muka isa, Dan Haka ina ganin anata shirin tafiya wajen Bridal shower amma naki, saboda Uwar gajiyar dana debo bazata barni na fita ko nan da can ba. Abinci da aka kawo mana naci, nayi wanka sannan na samu guri na kwanta, tun ina jin hayaniyar Yan matan har na koma Se ta Manya kawai.
Dakin da aka bawa Inna Ade, nida ita Zamui squatting, so bayan na yi Sallar ishai na shiga nayi mana shimfida sannan na fita kofar gidan, na zauna wayata a hannuna. A family dinmu, mu hudu ne kawai sa’anni gashi dukkansu zasui aure leaving only I behind. Ina a zaunen Ina hango Yaran dake bayanmu sunata hira da samari, se abin Yayi ta bani mamaki, ni da nake yayarsu bansan wannan ba amma kalle su.
Zama naji Anyi a gefena, of course nasan Yaya Suleiman ne, ko daga kamshin Perf dinsa. Murmushi nayi na kalleshi nace
“Yaya, ya akai ka ganeni? “
Baki ya bude na mamaki yace
“Haba princess, ai ko daga bacci na tashi aka Tara min mata se na ganeki, Kinsan how special kike a gurina?”
Wani sanyi naji cikin raina Ina Murmushi na rasa me nakeji a wannan lokacin, amma abu daya na sani, wannan feeling din bazai fadi da baki ba.
“Ya Postikum din? “
“Not bad”
Na fada Ina karewa gurin kallo, baice komai ba amma dukkanmu Munyi Shiru, bansan abinda yake a zuciyarshi a wannan lokacin ba, but ni tawa tafi farar takarda fari, yanayin iskar dake kadawa a hankali, hankalina a kwance Ina wasa da ganye daya fadi, weather cool and romantic.
Wajen goma da rabi, na koma daki, Inna ta kwanta amma Batayi bacci ba. Shirin kwanciya nayi sannan Nazo na kwanta gefenta, tareda sakin Ajiyar zuciya, jin wani yanayi me dadi, that moment irin dinnan kayi tafiya Ka gaji, kazo ka kwanta, Hatta kashin spine dinka se kaji dadi.
Kaina Inna ta shafa tana fadin
“Asma’u Fara ‘Yar Shehu. Yarinya ta girma. Allah yasa Kema naga Naki auren”
Murmushi nayi a raina na amsa Amin, sannan na ayyana wannan shi ne best moment daya kamaata muyi magana da ita. Gyara kwanciyarta nayi, na riko hannunta nace
“Inna Ade! “
Kallona tayi ta kuma kalli hannunmu da nayi Interwining dinsu, tace
“Ya akayi kawaliyya? “
Kaina na girgiza nace
“Ance min kince na fito da miji Ayimin aure ko? “
Kanta ta gyada tareda tashi ta zauna, nima Se nayi yadda tayi nace
“Inna aure lokaci ne, nasan Kinsan hakan tuntuni. Kuma kinga karatuna akwai matsala idan na tsaya aure. Kuma Abba cewa Yayi se nayi shekara uku sannan zan Fara kula samari”
Tunda na Fara magana ta tsareni da idonta, gaba daya se naji na takura tamkar ba wannan tsohuwar bace Dana saba da ita.
“Na fahimta sun aikoki Ki ja da abinda na fada musu kenan? “
Kaina na girgiza nace
“A’a wallahi Inna, Kinsan ko Maganar bamui dasu ba, kawai naji nayi miki magana ne. Kiyi hakuri “
Murmushi tayi tace
“Shikenan, amma da zarar miji yazo ki kawo shi, Karatu baya hana aure, Haka aure baya hana Karatu. Na fahimci bakida saurayi shiyasa….”
Katse ta nayi da sauri ina dariya, a Haka Maganar ta shiririce har mukai bacci munata hirar Mu. Washegari akai kamu, al’adarsu ta birgeni sosae. The next day akai daurin aure, aka Mika ta gidanta.
Interval din sati daya ne tsakanin bikin Nabila dana Rayhana, muna dawowa muka shiga shiryayen bikin gagaruman Masoya.Ban kasance mutum bace me son taro, shiyasa indai ana taro gaba daya se naji an takurawa rayuwata. Gashi kuma Kamar Hadin baki anzo an saka Bikunkuna uku, kowanne interval din kwanaki biyar ne. Tun alhamis muka tafi Faskari, Dan Baban Rayhana Dan can ne kuma acan zaayi bikin. Bana wani doki saboda naje Faskari Har Bazan irga sau nawa ba. Unlike yadda nayi ta zumudin zuwan Potiskum.
“Wai har yanzun Baki shirya ba, Haba ke kuwa Asma’u kowa ya shirya fa “
Kaina na dago daga kan pillon nace
“Ke rabani da wannan event din naku, wallahi na gaji”
Tunda muka zo na samu guri na kwanta Kamar yadda nayi a bikin Nabila, Tun can dama ban fiye son shiga cikin mutane ba, to Yanzun abin yafi tsamari. Hannuna ta ja tace
“Amma dai Kinsan aurena daban yake dana kowa ko? “
Kaina na dauke saboda na tsani naci, one halin Rayhana kenan. Fita tayi ni kuma na cigaba da kwanciyata ina chatting. Bata jima ba se Gata ta dawo da wayarta a hannu, ranta a bace ta miko min, Babu musu na karba ban duba ba na kara a Kunne na. Muryar Yaya Suleiman naji yace
“Banda musu, bazanji komai ba. Ki tashi ki shirya! “
Cire wayar nayi na mika mata nace
“Jarababbiya kawai”
Dariya tayi, ban dauki wani lokaci sosae ba na gama shiryawa, gidan uncle dinta zaayi cocktail party din. Dake yanada kudi, gidan Babba ne sosae, wajen da swimming pool yake anan akai decorating gurin. Tunda naje na samu gefe na zauna, Ina ta kallon yadda ake ta hidima, amma the only thing da nake so a wannan lokacin shi ne kadaici.
Da daddare Ina zaune Farfajiyar gidan, inda aka Kawata su da concrete chairs, ni daya ce a Hut din, se jotter a hannuna Ina revising mode of action din Wasu Antihelmentics . Wayata ce tayi ringing, daukar ta nayi na duba naga Ummaah ke kirana, dauka nayi tace Nazo naci Abinci. Amsa mata nayi sannan na mike Dan shiga ciki amma wayata ta kara katsemin hanzari, wannan karan Yaya Suleiman, bai samu yazo ba saboda yana call a asibiti. Komawa nayi na zauna tareda kara wayar kunnena nace
“Oppa! “
“Yan mata! Ya Faskari? “
Kallon compound din nayi sannan nace
“Alhamdulillah, ya asibiti? “
Dan Tsaki yayi yace
“Ki Bari kawai, ji nake kamar na gudo. Zakiyi mamakin irin aikin da nasha Yau “
Dariya nayi a hankali nace
“Ayya! Sannu. Hippocratic Oath! “
Murmushi yayi sannan yace
“Zaki ji me ake ji ne, ai Kin kusa kare preclinical dinki. “
Murmushin farin ciki nayi, saboda dadi nake ji idan na tuna wata Shekarar by now, na gama preclinical years dina, at least nayi halfway kenan. Mun jima munata hira dashi Har seda Ummaah ta turo aka tafi Dani sannan mukai sallama.
Kwana biu muka kara a Faskari, muka jiyo gida, Amarya aka kaita gidan Abdul. Tana ta kuka da muka rakata Har seda tasa naji Tsoro ya kamani, a ganina Mutumin dake ihun ayi mishi aure kuma Anyi yana wannan kukan, ni kuma suma zan dinga yi kenan.
A hankali rayuwa ta cigaba da gudana har shekara daya Tazo ta wuce, wata ta shigo cikin hukuncin Allah yadda nake Allah Allah shekarun da zan gama preclinical suzo, sunzo kuma I was successful. Batuna da Yaya Suleiman we’re still hooked sede ni ban fahimci inda relationship dinmu ya saka gaba ba, bansan Menene matsayina a gurinshi ba amma shi yanada Babban matsayi me kuma girma cikin rayuwata, shi ne Mutumin da ko Murmushi yayi se naji gaba daya lokaci ya tsaya cak, se naji Wasu butterflies na yawo cikin cikina. In a nutshell, Ina son Yaya Suleiman kuma banida wani buri a rayuwata irin naga mun zama officially one, Mata da miji. Tun ranar da na fahimci zazzafan son da nake mishi, ranar na Fara adduar Allah Ya karkato min da hankalinshi Kaina.
Akwai wani yammaci yazo school ya sameni, ranar nayi mamakin abinda nayi. Bana kwaliyya saboda looks dina ya isheni, I’m comfortable da yadda fuskata take, dukda mutane na cewa saboda Inada kyau shiyasa Bana kwaliyya. Tunda yace min zaizo na shiga wanka nayi kwaliyya ta ban mamaki, dake is not a usual thing, ba karamin kyau nayi ba. Wani bakin lace na dakko skirt da riga nasa, jikinshi Anyi zanen flowers Fuschia Pink kanana kanana. Yayimin kyau. Seda na dakko matching veil da Takalmi, na feshe jikina da constant turarena na Silent Woman, Dana kalla Kaina se naji kwakwalwar Kaina tana kwaba ta, Tana tuhumata akan zakewa da nakeyi amma dake zuciyata tayi Naam da hakan, haka nasa Kaina na fice inajin yadda roommates dina ke zuzuta kyaun da nayi. Kamar kullum a kan motarshi na sameshi Ya tsirawa kofar hostel idanu yana jiran isowata. Tunda na matso inda nasan tabbas zai ganeni nake tafiya cikin nutsuwa tareda counting takuna. Ina zuwa Naga ko idanunshi Ya kasa kiftawa balle ya dauke, wani farin ciki naji Ya mamaye min Raina,
“Oppa! “
Na fada Ina Murmushi genuinely, Ajiyar zuciya ya sauke yace
“Kinyi kyau sosae fa. Looking stunning “
Hannuna nasa na rufe fuskata saboda Murnar da nayi jin sakona ya isa. Kanshi Ya rausayr yace
“Nasan wannan kwalliyar wani gurin zakije, shiga mu wuce, zanyi magana dake dama”
Se naji Banji dadi ba, shi baisan danshi nayi ba amma zaice Unguwa zanje, shiga nayi duk yanayina ya canza, bai lura ba da yanayina ba, Waka yasa ta Celine Dion I love you! Gaba daya se atmosphere ta zama cool
_I wish I could go back to the very first time I saw you, should have made my move when you look into my eyes, Cuz by now I know that you feel the way that I do…._1
Zuciyata kawai fada min take, the song is for me, Dan ni Ya saka. He’s conveying his heart into mine. Gidan Adda Sa’ada mukaje, dama nasan bata nan, amma dan kar yaji danshi nayi kwalliya kawai se nace muje. Daga nan Grand square mukaje shan Ice cream. Ana kawo mana na Fara sha, shikam hankalinshi baya kan Ice cream din se wayarshi Dayake dannawa, bana fulako indai Ice cream ne, so kan Ya gama danne dannen da yake har na shanye nawa, se kawai ya turon nashi, da farko naki karba amma daga karshe na sha kayana. Seda na gama sannan yace
“Kun taba Maganar aure da Abba? “
Cikin rashin fahimta nace
“Aure? Kamar me kenan? “
“Irin ya taba fada miki lokacinda yake so kiyi aure? “
Shiru nayi Ina tunani sannan nace
“Eh, he mentioned it, lokacinda zan Fara zuwa school yace, idan na gama Year 3 dina Zan iya kawo mishi miji “
Murmushi yayi yace
“Yayi kyau, kinga nanda shekara daya kenan. “
Kaina na gyada yace
“Kafinnan na gama ginin da nake. “
Murmushi nayi naji dadi a raina, Wannan shi ya kara min kaimin Kara sonshi a raina. Tundaga wannan ranar bamu Kara makamanciiyar Maganar ba, naje na fadawa Anty Bintu, itadai bata cemin I should go on ba amma tace na iya takuna, haka Adda Sa’ada ita cewa tayi completely na rabu dashi amma na kasa. A Haka na kammalla 3 years dina, sannan na koma AKTH inda na Fara Clinical years dina.
Ranar Alhamis Nazo gida daga asibiti dake mun Fara Internal medical posting. Wajen laasar Ina daki Yaya Suleiman Ya kirani akan Nazo abokinshi yazo na kawo musu juice suna compound. Hijabina na dakko na fito, Ummaah na fadawa sannan na dakko musu na fita, zan iya kiran abin tsautsayi ko kuma nace ceto amma nasan nayi receiving shockest blow a rayuwata.Gaba dayansu sun juya min baya, so babu Wanda yaga tahowa ta a ciki, dukda takalmina yana Kara amma nafi tunanin discussion dinne Yayi zafi da yawa shiyasa basu Ankara da zuwana ba.
“Man kana nufin ka cemin Baka son yarinyar nan? “
“So Kamar Yaya Khamis? “
Yaya Suleiman Ya tambayeshi, banga yanayin fuskarshi ba tunda babu Dama, kawai naji lokaci daya jikina Yayi min nauyi na kasa baya balle nayi gaba, tamkar an dasa ni a gurin Haka na tsaya inajin yadda zuciyata ke bugawa da karfin gaske
“Ka fahimci me nake nufi Suleiman, Dan me yasa zakai haka, Kasan Baka sonta. You should have let her go”
“Ni na tsayar da ita? Bani bane”
“Amma Kasan Tana sonka…..”
Shiru yayi saboda juyowar da yayi ya ganni, wannan shi ne karo na uku da muka hadu dashi, sun Je gurina Ina school sau daya, na biyu sun fito daga Operation su kazo gurina sukaci Abinci, last month kenan. Amma na yaba da halayenshi, he’s a good person
“Ga juice din “
Na fada Ina aje musu Sannnan nayi saurin Juyawa cikin gida, duk cikinsu babu Wanda Yayi kokarin tsayar Dani, saboda fuskata kawai ta tabbatar musu naji komai.
“Kagani ko? Kaga abinda Kaja ko, gashi taji”
Khamis ya fada yana buga Bumber motar, dauke Kai Yaya Suleiman yayi yace
“Is not as if Dama nace Ina sonta ne, kawai tana birgeni, tana cikin Favorite mutane da nake ji dasu. Ina tunanin tayi mistaken wannan da soyayya”1
“Dukda haka ka cutar da ita, tunda kasan cewa tana sonka, kaga kenan yaudarar ta kayi”1
Hannu ya daga mishi yace
“To Se me? Nace ta soni ne, I’m sorry for that. “
Duk abinda suke fada Ina tsaye Inaji, Dan da nayi gaba ban tafi ba, jikin katuwar pillar dake kofar shiga palor na tsaya Dan nasan bazasi Shiru ba. Bantaba sanin zuciya Tana suya ba se wannan ranar, kirjina tamkar an zuba wuta Haka naji, ga Inata kyafta idanu ko zan samu hawaye su sakko amma hakan bai samu ba, Illa karawa kaina zafi da nayi.
Ina shiga ciki, Ummaah na fitowa daga dakinta, kallona tayi tace
“Asma’u me ya sameki? Meye idonki Yayi ja? “
Kaina na girgiza, da kyar bakina ya budu nace mata
“Tun dazun Haka yake, baki lura bane”
Kanta ta gyada, dakina na nufa Se ta katseni da fadin
“Na zata zaki daura abincin dare ne. “
Kaina na gyada na nufi kitchen, Inaji tana fadin Idan tayi tsami zanji. Tunda na shiga na kifa Kaina akan kitchen Island, ni daya nasan ciwon da zuciyata, Raina da kwakwalwata ke min, gaba daya I was in shock.
“Tashi ki fada min abinda ke damunki? “
Naji muryar Ummaah a tsakar kaina, da sauri a kuma firgice na dago, tana tsaye ta zuba min idonta, hakan da nayi nasan ta fahimci tabbas akwai wani abu amma Bazan fada ba, tunda I’m naturally introvert. Kasa ce mata komai nayi, se kawai na shiga store na dakko abinda zanyi amfani dashi, bata bar gurin ba Har seda taga tabbas bazanyi magana ba, sannan aikin Yayi nisa kawai se cemin tayi
“Koma Menene, kiyi hakuri Allah yana sane dake”
Wannan furucin da tayi yasa Wasu hawaye masu zafi suka shigo sakko min, saman fuskata. Ko damuwa in sharesu banyi ba na cigaba da aikin da nake suma tamkar Kara tunkudo su akeyi Haka suka ta zuba, gaba daya hankalin Ummaah ya tashi, tayi ta rarrashina amma kamar zugani take. Karshe cemin tayi
STORY CONTINUES BELOW

“Koma daki Ki huta, Bari nayi da kaina”
Hannuna na wanke na fita ba tareda nayi musu ba, Dan babu bakin musu a taredani, gani nake idan na sake na bude baki to kuma alamari baci Zaiyi. Hijabina naja na rufe fuskata saboda tsoron kada na hadu da Yaya Suleiman. God so kind, ban hadu dashi ba, da kowa ma Har naje daki na kwanta akan gado, kuka nayi tayi kamar Raina zai fita, na kasa tunani saboda Kaina ma a cunkushe yake.
Seda na gaji dan Kaina sannan na mike na shiga toilet, har wani jiri nake ji. Fuskata na wanke nayi alwala sannan na fito na tada sallah Maghrib. Ina idarwa naji sallamar Adda Sa’ada, cikeda mamaki na dago ina kallonta, itama ta tsura min idanu se kallona take, hakan se ya karya min zuciya, Wasu hawaye suka shiga sakko min akan kuncina, Dama tuntuni fuskata tayi jawur. Karasa shigowa Adda Sa’ada tayi ta zauna gefena tace
“Asma’u! Kiyi hakuri dan Allah, ki daina kukan ai Kinyi da yawa”
Hannuna nasa na share fuskata, se naji dan sanyi ya tsirgamin a raina, at least I’ve someone that’s here to comfort me.
“Adda Yaya Suleiman yace baya sona, wai shi bai sona”
Na fada Wasu hawayen na kara gudu Kan fuskata, Idanunta ta Dan runtse sannan ta bude su akaina tace
“Kince mishi kina sonshi ne? “
Da sauri na girgiza mata kaina, nasan banida wani aji daya rage, na rigada na zubar dashi akan nunawa abinda bai sona so, nasan Ina sonshi Kamar raina amma daidai da Rana daya ban taba ayyana nayi splitting masa abinda ke zuciyata ba, koda hakan na nufin zan zauce ne.
“To ya akai kika sani? “
Ban daina kukan ba Haka bakina baiyi Shiru na fada mata duk abinda naji, dukda nasan I’m going to have a scolding, tunda ba irin nasihar da Batayi min ba akan na rabu dashi naki, na tabbatar wannan ranar take gudar min, gashi kuma tazo din.
“Ki manta dashi, bashi kadai bane namiji a duniya. Nasan Menene so nasan idan zuciyarka tana son abu, mostly Baka ji baka gani, zuciyarka wannan abin kadai take so kuma akwai lokacin da zaki ji zaki iya zuwa kowanne extent dan ki samu abinda kike so. So kenan! Amma ni ban yarda kaje inda baasan darajar ka ba, ban yarda ka zubar da kimar ka a wajen namiji ba, so inaso kiyi hakuri, rabon kwado baya Hawa sama ko ya hau se ya fado. Take heart”
Mun jima tana ta bani baki, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na rakata ta gaida Abba sukai sallama da Ummaah ta tafi. Ina dawowa daga rakiyar na iske Yaya Suleiman yana tsaye a parlor alamun yana jiran wani abu, dauke kaina nayi tamkar ban ganshi ba, saboda ji nayi tamkar naje na rufeshi da duka amma babu halin hakan
“Asma’u! “
Naji Ya fadi sunana, tsayawa nayi cak kafin na juyo bance dashi komai ba se kallonshi da nake,
“Abba yana nemanki”
Idanuna na dan zaro nace
“Abba? “
Kanshi Ya gyada, fasa shiga dakin nawa nayi na nufi parlon Abba, yana zaune shida Ummaah se Yaya Halifa, muma gefe muka samu muka zauna bayan mun gaida Abba da Ummaah. Gaba daya naji na takura saboda shirun Abba, tunda na gama Year 3 dina nake gudun kebancewa da Abba saboda Ina tsoron yayimin Maganar aure, saboda nasan alkawarin da mukai tun kafin in shiga Medical school.
Gyaran muryarshi ya katse min tunanina, dagowa nayi na kalleshi, shima kallona Yayi sannan ya Kalli Yaya Suleiman kafin yace
“Halifa ayimana addua “
Take Yaya Halifa yayi opening prayers, wannan ya tabbatar min tabbas Maganar zaayi sede banda insight akan Maganar da Zaiyi amma nasan akanmu ne.
“Suleiman, Asma’u! “
A tare duka muka kalleshi, wani irin uneasiness Ya baibaiyeni. Sassauta fuskar shi Yayi, Dan yaga yanayin da nake ciki Kamar ace min kyat na zura a guje.
“Naga Dukkanku babu Wanda yake shirin zuwa Yayi min zancen aurenshi, to ni se naga bari na tuna muku. Inason kowannenku zuwa next week ya zomin da kwakwarar Maganar! “
A zabure nace
“Abba, next week? “
Kanshi Ya gyada yace
“Akwai problem da hakanne? “
Jikina a sanyaye na girgiza Kai sannan nayi kasa da kaina, gaba daya hankalina ya tashi, to ya zanyi ni? Wa xan cewa ya turo tunda ni ko saurayi bani dashi, Tundaga wannan lokacin hankalina ya gushe bansan abinda aka tattauna anan parlon ba dukda ina zaune amma hankalina baya gurin, Yayi nisa, Ya tafi nazarin maganganun Abba.
Washegari dana fito seda kowa ya tambayeni abinda ke damuna saboda yadda idanuna sukai zuruzuru, kana kallona Kasan Ina cikin damuwa amma nayi tunanin Dan da kyar bacci ya daukeni saboda Tashin hankali. Ko yadda nake aiki Ka kalla akwai alamar tambaya, komai bana jin dadinshi, kawai dai Inayi ne Dan babu yadda zanyi,. Na gama hada breakfast ban kai ga fitowa ba naji sallamar Yaya Suleiman, Dama tunda mukai wannan abin ba mu sake magana ba, banda kiran da yayi min. Zuciya kenan wani bangaren se yake Murnar ganinshi yayinda wani barin ke kallonshi a matsayin mayaudari, maha’inci kuma azzalumi.
“Asma’u Biyani! “
Juyowa nayi na kalleshi, Bazan iya tuna lokacinda naji ya kirani da Asma’u ba, Bazan iya tunawa ba.
“Sorry for what? “
Na tambaya ina iyakar kokarin nuna strenght dina, dukda lokacin battling ake internally, zuciyata gaba daya tayi rauni Har tana son affecting muryata.
“Nasan Kinji Duka Maganar da mukai nida Khamis jiya akan Maganarki. Bansan kina sona….. “
“Sonka? Ni? “
Na fada Ina nuna kaina da middle finger dina, Kaina na girgiza nace
“Meyasa zan soka? Haba Yaya Suleiman Kamar yadda Kake jina matsayin special sister Haka na dauke ka. Ina fata zakai clearing abinda ya cunkushe maka kanka! “
Daga Haka na raba ta gefenshi na fice, a fuskarshi naga disappointment, yaji haushi na fada masa Haka, yafi son nayi ta dakon sonshi bayan shi ba sona yake ba. Tundaga ranar na cireshi a cikin rayuwata, gaba daya na koma masa Asma’u ta da, Bama taba zama muyi Maganar Arziki Ni dashi, naji na tsaneshi bana son ganinshi a rayuwata.Wani irin mugun jiri ne yake neman kayar dani, bansan na damke trolley da aka hada kayan da zaayi surgery ba, take kuwa kowanne ya zube, Haka nima nabi trolley nayi baya zan fadi, amma na bude idona da kyau da suke min wani irin blurred vision, gaba daya head surgeon din, assistant, scrub nurses da Anaesthesist din suka jiyo suna kallona, bakina na bude danyin magana amma na kasa saboda wani baya da na kara yi, daga nan ban kara sanin me ake ciki ba, na suma.
Farkawa kawai nayi na ganni an maidani ward, hannuna an daura min drip yana shiga slowaly. A hankali na tashi na zauna ina tuna abinda ya faru, ranar shi ne karona na farko dana Fara shiga operation theater a rayuwata, tunda akace Dani zaayi surgery gaba daya hankalina ya tashi, saboda Ina tsoron jini, bana son ganin jini, amma nasan tunda na zabi yin medicine dolene nayi hakuri nayi adapting. Muna shiga, mukai changing sannan mukai scrubbing aka hada komai, ina gefen surgeon din yana tamin bayanin procedure da zaayi. Tunda ya karba scapel na runtse idona, Ina jin tsikar jikina yana tashi, yana yankawa naji yawu ya cika min Bakina, amma haka nayi composing kaina, har aka shiga deep, ai lokacinne naji jiri Ya fadar dani.
Kaina na dafe ina ayyana abinda ya faru bayan na fito, yadda na zubar da kayan aikin. Da kaina na cire drip din sannan na tashi na fito zuwa Nurses station, suna zaune dukkansu suna ta Rubutu cikin files din patient.
“Kin farka, Sannu! “
Daya daga cikinsu ta fada, zama nayi nace
“Yawwa, Sannunku da aiki”
Dukkansu suka dubani sannan na koma theater, lokacin sun gama suna lounge suna hutawa na shiga, gaba daya suka dago suna kallona, seda na gaidasu sannan na zauna nace
“Sir I’m sorry, I was carried away ne”
Kanshi Ya gyada yace
“Oh I see! Ya jikin naki Yanzun? “
Ajiyar zuciya me nauyi na sauke nace
“I’m feeling better, Alhamdulillah!”
Kanshi Ya gyada yace
“Kije hostel Ki huta, you eat before coming to theatre. “
Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na dauki kayana na nufi hostel Dan na huta. Wanka nayi sannan na kwanta akan gado take kuwa bacci yayi gaba dani, Dama tunda na dawo daga gida bana samun isashen bacci saboda tunanin yadda zan bulowa Abba nake, ya zanyi da Raina, Ina zan samu mijin da zanyi presenting ma Abba. Shiyasa ko abincin Arziki bana samu Ina ci, ko na Fara ma se Inji gaba daya Ya fita a Kaina. Ina ganin Harda hakan ma yasa na fadi, Dan gaba daya bana cikin nutsuwata.
Se bayan Sallar laasar sannan na tashi, wanka na karayi na shirya cikin simple Abaya nude peach nayi rolling da farin mayafi sannan na fito da wallet dita na tafi wani eatery nayi order milk shake da pancake da akai topping dinsa da strawberry. Ina fara ci naji gaba daya an zare min apepite dina, se kawai na jingina da kujerar da nake Kai na lumshe idona Wanda yake kokarin zubar da hawaye. Ban taba kawaowa zan iya shiga Tashin hankali makamancin wannan lokacin ba, gaba daya ji nake an saka min pressure da yawa, dama ace Ina da saurayi it will be better amma banida kowa ina Abba yake son na samu saurayi.
Mikewa nayi na fice bayan nayi settling bill din, a hankali naji iska me sanyi tana kadawa, Hatta rigar dake jikina seda ta kadu, yadda iskar keda sanyi Haka nan zuciyata ta Fara sanyaya. Na kusa hostel naji an Kira sunanna
“Dr. Shahada! “
Juyawa nayi inda Maganar ta taho, Dr. Ammar ne course mate dina, Dan Murmushi na saki suka karaso shida Dr. Umaymah. Suna zuwa Ammar yace min
“Shahada Oga Mansur yace bakida lafiya “
Faint smile nayi nace
“I zoomed out a theater. “
STORY CONTINUES BELOW

Gaba dayansu suka Fara dariya, nima ina tayasu, nan Umaymah ta bamu labarin yadda tayi nata dake O&G take. Munata dariya muka samu wani bench muka zauna munata hira, yawancin Kan yanayin karatunmu ne da kuma aiki, seda aka Kira Sallar Maghrib sannan muka tafi hostel nida Umaymah shi kuma Ammar ya wuce masjid.
Asiya kadai ce a dakin, ta gama dafa noodles, Ina shiga tace Nazo muci, kaina na girgiza tareda yi mata godiya sannan na kwanta akan gado na tunda period nake. Na jima a Haka se naji sallamar Amina Aminu, tashi nayi na zauna dan nasan gurina Tazo, hannunta dauke da handouts dinta ta zauna gefena tace
“Kai ashe kin samu sauki, akacemin bakida lafiya “
Dariya na danyi kadan nace
“Ki ce an bazani na fadi a theater, shit! “
Tashi tayi ta dakko katon mirror dake kafe a dakin ta kawo min, tareda haska min fuskata gaba daya nayi wata iri Kamar bani ba, duk na rame se haske Dana karayi, fuskata ta kankance. Seda ta tabbatar na gama sannan ta mayar dashi inda yake a kafe ta dawo tace
“Asma’u, zan iya cewa tunda nake kawaye bantaba Haduwa da Mutumin da nake so har cikin zuciyata irinki ba, ni ina daukarki matsayin yar Uwa wadda muka fito ciki daya da ita, Ina son halayenki they’re the best so far. Amma sede baki daukeni yadda na dauke Ki ba. Nayi tunanin kawaye sune mutanen da kake zuwa su Baka shoulders din da zakai kuka akai, nayi tunanin shekara hudu da Doriya da mukai daidai da Rana daya zaki cemin Amina gashi wannan abin yana damuna ya zanyi? Sede ni duk abinda ya sameni Shahada ce zata Fara ji….. “
Gaba daya naji kunya ta lullubeni saboda nasan Inada mugun zurfin ciki, bana son fadawa mutane damuwata Ina ganin tamkar na daura musu nauyi ne amma wannan karan Amina Na kaita bango tunda har tayi confronting dina.
“Amina Dan Allah kiyi hakuri, ba haka bane, kawai bana son Ina damun mutane da damuwata, se naga kamar zan takura su”
Kanta ta girgiza tace
“Ko daya Shahada, baki San idan kika fada ba Kamar kin rage tasirin damuwar, ba dole se kin fada min matsalarki ba amma at least ki samu Wanda kike ganin kin yadda dashi ki fada… “
Kaina na girgiza nace
“Kai Amina, ba haka bane wallahi Kinsan…. ” se kuma na kasa cewa komai Illa hawaye da suka Fara saukar min akan kuncina, hannuna ta rike tace
“Ya isa dan Allah, kada kiyi kuka roommates dinki suzo suna tamabayar ko lafiya. Nasan ke kadai kika san yadda kikeji amma ki sani Allah will always lay a helping hand! “
Daga nan bata kara magana ba se lallashina Har seda nayi shiru sannan na sanar da ita yadda mukai da Abba, nace
“Amina banida saurayi balle na tura, kuma Abba is very serious about it, na rasa ya zanyi ki bani shawara! “
Kallona tayi sannan tace
“Yaya Suleiman fa? “
Ai se ta kara tunzura ni, nayi ta kuka inajin Kamar zuciyata zata fito saboda zafin da take min, nanma lallashina tai tayi kafin tace
“Kun rabu kenan! Wannan kukan said it all. Kinsan wani abu, ni ina daukar aure a matsayin lokaci ne, idan yazo ko ka shirya ko baka shirya ba se kayi, sannan abune da Bazaa ce kayi rushing dinsa ba, ba Kasan hannun da zaka fada ba. Kwanakinnan aure Tsoro yake bani saboda yadda nake ganin anayi yana mutuwa, ana complain se naji Kamar kada nayi Shahada. Yawancin auren soyayya ne amma Se kiga an Kare da Tashin hankali, so Wanda suke son junansu kenan. Shahada tell Abba ya kara miki lokaci, Dan aure ba Nepa payment bane ko gidan haya balle a baka notice. Sannan kada wani pressure yasa ki fadawa unprepared marriage Baki San inda zaki fada ba. I hope I’ve helped! “
Naji dadin shawarar ta, ta saka na warware har tayi mana order aka kawo mana mukaci, mukai Karatu har 12am sannan ta Kara min nasiha ta tafi. Amma Se na kasa samun karfin gwiwar zuwa gida har lokacinda Abba ya bani Har ya wuce, kullum se Munyi waya dashi amma bai taba cemin uffan ba, Haka Ummaah nasan zuba min ido sukai. Kullum idan zan fita se nayi adduaar Haduwa da miji amma Ina ko tareni ma baayi sede ayita kallona Kamar zaa cinyeni amma babu me cewa wani abu.
Wata safiya mun gama ward rounds gaba daya mun taho yan team dinmu, Dr. Badamasi wani Consultant nabi office dinshi na consultation ina ganin yadda yake, yana tamin bayanin conditions iriri da management dinsu. Wayata dake cikin clutch dita tayi ringing, kallonshi nayi yace.
“Feel free, pick your call! “
“Thank you! “
Na fada sannan na dakko wayar, Sunan Dana gani seda gabana ya fadi, Yaya Suleiman ne, kashe wayar nayi na koma na cigaba da abinda nake amma kwatakwata hankalina yaki zama guri daya, se tunanin dalilin da yasa ya kirani nake, me zai ceminKarfe daya na Rana, Dr Badamasi yace na tafi na huta, fitowa nayi tareda kunna wayata na kira Amina Aminu Dan naji inda take, cemin tayi tana Lounge, can na tafi a hanya muna gaisawa da mutane. Naje zanyi kwana na shiga lounge din naga mutum a gabana Yayi min tsaye, dagowa nayi na kalleshi kamar yadda ya tsira min idanu, dauke kaina nayi nace
“Ya akai? “
“I need to talk to you “
Kaina na girgiza nace
“Sede wani lokacin Yaya Suleiman, Munada lectures “
Daga Haka na juya zuwa inda muke lectures, saboda bana son ya karyata ni ko kuma yaji saboda shi nayi karyar. Biyoni Yayi yace
“Asma’u yaushe muka fara yar haka dake, nasan posting kuke ta Yaya zakice min zakije lectures. Kiyi hakuri I know I was a monster, nasan kina sona amma…..”
Juyawa nayi na watsa mishi wani kallo na wulakanci nace
“Na taba ce maka Ina sonka? Ko na taba turowa nace ace dakai ina sonka? Ko daya banyi ba. Ka isheni ka dameni, ka rabu dani Haka manaa”
Hannuna yaja har seda muka zauna Kan Wasu concrete chairs, babu kowa a gurin kuma Allah yaso dukkanmu babu lab coat jikinmu.
“Naji bakya sona amma wannan ramar da Tashin hankalin dake akan fuskarki na Meye? “
“Ina ruwanka? Dama abinda kazo kaji Kenan? To ni Inada abinyi”
Daga Haka na mike zan tafi yayi saurin cewa
“Kada ki tafi Asma’u, kawarki nake so, kawarki Nadiya! “1
Bansan yadda naji a wannan lokacin ba, amma kafata kasa dagawa nayi, na tsaya cak inajin yadda kirjina yake wani irin bugawa, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun kadai nake ambata a raina, ji nake kamar ana ripping min zuciyata, Kawarki Nadiya na sake maimaitawa cikin kaina. Gabana yazo Ya tsaya yace
“Nadiya kawarki ita nake so, inda kin yadda kina sona dazan iya hakura da ita amma tunda perception dina ne Ina ganin gwara nabi son zuciyata”
Tunda ya Fara magana nake kallonshi, gaba daya kaina ya kulle na kasa tunanin abinda ya kamata nace mishi, se kawai na saki Murmushi me ciwo Wanda gwara ace kuka nayi tayi, amma tunda nace bana sonshi, ban taba sonshi ba, I’ve to prove myself.
“Yau zata dawo daga Yola, gobe Zanje na mata magana. “
Na fada a sanyaye na tafi cikin sanyin jiki, idanuna suka cicikko da kwalla, amma Banason nayi, nafi son Se na kebe Se nayi amma seda ta samu damar zubowa, saurin gogewa nayi na cigaba da tafiya, dakinsu Amina Aminu naje, babu kowa hakan yasa na kwanta gadonta nayi ta kuka, a raina Ina tsinewa Yaya Suleiman da yayi sanadin rabani da farin cikina. Seda nayi me isata sannan bacci yayi gaba dani.
Acan gida, Abba da Ummaah Har sun gaji da zuba idon ganin ta inda zan shigo gidan, tunda nayi sati biu Ummaah ke saka ran zuwana amma har nayi uku Ina neman karasa na hudu Bbu alamata. Ta kira Adda Sa’ada tayi mata complain Adda Sa’ada tace ta rabu dani Zanzo da kaina. Abba kanshi seda yace da Ummaah tace min ya janye min Maganar na dawo gida amma Ummaah tace ya barni Zanzo da kaina.
Se dare sannan na dawo hayyacina, bayan Munyi Karatu na koma dakinmu, nayi wanka na fito zan shirya kawai naga mutum akan gadona, Nadiya ce
“Omo… Omomo! Yaushe kika dawo”
Hannnuna taja na zauna tace
“Dazunnan Lady, Bazan iya jira Har Se gobe ba”
Murmushi nayi nace
“Bari nayi sauri na shirya mu fita waje.”
Tana ta min hira Har na gama shiryawa sannan muka fito tare, wani secluded area muka samu nayi mana order aka kawo sannan muka zauna. Nayi farin ciki saboda Rashin magana wani lokacin Yayi a rayuwa, da ban kasance marar surutu ba, da tabbas na fadawa Nadiya yadda mukai da Yaya Suleiman, Allah Ya taimaka indai mukai waya se nace mata idan ta dawo akwai magana, Dana tabbatar bazata taba amincewa da zancen soyayya da Yaya Suleiman ba.
STORY CONTINUES BELOW

“Ma’u duk kin rame, me yake damunki haka, kinganki kamar ba Asma’u ta ba”
Murmushi nayi nace
“Mhmm, Karatu ne yake cakar Dani, I’m about to start project. “
Been the Nadiya she always is, seta yadda da abinda nace nan muka fada hira sosae anan nace mata
“Nadiya Ya Farouq? “
Tabe Baki tayi tace
“Ba nace miki Munyi breaking ba, ai tun wannan fadan da mukai muka kasa fixing abin, se naji Ya fita kawai akaina, I can’t continue with someone like him. “
Kaina na gyada nace
“Ki dinga hakuri and whatever, Dama ke dashi since from the start you were not meant to be. Yaya Suleiman yace yana sonki kum…… “
Kallona tayi da confusion tace
“Yaya Suleiman Wanne? Naki Wai?”
Hannunta na kama ina Murmushi nace
“Meye kike wani panting saboda nace yana sonki, Eh Yaya Suleiman na gidanmu. Yaushe kike free na rakoki”
Tsira min idanu tayi tana kallona tamkar tana son karanto wani abun, kaina na dauke saboda idanuna are weak zasu iya badani Susa naji Kunyar da Bazan manta ba.
“Behind wannan smile din naki, Ina hango damuwa a tattare dake, Ki fada min abinda yake damunki mana, ni ce Nadiyanki fa”
Murmushi nayi nace
“Kinsan talks dinki yana sani kuka ko? Maganar Yaya Suleiman muke. Ya kike ganin. Can you? “
Kallona ta kuma yi, a take na fahimci me take nufi ba girgiza Kai nace
“Karkiyi tunannin dating muke da, A’a we were just favourite cousins kin gane? So ni ce babbar kawar Amarya, babbar Aminiyar Ango. How do you see it? Abin Yayi ko? “
Rungumeni tayi tace
“Duk tunanina soyayya kuke shiyasa nake hesitating karbar zancen. Ke a matsayin sister dita wacce shawara kika bani? “
Gyara Zamana nayi nace
“Ki amince, so far mun jima tare dashi kuma ko a family ana yabon shi. Beside Mamanshi batada matsala. Sede nace all the best “
Bakina na bude tareda kawar da kaina saboda hawaye da naji yana neman bada ni, hura iska nayi tayi har na hadiye hawayen sannan na samu muka cigaba da hirar mu.
Da daddare nayiwa Yaya Suleiman text din number ta, address dinta sannan nayi mishi fatan alkhairi, Ina kallo Yayi ticking alamun delivered ai se kawai na Fara kuka, na sadaukar da abinda nake so, na tabbatar kodan wannan Allah zai bani lada kuma ya duba lamurana.
Tun Ina tunanin Yaya Suleiman zai Kira har na fitar da rai, se Washegari da yamma ya kirani akan na shirya muje tare, kawai se naji Ya raina min Wayo da yawa hakan yasa nace tutorial Zanje kawai ya tafi. Kamar wasa Nadiya ta kirani tana tamin ihu, Dama Haka Yayana yake, haka ya hadu Haka ya iya soyayya, karshe kasa karasa Maganar mukai nayi pretending network baida kyau na kashe wayar.
Ranar da na cika sati biyar banje gida ba, muna ward, Senior Doctor da nake bi yana call so muna tare dashi Sega Amina Aminu tazo, seda ta gaida Dr Mike sannan suka gaisa da Nurses din kafin tace min
“Asma’u Kinyi Bakuwa! “
Kallonta nayi nace
“Wacece? “
“Zo muje Ki gani”
Allah yasa mun gama abinda zamuyi Hakanan na bita muka tafi lounge din da muke, Tundaga Nesa naji gabana yana faduwa, amma ban kara tambayarta bakuwar ba. Ina shiga na tarar da Ummaah a zaune gabanta an aje mata lemu da ruwa, se naji wani dadi ya mamayeni, naji sanyi a raina. Rungumeta nayi ta baya nace
“Ummaah! “
Hannuna ta bubbuga tace min
“Ai fushi mukeyi dake. Saboda Allah Asma’u sati biyar kina Kano amma Bazan kizo gida ba. Me akai miki? “
Murmushi nayi na zagayo na zauna, tareda kwantar da kaina kafadarta, Murmushi yaki barin fuskata nace
“Ummaaah bansan me zance muku ba, amma banida saurayin da zan kawawa Abba shiyasa”
Cikeda tausayi na tace
“Shiyasa? “
Kaina na gyada nace
“Ummaah! “
Kanta ta shiga gyadawa tace
“Komai nufi ne na Allah kada Ki takura Kanki, Allah is the perfect timer, so abinda yake naki zaixo sede idan lokaci baiyi ba “
Mun jima munata hira, Tana ta kwantar min da hankali har tace min wani sati zaaje tambayawa Yaya Suleiman auren Nadiya, dukda Nadiya ta fadamin amma seda naji gabana ya fadi, zuciyata ta motsa, nayi saurin kawar da hakan muka cigaba da hiraramu.
Ina samun sukuni na tafi gida, kullum ina zuwa daga can, the only time nake kwana cikin asibiti sede idan Munada call ne. Batun Suleiman tamkar da gayya yake Wasu abubuwan duk abinda ya faru tsakaninshi da Nadiya, ni ke Fara sani Tun Ina damuwa Har na hakura, a Haka Manya suka shiga aka saka rana. Ranar nayi kuka Kamar zan fitarda idona, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na hakura, a wannan lokacin muka fara exams na shiga final year.

Tunda muka fara exams na maida hankalina kacokan, na share duk Wasu Abu da zasu kawo min tsaiko akan exams din amma dake Allah shi ke handling komai, kuma bazakai cheating nature ba. A karshe dai I break the record, seda na fadi wani course under paeds. Omomomo! Nasha kuka Kamar zanyi hauka, saboda na tabbatar damuwar da nake ce ta sani a ciki. Abba was the only one that supported me amman su Yaya Halifa Kamar ya dakeni, yace na zauna wasa abinda banyi a baya ba shi nake kokarin nayi Yanzun, to nasani karatunnan shi kadai ne rufin asiri na. Dama a gidanmu idan kaga ana yaba maka, to sailing Kake successful amma da zarar Ance you failed babu Wanda zai bi bayanka.
Naji haushi Dan Hatta Adda Sa’ada wannan karan bamuyi da dadi da ita ba, hakan yasa na dawo hayyacina Naga Meye nakeyi? Kashe Kaina zanyi saboda wani namiji, Wanda ya manta abinda ya faru gaba daya, shi Yanzun house job dinshi Ya gama gaba daya, ya fara residency bayan nan aurenshi Zaiyi, to ni Meye na rike wannan abin cikin zuciyata? Nayi dwelling a rayuwar da ta riga ta wuce. A lokacin na kara fahimtar wani abu da son zuciya ya hanani gani, shi ne Suleiman bai yaudareni ba, ni na yaudari Kaina, ni nayi hurting Kaina, tunda shi baice yana sona ba, yasan ina sonshi to me zai min? Zaice Asma’u daina sona? Bazai yiwu ba. At the spot nayi making mental note cikin kaina akan wannan abin, wannan Maganar ta wuce Har abada sede a hira.
Nayi Karatu kamar babu gobe, Dama six weeks ne favor din kayi resit, kuma Alhamdulillah Inayi nai making, na zama final year medical student. A lokacin shirin bikin Nadiya da Yaya Suleiman yayi nisa sosae, amma saboda postings, Karatu ga kuma project yasa banyi wani active perticipation a shirin ba, sede duk abinda akai to zata kirani ta fada min, Haka ta bangaren Yaya Suleiman din duk ankon da muka fitar shi ya siya min.
Biki saura sati uku aka gama hada Lefe, Ummaah tace Nazo na gani kafin akai, koda zanyi recommending a kara wani abun. Yaya Suleiman yazo Ya daukeni shima bayan Ya gama aikinsa. Tunda muka gaisa bamu Kara magana ba, seda Nadiya ta kirashi tana tambayarshi Ko muna tare ta kirani ban dauka ba, to ya bani, bani Yayi mukai magana sannan nai mata sallama. To wannan ya bashi space din yimin magana, itama random talks ne kawai har mukaje gida.
Gidan da mutane sosae, familyn Baban Yaya Suleiman sunzo ganin kaya, dan haka dakina kawai na wuce nayi wanka sannan sun tattafi naje gurin Ummaah,
“Ummaah Sannu da gida”
“Doctor ta karaso, Sannu ya Karatu? “
Ta fada tana min murmushin dake healing zuciyata, akwatin na janyo Ina dubawa muna hira da ita, seda na gama tas sannan nace
“Ummaah, kayannan Sunyi kyau sosae, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi taro lafiya! “
Kaina ta shafa tace
“Amin Autar Ummaah, saura naki kuma ko? “
Murmushi nayi Ina maida kayan cikin trolley, amma karkashin raina Amin nake amsawa, gyara zamanta tayi tace
“Kinga baifi watanni bakwai Ya rage miki Ki kammalla karatunki ba, kiyi kokari ki saurari masu nemanki, nasan Inna Ade tayi Shiru da Maganar ne amma da zarar kin gama zata dawo da zancenĺ”
Kaina na gyada nace
“Inshaaa Allah Ummaah”
Dan abar Maganar auren kawai se na Fara mata labarin Project dina da nakeyi akan CKD (Chronic Kidney Disease) gaba daya ta bani hankalinta, ina mata bayani tana kara min bayanin Wasu abubuwan. A matsayinta na project coordinator a department dinta. A Haka Abba ya dawo daga gona, mukaje tare na mishi Sannu da zuwa sannnan na barta acan ni kuma na tafi gurin Yaya Halifa.
Lokacin biki yazo, dukda ba wani armashi Yayi ba, kasancewar bikin maza ne amma dukda hakan saboda yawan danginmu naji dadin bikin, kusan duk taron a gurin Nadiya nayi shi. Seda aka daura aure sannan na dawo gida, Dan Ummaah tace min Dani zaa dakko Matar Yaya Halifa daga Dutse. A motar Adda Sa’ada muka tafi, munata hira Har mukaje, mutanen suna da kirki, sun karrama mu, muka dakko Sister in-law muka taho da ita kano. Unguwa daya Nadiya da Adda Zannira matar Yaya Halifa, gidan baifi 50miles away ba, haka suke.
STORY CONTINUES BELOW

Rayuwa tana tafiya da dadi da babu dadi, amma dole duk yadda Tazo Haka zakai embracing dinta. A rayuwata na fuskanci kalubale da yawa daga gurin mutane da dama, Harda Wanda ban taba tunanin hakan ba. A Yanzun idan Bakayi aure ba, mutane kawai gani sukeyi Kaine baka so ba, Kaine Baka maida hankali ba. Ya Ilahil alamin! Ya Zakayi? Zakace dole se kayi aure lokacin bai zo ba, A’a aure da mutuwa lokaci ne, idan lokacin baiyi ba, Baka isa kayi ba.
Na kammalla karatuna at a very tender age, gaba daya shekaruna ashirin da uku na karba licence dina under Medical and Dental Council of Nigeria(MDCN, na zama cikakkiyar Medical doctor, ranar da nayi taking Hippocratic oath dina, ranar atttestation nayi farin ciki, nayi murna Kamar zanyi me, na Kalli ilahirin family na da suka zo, ai da kyar bakina ya budu nake karanto oath din. Muna gamawa na fito akai photo session, Yan gidanmu anata rungumeni a Haka muka gama na cire graduation gown din na rataya, cikin yan set dinmu naje mukai hotuna, Dan Wasu ba lallai ku Kara Haduwa dasu ba.
Muna komawa gida, na nufi dakin Inna, tana zaune gefen katuwar katifarta, ko sallama banyi ba na mika mata hannu nace
“Mun kunce ni dake, har na gama makaranta, na zama cikakkiyar Likita amma baki zo tayani murna ba. Na daina kawar dake. “
Tabe Baki tayi tana bina da wani kallo, Wanda bansan me yake nufi ba tace
“To se me Dan banje ba? Da dai aurenki ne da ni ce kan gaba “
Dariya nayi naje na zauna gefenta nace
“Kawata ta kaina, Karki damu ina dawowa daga service zanyi aure da izinin Allah”
Baki a bude tace
“Wani karatun ne kuma, ke Kinci ubanki, so kike se kin tsofe kafin kiyi aure. To babu inda zakije, miji zaki kawo ayi miki aure. “
Dariya na karayi nace
“Inna ba Karatu bane, maida wukar, bautar kasa zanyi. Kuma banda abinki aure ai lokaci ne….”
“Maganarki kenan kullum, aure lokacin ne, ki kalla sa’annin ki dukkansu Sun yi aure, Rayhana ‘Ya’yanta biyu amma ke kinata gantali”
Ta katseni, “Gantali” na maimata, se kawai nayi Murmushi nace
“Kawa kenan, ni bana fada da Kawata bari naje, idan kina son wani abu se kiyi min magana”
Daga Haka na mike gaba daya raina a jagule, saboda abinda Inna tace, Rayhana sa’a ta ce quite sure, amma lokacinda aka rubuta mana kaddara dole kowa road din da zai bi, daban take. Me yasa mutane basu gane komai MUKKADARI NE ba. Da Ummaah na Fara haduwa dake ta Tara mutane se shiga take tana fita, seda nace ta bari idan an kwana biu ayi walimar amma tace gwara tayi rana daya.1
“Na zata kin shirya, mutane na jiranki fa”
Kaina kawai na gyada nace
“Yaznun zanyi”
Juyawa nayi zan tafi daki Ta kwalla min kira na dawo, kallona tayi tace
“Akwai wani abu ne? Naga fuskarki tayi ja “
Taba fuskar nayi sannan na kirkiro Murmushi nace
“A’a Ummaah gajiya nayi, Bari naje”
Saurin Juyawa nayi saboda jin idanuna sun cicciko da kwalla, Se naji tace min
“Today Issa happy day, don’t let anyone destroy it. “
Kaina na gyada na tafi dakin, Adda Zannira ce a kwance da katon cikinta, ta saki fanka, zama nayi gefenta nace
“Adda Zanni, duk gajiyar ce”
Dagowa tayi ta kalleni tace
“Bari dai Adda Asma’u, Babyn ki ya takura min, na kagu Ya fito na Baki abinki. “
Dariya nayi tareda mikewa nace
“Kaji Adda Kamar gaske, Se Kinji zafin labor Kice kin fasa”
Dariya tayi tayi har na shiga wanka, Ina fitowa na shirya cikin wata red Abaya da Adda Habiba ta kawomin as gift, muka fita bayan nayi kwalliya akai ta hotuna. Se Washegari na samu damar bude gifts din da aka kawo min, yawancin duk gifts din daga yan gidanmu ne, Delivery kits, BP app, forceps da sauransu. Naji dadi sosae, kowa na bishi da text din godiya.
Ina kwance a daki sati daya da graduation dina, Inata tunanin Yanzun kuma Ina zaa fada, posting anyishi kuma Anyi posting dina Yobe state. In the next 2 weeks zan tafi. Shigowar Ummaah tasa na mike, kafin nayi magana tace
“Dakko Hijab dinki kizo”
Zan tambayeta lafiya naga ta juyar da kanta hakan yasa na mike na dauki Hijab din na saka muka fito, tunda naga Munyi dakin Inna Ade naji gabana Yayi mugun faduwa, tunda nake da Inna bata taba zuwa gidanmu tayi fin kwana uku ba, amma wannan karan kwananta goma sha biyu bata tafi ba, hakan ya tabbatar min da she’s up to something kuma tabbas akaina ne, Dan ta dauke min wuta, nima bana son case hakan yasa na tattara ta na watsar da ita.
Tana zaune kan katifa, tana murza goro a magogi Tana afawa a baki, nida nafi kowa saninta nasan wata tsiyar zatayi, sallamar da Ummaah tayi yasa ta juyo tana kallona, Nima kallonta nake se ji nayi tace
“To Zuwairiyya (Uwarta kenan!) da kikai tsaye dukana zakiyi? “
Da sauri Abba ya juyo yace min
“Asma’u come and sit here”
Jikina a matukar sanyaye na nufi gefenshi na zauna ina kara tantamar Anya Inna ce, ni tayi addressing da Zuwariyya? Ban gama tunanin hakan ba naji tacr
“Ke Asma’u, dago ki dubeni, idan wayannan mutanen sa’anni Ki ne, ni ba Abokiyar wasarki bace, Dan kin Raina mu zaki ce bazakiyi aure ba…. “
Da sauri na katse ta nace
“Inna yaushe nace bazanyi aure ba”
Abba ne yace
“Kar naji Bakinki! “
Shiru nayi amma a raina Ina ayyana ni Asma’u Fara Yar Shehu, Inna take dagawa murya Haka? Bazan iya tuna last time da ta kirani da Asma’u ba, I can even say she never, kawai cemin take Fara ‘Yar Shehu, Ta gaban goshin ko kuma Kawata. Amma yau Inna Ade ke cemin ita ba tsarata bace, kawai se naji hawaye sun Fara min zarya, kaina ya mugun Sarawa saboda bala’in da take. A karshe tace babu zancen zuwa Yobe!Hannuna nasa na goge fuskata Dan banga dalilin kuka ba, idan tun Yanzun Ina kuka to nan gaba kukan jini zanyi kenan. Nida Ummaah ta sallama, hakan yasa na mike na fito, kitchen na wuce na fara dama custard Dan inason na Fara sabawa da irin wannan abin, Ummaah ce ta biyoni taga ina kokarin Dama custard amma ya tsinke saboda bana cikin nutsuwata. Hannunta tasa ta dafa kafadata tace
“SABR! Asma’u, komai kika ga yana faruwa da bawa da sanin Allah. Kiyi hakuri “
Dan Murmushi nayi nace
“Ummaah babu komai, bari naje daki”
Tare muka fito da ita, daidai fitowar Abba da Inna, bakinta har kumfa yake saboda balai, Jakarta ce a hannun Abba hakan yasa na karasa na karbi Jakar sannan nace
“Inna tafiya zakiyi? “
Kallona tayi sannan tace
“Tafiya zanyi Kawa, yaushe zaki zo? “
Kaina na girgiza nace
“Babu rana,”
Daga Haka muka karasa Mota mukai mata sallama, ta shiga sannan driver ya tada motar se Kwalam. Dukkanmu haka muka tsaya har aka maida gate aka rufe amma babu Wanda ya matsa a gurin, kowannenmu tunanin zantukan Inna ke yawo cikin kanmu, Se can Abba ya juyo Ya kalleni yace
“Asma’u let’s talk”
Wucewa yayi dakinshi, nima na bishi yayinda Ummaah ta tafi daki. Yana zaune a Kan carpet na sameshi, yayi shiru not like my Police Father, duk Yayi Shiru fuskarshi looking pitiful, Se naji na kara takura, naji gaba daya Sauran space din dana bari a zuciyata Wanda Banji haushin Inna ba, baki daya se ya zamana duk ya turnuke ni, har ni kaina haushin Kaina nake ji, at least da nayi auren da ban jawo musu magana ba.
Zama nayi gefenshi nace
“Abba Dan Allah kayi hakuri, Inshaaa Allah zan kawo maka miji na…… “
Se na kasa karasawa saboda wani irin kuka da ya kubce min, kaina na durkushe Inata kuka, inajin yadda zuciyata ke wani irin zafi, na kasa ci gaba da Maganar seda Abba ya dafa kaina yace
“SABR! My Daughter. Ya isa hakan”
Sheshakar a hankali ta dauke min, hawayena na share na bude baki zanyi magana ya girgiza kanshi yace
“Saboda Bakiyi aure ba se ya zama laifinki? Ba laifinki bane, haka Allah Ya kaddara miki, babu Wanda ya tsallake kaddararshi. Koda zaki kara shekara goma a gidannan Bakiyi aure ba, I’ll say nothing. Bake kika hallici Kanki ba, shi daya halliceki yasan tanadin da yayi miki. So Karki kara kuka akan hakan, zakiyi aure amma se lokacin Yayi. And for Yobe, you have me, you’re your fathers daughter Bazan iya hanaki ba. Inna Ade zata sakko Kinji? “
Kaina na gyada ina Dan Murmushi saboda words dinsa are more of Opoid Analgesic (Pain reliever) a take sukai relieving duk wani bakin ciki da zuciyata ke ciki, a take naji wani karfin gwiwa da nutsuwa ya sameni. Bai barni na tafi muka zauna munata hira, gaba daya hirar yana sighting mini examples ne na rayuwa. Most thing da yayi capturing zuciyata shi ne da yace min
“Kinga Asma’u aure ba farilla bane, amma Sunna ce me karfin gaske, a wani gurin saboda Allah yace idan kayi aure tamkar ka cika rabin addininka ne, so kinga akwai falala sosae a aure. Kuma a society dinmu sun daukaka aure sosae da sosae, suna ganin mace is not complete without aure. Eh wani lokacin Haka ne amma kin tuna tarihin Nana Maryam Mahaifiyar Annabi Isah (AS). Batayi aure ba amma a kur’ani Sura guda ce da ita, so kinga zuciya is everything that matters. Ki maida hankalinki akan yadda zaki gyara lahirarki, aure zaizo sede idan lokaci baiyi ba “
Shikenan kuwa na samu lafiya, na wartsake na Fara shirin tafiya Camp. Wani yammaci na tafi gidan Rayhana bayan nayi sallar laasar, ita daya na samu a gidan ta gama aiki ko wanka Batayi ba, Yaran ba sanan sunje gidansu Abdul a sharada. Seda na zauna sannan tace
STORY CONTINUES BELOW

“Gwara da kika zo dama nemanki nake”
Zama nayi nace
“Kiyi wankan mana tukunna se muyi Maganar “
Tashi Tayi ta tafi toilet dan yin wankan, tamkar ana jira kawai se wayarta ta Fara ringing, hannuna na Kai na janyo ta, se naga Nabila cousin yana yawo akan screen din, hakan yasa na dauka amma kafin nayi sallama Se naji ance
“Haba darling, tun dazun nake jiranki amma baki hau whatsappp din ba, balle na samu naga pictures din ko sa rage min wani zafin, kuma nasan Abdul ai ba yanan”
Shiru nayi na kasa fahimtar me ake fada me kuma ake nufi, me yasa nake jin muryar namiji bayan sunan Nabila ne a jiki? Me yasa namiji da ba Abdul ba yake kiranta da darling….
“Baby are you there? Talk to me mana”
Ajiyar zuciya na sauke tareda sauke wayar daga kunnena na kashe gaba daya, zuciyata wasu irin wasiwasi take min, Se contemplating nake a Haka Rayhana ta fito, tayi kyau abinta, kamar asalin rayhanata amma se naji Kamar na rufe ta da duka, gaba daya haushinta Ya lullubeni, is she having an extra marital affairs kenan. Tabanin da tayi yasa na dago tareda mika mata wayarta nace
“Nabila cousin ta… “
Bata bari na karasa ba tace
“Kinyi picking, me kika ji? “
Gaba daya ta gigice hankalinta yayi mugun tashi Wanda hakan ya tabbatar min batada gaskiya, idanuna a kanta nace
“Nayi yace yana jiranki ki tura mishi hoton da zai rage masa zafi, ray…. “
Da sauri ta katseni Tana fadin
“Ba abinda kike tunani bane wallahi Sister, he’s just a colleague, tare mukai service dashi”
“I didn’t ask for all this and yet you are telling me, Rayhana me kikeyi dashi, da aureki da mijinki kike having affairs? Rayhana”
Kusa dani ta dawo tare da riko min hannuna tace
“Asma’u ki rufa min asiri, nima nasan ban kyauta ba, nasan abinda nake Haramun ne amma na rasa yadda zanyi”
Wani kallo nayi mata me cikeda bacin rai, nace
“Bakisan yadda zakiyi ba? Is this an excuse. Ke musulma ce and I’m sure Kinsan hukuncin abinda kike aikatawa”
Kuka ta Fara tana fadin
“Na sani Sis, amma banida option wannan ne kadai abinda nake ganin Zaiyi saving aure na. Idan na kalleki birgeni kike saboda Baki San the hell dake cikin aure ba, baki san bakin cikin dake cikin shi ba, nasha ayyana inama zaai overturning agogo, ya koma baya, I’ll never have chosen Abdul, I regretted that. “
Gaba daya se ta Fara bani tausayi, naji haushinta da nakeji ya Fara wucewa, hannunta na rike nace
“Is ok Rayhana, amma ko me Abdul yayi path din da kika bi bamai bullewa bace, halaka zakiyi, kinga kenan kin tashi with nothing, Babu duniya babu lahira even an ounce of pride babu.”
Hawayenta ta share tace min
“Kinji dadi Bakiyi aure ba, Nazo zan fada miki wannan abin. Tun muna secondary nake son aure, Kinsan Dalili? Saboda I’m thirsty, I want someone to quench that thirst for me, Inada strong sexual desire, zan iya ce miki dalilin aurena kenan. Abinda na fahimta about aure shi ne, Backbone na aure is sex, komai zaayi miki a gidanku amma babu me iya miki wannan se Kinyi aure, the new thing about aure shi ne sex, what about you are deprived of that? Ya kike ganin zaayi kenan? I was innocent and illiterate about it, Abdul tasted that thing to me Se dana saba nasan dadinshi sannan ya nuna he’s not in need, se ya koma a wata, we will have affair sau daya, Ina zan iya, nayi korafin, nayi Maganar, tun ina kunya Har na fito Asma’u nayi mishi barobaro amma yaki fahimta. Aurena zan kashe? Ina ganin Kamar dalilin yayi kadan Yasa nayi hakan, shiyasa na komawa Jabir dina. Nasha zuwa da niyyar fadawa Mama amma se tace, what matters shi ne na rike sirrina, kada na tonawa mijina asiri, kuma no matter what I’ve to save that marriage Dan shi kadai ne Gata na, bata taba saurara ta ba. Kece kadai kika bani hearing ears, Nagode “
Ni Kaina seda hawaye ya zubo min da ta gama fada, hannunta na kama nace
“I’m sorry, amma dukda haka baki nemawa kanki solution ba, me yasa a aure akai Waliyyi, run to him, tell him ga matsalarki. Kina ganin sex deprivation Yayi kadan ya kashe aure? Kinyi kuskure Dan a karshe zakiyi dana sani marar amfani, Rayhana quit all this games and tell them, ki fada musu matsalarki, kiyi istigfari, kiyi Tuba, tuba na gaske Wanda bazaki koma laifinki ba, Allah kadai zai daidaita rayuwar aurenki. Kiyi hakuri “
Tunda na dawo gida bayan na baro gidan Rayhana, na kasa nutsuwa, na rasa tunanin me zanyi. Dama idan Kai auren bashi kadai bane karshen matsala, who will ever think Rayhana da Abdul will end up in such a mess?YOBE, POTISKUM.
Abba da Ummaah, su suka rakoni har Potiskum inda anan NYSC orientation camp din yake, bansan yadda Abba ya shawo kan Inna Ade ba, amma nasan ya cika min alkawarin da yayi min akan Zanje Camp, gashi alkawari Ya cika. Tare dasu mukaje akai clearing dina da dukkan Wasu formalities sannan kuma mukai sallama suka juya.
Camp life was hectic amma it’s something memorable that happens once a rayuwar mutum. Sati biyu da nayi na rame ga lokacin ana Rana, nayi baki, gani Inada Dan wahalar sabawa da mutane, se ya zamana mutum daya muka saba da ita wata A’isha Kyaftun yar Gumel ce ta Jigawa State. Ita dinma dalili ne ya kawo hakan. Har nayi sati bana shiga harkar kowa, roommates dina dukkansu Christians ne so kullum sede mu gaisa kowa ya kama gabanshi.
Ranar Saturday mun kammalla dukkan abinda Zamui naje wani eatery zanci Abinci, Nazo entrance din naji wani yana fadin
“Kyaftun! Kyaftun!! “
Ko Juyawa banyi ba, na cigaba da tafiya ta amma se yazo yasha gabana yana fadin
“Amma Kinsan tun yaushe nake jiranki? Kinzo kuma kin wani bata rai kin wuce”
Juyowa nayi na kalleshi, shima kallona yake, dogo ne sosae Dan duk tsayina se na ganni dwarf a gabanshi, fuskarshi doguwa ce kuma komai dake cikinta Manya ne, ga uban saje daya aje, Wanda zaisa ayi mistaken dinsa a matsayin wani Babban mutum. Gaba daya analysis din nayi shi cikin nanosecond ne.
“May be you are talking to the wrong person”
Na fada masa Ina kokarin Juyawa na shiga ciki amma, Se naji wata murya irin tawa tace
“Zayyan! Kana ta jirana Ko? “
Juyawa nayi na Kalli me Maganar, seda gabana ya fadi saboda yadda fuskata take a Kan tata, baki bude nake Binta da kallo haka itama take ta kallona, se shi Zayyan din ne yace
“Allahu Akbar! Set of twins from different uterus. “
Kallonshi mukai a tare sannan ta miko min hannunta, take na zura nawa, instead mu shiga cikin Eatery din se kawai muka nufi wani karkashin bishiya muka zauna, Zayyan Ya tafi siyo mana juice. Hannunta ta bani tace
“A’isha Kyaftun Ismail, daga Gumel, Jigawa state amma a kano muke”
Kaina na gyada nace
“Nice to meet you, Sunana Asma’u Shahada Kwalam, yar Jigawa ce ni”
Murmushi ta karayi daidai dawowar Zayyan, hannunsa da Fanta biyu, coke daya, ya aje sannan ya zauna yana fadin
“Ban taba ganin Kama irin wannan ba, Anya ku din ba Twins bane aka samu akasi kuka rabu”
Dariya nayi, Kyaftun tace
“Ka Faye surutu matsalata da kai”
Kaina na girgiza nace
“Ni Kaina nayi mamakin ganinki, ban taba tunanin akwai irin mutanen da Baka hada komai dasu ba amma kana kama dasu Har haka”
Kanta ta gyada tace
“Seda na tsorata fa Asma’u, I never knew such is real! “
Daga Haka mukai ta hira Har na manta cewa Yunwa nakeji. Daga wannan ranar muka zama kawaye da ita, bacci kadai ne ke rabamu da ita, a gidanmu kowa yasan labarin Kyaftun haka nan nima labarina yaje gidansu. Lokacinda muka fito a camp, munata shiri nace
“Kyaftun kada Ki Kira kowa, zaa zo daga gida a daukemu “
Aje Jersey din hannunta tayi ta maida hankalinta kaina tace
“To, har Se anzo daukarmu Twin?”
Gyada Kaina nayi nace
“Eh mana, Bazan iya komawa da kaina ba ai”
STORY CONTINUES BELOW

Dariya tayi tace
“Small Baby, Nan da Kano ai ba big deal bane. Zamubi commercial car ni da kaina zan fadawa Ummaah haka”
Bata jira abinda zance ba ta kira Ummaah, har sun saba dan Twin batada duhun kai ko kadan , she’s a wise person sosae.
Haka na hakura Washegari muka tafi Tasha Inata jina a takure, Twin se dariya takeyi min tana tsokanata Fathers girl. Seda mukaje Kiyawa sannan Wasu passengers suka sauka, a Dutse aka Kara cika motar. Tunda muka dauki hanya na kwantar da kaina a kafadar Twin na Fara Bacci seda muka shigo Kano sannan ne ta tasheni, wata Ajiyar zuciya na sauke bayan na hango Birni, home sweet home na ayyana cikin raina. Muna sauka muka harhada kayanmu guri guda, Kyaftun taje samo mana Napep. Sallama naji a gefena hakan yasa na juya, tareda amsawa amma a ciki ciki, bakina daya motsa kawai ne zai fada maka nayi magana.
“Sunana Salis, ke fa? “
Kallonshi nayi nace
“Bashida amfani hakan”
Ina fadar Haka na tsugunna ina gyara Trolley Twin. Maimakon ya tafi se ya gyara tsayuwarshi yana fadin
“Tunda ni na tambaya ina ganin it’s important, so let me know “
Dauke kaina nayi, zuciyata tana fada min I shouldn’t miss the chance, wannan shi ne lokacinda ya kamata kiyi saurayi, ban gama tunanin ba balle nasan hukuncin da zan yanke Twin ta dawo, kawai Salis Ya juya gurinta tareda yi mata bayanin abinda ya faru, take ta karanto masa home address dinmu, number ta da sunana, Dama tun acan Potiskum ta fahimci banda saurayi, tayi mitar tareda fadin ita ta Yaya zata iya rayuwa babu opposite gender, ai masifa ne kayi sati daya bakaji muryar Wanda yake kallonka as something special ba. Daga Haka muka wuce shi ya bawa me Napep din kudin sannan Twin tayi masa godiya, tunda muka dauki hanya nake mitar ta zubar mana da mutunci, ta bari an biya abinda ya kamata mu biya, Tsaki kawai tayi tace is not like ya siye mune, is just a token of appreciation na bashi access da abinda yake so. Twin kenan duk ta inda na fito tasan yadda zata bullo min, ban taba wining akanta ba, so wannan karan bakina nayi bam dashi.
Gida muka fara zuwa Dan Dama alkawarin da tayi min kenan. kowa seda ya Jinjina halittar Allah. Seda muka ci Abinci muka huta sannan na tafi nida Adda Meeyna rakata, har gidansu mukaje, iyayenta masu kirki sede rayuwar gidan is far different from ours, zaka iya saka su a low social class amma kuma irin contented mutane ne, a zamana da ita bazaka tantance wani class suke ba. Allah yasa Nursing tayi abinta, tana da guarantee aiki.
Salis Mutumin Ingawa ne ta Katsina state, ko cikin muryarshi zaka dinga jin accent dinshi na yan can ne. Architecture ne so yana aiki da wani construction company a can Katsina. A yadda yayi min bayanin kanshi Bashida aure, amma yana kokarin yi. Hakan yasa na Fara sakin jikina dashi , Mussaman da yake na gaji da zama ni daya, wannan loneliness din ya isheni. Satina daya a gida na tafi Kwalam gaida Inna saboda ni Bazan iya fushi da ita ba. Kafin naje seda na biya gidansu Twin na gaida Innarta sannan ta rakani Tasha na wuce, nima na Fara yin abu da kaina. Se yamma na isa Kwalam, Ina shiga gidan tana zaune dokin kofa tayi Baki, bata lura Dani ba Har seda na karaso ciki sannan tace
“A’a Likita Bokan turai! “
Da murmushina na karasa gurin ina gaida mutane sannan na zauna Kan karamar kujerar da tasa aka kawo min na zauna muka gaisa sannan na wuce dakinta, Ina shiga Salis yana kirana, rabona da muyi waya dashi tun kwana biu da suka wuce, he’s not a frequent caller Nima kuma idan ya kirani na dauka idan bai kira ba yasha zamansa saboda bana son repeating mistakes dn da nayi a baya.
“Ran gimbiya Asma’u ya dade! “
Dan Murmushi nayi nace
“Tare da naka “
“Yanzun na shigo Kano Se nace bari dai Nazo naga Asma’u”
“Ayya! Nagode, amma ni kuma bana gari naje Kwalam”
Daga Haka baice zai zo ba, ya tsaya mukai random talks dashi, har Inna ta shigo jin yadda nake ta Murmushi tace
“To Siriki yazo kenan? “
Ban kulata ba na cigaba da maganata, Ashe yaji muryarta, muna gamawa yace na Kai mata, ni kuwa banyi musu ba na mika mata sannan nasa kaina na fita a dakin. Koda ta gama batace min komai ba Haka zalika Nima.
Washegari tun sassafe naje nayi yan gaishe gaishe sannan na dawo na kwanta, wajen daya nayi sallah nayi wanka sannan na shirya, tunda na tashi Inna take ta kaiwa da kawowa, seda ta shigo nace
“Inna me kikeyi ne”
Murmushi tayimin tace
“Bako zanyi”
Kaina na gyada na cigaba da kallon wani Korean drama Romantic Doctor cikin system dita. Se wajen Karfe biyu naji sallamar Salis, da farko ban yadda ba gani nake kawai hallucinations ne, amma Se naji Inna sunata gaisawa, kashe kallon nayi na sakko daga gadon, hijab na zura na fito, shi dinne kuwa a zaune shida wani ina tunanin friend dinsa ne. Mamaki sosae Ya cikani, sallama nayi hakan yasa suka dago suna kallona, Salis se Murmushi yake min shida Inna, zama nayi gefen Inna na gaishesu sannan nace
“Haka zuwa babu sanarwa”
Kafin ya bani amsa Inna Ade tace
“Naga ana rowarshi shiyasa nace yazo na ganshi”
Kaina na gyada nace
“Naga alama kuwa! “
Mikewa nayi zan koma ciki, Inna tace
“Fara yar shehu ina zakije kuma? Kizo kui hira mana”
Kaina na girgiza nace
“A’a ai wannan ba zuwana bane, zuwanki ne se kui hirar “
Abokinne Yayi dariya yace
“Alama ta nuna Doctor kishi take, Inna ki koma ciki kada kisa ayimana fushi”
Harara ta Inna tayi sannan tace
“Ni fita zanyi ma, ki dawo kui hirar”
Juyawa nayi na koma muka zauna munata hira, har suka ci Abinci sunata hirar kyan halayen Inna, Nidai a raina Murmushi kawai nakeyi, Dan Inna ba abar yabo bace.Seda Inna ta dawo wajen biyar na yamma, sannan suka Fara shirin tafiya, ta shiga daki aka hado su kuka, daddawa, yakuwa da Sauran abubuwan da ake Baka na karamci a kauye Dan su kaiwa iyayensu. Nidai Ikon Allah kawai nake kallo Dan ko mu mukazo se Inna ta gadama Sannnan zata bayar, rabon da tayi mana tarbar girma Tun kafin a fara rikicin aurena.+
Suma su Salis sunji dadi sosae, da zai tafi ya ciro sababbin 100 notes bandir daya ya aje mata, wata guda da Inna ta saki seda na firgita, sukuwa se dariya suke mata, tana ta godiya kamar zatayi kuka, Tana fadin Ashe alkhairi ne zuwa Yobe da tuni ta datse min hakan. Nidai Ko uffan ban tofa ba Illa kallon Inna da nake, na Kalli kudin sannan na Kalli Salis din. Kallona Yayi yace
“Tunda Kema gobe zaki tafi, ai da shiryawa kikai muka tafi duka”
Kafin nayi magana Inna tace
“Hakane kuwa fa, Maza Kawata hado kayanki Ku tafi”
Ikon Allah! Na fada a raina sannan na girgiza Kai nace
“Nagode Kuje kawai, zan taho gobe Inshaaa Allah”
“Idan Kin zauna me zakiyi? “
Inji Inna tana tsatsareni da ido, da mamaki na kalleta sannan nace
“Banje nayiwa Hannatu barka fa, kuma… “
Katseni tayi da fadin
“Auren Hafsa ya kusa, idan kinzo Nasaka a rakaki”
Shiru nayi na juya Dan hada kayana, Inaji tace musu su zauna Yanzun zan fito, Dama ban barbaza kaya ba balle nasha wuyar hadawa, kafin mintuna biyar na gama, har nayi zipping sannan Inna ta shigo tana fadin
“Ki hanzarta mana suna jiranki! “
Dagowa nayi nace
“Inna, me yasa kike Haka ne Dan Allah, Nifa Bance inason gayen nan ba, Meye zaki saka yazo sannan har ya Baki kudi Ki karba? “
Bakinta a bude irin mamaki dinnan tace
“To Sannu Uwar Ubana Hajara, ni nasan bakin halinki zaisa Ki rasa miji mana. “
Banza nayi mata na Fara hada handbag dita sannan nace
“Duk gorin da zakiyi mini akan aure indai lokaci baiyi ba, ba zanyi shi ba. “
Ai se ta Fara sababi na fada mata magana, kuma zatazo har Kano Se na maimaita Maganar a gaban Ubana Shahada, Nidai Ficewa nayi, Salis Ya karbi Trolley nayiwa matan gidan sallama muka dauki hanya. Bana son hayaniya shiyasa kaina ya ringa ciwo, ga abokin Salis din azabar surutu ne dashi, Se jana yake da magana, shikam Salis yasan halina hakan yasa yace ya rabu Dani. A Haka muka lallaba muka isa Kano, har gida suka kaini nayi musu godiya sannan na wuce.
Da mamaki Ummaah tace
“Ya kika dawo Yau? Ko wani abinne? “
Kaina na girgiza nace
“A’a Ummaah an samu masu zuwa Kano ne, se Inna tace yafi sauki na biyosu”
Se naga ta saki Ajiyar zuciya, ruwa nasha Wanda Ilham din Adda ta tareni dashi, ita ta kaimin kayana Har daki sannan nayi wanka. Can dare wajen 10pm Nazo zan kwanta se naji Ya kamata ace naji yadda su Salis sukaje ko ba komai ai Danni sukaje gurin Inna. Wannan shi ne karo na farko a karan Kaina na kira Salis, willingly.
“Yau wacce rana Doctor ta kirani da kanta? “
Shi ne abinda ya Fara fada kafin ma Ya amsa min sallamar da nayi, Murmushi nayi nace
“Na kira naji yadda kukaje, Nagode sosae da sosae. Allah Ya saka da alkhairi”
“Ni ne da godiya Doctor, Ayimin godiya gurin Inna sosae”
“Inshaaa Allah”
Se kuma mukai Shiru kowanne da tunanin da yake a ransa, Nidai nasan ina tunanin ruwan da ya ballo min ne, shi ne dai bansan yaya ba.
“Har Se yaushe zaki dauka, kafin Ki bani Dama? At least Asma’u kowanne relationship da kika gani, Baa Fara so farat daya, we’ve to rub our minds together, muga differences dinmu da yadda zamuyi overcoming dinsu. Amma ke ya kike gani”
Tashi nayi na zauna sannan nace
“Hakane abinda ka fada, ka ganni Yanzun duk family na aure suke so suga nayi, so idan Kasan Baka shirya ba, Ina ganin tarrayata da kai batada amfani! “
“C’mon Asma’u, kina tunanin yaudararki Nazo yi? Haba mana! I’m too good for that Kingane? Amma Se nake ganin auren zaifi dacewa bayan kin kammalla service dinki, kafin nan nima na shirya ko?”
Ban kawo komai ba na amince a ganina hakan ma abune me kyau, at least kafin nan nima na shirya sosae. Da haka na kara sakin jikina dashi da kuma zugar da Kyaftun take min, ga pressure Inna from other side.
Duk haduwarmu dashi yawancin gidan Adda Sa’ada muke Haduwa dashi, se lokacin da yazo Ya gaida Ummaah da Abba yayiwa Abba bayanin plan dinsa na se na gama Service kafin zai turo, Abba ya amince dan shima abinda yake so kenan. Abba ya kirani ya tambayeni yadda nake jin Salis, na amince? nace na amince, shikenan ya bashi damar soyayya Dani. Yayi seeking consent dina. Abba yasa akai bincike sosae akanshi kuma Alhamdulillah he worth a bashi aure.
“Ke Wai se yaushe zakiyi aure ne, Walahi kiyi aure shi ne rufin asirin mace”
Shine abinda na tsana a duniya, wannan tambayar, ko ya muke da mutum Se naji raina Ya baci, Nadiya ce na rasa abinda yake damunta, she always challenge me akan naki aure, naki tsayawa na bawa mutane chance, na zauna bokon da Bashida amfani.
“Keda yaushe kikai auren har da zaki dinga zakalkalewar wani yayi auren? Yaushe muka gama yanmatanci tare dake? “
Da mamaki sosae ta kalleni tace
“To Asma’u Meye abin fada? Is just an advice”
“Bana bukata Kinji? Ke karfinki ya Baki miji? It’s a matter of time, da kikace rufin asiri shi ne aure, asirina ai ba a bude kika ganshi ba “
Nima nasan babu dadi na gaya mata magana amma mutane Haka suke, yanmatan Yanzun da Sunyi aure se su zama tamkar Wasu preachers ko kuma scholars, su ta damunka akan kayi aure, as if badasu kuka gama zama ba. Haka dai muka rabu nida Nadiya babu dadi, Tama ta fushi Nikam nayi haka Dan gobe kada ta kara hakan.
General hospital Potiskum anan akai posting dina zanyi service, Itakuma Kyaftun tana Damaturu anan zatayi, by far mun rabu da juna but we’re still in touch da ita. Asibitin suka bani accommodation da abinda ya kamata, dama a shirye naje so ban koma yin wani abu ba. Kwana na biyu Salis Ya dameni akan zaizo nace mishi ya bari naga yanayin Garin tukunna. Seda nayi sati biyu sannan yazo. Ranar Saturday ne banida call, so ina dakina ina hutawa yazo. Shida Friend dinsa suka zo, Se naji hankalina ya kwanta na kaisu dakin. Suka ci Abinci sukai sallah sannan muka fita Verrender muka zauna ni dashi
“Asma’u Anya kina sona kuwa? “
Dagowa nayi na kalleshi nace
“Me ka gani ne? “
“Baki kula dani fa, Ki kalla naje gurin Abba, Ummaah ta sanni, Inna ma haka amma still kinki sakin jikinki da kyau. “
Dan Murmushi nayi nace
“Kai kake ganin hakan, amma ba haka bane”
Ya jima yana kallona Kamar yana son karantar wani abu, hakan yasa na takura nayi kasa idona, deep down ina jinshi a raina, but Tsoro nakeji, kuma na rasa tsoron Menene.
*Ramadan is fast coming our way! Let’s all have fate and even the slightest or glimpse of hope, that this plaque (Pandemic Covid 19) will be curbed before Ramadan. Let’s all raise hands and pray, don’t let anyone destroy your Imaan. It sure is a plaque, that’s bound to take away souls that are destined to die! You can’t do anything but take precautionary measures, make your Imaan still. Inshaaa Allah everything will be over! Aminnnn! When are we going for our Ramadan break? You all know we can’t take the story down before Ramadan.*