FARA YAR SHEHU COMPLETE

 FARA YAR SHEHU COMPLETE

Sunana Asma’u Shahada, Mahaifina Dan sanda ne Wanda ya taka Har matsayin CP that’s commissioner of police, sede yayi retire a halin Yanzun. Amma dukda haka baya zama saboda shi mutum ne me kazar kazar, he’s a patriotic citizen, never believe in zaman banza. yana da gonaki inda shi ne invest dinsa, to kusan kullum se yaje, hakan yasa koda yayi yayi retire amma bai huta ba

.

Asalinmu Yan Taura ne ta Jigawa, cikin garin Kwalam, kakanni  na a Kwalam suke. Malam Aminu shi ne kakana da ya haifi Mahaifina, manomi ne sosae, if I can say Abba anan yayi gadon noma, Don idan kaje kofar kudu kace gidan Sarkin Noma, don’t be amaze amma kowa ya sanshi. Inna Ade ita ce mahaifiyar Abba, sunanta Sa’adatu, so se aka cire karshen Sa’ade ake kiranta Ade. Nasha ayyanawa da kuma tunanin yadda akai har zaman Alhaji da Inna Ade Yayi wannan doruwar. Alhaji mutum ne me hakuri da kauda kai, bazaka taba fahimtar fadanshi Ko Maganar shi ba cuz the tone is always same. Inna Ade kam! Jarabar duniya, matar tana da fada na bugawa a Jarida, so far, zan iya cewa akwai possibility din Tasha ruwan Atafi da ake fada saboda sunyi zaman hadejia. Lol. Amma duk wannan hayaniyar tata, bana gani saboda muna mugun good time da ita, Tana sona kuma tana fito na fito da duk Wanda ya nemi takurawa rayuwata, koda Abba ne ko Ummaah, Yanzu Yanzu zata wanke su tas tas, su da suka haifeni kenan balle kuma yan uwana da ba ganinsu take da gashin Kai ba, wannan ai sede dan kansu su bar mata gurin. I knew her Best side so far.+

‘Ya’yansu takwas, Hajiya Uwani ita ce babbar yayarsu Abba, Tana aure a Majia ta Taura garinsu Nanaye. Tana da Yara wajen goma, kuma baki daya matar photocopy din Inna Ade ce plus Wasu mugayen halayenta Wanda basuda asali bare kuma tushe. Daga ita se Abba shi ne Shahada, kuma Mahaifina, na yadda partially da mutane su kace ana inheriting Uwar miji a gurin haihuwa, yeah akanmu Hakane. Abba shi daya Shi ne namiji, surrounded by sisters, haka nan Ummaah, kuma haka muke a gurinta.

Daga Abba se Umma Falmata, Tana can Adamawa anan take aure, dake Inna Ade asalinta daga can take. Asalin bafullatana ce, bansan yadda akai ta aura Alhaji ba, har ya dakko ta tun daga Uwa duniya Har Kwalam. Mabiyar ta Anty Hauwa ce, boss kenan, se Anty Shamsiyya , Anty Mero sai Anty Rakiya da Adda Ummiey wadda ita ce autarsu, kuma a gidanmu ta tashi, Dan Saar Adda Habiba ce, Tare akai musu aure abinsu.

Sauda Ummaah bakanuwa ce ‘yar koki, mahaifanta dukkansu yan nan cikin kanon ne. Ummaah ita kadai ce mace a gidansu, dukkan Yan uwanta maza ne, amma Dayake Allah shi yake tsarinsa bakwai daga cikinmu Duka mata ne se namiji daya tal. Babbar yayarmu Adda, Tana aure anan Kano, wani yaron Abba ta aura, me bi mata Yaya Halifa, sunan Alhajin Kwalam ne dashi shiyasa sunanshi yake a boye. Shidai baiyi aure ba se Karatu kamar zai cinye Boko, Yayi degree, Yayi Msc, banda PgD da yayi, da courses kanana kanana. Yanzun Haka PhD yakeyi. Duk gidanmu ni ce nafi shiri dashi saboda Ina son Karatu, I find joy and happiness in studying. Wannan yasa na zama Kamar kawarshi, I enjoyed been with him. Adda Sa’ada ita ce takwarar Inna Ade, as we all know a gida idan kana da takwara you seems to be in the most goodest relationship da ita, wannan karya ne when it comes to Inna Ade and Adda Sa’ada basu shiri Ko na mintina daya, hardly ka gansu tare. Tana aure a Niger state, Adda Habiba Saar Adda Ummiey ita ce a dutse, se Adda Meeyna, Adda Salma da Adda Maryam se ni kuma auta Kare nono as they always call me.

1995 aka haifeni, Ummaah da Inna Ade, sun bani labarin ranar da zaa haifeni, ranar kawar Inna Ade wadda ita ce Asma’u. Kawarta ce sosae, tun suna Yanmata Har seda akai musu aure. Kunsan aikin police federal aiki ne, so transfer Ko da yaushe ana cikinta. Amma lokacinda Ummaah ta samu cikina, shi ne lokacin da Abba yake ASP a kano, I was lucky baayi tafiye tafiya da cikina ba.

Ranar Alhamis ce, dake Inna Ade, in har Ummaah Nada ciki to duk sati se Tazo, Har Se Ummaah ta haihu kafin zata tattara ta tafi, wannan zaman an dinga balai da ita, musamman itada Adda Sa’ada, wani lokacin Abba ke raba fadan. Ile kuwa ranar sun gama yinta, Adda Sa’ada tayi girki Inna Ade tace Allah ya kasheta, ita tuwo zataci, Adda tace ita kuwa kitchen ta gama shigarshi a wannan ranar sede Inna tayi da kanta.

“Saude Saude! Ki fito Ki raba Dani da wannan shedaniyar yar taki”

Ummaah na daki, ita kadai tasan halinda take ciki, ta jiyo kiran da Inna Ade ke yi mata, Ta sani Ko Baa fada ba, Adda Sa’ada ce kawai Inna zata dinga ihu akanta. Gaba daya ta jike da gumi sharkaf, ta fito da kyar, daidai karasowar Inna Ade, Tana mitar rashin amsata da Ummaah tayi, kicibis sukai, abinka da Manya tana kallon fuskar Ummaah, tasan nakuda take, babu bata lokaci ta saka wani cousin din Abba, kawu balarabe wanda ke zaune gidanmu Ya dakko Mota suka wuce asibiti.

Ana karbar ta, Inna ta saka a sanar da Abba, Allah Ya taimaka ya tashi a aiki, hakan yasa ya nufo asibitin, Babu jimawa aka fito Dani cikin zani an haifeni, Inna Ade tace min kwatakwata da karbata baifi mintina uku ba, sakon rasuwar kawarta Asma’u ya iske ta. Ta shiga Tashin hankali marar misaltuwa, Inna Ade tayi ta kuka Abba yana lallashinta. Duk yadda akai ta hakura amma taki, se fadin

“Shahada, idan zaka saka a kaini Jimeta ka saka, idan baka sawa ka barni na tafi! “

Babu yadda ya iya haka yasa a ranar aka tafi da ita Jimeta. Seda akai kwana uku sannan ta dawo. Tana dawowa kuwa tace lallai sunan aminiyarta Zaa maida min. Ranar da na cika kwanaki bakwai aka rada min sunan Asma’u, Inna Ade tana cemin FARA ‘YAR SHEHU!

Na tabbatar once a rayuwar Abba da Ummaah, Sunyi regretting saka min wannan sunan, ba Dan komai ba se Dan Inna Ade. Duk weekend din duniya tana kano Tare dani, as I heard, bakina da sunanta Ya Fara budewa, sunanta na Fara kira.

Nayi shekaru biyu aka bawa Abba commissioner of police, sannan aka masa transfer zuwa Taraba state, inda anan ne Zaiyi commissioner din. Aka kammalla dukkan shirin tafiya, amma Inna Ade tayi tsalle tace babu me tafiya Dani, a gurinta zan zauna. Inna Ade yar daru ce ta gaske, waye Zaiyi musu Abba ko Ummaah? Babu. Haka aka tattara ta tafi Dani Kwalam su kuma suka wuce Taraba abinsu.

Da wannan rayuwar na tashi, babu Wanda na sani se Innata, a Haka Har na Fara Wayo nakai shekara hudu, duk lokacinda Abba yazo da niyyar tafiya Dani Dan Ya sani a makaranta, Se Inna ta Fara kuka,

“Shahada akan yarka zaka nuna min iyakata? “

Ummaah ta lallabashi Badan ransu yaso ba, suka kyaleni a gurinta, amma seda aka kaini central primary school dinsu. Ni mutum ce me wasa da kiriniya, I pay attention to nothing, so ko da mukai exams, it was beyond comment, ni na dakko ajin. Abba Kamar Zaiyi kuka Dan takaici, Yaya Halifa kam Kirirkiri Ya fito sukai ba dadi shida Inna Ade, bata kulashi ba saboda Tana yawan cewa, ita tasan darajar miji, so shi yana cin darajar sunanshi Aminu.

A Haka rayuwa ta cigaba da gungurawa, kullum hankalin iyayena yana kaina, as for me duk tunanina Inna ta haifeni, su ina daukarsu kawai yan uwanmu, Kamar yadda naga Sauran na zuwa. Seda nayi shekara bakwai sannan nayi wata rashin lafiya wadda seda muka kwanta a Aminu Kano. Munfi wata sannan na samu sauki, wannan shi ne asalin dawowata gidanmu, Inna ta hakura a cewarta kada mayu su lashe mata kurwata. God so kind!

Surprised? Ooooo

Ayshatuuu

Bayan dawowata abinda aka Fara kokarin yimin, shi ne makaranta. Dayake lokacin Ummaah ta gaji da binshi, se sukai settling baki daya a kano, shi kuma Yana zuwa ya koma. Adda Maryam kadai ke primary lokacin, itama kuma Tana Basic 5, a excel college. Spring aka kaini duk dan na dan farfado daga asarar da akai, Basic 1 aka kaini, amma matsalar ko two letter words ban iya ba. Bazan taba manta wannan abin ba.1

Ranar da aka Fara kaini school din, Inata murna abuna, saboda uniform din kawai birgeni yake, ga lunch box dina, Ummaah ta shake shi da chips, ga Caprisonne. Oolala! Yaya Halifa ne ya Fara kaini, seda ya rakani Har class sannan Yayi min kashedi, tareda fadawa uncle din ya saka min ido sosae, Aikuwa Ya saka, dan na amshi wuya hannun bawan Allah nan.

Abinda ya Fara sakawa na karaya nafi kowa girma a ajin, saboda Inada Girman jiki, ga yawanci duk sun iya turanci ni kuwa daga come and go babu abinda na sani, gashi Baa vernacular a school din. Se ya zamana idan na shiga har a tashi bana magana, saboda na taba gwada surutu da Hausa, aka fadawa uncle Ya zaneni. Tun daga lokacin na daddara bana taba gigin yin surutu.+

Idan na dawo gida bayan an tashi lesson, islamiyya ce zamu tafi nida su Adda, bazamu dawo ba se 5:30. Da anyi Sallar Maghrib, Yaya Halifa zaizo da Belt in dakko books dina, ina kuka Haka Zamui homework dina sannan ya koya min sabon abu, wannan belt din na gefe, bawai dukana Zaiyi ba amma ita ta barazana ce. Karshen dukan shi ne rankwashi. Duk yadda nake son kallo musamman cartoon banayi, ana gamawa zanyi Sallar ishai na kwanta. Cikin sati biyu gaba daya na fita a hayyacina saboda ban saba irin wannan rayuwar ba. Rayuwar Kwalam babu sawa bare takurawa, kullum se nayi kukan zan koma gurin Inna amma babu me kulani, se idan Boss din gidan tana nan Adda Salma ta bubbuge ni, so shirina da ita kadan ne.

Ana haka aka kawo wani new student, Emma a class dinmu, Shi duk yafi mu, gashi azzalumi babu hasken musulinci tattare da yaron nan, tunda yazo shikenan Sauran walwalar da nake da ita ta tafi. Ya rigada ya gane ban iya turanci ba kuma ko yayi min abu I can’t express myself hakan yasa yake cin zalina shida gang dinsa. Ranar duka gida aka makara, so ko breakfast bamuyi ba haka muka taho se daga baya Ummaah ta aiko driver ya kawo min Abinci, Inata murna saboda azabar yunwar da nake ji, amma ina karbowa Emma da mutanenshi suka karbe abincin, Ina kallo suka cinye, Aikuwa Na dinga kuka na tafi gurin uncle, it was embarrassing. Ina zuwa yace min

“Asma’u what happened? “

Gaba daya na diririce saboda bazan iya cewa “He ate my food” ba haka na gaji da tsayuwa na koma na zauna. Shikenan suka gane lagona Har dukana suke, gashi ni kuma a gida haushin kowa nakeji, ina ganin duk su suka jawo min, da ace Ina Kwalam waye zaimin haka? Ai babu shi idanba so yake yaga kaddamarwar Inna Ade ba.

Da sassafe Adda Meeyna na shirya ni, Inata kuka, kallona tayi tace

“Menene Wai? Yau kwana uku kenan kullum se Kinyi kuka. Makarantar ce baki so? “

Kaina na gyada, Wasu hawayen na sakko min nace

“Ni bazanje ba Adda zazzabi nake”

Wuyana ta taba sannan tayi dariya tace

“Yar gidan Inna, babu wani zazzabi fa, kede kawai kin zama yar baci”

Muna haka Adda Sa’ada, service take anan Kano, kuma mijinta ya tafi wani official assignment a Urk, ta shigo tana fadin

“To! Autar Ummaah me ya faru? “

Nan Adda Meeyna ta fada mata yadda mukai da ita. At this stage, iyaye ya kamata ku lura da wani abu, bullying yafi karkata a primary school, sosae Wanda suka fi karfinsu suke zaluntar su. Shiyasa yaro zai dinga kukan makaranta, saboda Wasu lokutan Yaran Zaa iya threatening dinsu su kasa fada, ya kamata kowacce Uwa ta zama alert.2

Shiru Adda Sa’ada tayi sannan ta kama hannuna muka fito, Ummaah ta fito dauke da bag pack dita, ganin fuskata kacekace da hawaye yasa taja ta tsaya, fuskarta da damuwa tace

STORY CONTINUES BELOW

“Uwata” Kamar yadda take kiran Adda Sa’ada, da yake Baa boye mata sunanta, “Me Ya sameta? “

Inajin tayi wannan tambayar na kara kwabe fuska, Inata kuka, Inaji Adda Sa’ada nayi mata bayani, dake Ummaah classroom teacher ce, take ta fahimci abinda yake faruwa. A ranar tare dukka mukaje school akai complain, haka a gaban class aka Zane Emma, shikenan na samu sauki, kuma na dage na Fara turanci, idan nayi ai tayumin dariya amma a hankali da taimakon family na, na samu nake iya hada sentence.

Har term din ya kare babu Inna Ade babu dalilinta, haka muma bamu samu Munje Kwalam ba, in banda Ummaah da Abba, nayi mitar nayi kukan har na hakura abuna. Ranar da akai Hutu na dawo Inata murna Dan zan dan huta at least, Tundaga tsakar gida nake jiyo muryar Inna Ade, matar is very lousy, inhar tana guri some miles away zaka dinga jiyo muryarta, bansan lokacinda na sake lunch box dina da school bag ba nayi parlor a guje ina fadin

“Inna Ade! “

Kanta na fada nayi mata wata runguma me karfi, itama rungumeni tayi tana shafa jikina tareda fadin

“Fara ‘yar shehu, Asma’u Sannu “

Sakinta nayi na dawo gefenta na zauna nace

“Inna Ina yini? “

“Lafiya lau, “

Tana magana Tana assessing jikina, se naga ta bata fuska ta kalla sashen da Ummaah take, zuwa lokacin na fahimci har Abba dasu Adda suna zazzaune Kamar Wanda ake wani karamin meeting.

“Saude amma Kinsan ba haka na kawo ‘yar shehu ba Ko? Ta Yaya na baku yarinya da kibarta Yanzun Nazo Naga kashi da rai? “

Ni Kaina seda nayi dariya, balle kuma su Adda, amma Ummaah tsakani da Allah Ta Fara kokarin kare kanta. Nanfa Inna ta hau sababi, ita kafata kafarta bazata barni anan ana cuta ta ba, Abba da Ummaah se hakuri suke bata. Se ka rantse da Allah ita ta haifeni, basu suka haifeni ba. Inajin wannan Maganar na Fara murna Dan tabbas a lokacin babu abinda nake adawa dashi kamar zaman gidanmu.1

Halayena Wanda na aje a kofar gida lokacinda zan dawo daga Kwalam su na bude, sabon shafin rashin mutunci, saboda I’m sure babu Wanda ya isa Ya taba ni tunda Inna Ade na nan, islamiyya na tattara na aje, Da daddare nayi ta rigima se nayi kallo, sannan da safe se eleven nake tashi. Babu Wanda ya cemin ci Kanki, se ana gobe Inna zata tafi, mun kammalla breakfast tace da Abba Wanda ke kokarin fita

“Shahada, gobe zan tafi Maganar Asma’u Fara da ita zan tafi.”

Abba ya bude baki Zaiyi magana yaga har ta tashi ta tafi, Nima gudun abinda zai biyo baya na take mata baya zuwa dakin da yake nata, Dan tun zuwanta na tare a can.

Adda Sa’ada ce ta mike ranta a mugun bace ta nufi dakin Yaya Halifa bansan abinda tace mishi ba, all I know ina kwance naji sallamar Adda Maryam, amsawa nayi sannan ta shigo, tareda tambayata inda Inna Ade take, bandaki na nuna ba tareda na furta komai ba, kanta ta gyada sannan tace min Yaya Halifa na nemana. Wata muguwar faduwar gaba naji, saboda babu Wanda nake Tsoro, har cikin raina kamar shi da Adda Salma. Mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na nufi dakinshi.

Da sallama bakina na isa, yana zaune gabanshi Wasu manyan text books ne, se wata dorina me Baki biyu a gefe. Jikina Se ya Fara rawa, naji tamkar na ruga gurin Innata amma who born me? Da kuwa Yayi min dukan mutuwa. Tsugunnawa nayi a gabanshi bakina na rawa nace

“Yaya gani”

“Na ganki” ya furta ko kallona baiyi ba, nafi mintina goma a Haka kafin ya daura kafafunshi akan table din yana kallona yace

“Idan Inna zata tafi gobe zaki bita? “

Shiru nayi saboda bansan right reply ba, zuciyata kowa yasan Inna Ade take son bi, amma wannan Zakin dake gabana, I don’t think zan iya fadar son raina. Ina tunani Ashe har ya dauki dorinar, sede jinta nayi a kafafuna dana mikar, wani tsalle na buga saboda azabar radadin da naji tareda bude baki zanyi ihu,

“Idan kika bari naji Kinyi Ko tari ne, se na karkarya ki na zubar anan. Dawo ki zauna”2

Its funny gaskiya, jiki na rawa na dawo na zauna inajin yadda kafafuna ke zugi, yaye skirt dina nayi, abinka da fara tuni gurin ya tashi Yayi jawur, hawaye tamkar an bude famfo haka ya dinga zubowa, kafin wani lokaci fuskata tayi jawur. Sakkowa yayi ya zauna gefena yace

“Kinsan idan na kara jin kince zaki koma Kwalam, wannan bulalar se ta karye a jikinki, kuma Yanzunnan kije Kicewa Inna bazaki bita ba”

Kaina na gyada cikin sauri sannan na mike, kamar haske har na isa kofa Ya dawo Dani akan na wanke fuskata. Ina Naga ta musu, toilet dinshi naje na wanke amma kana kallona zaka San nayi kuka, nasan idan Inna Ade ta ganni a Haka, kilan kashe Yaya Halifa zatayi hakan yasa na wuce dakin Ummaah na kwanta, ranar anan na kwana.

So you guys where truly waiting for me! I got it. Thank you so much for the comments and prayers! I got you

AyshatuuuA ka’ida tafiyar Inna da sassafe take yinta, duk inda goma take to ta kama hanya, Haka idan zuwa zatayi da sassafe take zuwa. Tunda mukai Sallar asuba, Ummaah ke harhada min kayana, ranta a mugun bace, I can swear cewar ban taba ganin fuskar ta a Haka ba, saboda ta kasance mutum ce me faraa, hardly kaga ranta a bace.

Ina kwance ni kuwa Bance mata komai ba, seda ta gama sannan ta dubeni tace

“Tashi kiyi wanka”

Ban Musa ba, na tafi bandaki nayi jika jika Kamar yadda na saba na fito. Da kanta ta shafa min Mai ta shirya ni sannan muka fita zuwa parlor, Har an hada breakfast, Yana aje an baza katuwar dining mat anan parlor, komai an kawo se ci Ya rage. Zama nayi gefen Inna da ta gama amsa gaisuwar Ummaah dukda an rigada an gaisa Tun asuba. Tana ta bani labarin kawayena na Kwalam, da yadda suke dokin dawowata amma ni jinta kawai nake, muna nan Sega su Adda sun fito kusan lokaci daya gaba dayansu, se Yaya Halifa fuskarshi a murtuke ya samu guri ya zauna yana wurga min harara, cikin rashin saa Inna ta lura da hararar, kawai gani nayi ta dada mishi Duka a bayanshi tareda fadin

“Dan banza kawai, uban me tayi maka da safiyar nan zaka kafa hararar ta? Dole yarinya tabi ta lalace, kun saka ta a gaba kamar mayu”+

Idaanuna sukai raurau alamar kuka, su kuwa banda dariya babu abinda suke, a Haka Abba da Ummaah suka iske mu, abincin duka babu wani armashi haka mukaci, ana gamawa Inna ta dubeni tace

“Maza Kawata tashi dakko kayanki kizo mu tafi”

Kowa a parlon zuba min idanu yayi, suna jiran ganin abinda zanyi. To everyone utmost amazement kallonta nayi nace

“A’a Inna Ade, kije ni bazanje ba”

Wani mugun kallo Tayi min zatayi magana se kuma ta juyar da kanta zuwa inda Adda Sa’ada ke zaune hannunta da tea mug tana kurba,

“Ahaf! Ni nasan zaayi Haka, wannan yayan suna gidannan ai na daina ganin daidai. Sa’adatu da Aminu ba. Nagode sosae Kunyi kokari. Amma ku sani Fara ‘yar shehu Ko kunso Ko kun ki tawa ce, barazanar ku babu abinda zatayi mata! “

Tana gamawa ta Mike tareda kallon Abba tace

“Zan wuce Shahada”

Abba da Ummaah Wanda suka rasa bakin magana suka mike tareda bin bayanta, Nikam dakin Ummaah na koma Inata kuka, wayaga samu da rashi.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya na hakura da zancen zuwa Kwalam na rungumi sabuwar rayuwar dake gabana. A wannan hutun sosae nayi Karatu, Yaya Halifa ba karamin kokari Yayi a Kaina ba. Babu Wanda yake min magana da Hausa seda turanci. Kafin Hutun ya kare har na Fara mayarwa. A bangaren islamiyya shima sosae nake abin kirki, hakan ba karamin dadawa su Abba yayi ba, shikenan aka daina takura min, tunda na riga nayi blending da yadda suke son na zama.

Duk Hutu idan akai Zaa kaini Kwalam nayi sati daya sannan na dawo. A Haka shekaru sukai ta ja har nakai shekaru goma sha biyu, lokacin ake ta cukwukun kaini secondary school. Matsalata daya ce wadda kusan kullum se anjini da Ummaah da Sauran sisters dina, bana Aikuwa, I’m very lazy, laziness dina Har ya saka jikina kanshi na gyara se ya zama abu, wanka se Ummaah tace min naje nayi, balle gashina, se nayi sati biu ban taje shi ba, idan aka samu nayi kitso zan iya 3 months ban tsefe ba. Kuma nafi kowa Baki idan akace Ni kazama ce, kuma deep down inside me nasan ni kazama ce, kuma san jiki shi ne ummul aba’isin kazantar.

Wani yammaci mun dawo daga islamiyya nida Adda Salma da Adda Maryam, tunda muka taho bakina yake a cunne Kamar Karin kunama, saboda Adda Salma tace kaina yana wari, Bance komai ba Har muka isa gida. Ina shiga dakinmu na tarar da kayana duka na cikin wardrobe an fito dasu an watsar a tsakiyar dakin.

Takaici kamar zanyi me, ciki na karasa Ina bin kayan da kallo, gaba daya an cakuda wankakku, gogaggu da masu datti. Idanuna taf da kwalla nayi kofa zan Kai Kara naji an bude kofar toilet an bude, komawa nayi, Adda Meeyna ce hannunta rikeda face towel tana goge wet face dinta.

“Yawwa kwashe kayannan ki fitar dasu, yarinya kamar ‘yar daji se shegiyar kazanta”

Tura bakina nayi na juya na tafi gurin Ummaah, Tana kitchen tana kada miyar dare,

“Ummaah kinga Adda Meeyna Gabaki daya ta Watson da kayana waje ko? “

Seda ta kashe Gas din sannan ta kalleni tace

“Ba kazanta kike ba Asma’u? Shekara goma sha biyu ace wanka se nace miki kiyi? Wallahi dama kisani ba NTIC kike so ba? Allah Bazaa kaiki ba, Gwaram zaki tafi, yadda ko sunana kikaji se Kinyi kuka, se seniors sun miki dukan da ko cewa akai kiyi kazanta bazakiyi marmarin hakan ba”

Ai daga jin hakan na Fara kuka ina bata hakuri amma ko kulani Batayi ba ta tafi daki, komawa nayi dakin Inata kuka, na tsugunna na Fara tsitsince kayan, Adda Maryam ce Tazo ta tayani muka gyara kayan, Wanda basuda guga na kaisu inda ake Tara kayan guga. Marasa wankin kuma na kaisu cikin laundry bin, ni Kaina dana kalla wardrobe din seda naji dadi, saboda yyai kyau. Sallah mukai sannan muka zauna ta tsefe min Kaina Dama kitson guda goma ne, ana cikin combing Adda Sa’ada ta shigo, gefenmu ta zauna bayan ta dage curtains sannan ta kura fanka tace

“Wannan se mutum Yayi suffocating saboda warin da Kanki yake”

Ni magana Tana min wahala, amma da ina magana nasan tabbas rashin kunya zanyi, so instead of rashin Kunyar sede na murguda Baki, bakin na murguda daidai shigowar Adda Salma, hannunta tasa ta gwabe min bakina tace

“Zaki sani, sena fasa fitsararren bakin nan naki”

Adda Meeyna dake kwance tayi saurin cewa

“Ku kyaleta Dan Allah, kada taji Kamar an takura mata”

Dage kafada Adda Salma tayi ta kara Ficewa, wata Uwar harara nabi bayanta dashi, ribbon nasa na tufke kan in a bun, inajin Adda Maryam na mitar gashina baida zuciya. Adda Sa’ada ta wanke min shi tas, tayimin drying sannan tayi min kalba Manya, ta saka nayi wanka ai ji nayi kamar an sakeni, wata fresh air tana shigata ta ko ina a Haka bacci ya daukeni.

Duk tunanina zancen zuwa Gwaram wasa Ummaah take, amma bayan sati uku lokacin Zaa shiga sabon session Naga anata shiri, tunda naji Ni Zaa kai nake ta kuka, saboda har ga Allah bana son zuwa. Hatta Abba dake bani goyon baya wannan Karon ban samu ba. The only person that stands for me was Yaya Halifa, shima dalilinshi kada background dina ya lalace amma yadda Ummaah ta dage nasan babu me juyata.

Da daddare naje dakin Abba na gaisheshi, Yana ta tsokanata yar boarding, kiran Inna Ade ya katse mana hirar, katsewa yayi ya kira suka gaisa sannan yace mata gani a kusa. Da murnata na karba sannan na mike na fito waje, cikeda murna na gaisheta, Tana tambayata yadda nake, nan kuma na Fara kuka ina fada mata Ummaah bata sona, ta takura min tace Abba ya kaini Gwaram. Dariya Inna tayi tace kada na damu karshen sati tana hanya.

Ranar asabar kuwa da sassafe se mukaji isowar ta, lokacin Inata bacci ban tashi ba, Maganar ta yasa na fito, gaba daya ta hade gidan da sababi da kuma fada. Gashi Abba da Ummaah basa nan so babu Wanda ya kulata a cikinsu. Tana zaune naje na zauna kusa da ita nace

“Inna kinzo? Sannu ya hanya?”

kaina ta shafa tace

“Lafiya kalau yar albarka”

Mikewa nayi na tafi kitchen na dakko abincin da aka riga aka hada mata na kawo mata, Tana ta saka min albarka, jin dadin hakan yasa duk wannan laziness din nawa naje na bude dakinta na share har da mopping lokacin ta gama cin Abinci, muka koma dakinta ina tayi mata complain akan zaman gidan. Nan kuwa ta hau Tana ta masifa har su Abba suka dawo.

Can Ina kwance Tun kayan Dana tashi daga bacci shi ne a jikina, ko wanka banyi ba, ga zafi da ake a gari, jikina Har stinky yake yana bashi amma ina kwance Kamar sarauniya, su kuma sisters dina suna can suna aiki. Sallamar Inna naji hakan yasa na tashi na zauna ina Mata Murmushi Dan nasan zancen zuwa Gwaram ya rushe. Gefena ta zauna tace

“Kawata, Ashe kazanta kikeyi? Nidai Allah Ya sani ban tashe ki da kazanta ba, Haka zalika bansan Saude da kazanta ba. Dan Haka ni bana goyon bayan rashin gaskiya, Gwaram zakije ta kodan kiyi hankali”

Hannunta na kama ina fadin

“Inna Allah zan dinga yin tsafta, Dan Allah Kice Ummaah tayi hakuri”

Kanta ta girgiza, wannan shi ne karo na farko da Inna ta juyamin baya, shine sanadin tafiyata GGSS Gwaram!

AyshatuuuBayan sati biyu duk wani shiri ya kammalla, I was tired of crying Dan Haka na hakura na zubawa sarautar Allah idanu, Ina ganin ta yadda zaa Fara. Saura kwana biyu na tafi, duk Yan gidanmu suka zo. Adda (Babbar yayarmu) ita ta hada min kayana, kana kallon kayan zai Baka insight din daga gidan Dana fito. Duk fadan da akai min akan tsafta ne, Adda tace min Ummaah tace indai ina tsafta to Zaa canza min makaranta naje dreamy NTIC dina.

Ranar Monday very early, Adda Sa’ada da Yaya Halifa suka rakani, Garin Yayi min nisa sosae amma its all sightseeing. Tunda muka shiga na Fara kuka, kuma na lura suma duk jikinsu Yayi sanyi. A office din principal muka shiga, Dama ta rigada tasan da zuwanmu, ina shiga na gaisheta suma suka gaisheta, ta zagayo inda nake ta tsaya tareda shafa kaina tace

“Asma’u how are you? “

“I’m fine”  na bata amsa da dasashiyar murya, Dan Murmushi tayi ganin ina kuka, zama mukai bayan tayi mana tayin seat, seda tayi cikecike sannan ta tura aka kira VP academic ta hada ni dashi. Nan sukai mata godiya, Har naje kofa tace

“I wish you a nice stay kinji”+

Kaina na gyada kawai, a raina Ina ayyana Wanne nice stay kuma a wannan uban dajin. A lokacin ji nake gaba daya rayuwata an gama tarwatsa min ita. Office din VP academic mukaje ya buden student file sannan ya tura SS3 aka kira masa head Girl, Nidai ina zaune babu uhm babu uhmm uhmm, Haka Tazo ta gaisheshi sannan ta gaida su Yaya Halifa fuskarta a sake.

“Ga Sister na baki, Dan Allah ki kula da ita”

Kai ta gyada tareda nufo inda nake tsaye ta riken hannuna, daga nan mukai sallama bayan su Yaya Halifa Sunyi mata alkhairi sannan aka bata amanata. Tunda naga fitar motarsu nake kuka, tana ta rarrashina ji nayi kamar nayi tsuntsunwa na koma Kano amma babu halin hakan. Haka na bita ta kaini class, gashi makarantar unity school ce, so you got to see different people from different places having different religion, what makes us united is that we’re Nigerians. Kamar munafuka haka na shiga ajin na zauna, se surutu ake, amma wannan head girl din na shigowa sukai Shiru. Seda nayi settling sannan ta koma nata class din.  Tunda na zauna ban tashi ba haka kuma bance uffan ba Har aka fita break, kuma Kamar sun hada Baki babu Wanda ya kulani, ina nan zaune duk suka fice se baifi kadan suka rage ba. Durkusar da kaina nayi nayi ta kuka Kamar raina zai fita, na jima a Haka sannan wata Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, ni bansan Wacece Anty Rashida ba but I guess wannan head girl dince. Binta nayi muka tafi, fuskata tayi jawur saboda yadda nayi kuka, ina wucewa anata nuna ni Wai new comer ce.

Ana tashi a class muka tafi zuwa hostel nabi ayari, Dutse hostel aka kaini kwanar Anty Rashida, ruwan wanka tasa aka kaimin nayi, ta gyaran kayana, nayi sallah sannan na bita dining, ana Fara zubawa aka zubamin wata taliya, masifar yunwar da nake ji tasa na daure naci, daga nan se prep na yamma, wannan slow slow din da nake har seda aka tareni ban samu sallar ishai ba, aka zanemu kuwa. Har na kwanta ranar kuka nake.

A hankali kuma na Fara warewa, sede kafin na ware a kalla nafi sati biyu a Haka, amma daga baya se na Fara yiwa mutane magana Kamar yadda Nima naga suna shiga harkata, ko ina na wuce se Anyi maganata saboda kwatakwata I don’t match with that environment. Zancen tsafta kuwa, ba koda yaushe muke samun ruwa ba, ni a Haka ma Inada Uwar kwana amma dukda haka se nayi kwana uku banda alwala babu ruwan dake zuba a jikina, tunda ba wani amfani take min ba, se nice ma take amfaniwa dani. ga Rana ga wuya da dealing a makarantar da kuma azabar aike. Kafin wata daya farar fatar da duk gidanmu mu biyu muke da ita ta Fara dafewa, na rame Kamar marar lafiya. Lokuta da dama idan naje class banida aiki idan ba kuka ba, na kasa sabawa da rayuwar. Ga duk yammaci da safe se nayi zazzabi to banida Wanda xan fadawa Dan Haka ni daya nake abuna, idanba wata Rumasa’u ba, to Anty Rashida kawai Wayo takeyi min.

Ana haka ranar visiting tazo, ana gobe visiting Anty Rashida ta tsefen Kaina ta wankemin tayi min Sabin kitso, Washegari tasa nayi wanka Wanda duk nasan na ganin ido ne. Ta dakko min sababbin check Wanda ban taba sawa ba, na saka take kuma se nayi kyau, idanun nan nawa Kamar na mujiya, Dama girma ne dasu to gashi na rame, hancina ya Kara tsawo, idan aka kalleni abinda ake gani kenan.

Muna zaune nida Rumasa’u, class dinmu daya haka dakinmu, so ita ina sakin jiki sosae da ita mun kuma saba.

“Asma’u ban taba ganin dariyarki ba irin ta yau, kodan visiting day ne”

Dariya nayi Ina rufe fuskata data dashe, kamar banida jini, Haka tafukan Hannayena suma duk Sunyi fayau dasu.

“Bazaki gane irin farin cikin da nake ciki ba Rumasa’u”

Kanta ta gyada tace

“Ai naga alama kam, amma….. “

Bata karasa Maganar tata ba, wata yar SS1 Tazo ta kirani Inji Anty Rashida, babu yadda banyi ba akan Rumasa’u Tazo muje amma taki, haka na hakura na tafi abuna. Tundaga Nesa na hango Ikhram yarinyar Adda, da wani irin gudu na kwasa, su basu ganni ba Dan Haka babu sanarwa na fada jikin Adda Meeyna, gaba daya suka jiyo suna fadin

“Yar boarding, Iyeee! “

Zama nayi gefen Adda Inata Murmushi amma na kasa magana. Duk se naga yanayinsu ya canja gaba daya se bina da kallo suke Kamar irin it’s the first time of them seeing me.

“Ummaaah bata zo ba? “

Kafin a bani amsa Sega motar su tayi parking, Yaya Halifa, Ummaah, Abba. Muna hada ido kawai na rufe fuskata Inata kuka, from nowhere naji wata irin karaya ta saukar min. Dukkansu sukai Shiru har nayi me isata na gama, sannann naja Adda Maryam muka Kira Anty Rashida. Ina dawoa na sauka Kan Abinci, duk yadda nake dauki amma haka na kasa cin abincin, su dai basu ce komai ba amma yanayinsu kadai ya nuna min they’re not happy da yadda suka Tarar Dani.

Har akai Sallar laasar sannan suka Fara shirin tafiya, Inata daurewa saboda kada nayi breaking, amma seda nayi kuka. Lokacin Abba ya dawo daga office din principal, kallona Yayi yace

“Akwai abinda kike bukata a hostel zaki dakko? “

Cikin rashin fahimta nace

“Abba? “

Kallon Yaya Halifa yayi yace

“Gobe kaje ka samo mata wani admission din, Bazan iya barinta a Haka ba”

Maimakon naji farin cikin da nake tuanin ji, se naji zanyu missing makarantar, gaba daya kayana na tattara na bawa Rumasa’u. Muka tafi gida, shima asibiti muka fara tsayawa Naga Likita sannan muka dawo gida. Ina shiga dakinmu toilet na wuce na dinga wanka Kamar zan cire fatar jikina, na fito na kwanta se bacci peacefully and calm.

AyshatuuuWashegari ana Fara kiran Sallar farko na tashi, na jima a zaune ina karewa dakin kallo ina kuma godewa Allah, da tuni ina can daji ga sanyin asuba Kamar zai kwashe ka. Kaina na girgiza tareda sakin murmushi na sakko daga gadon na nufi toilet. Nayi alwala sannan na dawo Ina karewa dakin kallo, yadda Adda Salma da Adda Maryam ke baccinsu hankali kwance, a raina na ayyana basu san irin abinda na gani ba, basu san yadda boarding take ba saboda ni daya tal nayi boarding a gidanmu. So I gat the best and weird experience.

Seda aka Fara iqamah sannan nasa hannuna na tashi Adda Maryam, ni kuma na tada sallah abuna. Kowa a gidanmu yasan ni da kaunar baccin bayan asuba amma tunda aka kaini Gwaram bana tunanin nayi baccin bayan Sallar asuba sau uku, so har na rigada na saba da hakan. Suna idarwa ko magana bamui dasu ba, suka wuce gado suka sake kudunduna, Nikam Shiru nayi a raina Ina jin tamkar an canja ni, I’m not that lazy Asma’u again, I’m a new person.

Kafin bakwai na safe nayi wanka na saka kaya sannan na fito parlor, babu kowa, gidan Shiru kowa baccinsa yake. Se can cleaners dinmu suka zo, kowa ya ganni se Yayi mamakin ganina a gida, sannan Tashin da nayi da wurwuri. Kitchen na tafi dan taya Baba Zulai me yi mana girki aiki. Ina shiga ta juyo da mamaki tace+

“Asma’u yaushe kika dawo? “

Dan Murmushi nayi nace

“Jiya, aiki zan tayaki”

Seda ta kalleni for some seconds kafin ta amsa min da to, haka Inata tayata tana koya min abubuwa, Dan babu abinda na iya, idan kaganni a kitchen to aiko ni akayi. Wajen Tara naji mutanen gidan sun Fara fitowa, ban leko ba, ina juya Irish din dake cikin mai. Muryar Ummaah naji tana fadin to ina Asma’u zataje da sassafen nan? Kun duba ko ina kuwa? Dan dariya nayi sannan na saki leak spoon din nace da Baba Zulai, bari naje gurin Ummaah, Dan da alamun ita bataji abinda naji ba.

Ina lekowa naga Sunyi cirkocirko harda Abba, karasa fitowa nayi Ina gaishesu, kowanne mamaki ne a fuskarshi, Abba yace

“Asma’u me kikeyi a kitchen? Kin tsoarata mu, yan uwanki basu ganki ba”

Dan Murmushi nayi nace

“Abba ina taya Baba aiki ne, bansan zaa nemeni ba”

Kanshi Ya gyada yace

“If that’s the case, naji dadi “

Daga Haka ya juya zuwa dakinshi, hannuna Ummaah ta kama tace

“Ya kika tashi da wurwuri? Keda bakida lafiya “

“Ummaaah ai na samu sauki, kuma a school Baa komawa bacci, so na rigada na saba”

“At least, yarinya ta gyaru ko Ba komi”

Adda Sa’ada ta fada, kafin muka zazzauna ana ta hira, yawanci su suke abinsu dan ni kawai jinsu nake. Da yammacin ranar Sega Inna tazo, Ashe Abba ne ya kirata, Tana ganina tace Bazan koma ba, Ummaah tace Dama wata makarantar Zaa canja min. Kwananta biyu ta koma Kwalam.

Satina biyu na warware gaba daya, babu wani abinda yake min ciwo, da Adda zata tafi tace zata tafi Dani Ummaah ta hana, a cewarta nema min admission ake. Wannan zaman da nayi kowa seda ya lura da transformation din da aka samu a tattare dani. Dukda ko aikin nake amma bana sauri, zan jima ban gama ba amma zanyi, Haka halitta take banida sauri.

New horizon college dake Minna nan aka samo min admission, wannan karan babu Wanda Yayi protesting haka aka kaini, nida cousin dita Rayhana amma ita tun Farkon term din aka kaita, so se nayi joining dinta.1

Naji dadin zaman makarantar, Dan aljanna ce compared to inda na baro, ga Karatu both western and Islamic, saboda dama Islamic union suka kafata.

Hutuna na farko Daddyn Rayhana ne yazo, munata murna zamu tafi gida, dayazo Ya dauketa ita kadai yace Abbana zai zo ya daukeni, tafiyarsu kuwa ba dadewa Abba da Ummaah sukazo tare, Ashe basa Kano, an tura Abba Delta state wani official assignment na wata daya, shi ne ya taho da Ummaah. Dukkansu sunji dadin ganina da kuma result dina, Haka muka dauki hanya wadda banda bacci babu abinda nakeyi, saboda Daren jiya bamuyi bacci ba, munata hada kayanmu da murnar zuwa gida.

A Mobile Base accommodation din yake, flat gida ne da two bedrooms se parlor, toilet da kuma kitchen. Ni na dauki daya su kuma suna daya. Idan ya tafi aiki se nida Ummaah mu danyi hira, muyi aiki Haka muke zama abinmu.

Satina daya amma zan iya irga sau nawa na leka kofar gida, ranar Ummaah Kamar an saukar mata da bacci, se bacci take, ni kuma na gaji da zama, kallon ya isheni kawai se na fito na zauna kofar gida, time to time Ina ganin wucewar mutane mazauna Base din. Na jima a zaune naji an kwado min ball a Kaina, da sauri na mike ina sosa gurin saboda ta shigeni bugun. Bakina na turo Ina jujjuyawa dan naga wanene. Wasu maza su biyu suka karaso se haki suke dukkansu sanye da jersey, Babban baifi saan Adda Habiba ba se karamin da baifi saan Adda Maryam ba. Suna zuwa karamin yace

” Ina ball din? “

Ya tambaya yana waigawa alamun nemanta yake, harara na wurga mishi tareda dauke ball din na nufi kofa zan shige gida, saboda rainin Wayo ne, by mere looking sunsan sun buga min tunda gashi ina sosa Kaina amma su ta ball din suke.

“Ina zaki Kai mana ball dinne? Bakyaji ne? “

Babban ya fada yana Hararata, wani haushi naji na dauki ball din na wulla mishi, take kuwa ta sauka a kirjinshi nace

“Feel the pain! “

Daga Haka na wuce gida na buga kofar tareda jingina a jiki ina maida numfashi, did I seriously hit him? Na tambayi Kaina, kafadata na girgiza na wuce zuwa kitchen na dakko ruwa nasha sannan na zauna ina maida numfashi. Ban kara fita ba Tundaga ranar saboda Ina ganin Kamar idan na fita to zamu hadu dasu.

“Ummaah Wai Haka zamuyi ta zama, ba zamu fita ba?”

Aje kayan hannunta tayi tace

“kin gaji da zama ne?”

Kaina na gyada nace

“Muje ko cikin gari ne mana”

Kanta ta gyada, daga nan ban kara cewa komai ba na maida hankalina kan kallon da nake, da daddare Abba ya dawo yace zamuje gidan abokinshi a cikin Base din, nafi kowa murna, Dan ni na Fara shiryawa na zauna jiransu, a Mota mukaje, gidan sak irin namu. Tun a kofa nake jin muryar maza sunata hayaniya, hannun Ummaah na rike Har muka shiga ciki, Maza ne guda uku suna game ta Chisel, ga board din a gabansu, saboda ihunsu ko sallamar da mukai I’m not sure idan sunji, wata mata wadda bata Kai Saar Ummaah ba, Ta fito daga dayan bedroom din tana fadin

“Wai Meye Haka duk kun cika gida da ihu, Iyeee! “

Take duka suka shiga taitayinsu, Se lokacin ta hango mu nida Ummaah a tsaye, yadda ta karbe mu fuskarta a sake ta karaso tana fadin

“Ihunsu bai barni naji sallamar ku ba, Dan Allah ku shigo”

A take naji ta birgeni, saboda na yadda da bahaushe da yace shimfudar fuska tafi ta tabarma. Bayanta muka bi, Ummaah ta zauna saman cushion ni kuma na zauna Kan carpet nace

“Anty Ina yini? “

Kanta ta girgiza tace

“Call me Ummiey, ya sunanki? “

“Asma’u” na bata amsa Ina Dan Murmushi, lokacin ne na fuskanci su waye ‘ya’yanta, sune Wanda na bugawa ball last week, bata rai nayi Inaji suna gaida Ummaah, Babansu ya fita ya shigo da Abba, nan aka kafa hira Se ni daya a gefe, su kuwa sun cigaba da game dinsu. Abbansu yace su matsa min nayi nima. A dadare na zauna gefen Babban, na tsakiyan shi ne Wanda ban gani ba ranar, Yana gwada min yadda ake chisel, dashi muka buga Ya cinye ni, aka kara yi yayi winning. Aje king din nayi kan board din nace

“Wayo kake min ko? “

Dariya yayi, Juyawa nayi na Kalli Babban yayansu, ya matsa gefe amma idonshi a Kaina. I can say ban taba saurin Sabo da mutane ba irin yadda nayi dasu ba. Matsowa yayi ya dauki king din yasa min a hannuna, dagowa nayi na kalleshi cikin ido shima kallona yake cikin ido and I can swear time stuck, saurin kasa nayi da idona inajin wani discomfort a tare dani, a hankali cikin nutsuwa ya gwada min and take na fahimta, dashi mukayi na cinye dukda nasan he gave me that chance. Kafin lokacin tafiyarmu yayi na ware Duka na saba dasu amma Abu daya na manta shi ne sunayansu, the only name that ring in my head sunan Mamansu UMMIEY!

AyshatuuuBamu Kara komawa wannan gidan ba, kamar Hadin baki suma basu zo gidanmu ba, sede naji Abba yace da Ummaah, Ummiey na gaisheta, su Assignment dinsu ya kare sun tafi, duk se naji babu dadi cikin zuciyata, the least thing I should do is to know their names, amma ta Yaya? Babu wata hanya, dan koda mukaje gidan Banji an ambaci sunan kowa ba a cikknsu.

Muma a Haka hutuna ya kare aka maida ni Minna, nan muka cigaba da Karatu. Duk Hutu xaazo a dauke mu, sannan visiting sau daya ake zuwa mana a term, so har mun rigada mun saba hakan. A Haka naje SS1, Adda Habiba, Adda Meeyna Da Adda Ummiey Sunyi aure, Adda Salma ma tayi aure dukda bata gama university ba amma Ance ta karasa a gidanta.

Gidan Ya rage daga ni se Adda Maryam da Yaya Halifa, Adda Maryam tana Kuwait Tana Karatu, so ko Nazo Hutu sede mu, zauna da Yaya Halifa, muyi Karatu Wanda a gurinshi baya karewa, Har ya samin mugun son karatun, na rigada na saba, hobby dina Karatu ne.

“Rayhana Kinsan na kasa karasa Haddar last page din suratul Nisa’i”

Na fadawa Rayhana, ina rikeda qurani ita kuma tana zura uniform zamu tafi Quran class dinmu.

“Bansan me yasa take baki wahala ba, ki Kara maimaitawa kafin time ya cika”

Idanuna na runtse sannan na bude, na tattara dukkan hankalina akan karatun, seda time Yayi ta gama shiryawa sannan muka tafi, gabana se faduwa yake, dan na tsana embarrassment, Allah Ya taimaka ina shiga akace Anyi mishi rasuwa he can’t make it, naji dadi hakan na wuce can extreme din class din nayi ta bita Har ta zauna sannan na dawo gefen Rayhana.+

Lokacinda muka shiga final year, ni nayi applying medicine and surgery, ita kuma Rayhana tayi applying Biochemistry, Kaf class dinmu Rayhana batada na biyu a chemistry, ita ce overall best chemistry student a duka set dinmu, bana jin ba zata iya ba.

Munyi graduation gaba daya daga secondary, Yaya Halifa ne yazo ya daukemu daga Minna, Kamar zanyi flying Haka nake ji, ko babu komai nasan at least na taka wani mataki a rayuwata.

Straight daga Minna Kwalam muka wuce saboda akwai bikin cousin dinmu da akeyi kuma Duka family dinmu sun hadu. A cikin gida muka sauka, ko Rayhana ban jira ba nayi ciki abuna, da Adda Meeyna na Fara haduwa hannunta dauke da Aarif, rungumeta nayi itama cikeda murna ta rungumeni sannan na karba Aarif nayi ciki. A dakin Inna na tarar dasu Ummaah, kowa yana tayi mana murna, muka gaisa sannan na shige cikin uwardakin Inna, bata cikin dakin hakan yasa na fada gadon Ina Murmushi tuna yarinta da yadda na rayu a dakin, irin bacin da nayi. Ina kwance idanuna a lumshe naji shigowar ta tana fadin

“Kawata, kina ina? “

Dagowa nayi tareda riko hannunta nace

“Ganinan Kawata, na sameku lafiya? “

“Lafiya lau, ya hanya? “

Fuskata na shafa Dan tun eight muka dakko hanya amma Se Yanzun laasar muka karaso, na gaji sosae.

“A gajiye nake Inna”

Hannuna dake cikin nata ta saki, tace

“Maza sakko kije kiyi wanka, kizo kici abinci. Se Ki huta”

“Fauziyya! Fauziyya!! Fauziyya!!! “

Inna ta kwalla mata kira, Se gata ta shigo da ciki a gaba, cousin dinmu ce sannan yayar Rayhana ce tare akai aurensu da Adda Salma, kuma kusan sa’anni ne Dan dai Adda Fauziyya ta bata watanni biyu.

“Maza jeki Ki hadawa Fara ‘yar shehu ruwan wanka”

Nasan halin Inna Ade, so banyi mamaki ba amma Adda Fauziyya da mamaki tace

“Haba Inna Ade, Wanne irin ruwan wanka kuma? “

Kugu Inna Ade ta kama kamar me shirin fada tace

“Ruwan wanka nawa ne? Ki wuce kije kiyi abinda na saki, yarinya ta dawo daga makaranta ko tausayinta bakwaji”

“Inna wallahi ina fama da kaina Bazan hadawa Asma’u ruwa ba, sede kada tayi wankan. Muma ai ‘ya’ya ne kuma jikoki, amma sede ki ware bi….. “

Bakinta Inna ta buge tana huci tareda fadin

“Eh lallai, ni Fauziyya ke yadawa magana, to idan bazaki hada ruwan ba, Uwarki ta hada”

Jin hakan yasa nayi saurin cewa

“Inna, ni bana jin wanka Yanzun, bani Abinci naci tukunna”

Allah Ya taimaka se ta fita kawo min Abinci, Itakuma Adda Fauziyya tasa hannunta ta dada min duka a cinya Sannnan ta fice, bakina na turo Ina sosa gurin, se kuma nayi dariya. Inna Ade Tashin hankali, Yanzu fa tsaf zata iya kiran Anty Hauwa ta hada ruwan, Aikuwa da na fadawa aya zakinta.

Ina nan kwance Sega Nu’aimah ta shigo da kwanukan Abinci, a gabana ta aje ta gaida ni sannan tace

“Adda Asma’u, Inna tace Wai ki fada idan kina son wani abu”

Kaina na girgiza nace

“I’m ok da hakan, kirawo min Rayhana muci”

Kanta ta gyada ta fita, kwanukan na bude Abinci Kala uku, kwadon rama da first, ga sachet water me sanyi da Fanta. Rayhana Tazo muka fara ci naji isowar mutanen Adamawa, Umma Falmata da tawagar ta. Babu Wanda ya tashi cikinmu seda muka gama sannan muka je muka gaida ta. Wajen shida muka shirya mukaje gurin kamu.

“A Ina zaki kwana? “

Ummaah ta tambayeni bayan an gama kamun, Adda Sa’ada tace

“Kiji Ummaah da bata Baki Kema kin sani ai”

Dariya nayi nace

“Allah Ya bamu alkhairi “

Daga Haka na koma gidan Inna Ade, parlonta duk Anyi shimfida, da yawa mutane sun Fara kwanciya, tsatsallake su nayi cikin dakin, ina zuwa na tarar Inna na sallah babu kowa kan gadonta, kwabe kayana nayi na canja sannan na kwanta akan gadon, ni nasan ba bacci nakeji ba kawai dai hutawa nake sonyi ga Inna idan ta Fara sallah har Se mutum ya gaji da jiranta. A hankali bacci ya Fara cin karfin idona, ban jima da baccin ba naji muryar Adda Fauziyya tana tashina, tashi nayi na zauna raina ya baci nace

“Adda na Fara bacci fa”

Harara ta tayi tace

“Na sani ai, sakkowa zakiyi ki wuce ki samu wani gurin ki kwanta”

“Saboda?”

Inna ta fada, Ashe ta idar da sallah, Juyawa Adda Fauziyya tayi tace

“Inna wallahi bana iya kwana a kasa dole se a gado, idan ba Haka ba da kyar nake tashi”

Tsaki Inna tayi tace

“Shashanci kenan, ke Kawata koma Ki kwanta, ke kuma Fauziyya kiyi ta tsayuwa amma gadonnan bazaki haushi ba”

Kawai se ta Fara kuka Wai Inna bata sonsu, ni take so to itama jika ce, Kaina na girgiza Dan halayen Adda Fauziyya basida kyau. Komawa nayi na kwanta, zuciyata babu dadin abinda ya faru.

Washegari aka daura aure, wajen laasar na shigo dakin Inata mika saboda gajiya, wata Hamma na buga daidai shigata dakin Inna, cak hammar ta tsaya saboda abinda na gani a gabana, Yaya Mukhtar yana zaune ya baje yana cin Abinci. Dagowa yayi ya kalleni sannan ya saki Murmushi tareda kallon Inna yace

“Inna Fara yar shehu ce haka, Aah yarinya ta girma”

Bata rai nayi na karasa shigowa ciki na zauna saman gado nace

“Kaima ai ka girma”

Dariya yayi yace

“Still with the futsara, Ashe baki canja Hali ba”

Se kuma nayi dariya na gaisheshi, ya tambayeni Ya makaranta, Inata jin dadi nace na gama secondary dina. Se kuma mukai Shiru, na kwanta inajin yana ta cewa Inna yadda na girma, na zama Yan mata.

“Ko dai kana ciki ne Mukhtar? “

Dariya yayi ya mike yana fadin

“Inna kenan! “

Ko kwakkwaran motsi kasa yi nayi, zuciyata ta Fara ayyana Ko dai Yana sona da gaske ne? Se nayi Murmushi saboda wani excitement da naji Ya lullube ni lokaci daya. Yaya Mukhtar sa’an Yaya Halifa ne, shi ne Babban yaron Umma Falmata, so a Adamawa suke shiyasa Haduwa dasu ba sosae ba, musamman shi da bai dade da dawowa daga Estonia ba. Mikewa nayi na zauna dan naji fitar Inna, kallon gurin da ya zauna nayi sannan na sake wani murmushin na canja kaya na Kara fita.

AyshatuuuAna gama biki muka koma Kano, Abba yasa Yaya Halifa yayi min registration a gateway computers inda zanyi certificate, saboda kada na zauna bana komai. Babu laifi naji dadin wannan shawarar. Ya zamana morning classes ne, 9am to 12noon, da yamma kuma naje islamiyya, so I’m always kind of busy hakanan.

Ranar jumaa ina ciwon ciki ko makaranta banje ba, Ummaah ta shigo ta kawo min magani da ruwa nasha, ban wani jima ba bacci yayi gaba dani bani na farka ba se bayan Sallar laasar. Ina tashi nayi wanka na canja kaya sannan na fito parlor. Da mamaki a fuskata ganin Yaya Mukhtar a zaune shi da Yaya Halifa suna hira.

Basu lura dani ba seda na zauna Kan cushion din dake gefen Yaya Halifa sannan yace

“Asma’u rikici”

Dan Murmushi nayi nace

“Yaya Ina wuni? Yaushe kazo? “

Kanshi Ya Dan shafa se Murmushi yake yace

“Lafiya lau, dazun nan”

Kaina na gyada tareda tambayarshi su umma Falmata, sannan Yaya Halifa ya tambayeni saukin jiki.

Da daddare Ummaah tana parlon Abba, Se ni daya a parlor, na kudundune kafafuna, dukkan hankalina yana kan kallon da nake, naji sallamar Yaya Mukhtar, dagowa nayi na kalleshi, murmushin nan nashi Yayi min, nima na mayar mishi inajin yadda Wasu knot ke kulluwa cikin cikina, kasa nayi da kaina har ya zauna gefen kujerar da nake, ya aje mug din hannunshi akan center table din yace+

“Me kika kalla haka?”

Kallon allon TV din nayi, Kamar ban San me nake kalla ba nace

“Uhmmmm! Korean drama ne “

Kanshi Ya gyada yace

“I see, amma how do you differentiate between cast din?”

“It’s simple ” na fada Ina gyara zamana nace ” Basu kama fa as long as you continue to watch film dinsu zaka gane each of them”

Kanshi Ya girgiza yace

“I doubt much, saboda komai nasu iri daya ne fa”

Murmushi nayi bance komai ba, saboda idan na biye shi I’ll miss some important scenarios. Shima kamar yasan thought din dake running cikin raina bai sake magana ba, Se maida hankalinshi da yayi akan kurbar only God knows what dake cikin mug din. Nima duk se hankalina ya rabu biyu, rabi yana ayyana abinda yazo yi gidanmu, Dan dazun naji Ummaah tana fadawa Baba Zulai zancen zuwanshi, akan a Kara Abinci dashi. Rabin hankalina yana kan kallon da nake.

So ba komai na fahimta ba, har episode din ya kare, Se kawai na mayar Aljazira Dan na Kalli news, wannan yana daya daga cikin horon Yaya Halifa a Kaina. Shirun da mukai se yasa atmosphere din ta zama so dull and tense, gashi ina jin idanunshi a Kaina so se na Fara wasa da fingers dina, at least I want to break the silence. But how? Na tambayi Kaina,

“Ehn… Yaya Mukhtar so Hutu kazo yi kenan?”

Kanshi Ya girgiza yace

“I’ve been employed ne”

Take faraa ta, ta karu nace

“Oh! Congratulations, amma nayi maka murna “

Wink yayimin, Idan da yasan yadda wink dinnan ya taba ni, bana tunanin zai Kara min, ji nayi kamar zanyi melting cikin kujerar, na fada muku how Charming Yaya Mukhtar yake? Kyanshi kadai will make someone fall for him over and over again. Jinin Fulani Dan Mahaifinshi asalin 0 Adamawa ne, so kana kallonshi kaga hakan.

“So ya makarantar, medicine dinne? “

Kaina na gyada nace

“Shi ne, nayi passing Post UTME kuma score din yayi tallying “

“Mashaaa Allah what a great news, so mun kusa samun Doctor in the family kenan? “

Dan blushing nayi sannan na kalla agogon dake kafe a parlor, idanuna na dan zaro nace

“Bari naje na kwanta, its late”

Hannunshi ya watsar cikin iska yace,

“Oh nima bari naje na kwanta”

Daga Haka na juya zuwa daki amma ban kai ga shiga ba naji yace

“Asma’u! “

Juyawa nayi na kalleshi, Murmushi yayi min sannan Yayi min waving yace

“Sweetest of dreams”

Take naji wani blood rush gaba daya jikina, hannuna nasa na dafe cheeks dina saboda wani Hot da naji Sunyi, ban bashi amsa ba na shige ciki, kofar na mayar na rufe sannan na jingina da ita, ji nake kamar faduwa zanyi, tamkar kafafuna bazasu dauki jikina ba, na jima a tsaye a gurin Inata Murmushi sannan na janye jikina Na fada gado, ranar tsabar farin ciki da annashuwa ko addua banyi ba nayi bacci balle canja kaya. Se wajen past two na farka a gigice, seda nayi yadda na saba sannan bacci ya daukeni.

Washegari kamar yadda na saba, bayan nayi sallah, wanka nayi na Nemo kaya Marasa nauyi saboda yanayin zafi Ya Fara shigowa. Kitchen na wuce na kwaba batter Banana pancake na Yaya Halifa, baifi 4 pieces nayi ba se abincin su Abba da Ummaah, babu wani Yawa abincin amma har Yaya Halifa yazo cin nashi ban gama ba.

“I wonder how you will become a doctor, Dan nasan watarana tabbas kafin Ki yunkura patient zai mutu”

Tura bakina nayi Dan wannan furucin kullum se najishi, sede idan banyi wani abu slow ba. Zama yayi ya ci sannan Yayi min sallama Ya tafi office. Ina kammalla breakfast dinsu Abba nayi parlonshi dashi, fitowarsu kenan, na gaishesu sannan na aje komai na koma kitchen Dan dafa noodles, Ina cikin duba wayata naji kamshin Elope, Wanda nasan mammallakin kamshin nan Yaya Mukhtar ne, se na samu Kaina da kasa Juyawa balle mu hada ido. Kaina na gefe nace

“Yaya Mukhtar an tashi lafiya? “

“Lafiya lau Princess”

Da sauri na kalleshi sede to my utmost amazement Bama kallona yake ba, hankalinshi yana Kan lemun daya shigo dashi, I was kind of disappointed. Amma Se nake ganin Anya ban zake ba, anya am I on the actual and right path? Allah kadai ya sani amma nasan one thing, akwai wani abu da nakeji a gameda Yaya Mukhtar, Wanda a hankali ya Fara gina kanshi cikin zuciyata. Ban taba tunanin ni sokuwa bace Ko kuma nace wawiya Se akan Yaya Mukhtar. Shidai bai taba cewa yana sona ba, sede yadda yake shiga al’amurana is different than any other.

Daga ranar tare muke fita, office dinshi a cikin Depot yake amma Se ya kaini har school sannan ya wuce abinshi. Wannan yasa muka saba sosae dashi, indai muna tare kuma mutane suna tare damu to tabbas se Kasan Inada wani special feelings akanshi.

Ranar da admission list Ya fito, nayi murna Kamar zan zauce,duk wani me sona seda ya tayani murna na samu Medicine , Rayhana ta samo biochemistry dukka a Bayero. A ranar ina kwance a dakina, nida Adda Meeyna Tazo, Sega Luba me mana Shara Tazo tace Nazo Inji Yaya Mukhtar, ko amsata banyi ba na mike zan tafi, wani fizgowa Adda Meeyna tayimin tace

“ke dallah zo, daga ya kiraki ke kuma busy body kin wani tashi, at least take your time mana, kija class dinki. “

Dariya nayi nace

“Kaji Adda Meeyna, is not as if saurayina ne fa”

Dariya itama tayi sosae tace

“Lallai yarinyar nan, wa zaku mayar Yara daga ke har Yaya Mukhtar din, ko makaho ya shafa yasan akwai magana “

Zamana na gyara nace

“Dan Allah sona yake? “

Se tayi sakale tana kallona, sannan tace

“To Dama baiyi proposing ba amma har kike wannan zakewar. Lallai Asma’u, ki maida hankalinki fa. Ba ayiwa maza haka”

Tabe Baki nayi jikina Yayi sanyi, nace

“Nifa kawai mutunci muke dashi babu wani abu”

“Mutunci ba, ni ban taba ganinki kin saki jiki da mutane kamarshi ba, to ki saurareni Dan abinda jikinki da idanunki ke fada you’re deeply in love with him, ki zauna kiyi sorting out kafin dare yayi miki. “

Bance komai ba na fita kiran amma Kamar an zare min laka haka naji, duk yadda nake daukin abin se naji Ya fita akaina and I found myself questioning myself me nakeyi? Da gaske sonshi nake? Bansani ba tunda gaba daya na shiga rudani.

Ayshatuuu*Ok, let’s talk about the plaque that’s threatening the whole globe, the famous Covid- 19. It’s something all of us should know. Precaution is better than curing, wash your hands frequently and pray hard. May Allah Azzawajal ease all our sufferings…..Don’t forget to pray for those Doctors, Nurses, Midwives and all health care team, know that their lives are at stake.*

“Congratulations Asma’u! Nayi matukar farin ciki da jin kin samu admission. Ina fatan zakiyi amfani da damarki, kiyi kokari dan Kinsan irin hard journey dake gabanki, I’m sure Kinsan Medicine ba wasa bane”

Kaina na gyada nace

“Na sani Abba, Inshaaa Allah bazan Baka kunya ba”

Murmushi yayi yace

“Idan kikayi haka zanfi kowa farin ciki, kuma kin taimaki Kanki, saboda duk abinda kika zama may be bana nan balle na Mora, amma nasan nayi miki Gata, inason kisa a ranki Dan Kanki zakiyi Karatu bawai ni zakiyiwa alfarma ba”+

Kanshi Ya girgiza yace

“No! Ni na rigada nayi nawa, na riga na taka matsayin dazan taka, Yanzun filin naku ne. Allah Ya bada saa “

Ya fada yana daukar remote, Amin na amsa mishi sannan nayi masa sallama Dan naje na kwanta, Har na kai bakin kofar parlon, naji yace

“Asma’u “

Dawowa nayi tareda zama inda na tashi,

“Ahaf kinga na manta, shiga bedroom dina Ki dakko min wata jaka”

Tashi nayi na shiga ciki, abinka da Ajiyar wani Se ban gani ba, karshe da kanshi yazo Ya dakko Jakar yana tsokanata Wai na Fara tsufa. Nidai Murmushi kawai nakeyi, sabuwar Apple system da sabuwar Samsung ya bani a matsayin gift. Nafi mintina biyar Ina mishi godiya, saboda Ina son surprise yana kayatar dani.

“Se last thing dazan fada miki shi ne Maganar aure, zakiyi aure amma ban yadda ki kawo min wani namiji ba Har Se kin kammalla pre-clinicals dinki, a lokacin I can marry you out in peace. Is that OK? “

Dukda ba haka Naso ba, Dan a lokacin babu wani abu dake birgeni irin naga nayi aure, akwai Wanda muka gama secondary dasu su hudu duk Sunyi aure so I always feel like inama fate dina irin tasu ce. Kuma koda Zaa kashe ni akan dalilin da yasa nake son aure bansani ba, ni dai kawai nayi aure.

Bayan sati uku, na gama registration da komai Se Fara attending lecture, Ummaah tayimin sababbin dunkuna, Yaya Halifa ya siyo min dukkan Wasu stationery da nake bukata, in fact kowa supporting dina yake a gidanmu, kowa seda yayi participating in one way or d other.

Na gama hada noodles Kamar yadda ya zame min jiki, duk dare ita nake ci as dinner, Ummaah Har ta gaji da fada, Har seda tace Yaya Halifa idan yaje shopping din groceries ya daina hadowa da ita, amma haka zan aika a siyo min a shago, Dan Dama bawai inason in dinga cin brand daya, nafi son Yau naci Cherie, gobe indomie jibi Dangote. Different taste you know!

Kan kitchen island din na aje plate din sannan na janyo wata stool na zauna akai na Fara ci, nayi rabi naji isowar Yaya Mukhtar, wani irin race Ya Fara ziyartar jikina, zuciyata tana ta murna jin kamshin turarenshi, idanuna wide open saboda daukin ganinshi, haka kunnuwana sun kagu suji ya furta wani abu. Duk hakan ya faru saboda Yayi sati daya baya gida yaje Adamawa ganin gida, Se yau ya dawo kuma bamu hadu ba, saboda ban wuni a gidan ba naje gurin Adda Maryam acan na yini.

Takunshi a nutse ya shigo, amma bai karaso inda nake ba, Se ya tsaya, dukda son kallonshi da nakeyi Naki daga Kaina amma nasan a tsaye yake kuma kallona yake, I can feel his eyes all over me. Ga kamshin turarenshi dake kokarin zautar dani. Spoon dina na aje tareda tura plate din na mike hannuna na rikeda Hot lime juice.

STORY CONTINUES BELOW

“Asma’u! “

Dagowa nayi a nutse na kalleshi kafin na sake Murmushi nace

“Yaushe ka shigo? Yaushe ka dawo?? “

Gyara tsayuwarshi Yayi yace

“Na amsa daya bayan daya? “

More like a question, hakan yasa na gyada Kaina ina Murmushi Kamar wata sokuwa.

“Dazu da safe Kinje gidan Maryam. Sannan na jima da shigowa amma banyi magana ba”

Kaina na gyada nace

“Ohhhhhh! I see, ya ka baro kowa da kowa? “

“Dukkansu lafiya”

Ya bani amsa a takaice, ko me yayi tunanin kawai se ya fice, so tunanina zai dawo se na koma na zauna, amma nafi mintina goma babu shi babu dalilinshi. Dan Tsaki nayi na fito na tafi daki Inata mita a raina, Raina Ya baci saboda Ina ganin dan me yasa zai fice ba tareda Yayi min sallama ba. Se dana kwanta se naji Kamar anya Inada ounce of hankali a tareda ni? Is not as if Mukhtar yace yana sona ne amma ni me yasa nake wannan abin. Juyi nayi tayi akan gado Inata jin haushin Kaina, tareda tuhumar Kaina akan rashin sanin darajata. Inda kuka ga yadda nayi sorting abin zakuyi tunanin Bazan kara kallonshi ta fuskar so ba amma da safe muna Haduwa wajen gaida Ummaah naji Bazan iya resisting ba, tamkar me zuba min charm a jikina hakan nake ji.

~BUK~

Sabuwar rayuwa kenan dana Fara, level one Dama kowa yasan basics ne, abinda aka koya maka a secondary school ne, though Malaman mu a secondary zasuce, if you go to university, you will go deep. A university ace, this has already been taught during your Olevel no need to go deep. Kunga Kamar kowa yana gudun responsibility dinsa ne.

First week dinmu duk ya kare a introduction ne, seda muka shiga second week sannan na Fara karbar citta, kowanne course Se ka cinyeshi tas babu wani compromise, idan ba Haka ba it’s either you change department or you get withdrawn. Shi ne abinda nafi Tsoro a rayuwata, bana son failure bana kaunarta.

“Ummaah hostel zan koma”

Na fada mata lokacinda na dawo da yamma a gajiye, ga Yunwa Dana kwaso.

“Me yasa? “

Kaina na dafe nace

“Ummaah wallahi wahala nake sha, kuma na dawo a gajiye Zaiyi wahala nayi Karatu sosae”

Kanta ta Jinjina tace

“Zanyiwa Abbanki da Halifa magana idan yaso se naji yadda zaayi”

Se naji wani sanyi ya ratsa ni at least gwara ayi hakan. Ban kara sati Ina day ba, gaba daya aka tattara na koma hostel, to hakan se yafi min sauki, ga muna tare da Rayhana se na jini safe.

Wani yammaci ina kwance a daki, babu lecture din yamma so Karatu nayi, na solving Wasu equation na 1301 sannan na dan kwanta na huta, at least kwalkwalwata ta Dan huta daga wannan charge data dauka. Nayi Shiru Ina bin yan dakin da kallo kowacce tana abinda ya dace. Wayata ta Fara ringing, janyota nayi inajin waye zai takura min ne? Amma ganin sunan Yaya Mukhtar na yawo a sama yasa babu shiri na tashi na zauna ina daidaita kaina,

“Assalamu alaikum “

Na fada Ina tabbatar da muryata tayi yadda ya dace, shima amsa ni yayi, se naji tamkar wannan ne Karo na farko dana Fara jin muryar shi

“Ina bakin hostel dinku”

Ya fada yana katse min tunanina, mikewa nayi zaune nace mishi I’ll be out In a jiffy. Kashe wayar nayi na janyo wani blue black skirt na zura, Dama akwai long sleeve top Fara a jikina, Se kawai na hijab kato na saka sannan nayi waje. Amma zuciyata se kwabata ta take, Tana tuna min da how reckless nake acting. Sede mafi rinjayen Zuciyar hakan yake so sannan Sauran sashen jikina sun amince da hakan. Kuma kowa yasan idan zuciya na son Abu to Tana acting kafin kwalkwalwa ta ankare, to anawa case din Hakane, Se nayi abu se daga baya inxo Inta jin haushin Kaina.

A waje Kamar yadda ya fada na iskeshi, yana zaune kan motarshi yana danne danne a wayarshi, Yayi kyau sosae, Dayake shi ba ma’abocin saka kananan kaya bane, yafi ga manyan Kaya, Dan kullum a cikin kaftan yake, ko Dan yasan suna mishi kyau ne Oho!

Fuskata dauke da Murmushi na iso inda nake nace

“Yaya, Sannu da zuwa”

Aje wayar yayi ya kalleni sannan yace

“Yawwa, ya lecture din? “

“Alhamdulillah! “

Na fada sannan mukai Shiru, Raina Ina ayyana se yaushe zai ce yana sona ne? Se yaushe, na gaji I can’t wait any longer kuma. Muna ta taba hira har Rayhana ta dawo, dakinmu taje anan akace mata na fita, tasan tabbas ina tareda Yaya Mukhtar hakan yasa ta fito. Tundaga Nesa take tafa hannunta har ta karaso tace

“Ikon Allah! Wai ku Meye tsakaninku ne? “

“Me idonki ya gane miki? “

Na fada Ina kauda Kaina amma kafin kalaman su gama sinking cikin kanta ya ce

“Babu komai tsakaninmu, we’re just cousins…. “

Bansan nace

“Cousins!?”

Na fada muryata da rauni a ciki, Murmushi yayi tareda dirowa daga saman motar yace

“Zan wuce, akwai sako gurin Ummaah? “

Da kyar na iya girgiza kaina Dan ko amsa balle sallama kasa bashi nayi, na wuce inajin tamkar zuciyata zatayi gobara Haka naji.

“Yaya Mukhtar tsakaninka da Allah me Kakeji akan Asma’u? “

Aje wayarshi yayi a vacant seat din gefenshi sannan ya kalla Rayhana yace

“Kinsan kina damuna Ko? “

Lumshe idonta tayi tace

“Yaya Mukhtar, be serious Dan Allah, kana sonta ko kuwa? “

Kanshi Ya shafa yana Murmushi yace

“Amma Kinsan tambayar nan tanada wahalar amsawa Ko? “

“Ka bani amsa, ina maka magana ba Yaya da kanwa ba, ina maka magana matsayin kawar Asma’u “

Dan Murmushi yayi yace

“I see, I’m flirting with her, shikenan? “

Kasa Matsawa tayi Kawai tana kallonshi sannan tana nazarin abinda ya fada, can tace

“Baka kyauta ba, kuma kusan how reckless wasa da Zuciyar mutum take Kamar kana wasa da ranta ne. Kafi kowa sanin dai Asma’u na sonka, Da har bata iya fahimtar inda kasa a gaba, Dan Haka idan kasan manufarka bata alkhairi bace then allow her and let her be. Kadai tuna Kanada kannai mata! “

Tana gama fadar Haka ta wuce shi a gurin, yayi shiru yana tunanin karfin Hali irin na Rayhana, amma wannan shi ne least abinda zata iya!

Ayshatuuu!Assalamu alaikum! Hi pipu. I was in a scenario today, I wanted to leave Kano to Jigawa because of the sudden boarder shut by the states. When I went to park, I spent more than two hours no vehicle, when it came you have to pay one thosand and above, what I noticed is that, people are just waiting for an opportunity su uzzurawa mutane, believe me wallahi in this plaque and Pandemic era, idan baka tausayawa talaja

🎶….So let me be the one and only, can I be your friend and honey, I’ll be your better man………If you’re my girl I’ll take you round the world, I’ll take you places where you’ve never ever been before, so give me your…… 🎶3

Wakar da kullum Lubna se ta jita a dakinmu, amma da yake I’m not a fan of Nigerian music, ban taba fuskantar abinda Psquare  ke fada ba se yau, may be hakan yana da nasaba da zafin da zuciyata keyi min, amma jin wakar se naji wani bakon yanayi yana mamaye min jikina, tamkar ana fizgata Ina jin wani tsumammen abu ya karade dukkan zuciyata. That’s Love, a hankali na karasa gadona na kwanta Ina kara nutsuwa da bude kunnuwana inajin wakar, har ta kare. Ta kara maida ita, tanayi tana miming dinta cikeda nishadi.

Anty Zubaida itama roommate muke, tana zaune gefen gado tacr

“Nikam Lubna shi wannan Hayaty yaushe zai tura ne? Wannan ban taba ganin irin soyayyar ku ba”

Idanuna na mayar kan Lubna da ke ta Murmushi amma ta kasa magana, I’m sure tuna shi take. Se naji Kamar nayi kuka, ko se yaushe zanji abinda ake ji? Ko se yaushe zaa furta min, a so ni kamar yadda nake so? It might never happen Kila?+

Shigowar Rayhana a hargitse yasa na dago ina kallonta, zama tayi gefena tace

“Zo ki rakani”

Mikewa nayi na dauki hijab din dana aje muka fita bayan nayiwa su Anty Zubaida sallama, a kofar hostel muka tsaya, hannunta cikin nawa amma jikinta rawa yake, hakan yasa na dubeta nace

“Me yake damunki, jikinki rawa yake fa? “

Kanta ta girgiza ba tareda ta furta komai ba, amma har lokacin jikinta bai daina rawa ba, gaba daya se naji jikina Yayi sanyi, tunda baifi two hours muka rabu ba, amma bansan me ya kada ta haka ba, it’s unlike her saboda ita mutum ce me taurin zuciya, kafin kaga abu ya saka ta cikin Haka zaka dade. Na bude baki da niyyar kara tambayarta se naga motar Abdul saurayinta Yayi parking a gidanmu, hannunta na saki daidai fitowarshi, Ko tsokanar da ya saba min baiyi min ba Illa, bude mata front seat da yayi ta shiga sannan ya bude min yace

“Bismillah”

Kallonshi nayi Amma Se yayi saurin zagayawa Ya koma seat dinshi, baki daya Kaina ya kulle na kasa tunanin abinda yake faruwa. Shiga nayi na zauna, ina jinshi suna magana kasakasa shida Rayhana, bana jin su hakan yasa na rike wayata gyam a hannuna, and na rigada nayi concluding cewar nothing is right, nothing is in place, dole akwai abinda ke faruwa. Jin anyi parking yasa na dago, se ganinmu nayi a kofar gidan mu, cikin sauri na bude kofar saboda yadda naji wani mugun Tsoro ya shige ni, Ashe banga komai ba saboda kofar gidan iya ganinka motoci ne Anyi parking dinsu, ta karamar kofa na shiga seda jiri Ya kusa yar Dani saboda gawa dana gani cikin makara, a ajje. Waye ya rasu? Na tambayi Kaina Sabida Abba da Yaya Halifa na tsaye sede kallonsu kadai ya isa yasa Kasan cewa suna cikin Tashin hankali. Tsayawa nayi na kasa gaba balle nata, se bin mutane nake da kallo kamar yadda ake kallona, mafi yawancin mutanen basu lura Dani ba.

Tattausan hannu naji cikin nawa, hakan yasa nayi saurin dago idanuna, fes cikin na Yaya Suleiman, idanunshi Sunyi jawur, ga jijiyoyin kanshi sun firfito waje, baice min komai ba haka zalika Nima Bance komai ba, se cikin gida, da Adda Salma na Fara Karo, Tana zaune a kofar parlor Tana waya, ba kuka take ba amma kallonta kawai zai saka mutum yaji ya karaya, inda take na nufa da sauri, tamkar duk wani kuzarina ya dawo nace

STORY CONTINUES BELOW

“Adda waye ya rasu? “

Hannuna ta rike tace cikin lallashi

“Kiyi hakuri…..”

Hannuna na kwace bansan me ya fusata ni ba, amma a lokacin gani nake idan banyi ihu ba, Adda Salma bazata jini ba, tamkar we’re miles apart Haka nake gani, nace

“Ki sakeni! Ki fada min waye ya rasu? “

A hankali naji abu me dumi Wanda babu ko tantama hawaye ne, ya fara zarya akan kumatunshi. Banyi Ko kokarin gogewa ba, se naji an dafa kafadata hakan yasa na juya da sauri, Ummaah ce, Idanunta Sunyi ja, sun cicciko da kwalla tace

“Mukhtar ya rasu! “

Tamkar saukar aradu, haka naji saukar Maganar nan cikin dodon kunnuwana, lokaci daya ganina, jina baki daya suka dauke bansan iya adadin lokacin Dana shafe ba, all I know bayan na nutsu na ganni a dakin Inna Ade, tana zaune da carbi hannunta tana ja, hawaye na diga mata.

“Inna Wai da gaske Yaya Mukhtar ya rasu? Ya tafi gaba daya? “

Bata amsa ni ba, se rungumoni da tayi hakan yasa na saki kuka me ciwo, babu abinda nake maimaitawa Se conversation dinmu da ko awanni uku bamui da rabuwa ba. To me ya sameshi? Ashe rabuwar kenan? Ashe shi kenan mun rabu? Ashe bazan kara ganinshi ba? Kukan da nake se naji is insufficient, wani kululun abu ya tokare min makoshina, sakin Inna nayi na kwanta a dandanyar tiles, may be hakan zaisa na rage jin abinda nake ji amma tamkar ana babbaka wuta cikin zuciyata Haka nake ji, duk yadda Inna taso na daina kuka abin ya gagara.

Bayan mun rabu nida Yaya Mukhtar, kuma bayan sun gama magana da Rayhana se ya tafi, tunda dama yace mata tafiya Zaiyi, yana fita daga cikin campus dinmu Ko kofar famfo bai je ba ya bugi wata Mota dake fitowa daga cikin wani layi. Da yake a karar kwana abin yazo, kafin azo rescuing dinshi Har ya rasu shi kuma Wanda sukai Karon kafarshi ta karye. Shi ne aka kira Abba saboda shi ne last call dinshi kuma akai saa Umma Falmata da Abba Imam sunzo gida, so tare sukaje asibiti aka dakko gawarshi, aka Kira mutanen Kwalam da yan uwan kusa!

Hawaye kam bai Ko tsaya ba, zuciyata ta kasa sukuni, ni nasan baa wasa da mutuwa amma da tabbas zan karyata rasuwar Yaya Mukhtar. Da kyar da sudin goshi aka samu nayi shiri, ko kanneshi da sukeuba daya bazasu nuna min jin rasuwar Mukhtar ba, I can’t believe cewar komai ya zama tarihi, his smile, his laughter, his caring. So komai na karshe ne.

Zuciyata bata karye ba seda naga Umma Falmata, se naji wani reason nake dashi na yin kukan rashinshi, abinda ta mallaka kwaya daya tak, ya tafi ya rasu lokacin da ake tsananin bukatarshi, haka rayuwar take.1

🎶Show me the meaning of been lonely, is this the feeling I need to walk with? Tell me why I can’t be there where you are? There’s something happening in my heart 💖

Washegari se lokacin na hadu da Rayhana, tun safe nayi wanka saboda Inada test din 1301, babu Wanda ya sani ma, amma ni nayiwa Kaina fadan na tafi, dan idan banyi test din ba, nasan nida medicine sede na Tara wata Shekarar. Dakin Ummaah naje na samu Umma Falmata da kishiyarta, tayi kuka marar har ta gaji, Har kasa na tsuggunna na gaisheta sannan na musu gaisuwa saboda a jiya babu wannan halin, Numa tausar nake so, kuma na samu Dan su Adda kusan a Kaina suka kwana Har nayi bacci, Dan kowa har ita Umma Falmata Sunyi tunanin soyayya muke basu San one sided feelings bane.

A kitchen na tarar da Ummaah nayi mata sallama tayi mamakin ganina a Haka amma fuskarta ta nuna jin dadi. Yaya Halifa ne ya kaini nida Rayhana bisa umarnin Abba. Duk wata nutsuwa da nasan Inada ita tattara ta nayi guri daya saboda nasan my future relies on each thing I wrote on that paper, Hakanan nayi sannan muka gama, naje hostel na kwaso abinda ya kamata, ban Tarar da kowa ba kasancewar sun tafi class. Se a bakin hostel ne naga Anty Zubaida, Tana kallona tace

“Asma’u me ya samu fuskarki? “

Tamkar an bude famfo na fashe da kuka, rikeni tayi tace

“Kiyi Shiru Kinji? “

Kaina na gyada sannan na fada mata abinda ya faru, ta jajanta min dukda bata sanshi ba, kuma ni ban sake dasu ba balle suji cikina. Kuma tunaninta muna tareda Rayhana shiyasa bata kirani ba.

A Napep Rayhana ke cemin

“Fara ‘yar shehu, kin yafewa Yaya Mukhtar? “

Kallonta nayi sannan nace

“Me Yayi min? “

Hawayenta ta share tace

“Ki yafe masa ko zai samu gafarar Allah saboda niyyarshi akanki Bamai kyau bace. Naji mutuwarshi kasancewata mutum ta karshe da tayi magana dashi. Ina fata zaki lura da darsain da Allah Yayi a rasuwarshi”

Nidai Bance da ita komai ba amma maganarta Se echo take min, niyyarshi bamai kyau bace? How comes? Nidai abinda na sani har zuciyata na yafe masa!

Ayshatuuu_Astagfirullah Wa’atubu ilayka_

🎶 Walking down the street of Nothing ville, where our love is young and free, can’t believe what an empty place it has to come to be, I’ll give my life away, if it only be the same! Cuz I can hear a voice inside of me, that’s calling out your name….. 🎶

Wannan wakar mistakenly naji ta a wayar Yaya Halifa, shikenan na tura ta, se naji tamkar danni da Mukhtar Westlife sukai wannan wakar. Kullum naji ta Se nayi kuka, kuma naki na daina jinta, harseda Lubna ta fadawa Rayhana sannan tayi deleting dinta daga wayata, amma a banza it already stuck in my upstairs!

A Haka na cigaba da rayuwata, dukda tabon rasuwar Mukhtar yana cikin zuciyata, ban kuma ga abinda zaiyi nasarar goge shi ba. Amma Allah yafi kowa sanin me zai faru, me kuma zai kasance, kuma shi daya ya tsara mana yadda rayuwar mu zata kasance.

Watan shi daya da rasuwa na Fara semester exams, na maida hankalina sosae wajen Karatu, ga kuma nasihar Ummaah da Abba da suke min akan it’s now or never, Haka Yaya Halifa kullum mukai waya se yace min, idan na Bari damuwa ta saka na fadi exams na sani na gama da rayuwata, ga Adda Sa’ada sun dawo Kano baki daya, kullum se ta aiko min da Abinci, dukdan nayi Karatu. To idan na tuna hakan se naji Kamar ya tafi karatun kawai nake son nayi.

Sati biyu muka dauka muna Exams, Dama nafi gane Karatu cikin dare hakan yasa ranar da aka gama exams, kamar zan fadi saboda baccin da nakeji, hakan yasa nayi deciding tafiya gidan Adda Sa’ada nasan anan zanyi bacci son raina, Dan Ummaah tace min jikokin duka suna gida, Nikam I can’t be that reckless.+

Wajen Karfe biyar na yamma na isa gidan, kofar a bude take hakan yasa na tura na shiga, a parking lot na tadda Mijinta Yaya Bilyaminu da wani abokinshi, dukkansu Juyawa sukai suna kallona, gurin na isa na gaishe da bakon sannan na gaida Yaya Bilyaminu.

“Young Doctor, Ya exams”

Hamma nayi, cikin sauri na rufe bakina ina A’uziyya tareda yin murmushin nace

“It’s over Alhamdulillah! “

Kanshi Ya gyada, hakan yasa na dan saci kallon abokin nashi, kwatakwata hankalinshi baya kanmu, se naji Banji dadi ba, at least I deserve a second glance, tunda ni mace ce, Fara ce nasan kuma abinda maza suke rubibi kenan, amma ni me yasa bana samun hakan. Se na fita fin a kirga amma ko kallo ban ishi maza ba, na rasa Wanne irin jini gareni. Kuma most mutanen da basu kaini ba, a kyau din, nutsuwa da komai zakusha mamakin yadda ake rubibinsu amma ni ko Oho!

Wucewa nayi ciki saboda idan na kara dadewa akwai matsala. Allah Sarki Addata ta kaina, Ina tunanin na manta ban fada muku Adda Sa’ada ita ce favorite sister dita ba, she’s the best I can ever ask for. Tana zaune akan cushion, Idanunta sanye cikin farin medical glasses dinta, ko ban Kalli karamin glass table din dake gabanta ba nasan aiki take, Architecture ce.1

Tana jin sallama ta, ta aje HB pencil din dake hannun ta, ta taho inda nake a tsaye, tasan me nake nufi I need a hug. Rungumeni tayi nima Haka tace

“Oyoyo Lil Sis, Ya Exams din? Oh kinga yadda kika kode kuwa? “

Dariya nayi na saketa Ina tattaba kumatuna, nace

“Kai Adda, ina wuni “

“Lafiya “

Ta amsa ni sannan muka wuce dakinta spare din, gado na fada Ina fadin

“Its been a while gaskiya”

Dariya tayi ta shige toilet nasan ruwan wanka take hada min, hakan yasa na tashi na cire kayana, Tana fitowa na shiga, na jima ina wanka kafin na fito, Har Kaina seda na wanke, dukda bawai opinion dina bane, Adda tace na wanke Dan akwai barbushin kazantar in store.

STORY CONTINUES BELOW

Bankai 30 minutes ba na gama shiryawa, wata carbon color gown na saka, irinta na Bubu ne, so babu inda ya kamani, bakin veil na yafa akai har ya sakko kirjina sannan na tsaya gaban dressing mirror ina kallon fuskata wadda ta zama pale tsabar yadda nash wahala kwana biyunnan. Chappette din dake aje kan Vanity Table na goga a tattausan siraran labbana, numfashi naja me karfi inajin wani sanyi a raina saboda kamshin vanilla da ya bugeni.

A parlor na zauna, Har lokacin mijinta bai dawo ba, Abinci naci muna Dan hira jefijefi, Har muka gangaro kan hirar Mukhtar, tace

“Amma Yanzun you’re over that ko? “

Dan Murmushi nayi nace

“Adda, Mukhtar bai taba cewa yana sona ba da. Kawai yana nuna min alamar Yana sona”

Glasses dinta ta cire, tamkar cirewar zaisa ta gaskata abinda nace. Kaina na gyada mata irin na tabbatarwa dinnan. Kai ta girgiza tace

“Tab, ban taba tunanin hakan ba, amma ke kina sonshi Ko? “

Dan dariya nayi, se naji ruwa ya Fara tarar min a idona, Kaina na girgiza nace

“Babu amfani Yanzun, tunda ko ina sonshi babu abinda zai canza cewar shi din ya rasu”

Kaina ta shafa tace

“Abinda nake son naji kenan. Ina son kisan, ke din me daraja ce, ke mace ce a priceless and uncut diamond, Wanda ya aureki shi daya yasan worth dinki. Kiyi hakuri da hukuncin Allah, rabonki yana nan zuwa. Dama Mukhtar is just a passerby. Kin gane? “

Kaina na gyada, ina share hawayen da ya Fara zubamin saman fuskata, Bance komai ba amma zuciyata ta nutsu, idan da ace victims Irina Zaa dinga tuna musu Allah yana sane dasu kuma yanada plan ga rayuwarsu, tabbas da basu zama abinda suke Yau ba.

🎶…..When you worry the most, there’s no easy way out, when you ready to go and your heart left in doubt, don’t give up on your faith. Love comes to those who believe it! And that’s the way it’s!  🎶1

Karfe takwas tuntuni bacci yayi gaba dani, bani na farka ba seda akai assalatu, nayi sallah Ko azkhar Se a gado na karasa, shima ban tabbatar ba Ko na kai karshe, bacci ya daukeni. Ban tashi ba se goma da rabi, wanka na farayi inajin tamkar wata sabuwar halitta ce Ni din, duk wannan gajiyar ta tafi, se wani karfi da nake ji, fuskata normal wannan paleness din da nake hangowa babu shi. Haka na kara kwana daya sannan na tafi gidan Ummaah . Ashe rabon zanyi tsintuwa ne, tsintuwa Babba kuwa sede a lokacin is insignificant a gurina.

A kofar gate Naga Abba shida wani mutum da ban taba manta fuskarshi ba, suna tsaye se hira suke, kuma alamun sun nuna cewar sun jima basu hadu ba. Da sallama na karasa Inda suke na gaishesu, Abba farin ciki sosae a fuskarshi, Mutumin yace

“Badai Asma’u bace ta girma haka ba? “

Dariya Abba yayi, yayinda na rufe fuskata da hijab din jikina ina Murmushi, naji Abba yace

“Ita ce fa, Yanzun level 2 zata shiga tana Medicine “

“Mashaaa Allah, amma naji dadi sosae. Kasan Abdujjabbar shima medicine Yayi, Yanzun Haka residency yake. “

Kai Abba ya gyada yana ta san barka, wucewa nayi inajin hirar ta koma ta Abdujjabbar da yawa, amma a raina tunani nake cikin su ukun waye Abdujjabbar???

Tunda na tashi Kaina ke ciwo, da kyar na fito zuwa kitchen, na bude emergency kit dinmu na balla Pcm guda biu na kora da ruwan dana taro daga sink din kitchen. Zama nayi kan stool tareda daura kaina kan kitchen island din dan naga Inada Sauran time daya rage na daura abinci. Ina nan kwance naji shigowar Ummaah, ban masan ta shigo ba seda naji hannunta a wuyana, hakan yasa na dubeta da sauri, tace

“Zazzabi kike ai Asma’u, tashi kije daki, kamar dole? “

Dukda azabar da gabban jikina sukeyi, kuma nasan zazzabi ne tun ina daki, but to me rashin lafiya is the worst enemy, na tsani na ganni ina jinya.

“Ummaah ki bari zan iya, kinga idan na kwanta dada rufeni zaiyi”

Kanta ta gyada, kamar ta amince se ta dawo tace

“Kin tabbatar? Nifa hankalina bai kwanta ba “

Faint smile nayi mata nace

“Ummaah ni ce fa”

Kaina ta shafa sannan ta fita, a hankali na Fara aiki amma mainmakon ya ragu se karuwa da yake, hakan yasa na bar abincin halfway, nasa Amal din Adda ta fadawa Ummaah Bazan iya karasawa ba.

Ina zuwa na kudunduna cikin bargo, hakorana Har karkarwa suke saboda sanyin da nake ji. Ummaah data zo seda ta tsorata, can se gata ta dawo da Yaya Suleiman Wanda da alamun zuwanshi kenan, naji dai last week ana cewa zai fara Internship a Nassarawa kuma anan gida zai zauna. Ban wani ji dadi ba.

Ummaah fita tayi ta barmu, se Aleeya yarinyar Adda Sa’ada, bude bargon yayi yace

“I’ll feel the temperature? “

Kamar tambaya amma kafin na bashi amsa se hannunsa me taushi naji a dokin wuyana, banida karfi amma dukda haka seda nayi kokarin ture hannunshi. Ficewa Yayi a raina Ina mitar wannan abu. Har bacci ya Fara daukata naji sallamar Adda Sa’ada data Yaya Suleiman. Se naji dadin zuwanta. Bude Kaina nayi Ina mata Sannu da zuwa, hannuna ta kama tana ta yimin Sannu, se lokacin naga syringe hannunshi yana hada allura gaba daya se naji raina Ya baci, kada dai ace allura zaimin? Ban gama tunanin hakan ba naji yace

“Sa’adatu gyara ta nayi mata allura”

“Sule bazaka daina cemin Sa’adatu ba right? “

Dariya yayi yace

“Tit for Tat! Gyarata Dan Allah “

Mutsu mutsu na Fara amma hakan bai hana Adda Sa’ada yaye min doguwar rigar dake jikina ba, Allah yasa akwai under skirt a ciki da naji kunya, da kanshi ya saukar da skirt din da pant dina ya caka. A take naji wata muguwar kunya ta lullubeni, ga haushinshi, ai yana cire Allurar na Fara kuka. A’a Se ya Fara lallashina Har da cewa1

“Sa’ada duk kun bata yarinyar nan, Har kukan allura take. “

Ayshatuuu*Anty Asma’u Madugu…… Thank you so much for always having my back, for been there for me…. Thank you. This page Issa token of appreciation from me.*

Naji haushin furucinshi sosae, se na bata fuska ina share hawayen fuskata. Dariya yayi sannan yace

“Kawo asaka canula”

Wanne musu zanyi, Dan hannu ai bazai hada fada ba, haka na mika yasa canular, Yayi allurai sannan yasa min infusion. Wani dadi naji a jikina, Tun Ina jin hirarsu Ko ince musunshi shida Adda Sa’ada Har nannauyen bacci yayi gaba dani. Bansan iyakar time din dana dauka Ina bacci ba. Amma nasan se da aka idar da Maghrib sannan na tashi. God so kind ba sallah zanyi ba. Koda na tashi, babu inda yake min ciwo se jikina da babu karfi. Amma haka na daure na sakko daga gadon, Amal na zaune da wayata a hannu Tana game. Kallonta nayi nace

“Amaly!”

Dagowa tayi, tana ganin yanayina ta saki Murmushi, se kuma ta aje wayar tayi waje. Kaina na girgiza na wuce bandaki Dan nayi wanka. Koda na fito yan dubiya sun cika dakin, kowanne na fadin Anty Sannu, ya jiki? Lafiya nayi ta fada sannan nace suje waje na saka kaya, dukkansu suka fice a hakan na samu na shirya Sannnan ya fito. Dakin Ummaah naje suna tareda Adda Sa’ada, dukkansu Sunyi farin cikin ganin na warware. Zama nayi ina cin Abinci munata hira.+

Ban jima ba, Ikhram Tazo akan naje Yaya Suleiman yana kirana. Bansan na zunbura Baki ba seda naji dariyar Adda Sa’ada tace

“Meye hakan ke kuwa? Ki wuce kije mana”

Mikewa nayi ina gunguni, Inaji tana bawa Ummaah labarin allura Yayi min shiyasa. Banji abinda Ummaah tace ba nayi gaba abina. A parlor na tadda shi Yara sun baibayeshi. Zama nayi fuskata a murtuke nace

“Gani Yaya Suleiman”

“To ku daga ni, Se da safe Zamui wasan”

Basu Musa ba suka daga shi, daya bayan daya suka wuce dining Dan tun fiwota naji ana fama dasu akan Anyi serving dinner, amma da yake wasa ne a ransu basu lura ba. Bana takura musu saboda duk ranar da suka tafi se naji na zama so empty tamkar Anyi min mutuwa. They’re company gaskiya.

“Na zata idan patient ya tashi, Doctor dinsa yake fada nema? See you “

Dauke kaina nayi bance komai ba, saboda bansan abinda zan ce dinba. Kafadarshi yayi shrugging yace

“Ya kikeji Yanzun? “

“Alhamdulillah “

Kanshi Ya gyada sannan ya mukamin Leda yace magunguna ne, godiya nayi mishi na koma dakina.

Bayan sati biyu ko barbushin zazzabi babu kuma na warke tas, babu wani abu dake damuna. Shima kuma baifi sau daya muke Haduwa a rana ba, kullum he’s busy a asibiti. Da sassafe ina kitchen Ina daka barkono zan zuba cikin Naman kai, inason Adan saka kadan saboda yadda yake fito da flavor din. Banji sallamar shi ba se ji nayi yace

“Haba early morning kinzo kina daka, bakuda grinder ne? “

Dagowa nayi na kalleshi from head to toe, babu karya jinin Inna Ade ne, zancen bazaiyi kyau ba wannan wasa ne.

“Bamuda ita amma tunda Kaima gidanku ne, idan ka siyo Bakayi shishigi ba”

Na zata zaiji haushi, Se naji yayi dariya sannan yace

“I’ll try, zansha coffee “

Yadda ya fadi coffee dinma daban ne, tamkar mace Haka yake da kakale kakale, kallonshi nayi sannan na juya Naman nace

“Bamu shan coffee, amma Munada Tea.”

Ban jira abinda zaice ba, na shige store saboda turarenshi gaba daya Ya dameni, bansan zama kusa dashi. Ina fitowa na samu ya zubar min da gyadar Dana Dama baki daya ta malale a Kasan kitchen, kawai tsayawa nayi ina kallonshi raina a jagule.

STORY CONTINUES BELOW

“Biyani Sweetheart, naxo janyo cup ya bare”

Bance komai ba na kashe Gas sannan na dakko cup cikin wani rack dake a rufe, ba lalle ka gani ba in ba kasan gurin ajiyarsu kenan ba. Mika mishi nayi sannan na bashi Tea bag nace

“Komai yana kan dining, don’t stress yourself”

Hannunsa Ya hade guri daya yace

“Kumaya”

Se nayi Murmushi hakan ya tabbatar masa na fahimci abinda yace. Da yamma na samu bakuncin Nadia, friend dita ce da mukai New Horizon tare, muna jimawa bamu hadu ba, dukda unguwarmu daya amma dake ita Tana Karatu a wannan Private University dake Yola yasa haduwarmu Se lokaci zuwa lokaci.

Lokacinda ta shigo Ina daki, Yaya Suleiman kuma yana parlour shida Yara, so seda suka gaisa sannan ya nuna mata dakina Wanda ta rigada ta sanshi tuntuni. Ina ninke kaya naji sallamar ta, rigarda ke hannuna na wullar Inata Murmushi na nufi inda take tsaye Tana kare min kallo.

“Oh Nadia, Oyoyo….. Is this a surprise? “

Hararata tayi tace

“Kinfi kowa dadin baki idan aka zo gurinki, amma Kira a waya ya gagara, and you always brag of I been your friend ko? “

Rufe bakina nayi ina Dan dariya kasakasa, idan da Sabo na saba da korafin Nadia, tanada zumunci Ina tunanin ba dan ita ba inaga da tuni we’re separated tuntuni amma ta rike abin.

Janyota ciki nayi na ture himilin kayan dake gefen gado nace

“Zauna mana, se magana kike”

Kanta ta gyada tace

“Bari na gaida Ummaah se na dawo”

Hannunta na kama nace

“Ummaah sunje Abuja zasuyi visa zuwa Hungary”

Kanta ta gyada tace

“Dan Allah su sani a jaka”

Dariya nayi sannan na fice na dakko mata juice da cake da fish pie. Na kawo mata, tanaci munata hira, Dan banida kamar ta, ko islamiyya ma class dinmu daya. A mutanen dana zauna dasu Wanda bamu hada komai dasu ba, tafi kowa tolerating halayena.

“Ya ake ciki, kuma karkice min babu wani motsi “

Langwabar da kaina nayi irin abin tausayi dinnan nace

“Nads karya kike so nayi miki? wallahi har Yanzun Ina nan as single as me zance miki? “

Dariya tayi sosae sannan tace

“Kiga yadda kike kwabe fuska Kamar wata marainiya”

Daidaita fuskata nayi nace

“To Ya zanyi, I’m lonely I need a partner”

Numfashi taja me karfi tace

“Dama loneliness dole ne, tunda shekaru sun kai, amma Kinsan me? Lokaci ne fa, kuma har kyayi karatunki a nutse babu takura. “

Kaina na gyada nace

“An Kai kudin Rayhana da Abdul “

Wani ihu Nadia ta buga tace

“Shegu ce Rayhana, Kice an kusa? “

Dariya nayi nace

“Ke Kina ganin idan Baa saka ranar nan bazasu samu matsala ba. Ya jira da yawa ai, tun muna Js2 fa”

Daga nan muka wuce kitchen Dan ta tayani mu hada dinner, a parlor har lokacin Yaya Suleiman na zaune, kallo yake cikin system dinshi, yana jin fitowar mu ya dago muka hada ido, dauke kaina nayi inajin Nadia suna Kara gaisawa, ni kuwa ko ta kanshi banbi ba na wuce kitchen, seda ta shigo sannan tace

“Ke wannan handsome din fa? “

Tabe Baki nayi nace

“Handsome kam, Dan Anty Shamsiyya ne kanwar Abba. Internship yake a Nasarawa. “

Kanta ta gyada tace

“Yayi miki laifi ne? Naga Kamar kuna fada “

Kaina na girgiza Ina kokarin kuna gas nace

“Ko daya wallahi, in fact he’s nice. Kawai dai bana son mu saba dashi yazo Ya mutu”

“Mutu kuma? Haba ke kuwa, kowa ai se lokacin shi Yayi, Mukhtar da ya rasu lokacin shi ne. To ya zaayi? “

Na amince da abinda tace amma haka kurum nake jin bana son sabawa dashi, a rayuwata na tsani rabuwa da mutane, I’m selfish nafi son idan na samu Abu to ya zama nawa, kada abinnan ya tafi, to a wannan rayuwar ta Yaya, ai bazai yiwu ba.

Nadia bata bar gidanmu ba se wajen Karfe Tara na dare akaxo aka dauke ta tafi, Se naji inama ta zauna dan naji dadin yinin ranar. Ban bar parlon ba se wajen twelve, muna ta kallo nida Yaya Halifa, can kuma Yaya Suleiman yayi joining dinmu, anan na sake dashi for the first time Tun zuwanshi gidanmu.

AyshatuuuHutuna Ya Kare na koma school, big lady na zama yar level 200, tunda naje registering courses dina Naga babu su basics dinnan da nayi a level 1 na Fara jin wani shaukin dadi. Community based medical education, physiology, Anatomy, pharmacology and many da zaisa naji yeah I’m a medical student. Koda muka koma, first week ne kadai nayi day amma second week na tattara kayana na koma hostel, Dan na lura the higher we go, the hotter it becomes.

Ranar Friday na fito daga lecture din Biochemistry, wayata a hannu na, sauri nake Zanje hostel na dakko jakata saboda na wuce gida kafin a shiga sallah. wayata ringing tayi, na dakko na duba, Yaya Suleiman ne,

“Ajhumma! “

Ya fada Ina picking, dariya nayi nace

“Ajhussi! “

Se muka kara kwashewa dariya, sannan yace

“Nazo wucewa ta school dinku nace bari na dakko Sweetheart”

Cikin jin dadi nace

“Kai Yaya Suleiman, naji dadi, ka jirani kofar hostel dinmu, jakata kawai Zan dakko”

“At your service Ma’am “

Ko bana kusa nasan saluting dina Yayi, nayi Murmushi na katse wayar. Na tuna ranar da ya Fara cemin Ajhumma, naji haushi sosae, saboda ni nasan I’m not Ajhumma. Ina school ranar ya kirani da daddare lokacin mundan Fara sakewa da juna, yace min Ajhumma, I was like Kasan me kake fada kuwa, se yayi ta dariya, so ni kuma se nace mishi Ajhussi. Shikenan mukai naming kanmu, dake gaba dayanmu die hard fans din Korean dramas ne. Munada abubuwa sosae that are related ni dashi. I can even say, hakan ya karawa relationship dinmu karfi.+

Wani sanyi naji cikin raina, I’m sure kowacce mace ta samu Yaya Suleiman tabbas ta gama morewa, halayenshi sunada kyau, kuma kowa zaiji dadin zama dashi. Books dina na dauka sannan na fito kafadata sabe da handbag dita na wuce dakin su Rayhana. Tana kwance da waya a kunnenta, na tabbatar Maganar daya ce, Abdul ne.

“Ke Baki jiya da waya ne, kullum ace kuna Abu daya. Haba Dan Allah! “

Na fada bayan na tsaya a kanta, Allah su Rayhana are irritating, kauda wayar tayi daga kunnenta tace min

“Duk ranar da kika Fara soyayya, soyayya da right man dinki, se kin fini sannan zaki gane abinda nake ji. So ya ake ciki? “

Harara na wurga mata tareda sakin Tsaki nace

“Zan tafi, kin fasa zuwan? “

Maida wayar tayi kunnenta, tayi mishi sallama, sannan tace

“Oh Asma’u, Karatu zanyi kije kawai. “

Kaina na gyada na wuce, har naje kofar fita a dakinsu naji ta kwalla min kira, Juyawa nayi nace

“Sauri nake fa”

“Haushi kika ji ne?”

Kaina na girgiza nace

“Ke Wanne haushi, nasan bawai Karatu zakiyi ba, Abdul ne kawai zaizo. Allah yasa nanda 2 weeks kina gidanshi ma huta muma. Amma….”

Tsaki nayi na fice, na rasa wannan jarababbiyar soyayyar tsakanin Abdul da Rayhana, kamar mayu kullum suna waya, abin haushi yake bani, kuma bansan me yasa nake jin hakan ba. Yaya Suleiman na zaune a drivers seat, ya kurawa kofar hostel ido, da dukkan alamu jirana yake yi. Straight inda yake na nufa, fuskata se Murmushi ne akanta, kamar bakina zai yage, is this what I’ve been missing, dama Haka akeji a soyayyar?

“Yaya kayi ta jirana Ko? Sorry “

Murmushi yayi yace

“Anything for Princess, nasan an tsaya yin girls stuff ne ko? “

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi na kuma saki nace

“Kamar ka sani, muje Ko?”

Kanshi Ya gyada tareda yiwa motar key muka dauki hanya, seda muka fita wajen mun hau titi yake tambayata Baiga Rayhana ba, nace Rayhana ta zauna yin ayyuka. Kanshi Ya gyada dan naga shi da ita ba wani good time suke ba, unlike itada Yaya Mukhtar marigayi. A gida muna shiga nasan Yau Inada Babbar Bakuwa, Inna Ade, tamkar yadda na saba haka na shiga a guje Tana parlor tayi daidai, gabanta an cikashi da abubuwa, Abinci ne nama ne and stuffs. Rungumeta nayi nace

“Kawata! Sannu da zuwa”

Itama bakinta ta bude Wanda hakora suka Fara Ficewa sannan ga yadda goro ya rinar dasu. Tace

“Kawata, Karatu ya boye min ke”

Dariya nayi Ina gyara zamana nace

“Ya zanyi kawaliyya? Nasan Kema zakiji dadi ace kawarki Likita ce ko? “

Kanta ta gyada Tana kare min kallo tace

“Wannan haka yake amma se naga kin yi rama, Ina fata babu matsala”

Kaina na girgiza Ina tauna Apple din dana dauka akan table din gabanta nace

“Ko daya, kawai Karatu ne. “

Kanta ta gyada tace

“Allah Ya bada saa, kije kiyi wanka. “

Tura bakina nayi nace

“Kai Inna, wari nakeyi? “

Harara ta tayi tace Hali Zanen dutse. Nayi dariya sannan na tafi na Kai kaina wajen Ummaah, tunda na ganta, naji jikina Yayi sanyi, saboda yanayunta kawai ya nuna min babu lafiya. Zama nayi nace

“Ummaah, Menene? “

Murmushi tayi Wanda ko makoshi bai kai ba, balle ace daga zuciya yake. Tace

“Babu komai, kin dawo? Ya Naga baku taho da Rayhanar ba? “

Kaina na girgiza nace

“Zatayi aiki shiyasa”

Daga Haka na mike na tafi dakina. Inna kwananta biyu amma ni bansan dalilin zuwanta ba Dan babu Wanda ya fada min, sede ni din ba yarinya bace, nasan definitely akwai abinda ke faruwa, amma tunda kowa boyewa yake, Meye nawa na bincike. Se naji Dama ban dawo ba, saboda yanayinsu duka ba cikin jin dadi suke ba.

Ranar Monday mukai sallama da Inna Ade, Dan zata wuce Kwalam, Haka nima zan wuce school. Na tafi abuna. Wajen Karfe biyar na yamma Adda Sa’ada ta kirani akan gata ta shigo cikin school dinmu, Nazo wani eatery mu hadu. Haka na Mike da duk Gajiyata na tafi, ita tayi mana order chilled Fanta, Danni inason Fanta babu ruwana da kakale kakale. Yadda ta tsira min idanu yasa gaba daya na kasa sakewa balle na sha lemun.

“Asma’u kisha mana”

Langwabar da kaina nayi nace

“Adda nasan dole wani abu ya kawoku, Ki fada min Bazan iya sha ba. “

Hannuna ta kama tace

“Ki saurareni da kyau kinji”

Ban bata amsa ba na gyada Kaina, se ta cigaba da fadin

“Kinada saurayi? “

OK, to me tambayar Tazo min a bazata, Abu ne daban yi expecting ba, amma ya zanyi dole na bada amsa. Kaina na girgiza nace

“A’a Adda, wani abu ne? “

Kanta ta gyada tace

“Suleiman fa? “

Shiru nayi bansan yadda zan Fara mata bayani ba, nida Suleiman babu Wanda yace yana son wani amma kuma dukkanmu muna son junanmu, balle ni ai kada wani yaji labari, ina sonshi sosae, son abinda ban taba yiwa wani abu ba. Kuma duk yadda muka zauna da mutum Ko awa ne se ya fahimci shakuwar mu nida shi.

“Kinyi Shiru Asma’u “

Kaina na girgiza nace

“Adda, baice yana sona ba amma…. “

“Amma me? Mistake din da kikayi akan Mukhtar shi kike son kara maimaitawa. Me yake damunki ne Wai? “

Tura bakina nayi nace

“Kai Adda, yana sona ne fa, kawai nasan zai fada idan time Yayi “

Idanunta ta kafeni dasu sannan tace

“Bakida hankali dama Har Yanzun? Wa yace miki ana haka. Ki daina kulashi kina jina ko”

Juyar da kaina nayi bansan yadda zanyi ba, ta Yaya Adda zatace na rabu da only source of happiness dina, kaina na girgiza Se kuma tace

“Kinsan Inna tazo weekend dinnan. Baki San me ya kawota ba right?”

Kaina na girgiza, gabana yana faduwa nace

“Me ya kawota? “

“Zancen aurenki!”

Da mamaki sosae nace

“Ni? Aurena? Haba dai “

Dariya tayi tace

“Saboda Sajida, Nabila da Rayhana dukka sa’anninki ne kuma zasuyi aure, shi ne tazo ta bawa Ummaah da Abba notice. Idan Kinada wani saurayi Ki turashi yayi gaisuwa idan yaso ayi Maganar daga baya. “

Raina a mugun bace nace

“Lallai! Nifa banda saurayi banda Yaya Suleiman sede idan shi zan tura”

Duka ta kaimin Tana fadin

“Dallah rufe min bakinki a gurin, Suleiman ai yafi kowa sanin halin da ake ciki, idan da yana sonki kinsan da tuni yayi magana. Abinda nakeso dake Kiyiwa Allah ki daina grumping fuskarki, ko a samu mashinshini”

Nidai Bance komai ba, Raina Ya baci sosae amma ko daya hankalina bai tashi ba, saboda nasa a raina, aure da mutuwa lokaci ne.

AyshatuuuA hankali na ja kafafuna cikin hostel, duk jikina Yayi sanyi Dan ko sallamar Arziki bamui nida Adda Sa’ada ba. Meye kuma Inna Ade take nufi da rayuwata zatace Ayimin aure, idan na tuna agreement din da mukai da Abba, har Yanzun akwai more than a year zuwa lokacin da ya yarda na kawo mishi mijin aure, but see what this old woman is talking about.

Koda na koma daki, rasa inda zan saka raina nayi naji dadi, gaba daya se nakeji Tsoro yana addabar zuciyata. Alwala naje nayi na gabatar da Sallar Maghrib sannan na dauki wayata na kira Yaya Suleiman. Ringing biyu ya dauka yana fadin

“Ajhumma!”

Se naji na kasa ce masa Ajhussi Kamar yadda muka saba, nace

“Yaya Suleiman, kana ina? “

“Akwai wani abu ne? Ina gida “

Kaina na gyada Banji dadi ba, saboda it’s bothersome nace yazo Ya kaini Unguwa.

“Shikenan kawai”

Kanshi Ya girgiza yace

“Nasan dole akwai wani abu, ko daga muryarki ma, tell me do I have to come over? “

Kaina na gyada inajin bacin rai na yana dan sauka kadan kadan nace

“Gidan Anty Bintu zaka kaini Dan Allah “

Dariya yayi yace

” You don’t have to plead princess, on my way “

Ko godiyar dake bakina banyi ba, ya kashe wayar. Haka na janyo Hisnul Muslim dina Dan nayi azkar. Ina kammalawa yayi min waya na fito, Seda naje zan shiga front seat sannan na fahimci shida wani abokinshi ne, zagayawa nayi na koma baya. Seda ya Fara driving kafin na gaida abokin yana ta Murmushi yana fadin

“A’a dole mutumina, wannan kyakywar yarinya Haka, dole komai kace Asma’u “

Duka Yaya Suleiman Ya kai masa a kafada yana dan dariya kasakasa yayinda naji wani sassanyan farin ciki ya lullubeni. Kenan har Abokanshi sunsan Asma’u, kenan yana labarina cikin friends dinsa? Se na saki Ajiyar zuciya. Hisham sunan abokin, so shima Intern ne a AKTH sede shi ba Doctors bane, physiotherapist ne.

“Asma’u, Kinsan yadda kike kuwa a gurin Yayanki, a asibiti babu Wanda baisan sunanki ba…… “

Steeree Yaya Suleiman Ya buga da hannunshi, hakan yasa Hisham kallonshi kuma Yayi Shiru, Nima daga idanuna nayi Ina kallonshi ta rear mirror, se naga kamar ranshi ya baci ba Kamar zuwanshi ba. To me yasa? Ko baya son na sani ne? Kaina na sunkuyar na cigaba da danne danne a wayata amma badan ina fahimtar abinda nakeyi ba, Gabaki daya hankalina da kwakwalwar Kaina suna wajen Maganar da Hisham yayi, idan kuwa Hakane kuma da gaske ne, babu tantama soyayya ce.

A kalle kalle na, abinda na fahimci soyayya ba se an furta ba, Caring, showing concern, protection shi ne soyayya. Wanene Yaya Suleiman baiyi exhibiting ba, babu shi, so Far zan iya cewa shima yana jin abinda Zuciyar Asma’u takeji.

Anty Bintu last born dinsu Ummaah ce, kuma itace favourite Aunt dina, dukkan wani abu da ya sameni bayan Adda Sa’ada, to ita ce ta biyu da take sani. Tana sona sosae kuma ban taba kaimata kuka na ba, bata lallasheni ba.

Koda naje tana tsakar gida, ta gama kada miyar dare akan murhu, Tana jin sallama ta, Ya’yanta su uku suka yo Kaina, suna murna. Tabarmar da aka shimfida a tsakar gida na samawa Kaina matsuguni munata hira da Yaran. A Haka ta karaso muka gaisa aka zubamin tuwo.

“Wannan zuan Daren nasan dole akwai abinda ya faru da bazai fadi a waya ba Ko? “

Kaina na gyada ina gyara zamana nace

“Anty Inna Ade ce! “

Kawai se naga hawaye ya gangaro min, cikin sauri nasa hannuna na dauke shi amma hakan bai samu ba, Dan take Wasu suka Fara gangarowa, it’s sure unlike me kuka cikin mutane, ni ban yadda wani ya fahimci weakness dina ba, hakan yasa duk halinda nake ciki nafi so nayi kuka ni daya a toilet, amma see this useless tears!

STORY CONTINUES BELOW

“Kanki Inna Ade ta dawo kuma?”

Kaina na gyada nace “Tace Wai Ayimin aure, gaba daya ta dagawa su Ummaah hankali, kuma ni babu Wanda ya taba cewa yana sona, kowa sede yace Inada kyau! “

Kanta ta gyada, wannan Maganar repetition ce, ta rigada taji ta bakin Ummaah da Adda Sa’ada.

“Share hawayenki kijini. Yaushe zaku je bikin nabila”

Hawayen na share Kamar yadda tace, nace

“Kashen satunnan zamu tafi”

Kanta ta gyada tace

“Then zakije Kiyiwa Inna Ade magana, saboda a Yanzun mafitar da kike da ita kenan. “

Nima naji hakan ne ya dace, idan kuma ba Haka ba to tabbas abun ba Zaiyi dadi ba. Mun jima da ita Har nayi Sallar ishai sannan Yaya Suleiman Ya dawo na fita ya maidani makaranta shi kuma ya wuce.

Karshen sati muka tafi Fotuskum, inda anan ake rikon Nabila, kuma saboda karar da iyayenta sakaiwa marikan, aka yanke acan zaayi biki da komai. Da yamma likis muka isa, Dan Haka ina ganin anata shirin tafiya wajen Bridal shower amma naki, saboda Uwar gajiyar dana debo bazata barni na fita ko nan da can ba. Abinci da aka kawo mana naci, nayi wanka sannan na samu guri na kwanta, tun ina jin hayaniyar Yan matan har na koma Se ta Manya kawai.

Dakin da aka bawa Inna Ade, nida ita Zamui squatting, so bayan na yi Sallar ishai na shiga nayi mana shimfida sannan na fita kofar gidan, na zauna wayata a hannuna. A family dinmu, mu hudu ne kawai sa’anni gashi dukkansu zasui aure leaving only I behind. Ina a zaunen Ina hango Yaran dake bayanmu sunata hira da samari, se abin Yayi ta bani mamaki, ni da nake yayarsu bansan wannan ba amma kalle su.

Zama naji Anyi a gefena, of course nasan Yaya Suleiman ne, ko daga kamshin Perf dinsa. Murmushi nayi na kalleshi nace

“Yaya, ya akai ka ganeni? “

Baki ya bude na mamaki yace

“Haba princess, ai ko daga bacci na tashi aka Tara min mata se na ganeki, Kinsan how special kike a gurina?”

Wani sanyi naji cikin raina Ina Murmushi na rasa me nakeji a wannan lokacin, amma abu daya na sani, wannan feeling din bazai fadi da baki ba.

“Ya Postikum din? “

“Not bad”

Na fada Ina karewa gurin kallo, baice komai ba amma dukkanmu Munyi Shiru, bansan abinda yake a zuciyarshi a wannan lokacin ba, but ni tawa tafi farar takarda fari, yanayin iskar dake kadawa a hankali, hankalina a kwance Ina wasa da ganye daya fadi, weather cool and romantic.

Wajen goma da rabi, na koma daki, Inna ta kwanta amma Batayi bacci ba. Shirin kwanciya nayi sannan Nazo na kwanta gefenta, tareda sakin Ajiyar zuciya, jin wani yanayi me dadi, that moment irin dinnan kayi tafiya Ka gaji, kazo ka kwanta, Hatta kashin spine dinka se kaji dadi.

Kaina Inna ta shafa tana fadin

“Asma’u Fara ‘Yar Shehu. Yarinya ta girma. Allah yasa Kema naga Naki auren”

Murmushi nayi a raina na amsa Amin, sannan na ayyana wannan shi ne best moment daya kamaata muyi magana da ita. Gyara kwanciyarta nayi, na riko hannunta nace

“Inna Ade! “

Kallona tayi ta kuma kalli hannunmu da nayi Interwining dinsu, tace

“Ya akayi kawaliyya? “

Kaina na girgiza nace

“Ance min kince na fito da miji Ayimin aure ko? “

Kanta ta gyada tareda tashi ta zauna, nima Se nayi yadda tayi nace

“Inna aure lokaci ne, nasan Kinsan hakan tuntuni. Kuma kinga karatuna akwai matsala idan na tsaya aure. Kuma Abba cewa Yayi se nayi shekara uku sannan zan Fara kula samari”

Tunda na Fara magana ta tsareni da idonta, gaba daya se naji na takura tamkar ba wannan tsohuwar bace Dana saba da ita.

“Na fahimta sun aikoki Ki ja da abinda na fada musu kenan? “

Kaina na girgiza nace

“A’a wallahi Inna, Kinsan ko Maganar bamui dasu ba, kawai naji nayi miki magana ne. Kiyi hakuri “

Murmushi tayi tace

“Shikenan, amma da zarar miji yazo ki kawo shi, Karatu baya hana aure, Haka aure baya hana Karatu. Na fahimci bakida saurayi shiyasa….”

Katse ta nayi da sauri ina dariya, a Haka Maganar ta shiririce har mukai bacci munata hirar Mu. Washegari akai kamu, al’adarsu ta birgeni sosae. The next day akai daurin aure, aka Mika ta gidanta.

Interval din sati daya ne tsakanin bikin Nabila dana Rayhana, muna dawowa muka shiga shiryayen bikin gagaruman Masoya.

AyshatuuuuBan kasance mutum bace me son taro, shiyasa indai ana taro gaba daya se naji an takurawa rayuwata. Gashi kuma Kamar Hadin baki anzo an saka Bikunkuna uku, kowanne interval din kwanaki biyar ne. Tun alhamis muka tafi Faskari, Dan Baban Rayhana Dan can ne kuma acan zaayi bikin. Bana wani doki saboda naje Faskari Har Bazan irga sau nawa ba. Unlike yadda nayi ta zumudin zuwan Potiskum.

“Wai har yanzun Baki shirya ba, Haba ke kuwa Asma’u kowa ya shirya fa “

Kaina na dago daga kan pillon nace

“Ke rabani da wannan event din naku, wallahi na gaji”

Tunda muka zo na samu guri na kwanta Kamar yadda nayi a bikin Nabila, Tun can dama ban fiye son shiga cikin mutane ba, to Yanzun abin yafi tsamari. Hannuna ta ja tace+

“Amma dai Kinsan aurena daban yake dana kowa ko? “

Kaina na dauke saboda na tsani naci, one halin Rayhana kenan. Fita tayi ni kuma na cigaba da kwanciyata ina chatting. Bata jima ba se Gata ta dawo da wayarta a hannu, ranta a bace ta miko min, Babu musu na karba ban duba ba na kara a Kunne na. Muryar Yaya Suleiman naji yace

“Banda musu, bazanji komai ba. Ki tashi ki shirya! “

Cire wayar nayi na mika mata nace

“Jarababbiya kawai”

Dariya tayi, ban dauki wani lokaci sosae ba na gama shiryawa, gidan uncle dinta zaayi cocktail party din. Dake yanada kudi, gidan Babba ne sosae, wajen da swimming pool yake anan akai decorating gurin. Tunda naje na samu gefe na zauna, Ina ta kallon yadda ake ta hidima, amma the only thing da nake so a wannan lokacin shi ne kadaici.

Da daddare Ina zaune Farfajiyar gidan, inda aka Kawata su da concrete chairs, ni daya ce a Hut din, se jotter a hannuna Ina revising mode of action din Wasu Antihelmentics .  Wayata ce tayi ringing, daukar ta nayi na duba naga Ummaah ke kirana, dauka nayi tace Nazo naci Abinci. Amsa mata nayi sannan na mike Dan shiga ciki amma wayata ta kara katsemin hanzari, wannan karan Yaya Suleiman, bai samu yazo ba saboda yana call a asibiti. Komawa nayi na zauna tareda kara wayar kunnena nace

“Oppa! “

“Yan mata! Ya Faskari? “

Kallon compound din nayi sannan nace

“Alhamdulillah, ya asibiti? “

Dan Tsaki yayi yace

“Ki Bari kawai, ji nake kamar na gudo. Zakiyi mamakin irin aikin da nasha Yau “

Dariya nayi a hankali nace

“Ayya! Sannu. Hippocratic Oath! “

Murmushi yayi sannan yace

“Zaki ji me ake ji ne, ai Kin kusa kare preclinical dinki. “

Murmushin farin ciki nayi, saboda dadi nake ji idan na tuna wata Shekarar by now, na gama preclinical years dina, at least nayi halfway kenan. Mun jima munata hira dashi Har seda Ummaah ta turo aka tafi Dani sannan mukai sallama.

Kwana biu muka kara a Faskari, muka jiyo gida, Amarya aka kaita gidan Abdul. Tana ta kuka da muka rakata Har seda tasa naji Tsoro ya kamani, a ganina Mutumin dake ihun ayi mishi aure kuma Anyi yana wannan kukan, ni kuma suma zan dinga yi kenan.

A hankali rayuwa ta cigaba da gudana har shekara daya Tazo ta wuce, wata ta shigo cikin hukuncin Allah yadda nake Allah Allah shekarun da zan gama preclinical suzo, sunzo kuma I was successful. Batuna da Yaya Suleiman we’re still hooked sede ni ban fahimci inda relationship dinmu ya saka gaba ba, bansan Menene matsayina a gurinshi ba amma shi yanada Babban matsayi me kuma girma cikin rayuwata, shi ne Mutumin da ko Murmushi yayi se naji gaba daya lokaci ya tsaya cak, se naji Wasu butterflies na yawo cikin cikina. In a nutshell, Ina son Yaya Suleiman kuma banida wani buri a rayuwata irin naga mun zama officially one, Mata da miji. Tun ranar da na fahimci zazzafan son da nake mishi, ranar na Fara adduar Allah Ya karkato min da hankalinshi Kaina.

Akwai wani yammaci yazo school ya sameni, ranar nayi mamakin abinda nayi. Bana kwaliyya saboda looks dina ya isheni, I’m comfortable da yadda fuskata take, dukda mutane na cewa saboda Inada kyau shiyasa Bana kwaliyya. Tunda yace min zaizo na shiga wanka nayi kwaliyya ta ban mamaki, dake is not a usual thing, ba karamin kyau nayi ba. Wani bakin lace na dakko skirt da riga nasa, jikinshi Anyi zanen flowers Fuschia Pink kanana kanana. Yayimin kyau. Seda na dakko matching veil da Takalmi, na feshe jikina da constant turarena na Silent Woman, Dana kalla Kaina se naji kwakwalwar Kaina tana kwaba ta, Tana tuhumata akan zakewa da nakeyi amma dake zuciyata tayi Naam da hakan, haka nasa Kaina na fice inajin yadda roommates dina ke zuzuta kyaun da nayi. Kamar kullum a kan motarshi na sameshi Ya tsirawa kofar hostel idanu yana jiran isowata. Tunda na matso inda nasan tabbas zai ganeni nake tafiya cikin nutsuwa tareda counting takuna. Ina zuwa Naga ko idanunshi Ya kasa kiftawa balle ya dauke, wani farin ciki naji Ya mamaye min Raina,

“Oppa! “

Na fada Ina Murmushi genuinely, Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Kinyi kyau sosae fa. Looking stunning “

Hannuna nasa na rufe fuskata saboda Murnar da nayi jin sakona ya isa. Kanshi Ya rausayr yace

“Nasan wannan kwalliyar wani gurin zakije, shiga mu wuce, zanyi magana dake dama”

Se naji Banji dadi ba, shi baisan danshi nayi ba amma zaice Unguwa zanje, shiga nayi duk yanayina ya canza, bai lura ba da yanayina ba, Waka yasa ta Celine Dion I love you! Gaba daya se atmosphere ta zama cool

_I wish I could go back to the very first time I saw you, should have made my move when you look into my eyes, Cuz by now I know that you feel the way that I do…._1

Zuciyata kawai fada min take, the song is for me, Dan ni Ya saka. He’s conveying his heart into mine. Gidan Adda Sa’ada mukaje, dama nasan bata nan, amma dan kar yaji danshi nayi kwalliya kawai se nace muje. Daga nan Grand square mukaje shan Ice cream. Ana kawo mana na Fara sha, shikam hankalinshi baya kan Ice cream din se wayarshi Dayake dannawa, bana fulako indai Ice cream ne, so kan Ya gama danne dannen da yake har na shanye nawa, se kawai ya turon nashi, da farko naki karba amma daga karshe na sha kayana. Seda na gama sannan yace

“Kun taba Maganar aure da Abba? “

Cikin rashin fahimta nace

“Aure? Kamar me kenan? “

“Irin ya taba fada miki lokacinda yake so kiyi aure? “

Shiru nayi Ina tunani sannan nace

“Eh, he mentioned it, lokacinda zan Fara zuwa school yace, idan na gama Year 3 dina Zan iya kawo mishi miji “

Murmushi yayi yace

“Yayi kyau, kinga nanda shekara daya kenan. “

Kaina na gyada yace

“Kafinnan na gama ginin da nake. “

Murmushi nayi naji dadi a raina, Wannan shi ya kara min kaimin Kara sonshi a raina. Tundaga wannan ranar bamu Kara makamanciiyar Maganar ba, naje na fadawa Anty Bintu, itadai bata cemin I should go on ba amma tace na iya takuna, haka Adda Sa’ada ita cewa tayi completely na rabu dashi amma na kasa. A Haka na kammalla 3 years dina, sannan na koma AKTH inda na Fara Clinical years dina.

Ranar Alhamis Nazo gida daga asibiti dake mun Fara Internal medical posting. Wajen laasar Ina daki Yaya Suleiman Ya kirani akan Nazo abokinshi yazo na kawo musu juice suna compound. Hijabina na dakko na fito, Ummaah na fadawa sannan na dakko musu na fita, zan iya kiran abin tsautsayi ko kuma nace ceto amma nasan nayi receiving shockest blow a rayuwata.2

AyshatuuuOne love to you all!

Gaba dayansu sun juya min baya, so babu Wanda yaga tahowa ta a ciki, dukda takalmina yana Kara amma nafi tunanin discussion dinne Yayi zafi da yawa shiyasa basu Ankara da zuwana ba.

“Man kana nufin ka cemin Baka son yarinyar nan? “

“So Kamar Yaya Khamis? “

Yaya Suleiman Ya tambayeshi, banga yanayin fuskarshi ba tunda babu Dama, kawai naji lokaci daya jikina Yayi min nauyi na kasa baya balle nayi gaba, tamkar an dasa ni a gurin Haka na tsaya inajin yadda zuciyata ke bugawa da karfin gaske

“Ka fahimci me nake nufi Suleiman, Dan me yasa zakai haka, Kasan Baka sonta. You should have let her go”

“Ni na tsayar da ita? Bani bane”

“Amma Kasan Tana sonka…..”

Shiru yayi saboda juyowar da yayi ya ganni, wannan shi ne karo na uku da muka hadu dashi, sun Je gurina Ina school sau daya, na biyu sun fito daga Operation su kazo gurina sukaci Abinci, last month kenan. Amma na yaba da halayenshi, he’s a good person+

“Ga juice din “

Na fada Ina aje musu Sannnan nayi saurin Juyawa cikin gida, duk cikinsu babu Wanda Yayi kokarin tsayar Dani, saboda fuskata kawai ta tabbatar musu naji komai.

“Kagani ko? Kaga abinda Kaja ko, gashi taji”

Khamis ya fada yana buga Bumber motar, dauke Kai Yaya Suleiman yayi yace

“Is not as if Dama nace Ina sonta ne, kawai tana birgeni, tana cikin Favorite mutane da nake ji dasu. Ina tunanin tayi mistaken wannan da soyayya”1

“Dukda haka ka cutar da ita, tunda kasan cewa tana sonka, kaga kenan yaudarar ta kayi”1

Hannu ya daga mishi yace

“To Se me? Nace ta soni ne, I’m sorry for that. “

Duk abinda suke fada Ina tsaye Inaji, Dan da nayi gaba ban tafi ba, jikin katuwar pillar dake kofar shiga palor na tsaya Dan nasan bazasi Shiru ba. Bantaba sanin zuciya Tana suya ba se wannan ranar, kirjina tamkar an zuba wuta Haka naji, ga Inata kyafta idanu ko zan samu hawaye su sakko amma hakan bai samu ba, Illa karawa kaina zafi da nayi.

Ina shiga ciki, Ummaah na fitowa daga dakinta, kallona tayi tace

“Asma’u me ya sameki? Meye idonki Yayi ja? “

Kaina na girgiza, da kyar bakina ya budu nace mata

“Tun dazun Haka yake, baki lura bane”

Kanta ta gyada, dakina na nufa Se ta katseni da fadin

“Na zata zaki daura abincin dare ne. “

Kaina na gyada na nufi kitchen, Inaji tana fadin Idan tayi tsami zanji. Tunda na shiga na kifa Kaina akan kitchen Island, ni daya nasan ciwon da zuciyata, Raina da kwakwalwata ke min, gaba daya I was in shock.

“Tashi ki fada min abinda ke damunki? “

Naji muryar Ummaah a tsakar kaina, da sauri a kuma firgice na dago, tana tsaye ta zuba min idonta, hakan da nayi nasan ta fahimci tabbas akwai wani abu amma Bazan fada ba, tunda I’m naturally introvert. Kasa ce mata komai nayi, se kawai na shiga store na dakko abinda zanyi amfani dashi, bata bar gurin ba Har seda taga tabbas bazanyi magana ba, sannan aikin Yayi nisa kawai se cemin tayi

“Koma Menene, kiyi hakuri Allah yana sane dake”

Wannan furucin da tayi yasa Wasu hawaye masu zafi suka shigo sakko min, saman fuskata. Ko damuwa in sharesu banyi ba na cigaba da aikin da nake suma tamkar Kara tunkudo su akeyi Haka suka ta zuba, gaba daya hankalin Ummaah ya tashi, tayi ta rarrashina amma kamar zugani take. Karshe cemin tayi

STORY CONTINUES BELOW

“Koma daki Ki huta, Bari nayi da kaina”

Hannuna na wanke na fita ba tareda nayi musu ba, Dan babu bakin musu a taredani, gani nake idan na sake na bude baki to kuma alamari baci Zaiyi. Hijabina naja na rufe fuskata saboda tsoron kada na hadu da Yaya Suleiman. God so kind, ban hadu dashi ba, da kowa ma Har naje daki na kwanta akan gado, kuka nayi tayi kamar Raina zai fita, na kasa tunani saboda Kaina ma a cunkushe yake.

Seda na gaji dan Kaina sannan na mike na shiga toilet, har wani jiri nake ji. Fuskata na wanke nayi alwala sannan na fito na tada sallah Maghrib. Ina idarwa naji sallamar Adda Sa’ada, cikeda mamaki na dago ina kallonta, itama ta tsura min idanu se kallona take, hakan se ya karya min zuciya, Wasu hawaye suka shiga sakko min akan kuncina, Dama tuntuni fuskata tayi jawur. Karasa shigowa Adda Sa’ada tayi ta zauna gefena tace

“Asma’u! Kiyi hakuri dan Allah, ki daina kukan ai Kinyi da yawa”

Hannuna nasa na share fuskata, se naji dan sanyi ya tsirgamin a raina, at least I’ve someone that’s here to comfort me.

“Adda Yaya Suleiman yace baya sona, wai shi bai sona”

Na fada Wasu hawayen na kara gudu Kan fuskata, Idanunta ta Dan runtse sannan ta bude su akaina tace

“Kince mishi kina sonshi ne? “

Da sauri na girgiza mata kaina, nasan banida wani aji daya rage, na rigada na zubar dashi akan nunawa abinda bai sona so, nasan Ina sonshi Kamar raina amma daidai da Rana daya ban taba ayyana nayi splitting masa abinda ke zuciyata ba, koda hakan na nufin zan zauce ne.

“To ya akai kika sani? “

Ban daina kukan ba Haka bakina baiyi Shiru na fada mata duk abinda naji, dukda nasan I’m going to have a scolding, tunda ba irin nasihar da Batayi min ba akan na rabu dashi naki, na tabbatar wannan ranar take gudar min, gashi kuma tazo din.

“Ki manta dashi, bashi kadai bane namiji a duniya. Nasan Menene so nasan idan zuciyarka tana son abu, mostly Baka ji baka gani, zuciyarka wannan abin kadai take so kuma akwai lokacin da zaki ji zaki iya zuwa kowanne extent dan ki samu abinda kike so. So kenan! Amma ni ban yarda kaje inda baasan darajar ka ba, ban yarda ka zubar da kimar ka a wajen namiji ba, so inaso kiyi hakuri, rabon kwado baya Hawa sama ko ya hau se ya fado. Take heart”

Mun jima tana ta bani baki, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na rakata ta gaida Abba sukai sallama da Ummaah ta tafi. Ina dawowa daga rakiyar na iske Yaya Suleiman yana tsaye a parlor alamun yana jiran wani abu, dauke kaina nayi tamkar ban ganshi ba, saboda ji nayi tamkar naje na rufeshi da duka amma babu halin hakan

“Asma’u! “

Naji Ya fadi sunana, tsayawa nayi cak kafin na juyo bance dashi komai ba se kallonshi da nake,

“Abba yana nemanki”

Idanuna na dan zaro nace

“Abba? “

Kanshi Ya gyada, fasa shiga dakin nawa nayi na nufi parlon Abba, yana zaune shida Ummaah se Yaya Halifa, muma gefe muka samu muka zauna bayan mun gaida Abba da Ummaah. Gaba daya naji na takura saboda shirun Abba, tunda na gama Year 3 dina nake gudun kebancewa da Abba saboda Ina tsoron yayimin Maganar aure, saboda nasan alkawarin da mukai tun kafin in shiga Medical school.

Gyaran muryarshi ya katse min tunanina, dagowa nayi na kalleshi, shima kallona Yayi sannan ya Kalli Yaya Suleiman kafin yace

“Halifa ayimana addua “

Take Yaya Halifa yayi opening prayers, wannan ya tabbatar min tabbas Maganar zaayi sede banda insight akan Maganar da Zaiyi amma nasan akanmu ne.

“Suleiman, Asma’u! “

A tare duka muka kalleshi, wani irin uneasiness Ya baibaiyeni. Sassauta fuskar shi Yayi, Dan yaga yanayin da nake ciki Kamar ace min kyat na zura a guje.

“Naga Dukkanku babu Wanda yake shirin zuwa Yayi min zancen aurenshi, to ni se naga bari na tuna muku. Inason kowannenku zuwa next week ya zomin da kwakwarar Maganar! “

A zabure nace

“Abba, next week? “

Kanshi Ya gyada yace

“Akwai problem da hakanne? “

Jikina a sanyaye na girgiza Kai sannan nayi kasa da kaina, gaba daya hankalina ya tashi, to ya zanyi ni? Wa xan cewa ya turo tunda ni ko saurayi bani dashi, Tundaga wannan lokacin hankalina ya gushe bansan abinda aka tattauna anan parlon ba dukda ina zaune amma hankalina baya gurin, Yayi nisa, Ya tafi nazarin maganganun Abba.

Washegari dana fito seda kowa ya tambayeni abinda ke damuna saboda yadda idanuna sukai zuruzuru, kana kallona Kasan Ina cikin damuwa amma nayi tunanin Dan da kyar bacci ya daukeni saboda Tashin hankali. Ko yadda nake aiki Ka kalla akwai alamar tambaya, komai bana jin dadinshi, kawai dai Inayi ne Dan babu yadda zanyi,. Na gama hada breakfast ban kai ga fitowa ba naji sallamar Yaya Suleiman, Dama tunda mukai wannan abin ba mu sake magana ba, banda kiran da yayi min. Zuciya kenan wani bangaren se yake Murnar ganinshi yayinda wani barin ke kallonshi a matsayin mayaudari, maha’inci kuma azzalumi.

“Asma’u Biyani! “

Juyowa nayi na kalleshi, Bazan iya tuna lokacinda naji ya kirani da Asma’u ba, Bazan iya tunawa ba.

“Sorry for what? “

Na tambaya ina iyakar kokarin nuna strenght dina, dukda lokacin battling ake internally, zuciyata gaba daya tayi rauni Har tana son affecting muryata.

“Nasan Kinji Duka Maganar da mukai nida Khamis jiya akan Maganarki. Bansan kina sona….. “

“Sonka? Ni? “

Na fada Ina nuna kaina da middle finger dina, Kaina na girgiza nace

“Meyasa zan soka? Haba Yaya Suleiman Kamar yadda Kake jina matsayin special sister Haka na dauke ka. Ina fata zakai clearing abinda ya cunkushe maka kanka! “

Daga Haka na raba ta gefenshi na fice, a fuskarshi naga disappointment, yaji haushi na fada masa Haka, yafi son nayi ta dakon sonshi bayan shi ba sona yake ba. Tundaga ranar na cireshi a cikin rayuwata, gaba daya na koma masa Asma’u ta da, Bama taba zama muyi Maganar Arziki Ni dashi, naji na tsaneshi bana son ganinshi a rayuwata.

AyshatuuuWani irin mugun jiri ne yake neman kayar dani, bansan na damke trolley da aka hada kayan da zaayi surgery ba, take kuwa kowanne ya zube, Haka nima nabi trolley nayi baya zan fadi, amma na bude idona da kyau da suke min wani irin blurred vision, gaba daya head surgeon din, assistant, scrub nurses da Anaesthesist din suka jiyo suna kallona, bakina na bude danyin magana amma na kasa saboda wani baya da na kara yi, daga nan ban kara sanin me ake ciki ba, na suma.

Farkawa kawai nayi na ganni an maidani ward, hannuna an daura min drip yana shiga slowaly. A hankali na tashi na zauna ina tuna abinda ya faru, ranar shi ne karona na farko dana Fara shiga operation theater a rayuwata, tunda akace Dani zaayi surgery gaba daya hankalina ya tashi, saboda Ina tsoron jini, bana son ganin jini, amma nasan tunda na zabi yin medicine dolene nayi hakuri nayi adapting. Muna shiga, mukai changing sannan mukai scrubbing aka hada komai, ina gefen surgeon din yana tamin bayanin procedure da zaayi. Tunda ya karba scapel na runtse idona, Ina jin tsikar jikina yana tashi, yana yankawa naji yawu ya cika min Bakina, amma haka nayi composing kaina, har aka shiga deep, ai lokacinne naji jiri Ya fadar dani.+

Kaina na dafe ina ayyana abinda ya faru bayan na fito, yadda na zubar da kayan aikin. Da kaina na cire drip din sannan na tashi na fito zuwa Nurses station, suna zaune dukkansu suna ta Rubutu cikin files din patient.

“Kin farka, Sannu! “

Daya daga cikinsu ta fada, zama nayi nace

“Yawwa, Sannunku da aiki”

Dukkansu suka dubani sannan na koma theater, lokacin sun gama suna lounge suna hutawa na shiga, gaba daya suka dago suna kallona, seda na gaidasu sannan na zauna nace

“Sir I’m sorry, I was carried away ne”

Kanshi Ya gyada yace

“Oh I see! Ya jikin naki Yanzun? “

Ajiyar zuciya me nauyi na sauke nace

“I’m feeling better, Alhamdulillah!”

Kanshi Ya gyada yace

“Kije hostel Ki huta, you eat before coming to theatre. “

Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na dauki kayana na nufi hostel Dan na huta. Wanka nayi sannan na kwanta akan gado take kuwa bacci yayi gaba dani, Dama tunda na dawo daga gida bana samun isashen bacci saboda tunanin yadda zan bulowa Abba nake, ya zanyi da Raina, Ina zan samu mijin da zanyi presenting ma Abba. Shiyasa ko abincin Arziki bana samu Ina ci, ko na Fara ma se Inji gaba daya Ya fita a Kaina. Ina ganin Harda hakan ma yasa na fadi, Dan gaba daya bana cikin nutsuwata.

Se bayan Sallar laasar sannan na tashi, wanka na karayi na shirya cikin simple Abaya nude peach nayi rolling da farin mayafi sannan na fito da wallet dita na tafi wani eatery nayi order milk shake da pancake da akai topping dinsa da strawberry. Ina fara ci naji gaba daya an zare min apepite dina, se kawai na jingina da kujerar da nake Kai na lumshe idona Wanda yake kokarin zubar da hawaye. Ban taba kawaowa zan iya shiga Tashin hankali makamancin wannan lokacin ba, gaba daya ji nake an saka min pressure da yawa, dama ace Ina da saurayi it will be better amma banida kowa ina Abba yake son na samu saurayi.

Mikewa nayi na fice bayan nayi settling bill din, a hankali naji iska me sanyi tana kadawa, Hatta rigar dake jikina seda ta kadu, yadda iskar keda sanyi Haka nan zuciyata ta Fara sanyaya. Na kusa hostel naji an Kira sunanna

“Dr. Shahada! “

Juyawa nayi inda Maganar ta taho, Dr. Ammar ne course mate dina, Dan Murmushi na saki suka karaso shida Dr. Umaymah. Suna zuwa Ammar yace min

“Shahada Oga Mansur yace bakida lafiya “

Faint smile nayi nace

“I zoomed out a theater. “

STORY CONTINUES BELOW

Gaba dayansu suka Fara dariya, nima ina tayasu, nan Umaymah ta bamu labarin yadda tayi nata dake O&G take. Munata dariya muka samu wani bench muka zauna munata hira, yawancin Kan yanayin karatunmu ne da kuma aiki, seda aka Kira Sallar Maghrib sannan muka tafi hostel nida Umaymah shi kuma Ammar ya wuce masjid.

Asiya kadai ce a dakin, ta gama dafa noodles, Ina shiga tace Nazo muci, kaina na girgiza tareda yi mata godiya sannan na kwanta akan gado na tunda period nake. Na jima a Haka se naji sallamar Amina Aminu, tashi nayi na zauna dan nasan gurina Tazo, hannunta dauke da handouts dinta ta zauna gefena tace

“Kai ashe kin samu sauki, akacemin bakida lafiya “

Dariya na danyi kadan nace

“Ki ce an bazani na fadi a theater, shit! “

Tashi tayi ta dakko katon mirror dake kafe a dakin ta kawo min, tareda haska min fuskata gaba daya nayi wata iri Kamar bani ba, duk na rame se haske Dana karayi, fuskata ta kankance. Seda ta tabbatar na gama sannan ta mayar dashi inda yake a kafe ta dawo tace

“Asma’u, zan iya cewa tunda nake kawaye bantaba Haduwa da Mutumin da nake so har cikin zuciyata irinki ba, ni ina daukarki matsayin yar Uwa wadda muka fito ciki daya da ita, Ina son halayenki they’re the best so far. Amma sede baki daukeni yadda na dauke Ki ba. Nayi tunanin kawaye sune mutanen da kake zuwa su Baka shoulders din da zakai kuka akai, nayi tunanin shekara hudu da Doriya da mukai daidai da Rana daya zaki cemin Amina gashi wannan abin yana damuna ya zanyi? Sede ni duk abinda ya sameni Shahada ce zata Fara ji….. “

Gaba daya naji kunya ta lullubeni saboda nasan Inada mugun zurfin ciki, bana son fadawa mutane damuwata Ina ganin tamkar na daura musu nauyi ne amma wannan karan Amina Na kaita bango tunda har tayi confronting dina.

“Amina Dan Allah kiyi hakuri, ba haka bane, kawai bana son Ina damun mutane da damuwata, se naga kamar zan takura su”

Kanta ta girgiza tace

“Ko daya Shahada, baki San idan kika fada ba Kamar kin rage tasirin damuwar, ba dole se kin fada min matsalarki ba amma at least ki samu Wanda kike ganin kin yadda dashi ki fada… “

Kaina na girgiza nace

“Kai Amina, ba haka bane wallahi Kinsan…. ” se kuma na kasa cewa komai Illa hawaye da suka Fara saukar min akan kuncina, hannuna ta rike tace

“Ya isa dan Allah, kada kiyi kuka roommates dinki suzo suna tamabayar ko lafiya. Nasan ke kadai kika san yadda kikeji amma ki sani Allah will always lay a helping hand! “

Daga nan bata kara magana ba se lallashina Har seda nayi shiru sannan na sanar da ita yadda mukai da Abba, nace

“Amina banida saurayi balle na tura, kuma Abba is very serious about it, na rasa ya zanyi ki bani shawara! “

Kallona tayi sannan tace

“Yaya Suleiman fa? “

Ai se ta kara tunzura ni, nayi ta kuka inajin Kamar zuciyata zata fito saboda zafin da take min, nanma lallashina tai tayi kafin tace

“Kun rabu kenan! Wannan kukan said it all. Kinsan wani abu, ni ina daukar aure a matsayin lokaci ne, idan yazo ko ka shirya ko baka shirya ba se kayi, sannan abune da Bazaa ce kayi rushing dinsa ba, ba Kasan hannun da zaka fada ba. Kwanakinnan aure Tsoro yake bani saboda yadda nake ganin anayi yana mutuwa, ana complain se naji Kamar kada nayi Shahada. Yawancin auren soyayya ne amma Se kiga an Kare da Tashin hankali, so Wanda suke son junansu kenan. Shahada tell Abba ya kara miki lokaci, Dan aure ba Nepa payment bane ko gidan haya balle a baka notice. Sannan kada wani pressure yasa ki fadawa unprepared marriage Baki San inda zaki fada ba. I hope I’ve helped! “

Naji dadin shawarar ta, ta saka na warware har tayi mana order aka kawo mana mukaci, mukai Karatu har 12am sannan ta Kara min nasiha ta tafi. Amma Se na kasa samun karfin gwiwar zuwa gida har lokacinda Abba ya bani Har ya wuce, kullum se Munyi waya dashi amma bai taba cemin uffan ba, Haka Ummaah nasan zuba min ido sukai. Kullum idan zan fita se nayi adduaar Haduwa da miji amma Ina ko tareni ma baayi sede ayita kallona Kamar zaa cinyeni amma babu me cewa wani abu.

Wata safiya mun gama ward rounds gaba daya mun taho yan team dinmu, Dr. Badamasi wani Consultant nabi office dinshi na consultation ina ganin yadda yake, yana tamin bayanin conditions iriri da management dinsu. Wayata dake cikin clutch dita tayi ringing, kallonshi nayi yace.

“Feel free, pick your call! “

“Thank you! “

Na fada sannan na dakko wayar, Sunan Dana gani seda gabana ya fadi, Yaya Suleiman ne, kashe wayar nayi na koma na cigaba da abinda nake amma kwatakwata hankalina yaki zama guri daya, se tunanin dalilin da yasa ya kirani nake, me zai cemin?

AyshatuuuKarfe daya na Rana, Dr Badamasi yace na tafi na huta, fitowa nayi tareda kunna wayata na kira Amina Aminu Dan naji inda take, cemin tayi tana Lounge, can na tafi a hanya muna gaisawa da mutane. Naje zanyi kwana na shiga lounge din naga mutum a gabana Yayi min tsaye, dagowa nayi na kalleshi kamar yadda ya tsira min idanu, dauke kaina nayi nace

“Ya akai? “

“I need to talk to you “

Kaina na girgiza nace

“Sede wani lokacin Yaya Suleiman, Munada lectures “

Daga Haka na juya zuwa inda muke lectures, saboda bana son ya karyata ni ko kuma yaji saboda shi nayi karyar. Biyoni Yayi yace

“Asma’u yaushe muka fara yar haka dake, nasan posting kuke ta Yaya zakice min zakije lectures. Kiyi hakuri I know I was a monster, nasan kina sona amma…..”

Juyawa nayi na watsa mishi wani kallo na wulakanci nace

“Na taba ce maka Ina sonka? Ko na taba turowa nace ace dakai ina sonka? Ko daya banyi ba. Ka isheni ka dameni, ka rabu dani Haka manaa”+

Hannuna yaja har seda muka zauna Kan Wasu concrete chairs, babu kowa a gurin kuma Allah yaso dukkanmu babu lab coat jikinmu.

“Naji bakya sona amma wannan ramar da Tashin hankalin dake akan fuskarki na Meye? “

“Ina ruwanka? Dama abinda kazo kaji Kenan? To ni Inada abinyi”

Daga Haka na mike zan tafi yayi saurin cewa

“Kada ki tafi Asma’u, kawarki nake so, kawarki Nadiya! “1

Bansan yadda naji a wannan lokacin ba, amma kafata kasa dagawa nayi, na tsaya cak inajin yadda kirjina yake wani irin bugawa, Innalillahi wa Inna ilahil rajiun kadai nake ambata a raina, ji nake kamar ana ripping min zuciyata, Kawarki Nadiya na sake maimaitawa cikin kaina. Gabana yazo Ya tsaya yace

“Nadiya kawarki ita nake so, inda kin yadda kina sona dazan iya hakura da ita amma tunda perception dina ne Ina ganin gwara nabi son zuciyata”

Tunda ya Fara magana nake kallonshi, gaba daya kaina ya kulle na kasa tunanin abinda ya kamata nace mishi, se kawai na saki Murmushi me ciwo Wanda gwara ace kuka nayi tayi, amma tunda nace bana sonshi, ban taba sonshi ba, I’ve to prove myself.

“Yau zata dawo daga Yola, gobe Zanje na mata magana. “

Na fada a sanyaye na tafi cikin sanyin jiki, idanuna suka cicikko da kwalla, amma Banason nayi, nafi son Se na kebe Se nayi amma seda ta samu damar zubowa, saurin gogewa nayi na cigaba da tafiya, dakinsu Amina Aminu naje, babu kowa hakan yasa na kwanta gadonta nayi ta kuka, a raina Ina tsinewa Yaya Suleiman da yayi sanadin rabani da farin cikina. Seda nayi me isata sannan bacci yayi gaba dani.

Acan gida, Abba da Ummaah Har sun gaji da zuba idon ganin ta inda zan shigo gidan, tunda nayi sati biu Ummaah ke saka ran zuwana amma har nayi uku Ina neman karasa na hudu Bbu alamata. Ta kira Adda Sa’ada tayi mata complain Adda Sa’ada tace ta rabu dani Zanzo da kaina. Abba kanshi seda yace da Ummaah tace min ya janye min Maganar na dawo gida amma Ummaah tace ya barni Zanzo da kaina.

Se dare sannan na dawo hayyacina, bayan Munyi Karatu na koma dakinmu, nayi wanka na fito zan shirya kawai naga mutum akan gadona, Nadiya ce

“Omo… Omomo! Yaushe kika dawo”

Hannnuna taja na zauna tace

“Dazunnan Lady, Bazan iya jira Har Se gobe ba”

Murmushi nayi nace

“Bari nayi sauri na shirya mu fita waje.”

Tana ta min hira Har na gama shiryawa sannan muka fito tare, wani secluded area muka samu nayi mana order aka kawo sannan muka zauna. Nayi farin ciki saboda Rashin magana wani lokacin Yayi a rayuwa, da ban kasance marar surutu ba, da tabbas na fadawa Nadiya yadda mukai da Yaya Suleiman, Allah Ya taimaka indai mukai waya se nace mata idan ta dawo akwai magana, Dana tabbatar bazata taba amincewa da zancen soyayya da Yaya Suleiman ba.

STORY CONTINUES BELOW

“Ma’u duk kin rame, me yake damunki haka, kinganki kamar ba Asma’u ta ba”

Murmushi nayi nace

“Mhmm, Karatu ne yake cakar Dani, I’m about to start project. “

Been the Nadiya she always is, seta yadda da abinda nace nan muka fada hira sosae anan nace mata

“Nadiya Ya Farouq? “

Tabe Baki tayi tace

“Ba nace miki Munyi breaking ba, ai tun wannan fadan da mukai muka kasa fixing abin, se naji Ya fita kawai akaina, I can’t continue with someone like him. “

Kaina na gyada nace

“Ki dinga hakuri and whatever, Dama ke dashi since from the start you were not meant to be. Yaya Suleiman yace yana sonki kum…… “

Kallona tayi da confusion tace

“Yaya Suleiman Wanne? Naki Wai?”

Hannunta na kama ina Murmushi nace

“Meye kike wani panting saboda nace yana sonki, Eh Yaya Suleiman na gidanmu. Yaushe kike free na rakoki”

Tsira min idanu tayi tana kallona tamkar tana son karanto wani abun, kaina na dauke saboda idanuna are weak zasu iya badani Susa naji Kunyar da Bazan manta ba.

“Behind wannan smile din naki, Ina hango damuwa a tattare dake, Ki fada min abinda yake damunki mana, ni ce Nadiyanki fa”

Murmushi nayi nace

“Kinsan talks dinki yana sani kuka ko? Maganar Yaya Suleiman muke. Ya kike ganin. Can you? “

Kallona ta kuma yi, a take na fahimci me take nufi ba girgiza Kai nace

“Karkiyi tunannin dating muke da, A’a we were just favourite cousins kin gane? So ni ce babbar kawar Amarya, babbar Aminiyar Ango. How do you see it? Abin Yayi ko? “

Rungumeni tayi tace

“Duk tunanina soyayya kuke shiyasa nake hesitating karbar zancen. Ke a matsayin sister dita wacce shawara kika bani? “

Gyara Zamana nayi nace

“Ki amince, so far mun jima tare dashi kuma ko a family ana yabon shi. Beside Mamanshi batada matsala. Sede nace all the best “

Bakina na bude tareda kawar da kaina saboda hawaye da naji yana neman bada ni, hura iska nayi tayi har na hadiye hawayen sannan na samu muka cigaba da hirar mu.

Da daddare nayiwa Yaya Suleiman text din number ta, address dinta sannan nayi mishi fatan alkhairi, Ina kallo Yayi ticking alamun delivered ai se kawai na Fara kuka, na sadaukar da abinda nake so, na tabbatar kodan wannan Allah zai bani lada kuma ya duba lamurana.

Tun Ina tunanin Yaya Suleiman zai Kira har na fitar da rai, se Washegari da yamma ya kirani akan na shirya muje tare, kawai se naji Ya raina min Wayo da yawa hakan yasa nace tutorial Zanje kawai ya tafi. Kamar wasa Nadiya ta kirani tana tamin ihu, Dama Haka Yayana yake, haka ya hadu Haka ya iya soyayya, karshe kasa karasa Maganar mukai nayi pretending network baida kyau na kashe wayar.

Ranar da na cika sati biyar banje gida ba, muna ward, Senior Doctor da nake bi yana call so muna tare dashi Sega Amina Aminu tazo, seda ta gaida Dr Mike sannan suka gaisa da Nurses din kafin tace min

“Asma’u Kinyi Bakuwa! “

Kallonta nayi nace

“Wacece? “

“Zo muje Ki gani”

Allah yasa mun gama abinda zamuyi Hakanan na bita muka tafi lounge din da muke, Tundaga Nesa naji gabana yana faduwa, amma ban kara tambayarta bakuwar ba. Ina shiga na tarar da Ummaah a zaune gabanta an aje mata lemu da ruwa, se naji wani dadi ya mamayeni, naji sanyi a raina. Rungumeta nayi ta baya nace

“Ummaah! “

Hannuna ta bubbuga tace min

“Ai fushi mukeyi dake. Saboda Allah Asma’u sati biyar kina Kano amma Bazan kizo gida ba. Me akai miki? “

Murmushi nayi na zagayo na zauna, tareda kwantar da kaina kafadarta, Murmushi yaki barin fuskata nace

“Ummaaah bansan me zance muku ba, amma banida saurayin da zan kawawa Abba shiyasa”

Cikeda tausayi na tace

“Shiyasa? “

Kaina na gyada nace

“Ummaah! “

Kanta ta shiga gyadawa tace

“Komai nufi ne na Allah kada Ki takura Kanki, Allah is the perfect timer, so abinda yake naki zaixo sede idan lokaci baiyi ba “

Mun jima munata hira, Tana ta kwantar min da hankali har tace min wani sati zaaje tambayawa Yaya Suleiman auren Nadiya, dukda Nadiya ta fadamin amma seda naji gabana ya fadi, zuciyata ta motsa, nayi saurin kawar da hakan muka cigaba da hiraramu.

Ina samun sukuni na tafi gida, kullum ina zuwa daga can, the only time nake kwana cikin asibiti sede idan Munada call ne. Batun Suleiman tamkar da gayya yake Wasu abubuwan duk abinda ya faru tsakaninshi da Nadiya, ni ke Fara sani Tun Ina damuwa Har na hakura, a Haka Manya suka shiga aka saka rana. Ranar nayi kuka Kamar zan fitarda idona, har seda naji zuciyata tayi sanyi sannan na hakura, a wannan lokacin muka fara exams na shiga final year.

2

AyshatuuuTunda muka fara exams na maida hankalina kacokan, na share duk Wasu Abu da zasu kawo min tsaiko akan exams din amma dake Allah shi ke handling komai, kuma bazakai cheating nature ba. A karshe dai I break the record, seda na fadi wani course under paeds. Omomomo! Nasha kuka Kamar zanyi hauka, saboda na tabbatar damuwar da nake ce ta sani a ciki. Abba was the only one that supported  me amman su Yaya Halifa Kamar ya dakeni, yace na zauna wasa abinda banyi a baya ba shi nake kokarin nayi Yanzun, to nasani karatunnan shi kadai ne rufin asiri na. Dama a gidanmu idan kaga ana yaba maka,  to sailing Kake successful amma da zarar Ance you failed babu Wanda zai bi bayanka.

Naji haushi Dan Hatta Adda Sa’ada wannan karan bamuyi da dadi da ita ba, hakan yasa na dawo hayyacina Naga Meye nakeyi? Kashe Kaina zanyi saboda wani namiji, Wanda ya manta abinda ya faru gaba daya, shi Yanzun house job dinshi Ya gama gaba daya, ya fara residency bayan nan aurenshi Zaiyi, to ni Meye na rike wannan abin cikin zuciyata? Nayi dwelling a rayuwar da ta riga ta wuce. A lokacin na kara fahimtar wani abu da son zuciya ya hanani gani, shi ne Suleiman bai yaudareni ba, ni na yaudari Kaina, ni nayi hurting Kaina, tunda shi baice yana sona ba, yasan ina sonshi to me zai min? Zaice Asma’u daina sona? Bazai yiwu ba. At the spot nayi making mental note cikin kaina akan wannan abin, wannan Maganar ta wuce Har abada sede a hira.+

Nayi Karatu kamar babu gobe, Dama six weeks ne favor din kayi resit, kuma Alhamdulillah Inayi nai making, na zama final year medical student. A lokacin shirin bikin Nadiya da Yaya Suleiman yayi nisa sosae, amma saboda postings, Karatu ga kuma project yasa banyi wani active perticipation a shirin ba, sede duk abinda akai to zata kirani ta fada min, Haka ta bangaren Yaya Suleiman din duk ankon da muka fitar shi ya siya min.

Biki saura sati uku aka gama hada Lefe, Ummaah tace Nazo na gani kafin akai, koda zanyi recommending a kara wani abun. Yaya Suleiman yazo Ya daukeni shima bayan Ya gama aikinsa. Tunda muka gaisa bamu Kara magana ba, seda Nadiya ta kirashi tana tambayarshi Ko muna tare ta kirani ban dauka ba, to ya bani, bani Yayi mukai magana sannan nai mata sallama. To wannan ya bashi space din yimin magana, itama random talks ne kawai har mukaje gida.

Gidan da mutane sosae, familyn Baban Yaya Suleiman sunzo ganin kaya, dan haka dakina kawai na wuce nayi wanka sannan sun tattafi naje gurin Ummaah,

“Ummaah Sannu da gida”

“Doctor ta karaso, Sannu ya Karatu? “

Ta fada tana min murmushin dake healing zuciyata, akwatin na janyo Ina dubawa muna hira da ita, seda na gama tas sannan nace

“Ummaah, kayannan Sunyi kyau sosae, Allah Ya sanya alkhairi yasa ayi taro lafiya! “

Kaina ta shafa tace

“Amin Autar Ummaah, saura naki kuma ko? “

Murmushi nayi Ina maida kayan cikin trolley, amma karkashin raina Amin nake amsawa, gyara zamanta tayi tace

“Kinga baifi watanni bakwai Ya rage miki Ki kammalla karatunki ba, kiyi kokari ki saurari masu nemanki, nasan Inna Ade tayi Shiru da Maganar ne amma da zarar kin gama zata dawo da zancenĺ”

Kaina na gyada nace

“Inshaaa Allah Ummaah”

Dan abar Maganar auren kawai se na Fara mata labarin Project dina da nakeyi akan CKD (Chronic Kidney Disease) gaba daya ta bani hankalinta, ina mata bayani tana kara min bayanin Wasu abubuwan. A matsayinta na project coordinator a department dinta. A Haka Abba ya dawo daga gona, mukaje tare na mishi Sannu da zuwa sannnan na barta acan  ni kuma na tafi gurin Yaya Halifa.

Lokacin biki yazo, dukda ba wani armashi Yayi ba, kasancewar bikin maza ne amma dukda hakan saboda yawan danginmu naji dadin bikin, kusan duk taron a gurin Nadiya nayi shi. Seda aka daura aure sannan na dawo gida, Dan Ummaah tace min Dani zaa dakko Matar Yaya Halifa daga Dutse. A motar Adda Sa’ada muka tafi, munata hira Har mukaje, mutanen suna da kirki, sun karrama mu, muka dakko Sister in-law muka taho da ita kano. Unguwa daya Nadiya da Adda Zannira matar Yaya Halifa, gidan baifi 50miles away ba, haka suke.

STORY CONTINUES BELOW

Rayuwa tana tafiya da dadi da babu dadi, amma dole duk yadda Tazo Haka zakai embracing dinta. A rayuwata na fuskanci kalubale da yawa daga gurin mutane da dama, Harda Wanda ban taba tunanin hakan ba. A Yanzun idan Bakayi aure ba, mutane kawai gani sukeyi Kaine baka so ba, Kaine Baka maida hankali ba. Ya Ilahil alamin! Ya Zakayi? Zakace dole se kayi aure lokacin bai zo ba, A’a aure da mutuwa lokaci ne, idan lokacin baiyi ba, Baka isa kayi ba.

Na kammalla karatuna at a very tender age, gaba daya shekaruna ashirin da uku na karba licence dina under Medical and Dental Council of Nigeria(MDCN, na zama cikakkiyar Medical doctor, ranar da nayi taking Hippocratic oath dina, ranar atttestation nayi farin ciki, nayi murna Kamar zanyi me, na Kalli ilahirin family na da suka zo, ai da kyar bakina ya budu nake karanto oath din. Muna gamawa na fito akai photo session, Yan gidanmu anata rungumeni a Haka muka gama na cire graduation gown din na rataya, cikin yan set dinmu naje mukai hotuna, Dan Wasu ba lallai ku Kara Haduwa dasu ba.

Muna komawa gida, na nufi dakin Inna, tana zaune gefen katuwar katifarta, ko sallama banyi ba na mika mata hannu nace

“Mun kunce ni dake, har na gama makaranta, na zama cikakkiyar Likita amma baki zo tayani murna ba. Na daina kawar dake. “

Tabe Baki tayi tana bina da wani kallo, Wanda bansan me yake nufi ba tace

“To se me Dan banje ba? Da dai aurenki ne da ni ce kan gaba “

Dariya nayi naje na zauna gefenta nace

“Kawata ta kaina, Karki damu ina dawowa daga service zanyi aure da izinin Allah”

Baki a bude tace

“Wani karatun ne kuma, ke Kinci ubanki, so kike se kin tsofe kafin kiyi aure. To babu inda zakije, miji zaki kawo ayi miki aure. “

Dariya na karayi nace

“Inna ba Karatu bane, maida wukar, bautar kasa zanyi. Kuma banda abinki aure ai lokaci ne….”

“Maganarki kenan kullum, aure lokacin ne, ki kalla sa’annin ki dukkansu Sun yi aure, Rayhana ‘Ya’yanta biyu amma ke kinata gantali”

Ta katseni, “Gantali” na maimata, se kawai nayi Murmushi nace

“Kawa kenan, ni bana fada da Kawata bari naje, idan kina son wani abu se kiyi min magana”

Daga Haka na mike gaba daya raina a jagule, saboda abinda Inna tace, Rayhana sa’a ta ce quite sure, amma lokacinda aka rubuta mana kaddara dole kowa road din da zai bi, daban take. Me yasa mutane basu gane komai MUKKADARI NE ba. Da Ummaah na Fara haduwa dake ta Tara mutane se shiga take tana fita, seda nace ta bari idan an kwana biu ayi walimar amma tace gwara tayi rana daya.1

“Na zata kin shirya, mutane na jiranki fa”

Kaina kawai na gyada nace

“Yaznun zanyi”

Juyawa nayi zan tafi daki Ta kwalla min kira na dawo, kallona tayi tace

“Akwai wani abu ne? Naga fuskarki tayi ja “

Taba fuskar nayi sannan na kirkiro Murmushi nace

“A’a Ummaah gajiya nayi, Bari naje”

Saurin Juyawa nayi saboda jin idanuna sun cicciko da kwalla, Se naji tace min

“Today Issa happy day, don’t let anyone destroy it. “

Kaina na gyada na tafi dakin, Adda Zannira ce a kwance da katon cikinta, ta saki fanka, zama nayi gefenta nace

“Adda Zanni, duk gajiyar ce”

Dagowa tayi ta kalleni tace

“Bari dai Adda Asma’u, Babyn ki ya takura min, na kagu Ya fito na Baki abinki. “

Dariya nayi tareda mikewa nace

“Kaji Adda Kamar gaske, Se Kinji zafin labor Kice kin fasa”

Dariya tayi tayi har na shiga wanka, Ina fitowa na shirya cikin wata red Abaya da Adda Habiba ta kawomin as gift, muka fita bayan nayi kwalliya akai ta hotuna. Se Washegari na samu damar bude gifts din da aka kawo min, yawancin duk gifts din daga yan gidanmu ne, Delivery kits, BP app, forceps da sauransu. Naji dadi sosae, kowa na bishi da text din godiya.

Ina kwance a daki sati daya da graduation dina, Inata tunanin Yanzun kuma Ina zaa fada, posting anyishi kuma Anyi posting dina Yobe state. In the next 2 weeks zan tafi. Shigowar Ummaah tasa na mike, kafin nayi magana tace

“Dakko Hijab dinki kizo”

Zan tambayeta lafiya naga ta juyar da kanta hakan yasa na mike na dauki Hijab din na saka muka fito, tunda naga Munyi dakin Inna Ade naji gabana Yayi mugun faduwa, tunda nake da Inna bata taba zuwa gidanmu tayi fin kwana uku ba, amma wannan karan kwananta goma sha biyu bata tafi ba, hakan ya tabbatar min da she’s up to something kuma tabbas akaina ne, Dan ta dauke min wuta, nima bana son case hakan yasa na tattara ta na watsar da ita.

Tana zaune kan katifa, tana murza goro a magogi Tana afawa a baki, nida nafi kowa saninta nasan wata tsiyar zatayi, sallamar da Ummaah tayi yasa ta juyo tana kallona, Nima kallonta nake se ji nayi tace

“To Zuwairiyya (Uwarta kenan!) da kikai tsaye dukana zakiyi? “

Da sauri Abba ya juyo yace min

“Asma’u come and sit here”

Jikina a matukar sanyaye na nufi gefenshi na zauna ina kara tantamar Anya Inna ce, ni tayi addressing da Zuwariyya? Ban gama tunanin hakan ba naji tacr

“Ke Asma’u, dago ki dubeni, idan wayannan mutanen sa’anni Ki ne, ni ba Abokiyar wasarki bace, Dan kin Raina mu zaki ce bazakiyi aure ba…. “

Da sauri na katse ta nace

“Inna yaushe nace bazanyi aure ba”

Abba ne yace

“Kar naji Bakinki! “

Shiru nayi amma a raina Ina ayyana ni Asma’u Fara Yar Shehu, Inna take dagawa murya Haka? Bazan iya tuna last time da ta kirani da Asma’u ba, I can even say she never, kawai cemin take Fara ‘Yar Shehu, Ta gaban goshin ko kuma Kawata. Amma yau Inna Ade ke cemin ita ba tsarata bace, kawai se naji hawaye sun Fara min zarya, kaina ya mugun Sarawa saboda bala’in da take. A karshe tace babu zancen zuwa Yobe!

1

Awnnnnnnnnnnnm……. A page is here, to all my followers I say Kumaya!

One word for

Fara ‘Yar Shehu

Inna Ade

1

AyshatuuuHannuna nasa na goge fuskata Dan banga dalilin kuka ba, idan tun Yanzun Ina kuka to nan gaba kukan jini zanyi kenan. Nida Ummaah ta sallama, hakan yasa na mike na fito, kitchen na wuce na fara dama custard Dan inason na Fara sabawa da irin wannan abin, Ummaah ce ta biyoni taga ina kokarin Dama custard amma ya tsinke saboda bana cikin nutsuwata. Hannunta tasa ta dafa kafadata tace

“SABR! Asma’u, komai kika ga yana faruwa da bawa da sanin Allah. Kiyi hakuri “

Dan Murmushi nayi nace

“Ummaah babu komai, bari naje daki”

Tare muka fito da ita, daidai fitowar Abba da Inna, bakinta har kumfa yake saboda balai, Jakarta ce a hannun Abba hakan yasa na karasa na karbi Jakar sannan nace

“Inna tafiya zakiyi? “

Kallona tayi sannan tace

“Tafiya zanyi Kawa, yaushe zaki zo? “

Kaina na girgiza nace

“Babu rana,”

Daga Haka muka karasa Mota mukai mata sallama, ta shiga sannan driver ya tada motar se Kwalam. Dukkanmu haka muka tsaya har aka maida gate aka rufe amma babu Wanda ya matsa a gurin, kowannenmu tunanin zantukan Inna ke yawo cikin kanmu, Se can Abba ya juyo Ya kalleni yace+

“Asma’u let’s talk”

Wucewa yayi dakinshi, nima na bishi yayinda Ummaah ta tafi daki. Yana zaune a Kan carpet na sameshi, yayi shiru not like my Police Father, duk Yayi Shiru fuskarshi looking pitiful, Se naji na kara takura, naji gaba daya Sauran space din dana bari a zuciyata Wanda Banji haushin Inna ba, baki daya se ya zamana duk ya turnuke ni, har ni kaina haushin Kaina nake ji, at least da nayi auren da ban jawo musu magana ba.

Zama nayi gefenshi nace

“Abba Dan Allah kayi hakuri, Inshaaa Allah zan kawo maka miji na…… “

Se na kasa karasawa saboda wani irin kuka da ya kubce min, kaina na durkushe Inata kuka, inajin yadda zuciyata ke wani irin zafi, na kasa ci gaba da Maganar seda Abba ya dafa kaina yace

“SABR! My Daughter. Ya isa hakan”

Sheshakar a hankali ta dauke min, hawayena na share na bude baki zanyi magana ya girgiza kanshi yace

“Saboda Bakiyi aure ba se ya zama laifinki? Ba laifinki bane, haka Allah Ya kaddara miki, babu Wanda ya tsallake kaddararshi. Koda zaki kara shekara goma a gidannan Bakiyi aure ba, I’ll say nothing. Bake kika hallici Kanki ba, shi daya halliceki yasan tanadin da yayi miki. So Karki kara kuka akan hakan, zakiyi aure amma se lokacin Yayi. And for Yobe, you have me, you’re your fathers daughter Bazan iya hanaki ba. Inna Ade zata sakko Kinji? “

Kaina na gyada ina Dan Murmushi saboda words dinsa are more of Opoid Analgesic (Pain reliever) a take sukai relieving duk wani bakin ciki da zuciyata ke ciki, a take naji wani karfin gwiwa da nutsuwa ya sameni. Bai barni na tafi muka zauna munata hira, gaba daya hirar yana sighting mini examples ne na rayuwa. Most thing da yayi capturing zuciyata shi ne da yace min

“Kinga Asma’u aure ba farilla bane, amma Sunna ce me karfin gaske, a wani gurin saboda Allah yace idan kayi aure tamkar ka cika rabin addininka ne, so kinga akwai falala sosae a aure. Kuma a society dinmu sun daukaka aure sosae da sosae, suna ganin mace is not complete without aure. Eh wani lokacin Haka ne amma kin tuna tarihin Nana Maryam Mahaifiyar Annabi Isah (AS). Batayi aure ba amma a kur’ani Sura guda ce da ita, so kinga zuciya is everything that matters. Ki maida hankalinki akan yadda zaki gyara lahirarki, aure zaizo sede idan lokaci baiyi ba “

Shikenan kuwa na samu lafiya, na wartsake na Fara shirin tafiya Camp. Wani yammaci na tafi gidan Rayhana bayan nayi sallar laasar, ita daya na samu a gidan ta gama aiki ko wanka Batayi ba, Yaran ba sanan sunje gidansu Abdul a sharada. Seda na zauna sannan tace

STORY CONTINUES BELOW

“Gwara da kika zo dama nemanki nake”

Zama nayi nace

“Kiyi wankan mana tukunna se muyi Maganar “

Tashi Tayi ta tafi toilet dan yin wankan, tamkar ana jira kawai se wayarta ta Fara ringing, hannuna na Kai na janyo ta, se naga Nabila cousin yana yawo akan screen din, hakan yasa na dauka amma kafin nayi sallama Se naji ance

“Haba darling, tun dazun nake jiranki amma baki hau whatsappp din ba, balle na samu naga pictures din ko sa rage min wani zafin, kuma nasan Abdul ai ba yanan”

Shiru nayi na kasa fahimtar me ake fada me kuma ake nufi, me yasa nake jin muryar namiji bayan sunan Nabila ne a jiki? Me yasa namiji da ba Abdul ba yake kiranta da darling….

“Baby are you there? Talk to me mana”

Ajiyar zuciya na sauke tareda sauke wayar daga kunnena na kashe gaba daya, zuciyata wasu irin wasiwasi take min, Se contemplating nake a Haka Rayhana ta fito, tayi kyau abinta, kamar asalin rayhanata amma se naji Kamar na rufe ta da duka, gaba daya haushinta Ya lullubeni, is she having an extra marital affairs kenan. Tabanin da tayi yasa na dago tareda mika mata wayarta nace

“Nabila cousin ta… “

Bata bari na karasa ba tace

“Kinyi picking, me kika ji? “

Gaba daya ta gigice hankalinta yayi mugun tashi Wanda hakan ya tabbatar min batada gaskiya, idanuna a kanta nace

“Nayi yace yana jiranki ki tura mishi hoton da zai rage masa zafi, ray…. “

Da sauri ta katseni Tana fadin

“Ba abinda kike tunani bane wallahi Sister, he’s just a colleague, tare mukai service dashi”

“I didn’t ask for all this and yet you are telling me, Rayhana me kikeyi dashi, da aureki da mijinki kike having affairs? Rayhana”

Kusa dani ta dawo tare da riko min hannuna tace

“Asma’u ki rufa min asiri, nima nasan ban kyauta ba, nasan abinda nake Haramun ne amma na rasa yadda zanyi”

Wani kallo nayi mata me cikeda bacin rai, nace

“Bakisan yadda zakiyi ba? Is this an excuse. Ke musulma ce and I’m sure Kinsan hukuncin abinda kike aikatawa”

Kuka ta Fara tana fadin

“Na sani Sis, amma banida option wannan ne kadai abinda nake ganin Zaiyi saving aure na. Idan na kalleki birgeni kike saboda Baki San the hell dake cikin aure ba, baki san bakin cikin dake cikin shi ba, nasha ayyana inama zaai overturning agogo, ya koma baya, I’ll never have chosen Abdul, I regretted that. “

Gaba daya se ta Fara bani tausayi, naji haushinta da nakeji ya Fara wucewa, hannunta na rike nace

“Is ok Rayhana, amma ko me Abdul yayi path din da kika bi bamai bullewa bace, halaka zakiyi, kinga kenan kin tashi with nothing, Babu duniya babu lahira even an ounce of pride babu.”

Hawayenta ta share tace min

“Kinji dadi Bakiyi aure ba, Nazo zan fada miki wannan abin. Tun muna secondary nake son aure, Kinsan Dalili? Saboda I’m thirsty, I want someone to quench that thirst for me, Inada strong sexual desire, zan iya ce miki dalilin aurena kenan. Abinda na fahimta about aure shi ne, Backbone na aure is sex, komai zaayi miki a gidanku amma babu me iya miki wannan se Kinyi aure, the new thing about aure shi ne sex, what about you are deprived of that? Ya kike ganin zaayi kenan? I was innocent and illiterate about it, Abdul tasted that thing to me Se dana saba nasan dadinshi sannan ya nuna he’s not in need, se ya koma a wata, we will have affair sau daya, Ina zan iya, nayi korafin, nayi Maganar, tun ina kunya Har na fito Asma’u nayi mishi barobaro amma yaki fahimta. Aurena zan kashe? Ina ganin Kamar dalilin yayi kadan Yasa nayi hakan, shiyasa na komawa Jabir dina. Nasha zuwa da niyyar fadawa Mama amma se tace, what matters shi ne na rike sirrina, kada na tonawa mijina asiri, kuma no matter what I’ve to save that marriage Dan shi kadai ne Gata na, bata taba saurara ta ba. Kece kadai kika bani hearing ears, Nagode “

Ni Kaina seda hawaye ya zubo min da ta gama fada, hannunta na kama nace

“I’m sorry, amma dukda haka baki nemawa kanki solution ba, me yasa a aure akai Waliyyi, run to him, tell him ga matsalarki. Kina ganin sex deprivation Yayi kadan ya kashe aure? Kinyi kuskure Dan a karshe zakiyi dana sani marar amfani, Rayhana quit all this games and tell them, ki fada musu matsalarki, kiyi istigfari, kiyi Tuba, tuba na gaske Wanda bazaki koma laifinki ba, Allah kadai zai daidaita rayuwar aurenki. Kiyi hakuri “

Tunda na dawo gida bayan na baro gidan Rayhana, na kasa nutsuwa, na rasa tunanin me zanyi. Dama idan Kai auren bashi kadai bane karshen matsala, who will ever think Rayhana da Abdul will end up in such a mess?

AyshatuuuYOBE,  POTISKUM.

Abba da Ummaah, su suka rakoni har Potiskum inda anan NYSC orientation camp din yake, bansan yadda Abba ya shawo kan Inna Ade ba, amma nasan ya cika min alkawarin da yayi min akan Zanje Camp, gashi alkawari Ya cika. Tare dasu mukaje akai clearing dina da dukkan Wasu formalities sannan kuma mukai sallama suka juya.

Camp life was hectic amma it’s something memorable that happens once a rayuwar mutum. Sati biyu da nayi na rame ga lokacin ana Rana, nayi baki, gani Inada Dan wahalar sabawa da mutane, se ya zamana mutum daya muka saba da ita wata A’isha Kyaftun yar Gumel ce ta Jigawa State. Ita dinma dalili ne ya kawo hakan. Har nayi sati bana shiga harkar kowa, roommates dina dukkansu Christians ne so kullum sede mu gaisa kowa ya kama gabanshi.

Ranar Saturday mun kammalla dukkan abinda Zamui naje wani eatery zanci Abinci, Nazo entrance din naji wani yana fadin

“Kyaftun! Kyaftun!! “

Ko Juyawa banyi ba, na cigaba da tafiya ta amma se yazo yasha gabana yana fadin

“Amma Kinsan tun yaushe nake jiranki? Kinzo kuma kin wani bata rai kin wuce”

Juyowa nayi na kalleshi, shima kallona yake, dogo ne sosae Dan duk tsayina se na ganni dwarf a gabanshi, fuskarshi doguwa ce kuma komai dake cikinta Manya ne, ga uban saje daya aje, Wanda zaisa ayi mistaken dinsa a matsayin wani Babban mutum. Gaba daya analysis din nayi shi cikin nanosecond ne.+

“May be you are talking to the wrong person”

Na fada masa Ina kokarin Juyawa na shiga ciki amma, Se naji wata murya irin tawa tace

“Zayyan! Kana ta jirana Ko? “

Juyawa nayi na Kalli me Maganar, seda gabana ya fadi saboda yadda fuskata take a Kan tata, baki bude nake Binta da kallo haka itama take ta kallona, se shi Zayyan din ne yace

“Allahu Akbar! Set of twins from different uterus. “

Kallonshi mukai a tare sannan ta miko min hannunta, take na zura nawa, instead mu shiga cikin Eatery din se kawai muka nufi wani karkashin bishiya muka zauna, Zayyan Ya tafi siyo mana juice. Hannunta ta bani tace

“A’isha Kyaftun Ismail, daga Gumel, Jigawa state amma a kano muke”

Kaina na gyada nace

“Nice to meet you, Sunana Asma’u Shahada Kwalam, yar Jigawa ce ni”

Murmushi ta karayi daidai dawowar Zayyan, hannunsa da Fanta biyu, coke daya, ya aje sannan ya zauna yana fadin

“Ban taba ganin Kama irin wannan ba, Anya ku din ba Twins bane aka samu akasi kuka rabu”

Dariya nayi, Kyaftun tace

“Ka Faye surutu matsalata da kai”

Kaina na girgiza nace

“Ni Kaina nayi mamakin ganinki, ban taba tunanin akwai irin mutanen da Baka hada komai dasu ba amma kana kama dasu Har haka”

Kanta ta gyada tace

“Seda na tsorata fa Asma’u, I never knew such is real! “

Daga Haka mukai ta hira Har na manta cewa Yunwa nakeji. Daga wannan ranar muka zama kawaye da ita, bacci kadai ne ke rabamu da ita, a gidanmu kowa yasan labarin Kyaftun haka nan nima labarina yaje gidansu. Lokacinda muka fito a camp, munata shiri nace

“Kyaftun kada Ki Kira kowa, zaa zo daga gida a daukemu “

Aje Jersey din hannunta tayi ta maida hankalinta kaina tace

“To, har Se anzo daukarmu Twin?”

Gyada Kaina nayi nace

“Eh mana, Bazan iya komawa da kaina ba ai”

STORY CONTINUES BELOW

Dariya tayi tace

“Small Baby, Nan da Kano ai ba big deal bane. Zamubi commercial car ni da kaina zan fadawa Ummaah haka”

Bata jira abinda zance ba ta kira Ummaah, har sun saba dan Twin batada duhun kai ko kadan , she’s a wise person sosae.

Haka na hakura Washegari muka tafi Tasha Inata jina a takure, Twin se dariya takeyi min tana tsokanata Fathers girl. Seda mukaje Kiyawa sannan Wasu passengers suka sauka, a Dutse aka Kara cika motar. Tunda muka dauki hanya na kwantar da kaina a kafadar Twin na Fara Bacci seda muka shigo Kano sannan ne ta tasheni, wata Ajiyar zuciya na sauke bayan na hango Birni, home sweet home na ayyana cikin raina. Muna sauka muka harhada kayanmu guri guda, Kyaftun taje samo mana Napep. Sallama naji a gefena hakan yasa na juya, tareda amsawa amma a ciki ciki, bakina daya motsa kawai ne zai fada maka nayi magana.

“Sunana Salis, ke fa? “

Kallonshi nayi nace

“Bashida amfani hakan”

Ina fadar Haka na tsugunna ina gyara Trolley Twin. Maimakon ya tafi se ya gyara tsayuwarshi yana fadin

“Tunda ni na tambaya ina ganin it’s important, so let me know “

Dauke kaina nayi, zuciyata tana fada min I shouldn’t miss the chance, wannan shi ne lokacinda ya kamata kiyi saurayi, ban gama tunanin ba balle nasan hukuncin da zan yanke Twin ta dawo, kawai Salis Ya juya gurinta tareda yi mata bayanin abinda ya faru, take ta karanto masa home address dinmu, number ta da sunana, Dama tun acan Potiskum ta fahimci banda saurayi, tayi mitar tareda fadin ita ta Yaya zata iya rayuwa babu opposite gender, ai masifa ne kayi sati daya bakaji muryar Wanda yake kallonka as something special ba. Daga Haka muka wuce shi ya bawa me Napep din kudin sannan Twin tayi masa godiya, tunda muka dauki hanya nake mitar ta zubar mana da mutunci, ta bari an biya abinda ya kamata mu biya, Tsaki kawai tayi tace is not like ya siye mune, is just a token of appreciation na bashi access da abinda yake so. Twin kenan duk ta inda na fito tasan yadda zata bullo min, ban taba wining akanta ba, so wannan karan bakina nayi bam dashi.

Gida muka fara zuwa Dan Dama alkawarin da tayi min kenan. kowa seda ya Jinjina halittar Allah. Seda muka ci Abinci muka huta sannan na tafi nida Adda Meeyna rakata, har gidansu mukaje, iyayenta masu kirki sede rayuwar gidan is far different from ours, zaka iya saka su a low social class amma kuma irin contented mutane ne, a zamana da ita bazaka tantance wani class suke ba. Allah yasa Nursing tayi abinta, tana da guarantee aiki.

Salis Mutumin Ingawa ne ta Katsina state, ko cikin muryarshi zaka dinga jin accent dinshi na yan can ne. Architecture ne so yana aiki da wani construction company a can Katsina. A yadda yayi min bayanin kanshi Bashida aure, amma yana kokarin yi. Hakan yasa na Fara sakin jikina dashi , Mussaman da yake na gaji da zama ni daya, wannan loneliness din ya isheni. Satina daya a gida na tafi Kwalam gaida Inna saboda ni Bazan iya fushi da ita ba. Kafin naje seda na biya gidansu Twin na gaida Innarta sannan ta rakani Tasha na wuce, nima na Fara yin abu da kaina. Se yamma na isa Kwalam, Ina shiga gidan tana zaune dokin kofa tayi Baki, bata lura Dani ba Har seda na karaso ciki sannan tace

“A’a Likita Bokan turai! “

Da murmushina na karasa gurin ina gaida mutane sannan na zauna Kan karamar kujerar da tasa aka kawo min na zauna muka gaisa sannan na wuce dakinta, Ina shiga Salis yana kirana, rabona da muyi waya dashi tun kwana biu da suka wuce, he’s not a frequent caller Nima kuma idan ya kirani na dauka idan bai kira ba yasha zamansa saboda bana son repeating mistakes dn da nayi a baya.

“Ran gimbiya Asma’u ya dade! “

Dan Murmushi nayi nace

“Tare da naka “

“Yanzun na shigo Kano Se nace bari dai Nazo naga Asma’u”

“Ayya! Nagode, amma ni kuma bana gari naje Kwalam”

Daga Haka baice zai zo ba, ya tsaya mukai random talks dashi, har Inna ta shigo jin yadda nake ta Murmushi tace

“To Siriki yazo kenan? “

Ban kulata ba na cigaba da maganata, Ashe yaji muryarta, muna gamawa yace na Kai mata, ni kuwa banyi musu ba na mika mata sannan nasa kaina na fita a dakin. Koda ta gama batace min komai ba Haka zalika Nima.

Washegari tun sassafe naje nayi yan gaishe gaishe sannan na dawo na kwanta, wajen daya nayi sallah nayi wanka sannan na shirya, tunda na tashi Inna take ta kaiwa da kawowa, seda ta shigo nace

“Inna me kikeyi ne”

Murmushi tayimin tace

“Bako zanyi”

Kaina na gyada na cigaba da kallon wani Korean drama Romantic Doctor cikin system dita. Se wajen Karfe biyu naji sallamar Salis, da farko ban yadda ba gani nake kawai hallucinations ne, amma Se naji Inna sunata gaisawa, kashe kallon nayi na sakko daga gadon, hijab na zura na fito, shi dinne kuwa a zaune shida wani ina tunanin friend dinsa ne. Mamaki sosae Ya cikani, sallama nayi hakan yasa suka dago suna kallona, Salis se Murmushi yake min shida Inna, zama nayi gefen Inna na gaishesu sannan nace

“Haka zuwa babu sanarwa”

Kafin ya bani amsa Inna Ade tace

“Naga ana rowarshi shiyasa nace yazo na ganshi”

Kaina na gyada nace

“Naga alama kuwa! “

Mikewa nayi zan koma ciki, Inna tace

“Fara yar shehu ina zakije kuma? Kizo kui hira mana”

Kaina na girgiza nace

“A’a ai wannan ba zuwana bane, zuwanki ne se kui hirar “

Abokinne Yayi dariya yace

“Alama ta nuna Doctor kishi take, Inna ki koma ciki kada kisa ayimana fushi”

Harara ta Inna tayi sannan tace

“Ni fita zanyi ma, ki dawo kui hirar”

Juyawa nayi na koma muka zauna munata hira, har suka ci Abinci sunata hirar kyan halayen Inna, Nidai a raina Murmushi kawai nakeyi, Dan Inna ba abar yabo bace.

Ayshatuuu”Thank you sir!”

Kawai nace mishi ba tareda na bari kalamamsa sun shiga kaina ba, nasan I’m skilled person duk wanda yayi aiki dani komin yadda ya kware to tabbas se yasan nima na maida hankali. Cikin lounge yaje ya zauna aka kai masa folder yayi documenting sannan ya yiwa kowa bangajiya kafin ya tafi, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan na fita baki daya daga OT. Ward na koma na karasa ayyukan da suka kamata nayi sannan na tashi gaba daya.

Washegari ranar friday, muna kammalla ward tounds dinmu na shirya dan tafiya kano a raina ina tunanin ya kamata yau ba se gobe ba na fadawa Abba kudirina. Misalin karfe uku na isa gida saboda na biya gidan Adda Maryam da nayi niyyar se yamma na koma gida amma ta bata min rai shiyasa na taho. Ina gidan kanin mijinta wani Nasir yazo, that wasn’t the first time dana hadu dashi a gidan sede baifi sau daya muka taba magana ta minti uku dashi ba kullum daga gaisuwa bamu karawa saboda naga dan raijin wayo me, ni kuwa bana cikin wannan class din. Tunda ya shigo muka gaisa naja mutuncin kaina na cigaba da kallona sunata hira shida Adda, can sega mijinta ya dawo, Yaya Mansur muka gaisa ya zauna yana ta jana da hira dake he’s very jovial to tamu ta zo daya dashi.+

“Kina wuta fa matar nan, nazo kofar gidana naga wata benz, so inata tunanin wa muka samu? Seda na hango wannan ear piece din naku kafin na gane ashe kece”

Dariya nayi dan Na fahimci stethoscope yake nufi, nace

“Babu wani wuta fa Yaya, amfani ake da dama”

Murmushi yayi ya gyada kai yace

“Yeah! Allah ya kawo miji na gari”

Amin na bashi amsa ina murmushi, kallona Adda tayi tace

“Kamar gaske”

Ko kulata banyi ba  tashi tayi ta wuce ciki itada yayan, bata jima ba ta dawo hakan yasana wuce kitchen akan na duba abinci dan a daura wani, idan naje gidan sisters dina se nayi musu dinner nake tafiya. Kamar daga sama naji Adda Maryam na cewa Nasir

“Kaima kaki kayi aure kamar Asmau, ko baka da budurwa ne?”

Shiru nayi inason jin amsarshi se yayi dariya yace

“Kai time baiyiba, se an tara tukunna”

Gyara zamamta tayi tace

“Kaga Asmau shes 27 years yanzun, gata medical doctor, babu wani serious magana akanta, bana tunanin tana da saurayi gaba daya so idan tayi maka why won’t you tag along kuyi aure”

Idanuna na lumshe jikina har bari yake na rufe warmer da sauri zan fito kawai naji yadda gayen yake babbaka dariya hakan yasa na tsaya, naji yace

“Kina da abubuwan dariya Antinmu, ni wannan kanwar taki ai ta girmeni ma……in a mocking way ya fada, se naji kafafuna sunyi wani sanyi…..27 kikace? Tabdi! Beside ni fa bazan iya auran health workers ba ke wallahi ko a kafa aka daura min su se na kunce”

Tamkar walkiya haka na ganni a  parlon, wani irin mugun kallo na masa nace

“Ai ko maza sun kare nafi karfin na aureka, Adda na gode”

Daga haka na dauki jakata dama veil dina tuntuni yake a jikina nayi waje na barsu baki a sake, mota ta na bude na shiga se kuma nayi shiru ina ganin menene abin fushi har haka? Me yasa raina ya baci dan anyi talla ta, tunda auren yaki zuwa may be kilan ta hakanne zan samu miji. Zuciyata se ta kasu biyu wata na blaming dina wata na tafarfasa tana ganin an raina min hankali ajina ya wuce ayi kamar ana nanawa namiji yana kin karba.

Ina gama parking sega Yaya suleiman, tsayawa yayi yana kallona ni at first ban ma wani lura dashi ba kokari nake na bawa Baba me gadi key din ya shigo da kayan da nazo dasu. Ji nayi yace

STORY CONTINUES BELOW

“Ajhumma!”

Nasan shi daya ke kirana da wannan sunan hakan yasa na dago fuskata a sake na dubeshi nace

“Oppa”

Se naji na tuna da, kamar yadda oppa yake nufin Yaya a korea, yawanci suna fadawa saurayi hakan, tone din da suke using kadai kasan cewar bawai brother yake nufi ba aa sede something else. A wancan lokacin I’m feeling the same, lokacin dana fada se naji wani sanyi a raina but see me today, saying oppa plainly and emotionless rayuwa kenan. Yaya suleiman da naso na kaunace and so much badly wanted na zama mallakinsa amma ya dubi idanuna yace kawata yake son nayi hooking dinsu tare, i felt shattered. That’s then!

“Ya aikin? Kinyi kudi kin manta damu, kullum Nadia tana cigiyarki ko ziyara baki kawo mana”

“Aiki sede godiyar Allah. A gaida Nadia da yara”

Na fada saboda zancen babu ziyara ba mutum daya le zumunci ba both parties keyi, bantaba tunanin zan rabu da raihana da Nadia ba Amma yanzun ni ko numbers dinsu bani dashi. Duk yadda Yaya suleiman yaso na tsaya na nuna masa a gajiye nake dole hakanan yayi hakuri na shige gida. Ummaah Na parlor a zaune itada Asiya na shigo, Asiya ta rungumeni sannan ta bamu guri. Gaisawa nayi da Ummaah tace

“Ina kika tsaya? An shigo da kaya amma ke shiru”

“Nida Yaya suleiman na tsaya”

Bata kara cewa komai ba haka nima se na mike na wuce na tafi dakin Inna, tana zaune kamar kullum ana goga goro. Karba nayi kamar yadda na saba ina gurza mata muna dan taba hira abin mamaki. Hirar arxiki kuma wadda na jima bamui nida ita ba. Tana ta bani labarin ‘yan matancinsu ita da fara yar shehu

“Naso Asmau fara yar shehu ta rayu zuwa wannan lokacin ta ganki. Kawata ce wadda banda kamarta kuma ko bayan data mutu babu wanda ya maye min gurbinta, da yake ita mahaifiyar ta yar Mambila ce to dukkan mu tafi mu kyau, kyakyawa ce ta gaske hakan yasa tun muna shekaru tara aka sakata a lalle, naso kin biyo farin jininta da tuni kina dakinki, da kuma ace shahada da Saude sun barki hannuna da tuni baki shiga wannan kuncin ba.”

Dan murmushi nayi nace

“Inna lokaci ne”

Kanta ta gyada tace

“Da farko nayi tunanin laifinki ne shiyasa na matsa miki, amma a shekarunki na san kowacec so take ta ganta dakin miji. Ina fatan baki rikeni a ranki ba”

Rungumeta nayi da sauri ina dariya nace

“Waye yake fada da kawar shi? Sede idan kawancen bai kai zuci ba”

A wannan na samu sauki, ranar aka tuna da tare muka kwana, Abba nata tsokanar mu wai yau mun hada kai. Da safe nayi dukkan abinda ya dace wanda ya kamata sannan na koma bacci. Wajen sha daya nayi wanka nasan Saturday ce Abba bazai je gona ba, dan baya fita Friday da Saturday he always say they’re meant for rest. Kuma haka yake. Yana zaune shida Ummaah suna kallon Aljazeera, yau mun samu bakuntar yaran Yaya halifa dana Adda ummiey so suma suna parlon se kinji suke. Ina zama muka gaisa yaran suka gaisa se Ummaah ta fita naji dadin hakan sosae a raina dama bana son tana nan bazata bari nayi magana cikin nutsuwa ba.

“Nasan wannan zaman akwai magana, ina jinki”

Abba ya fada yana rage volume din, zamana na gyara nace

“Abba kayi hakuri dukda baka taba magana ba amma nasan kullum yana ranka, nima ba haka naso ba Abba na kai har lolacinnan banyi aure ba”

Murmushi yayi min yace

“Asmau! Ai bake kika hana kanki ba, shima Allah ba hanaki yayi ba he’s testing our faith kin gane?”

Kaina na gyada yace

“So, ki dage da addua Allah baya bacci. Ban taba miki zancen aure ba, bawai bana so kiyi ba ko kuma irin ban damu dinnan ba, ko daya I’m worried, sede ya zanyi idan na takura miki me zai canza?..”

Kanshi ya girgiza yace

“…Nothing my dear, ‘ya’yana takwas kowanne is educated islamically and western, bakwai sunyi aure kowanne peacefully, ke daya kika rage idan na kasa hakuri me nace da Allah? Ban gode bisa abinda yayiwa ‘ya’yana bakwai ba. Kinsan musulinci is wonderful, komai is open sede idan baka sani ba. Aure abu ne me girma, sunnah ce me karfin gaske sede mu bamu dauka sunna bace kawai aure wajibi ne idan bakai ba gani ake kaika jawo amma i know kinsan tarihin Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S batayi aure ba amma sura kacokan sunanta ne, so bawai se kayi aure zaka samu yardar Allah ba kede ki tuna tarbiyar da nayi miki kawai, ki kare mutucinki da martabarki. I tried as much as i can na zama mutumin arxiki saboda ku, nasan ko bani da rai zaace wannan yaran CP Shahada ce, amma idan na zama mutumin banza akwai matsala abinda zai zama rightfully yours zaa iya denying muku.”

Se naji sanyi cikin raina saboda maganar shi tayi min dadi naji sanyi da farin ciki a raina. Gyara zamana nayi nace

“Abba na samu wata school a America, idan ka yadda ina son zuwa”1

Shiru yayi yana ta kallona har seda yasa na fara jin uneasiness, se yayi murmushi yace

“Zan iya yin tunani da shawara?”

Kaina na gyada nace

“Sure Abba”

“I’ll get back to you”

_I left you guys waiting and I’m so sorry for that. Nayi typing wannan breakfast din for you all, ina fatan I’ll get some mind blowing and awesome comments from you guys as always. Yeah! Ina ganin comments dinku na karanta but replying duka will be hectic y”all know that Nagode sosae Allah ya bar zumunci. Daga yau zanje hutu saboda my friend is getting married, pray please. Is an important biki da bazan iya typing ba har se naga na rakata dakin miji kafin na dawo nutsuwata. I hope zaku min uzuri as usual_

1

_*Yours Truly*_

Ayshatuuuu😍Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da naji ya tabbatar min it’s a no kenan. Hakan yasa na dangana ba tare da na kara masa magana ba. Wani sati na dawo na tarar da Ummaah ta cika fam kamar zata fashe dama wannan mood din kam ai na saba dashi. Tunda naga haka na kama kaina tareda jan mutumcina. Washegari inadakin inna muna hira ta aiko Asiya akan ta kirani. Ina zuwa na ganta a zaune gefen gado tana ta karkada kafa, zama nayi kan carpet nace

“Ummaah gani”

Key din motarta ta mika min tace

“Dakko hijab dinki zamu fita”

Babu musu na mike hannuna rikeda key din na tafi dakina, dama atamfa ce jikina dinkin skirt da riga so kawai se na dauki hijab coffee dake atamfar da coffee jiki, shoe rack dina na duba na dauki wani flat milk vine se purse sannan na fito , ganin tana jirana yasa ko Inna banyiwa sallama ba kawai na wuce gaba tana bayana. Seda nayi warming motar sannan nayi addua kafin muka fita. Kallonta nayi tana ta danne danne a wayarta nace+

“Ummaah ina zamuje?”

Dago idonta tayi ta kalleni, then ni kuma na rigada na maida hankalina akan titi tace

“Gidan Hajiya Zakiyya zaki kaini”

Seda naji kaina ya sara min baa taba matar da bana so a kawayen Ummaah ba kamar wannan matar, tana daya daga cikin masu zuga Ummaah akaina. Babu yadda na iya haka na dauki hanya amma bakina banda neman agajin Allah babu abinda nakeyi nasan shi kadai yasan abinda nake going through kuma shi zai kawo min dauki. A hanya na tsaya a filling station nayi mata full tank sannan muka karasa gidan. Ina parking nayi wining glasses din sannan muka fito, tana gaba ina baya muka shiga gidan, sunada kudi haka kishiyoyinta uku kuma ita ce ta biyu amma kana shiga zaka san ragamar gidan a hannunta take ita take juya kowa har shi mijin so bana son wannan kawancen. A katon parlonta muka zauna sannan yan aikinta suka cika mana gaba da abinci kafin taxo, tana shigowa tazo ta rungumeni tana fadin

“Daughter da bata zuwa gurin mamanta ko”

Dan murmushi nayi nace

“Aiki ke hanani wallahi amma ai bazan manta Mami ba”

Zama tayi suka gaisa da Ummaah ni kam na bude exotic na tsiyaya na sha bana son tace naki cin komai. Ina nan zaune inaji suna magana kasa kasa se kuma can Mami tace min

“Asmau jeki daki ki jiramu”

Mikewa nayi na tafi dakin tareda crashing akan gadon na dauki wayata ina random searching da ban masan me nake dubawa ba, baki daya hankalina yana parlon. Har nayi waya da kyaftun ta dan dauke min kewa sannan ta kara reassuring dina sannan naji hankalina ya kwanta. Wata Nannyyy ta shigo tace min nazo inji Ummaah. Mikewa nayi na gyara zaman hijab dina sannan na fito kwatkwata idona bai ma lura da mutumin dake zaune ba seda na zauna sannan na ganshi a zaune, mutumin yafi kama da boka gaba dayanshu a birkice yake gashi fal fuskarshi yana zaune se karkada kafa yake, ga wani wari dake tashi kuma nasan tabbas daga jikinshi ne, dan lokacinda muka zo parlon banda kamshin lavender babu abinda yake, i love the scent of lavender so duk inda naji shi se matar ta fado min saboda kamshin gidanta na dindin kenan.

Abu daya da bana tolerating duk kawaici na shi ne wari bana iya jurewa, ko minti daya ban cika ba kawai se naji cikina ya fara kadawa zuciyata tana tashi, i was completely nauseous. Kallon Ummaah nayi zanyi magana kawai naga mutumin yayo kaina gadangadan, fusace na mike tare da ja da baya ina muzurai, instead ya tsaya se naga ya nannada malum malum dinshi yana neman kai hannu jikina,

“Karka taba ni, Ummaah kina kallo?”

Kamar bai ji ba haka ya dinga bina har nakai bango, idanuna na runtse bakina yana ambatar sunan Allah kawai se naji hannunshi yana shafa fuskata, wata muguwar kara na saki tareda zubewa a gurin sumammiya. Bansan me ya faru ba i don’t even know, na dai san daga baya wai ashe me maganin aljanu ne aka dakko shi saboda ana tunanin aljanu ne suka kama ni shiaysa na ki nayi aure. A gado na sameni lokacinda na farka ni kadai, koda na tashi se na fara jin kaurin tukake, tashi nayi na zauna anan naga yadda hayaki ke tashi wai duk ni akewa turare, gaba daya zuciyata tayi min nauyi, kirjina banda zafi babu abinda yakeyi. Tashi nayi zan fita naji an maida ni gadon, se lokacin na lura da Ummaah da Mami da kuma bokan dan a gurina he’s never near Allah wannan mutumin tsubbu yake. Inaji ina gani haka ya kwara min wannan ya zuban wannan, idan nayi ihu se yace aljannun ne hakan yasa kawai nayi shiru. Haka ya gama ya bada wasu layu da itatuwa da saiwoyi da wasu kulle kulle da zaa binne. ita kuma Ummaah se godiya take mishi, kuka ne ya kwace min, kukan takaici, kukan bakin ciki, kukan tausayin kaina, kukan rashin madaga, se naji duk na sare naji kamar ni rahama ta sauka daga kaina. Nafi awa ina kuka tun Ummaah na cewa aljanun ne har naga hankalinta ya fara kaiwa kaina, ganin haka yasa Mami tace nayi wanka, kaina na girgiza ina cigaba da razgar kuka abuna.

Se laasar bayan nayi sallah sannan muka tafi, fuskata tayi jawur kada ma idanuna suji labari. Koda muka tashi tafiya kasa driving nayi saboda yadda jikina ke shaking. Dole haka mami ta bada driver ya kaimu gida sannan ya juya. Dakina na shige na kulle tareda saka key na datse, banma hau gado ba anan jikin kofar na silale a baki na dinga kuka kamar raina zai fita, ban taba tunanin haka ake bakin ciki ba, nayi ta kuka har bansan iyakar lokacin dana dauka a wannan gurin kuma cikin wannan halin ba. Time to time nakan ji ana min knocking amma ko a jikina banma ni da niyyar tashi.

Ban kara fitowa ba se washegari, dake na saba dama ba fitowa nake sosae ba tunda zaman gidan ya zama tamkar a living hell hakan yasa na koma zamana kawai sede aiki ya fitar dani. Ummaah tun daren take kirana a waya amma naki dagawa saboda bansan abinda zance mata ba. Seda nayi wanka sannan na zura wata purple abaya da stones a jiki se walwali take. Comb na dakko na taje kaina na tufike da karamin ribbon sannan na shafa balm a lips dina da yayi ja, kallon fuskata nayi har lokacin bata ware sosae ba ta kumbura saboda rashin bacci da kuka. Ummaah na zaune a parlor hankalinta dukka ta tattara shi akan kofar tawa, ina fitowa idanuna ya sauka a kanta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaisheta nayi ta amsa jikinta a sanyaye ni kuma na wuce kitchen. Ina cikin dama kunu naji shigowar t, kujera ta ja ta zauna sannan tace min

“Asmau kinada hankali kuwa? Kinsan yadda kika tsoratar dani ki shiga daki ki kulle ko a jikinki? Kinsan banyi bacci ba?”

Bance mata komai ba na cigaba da abinda nake, jin nayi shiru yasa ta dawo gabana tareda daka min duka tace

“Bakya ji ne ?”

Na kyafta ido se hawaye, raina a mugun bace nace

“Ummaah me zance miki? Ya kike so nayi? Nidai nasan this wasn’t my mother, uwata ba haka take ba wani ya canja min ke.”

Sororo tayi tana kallona kafin tace

“Saboda na kaiki gurin malami shiyasa zaki fadi haka?”

Kaina na girgiza nace

“Ummaah saboda banyi aure ba shi ne kike kokarin saida imaninki, ke kanki Kinsan wannan mutumin is never near malami, kawai dai kin bi son ranki ne….”

Wani bugu ta kaiwa bakina hakan yasa nayi saurin rufe bakin, fita tayi ni kuma na zauna na dasa sabon kuka.

AyshatuuuuA fragile heart was broken before, i don’t  think it could endure another pain, a piece of voice from deep inside that calling you to make you relaxed!

Wannan kwanaki biyun dana kara sun zame min kwanakin da bazan taba mantawa a rayuwata ba, tunda nake addua i was never specific sede nace Allah ya zaba min mafi alkhairi, a ganina hakan shi ne daidai amma tunda naga an fara haka yasa na dukufa adduar Allah yasa nayi aure cikin kankanin lokaci. Ana gobe zan tafi da daddare na dawo daga gidan yaya Halifa saboda gidan babu dadi, daga ni se Asiya se ummaah and I couldn’t, i was suffocating hakan yasa na tafi tun sassafe, Inna ade da Abba sunje umra , jikokin gidan kowa yana gidansu hakan yasa naji zaman ya isheni. Mun jima nida yaya Halifa ina kora mishi bayanin halin da nake ciki. To me zaiyi shi dinma Ummaah ta haifeshi, highest thing shi ne ban hakuri kuma shi din ya bani, ya nuna min Allah yana sane dani kuma komai kaga ya faru to da saninshi. Those words kept me going.

+

Kwana na biyu da dawowa daga kano, na koma aiki na saboda damuwar ma batada amfani. Da yamma ina kwance a daki ba call nake ba so bayan na gama abinda zanyi na fita kasuwa nayo cefane na dawo . Ranar i was craving for dambun shinkafa. Haka na zauna na daura a cikin steamer na koma na fara soya kazar da zanyi pepper chicken da ita. Ina nan zaune na saka wani chilled chapman a gabana ina sha se naji message ping, mikewa nayi da sauri na isa ga wayar tareda tapping message din

A 40year old null para with a diagnosis of ectopic pregnancy and ? Typhoid perforation. booked for ex-lap. Prepare for emergency ex-lap ASAP.

Na karanta yafi sau shida ina kara duba number data turon da mamaki, wannan ai aikin general surgeons ne kuma ma idan ance saboda ectopic dinne I’m not on call. Mikewa nayi na kashe steamer sannan na juye abincin cikin warmer se kadan nasa a plate na saka salad da naman na fara ci. Banma kara komawa takan message din ba saboda a tunanina mistake akai. Seda na gama na gyara dakin sannan naga call din Dr halima yana shigowa, hannuna na goge jikin towel na dauka, ko gaisuwata bata amsa ba tace

“Asmau bakiga message ya shigo wayarki ba?”

“Na gani, I thought mistake ne shiyasa na share”

Cikeda damuwa tace

“This is unlike you, kije yanzun patient din tana Female surgical ward kiyi reviewing dinta”

Kaina Na gyada nace

“Amma bani bace da call bafa”

“Just follow orders kinji, nima order aka bani”

Katse call din mukai inata bubbuga kafa da zumbura baki hakanan dai na samu na dakko kayana na kullum yau pink nasa wando da riga na soft cotton yadi na saba back pack dita na fita. A ward na sameta mugun restless, ciwo yana damunta hakan yasa nayi order a mata allura kafin na kira a kawo ta: daga nan OT na wuce, na samu sun shirya kawai jurana ake hakan yasa na kira dan a kawo patient din. Ana kawo ta na dubi scrub nurse din nace

“Sister, waye zamuyi surgery din dashi?”

Dariya tayi tace

“Baki sani ba dama”

Kafin na bata amsa naji wannan deep voice din tashi, dukda sau daya na taba ji amma hakan baisa na manta da ita ba.

“Evening everyone”

Juyawa nayi da sauri tareda bashi hanya nace

“Welcome sir”

Kanshi ya gyada min sannan ya bawa mazan gurin hannu sukai musabaha ya shiga ciki yayi changing sannan muka fara. Tunda na mika masa scapel yake min tambaya akan conditions din matar, God so kind nima book worm ce so yana tambaya ina amsa shi inda gyara yana min yana kara clarifying min abubuwa. Haka mukai almost 4hours muna abu daya, se bayan maghrub muka gama aka maida ita ward mukai sallah sannan yace  a kawo masa folder yayi documenting. Ni na kai masa yace

“Sit please!”

Zama nayi kamar yadda yace, idanunshi ya maida kan folder yana going through hx matar.

“What’s your name?”

Dagowa nayi na kalleshi amma bani yake kallo ba amma nasan dani yake tunda ni dashi ne kadai cikin office din

“Asmau Shahada”

Kanshi ya gyada yace

“A ina kikai training dinki?”

Shortly nace dashi

“BUK, sir”

“Good!”

Daga haka baice komai ba se can ya mika min folder yace nayi rubutun. Zama nayi yana kallo ina rubutawa yana kara guiding dina har na dan saki jikina. Muna gamawa yace min

“You’ve done a good job. We meet some other time”

Kaina Na gyada ya fita ni kuma na koma na zauna ina maida numfashi. Tun daga lokacin shi kenan indai zaiyi aiki kowa yasan I’m his partner tun abin yana damuna har na sake na saba.

Wata Wednesday mun gama ward round, banyi breakfast ba ranar saboda kadan ya rage ban makara ba hakan yasa na tafi cafeteria dan cin abinci. Tsirarin mutane na tarar suna cin abinci, wasu sun gama, seda nayi order sannan na dawo na zaune ina jiran a kawo min. Nayi nisa sosae a cikin wayata ina chatting naji alamar an zauna gefe na. Da sauri na dago wani mutumi ne in his mid thirties ya tsareni da idonshi, the gaze was so intense hakan yasa nace

“How may i help you”

Wani murmushi ya saki yace

“Finally, na samu ganin workaholic Dr Shahada. How far?”

Bansan amsar da zan bashi ba hakan yasa nayi shiru tareda maida hankalina kan wayata, i knew him somewhere amma na rasa a ina na sanshi. Shima bai kara cemin komai ba seda aka kawo min abincin se na maida shi akan ayi packaging ba anan zanci ba. Se naji yayi dariya yace

“Doctor, ya zaki ce ayi packaging?”

Dagowa nayi na kalleshi nace

“Ka takura min”

Murmushi yayi yace

“Tun yanzun, ai abinda zuciya ke so no way ta bar abinnan”

Mikewa nayi naje counter cashier na biya sannan na fice kawai, ashe yana bayana seda nayi nisa sannan yace

“Doctor, you shunning me?”

Tsayawa nayi nace

“Idan abu kake so ina ganin wannan is not right kazo ta haka, dan Allah idan wani abunne follow the right route”

Daga haka na juya zan tafi, to my utmost amazement kawai se ya ruko hannuna cikin sauri na juyo, mamaki kamar ya kashe ni, kafin nayi yunkurin cire hannun se ji nayi ance

“Asmau!”

A tsorace na dago idanuna only to see MD a tsaye ya tsareni da idanunshi da suka kada sukai ja, sunkiyar da kaina nayi tareda kwace hannuna, tuntuni idanuna sun fara kokarin kawo ruwa. Yana isowa gurin yace

“Meet me in my office yanxunnan!”

1

AyshatuuuuTamkar an daddatse min joint dina haka naji, ilahirin jikina yayi sanyi na rasa abinda yake min dadi. Lumshe idona nayi na dubi useless, unreasonable Ashole dake tsaye yana wani irin smirking, idanuna na lumshe raina a mugun bace kawai na juya na tafi. Once in a lifetime kowa yana experiencing such embarrassment, tunda nake ban taba jin kunya irin wadda naji ba. Tamkar anmin duka haka na tafi ina tunanin ta inda zan fara hada idanu dashi. Taya mutum zaiji ace mutumin dake ganin mutumcin ka ace yaga wani ya rike hannunka nasan Allah kadai zao fitar dani.1

Banyi gigin zuwa office dinshi ba saboda bansan wanne ido zan kalleshi ba kawai se na juya na tafi mota ta nayi mata key se gida, dukda hankalina yana kanshi Amma zuciyata gargadi na take akan kada fa na zake, tayi kuwa nasara haka na basar na tafi daki naci abinci sannan na kwanta, a raina ina fadin aikin ma na yau na fasa bazanyi ba.

Shikam acan a mugun fusace ya isa office dinshi, yana shiga yayi slamming kofar da karfi tareda fadawa kan cushion ya zauna, cushions ne guda hudu tsakiya center table ne me kyau covered with glass baki daya. Zama yayi ya daura kafafunshi akan table din. Wani zafi ne ke karyo masa se gumi yake ka rantse da Allah yana karkashin kwalleliyar rana ne, nan kuwa cikin niimar split yake har biyu a cikin office din. Coat dinshi ya cire ya aje gefe sannan ya sassauta necktie dinshi tareda kurawa kofar idanu yana expecting shigowar Asmau amma har awa daya ta shude babu Asmau babu alamar ta. Mikewa yayi ya fara pacing a cikin office din, me yarinyar nan take nufi dashi yace tazo sannan taki zuwa ta sameshi,  kanshi ya girgiza daidai knocking a kofar hakan yasa a sukwane yace

“Yes, come in please”

Kofar aka turo idanunshi a kafe yana jiran ganin wannan farar fuskar tata amma maimakon ganinta se yaga ashe Director Admins and finance ne, se lokacin ya tuna sunada magana dashi. Daidaita kanshi yayi cikin sauri ya koma seat dinshi tareda masa izinin zama, seda suka gaisa kafin ya bude file ya fara briefing dinshi amma rabin hankalin Dr Kwaccido baya gurin tunnainshi kodai mutumin da ya gani tareda Asmau ya gudu da ita ne? Kodai dama saurayinta ne cikin sauri ya matsar da wannan thought din a ranshi, it took him almost 2 months yana bincike a ciki da wajen asibiti akan Asmau, babu inda yaji tana da wani tsayayen magana a kanta….

“Sir, you’re not concentrating, ko mu hadu gobe?”

Kanshi ya dafe cikeda damuwa yace

“I’ll be glad, thank you”

Haka ya tattare kayan shi ya tafi shi kuma ya cigaba da jiran tsamanni amma har yaje azahar ya dawo bata zo ba, sau da dama se ya fara dialing numbers dinta da yayi storing dinsu a kwakwalwar kanshi tun ranar da Dr halima ta bashi ita amma ya kasa, baisan abinda zaice mata ba, zuciyatshi tasha gargadin shi akan wannan kallon ruwan da yake kada wankin hula ya kaishi dare. Ko kuma garin bari ya huce har ya zama rabon wasu, kanshi ya girgiza dan baya tunanin zai iya bari hakan ta faru.

Wajen laasar ya kammalla komai na ayyukan ranar, hannunshi rikeda briefcase da suit dinsa yana waya ya fito, messenger dinshi ya karba tareda kai mishi mota, godiya yayi masa sannan ya wuce cikin motar yana baza idon ganin ta inda zata bullo amma bai ganta ba haka ya tafi dik babu dadi, haka nan yaje gida. Kamar yadda ya saba ganin gidan it was so empty ya zaiyi tunda haka kaddra ta zabar masa kuma hakanan zai karbeta babu yadda zai iya. Straight bedroom dinshi ya wuce yayi wanka yayi alwala sannan ya zura jallabiya brown me gajeran hannu ya dawo parlor ya zauna. Babu jimawa yaji ana knocking wanda yasan ba kowa bae illa sabiu cook dinsa, sunyi waya yace masa ya fita dan yun wata gaisuwa. Shigowa yayi ya risina ya gaisheshi sannan ya wuce kitchen dan hada masa abinci, idanunshi ya lumshe yana bin parlon da kallo, ko ina a share yake, tiles din se kyallin mop suke amma kana kallon yadda komai Na parlon yake kasan babu mace a gidan. It’s obvious kana shiga zaka fahimci hakan, kanshi ya shafa yana jin lokaci yayi da zaiyi uncaging zuciyarshi hakanan, ya kamata ya fito daga dreadful past life dinshi ya cigaba da rayuwa, wannan zuciyar tana bukatar aboki, ya kara kallon katon parlon da hasaso gadon shi, yana bukatar living partner, he sure needs a soulmate.

STORY CONTINUES BELOW

Washegari ranar alhamis, kamar kowanne sati ita ce ranar da muke surgery ni da Dr Kwaccido. So ranar tunda nayi asuba na ko wanka banyi ba Na tafi Paediatric surgical ward, nan patient din yake. Yaron shekarashi biyar yana fama da umbilical hernia. Though condition din is a minor one amma a haka yayi mana booking. Ina zuwa anesthetist din tana zuwa, tare mukai reviewing dinshi kowa yayi documenting abinda ya samu sannan muka rabu. Gaba daya ji nake inama inada excuse din da zan bayar dan bana sam haduwa dashi kwata kwata amma ina na babu wannan, se goma na safe sannan na fito, fuskata tayi yar fayau tsabar fargaba da damuwar da nake ciki idanuna duk sun fada sunken in. Yanayi na ma kawai zaka kalla kasan akwai tambaya. Ina zuwa office na samu kan sofar dake gefe na dan kwanta ai bacci yace idan kaci bashi na se ka biya and it happen.

Bansan ashe har time ya tafi ba, se can naji ana knocking kofar office dina, ko kafin na tattara guntun karfin da ya rage na tashi, tuni kofar was flung open. Wannan kyakyawar fuskar tashi me cikeda haiba da kwarjini tasa nayi saurin tashi ina lalubar veil dina, wannan idanuna nashi that always shine me kamar an zuba musu mai cikinsu ya tsareni dasu, a take naji kamar anyimin duka, yunkurun da nake na daina se kasa da nayi da kaina ina jin an takura ni da yawa. Yana tsaye tareda harde hannyansa a kirjinshi shi bai zauna ba bai kuma nema gurin zaman ba. Kafin na kara yunkurawa naji yace

“Sleeping on duty?”

Da sauri na muskuta tareda girgiza kaina nace

“Sir, banida lafiya ne”

A take naga yanayin fuskar shi ya canja, shigowar shi tamkar wani zaki haka ya shigo ranshi a hade amma yanzun se naga damuwa ta dauke bacin ran dake ciki. Daidaita tsayiwarshi yayi cikin wata tattausar murya wadda babu wani da namiji daya taba amfani da ita wajen yimin magana yace

“Sannu, kinsha magani?”

Kaina Na girgiza nace

“I was about to, se bacci ya daukeni.”

Kanshi ya gyada se kuma ya fita, hakan yasa na sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda lumshe idona, ni nasan banda lafiya amma a matsayina ta likita bana tunanin nasan me yake damuna, ban kuma san wanne irin taimako zan bawa kaina ba, nasan kilan tarin damuwar da nasa a zuciyata ce take neman kayar dani…..Soft knock akai jikin kofar, bakina a hankali na bude tareda bada izinin shigowa, shi dinne ya dawo sede wannan karan ya samu rakiyar head of medical department da kuma chief pharmacist. Inata kokarin mikewa ya hanani tareda bawa Dr Mansur damar ya dubani, BP na ya fara dubawa, kawai gani nayi ya cire glasses dinshi yace1

“Her BP is reading 70/40mmHg sir”

Yana fadar haka se naji tamkar an saukar da min symptoms, baice komai ba illa bina da yake da idanunshi me tuhumata akan Me ya faru? Nidai kasa kawai nayi da kaina ina jin ana min prescription sannan aka kira pharmacy suka kawo. Drip aka fara daura min yana fara shiga wani wahallalen bacci yayi gaba dani. Se can bayan wasu awoyi sannan na farka , ina office dina amma ba kamar dazun ba, ina bude idona da kyaftun na fara cin karo tana sallar laasar. Cikin sauri na yunkura inajin karfi a jikina ba Kamar dazun da nake jin jiri ba.

Toilet na shiga nayi alwala sannan nazo na zauna dan har lokacin jikina gashi nan dai, a zaunen nayi both zuhr da asr sannan na kwantar da kaina akan cushion ina lumshe idona.

“Ya jikin Twin?”

Bude idanuna nayi tareda yin kalar tausayi na dubeta har lokacin uniform ne jikinta alamu sun nuna kilan ko ward ba taje ba, ga Afeeyya ‘yar 5 months ta shimfidar da ita a yar corner se baccinta take peacefully.

“Twin Alhmdllh. Yaushe kika zo? Waye ya fada miki?”

Wani kallo tayimin wanda ta saba yimin idan gulma ta motsa, hakan yasa na cuna bakina ina dauke kai. Dariya tayi wadda tasa dole nima nayi sannan ta matso tace min

“Boss ne, da kanshi yazo har ward ya tafi dani, he left here not long ago.”

Kaina na gyada kawai ba tareda nace komai ba, dan bansan me zance din ba. Sake matsowa tayi kamar zata shige jikina hakan yasa na ture ta baya da dan guntun karfin nawa daya rage nace

“Ke munafuka ce”

Shrugging shoulders dinta tayi tace

“Oho! Baby bude baki zakiyi kimin bayani, me yake faruwa.  Kinga yadda ya rikice? Ni daya shigo ward dinmu I thought something terrible happened ashe Twin ce babu lafiya”

Hararata nayi nace

“Kede Allah ya sawwake miki, he’s none but my boss and partner aiki na”

Tsareni tayi da idanu irin she needs more, tsaki nayi nace

“Dan Allah ki bani abinci I’m starving”

Hakuri ta bani sannan ta hada min wani tea me kauri, yayi min dadi kodan ina cikin yunwa ne oho, seda na shanye tas sannan tace an tafi a kawo abinci. Bata kara min zancen ba tunda tasan da akwai wani abu da zan fada mata, tsakani na da ita babu boye boye so we still maintain the status. Tunda nayi shiru na fada tunani, anya yadda zuciyata ta adana Dr Kwaccido matsayin shugabana da kuma partner aiki? Ina tantamar hakan, duk wanda nayi aiki dashi zai nuna yaji dadi kuma zaiyi kokarin maintaining dina tun ina house job amma shi nashi salan caring din ya banbanta dana kowa. To amma someone like him…. Sallamar shi yasa nayi saurin bude idanuna, a hankali na amsa wanda iya bakina ne kawai ya motsa, muna hada ido ya sakar min wani murmushi. I swear seda tsikar jikina ta tashi, those eyes of his will definitely not allow me to live in peace sede idan kullum zan kasance ina kallonsu ne.

Gaisawa sukai da kyaftun sannan ya mika mata ledar hannunshi yace abinci nane, gefena ya dawo ya tsugunna yace

“Are you ok?”

Kaina na gyada nace

“Much better. Thank……”

Shush yayi min sannan yayimin murmushi yace

“Kici abinci zanje office”

Se na samu kaina da yi masa murmushi nace

“Allah ya bada saa”

Kanshi ya gyada ya dubi kyaftun dake rike da Afeeyya data riga ta tashi ya bata sallahun lallai naci abinci. Aikuwa yana fita ta fara tsokanata wai wallahi so na yake nidai ban kulata ba dan bazan saka abin a raina ba balle ayi back stabbing dina!

2

Your comments keep me going……..

AyshatuuuuIna kammalla cin abincin naji wani karfi yazo min, duk wannan kasalar babu ita, mikewa nayi na tattara gurin sannan nace da Kyaftun mu tafi gida dan ina son nayi wanka na canja kayan jikina. Babu musu ta tattara kayanta muka fita, bani da wani karfin da zan iya driving hakan yasa kyaftun karbar key din ita kuma Afeeyya na karbe ta, mun saba da ita sosae bata min kiwa dan wani sa’in se tayi ta kallona ni da kyaftun tana tantamar gurin wa zataje tunda kowa yasan nida mahaifiyar ta kama  muke sosae, banbanci na da kyaftun nafi ta haske ita kuma ta fini tsayi sannan ita ba a rame take ba, wadda tashin hankali da damuwa yasa na koma hakan.+

Muna shiga na aje Afeeyya na shiga wanka, simple gown nasa ta wani pure cotton yard maroon, free gown ce se stones da aka mata ado dashi. Scarf milk na dakko Na daura sannan na murje jikina da turaren kullum La’eeqa da soft. Lumshe idanuna nayi na dawo na zauna inajin wani daddan yanayi a jikina. Kallon kyaftun nayi da take kokarin hada pap din Afeeyya,

“Ki kirashi kice kin dawo gida, let him not waste his time checking on you a office”

Dan bata fuska nayi tareda fadi

“Is there need for that?”

Kanta ta girgiza tana hararata tace

“Kina da matsala kinsan da hakan? How….?”

Se tayi shiru tareda daukar Afeeyya ta daura ta cinyarta ta fara feeding dinta, wayata dake gefena naji ta fara ringing hakan yasa na kai hannuna na dauka, Adda Sa’ada ce cikin sauri nayi picking dan ta rigada tasan banida lafiya, i texted her though ina tunanin se lokacin ta gani. Ina picking tace

“Fara what happened?”

Dan murmushi nayi jin muryarta duk da damuwa nace

“Ba wani abu bane kawai BP na yayi low”

Ai fa kamar famfo ta fara zuba, tana tamin fada akan tasan na takurawa kaina ne shiyasa hakan ta faru, seda ta gama fadan sannan ta dawo nasiha tana fadin

“Komai da kike gani is a matter of time, da ace tsangwama da takura kai yana sawa kayi abu, da tuni kinyi aure amma shi Allah is wonderful, he’s a perfect timer. Lokaci ne da zarar yazo zakiji it worth the wait!”

What will life be without Adda Sa’ada? Hell na ayyana a raina, bazan iya fadar abubuwan da matar tayimin a rayuwa ba amma she sticks around bata taba nuna min laifina bane da banyi aure ba, Anty Bintu, Yaya Halifa da Adda Meeyna. Banda kamar su. Ina aje wayar kyaftun ta mike tana fadin

“Kada ki zama kina manta alkhairi kuma kada ki bari a golden opportunity like this ya wuce ki. Zan tafi gida, se dare zamu dawo da Daddyn Afeeyya.”

Mikewa nayi a hankali dan bawai malaise din dake damuna ya tafi duka bane, yanzun ma jina nake kamar zan fadi dan dai ina daurewa ne. Hannunta na riko nace

“Ki fahimci abinda nake nufi, i can’t just throw myself on him kamar yadda nayi akan mukhtar (RIP) da kuma Suleiman. I was back stabbed kuma laifin waye? Nawa ne saboda ina ganin dukkan wanda yadan nuna kulawa akaina sona yake. Kina son na kara haka, repeating same mistake is nothing but foolishness”

Zaunar dani tayi dan taga alamar zan iya faduwa ta rike hannuna tace

“Ki fahimci abinda nake nufi nima, ba ina nufin you start chasing him, stalking him and stuffs. Kinsan dai ya miki abin kirki to ko thank you ne he deserves it.”

Kaina na gyada in agreement na dauki wayata and I sent him

Thank you, jiki yayi sauki. Na bar office ina gida

A gurina they were only a plain words amma a gurinshi yayi ta nanatawa saboda dukkan abinda zai fito daga gurina yana daukar abin me muhimmanci. Baiyi min reply ba har kyaftun suka kawo min abinci naci suka tafi na kulle dakin na kwanta tunanin rayuwata yayi min rubdugu, addua a bakina kan Allah yasa Ummaah ta fahimci rayuwa, ta fahimci cewar lokacin zai zo. Da wannan bacci yayi gaba dani se can cikin baccin naji vib din wayata, bansan yaushe rabon da naji an kirani past 10 so da mamaki na bude idona tareda mika hannu na cira wayar, take idanuna suka bude ganin number da take kira, Dr Kwaccido na ayyana a raina at this time, kifar da wayar nayi inajin yadda ilahirin jikina ya mutu, ina ayyana me yasa zai kirani, wata zuciyar tace just to check on you, kaina Na girgiza na ba tareda na yarda da uzurin da zuciyata ta kawo ba. Amma se na samu kaina da kasa nutsuwa, na janyo wayar na kalla 1 missed call, na danyi tsaki ina mitar har yaushe zaayiwa mutum call daya as if baa damu ba. Haka na gama yan mitocina na bude wayata ina kallon pictures dinsu Amalin Adda Habiba sunyi birthday itada Aarif last week. 

STORY CONTINUES BELOW

Washegari bayan nayi sallar asuba dake friday ce hakan yasa ban bar kan praying mat din ba har seda na karanta kahfi savoda nasan idan na bar gurin ba lallae nayi ba, ill be much occupied. Ina kammlawa na mike anan wayata ta katse min hanzari, ganin number seda zuciyata tayi fluttering, it kept jumping har hakan ya bani tsoro, but ya zanyi dole nayi picking call din saboda banda uzuri. Dauka nayi murya can kasa nace

“Good morning sir”

Manly muryar nan tashi me saka naji waves electrons cikin jikina ya amsa da fadin

“Morning Asmau”

I can swear akan ban taba jin wani ya fada Asmau so correctly kamar shi ba, kowanne harafi seda aka bashi hakkinshi, har seda naji ina bukatar nayi ta jin shi yana kiran sunan.

“Ya jikin naki?”

Dan murmushi nayi nace

“Yayi sauki, Alhmdllh”

“Alhamdulillah, zuwa karfe biyu zan wuce kano, ki zama ready zamu tafi tare”

Baki bude na tsaya ina tunanin abinda yace min, seda ya kara maimaitawa kafin nace

“Sir zan fara call gobe, so bazan samu damar zuwa ba and thank you”

“Na rigada nayi arranging yadda zaayi, ya kamata ki huta saboda ciwonki stress ne”

Se na kasa musa mishi haka mukai sallama bayan yace zai aiko min breakfast sannan nayi bacci kafin time din. Nidai na rasa tantance me hakan ke nufi na kuma kasa fahimtar inda zuciyata tasa gaba da kuma wanne tarba tayiwa alamarin. 8am na bugawa aka kawo min abincin, cikin basket aka jero shi, messenger daya kawo na bashi 500 yana ta godiya ya tafi. Chips ne cikin bowl se farfesun kayan ciki shima a bowl, tea me kauri cikin wani karamin flask. Gefe leda ce a aje na bude tareda ciro abinda ke ciki, rose flower ce hade da greeting card, mamaki sosae ya kamani na bude greeting card din naga na get well soon ne, a kasa yayi rubutu cikin rubutun da ban taba kawowa ya iya ba kasancewar kowa yasan handwritings din Doctors bashida kyau amma yadda yayi rubutun kamar calligraphy lettering style yayi amfani dashi.1

Come on, get back on your feet and continue that gorgeous smile of yours. Quick Shifaaa Cara Mia!

Shine abinda ya rubuta, zuciyata nasan dama is froze, dan tunda Salis ya betraying feelings dina shikenna na daskarar da ita, ga mamakina wannan kalaman nashi take suka raga raga da wannan kankarar, wani bugu da zuciyata ta shiga yi har seda nayi tsoron kada a samu over extension. Jikina yayi sanyi na kalla rose 🌹 din na shafa na shinshina a karshe na rungume ta a kirjina ina adduar Allah yasa daga shi ne. Greeting card na dauka na kara nanata rubutun ina bin kowacce kalma daki daki, komai na fahimta banda wannan cara mia din kuma babu me amsa min. Abinci kadan naci sega kyaftun tayi ta ihu tana murna tana fadin

“Yarinya kin saka yan maza a gaba fa, kinyi kamun full package”

Se na samu kaina da fara yarda da zancenta, kodai so na yake, ko dai……haka nayi ta tunanin kafin can bacci ya daukeni se wajen 12pm na tashi nayi wanka na hada kayan dazan bukata sannnan na yi sallah na karasa abincin da na rage na wanke na kife kafin na fara neman kaya. Ni dama ba maabociyar kwalliyya bace dan powder ma se kayi da gaske nake siya hakan yasa na zizara khol tareda shafa charpet kan tattausan lebena da ya fara bushewa har fata na neman dagowa. Dana kalla madubi se naga nayi kyau daidai yadda ya kamata. Wani lace na dakko me laushin gaske irin vapers dinnan ne. Background din Coffee ne se designs din suka tashi milk da zaren gold a jiki. Skirt da riga ne nasa na daura dankwali tareda dakko matching veil da takalmi, har na manta last dana nutsu nayi shigar arxiki. 1:50 daidai wayar shi ta shigo akan yana jirana, kara gyara zaman veil dina nayi sannan na dauki abinda zan dauka na fita. Yana tsaye gefen motar yayi shigar da ban taba gani ba, yana cikin farar shadda ta zarce ayi masa coffee aiki, kanshi sanye da zannan bukar yayi kyau very charming. Dake quarters din namu babu mutane yawancin an tattafi weekend masu aiki nayi yasa yake tsaye shi daya. Back seat nasa kayan sannan na shiga gefenshi danshi tunda na kusa karasowa ya koma ciki ya tashi motar. Tunda Na gaisheshi ya amsa ban kara ko tari ba haka shima se gudunshi da yakeyi, seda mukaje wudil ne ya tsaya karbar document ni kuma na samu saken kiran kyaftun na mata sallama. Yana dawowa ya kalleni tareda fadin

“You look disturbed, akwai abinda zan taimaka miki dashi?”

Cikin sauri na karkada kai alamar aa tareda lumshe idanuna ina shakar kamshin turarena nashi da kuma car freshner da ya saka, ga sanyin AC. Yanayin was so romantic. A hankali naji waka ta fara fita cikin speakers din, hannunsa yasa yayi increasing volume din tareda fadin

“Shirin yayi yawa, enjoy please”

🎶I’ve been looking for you everywhere, I’ve been asking god when I’ll found you dear? I know some times last days where you least expect. But I’ll be patient i go wait, wait for you my dear. wherever you are, you have my heart, my darling take me yes I’m. I’ll be loving you from now till i found you my love. I hope say you like me d way i be, i go dey wait for you day and night dear future wife. 🎵

🎤When I need you will you be there my dear? I’ll make silly mistakes please forgive me dear, we have a long a way to waka, hold my hands my dear. Wherever you are you have my heart my darling, I’ll wait for you day and night dear future wife.🎷

1

Tamkar kada wakar ta kare haka naji, idanuna na bude tareda kallon sadhin shi, murmushi ne kwance a fuskarshi wanda tsabar yadda ya kayatar dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi:

“Nayi kyau ne?”

Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani.

AyshatuuuuHar kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace

“Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan”

Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace

“Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?”

Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda fadin

“Monday very early zanzo mu tafi”

Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni. Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada ‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.+

Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace

“Ummaah barka da gida”

Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace

“Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS”

Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace

“Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta”

Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka.

“Ya A’isha da halima da me gidan?”

Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana ringing and it was him calling, haka nan na karasa jiki a sanyaye na dauki wayar tareda karawa a kunnena nace

“Barka da dare Sir”

“Barka dai Asmau. Ya saukin jikin?”

Se dana kalla kaina kafin na amsa masa da sauki se kuma mukai shiru dan nidai bansan me zance msa ba kuma baya son godiya. Hakan yasa nayi shiru. Se can yace

“Kiyi bacci and ki tabbatar kinci abinci”

Kamar wata doluwa haka na shiga gyada kaina in agreement amma sede bama gani na yake ba balle, seda yace

“Huh! Asmau?”

Sannan nace

“Inshaaa Allah Sir”

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka mukai hanging, wani irin raruma nayiwa wayar taredq rungume ta a kirjina inajin wani farin ciki marar misaltuwa. Murmushi kuwan from ear to ear kamar bakina zai yage. Can kuma na kashe wutar tareda yin addua na kara lula duniyar tunani a haka daddan bacci ya daukeni, it was peaceful dan ko mafarkan da nayi where of love. Dan haka da asuba dana tashi komai lafiya lau jikina ba wannan rashin kuzarin se ma wani karfi da nake ji. Hakan ya bani mamaki amma a kasan zuciyata nasan menene nasan dalili. Ina idar da sallah na janyo babban quran dina na fara tilawa a kalla nayi izu daya kafin nayi azkhar lokacin tuni gari ya waye hakan yasa na gyara dakina na shiga wanka. Ina fitowa na zura wata morning gown ta wani silk purple yadi. Kaina na zura hula sannan na tafi kitchen.

Na jima tsaye a jikin working surface ina karewa kitchen din kallo wanda a zahiri kenan amma a badini ina tuannin bidirin da aka sha a kitchen din, tun daga Yaya mukhtar down to Yaya Suleiman. Kowannensu it started at this very place. Ajiyar zuciya me nauyi na sauke ina kara kallon guraren tareda saka hannuna ina tattabawa wasu nayi murmushi a haka na kashe time din da bansan iya adadinshi ba. Se can dana fara jin motsin yan gidan sun tashi sannan na dukufa fara aiki. Na kusa gamawa Mama da Asiya suka zo muka karasa na wuce na gaida Inna sannan Abba da Ummaah. Muna kammalla breakfast na koma daki na dudduba wasu soft copy pages da aka turon akan Breast cancer da Cervical cancer. Ban wani dauki time ba na gama na janyo system dita na fara aikin da na saba wato kallon korean movies, wani Love In The Moonlight.

Gaba daya na sakankance ina kallona naji an turo kofar dakin, normally mun saba indai zaka shiga dakin koma waye seka yi knocking da sallama kafin ka shiga. Hakan yasa na dago da sauri tareda pausing film din, mamaki sosae ya kamani ganin  Nadia, its been long da naga kafafunta a cikin gidanmu kuma dakina. Mikewa nayi ina sakin murmushi nace

“Nads manyan mata, sannu da zuwa”

“Yawwa!”

Kawai tace min se ban wani damu ba tazo ta zauna nace

“Bari a kawo ruwa, yau akwai hirar yaushe gamo kenan”

Na fada ina kokarin tashi daga gefenta, hannunta tasa ta rike nawa, hakan yasa nayi saurin kallonta kafin nayi magana tayi beating dina to it tace

“Bashi ya kawo ni ba. Kina kallon yanayi na kinsan ba ruwa nazo sha ba. Gargadi nazo nayi miki, mijina Suleiman nawa ne ni daya kinganshi yafi karfin wadda tayi kwantai ta gama aiki cikin kartin maza irinki. Saboda kin kasa auruwa you decided kizo kimin snatching miji? Kul dinki!”2

I was dazed, confused and amazed! Tunda ta fara magana nake kallonta da tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa ya fit baro baro akan fuskata. Tana gama fada ta hankadar da hannuna ta mike da niyyar fita, nasa hannuna na riketa ina kallon idanunta wanda na rasa meye a cikinsu amma nawa firgici ne a cikinsu

“Ta yaya zaki fita baki fahimtar dani abunda maganar ki take nufi ba, Nadia ni ce fa”

Hannunta ta kwace kamar wata damisa, cikin daga murya tace

“Se me dan kece? Ai nasan ke dince shiyasa na sassauta miki, tunda bakiji kunyar kawancenmu kin kai idanunki kan mijina ba bazanji kunyar na miki gargadi ba. Me mijina zaiyi dake tsofe tsofe dake…..”

Ban barta ta karasa ba na wanka mata mari ina wani irin huci, i was boiling in,

“Kada ki kuskura Nadia…..”

Se na dunkule hannuna na kasa karasawa, zuciyata na fada min Nadia ce fa, wannan dinnan, kin manta ta? She doesn’t deserve this. Bana tunanin akwai circumstance da zai zo na manta matsayin rayhana da Nadia a rayuwata, sudai zasu iya mantua amma ni nasan alheri bana mantawa dashi. Ai tana ganin nayi shiru ta fara zage zage wanda ya janyo hankalin Inna da Ummaah dasu Mama, su basu san ta shigo bama dan kowanne na dakinsu. Ummaah tazo tana fadin

STORY CONTINUES BELOW

“Nadia me ya faru? Me ya hadaku?”

Wani mugun kallo tayiwa Ummaah tace

“Ki fada mata ta fita harkar mijina, mijina yafi karfin ta shi ba tsaranta bane, idan ba haka ba……”

Gaba daya har Inna muka tsaya muna kallonta da tsananin mamaki, kuma shirun da mukai mata baisa tayi shiru ba sema kara daga mirya da takeyi a haka Abba ya fito ya samemu a tsatsaye, Nadia tana ta wulakanci ita me miji. Kallonta yayi yace

“Kiyi hakuri ki koma dakinki, ni na miki alkawarin Asmau bazata taba auren mijinki ba, itama nata yana nan tafe da izinin Allah”

Kawai tana bude bakinta se cewa tayi

“Better!”

Ta juya ta fice, tana fita naji wani irin yanayi me wiyar na fada ya lullubeni, kaina kamar zai tsage gida biyu, idanuna da suke neman lumshewa na bude da karfin gaske nace

“Abba me ya faru”

Ashe yaya Suleiman ya samu Ummaah akan yana sona zai aureni tace masa aa kar ya manta abinda ke tsakanina da matar shi, bai jiba ya samu Inna ita kuwa kowa yasan yana daya daga cikin favorite jikokinta hakan yasa tayi naam da maganar. Kallon Inna nayi kamar zan daketa idanuna se hawaye ke zubowa, gaba daya na manta Inna bata jin turanci nace

“For goodness sake, Inna why will you do this? Danme? Kinsa yarinya yar cikinku tazo tayi muku fitsara. Saboda banyi aure ba, kun taba ganin macen da takai age dina bata damu tayi aure ba, in bai zo ba zan fita titi nayi shelar wa yake sona? Waye zai aureni…!”

Wani abu naji ya tokaren makoshi hakan yasa na juya dan tafiya daki amma wani mugun jiri ya kwashe ni se gani a kasa, dukkansu suka yo kaina dan tashina amma na mike seda Abba ya rikeni aka kaini har daki daidai shigowar yaya Suleiman a birkice, Abba yace baya son yaji komai kawai yazo ya dubani. Yana dubani ya daura min drip se na lumshe idona kamar me bacci hakan yasa suka fita dan na samu na dan huta amma maimakon na mutsu se kawai na tashi na hada kaina da gwiwa na dinga kuka, a raina ina ayyana yadda rayuwa ta juya, ni Nadia tazo har guda ta ciwa mutunci akan mijinta? Su Ummaah basu tsira ba. Asiya ce ta shigo ta sameni a hakan ta zauna tana ta lallashina har nayi shiru sannan ta dauki wayata dan nace duk wanda ya kira tace banda lafiya.

Misalin karfe bakwai na dare nayi sallar maghrib, na dan nutsu ba kamar da safen ba shima Abba da Ummaah suka zo sukai ta lallashina tareda nuna min haka rayuwar take, we must expect worst from life, it’s a trial which are never meant to be easy. Wannan ya karfafa min gwiwa har nasha tea sannan nayi wanka amma idanuna kadai zaka kalla kasan kodai ina cikin damuwa ko banda lafiya.

“Yar fara tashi maza maza ki canja kaya kizo parlor kinyi baki”

“Baki?”

Na maimaita ina kallon Ummaah data bude wardrobe dina da alamun kaya take nemo min kaya, mikewa nayi jin bata bani amsa ba nace

“Ummaah su waye?”

Juyowa tayi tana kallona kafin tace

“MD dinku ne”

Idanu na zaro cikeda mamakin abinda ya kawoshi, taba ni Ummaah tayi tace

“Tun dazun sukazo so kiyi sauri kisa wani abin kizo”

Idanuna Na lumshe ina jin wani mintsini da ale min a cikin zuciyata na farin ciki, kallon kayana nayi ba tareda daukar ko daya ba na rufe na nufi inda Abayas dina suke na samo wata simple royal blue abaya wadda egde dinta aka mata ado da wani silk blue material yayi kyau. Mayafin na yafa bayan na wanke fuskata na fito parlor Amma maimakon na ganshi se wata yar karamar yarinya wadda shekarunta bazasu wuce shekara biyar ba, sanye take da jeans se top an saka mata hula kalar top din. Wasa take da throw pillow din kan cushion din da take kai, gefenta wata middle aged mata ce tana zaune da waya a hannunta amma kamar da suke da wannan yarinyar ta baci. Hakan yasa naji hankalina ya kwanta daga tantamar da zuciyata take. A hankali na karasa inda matar take Na tsugunna a gefenta nace

“Barka da zuwa, ina yini?”

Da sauri ta dagani Na zauna gefenta tana ta murmushi kamar bakinta zai yage tace

“Mashaaa Allah, Alhamdulillah! Barka dai Asmau ya jikin naki?”

A kunyace nace

“Alhamdulillah!”

Dan yadda idanunta ke sparkling daga gani na kamar irin abinda kake jira dinnan shekara da shelaru ne yazo.”

“Yayi kyau, Raudha bakiga Anty ba, zo ki gaisheta”

Yarinyar tazo tayi hugging dina ta gaisheni , ina murmushi na zaunar da ita kaina naace

“Raudha”

Kallon Maman ta tayi tace

“Amiey, wannan ce Matar uncle Abbas din?”

Da sauri na kalli yarinyar dake shafa fuskata sannan na kalli uwar dake kallona with love a idanunta tace

“Inshaaa Allah”

Kunya ta kamani sosae, zuciyata wani irin bugawa take na kasa tantance a wanne yanayi nake ciki farin ciki ne ko mamaki. Kafin ta kara magana Ummaah da mama suka zo dauke da abinci akan tray, sannan ta zauna suka gaisa inajin tana fada mata su asalinsu iyayensu yan sokoto ne amma dukkansu a hadejia aka haifesu ta jigawa hakan yasa suke indigene tunda sun samu by birth. Nidai hankalina yana kan Raudha da nake feeding tana ta bani labarin Uncle Abbas. Can sega Abba ya shigo, har kasa Maman Raudha ta tsugunna ta gaisheshi ya kirani parlonshi. Tunda nasa kaina nasan Dr Kwaccido na ciki saboda kamshin turaraenshi daya baibaye ko ina Na parlon. Abba fita yayi so daga ni se shi se Raudha data biyoni tana ta tsalle tsallenta.

Cikeda damuwa yace

“Me yake damunki ne kin kalle ki kuwa? Nasa ki taho gida ki huta amma you are still falling sick. Y kike so nayi ne?”

Da sauri na dago kaina ina kallonshi, ya dage girarshi yace

“I care of course! My heart flutters whenever I see you or i remember you. Can you do me the favor of marrying a bachelor like me?”

9

Rate the page on a scale of ten

3

Ayshatuuuu ❣️Ban taba jin gidan mu ya isheni ba se wannan karan, seda naji inama nayi zamana a dutse ban dawo ba. Tunda nan din dana dawo dan samun relief kwatakwata abin ya gagara, se ma karin wani tension din da na samu.

Washegari, babu kowa gidan dukkansu sun tafi hakan yasa na fito da wurwuri na shiga kitchen dan hada breakfast se na samu Asiya ta fara hakan yasa nayi joining dinta muka kammalla. Ina cikin wanke hannu na cikin sink naji maganar Abba da Yaya Halifa, cikin sauri na fito dan ranar nake tunanin zuwa gidan shi. Suna zazzaune na samesu, gaishesu na fara yi sannan na tambayeshi su anty Zannira yace min dukkansu suna lafiya. Munata hira yawanci shi da Abba ne sede nayi ta dariya a haka Ummaah ta same mu. Gefen Abba ta zauna suka gausa da Yaya halifa sannan na gaisheta nima, amsa min tayi normal kamar ba jiya ta tara min jamaa ba. Nayi tunanin inama wani yayi min abinda Ummaah tayi min, inaga nida shi har abada amma Ummaah Ummaah ce tafi gaban komai, everything she said I consider it as frustration.+

Key Abba ya miko min yace

“Auta yau shekararki ashirin da shida, Allah yayi miki albarka. Ga gift dina”

Gaba daya na manta da wai yau birthday dina, tabbas girma ya hau kaina I couldn’t believe cewar I’m 26 years already. Kallon key din nayi na mota ne, ai wani ihu na buga ina fadin

“Abba mota? Abba nagode Abba Allah ya saka maka da mafificin alkhairi”

Na juya gurin Ummaah data tsira min idanu tana kallona, da murana na mika mata key din nace

“Ummaah kinga gift din Abba”

Maimakon ta karba se cewa tayi

“Haba Sir…”

Dake haka take kiranshi a matsayinshi na tsohon dan sanda

“…ta yaya zaka siya mata mota? Mu da muke son ta kawo miji tayi aure”

Gaba daya se naji murnar ta dauke min, dukkan mu muka saka mata ido muna kallonta da mamaki, nidai inajin anya Ummaah ta ce kuwa? Is she really my mom ko wani ke zugata haka? Abba yayi murmushi yace

“Madam, meye hadin siya mata mota da samun mijin aure? I see nothing”

“Dama baza kaga komai ba amma ai wannan maza tsoron tunkarar ta zasu dinga yi, gata likita ga mota”

Dariya sosae Abba yayi sannan ya dubi Yaya halifa kafin ya kara kallonta fuskarta a hade kamar hadari, yace

“Halifa, kaji zancen mamanka fa. Can you imagine? What if ta dalilin motar zata samu miji. Kema mutane sun fara miki wannan hudubar? Aure ai nufin Allah ne kuma ko shekara arba’in Asmau ta kai babu miji bazan takura mata ba, saboda abu daya na sani everything lies on it timing!”

Daga wannan maganar abin mamaki Ummaah ta fara kuka wai Abba ya fada mata magana sannan wai shi yake daure min wani guri shiyasa naki bada hankali nayi aure. Gaba daya hankali na yayi masifar tashi, na dinga bata hakuri ina lallashi amma ko kallona batayi ba, se na fara kuka nima naji gaba daya tamkar an kifar min da duniyar da nake ciki. Yaya Halifa yasa ni muka fita yana ta bani baki tareda nuna min komai zai wuce.

Da yamma naji gidan ya isheni, kamar ana hadamin wuta haka na dinga ji, babu sauki naje nace da Ummaah zanje gurin Adda Sa’ada, bata hanani ba se cewa tayi

“Gwara ki dinga fita ko kya samu mashinshini.”

Har na tafi ina mamakin Ummaah, mota ta kirar peugeot 206 blue na bude nayi addua sannan na tafi. Adda Sa’ada tayimin murna sosae, da muka kebe na dinga fada mata abubuwan dake faruwa , tayi ta bani hakuri akan lokaci ne sede I’m frustrated na gaji hakanan, bansan yaushe ne har laolacin zai zo ba.

Da daddare bayan na idar da sallar ishai na tafi parlon Abba dama seda na tabbatar Ummaah na dakinta sannan naje. Yana zaune ya gama cin tuwo na shigo tareda zama inda ya nuna min. Shiru nayi na rasa me zance masa saboda nauyinshi naji. Can yace

“Asmau ya akai ne?”

Kaina na girgiza nace

“Abba gobe zan koma dutse sa…”

“Saboda me? Ba kince min two weeks zakiyi ba, is just five days kawai fa”

Se na rasa me zance masa tunda ni dai I’m not used to karya amma bana son ce masa pressure Ummaah ce ke damuna tunda dazun naga sun samu sabani akaina.

“Asmau, Rukayya ce ko? Ita take damunki akan aure ko? Kada ki damu kinji ko komai lolaci ne, kada kiji haushinta nata salon kilawar ne. Kibar tafiya dutse ki kara hutawa kinji.”

Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na tafi nayiwa Ummaah sallama. Har naje bakin kofa se naji tace

“Asmau zo nan”

Jiki a sanyaye na koma na zauna kan carpet, gaba daya mun zama sirikai nida ita , idan ina tare da ita se naji wani irin nervousness na damuna. Drawer ta janyo ta fito da wata leda ta aje batace komai ba haka nima se shiru nayi ina fidgeting da hannuna. Asiya babu jimawa ta shigo da wani kasko cikeda ga garwashi, ajewa tayi a gurinda babu carpet saboda kar ya kone. Tana fita Ummaah ta mike tareda min alamar na bita, hakanan babu yadda zanyi na bita, wasu itatuwa ta ciro a ledar ta watsa cikin garwashin take kuwa wani mugun hayaki ya tashi, seda gabana ya fadi. Haka tasa Na tsugunna ta samu wani thick towel ta lulluba min. Na dinga tari ga mugun gumi da ya dinga karyo min Amma Ummaah seda nayi more than 10 minutes a haka sannan ta yayeni.  Dana mike se layi har seda ta rikeni sannan ta hada min ruwan wanka shima wasu magunguna ne a ciki amma ko uffan bance ba haka nayi, ina fitowa ta bani mai na shafa sannnan ta sallamrni na tafi.

Seda na jera kwana biyu kullum se anyi sau biyu kafin wani lokacin na fita a hayyacina, na rame na lalace nayi duhu. Babu arxiki na cewa Abba tafiya zanyi dan bazan iya zama ba. Shima duk abinda ake ya sani dan tuntuni na fahimci maganin farin jini ko na samun miji akemin, i cant afford losing my iman saboda hakan.

Da naje yiwa Ummaah sallama tace min

“Asmau akwai bikin Amratu, ina fatan zakizo”

Kaina na gyada amma deep down nasan wallahi bazan zo ba dan na rigada na rantse bana son zuwa na zama topic of discussion.

Da motata na tafi, wannan shi ne karon farko dana fara tuki me nisa and alhamdulillhi naje lafiya. Dakin kyaftun na wuce bayan na tsaya na zubarda magungunan da Ummaah ta bani cikin incinerator sannan na shiga. Tana zaune ta gama girki kenan na shigo nayi wujigawujiga dani kamar an jefoni. Tace

“Twin meye hakan? Me yake damunki?”

Zama nayi nace

“Bani abinci kede”

Babu musu ta zubomin shinkafa da wake da kifi se dressed salad da zobo, nasan gandar kyaftun hakan yasa nace

“Kinyi Bako ne?”

Fuskarta ta kwabe tace

“Dr Lamin ne yayi lunch a gurinna”

Kallonta nayi for some minutes kafin na cigaba da cin abinci na , seda na gama tas nayi wanka na dakko zani daga cikin wardrobe dinta na daura hade da top na dawo na zauna nace

“Twin, meye tsakanin keda lamin abin yafi karfin kawance sede wani abin”

Murmushi ta fara kamar na mata albishor tace

“We’re dating har yaje Bama”

Idanuna a waje , se kuma na saki murmushi nace

“Alhamdulillah, yafi muku ai kun zauna da kuna raina mana hankali”

Hakanan mukai ta hira har ta shirya zata tafi night duty sannan taga motar dan bance mata da ita nazo ba da dauki bazai batta muyi hirar ba.

AyshatuuuuuuChromic din hannuna na aje sannan aka miko min gauze na rufe muka rufe da plaster sannan na kalli kowa tareda sakin murmushi bayan na cire google din idanuna nace

“Alhamdulillah, nice job everyone!”

Dukka team din murmushi sukaimin kowa yana kokarin karasa abinda ya kamata, Apron na cire na wulla cikin bin, fitowa nayi tareda cire mask din dake fuskata na danyi mika sannan na tafi lounge dinmu dake cikin OT bayan na karba patients folder a gurin chief anesthetist naje na zauna kan cushion ina documenting aikina. Koda na kammalla banida wani aiki daya rage min hakan yasa na zauna tareda lumshe idanuna kamar wadda take bacci amma ba baccin nake ba, ina naga idon bacci? Matar da ko da daddare se nayi da gaske baccin ke daukeni balle yanzun ido na ganin ido, da dinma guri na samu amma yanzun babu halin hakan, dan damuwar da nake ciki kadai ta isa ta samin insomnia. Bansan adadin lokacin dana dauka a hakan ba se naji an bubbuga min kujerar da nake kai hakan yasa nayi firgigit na bude idona da sukai ja. Dr. Fadima ce tana tsaye ta zubamin ido, zama na gyara tareda kirkiro murmushi nace+

“Doctor yaushe kika shigo?”

Zama tayi kujerar dake facing dina se center table dake tsakaninmu, coke ne a hannunta chilled dan kadan ya rage yayi kankara. Tunda nake ban taba ganin coke addict irinta ba, kullum muka hadu se nayi mata fada amma sede tayi dariya kawai tace ai ina exercise ko kuma ace min inada glucometer. Haka dai take tana da kirki tare mukai medical training dinmu a Bayero.

“Dr Shahada, me yake damunki?”

Dan murmushi nayi nace

“Me kika gani? Am I looking terrible?”

“More than”

Ta fada tana hararata, murmushi na kumayi nace

“Kinsan yadda rayuwa take, mutum baa rabashi da matsala sede addua kawai”

Gyara zama tayi tace

“Amma naki ya fito da yawa, kowa ya kalleki yasan kina cikin damuwa. Kinga yadda kika koma kuwa? Idanunki are all sunken, you hardly concentrate.”

Dan runtse idanuna nayi sannan nace

“I’m trying”

Shi kadai ne abinda ya fito daga bakina, kanta ta gyada tace

“Anjima ki shirya tunda baki komai se mu fita, you need a fresh air”

Kaina na gyada nayi mata godiya sannan muka koma hirar aiki anan take bani labarin MD ya kusa retire, duk se naji babu dadi dukda bansan shi personally ba amma mutumin yasan me yake, i happened to attend a seminar dashi.

Da yamma kuwa muka fita wani hanan hangout, mukai ta hira da ita sannan muka ci abinci danni ko lunch banyi ba, dama kyaftun ke takurani naci, to taje off se ni daya. Sahad mukaje mukai shopping sannan muka koma asibiti. Se naji tamkar ta bani therapy ne. Washegari saturday, kuma shi ne ranar daurin auren Amratu, tun jiya akai kamu da mothers’ eve dama bazanje ba, koda su Ummaah suka kirani nace ai aiki ya cabe min bazan iya zuwa ko ina ba, Ummaah tayi fadan ta tareda jadadda min akan next weekend na tabbatar naje kwalam bikin wata neice dita, wannan nasan bazan tsallake ba, dole ne naje idan kuma ba wani problem nake son karawa kaina ba.

Ranar sunday muka hadu, Dr lamin, Dr Hafiz, Dr fadima, Dr Habiba, kyaftun dani muka shirya zuwa rock climbing. Tunda na tashi da asuba nayi wanka nayi mana toasting bread sannan na daukar mana drinks. Cikin leggings da knee length top maroon na shirya, nasa hula maroon se nayi rolling veil karami sannan nasa wani black canvas na tsaya a meeting point. Anan na tarar da Lamin da Habiba. Muka gagaisa sega kyaftun da fadima. Dr Hafiz ne ma yadan yi delaying har muka so makara. Garu mukaje inda zamu wani mutumi yazo danyi mana rakiya , tunda muka fara hawa dutse na fara ihu saboda abin ba na wasa bane, a daddafe wani lokacin se an ja hannunmu sannan muke iya hawa a haka dai muka kai karshen gurin. The amazing veiw ever. Aerial view din was wow mukai ta hotuna, nayi farin ciki, nayi dariya wadda take from the bottom of my heart bawai yake ba kamar yadda na saba yi. A wannan lolacin na manta cewar inada damuwa na manta da duk wasu matsalolina na kalla sama saboda yadda nake very high se naga kamr zan taba gajimare. I was so happy.1

STORY CONTINUES BELOW

Wajen sha daya muka koma prison dinmu, kowa ya tafi dakinshi, ina zuwa na cika bath da ruwan dumi na shiga da towel na gasa jikina, ina fitowa na sha pain reliever naci pasta sannan n kulle dakin na fara bacci, God so kind period nake bani Na tashi ba se wajen biyar da rabi shima knocking ne ya tadani. A kasalance na mike tareda tambayar waye amma babu amsa hakan yasa kawai na wuce toilet na sake wanka sannan na shirya.

Sati na kamawa ranar Friday, muna gama rounds na dauki hanya zuwa kwalam. Lokacin da naje zanyi sallama da kyaftun seda ta cemin nayi hakuri duk abinda zan tarar. Tabbas nasan ba wani abin arziki zan tarar ba, banda tsangwama da kuma nuna ni da zaa dinga yi. Anan sakkowa a massallacin jumaa ina shiga garin. Straight Cikin gida na wuce nidai nasan ba tarbar dana saba gani zan tarar ba a gurin Inna amma dukda haka na rugada na saba, indai nazo kwalam da dadi da babu dadi to gurinta nake zama saboda ko me inna zatayi min bazan taba manta alkhairin ta akaina ba. Wannan rikon da tayi min ma kadai ya isa balle yadda ta fifita ni akan sauran jikokinta.

Acan gefe nayi parking sannan na ciro trolley ta na rataya hand bag dita a kafada na doshi gidan. Muna dan gaisawa da mutane har Ikram yarinyar Adda Habiba da Badar yarinyar Yaya Hauwa sukazo suka karba kayan nawa muka shiga ciki. Gidan a cike yake anata kidan kwarya wasu na rawa, gefe ana sauke abinci a haka na kutsa kai ina gaida mutane wasu su ganeni wasu suce ai na girma duk kammani na sun canja, nidai nawa murmushi kawai.

A dakin inna na tarar dasu Adda da wasu daga cikin cousins dinmu, sunata shiri zaaje gurin kamu banma shige ciki ba na zauna cikinsu munata gaisawa yawanci na jima banga mutane ba kowa se cewa yake na zama babbar mace nayi kudi aure kawai ya ragemin. Sede inyi murmushi kawai. Adda Maryam ita ta tayimin ankon so gurinta na karba nawa na saka ko Inna bamu hadu da ita ba na tafi.

Wajen sallar ishai na dawo a gajiye seda na biya ta gida na gaida Ummaah sannan na taho. Nanma banga Innar ba, babu mutane sosae hakan yasa nayi shirin bacci bayan nayi wanka nazo n haye gadon cikeda kewarshi. Rigingine nayi ina kallon roofing din gadon tareda tuna rayuwar da nayi akan gadon, lokacin i was living peaceful banida wani tashin hankali daya takura min amma yanxun wace ni. Wayata na janyo na bude wani Emdex application ne na drugs, na cigaba da studying magungunan. A hankali bacci yayi gaba dani ba tareda na sani ba dama nayi addua kafin na fara karatun.

Na jima da yin baccin kamar daga sama naji ana tashi na, da kyar na bude idona raina duk a jagule saboda i hate it idan aka katse min baccin dare. Inna ce a tsaye tana kallona hakan yasa na tashi daga kwancen da nake tareda gyara zaman hular kaina nace

“Inna an wuni lafiya? Ya taro?”

“Lafiya lau”

Ta bani amsa sannan tace

“Asmau wannan gadon da kika kwanta akai ki sakko ki dawo kasa”

Kallonta nayi da rashin fahimta nace

“Ai zai ishemu mu kwanta ni dake, se kace nayi kiba”

Kawar da kanta tayi tace

“Kinga Amina da Nusaiba ne zasu kwanta akai saboda kinga su ciki ne dasu, kuma me aure bai saba kwanciyar kasa ba”

Kallonta nake sosae, maganar ta dakeni idan tacemin sakko Asmau wasu zasu kwanta saboda ciki, ni ai ba hauka nake ba nasan me ciki need something comfy babu yadda zaayi me ciki ya kwanta dandaryar kasa but meye se ance me aure bai saba kwanciyar kasa ba wato dole se an nuna min ni din banyi aure ba kenan. Kaina na gyada nace

“To ni ina zan kwana kenan?”

Tabarma dake gefe ta nuna min tace

“Ki sakko ki shimfida ta”

Wani mugun takaici ya kamani nace

“Inna, kinfi kowa sanin bana bacci akan tabarma, ina laifin waccan katifar”

Na nuna mata extra katifar ta da take jingine, a hasale tace min

“Ke sakko daga gadonnan, idan baki son tabarmar kina iya tafiya wani gurin. Yarinya se tsirin masifa da ruwan ido, dole ki kasa aure”

Yadda nake kallonta seda yasa ta dauke kanta naji haushi sosae yadda har bazan iya fada ba, kaina na girgiza tareda sakkowa daga gadon na finciki hijab dina da wayoyina nayi waje amma se na dawo har lokacin tana tsaye bance mata ci kanki ba na janyo trolley na da hand bag dita na nufi kofa se ta biyoni tana fadin

“Matsalata dake kawata zuciya, meye abin hada kaya?”

Juyowa hawaye ya cika min idanu nace

“Aure Allah yake sawa ayu, idan lokacina yayi zanyi, gorinku da duk wani tsangwama ta bazai saka nayi ba.”

Kafin na gama tuni wasu daga cikin mutanen dake parlor sunzo suna tambayata me ya faru babu wanda na kula nayi ficewata Allah yasa bankai motata gida ba hakan yasa na bude motar na shiga tare da kifa kaina jikin steer wheel na fara kuka, a raina ina rokon Allah ko aron wucin gadi ne yasa nayi, ko ma wanene kawai Allah yasa nayi aure na huta. Seda na gaji da kukan sannan na kira Adda zannira akan ta bude min gida ina nan tafe. A takaice dai acan na kwana, juyin duniya Yaya Halifa yayi akan na fada masa meye matsalata naki suka hakura suka kyaleni.

Washegari ban fita ko ina ba ina daki ina jinyar zuciyata bansan waye yace ma Inna ina gidan ba se gata tazo da kwanuka wai na kari nace mata ni na koshi bazan ci ba, ta kada ta raya naki, ko ji tayi abinda tayimin bai dace ba oho mata dai. Da yamma kuma sega Ummaah itama abin mamaki lallashina ta dinga yi har ta tsareni naci abinci sannan ta tafi. Da daddare mamansu Rahina taxo biko akan na koma can gurin inna amma nace ni sede wata kuma, ba dai aure bane to nayi alkawarin ko dan cocaine ne yace yana sona aurenshi zanyi, na gaji da wannan masifar har ina?

AyshatuuuuWayata na kalla a karo na barkatai ina kallon text din da Ummaah ta turo min kusan awa daya data shude , numbers ne har guda biyu na GLO da MTN a kasan an rubuta Barr. Ishaq. Kifar da wayar nayi kawai ina jiran inji kiranta dan tayi min karin bayani amma shiru bata kira ba, nima kuma ba kira zanyi ba saboda ina tsoron abinda zatace min, bana son hooking stuffs dinnan gwara no matter how bad a situation is gwara ace shidin ya fara ganinka yace yana so, dan bahushe yace matar cushe bata da kwarjini. I believe in that also.+

Hakan yasa na mike na cigaba da gyaran daki. Ranar call nake so yamma nayi Na shirya na dauki stethoscope da key din mota da wayoyina na fita. Call room naje Na zauna a gefe ina chatting a wayata ni kadai ce cikin dakin, se can aka kirani a Emergency hakan yasa na tashi na tafi na tarar da wani fatal accident. Tabbas aikin asibiti dole yasa ka kara gaskata iko da daukaka ta ubangiji, mutum ba komai bane a rayuwa duk wannan dagun kai da dagawa amma lokaci daya Allah zai iya reforming halittar shi muga ta karshen girman kai. Mutanen da sukai accident su goma ne cikin wata golf, i wonder yadda sukai squeezing kansu cikin wannan karamar motar.

Ina shiga na adana wayoyina da sauran abin amfani, O’C dake duty su uku muka hadu dasu dan ceto ran mutanen, amma uku seda suka mutu babu yadda zakayi, sede you will be contented kayi abinda ya kamata tunda duk munsan death is inevitable. Haka sauran bakwai muka sakasu cikin class din daya dace bamu muka zauna ba se bayan sallar ishai. A matukar gajiye mukai sallah sannan na dawo dan nayi documenting aikin, sannan mukai sallama na koma lounge anan na tarar da missed calls din Ummaah. Ina zama na fara kiranta ta dauka nace

“Ummaah inata aiki kika kira, ya gida?”

“Lafiya lau”

Ta bani amsa sannan tace

“Kinga numbers da na turo miki dazun?”

Seda gabana ya fadi nace cikin sanyin jiki

“Na gani Ummaah, inata son na kiraki”

“Ni dana matsu ai na kira, kinsan Hajiya Barira right?”

Kaina na gyada kamar tana ganina nace

“Eh, Ummin Kaduna ko?”

Kawar Ummaah ce irin childhood friend dinnan ce , kowa yasan yadda Ummaah ke ji da ita haka itama indai zatazo kano to se kin ganta tazo gurinta.

“Yawwa, wannan Ishaq din danta ne na uku zaiyi aure shine nake son ku daidaita kanku, kinga kema kya samu ki huta da gorin mutane”

Se nayi shiru tareda adduar Allah yasa ba nufinta in kirashi ba, jin nayi shiru yasa tace

“Baki jina je Asmau?”

“Ummaah to me zanyi yanzun?”

“Kiranshi zakiyi mana, me kike jira da? Come on ki kirashi kice kece wadda Hajia tayi mishi magna akai”

Se naji raina ya baci ni zan kirashi ma bashi ba, ok ya raina ni kenan. Ni na gaji da yadda Ummaah ke hadani da yaron kawayenta suna raina min hankali dan wannan shine third time ana hakan.

” Ummaah, dan Allah karki sani nayi haka, shi ku bashi number ta ya kirani mana amma hakan kamar irin neman kai akeyi dani ne?”

Baki bude Ummaah tace

“Oh da baki gane ba? Shi ai bashi yake nema ba mu muke nema so mu zamui proposing kingane?”

Kaina gaba daya se ya kume, I couldn’t think straight wanne irin ni nake nema ni zanyi proposing? Kawai se nace

“Shikenan”

Kafin muyi sallama ta tambayeni ni na tura mata kudi nace eh, tayi ta shimin albarka har naji dadi sannan na kashe wayar inajin wani abu ya tokare min kirjina, da kyar nake iya fuzgar numfashi na, idona yayi ja ina fatan Allah ya kawomin dauki a rayuwata, ya kawo min miji nayi aure. Dan nasan bani kadai ce a duniya nakai shekarun nan banyi aure ba amma kowa ya takura min an hanani zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hannuna nasa na rufe fuskata nayi ta kuka kamar raina zai fita ina fatan as my tears cascade down my cheeks, all my worries will be gone and my pains will be ease!

Ina gama kukan lokacin already goma tayi ko lunch banyi ba balle dinner, yunwa nakeji amma bana tunanin inada nutsuwar zama naci abinci. Mikewa nayi na fito daidai shigowar kiran kyaftun ,  se naji wani sanyi cikin raina at least someone cares. Ina dauka ta tambayeni inda nake , ko minti biyar ba ayi ba se gata da basket a hannunta, tunda ta kalleni se naji jkinta yayi sanyi , zama tayi ta hadamin tea ta bani babu musu nasha sannan ta zuba min Arabian sphaghetti tasha vegetables haka naci sannan tace

“Wannan kuburin na ido me ya faru?”

Lumshe idona nayi ai kamar ance lacrimal glands su sake hawaye se suka wanken fuska, hannuna ta rike batace min komai ba se kallona da takeyi , se can tace

“Asmau menene akan aurenne?”

Kaina na gyada na fada mata komai daya faru, se cemin tayi

“Ki kirashi kinji”

Wani kallo nayi mata irin are you mad dinnan? Murmushi tayi tace

“Ummaah ce tafi karfin komai, just do it saboda haka Ummaah tace”

Haka na kwana ina tunanin yadda zan bullowa koda safe dana fadawa Adda Sa’ada cewa tayi nayiwa Ummaah biyayya hakan kuwa nayi dukda jikina a matukar sanyaye yake haka Na kirashi, tunda ya dauka ko sallamar da nayi bai amsa ba yace

“How may i help you?”

Duk se naji na muzanta amma haka na daure nace

“I’m Asmau shahada, ni ce wadda hajianka tayi maka magana akaina”

Maimakon naji tone dinshi ya canja se naji ya kara tamkewa yace

“Ya akai to?”1

Na kasa cewa komai se wasa nake da hannuna tareda jin mugun haushinshi kamar na shako shi haka naji, jin nayi shiru se cewa yayi

“Kinga idan kin shirya bayanin kanki kya kira but I’ve better things to do!”1

Kit! Ya kashe hannuna na rawa na ciro wayar ina kallonta da gaske yayi hanging, take nayi deleting numbers dinshi daga wayata baki daya inajin tamkar na shake kaina tabbas Ummaah ta gama dani. Da daddare ta kirani akan ko na kirashi na fada mata yadda muaki dashi, tsaki tayi tace na kyaleshi to wannan ya dan sayaya min rai.

1

Ana fara tafiya aikin hajji na tafi nima, i badly want to talk to Allah, lokacinda na ganni gaban kaaaba se kuka na rasa abin roka, se kankame jikina da nayi saboda yadda dukkn tsikar jikina ke tashi. Na jima sannan na samu nayi addua dake lokacin mune daukar farko i got the space. A wannan lokacin alkawarin Allah ya cika kyaftun ta auri Dr Lamin.

Bayan na dawo nigeria da hope akan nasan da izinin Allah kukana ya zo karshe. Nasan soonest alkawarin Allah zai tabbata kaina amma shiru har shekara take neman zagayowa, banma kara saurayi ba duk yadda nakejin nakai babu wanda ya kalleni da sunan yana sona, nasha tsayawa gaban mirror na kalli kaina, inga ina nake da makusa. Ni fara ce fari sosae har wani yellow yellow nake, idan nayi mirmushi bayan dimple dake lotsawa a both sides na kumatu na, akwai wata jijiya green dake fitowa rado rado a goshina. Idanuna normal suke kamar na kowa sede eye balls dina manya ne kuma deep chocolate orbs nake dashi. Hancina dogo ne bakina daidai ni da kaina nasan im a beauty, akaina na fahimci kyau baya kawo miji se lokaci yayi.

Pressure kam se wadda ban fada ba amma akwai lokacinda nayi wata hudu banje kano ba ina dutse saboda Ummaah kamar ta dakeni idan muka hadu ga inna kamar danni ta koma kano saboda girma, kullum gorin yau daban na gobe daban. So se na daina zuwa gidan gaba daya, sukai cigiyar duniya suka rasa. Ranar wata monday na shiga OT yin Appendectomy, ina fitowa straight dama daki nayi niyyar tafiya dan na shirya zanje wata seminar, da sauri na kalla office din Chief Anaestethist saboda jiyo muryar da Abba da nayi. Banma yi niyyar shiga ba haka na shiga and there i saw him sitting looking at me. Da sauri naje na rungumeshi nace

“Abbana”

Hararar wasa yayi min yace

“Nazo biko ne, tunda laifin wasu ya shafeni”

Dariya nayi tareda rufe fuskata , i cant remember ni ina dariya genuinely har haka ba. Ranar se dare ya tafi ko seminar bankje ba, tare mukai lunch a cafeteria se naji ina missing gida sosae. Lallashi na yayi yana nuna min komai zaizo karshe. Haka sati na kamawa naje kano se naga babu wanda ya takira min like always do.

AyshatuuuuHannuna na zura cikin aljuhun lab coat dita na ciro wayata saboda jin alamar shigowar message a wayata. Message dinne kuwa daga chief obstetrician dake last month na koma gynae team na bar surgical team na fara residency dina. Kallon metron din nayi nace mata

“Mummy, zanje meeting idan akwai matsala a kirani”

Kanta ta gyada tareda min fatan alkhairi, inason matar she’s mother figure, a dan zaman da nayi a ward dinta tana yawan bani shawarwari masu amfani tamkar tasan matsalata akan aure take kullum ni da sauran nurses dinta akwai topic din da zaayi discussing akai. Kuma baka isa kace ka zauna bakayi gaining wani abu ba. Office din Dr halima na wuce dake ita ce chief din tamu, na tsaya ni da Dr hafiz se gata ta fito in her usual outfit wato lace gown an daura lab coat akai, irin classy mutanen ne yar gayun gayu sosae. Da sauri na karasa inda take nace

“Maam naga message dinki gani”

“Yaawa nima yanzun nake shirin kiranki muje meeting zaayi na tarbar sabon MD”1

Kaina na gyada tareda bin bayanta munata dan hira jefijefi, a office din Dr Mahmud anan muka zazzauna akai briefing kowa akan washegari sabon MD da akai posting zai fara aiki , seda Dr Rashida ta ja mana kunne akan kowa yayi watching takunshi saboda baya wasa mutumin idan zaayi aiki ayi dan shi baya daukar kailula. Ta tsoratar damu sosae Amma banji komai ba dana nasan bana barin aiki Na unfinished. Haka muka gama se kuma muka koma office din Dr halima danyin meeting da sauran yan team dinmu. Kafin wani lokaci dukkan asibitin kowa ya shiga hankalinsa ko ward ka shiga se gyare gyare akeyi da fito da sabbabin linens a haka dai ranar ta kare na tafi gidan kyaftun.+

Washegari da safe da wurwuri na gama shirina nayi breakfast dan nasan it will be a busy day i know. Hakanan na fito na shirya cikin coffee wando da riga na soft cotton yadi lab coat na daura ban mayi buttoning ba na rataya stethoscope dina a wuya sannan nayi rolling da karamin coffee veil. Kallon kaina nayi a jikin mirror babu laifi idanuna sun fara dawowa hayyacinsu, wannan zurmawar da yayi ciki duk yadan fito dan hankalina ya fara kwanciya na daina tsangwamawa kaina tunda nasan wannan bashi zai bani miji ba.

Gynae emergency na fara zuwa muka gaisa da staffs din gurin sannan aka bani patient din da zanyi reviewing. Ina cikin aikin Dr halima ta karaso mukai rounds sannan muka shiga labor room nanma stable babu wani damuwa sosae a ciki nan muka gama sannan nida ita muka fita. Ko ina cikin asibitin tas yake kowa ya shiga taitayimsa haka kowa yana post dinsa se naji zuciyata tana kwadayin ganin waye wannan sabon MD, naji dadi a raina saboda kowa zai dawo hayyacinsa kowa ya fahimci abinda ya taramu a asibitin.

Karfe goma dukkanmu muna tsaye a reception Doctors mu shida daga kowacce cader mutum uku muna tsaye dan tarbarshi, wayata tayi ringing na dauka Dr Ema ne wani house officer ne su na bari a labor room akan duk yadda ake ciki su kirani, seda muka gama magana dadhi sannan na fadawa Dr halima ta fadamin yadda zamuyi kawai se na juya na tafi, ina zuwa na tarar matar tana wani irin massive bleeding babu anyi anyi ya tsaya yaki hakan yasa nabi shawarar da sister ta bayar akan mu cire mahaifar kawai, dole muka tafi OT and that’s how i missed ganin sabon MD.

A wannan satin kowa ka kalla cikin asibitin kasan ya dawo hayyacinsa, aiki kowa yake ka’in da na’in nidai bamu taba haduwa dashi ba har yayi wata a asibitin. Kowa complain yake akan ya takurawa mutane, to dama hakane idan mutum yazo yana kwatanta gaskiya tabbas kowa zai tsane shi.

Ranar wata litinin nayi aiki na gaji daga nan na tafi Amenity unit wajen kyaftun, mun jima da ita muna hira sannan na tashi n koma lounge. Muna da yawa cikin lounge din masu cin abinci nayi haka wasu na research inda na saba zama naje na zauna bayan mun gaggaisa da Doctors din. Wata Dr hajja watching buddy dita ce ta kawo min wani romantic doctor korean film.1

“Shahada watch this film yayi kyau sosae fa”

Bakina na tabe nace

“Rabani da wannan romantic films din nasu, ana nuna soyayyar da bata existing gaba daya”

Dariya tayi tace

“Hooo Anty Asmau i cant wait naga wanda zaki aura, bama romantic din bane ba, surgeries ne kalakala a ciki zaki karu”

Da haka tasa na karba film din cikin flash dina, komawa na gyara zamana kan cushion din nayi na fixing wayata a charge tareda dan runtse idona a hanaklai bacci ya fara kokarin fizgata, dama gefena wasu house officers ne mata suna zaune Ina jin dayar tace

“Ke kinga sabon MD kuwa”

Bude idona nayi a hankali na kallesu amma duk saboda yadda suka zama engrossed ko effect din idanuna basuji ba, dayar tace

“Kin ganshi ne ke?”

“Sosae ma, though daga nesa ne, ban taba ganin mutumin da fada yake mishi kyau ba se shi, baya murmushi fa amma he’s so cute mashaaa Allah”

Ta fada tana rungume fuskarta da palms dinta, se grinning take, se suka bani dariya. Na dauka ni kadai nayi shashancin admiring maza da kuma one side love ashe inada yan uwa.

“Awnnnn I’m crushing him already”

Wayata ta katse min hanzari da ringing, kaina na kaudar da sauri, tareda sakin siririn tsaki sannan na janyo wayar wata sabuwar number ce, picking nayi tareda karawa a kunnena

“Dr Shahada, Dr halima ce”

Da sauri na gaisheta se tace min

“Kina jina ko? Akwai wata middle age woman a labor room kamar ta samu ruptured uterus, kije yanzun kiyi reviewing dinta in the next 20 minutes zakui mata aiki a OT keda MD”

Ambatar MD seda gabana ya fadi me yasa nida MD. Mikewa nayi na tattara kayana na fita cikin sauri, muryar Dr halima nayi min echo a kunnena

“Nasan zaki iya, i trust your skills amma ki kula sosae sannan kiyi komai da sauri amma with care, kada ki bari ya kamaki da wani matsala. All the best”

Ina shiga labor ward na karanta write up din matar naje nayi assessing dinta sannan na zauna aka shiryata daga nan na wuce OT nayi changing, ranar chief anesthetist din shi zai bamu anesthesia da kanshi sabida wannan shi ne first time da zaiyi aiki a OT tunda yazo. Cikin five minutes suka kammalla komai hakan yasa na kira Dr halima na sanar mata mun kammalla.

“Bara na turo miki digits dinsa ki fada masa kun shirya”

Idanuna a warwaje nace

“Kai dan Allah ki fada masa”

Dariya ta danyi tace

“Shima mutum ne kamar ni”

Daga haka tayi hanging, se na rike wayar sororo ina kallo, aikuwa sega pop din message nata ya shigo, Dr Kwaciddo nayi ta nanatawa kafin da kyar nayi summoning courage na kira shi, muryata a dan rikice nace

“Sir I’m Dr Shahada, muna jiranka a OT koami is set.”

Cikin stern voice yace

“Alright! I’ll be there inshaaa Allah”

Sauke wayar nayi tareda sakin ajiyar zuciya, se naji ya burgeni da yace inshaaa Allah. Ina nan tsaye baifi 10 minutes ba se naji shigowar shi. Dogo ne sosae dan idan na karu jikinshi Allah yasa zan kai aljihun gaban rigarshi, nima a mata bana cikin sahun gajeru amma this is to show how tall he’s. Ba siriri bane da ace bashida tsayi kibarshi se tafi fitowa amma dake yana da tsayi se ta shanye kibar. Shi ba fari bane yafi ga a kirashi baki sede not that dark, ga jin dadi se yasa fatarshi take glowing, smoothly tamkar mace kana kallon fuskarsa kaga ta bafullatanni ko ba usul ba amma an samu trait din cikin jini. Wannan shine MD or i can call him Dr Kwaccido.

Hannunsa ya tafa yana fadin

“Set?”

Kaina na gyada nace

“Set sir!”

Ciki muka shiga bayan mun jira yayi changing, yadda yake aiki will tell you shidin ba na yau bane yasan scalpel scapel tasan da zamanshi. I was extra careful akan aikin har muka gama muka stitching gurin sannan ya kalleni yace

“It’s nice working with you”

1

Ayshatuu1″Thank you sir!”

Kawai nace mishi ba tareda na bari kalamamsa sun shiga kaina ba, nasan I’m skilled person duk wanda yayi aiki dani komin yadda ya kware to tabbas se yasan nima na maida hankali. Cikin lounge yaje ya zauna aka kai masa folder yayi documenting sannan ya yiwa kowa bangajiya kafin ya tafi, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan na fita baki daya daga OT. Ward na koma na karasa ayyukan da suka kamata nayi sannan na tashi gaba daya.

Washegari ranar friday, muna kammalla ward tounds dinmu na shirya dan tafiya kano a raina ina tunanin ya kamata yau ba se gobe ba na fadawa Abba kudirina. Misalin karfe uku na isa gida saboda na biya gidan Adda Maryam da nayi niyyar se yamma na koma gida amma ta bata min rai shiyasa na taho. Ina gidan kanin mijinta wani Nasir yazo, that wasn’t the first time dana hadu dashi a gidan sede baifi sau daya muka taba magana ta minti uku dashi ba kullum daga gaisuwa bamu karawa saboda naga dan raijin wayo me, ni kuwa bana cikin wannan class din. Tunda ya shigo muka gaisa naja mutuncin kaina na cigaba da kallona sunata hira shida Adda, can sega mijinta ya dawo, Yaya Mansur muka gaisa ya zauna yana ta jana da hira dake he’s very jovial to tamu ta zo daya dashi.+

“Kina wuta fa matar nan, nazo kofar gidana naga wata benz, so inata tunanin wa muka samu? Seda na hango wannan ear piece din naku kafin na gane ashe kece”

Dariya nayi dan Na fahimci stethoscope yake nufi, nace

“Babu wani wuta fa Yaya, amfani ake da dama”

Murmushi yayi ya gyada kai yace

“Yeah! Allah ya kawo miji na gari”

Amin na bashi amsa ina murmushi, kallona Adda tayi tace

“Kamar gaske”

Ko kulata banyi ba  tashi tayi ta wuce ciki itada yayan, bata jima ba ta dawo hakan yasana wuce kitchen akan na duba abinci dan a daura wani, idan naje gidan sisters dina se nayi musu dinner nake tafiya. Kamar daga sama naji Adda Maryam na cewa Nasir

“Kaima kaki kayi aure kamar Asmau, ko baka da budurwa ne?”

Shiru nayi inason jin amsarshi se yayi dariya yace

“Kai time baiyiba, se an tara tukunna”

Gyara zamamta tayi tace

“Kaga Asmau shes 27 years yanzun, gata medical doctor, babu wani serious magana akanta, bana tunanin tana da saurayi gaba daya so idan tayi maka why won’t you tag along kuyi aure”

Idanuna na lumshe jikina har bari yake na rufe warmer da sauri zan fito kawai naji yadda gayen yake babbaka dariya hakan yasa na tsaya, naji yace

“Kina da abubuwan dariya Antinmu, ni wannan kanwar taki ai ta girmeni ma……in a mocking way ya fada, se naji kafafuna sunyi wani sanyi…..27 kikace? Tabdi! Beside ni fa bazan iya auran health workers ba ke wallahi ko a kafa aka daura min su se na kunce”

Tamkar walkiya haka na ganni a  parlon, wani irin mugun kallo na masa nace

“Ai ko maza sun kare nafi karfin na aureka, Adda na gode”

Daga haka na dauki jakata dama veil dina tuntuni yake a jikina nayi waje na barsu baki a sake, mota ta na bude na shiga se kuma nayi shiru ina ganin menene abin fushi har haka? Me yasa raina ya baci dan anyi talla ta, tunda auren yaki zuwa may be kilan ta hakanne zan samu miji. Zuciyata se ta kasu biyu wata na blaming dina wata na tafarfasa tana ganin an raina min hankali ajina ya wuce ayi kamar ana nanawa namiji yana kin karba.

Ina gama parking sega Yaya suleiman, tsayawa yayi yana kallona ni at first ban ma wani lura dashi ba kokari nake na bawa Baba me gadi key din ya shigo da kayan da nazo dasu. Ji nayi yace

STORY CONTINUES BELOW

“Ajhumma!”

Nasan shi daya ke kirana da wannan sunan hakan yasa na dago fuskata a sake na dubeshi nace

“Oppa”

Se naji na tuna da, kamar yadda oppa yake nufin Yaya a korea, yawanci suna fadawa saurayi hakan, tone din da suke using kadai kasan cewar bawai brother yake nufi ba aa sede something else. A wancan lokacin I’m feeling the same, lokacin dana fada se naji wani sanyi a raina but see me today, saying oppa plainly and emotionless rayuwa kenan. Yaya suleiman da naso na kaunace and so much badly wanted na zama mallakinsa amma ya dubi idanuna yace kawata yake son nayi hooking dinsu tare, i felt shattered. That’s then!

“Ya aikin? Kinyi kudi kin manta damu, kullum Nadia tana cigiyarki ko ziyara baki kawo mana”

“Aiki sede godiyar Allah. A gaida Nadia da yara”

Na fada saboda zancen babu ziyara ba mutum daya le zumunci ba both parties keyi, bantaba tunanin zan rabu da raihana da Nadia ba Amma yanzun ni ko numbers dinsu bani dashi. Duk yadda Yaya suleiman yaso na tsaya na nuna masa a gajiye nake dole hakanan yayi hakuri na shige gida. Ummaah Na parlor a zaune itada Asiya na shigo, Asiya ta rungumeni sannan ta bamu guri. Gaisawa nayi da Ummaah tace

“Ina kika tsaya? An shigo da kaya amma ke shiru”

“Nida Yaya suleiman na tsaya”

Bata kara cewa komai ba haka nima se na mike na wuce na tafi dakin Inna, tana zaune kamar kullum ana goga goro. Karba nayi kamar yadda na saba ina gurza mata muna dan taba hira abin mamaki. Hirar arxiki kuma wadda na jima bamui nida ita ba. Tana ta bani labarin ‘yan matancinsu ita da fara yar shehu

“Naso Asmau fara yar shehu ta rayu zuwa wannan lokacin ta ganki. Kawata ce wadda banda kamarta kuma ko bayan data mutu babu wanda ya maye min gurbinta, da yake ita mahaifiyar ta yar Mambila ce to dukkan mu tafi mu kyau, kyakyawa ce ta gaske hakan yasa tun muna shekaru tara aka sakata a lalle, naso kin biyo farin jininta da tuni kina dakinki, da kuma ace shahada da Saude sun barki hannuna da tuni baki shiga wannan kuncin ba.”

Dan murmushi nayi nace

“Inna lokaci ne”

Kanta ta gyada tace

“Da farko nayi tunanin laifinki ne shiyasa na matsa miki, amma a shekarunki na san kowacec so take ta ganta dakin miji. Ina fatan baki rikeni a ranki ba”

Rungumeta nayi da sauri ina dariya nace

“Waye yake fada da kawar shi? Sede idan kawancen bai kai zuci ba”

A wannan na samu sauki, ranar aka tuna da tare muka kwana, Abba nata tsokanar mu wai yau mun hada kai. Da safe nayi dukkan abinda ya dace wanda ya kamata sannan na koma bacci. Wajen sha daya nayi wanka nasan Saturday ce Abba bazai je gona ba, dan baya fita Friday da Saturday he always say they’re meant for rest. Kuma haka yake. Yana zaune shida Ummaah suna kallon Aljazeera, yau mun samu bakuntar yaran Yaya halifa dana Adda ummiey so suma suna parlon se kinji suke. Ina zama muka gaisa yaran suka gaisa se Ummaah ta fita naji dadin hakan sosae a raina dama bana son tana nan bazata bari nayi magana cikin nutsuwa ba.

“Nasan wannan zaman akwai magana, ina jinki”

Abba ya fada yana rage volume din, zamana na gyara nace

“Abba kayi hakuri dukda baka taba magana ba amma nasan kullum yana ranka, nima ba haka naso ba Abba na kai har lolacinnan banyi aure ba”

Murmushi yayi min yace

“Asmau! Ai bake kika hana kanki ba, shima Allah ba hanaki yayi ba he’s testing our faith kin gane?”

Kaina na gyada yace

“So, ki dage da addua Allah baya bacci. Ban taba miki zancen aure ba, bawai bana so kiyi ba ko kuma irin ban damu dinnan ba, ko daya I’m worried, sede ya zanyi idan na takura miki me zai canza?..”

Kanshi ya girgiza yace

“…Nothing my dear, ‘ya’yana takwas kowanne is educated islamically and western, bakwai sunyi aure kowanne peacefully, ke daya kika rage idan na kasa hakuri me nace da Allah? Ban gode bisa abinda yayiwa ‘ya’yana bakwai ba. Kinsan musulinci is wonderful, komai is open sede idan baka sani ba. Aure abu ne me girma, sunnah ce me karfin gaske sede mu bamu dauka sunna bace kawai aure wajibi ne idan bakai ba gani ake kaika jawo amma i know kinsan tarihin Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S batayi aure ba amma sura kacokan sunanta ne, so bawai se kayi aure zaka samu yardar Allah ba kede ki tuna tarbiyar da nayi miki kawai, ki kare mutucinki da martabarki. I tried as much as i can na zama mutumin arxiki saboda ku, nasan ko bani da rai zaace wannan yaran CP Shahada ce, amma idan na zama mutumin banza akwai matsala abinda zai zama rightfully yours zaa iya denying muku.”

Se naji sanyi cikin raina saboda maganar shi tayi min dadi naji sanyi da farin ciki a raina. Gyara zamana nayi nace

“Abba na samu wata school a America, idan ka yadda ina son zuwa”1

Shiru yayi yana ta kallona har seda yasa na fara jin uneasiness, se yayi murmushi yace

“Zan iya yin tunani da shawara?”

Kaina na gyada nace

“Sure Abba”

“I’ll get back to you”

_I left you guys waiting and I’m so sorry for that. Nayi typing wannan breakfast din for you all, ina fatan I’ll get some mind blowing and awesome comments from you guys as always. Yeah! Ina ganin comments dinku na karanta but replying duka will be hectic y”all know that Nagode sosae Allah ya bar zumunci. Daga yau zanje hutu saboda my friend is getting married, pray please. Is an important biki da bazan iya typing ba har se naga na rakata dakin miji kafin na dawo nutsuwata. I hope zaku min uzuri as usual_

1

_*Yours Truly*_

Ayshatuuuu😍Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da naji ya tabbatar min it’s a no kenan. Hakan yasa na dangana ba tare da na kara masa magana ba. Wani sati na dawo na tarar da Ummaah ta cika fam kamar zata fashe dama wannan mood din kam ai na saba dashi. Tunda naga haka na kama kaina tareda jan mutumcina. Washegari inadakin inna muna hira ta aiko Asiya akan ta kirani. Ina zuwa na ganta a zaune gefen gado tana ta karkada kafa, zama nayi kan carpet nace

“Ummaah gani”

Key din motarta ta mika min tace

“Dakko hijab dinki zamu fita”

Babu musu na mike hannuna rikeda key din na tafi dakina, dama atamfa ce jikina dinkin skirt da riga so kawai se na dauki hijab coffee dake atamfar da coffee jiki, shoe rack dina na duba na dauki wani flat milk vine se purse sannan na fito , ganin tana jirana yasa ko Inna banyiwa sallama ba kawai na wuce gaba tana bayana. Seda nayi warming motar sannan nayi addua kafin muka fita. Kallonta nayi tana ta danne danne a wayarta nace+

“Ummaah ina zamuje?”

Dago idonta tayi ta kalleni, then ni kuma na rigada na maida hankalina akan titi tace

“Gidan Hajiya Zakiyya zaki kaini”

Seda naji kaina ya sara min baa taba matar da bana so a kawayen Ummaah ba kamar wannan matar, tana daya daga cikin masu zuga Ummaah akaina. Babu yadda na iya haka na dauki hanya amma bakina banda neman agajin Allah babu abinda nakeyi nasan shi kadai yasan abinda nake going through kuma shi zai kawo min dauki. A hanya na tsaya a filling station nayi mata full tank sannan muka karasa gidan. Ina parking nayi wining glasses din sannan muka fito, tana gaba ina baya muka shiga gidan, sunada kudi haka kishiyoyinta uku kuma ita ce ta biyu amma kana shiga zaka san ragamar gidan a hannunta take ita take juya kowa har shi mijin so bana son wannan kawancen. A katon parlonta muka zauna sannan yan aikinta suka cika mana gaba da abinci kafin taxo, tana shigowa tazo ta rungumeni tana fadin

“Daughter da bata zuwa gurin mamanta ko”

Dan murmushi nayi nace

“Aiki ke hanani wallahi amma ai bazan manta Mami ba”

Zama tayi suka gaisa da Ummaah ni kam na bude exotic na tsiyaya na sha bana son tace naki cin komai. Ina nan zaune inaji suna magana kasa kasa se kuma can Mami tace min

“Asmau jeki daki ki jiramu”

Mikewa nayi na tafi dakin tareda crashing akan gadon na dauki wayata ina random searching da ban masan me nake dubawa ba, baki daya hankalina yana parlon. Har nayi waya da kyaftun ta dan dauke min kewa sannan ta kara reassuring dina sannan naji hankalina ya kwanta. Wata Nannyyy ta shigo tace min nazo inji Ummaah. Mikewa nayi na gyara zaman hijab dina sannan na fito kwatkwata idona bai ma lura da mutumin dake zaune ba seda na zauna sannan na ganshi a zaune, mutumin yafi kama da boka gaba dayanshu a birkice yake gashi fal fuskarshi yana zaune se karkada kafa yake, ga wani wari dake tashi kuma nasan tabbas daga jikinshi ne, dan lokacinda muka zo parlon banda kamshin lavender babu abinda yake, i love the scent of lavender so duk inda naji shi se matar ta fado min saboda kamshin gidanta na dindin kenan.

Abu daya da bana tolerating duk kawaici na shi ne wari bana iya jurewa, ko minti daya ban cika ba kawai se naji cikina ya fara kadawa zuciyata tana tashi, i was completely nauseous. Kallon Ummaah nayi zanyi magana kawai naga mutumin yayo kaina gadangadan, fusace na mike tare da ja da baya ina muzurai, instead ya tsaya se naga ya nannada malum malum dinshi yana neman kai hannu jikina,

“Karka taba ni, Ummaah kina kallo?”

Kamar bai ji ba haka ya dinga bina har nakai bango, idanuna na runtse bakina yana ambatar sunan Allah kawai se naji hannunshi yana shafa fuskata, wata muguwar kara na saki tareda zubewa a gurin sumammiya. Bansan me ya faru ba i don’t even know, na dai san daga baya wai ashe me maganin aljanu ne aka dakko shi saboda ana tunanin aljanu ne suka kama ni shiaysa na ki nayi aure. A gado na sameni lokacinda na farka ni kadai, koda na tashi se na fara jin kaurin tukake, tashi nayi na zauna anan naga yadda hayaki ke tashi wai duk ni akewa turare, gaba daya zuciyata tayi min nauyi, kirjina banda zafi babu abinda yakeyi. Tashi nayi zan fita naji an maida ni gadon, se lokacin na lura da Ummaah da Mami da kuma bokan dan a gurina he’s never near Allah wannan mutumin tsubbu yake. Inaji ina gani haka ya kwara min wannan ya zuban wannan, idan nayi ihu se yace aljannun ne hakan yasa kawai nayi shiru. Haka ya gama ya bada wasu layu da itatuwa da saiwoyi da wasu kulle kulle da zaa binne. ita kuma Ummaah se godiya take mishi, kuka ne ya kwace min, kukan takaici, kukan bakin ciki, kukan tausayin kaina, kukan rashin madaga, se naji duk na sare naji kamar ni rahama ta sauka daga kaina. Nafi awa ina kuka tun Ummaah na cewa aljanun ne har naga hankalinta ya fara kaiwa kaina, ganin haka yasa Mami tace nayi wanka, kaina na girgiza ina cigaba da razgar kuka abuna.

Se laasar bayan nayi sallah sannan muka tafi, fuskata tayi jawur kada ma idanuna suji labari. Koda muka tashi tafiya kasa driving nayi saboda yadda jikina ke shaking. Dole haka mami ta bada driver ya kaimu gida sannan ya juya. Dakina na shige na kulle tareda saka key na datse, banma hau gado ba anan jikin kofar na silale a baki na dinga kuka kamar raina zai fita, ban taba tunanin haka ake bakin ciki ba, nayi ta kuka har bansan iyakar lokacin dana dauka a wannan gurin kuma cikin wannan halin ba. Time to time nakan ji ana min knocking amma ko a jikina banma ni da niyyar tashi.

Ban kara fitowa ba se washegari, dake na saba dama ba fitowa nake sosae ba tunda zaman gidan ya zama tamkar a living hell hakan yasa na koma zamana kawai sede aiki ya fitar dani. Ummaah tun daren take kirana a waya amma naki dagawa saboda bansan abinda zance mata ba. Seda nayi wanka sannan na zura wata purple abaya da stones a jiki se walwali take. Comb na dakko na taje kaina na tufike da karamin ribbon sannan na shafa balm a lips dina da yayi ja, kallon fuskata nayi har lokacin bata ware sosae ba ta kumbura saboda rashin bacci da kuka. Ummaah na zaune a parlor hankalinta dukka ta tattara shi akan kofar tawa, ina fitowa idanuna ya sauka a kanta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaisheta nayi ta amsa jikinta a sanyaye ni kuma na wuce kitchen. Ina cikin dama kunu naji shigowar t, kujera ta ja ta zauna sannan tace min

“Asmau kinada hankali kuwa? Kinsan yadda kika tsoratar dani ki shiga daki ki kulle ko a jikinki? Kinsan banyi bacci ba?”

Bance mata komai ba na cigaba da abinda nake, jin nayi shiru yasa ta dawo gabana tareda daka min duka tace

“Bakya ji ne ?”

Na kyafta ido se hawaye, raina a mugun bace nace

“Ummaah me zance miki? Ya kike so nayi? Nidai nasan this wasn’t my mother, uwata ba haka take ba wani ya canja min ke.”

Sororo tayi tana kallona kafin tace

“Saboda na kaiki gurin malami shiyasa zaki fadi haka?”

Kaina na girgiza nace

“Ummaah saboda banyi aure ba shi ne kike kokarin saida imaninki, ke kanki Kinsan wannan mutumin is never near malami, kawai dai kin bi son ranki ne….”

Wani bugu ta kaiwa bakina hakan yasa nayi saurin rufe bakin, fita tayi ni kuma na zauna na dasa sabon kuka.

AyshatuuuuA fragile heart was broken before, i don’t  think it could endure another pain, a piece of voice from deep inside that calling you to make you relaxed!

Wannan kwanaki biyun dana kara sun zame min kwanakin da bazan taba mantawa a rayuwata ba, tunda nake addua i was never specific sede nace Allah ya zaba min mafi alkhairi, a ganina hakan shi ne daidai amma tunda naga an fara haka yasa na dukufa adduar Allah yasa nayi aure cikin kankanin lokaci. Ana gobe zan tafi da daddare na dawo daga gidan yaya Halifa saboda gidan babu dadi, daga ni se Asiya se ummaah and I couldn’t, i was suffocating hakan yasa na tafi tun sassafe, Inna ade da Abba sunje umra , jikokin gidan kowa yana gidansu hakan yasa naji zaman ya isheni. Mun jima nida yaya Halifa ina kora mishi bayanin halin da nake ciki. To me zaiyi shi dinma Ummaah ta haifeshi, highest thing shi ne ban hakuri kuma shi din ya bani, ya nuna min Allah yana sane dani kuma komai kaga ya faru to da saninshi. Those words kept me going.

+

Kwana na biyu da dawowa daga kano, na koma aiki na saboda damuwar ma batada amfani. Da yamma ina kwance a daki ba call nake ba so bayan na gama abinda zanyi na fita kasuwa nayo cefane na dawo . Ranar i was craving for dambun shinkafa. Haka na zauna na daura a cikin steamer na koma na fara soya kazar da zanyi pepper chicken da ita. Ina nan zaune na saka wani chilled chapman a gabana ina sha se naji message ping, mikewa nayi da sauri na isa ga wayar tareda tapping message din

A 40year old null para with a diagnosis of ectopic pregnancy and ? Typhoid perforation. booked for ex-lap. Prepare for emergency ex-lap ASAP.

Na karanta yafi sau shida ina kara duba number data turon da mamaki, wannan ai aikin general surgeons ne kuma ma idan ance saboda ectopic dinne I’m not on call. Mikewa nayi na kashe steamer sannan na juye abincin cikin warmer se kadan nasa a plate na saka salad da naman na fara ci. Banma kara komawa takan message din ba saboda a tunanina mistake akai. Seda na gama na gyara dakin sannan naga call din Dr halima yana shigowa, hannuna na goge jikin towel na dauka, ko gaisuwata bata amsa ba tace

“Asmau bakiga message ya shigo wayarki ba?”

“Na gani, I thought mistake ne shiyasa na share”

Cikeda damuwa tace

“This is unlike you, kije yanzun patient din tana Female surgical ward kiyi reviewing dinta”

Kaina Na gyada nace

“Amma bani bace da call bafa”

“Just follow orders kinji, nima order aka bani”

Katse call din mukai inata bubbuga kafa da zumbura baki hakanan dai na samu na dakko kayana na kullum yau pink nasa wando da riga na soft cotton yadi na saba back pack dita na fita. A ward na sameta mugun restless, ciwo yana damunta hakan yasa nayi order a mata allura kafin na kira a kawo ta: daga nan OT na wuce, na samu sun shirya kawai jurana ake hakan yasa na kira dan a kawo patient din. Ana kawo ta na dubi scrub nurse din nace

“Sister, waye zamuyi surgery din dashi?”

Dariya tayi tace

“Baki sani ba dama”

Kafin na bata amsa naji wannan deep voice din tashi, dukda sau daya na taba ji amma hakan baisa na manta da ita ba.

“Evening everyone”

Juyawa nayi da sauri tareda bashi hanya nace

“Welcome sir”

Kanshi ya gyada min sannan ya bawa mazan gurin hannu sukai musabaha ya shiga ciki yayi changing sannan muka fara. Tunda na mika masa scapel yake min tambaya akan conditions din matar, God so kind nima book worm ce so yana tambaya ina amsa shi inda gyara yana min yana kara clarifying min abubuwa. Haka mukai almost 4hours muna abu daya, se bayan maghrub muka gama aka maida ita ward mukai sallah sannan yace  a kawo masa folder yayi documenting. Ni na kai masa yace

“Sit please!”

Zama nayi kamar yadda yace, idanunshi ya maida kan folder yana going through hx matar.

“What’s your name?”

Dagowa nayi na kalleshi amma bani yake kallo ba amma nasan dani yake tunda ni dashi ne kadai cikin office din

“Asmau Shahada”

Kanshi ya gyada yace

“A ina kikai training dinki?”

Shortly nace dashi

“BUK, sir”

“Good!”

Daga haka baice komai ba se can ya mika min folder yace nayi rubutun. Zama nayi yana kallo ina rubutawa yana kara guiding dina har na dan saki jikina. Muna gamawa yace min

“You’ve done a good job. We meet some other time”

Kaina Na gyada ya fita ni kuma na koma na zauna ina maida numfashi. Tun daga lokacin shi kenan indai zaiyi aiki kowa yasan I’m his partner tun abin yana damuna har na sake na saba.

Wata Wednesday mun gama ward round, banyi breakfast ba ranar saboda kadan ya rage ban makara ba hakan yasa na tafi cafeteria dan cin abinci. Tsirarin mutane na tarar suna cin abinci, wasu sun gama, seda nayi order sannan na dawo na zaune ina jiran a kawo min. Nayi nisa sosae a cikin wayata ina chatting naji alamar an zauna gefe na. Da sauri na dago wani mutumi ne in his mid thirties ya tsareni da idonshi, the gaze was so intense hakan yasa nace

“How may i help you”

Wani murmushi ya saki yace

“Finally, na samu ganin workaholic Dr Shahada. How far?”

Bansan amsar da zan bashi ba hakan yasa nayi shiru tareda maida hankalina kan wayata, i knew him somewhere amma na rasa a ina na sanshi. Shima bai kara cemin komai ba seda aka kawo min abincin se na maida shi akan ayi packaging ba anan zanci ba. Se naji yayi dariya yace

“Doctor, ya zaki ce ayi packaging?”

Dagowa nayi na kalleshi nace

“Ka takura min”

Murmushi yayi yace

“Tun yanzun, ai abinda zuciya ke so no way ta bar abinnan”

Mikewa nayi naje counter cashier na biya sannan na fice kawai, ashe yana bayana seda nayi nisa sannan yace

“Doctor, you shunning me?”

Tsayawa nayi nace

“Idan abu kake so ina ganin wannan is not right kazo ta haka, dan Allah idan wani abunne follow the right route”

Daga haka na juya zan tafi, to my utmost amazement kawai se ya ruko hannuna cikin sauri na juyo, mamaki kamar ya kashe ni, kafin nayi yunkurin cire hannun se ji nayi ance

“Asmau!”

A tsorace na dago idanuna only to see MD a tsaye ya tsareni da idanunshi da suka kada sukai ja, sunkiyar da kaina nayi tareda kwace hannuna, tuntuni idanuna sun fara kokarin kawo ruwa. Yana isowa gurin yace

“Meet me in my office yanxunnan!”

1

AyshatuuuuTamkar an daddatse min joint dina haka naji, ilahirin jikina yayi sanyi na rasa abinda yake min dadi. Lumshe idona nayi na dubi useless, unreasonable Ashole dake tsaye yana wani irin smirking, idanuna na lumshe raina a mugun bace kawai na juya na tafi. Once in a lifetime kowa yana experiencing such embarrassment, tunda nake ban taba jin kunya irin wadda naji ba. Tamkar anmin duka haka na tafi ina tunanin ta inda zan fara hada idanu dashi. Taya mutum zaiji ace mutumin dake ganin mutumcin ka ace yaga wani ya rike hannunka nasan Allah kadai zao fitar dani.1

Banyi gigin zuwa office dinshi ba saboda bansan wanne ido zan kalleshi ba kawai se na juya na tafi mota ta nayi mata key se gida, dukda hankalina yana kanshi Amma zuciyata gargadi na take akan kada fa na zake, tayi kuwa nasara haka na basar na tafi daki naci abinci sannan na kwanta, a raina ina fadin aikin ma na yau na fasa bazanyi ba.

Shikam acan a mugun fusace ya isa office dinshi, yana shiga yayi slamming kofar da karfi tareda fadawa kan cushion ya zauna, cushions ne guda hudu tsakiya center table ne me kyau covered with glass baki daya. Zama yayi ya daura kafafunshi akan table din. Wani zafi ne ke karyo masa se gumi yake ka rantse da Allah yana karkashin kwalleliyar rana ne, nan kuwa cikin niimar split yake har biyu a cikin office din. Coat dinshi ya cire ya aje gefe sannan ya sassauta necktie dinshi tareda kurawa kofar idanu yana expecting shigowar Asmau amma har awa daya ta shude babu Asmau babu alamar ta. Mikewa yayi ya fara pacing a cikin office din, me yarinyar nan take nufi dashi yace tazo sannan taki zuwa ta sameshi,  kanshi ya girgiza daidai knocking a kofar hakan yasa a sukwane yace

“Yes, come in please”

Kofar aka turo idanunshi a kafe yana jiran ganin wannan farar fuskar tata amma maimakon ganinta se yaga ashe Director Admins and finance ne, se lokacin ya tuna sunada magana dashi. Daidaita kanshi yayi cikin sauri ya koma seat dinshi tareda masa izinin zama, seda suka gaisa kafin ya bude file ya fara briefing dinshi amma rabin hankalin Dr Kwaccido baya gurin tunnainshi kodai mutumin da ya gani tareda Asmau ya gudu da ita ne? Kodai dama saurayinta ne cikin sauri ya matsar da wannan thought din a ranshi, it took him almost 2 months yana bincike a ciki da wajen asibiti akan Asmau, babu inda yaji tana da wani tsayayen magana a kanta….

“Sir, you’re not concentrating, ko mu hadu gobe?”

Kanshi ya dafe cikeda damuwa yace

“I’ll be glad, thank you”

Haka ya tattare kayan shi ya tafi shi kuma ya cigaba da jiran tsamanni amma har yaje azahar ya dawo bata zo ba, sau da dama se ya fara dialing numbers dinta da yayi storing dinsu a kwakwalwar kanshi tun ranar da Dr halima ta bashi ita amma ya kasa, baisan abinda zaice mata ba, zuciyatshi tasha gargadin shi akan wannan kallon ruwan da yake kada wankin hula ya kaishi dare. Ko kuma garin bari ya huce har ya zama rabon wasu, kanshi ya girgiza dan baya tunanin zai iya bari hakan ta faru.

Wajen laasar ya kammalla komai na ayyukan ranar, hannunshi rikeda briefcase da suit dinsa yana waya ya fito, messenger dinshi ya karba tareda kai mishi mota, godiya yayi masa sannan ya wuce cikin motar yana baza idon ganin ta inda zata bullo amma bai ganta ba haka ya tafi dik babu dadi, haka nan yaje gida. Kamar yadda ya saba ganin gidan it was so empty ya zaiyi tunda haka kaddra ta zabar masa kuma hakanan zai karbeta babu yadda zai iya. Straight bedroom dinshi ya wuce yayi wanka yayi alwala sannan ya zura jallabiya brown me gajeran hannu ya dawo parlor ya zauna. Babu jimawa yaji ana knocking wanda yasan ba kowa bae illa sabiu cook dinsa, sunyi waya yace masa ya fita dan yun wata gaisuwa. Shigowa yayi ya risina ya gaisheshi sannan ya wuce kitchen dan hada masa abinci, idanunshi ya lumshe yana bin parlon da kallo, ko ina a share yake, tiles din se kyallin mop suke amma kana kallon yadda komai Na parlon yake kasan babu mace a gidan. It’s obvious kana shiga zaka fahimci hakan, kanshi ya shafa yana jin lokaci yayi da zaiyi uncaging zuciyarshi hakanan, ya kamata ya fito daga dreadful past life dinshi ya cigaba da rayuwa, wannan zuciyar tana bukatar aboki, ya kara kallon katon parlon da hasaso gadon shi, yana bukatar living partner, he sure needs a soulmate.

STORY CONTINUES BELOW

Washegari ranar alhamis, kamar kowanne sati ita ce ranar da muke surgery ni da Dr Kwaccido. So ranar tunda nayi asuba na ko wanka banyi ba Na tafi Paediatric surgical ward, nan patient din yake. Yaron shekarashi biyar yana fama da umbilical hernia. Though condition din is a minor one amma a haka yayi mana booking. Ina zuwa anesthetist din tana zuwa, tare mukai reviewing dinshi kowa yayi documenting abinda ya samu sannan muka rabu. Gaba daya ji nake inama inada excuse din da zan bayar dan bana sam haduwa dashi kwata kwata amma ina na babu wannan, se goma na safe sannan na fito, fuskata tayi yar fayau tsabar fargaba da damuwar da nake ciki idanuna duk sun fada sunken in. Yanayi na ma kawai zaka kalla kasan akwai tambaya. Ina zuwa office na samu kan sofar dake gefe na dan kwanta ai bacci yace idan kaci bashi na se ka biya and it happen.

Bansan ashe har time ya tafi ba, se can naji ana knocking kofar office dina, ko kafin na tattara guntun karfin da ya rage na tashi, tuni kofar was flung open. Wannan kyakyawar fuskar tashi me cikeda haiba da kwarjini tasa nayi saurin tashi ina lalubar veil dina, wannan idanuna nashi that always shine me kamar an zuba musu mai cikinsu ya tsareni dasu, a take naji kamar anyimin duka, yunkurun da nake na daina se kasa da nayi da kaina ina jin an takura ni da yawa. Yana tsaye tareda harde hannyansa a kirjinshi shi bai zauna ba bai kuma nema gurin zaman ba. Kafin na kara yunkurawa naji yace

“Sleeping on duty?”

Da sauri na muskuta tareda girgiza kaina nace

“Sir, banida lafiya ne”

A take naga yanayin fuskar shi ya canja, shigowar shi tamkar wani zaki haka ya shigo ranshi a hade amma yanzun se naga damuwa ta dauke bacin ran dake ciki. Daidaita tsayiwarshi yayi cikin wata tattausar murya wadda babu wani da namiji daya taba amfani da ita wajen yimin magana yace

“Sannu, kinsha magani?”

Kaina Na girgiza nace

“I was about to, se bacci ya daukeni.”

Kanshi ya gyada se kuma ya fita, hakan yasa na sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda lumshe idona, ni nasan banda lafiya amma a matsayina ta likita bana tunanin nasan me yake damuna, ban kuma san wanne irin taimako zan bawa kaina ba, nasan kilan tarin damuwar da nasa a zuciyata ce take neman kayar dani…..Soft knock akai jikin kofar, bakina a hankali na bude tareda bada izinin shigowa, shi dinne ya dawo sede wannan karan ya samu rakiyar head of medical department da kuma chief pharmacist. Inata kokarin mikewa ya hanani tareda bawa Dr Mansur damar ya dubani, BP na ya fara dubawa, kawai gani nayi ya cire glasses dinshi yace1

“Her BP is reading 70/40mmHg sir”

Yana fadar haka se naji tamkar an saukar da min symptoms, baice komai ba illa bina da yake da idanunshi me tuhumata akan Me ya faru? Nidai kasa kawai nayi da kaina ina jin ana min prescription sannan aka kira pharmacy suka kawo. Drip aka fara daura min yana fara shiga wani wahallalen bacci yayi gaba dani. Se can bayan wasu awoyi sannan na farka , ina office dina amma ba kamar dazun ba, ina bude idona da kyaftun na fara cin karo tana sallar laasar. Cikin sauri na yunkura inajin karfi a jikina ba Kamar dazun da nake jin jiri ba.

Toilet na shiga nayi alwala sannan nazo na zauna dan har lokacin jikina gashi nan dai, a zaunen nayi both zuhr da asr sannan na kwantar da kaina akan cushion ina lumshe idona.

“Ya jikin Twin?”

Bude idanuna nayi tareda yin kalar tausayi na dubeta har lokacin uniform ne jikinta alamu sun nuna kilan ko ward ba taje ba, ga Afeeyya ‘yar 5 months ta shimfidar da ita a yar corner se baccinta take peacefully.

“Twin Alhmdllh. Yaushe kika zo? Waye ya fada miki?”

Wani kallo tayimin wanda ta saba yimin idan gulma ta motsa, hakan yasa na cuna bakina ina dauke kai. Dariya tayi wadda tasa dole nima nayi sannan ta matso tace min

“Boss ne, da kanshi yazo har ward ya tafi dani, he left here not long ago.”

Kaina na gyada kawai ba tareda nace komai ba, dan bansan me zance din ba. Sake matsowa tayi kamar zata shige jikina hakan yasa na ture ta baya da dan guntun karfin nawa daya rage nace

“Ke munafuka ce”

Shrugging shoulders dinta tayi tace

“Oho! Baby bude baki zakiyi kimin bayani, me yake faruwa.  Kinga yadda ya rikice? Ni daya shigo ward dinmu I thought something terrible happened ashe Twin ce babu lafiya”

Hararata nayi nace

“Kede Allah ya sawwake miki, he’s none but my boss and partner aiki na”

Tsareni tayi da idanu irin she needs more, tsaki nayi nace

“Dan Allah ki bani abinci I’m starving”

Hakuri ta bani sannan ta hada min wani tea me kauri, yayi min dadi kodan ina cikin yunwa ne oho, seda na shanye tas sannan tace an tafi a kawo abinci. Bata kara min zancen ba tunda tasan da akwai wani abu da zan fada mata, tsakani na da ita babu boye boye so we still maintain the status. Tunda nayi shiru na fada tunani, anya yadda zuciyata ta adana Dr Kwaccido matsayin shugabana da kuma partner aiki? Ina tantamar hakan, duk wanda nayi aiki dashi zai nuna yaji dadi kuma zaiyi kokarin maintaining dina tun ina house job amma shi nashi salan caring din ya banbanta dana kowa. To amma someone like him…. Sallamar shi yasa nayi saurin bude idanuna, a hankali na amsa wanda iya bakina ne kawai ya motsa, muna hada ido ya sakar min wani murmushi. I swear seda tsikar jikina ta tashi, those eyes of his will definitely not allow me to live in peace sede idan kullum zan kasance ina kallonsu ne.

Gaisawa sukai da kyaftun sannan ya mika mata ledar hannunshi yace abinci nane, gefena ya dawo ya tsugunna yace

“Are you ok?”

Kaina na gyada nace

“Much better. Thank……”

Shush yayi min sannan yayimin murmushi yace

“Kici abinci zanje office”

Se na samu kaina da yi masa murmushi nace

“Allah ya bada saa”

Kanshi ya gyada ya dubi kyaftun dake rike da Afeeyya data riga ta tashi ya bata sallahun lallai naci abinci. Aikuwa yana fita ta fara tsokanata wai wallahi so na yake nidai ban kulata ba dan bazan saka abin a raina ba balle ayi back stabbing dina!

2

Your comments keep me going……..

AyshatuuuuIna kammalla cin abincin naji wani karfi yazo min, duk wannan kasalar babu ita, mikewa nayi na tattara gurin sannan nace da Kyaftun mu tafi gida dan ina son nayi wanka na canja kayan jikina. Babu musu ta tattara kayanta muka fita, bani da wani karfin da zan iya driving hakan yasa kyaftun karbar key din ita kuma Afeeyya na karbe ta, mun saba da ita sosae bata min kiwa dan wani sa’in se tayi ta kallona ni da kyaftun tana tantamar gurin wa zataje tunda kowa yasan nida mahaifiyar ta kama  muke sosae, banbanci na da kyaftun nafi ta haske ita kuma ta fini tsayi sannan ita ba a rame take ba, wadda tashin hankali da damuwa yasa na koma hakan.+

Muna shiga na aje Afeeyya na shiga wanka, simple gown nasa ta wani pure cotton yard maroon, free gown ce se stones da aka mata ado dashi. Scarf milk na dakko Na daura sannan na murje jikina da turaren kullum La’eeqa da soft. Lumshe idanuna nayi na dawo na zauna inajin wani daddan yanayi a jikina. Kallon kyaftun nayi da take kokarin hada pap din Afeeyya,

“Ki kirashi kice kin dawo gida, let him not waste his time checking on you a office”

Dan bata fuska nayi tareda fadi

“Is there need for that?”

Kanta ta girgiza tana hararata tace

“Kina da matsala kinsan da hakan? How….?”

Se tayi shiru tareda daukar Afeeyya ta daura ta cinyarta ta fara feeding dinta, wayata dake gefena naji ta fara ringing hakan yasa na kai hannuna na dauka, Adda Sa’ada ce cikin sauri nayi picking dan ta rigada tasan banida lafiya, i texted her though ina tunanin se lokacin ta gani. Ina picking tace

“Fara what happened?”

Dan murmushi nayi jin muryarta duk da damuwa nace

“Ba wani abu bane kawai BP na yayi low”

Ai fa kamar famfo ta fara zuba, tana tamin fada akan tasan na takurawa kaina ne shiyasa hakan ta faru, seda ta gama fadan sannan ta dawo nasiha tana fadin

“Komai da kike gani is a matter of time, da ace tsangwama da takura kai yana sawa kayi abu, da tuni kinyi aure amma shi Allah is wonderful, he’s a perfect timer. Lokaci ne da zarar yazo zakiji it worth the wait!”

What will life be without Adda Sa’ada? Hell na ayyana a raina, bazan iya fadar abubuwan da matar tayimin a rayuwa ba amma she sticks around bata taba nuna min laifina bane da banyi aure ba, Anty Bintu, Yaya Halifa da Adda Meeyna. Banda kamar su. Ina aje wayar kyaftun ta mike tana fadin

“Kada ki zama kina manta alkhairi kuma kada ki bari a golden opportunity like this ya wuce ki. Zan tafi gida, se dare zamu dawo da Daddyn Afeeyya.”

Mikewa nayi a hankali dan bawai malaise din dake damuna ya tafi duka bane, yanzun ma jina nake kamar zan fadi dan dai ina daurewa ne. Hannunta na riko nace

“Ki fahimci abinda nake nufi, i can’t just throw myself on him kamar yadda nayi akan mukhtar (RIP) da kuma Suleiman. I was back stabbed kuma laifin waye? Nawa ne saboda ina ganin dukkan wanda yadan nuna kulawa akaina sona yake. Kina son na kara haka, repeating same mistake is nothing but foolishness”

Zaunar dani tayi dan taga alamar zan iya faduwa ta rike hannuna tace

“Ki fahimci abinda nake nufi nima, ba ina nufin you start chasing him, stalking him and stuffs. Kinsan dai ya miki abin kirki to ko thank you ne he deserves it.”

Kaina na gyada in agreement na dauki wayata and I sent him

Thank you, jiki yayi sauki. Na bar office ina gida

A gurina they were only a plain words amma a gurinshi yayi ta nanatawa saboda dukkan abinda zai fito daga gurina yana daukar abin me muhimmanci. Baiyi min reply ba har kyaftun suka kawo min abinci naci suka tafi na kulle dakin na kwanta tunanin rayuwata yayi min rubdugu, addua a bakina kan Allah yasa Ummaah ta fahimci rayuwa, ta fahimci cewar lokacin zai zo. Da wannan bacci yayi gaba dani se can cikin baccin naji vib din wayata, bansan yaushe rabon da naji an kirani past 10 so da mamaki na bude idona tareda mika hannu na cira wayar, take idanuna suka bude ganin number da take kira, Dr Kwaccido na ayyana a raina at this time, kifar da wayar nayi inajin yadda ilahirin jikina ya mutu, ina ayyana me yasa zai kirani, wata zuciyar tace just to check on you, kaina Na girgiza na ba tareda na yarda da uzurin da zuciyata ta kawo ba. Amma se na samu kaina da kasa nutsuwa, na janyo wayar na kalla 1 missed call, na danyi tsaki ina mitar har yaushe zaayiwa mutum call daya as if baa damu ba. Haka na gama yan mitocina na bude wayata ina kallon pictures dinsu Amalin Adda Habiba sunyi birthday itada Aarif last week. 

STORY CONTINUES BELOW

Washegari bayan nayi sallar asuba dake friday ce hakan yasa ban bar kan praying mat din ba har seda na karanta kahfi savoda nasan idan na bar gurin ba lallae nayi ba, ill be much occupied. Ina kammlawa na mike anan wayata ta katse min hanzari, ganin number seda zuciyata tayi fluttering, it kept jumping har hakan ya bani tsoro, but ya zanyi dole nayi picking call din saboda banda uzuri. Dauka nayi murya can kasa nace

“Good morning sir”

Manly muryar nan tashi me saka naji waves electrons cikin jikina ya amsa da fadin

“Morning Asmau”

I can swear akan ban taba jin wani ya fada Asmau so correctly kamar shi ba, kowanne harafi seda aka bashi hakkinshi, har seda naji ina bukatar nayi ta jin shi yana kiran sunan.

“Ya jikin naki?”

Dan murmushi nayi nace

“Yayi sauki, Alhmdllh”

“Alhamdulillah, zuwa karfe biyu zan wuce kano, ki zama ready zamu tafi tare”

Baki bude na tsaya ina tunanin abinda yace min, seda ya kara maimaitawa kafin nace

“Sir zan fara call gobe, so bazan samu damar zuwa ba and thank you”

“Na rigada nayi arranging yadda zaayi, ya kamata ki huta saboda ciwonki stress ne”

Se na kasa musa mishi haka mukai sallama bayan yace zai aiko min breakfast sannan nayi bacci kafin time din. Nidai na rasa tantance me hakan ke nufi na kuma kasa fahimtar inda zuciyata tasa gaba da kuma wanne tarba tayiwa alamarin. 8am na bugawa aka kawo min abincin, cikin basket aka jero shi, messenger daya kawo na bashi 500 yana ta godiya ya tafi. Chips ne cikin bowl se farfesun kayan ciki shima a bowl, tea me kauri cikin wani karamin flask. Gefe leda ce a aje na bude tareda ciro abinda ke ciki, rose flower ce hade da greeting card, mamaki sosae ya kamani na bude greeting card din naga na get well soon ne, a kasa yayi rubutu cikin rubutun da ban taba kawowa ya iya ba kasancewar kowa yasan handwritings din Doctors bashida kyau amma yadda yayi rubutun kamar calligraphy lettering style yayi amfani dashi.1

Come on, get back on your feet and continue that gorgeous smile of yours. Quick Shifaaa Cara Mia!

Shine abinda ya rubuta, zuciyata nasan dama is froze, dan tunda Salis ya betraying feelings dina shikenna na daskarar da ita, ga mamakina wannan kalaman nashi take suka raga raga da wannan kankarar, wani bugu da zuciyata ta shiga yi har seda nayi tsoron kada a samu over extension. Jikina yayi sanyi na kalla rose 🌹 din na shafa na shinshina a karshe na rungume ta a kirjina ina adduar Allah yasa daga shi ne. Greeting card na dauka na kara nanata rubutun ina bin kowacce kalma daki daki, komai na fahimta banda wannan cara mia din kuma babu me amsa min. Abinci kadan naci sega kyaftun tayi ta ihu tana murna tana fadin

“Yarinya kin saka yan maza a gaba fa, kinyi kamun full package”

Se na samu kaina da fara yarda da zancenta, kodai so na yake, ko dai……haka nayi ta tunanin kafin can bacci ya daukeni se wajen 12pm na tashi nayi wanka na hada kayan dazan bukata sannnan na yi sallah na karasa abincin da na rage na wanke na kife kafin na fara neman kaya. Ni dama ba maabociyar kwalliyya bace dan powder ma se kayi da gaske nake siya hakan yasa na zizara khol tareda shafa charpet kan tattausan lebena da ya fara bushewa har fata na neman dagowa. Dana kalla madubi se naga nayi kyau daidai yadda ya kamata. Wani lace na dakko me laushin gaske irin vapers dinnan ne. Background din Coffee ne se designs din suka tashi milk da zaren gold a jiki. Skirt da riga ne nasa na daura dankwali tareda dakko matching veil da takalmi, har na manta last dana nutsu nayi shigar arxiki. 1:50 daidai wayar shi ta shigo akan yana jirana, kara gyara zaman veil dina nayi sannan na dauki abinda zan dauka na fita. Yana tsaye gefen motar yayi shigar da ban taba gani ba, yana cikin farar shadda ta zarce ayi masa coffee aiki, kanshi sanye da zannan bukar yayi kyau very charming. Dake quarters din namu babu mutane yawancin an tattafi weekend masu aiki nayi yasa yake tsaye shi daya. Back seat nasa kayan sannan na shiga gefenshi danshi tunda na kusa karasowa ya koma ciki ya tashi motar. Tunda Na gaisheshi ya amsa ban kara ko tari ba haka shima se gudunshi da yakeyi, seda mukaje wudil ne ya tsaya karbar document ni kuma na samu saken kiran kyaftun na mata sallama. Yana dawowa ya kalleni tareda fadin

“You look disturbed, akwai abinda zan taimaka miki dashi?”

Cikin sauri na karkada kai alamar aa tareda lumshe idanuna ina shakar kamshin turarena nashi da kuma car freshner da ya saka, ga sanyin AC. Yanayin was so romantic. A hankali naji waka ta fara fita cikin speakers din, hannunsa yasa yayi increasing volume din tareda fadin

“Shirin yayi yawa, enjoy please”

🎶I’ve been looking for you everywhere, I’ve been asking god when I’ll found you dear? I know some times last days where you least expect. But I’ll be patient i go wait, wait for you my dear. wherever you are, you have my heart, my darling take me yes I’m. I’ll be loving you from now till i found you my love. I hope say you like me d way i be, i go dey wait for you day and night dear future wife. 🎵

🎤When I need you will you be there my dear? I’ll make silly mistakes please forgive me dear, we have a long a way to waka, hold my hands my dear. Wherever you are you have my heart my darling, I’ll wait for you day and night dear future wife.🎷

1

Tamkar kada wakar ta kare haka naji, idanuna na bude tareda kallon sadhin shi, murmushi ne kwance a fuskarshi wanda tsabar yadda ya kayatar dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi:

“Nayi kyau ne?”

Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani.

AyshatuuuuHar kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace

“Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan”

Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace

“Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?”

Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda fadin

“Monday very early zanzo mu tafi”

Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni. Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada ‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.+

Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace

“Ummaah barka da gida”

Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace

“Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS”

Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace

“Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta”

Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka.

“Ya A’isha da halima da me gidan?”

Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana ringing and it was him calling, haka nan na karasa jiki a sanyaye na dauki wayar tareda karawa a kunnena nace

“Barka da dare Sir”

“Barka dai Asmau. Ya saukin jikin?”

Se dana kalla kaina kafin na amsa masa da sauki se kuma mukai shiru dan nidai bansan me zance msa ba kuma baya son godiya. Hakan yasa nayi shiru. Se can yace

“Kiyi bacci and ki tabbatar kinci abinci”

Kamar wata doluwa haka na shiga gyada kaina in agreement amma sede bama gani na yake ba balle, seda yace

“Huh! Asmau?”

Sannan nace

“Inshaaa Allah Sir”

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka mukai hanging, wani irin raruma nayiwa wayar taredq rungume ta a kirjina inajin wani farin ciki marar misaltuwa. Murmushi kuwan from ear to ear kamar bakina zai yage. Can kuma na kashe wutar tareda yin addua na kara lula duniyar tunani a haka daddan bacci ya daukeni, it was peaceful dan ko mafarkan da nayi where of love. Dan haka da asuba dana tashi komai lafiya lau jikina ba wannan rashin kuzarin se ma wani karfi da nake ji. Hakan ya bani mamaki amma a kasan zuciyata nasan menene nasan dalili. Ina idar da sallah na janyo babban quran dina na fara tilawa a kalla nayi izu daya kafin nayi azkhar lokacin tuni gari ya waye hakan yasa na gyara dakina na shiga wanka. Ina fitowa na zura wata morning gown ta wani silk purple yadi. Kaina na zura hula sannan na tafi kitchen.

Na jima tsaye a jikin working surface ina karewa kitchen din kallo wanda a zahiri kenan amma a badini ina tuannin bidirin da aka sha a kitchen din, tun daga Yaya mukhtar down to Yaya Suleiman. Kowannensu it started at this very place. Ajiyar zuciya me nauyi na sauke ina kara kallon guraren tareda saka hannuna ina tattabawa wasu nayi murmushi a haka na kashe time din da bansan iya adadinshi ba. Se can dana fara jin motsin yan gidan sun tashi sannan na dukufa fara aiki. Na kusa gamawa Mama da Asiya suka zo muka karasa na wuce na gaida Inna sannan Abba da Ummaah. Muna kammalla breakfast na koma daki na dudduba wasu soft copy pages da aka turon akan Breast cancer da Cervical cancer. Ban wani dauki time ba na gama na janyo system dita na fara aikin da na saba wato kallon korean movies, wani Love In The Moonlight.

Gaba daya na sakankance ina kallona naji an turo kofar dakin, normally mun saba indai zaka shiga dakin koma waye seka yi knocking da sallama kafin ka shiga. Hakan yasa na dago da sauri tareda pausing film din, mamaki sosae ya kamani ganin  Nadia, its been long da naga kafafunta a cikin gidanmu kuma dakina. Mikewa nayi ina sakin murmushi nace

“Nads manyan mata, sannu da zuwa”

“Yawwa!”

Kawai tace min se ban wani damu ba tazo ta zauna nace

“Bari a kawo ruwa, yau akwai hirar yaushe gamo kenan”

Na fada ina kokarin tashi daga gefenta, hannunta tasa ta rike nawa, hakan yasa nayi saurin kallonta kafin nayi magana tayi beating dina to it tace

“Bashi ya kawo ni ba. Kina kallon yanayi na kinsan ba ruwa nazo sha ba. Gargadi nazo nayi miki, mijina Suleiman nawa ne ni daya kinganshi yafi karfin wadda tayi kwantai ta gama aiki cikin kartin maza irinki. Saboda kin kasa auruwa you decided kizo kimin snatching miji? Kul dinki!”2

I was dazed, confused and amazed! Tunda ta fara magana nake kallonta da tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa ya fit baro baro akan fuskata. Tana gama fada ta hankadar da hannuna ta mike da niyyar fita, nasa hannuna na riketa ina kallon idanunta wanda na rasa meye a cikinsu amma nawa firgici ne a cikinsu

“Ta yaya zaki fita baki fahimtar dani abunda maganar ki take nufi ba, Nadia ni ce fa”

Hannunta ta kwace kamar wata damisa, cikin daga murya tace

“Se me dan kece? Ai nasan ke dince shiyasa na sassauta miki, tunda bakiji kunyar kawancenmu kin kai idanunki kan mijina ba bazanji kunyar na miki gargadi ba. Me mijina zaiyi dake tsofe tsofe dake…..”

Ban barta ta karasa ba na wanka mata mari ina wani irin huci, i was boiling in,

“Kada ki kuskura Nadia…..”

Se na dunkule hannuna na kasa karasawa, zuciyata na fada min Nadia ce fa, wannan dinnan, kin manta ta? She doesn’t deserve this. Bana tunanin akwai circumstance da zai zo na manta matsayin rayhana da Nadia a rayuwata, sudai zasu iya mantua amma ni nasan alheri bana mantawa dashi. Ai tana ganin nayi shiru ta fara zage zage wanda ya janyo hankalin Inna da Ummaah dasu Mama, su basu san ta shigo bama dan kowanne na dakinsu. Ummaah tazo tana fadin

STORY CONTINUES BELOW

“Nadia me ya faru? Me ya hadaku?”

Wani mugun kallo tayiwa Ummaah tace

“Ki fada mata ta fita harkar mijina, mijina yafi karfin ta shi ba tsaranta bane, idan ba haka ba……”

Gaba daya har Inna muka tsaya muna kallonta da tsananin mamaki, kuma shirun da mukai mata baisa tayi shiru ba sema kara daga mirya da takeyi a haka Abba ya fito ya samemu a tsatsaye, Nadia tana ta wulakanci ita me miji. Kallonta yayi yace

“Kiyi hakuri ki koma dakinki, ni na miki alkawarin Asmau bazata taba auren mijinki ba, itama nata yana nan tafe da izinin Allah”

Kawai tana bude bakinta se cewa tayi

“Better!”

Ta juya ta fice, tana fita naji wani irin yanayi me wiyar na fada ya lullubeni, kaina kamar zai tsage gida biyu, idanuna da suke neman lumshewa na bude da karfin gaske nace

“Abba me ya faru”

Ashe yaya Suleiman ya samu Ummaah akan yana sona zai aureni tace masa aa kar ya manta abinda ke tsakanina da matar shi, bai jiba ya samu Inna ita kuwa kowa yasan yana daya daga cikin favorite jikokinta hakan yasa tayi naam da maganar. Kallon Inna nayi kamar zan daketa idanuna se hawaye ke zubowa, gaba daya na manta Inna bata jin turanci nace

“For goodness sake, Inna why will you do this? Danme? Kinsa yarinya yar cikinku tazo tayi muku fitsara. Saboda banyi aure ba, kun taba ganin macen da takai age dina bata damu tayi aure ba, in bai zo ba zan fita titi nayi shelar wa yake sona? Waye zai aureni…!”

Wani abu naji ya tokaren makoshi hakan yasa na juya dan tafiya daki amma wani mugun jiri ya kwashe ni se gani a kasa, dukkansu suka yo kaina dan tashina amma na mike seda Abba ya rikeni aka kaini har daki daidai shigowar yaya Suleiman a birkice, Abba yace baya son yaji komai kawai yazo ya dubani. Yana dubani ya daura min drip se na lumshe idona kamar me bacci hakan yasa suka fita dan na samu na dan huta amma maimakon na mutsu se kawai na tashi na hada kaina da gwiwa na dinga kuka, a raina ina ayyana yadda rayuwa ta juya, ni Nadia tazo har guda ta ciwa mutunci akan mijinta? Su Ummaah basu tsira ba. Asiya ce ta shigo ta sameni a hakan ta zauna tana ta lallashina har nayi shiru sannan ta dauki wayata dan nace duk wanda ya kira tace banda lafiya.

Misalin karfe bakwai na dare nayi sallar maghrib, na dan nutsu ba kamar da safen ba shima Abba da Ummaah suka zo sukai ta lallashina tareda nuna min haka rayuwar take, we must expect worst from life, it’s a trial which are never meant to be easy. Wannan ya karfafa min gwiwa har nasha tea sannan nayi wanka amma idanuna kadai zaka kalla kasan kodai ina cikin damuwa ko banda lafiya.

“Yar fara tashi maza maza ki canja kaya kizo parlor kinyi baki”

“Baki?”

Na maimaita ina kallon Ummaah data bude wardrobe dina da alamun kaya take nemo min kaya, mikewa nayi jin bata bani amsa ba nace

“Ummaah su waye?”

Juyowa tayi tana kallona kafin tace

“MD dinku ne”

Idanu na zaro cikeda mamakin abinda ya kawoshi, taba ni Ummaah tayi tace

“Tun dazun sukazo so kiyi sauri kisa wani abin kizo”

Idanuna Na lumshe ina jin wani mintsini da ale min a cikin zuciyata na farin ciki, kallon kayana nayi ba tareda daukar ko daya ba na rufe na nufi inda Abayas dina suke na samo wata simple royal blue abaya wadda egde dinta aka mata ado da wani silk blue material yayi kyau. Mayafin na yafa bayan na wanke fuskata na fito parlor Amma maimakon na ganshi se wata yar karamar yarinya wadda shekarunta bazasu wuce shekara biyar ba, sanye take da jeans se top an saka mata hula kalar top din. Wasa take da throw pillow din kan cushion din da take kai, gefenta wata middle aged mata ce tana zaune da waya a hannunta amma kamar da suke da wannan yarinyar ta baci. Hakan yasa naji hankalina ya kwanta daga tantamar da zuciyata take. A hankali na karasa inda matar take Na tsugunna a gefenta nace

“Barka da zuwa, ina yini?”

Da sauri ta dagani Na zauna gefenta tana ta murmushi kamar bakinta zai yage tace

“Mashaaa Allah, Alhamdulillah! Barka dai Asmau ya jikin naki?”

A kunyace nace

“Alhamdulillah!”

Dan yadda idanunta ke sparkling daga gani na kamar irin abinda kake jira dinnan shekara da shelaru ne yazo.”

“Yayi kyau, Raudha bakiga Anty ba, zo ki gaisheta”

Yarinyar tazo tayi hugging dina ta gaisheni , ina murmushi na zaunar da ita kaina naace

“Raudha”

Kallon Maman ta tayi tace

“Amiey, wannan ce Matar uncle Abbas din?”

Da sauri na kalli yarinyar dake shafa fuskata sannan na kalli uwar dake kallona with love a idanunta tace

“Inshaaa Allah”

Kunya ta kamani sosae, zuciyata wani irin bugawa take na kasa tantance a wanne yanayi nake ciki farin ciki ne ko mamaki. Kafin ta kara magana Ummaah da mama suka zo dauke da abinci akan tray, sannan ta zauna suka gaisa inajin tana fada mata su asalinsu iyayensu yan sokoto ne amma dukkansu a hadejia aka haifesu ta jigawa hakan yasa suke indigene tunda sun samu by birth. Nidai hankalina yana kan Raudha da nake feeding tana ta bani labarin Uncle Abbas. Can sega Abba ya shigo, har kasa Maman Raudha ta tsugunna ta gaisheshi ya kirani parlonshi. Tunda nasa kaina nasan Dr Kwaccido na ciki saboda kamshin turaraenshi daya baibaye ko ina Na parlon. Abba fita yayi so daga ni se shi se Raudha data biyoni tana ta tsalle tsallenta.

Cikeda damuwa yace

“Me yake damunki ne kin kalle ki kuwa? Nasa ki taho gida ki huta amma you are still falling sick. Y kike so nayi ne?”

Da sauri na dago kaina ina kallonshi, ya dage girarshi yace

“I care of course! My heart flutters whenever I see you or i remember you. Can you do me the favor of marrying a bachelor like me?”

9

Rate the page on a scale of ten

3

Ayshatuuuu ❣️Tantama na shiga yi akan abinda naji ya fito daga bakinshi, favor yace nayi mishi na aureshi ko kuma auditory hallucination ne ya sameni lokaci guda. Idanuna na dago na sauke cikin nashi wanda ya tsareni dasu, zaku rantse da Allah kuce amsar tambayar tashi cikin idanuwan shi take.

“Can you do me a favor of marrying a bachelor like me?”

Ya kara maimaitawa, haka kowa yake ji idan akai masa proposing. Yanayi ne sabo da ban taba jin makamancin irinshi ba, to ta ina zanji tunda babu mahalukin daya taba cewa zai aureni? Kowa sede yazo ya gama wasa da zuciyata sannan ya wullar da ita inda yaga dama.

“Asmau, ba se kin amsa ni yanzun ba, sede kin ganni bana da hakurin jira, waiting really sucks kingane?”1

A hankali na gyada kaina kamar wata sokuwa shi kuma ya cigaba da fadin+

“Ni ba yaro bane, kema you don’t look like a teenager, gaba dayanmu adult ne mu. To ya kamata dukkan approach dinmu ya zama very matured. Dan Allah Asmau don’t make me wait!”

Kasa nayi da kaina inajin wani sashe na zuciyata na fadin kice kin yadda, kice kin amince amma bazan iya ba shima ba lokaci daya yaji yana sona zai aureni ba, it took him time kafin ya fahimci me yake bukata. Shirun da mukai yafi na mintina biyar kafin yayi breaking silence din da fadin

“Ashe dubiya nazo fa, ya jikin naki?”

Dan murmushi nayi a raina ina fadin jinya kam ai ta tafi sede wata amma ka rigada ka wanke duk wani dafi da tsatsa dake kanta. A zahiri nace

“Jiki yayi sauki Alhmdllh. Nagode…….”

Mikewa yayi yana hararata yace

“Ki cigaba da godiyar nan dana hana”

Mikewa nima nayi ina murmushi nace

“Idan akai maka abin arxiki, is not bad when you show your gratitude right?”

Bansan ya expression din fuskata yake ba da nayi maganar, abu daya na sani nadan daga girata. To yadda ya tsaya yana kallona da bakinshi da hancinshi ya shagala sosae har seda na rufe fuskata da gefen veil dina kafin ya girgiza kanshi yana wani irin murmushi wanda idan zai kwana yanayi bana tunanin zan gaji da kallonshi, he looked so charming and loving.

“Hakane kam, why not ki adana mana hakan se right time yayi”

Dan murmushi nayi bance komai ba Shima se yace zai tafi yana son sallama da Abba, kallon snacks din da aka kawo mishi dadu lemu nayi amma bai taba komai ba hakan yasa nace

“Ummaah zatayi magana baka ci komai ba”

Kallon gurin yayi sannan ya kalleni yace

“Bake bace kinzo kinata kallona ta yaya zanci abu na kware”

His funny side na ayyana a raina ina dariya, karshe se packaging akai musu, su su Raudha sunci nasu. Seda yaje ya gaida Inna tana ce masa

“Kai yanzun Abbas ka rasa wa kake so se wannan kodaddadiyar, ina laifin ni?”

Yayi dariya yace

“Ai karki damu kece uwargida kuma mowa, ita zata shigo a yar aiki ne.”

Gaba daya mukai dariya inata kallon shi ban taba tunanin he has this side ba, farkon ganina dashi kawai naga serious mutum da bai san bata lokaci ko wasa ba, shidai foremost thing shi ne kayi aikinka kada ya kama ka da laifi. Na yadda da mutane sukace never judge a book by its own cover!

“Ko kada Na tafi ne, naga se kallona ake?”

Hararshi nayi ina mita cikin raina akan dalilin da yasa nake ta kallonshi. Nan yaje gurin Ummaah nan babu wasa se girmamawa da darajawa kafin su Raudha suka tashi bayan Abba da Ummaah sunyi mata kyauta nima na duba dakina na samo chocolate da sweet na bata, suka aje min kayan dubiya inata mitar hakan na rakasu har bakin mota. Ina saitin Maman Raudha tace min

STORY CONTINUES BELOW

“Se munji magana me dadi”

Dan murmushi nayi cikeda kunya ina shafa fusakar Raudha, kallona yayi daga dayan gefen yace

“Kiyi bacci da wuri very early zamu wuce”

Kaina na gyada masa suka tafi ni kuma na koma gida, tamkar bani nake kukan nan da nayi dazun ba, i was so so happy har dana shiga daki kawai kan gado na fada tareda rungumo pillow a kirjina ina jin kamar zan maida shi cikin jikina, farin cikin da nake ciki kasa misaltuwa yayi, mikewa nayi na dauro alwala nazo nayi raka’o’i biyu na godiya ga Allah inajin a jikina komai yazo karshe. Jin Ummaah na kirani yasa na cire hijabin tareda wullar dashi na daidaita kaina na fito sede fuskata betrayed me dan wani kyakyawan murmushi ne yaki barinta, dukkan dimples dina a lotse suke.

Kallona Ummaah tayi sannan tace

“Yar fara wannan murmushi haka?”

Rufe fuskata nayi nace

“Kai Ummaah”

Jikinta na kwanto ta shafa bayana tace

“Allah ya zaba mafi alkhairi, kiyi istikhara ki nutsu sosae. Duk wanda yasa Allah a lamarinshi bazai taba dana sani zabin shi ba. Ok?”

Kaina na gyada na tafi gurin Abba shikam tambayoyi yayi tayi min akan Dr Abbas wanda na sani na fada idan ban sani ba kuma nayi shiru. Nasiha sosae yayimin se naji kamar auren gobe ne, harda kwalla ta.

Washegari sunday muka tashi da mummunan labarin sakin da yaya Suleiman yayiwa Nadia, ni gaba daya na manta da abinda ya faru kwatkwata. Inna ta dinga murna tace gwara taje ta koyo tarbiyya Ummaah ta korashi akan indai ya dauketa kamar ta haifeshi to ya mayar da Nadia, saki ba koda yaushe yake gyara ba kuma Nadia tayi rashin hankali amma se ya barta da kunyar haduwa damu ma nan gaba. Abba daya ji kamar zai daki yaya Suleiman yace ya wuce ya dawo da ita.  Wajen laasar ina zaune a parlor da system dina ina kara harhada presentation din da zanyi akan Spinal Bifida, dake duk monday akeyi kuma wannan turn dinmu ne.

Kamar daga sama naji sallamar Yaya Suleiman ko dagowa banyi ba amma na amsa sallamar, zama yayi se lokacin na dago naga shida Nadia ne, tayi zuru zuru idanunta sunyi jawur, dan murmushi na kirkiro na musu sannu da zuwa tareda kwalla kiran Asiya akan ta kira Ummaah nikuwa na cigaba da aikina. Ummaah na zuwa na tattara kayana na koma daki dan nasan hakuri aka zo bayarwa ni kam meye nawa a ciki. Ta rigada ta nuna min matsayina gurinta so ko komai ya koma normal alwai abinda har abada an wuce gurin.

Ina karasa kallon love in the moonlight se naji ta turo kofar ta shigo, pausing episode din nayi har ta zauna ta kasa magana haka nima tunda ni banida abin ce mata. Hannuna ta kama tace

“Kiyi hakuri”

Kaina na gyada nace

“Ya wuce”

Se mukai shiru nikam na cigaba da kallona har ta gaji da kanta tayi min sallama. Kamar jira ake ta fita sega kira ya shigo, seda nayi murmushi kafin na daga kiran

“Sir barka da yamma”

“Barka dai Asmau, kin gama compiling presentation din?”

Kaina na gyada nace

“Eh na gama”

“Nice of you, turo min na gani”

Kaina na sake gyadawa nace

“Sure Sir”

Daga haka mukai hanging na tura masa ta mail sannan na tafi nayi sallah se wajen tara na dare ya turon na duba naga corrections din da yayi.

Washegari karfe shida da rabi na gama shiryawa, tea kadai nasha yazo muka tafi. Tunda muka gaisa bai kara cemin komai ba seda muka wuce mariri sannan yace

“Asmau ya maganar mu?”

Da sauri na kalleshi bama kallona yake ba idanunshi yana kan titi hakan yasa na janye idanuna slowly ina tuna maganar Adda Sa’ada data cemin yanzun babu jira, babu sanya kawai i should let things flow naturally kawai.

“Can i blow the winds up for you? Can i treat you like the most precious lady that ever existed in this world? Can you do me the favor of marrying me?”

Ya fada yana kallona bayan yayi parking gefen titi, bazan iya daurewa ba, ba zan iya ja ba kuma words din are so sincere yadda suke fitowa daga bakinshi. Kawai ce mishi nayi

“You most welcome!”1

Kallona ya dinga yi da wani kwantaccen murmushi daya kara kayatar da fuskarshi yayi kyau, ga rana data ratso ta window ta sauka kan fuskokin mu. Dauke idona nayi ina murmushi tateda jin wata nutsuwa ta mamaye ni kamar wani puzzle ya kamata na jera kuma na jera din.

“Naso ace ke din halaliya tace , i would have hug you kiji yadda zuciyata take bugawa. Babu damuwa soon, very soon zan cika mana burinmu. Inshaaa Allah bazkiyi dana sanin amincewa da aurena ba”1

I was emotionless ban ma dago ba ganin bazanyi magana ba yasa ya fara driving muka koma hanya har lokacin kaina yana kasa ina wasa da zoben dake hannuna. Cikin wannan yanayin na tsinkayi muryar shi yana fadin

“Sunana Abbas Aliyu Kwaccido, mu asalinmu fulanin sokoto ne. Kwaccido family name dinmu ne. Mahaifina shi ne dan sokoto, mahaifyata yar kebbi ce a arugungu. So kinga dukkan su dai kusa da kusa suke. Mahaifina dan kasuwa ne wasu dalilai yasa ya koma hadejia gaba daya da zama. Babban yayana Umar shi kadai aka haifa a sokoto suna zuwa hadejia babu jimawa ya rasu. Ni ne dansu na biyu a yanzun ni ne babba a gidan daga ni se Maman Raudha wadda mukazo dubaki da ita. Se autar mu hajara ita ce kamar zakuyi sa’anni da ita kuma tana sokoto tana aure. Bayan barin Alhaji sokoto se ya samu wasu yan uwanshi suka biyo shi shi ne muka tada wani familyn anan. Se ya zaman mu mun tashi a matsayin yan jigawa tunda mun samu indigene by birth. A hadejia nayi primary school dina, seda na gama sannan aka kaini unity school a kwara anan nayi secondary dina baki daya har na kammalla. Allah ya taimakeni sciences nayi, kuma WAEC dina tayi kyau so da aka tashi bada scholarship harda ni anan naje russia nayi medicine and surgery, duk shekara ina dawowa hutu haka dana gama nazo nayi internship dina na koma nayi Family medicine se suka rikeni nayi musu aiki na shekara biyu a haka ina kara fadada karatu na har na samu na dawo. A Aminu kano na fara aiki kafin na koma murtala muhd daga nan na tafi germany nayi wani course akan dialysis. Ina dawowa aka bani MD a hadejia bayan na koma Kazaure se kuma na dawo nan only to meet the love of my life”2

Murmushi mukai dukka a tare sede na gamsu da bayanan sa amma akwai abinda nake bukatar ji daga bakinshi kamar yasan me nake tunani yace

“Izzatu, cousin dita ce. Mahaifinta shi ne babban yayan su Hajiya. Itada Maman Raudha sa’anni suke dukda Maman Raudha ta gurmeta da akalla shekara daya amma duka same boat suke. A lokacin suna Abuja da sauran yan uwanta daga baya mahaifinta aka bashi Ambassador a Russia so kusan duk karatun da nayi a embassy dinsu na zauna. Dukkansu maza ne a gidan ita daya ce mace kuma basu jituwa da ita saboda been the only female child se ta zama over pampered child. Kusan ko da yaushe muna tare da ita ni nake kaita makaranta kuma na dakko ta. Bazan iya cewa ga lokacin dana fara sonta ba na dai san wannan shakuwar ita ta rikeda mana ta zama zazzafar soyayya. Ban taba son wani abu kamar yadda na so Izzy ba, she was everything I ever wanted Asmau amma Allah is the best planner. Muna haka na gama karatuna, lokacinda zan taho tayi kuka a ganinta mun rabu kenan shi ne dalilin da yasa na dawo na karba aikin da aka bani a lokacin tana year 2 a nursing son sena jira ta gama muyi aure amma Abban Abuja yace da zarar zan koma nigeria da matata zan tafi. Hakan ba karamin dadi yayi mana ba, aka shiga shiru mudai kullum a shiriritar soyayya muke. Haka lokaci yazo muka dawo nigeria dan ayi aure. Sede tunda aka fara bikin Izzy ke wasu irin weird maganganu kamar Allah sarki naso na zama matarka da maganganu iri iri wanda sede nayi dariya har aka daura aure….”

Se yayi shiru tareda parking motarshi a gefe, dagowa nayi na kalleshi he looked disturbed, idanunshi har sun canja, se naji jikina yayi sanyi hakan yasa na bude baki zanyi magana amma yace

“I’m sorry it’s still hurting zan karasa miki wani time din”

Kaina na gyada muka cigaba da tafiya cikin wani yanayi me zafi, atmosphere was tensed shi yana tunanin Izzatunshi yayinda nake tunain me ya faru suka rabu da izzatu?

1

AyshatuuuuCikin nutsuwa na maida hankalina wajen presenting spinal bifida, condition ne dayake affecting yara, mukan kirashi “congenital defect” tun lokacin yaro yana ciki spine dinsa “laka” bata rufu ba, hakan is a very rare cases da yafi affecting whites amma anan dinma ana samu. Cause dinshi dai takamaimai baa sani ba sede hankali yafi karkata a rashin sinadarin folic acid a jikin uwa lokacinda tana dauke da ciki.

Ina kamallawa hannun daya fara clapping na MD ne, se kuma sauran suka dauka aka cigaba. Nayi murmushi ina jin dadi sannan na fara amsa questions da kuma consultants da suke kara min wasu points din. Se wajen tara kowa ya nufi office dinshi ready to start the work of the day. Dakina na koma dan na canja kaya saboda ba wears din aiki bane a jikina, seda Na kammalla shirina tsaf na nemo powder cikin wani kit na shafa, na murza kohl nasa lip balm sannan na kalli kaina, nayi tsaf dani se wani murmushi da yake kwance kan fuskata da yaki ya bar kanta, ni kaina na manta lokacin da na fito cikin nutsuwa ta haka, wanka dai bana fasa shi amma fuskata kullum maiko take tun Dr fadima na mita hakan har ta tattara ta kyaleni.+

Kulle dakin nayi na nufi lounge dan nasan house officers din da zamui rounds dasu suna can kamar yadda na umarcesu su jirani. Ina shiga dukkansu suka mike tareda gaisheni. Da murmushi nace

“Are we ready?”

Dukkansu suka amsa sannan muka fito, tamkar wata sabuwar halitta haka nake jin kaina yadda nake jin jikina light like a feather, se nake jin sassanyar iskar dake kadawa tamkar zata daga ni sama. Ina jinsu suna kuskus din abinda ya sani nake wannan farin cikin hakan abinda wasu dagacikinsu basu taba katarin gani ba.

Ina stepping kafata cikin labor ward naji ana fadin

“Kira Dr Shahada matar nan so take tayi parking!”

Ni kaina gaba na seda ya fadi, is it a welcome? Na tambaya kaina kafin na cire stethoscope din dake wuyana na mikawa Dr Ruwaida nayi ciki da sauri suka biyo bayana, tana ganina Sister Naima ta saki ajiyar zuciya, gloves na dauka na zura a hannuna sannan na karaso gurin ina fadin

“Sister me ya faru?”

Tana ta kokarin securing second line tace min

“PPH 2• home delivery. Sunce tayi bleeding sosae on their way coming, jikinta ya nuna though on arrival babu active bleeding sede she’s paper white kuma mata kadai suka zo babu maza”

Kaina na gyada ina kallon ta nace

“Shock zata shiga anytime from now, NASG fa?”

Tace

“Ana hadowa”

Muna tsaye muna jira sega kakarta ce ko babarta no can tell, irin fulanin kauyen nan ne, tana tsayawa tareda kama hannun matar tana mata fullanci nace mata

“Baba har yanzun mazan babu wanda yazo”

Kai ta girgiza tace

“Basu zo ba malama”

Na danyi tsaki nace

“Mijinta baisan kun taho bane ko ko?”

Dariyar yake matar tayi wanda kana kallo is painful tace

“Rayuwa ce kawai”

Ban kara cewa komai ba tunda Na fahimci abinda take nufi. Baa fi minti biyu ba se gashi an kawo NASG muka shimfuda akan wani vacant bed sannan aka ciccibo ta muka daura ta, tana ta shure shure a haka muka fara kokarin daura mata amma wannan tsohuwar taxo ta rike hannuna tace

“‘Yata ki kyaleta da wannan abin kawai bana so”

Kallonta nayi nace

“Baba wannan shi ne taimakon da zamuyu mata kafin mu samu jini”

Matar nan fir taki, muna haka Metron ta shigo nayi mata bayani tace

“Kun manta ethics dinku, patient’s right, idan kuma kuna gama sawa ta rasu fa, zata iya cewa abin ya kasheta allow her”

Se lokacin na tuna hakan, aikuwa muka kyalleta se mukai waya lab a ara mana jini amma kafin a kawo jinin matar ta rasu, it was touching dan babar tace dalilin da yasa mijin yaki zuwa yace jininta wahala yake kuma shi baisan inda zai samu ba. Mazan kauye kenan basu masan meye amfanin aure ba balle su san darajar auren ko dalilin da yasa ake yinshi.

Gaba daya ranar sukuku nayi ta babu wani walwala a tare dani, bawai ban taba ganin mutuwa ba, no amma akwai mutuwar da will stick in your mind forever. Office na wuce dan lokacin da zanyi assignment dina yayi dake ina course na IMCI (Integrated Management of Childhood Illnesses). Glasses dina na saka na bude system dita na fara shigarwa. Wani soft knock naji a jikin kofar hakan yasa na dago tare da kallon kofar, se na tuna cewar ai nayi locking kofar. Dan tsaki na saki tareda mikewa na nufi kofar, ina budewa nayi kyakyawan gani. Yeah kyakyawan gani mana tunda kuwan naga sanyin idaniya ta, naga abinda yasa na saki murmushi a take a gurin.

Tsayawa nayi ina maida masa martanin murmushin da yake min. Seda yace min

“Rowar office din kike min? Kin tsaya a kofa as if I’m not welcome”

Dariya nayi kadan tareda matsawa se ya dage kafadarshi yace

“I was passing by nace bari naga yadda kike”

Cikin jin dadi nace

“Thank you”

Kanshi ya girgiza ni kuma na koma ciki bayan naga tafiyarshi. Tunda na zauna na kasa tabuka komai ina tunanin labarin da Doctor ya bani dazun, I’m so curious nasan me ya faru da Izzy, aure tayi ko kuma hanata auren shi akai. Tunani kalakala babu wanda bai zo min ba har tunani nayi kodai Raudha yar shi ce kuma ita ce fruit of love dinsu. Gaba daya na rasa tunanin me zanyi kuma dan kuwa wannan puzzle ne dana kasa solving.

Manage please…..No complain

Ayshatuuuu🎶Can’t you see? He’s my everything, I’ll wait on him all the days of my life! Can’t you hear? This sweet song he gave? Like cool rain drops falling on a sunny day🎵

Kwanaki a hankali suke shudewa suna wucewa ba tareda saka ran zasu kara dawowa ba, sun tafi tafiya ta har abada. Rayuwar gaba daya is too short wasu abubuwan suna faruwa Amma kwatkwata bamu fahimta, we’re so much engrossed da son kyalekyalen duniya not knowing rayuwar gaba daya ta kusan karewa.

A kalla tafiya tsakanina da Dr Abbas tayi nisa mutane da yawa cikin asibiti sun fahimci meke tsakanin ni dashi. We barely hold giggling and grinning idan muka hadu. Akwai wani lokacin banma san me ya faru ba, kawai an kirani naje OT akan wani aiki da zamuyi. Tun daga kofar OT nasan yana ciki saboda bambamin fadan da yake tayi babu kakkautawa, muryar shi was at it’s highest pitch haka. Tamkar kada na shiga dan ni ban taba ganin fadan shi ba hakan yasa naji gaba daya I’m weak. Na juya zan fita kenan naji muryar Dr Lamin yace+

“Asmau!”

Juyawa nayi fuskata looking dull na karkaro murmushi nace

“Abban Afeeyya, ina kwana?”

“Lafiya lau”

Ya bani amsa sannan yace

“Dan Allah shiga ciki, a patient died on couch, may be idan ya ganki fadan zai ragu”

Baki na bude da niyyar protesting se ya riga ni da fadin

“Just save them please”

Ba yadda na iya haka na shiga ciki, suna tsatsaye a clean area, dukkansu idonsu ya raina fata shi kuma se kumfar baki yake. Banyiwa kowa magana ba kawai na nufi cikin lounge din bayan na tabbatar mun hada ido dashi, kamar minti biyu naji muryarshi yana fadin

“All of you should get out of my sight”

Ajiyar zauciya na sauke, bayan wasu mintina na fito shi dinma baya nan se chief anesthetist na samu yana ta dariya na zauna kujerar dake facing tashi nace

“Me ya faru?”

Dariya ya kara yi yace

“Kin ceci mutane fa, shigowa office nayi na kiraki nasan ke kadai zai gani wannan temper ta sauka”

Kaina Na girgiza dan shikam ya rigada ya san meye tsakanin mu, gashi MD is making it obvious to everyone cewar nidin ni ce farin cikin shi da nutsuwar shi. Mikewa nayi nace

“Ba haka bane, kawai na shigo daidai lokacin da zai gama fadan ne. I guess it’s a coincidence”

Wani kallo yayi min yace

“No, ni ba haka na gani ba, kina shigowa duk wannan fadan dake idanunshi sukai melting especially kin shigo baki kula shi ba.”

Dan dariya nayi kadan nace

“Oga baka da dama”

Yace

“Of course, Inata adduar idan mijinki yazo Allah ya baki miji na gari wanda zaki zama sanyin idaniyar shi. Kinsan there’s a great wisdom akan hakuri amma mutane kalilan ke fahimta, kede a rayuwarki kinci ribar hakuri. Ya fada min har manya sunyi magana ko?”

Se lokacin na tuna MD ya taba fada min Chief abokin shi ne, like ko sunyi school daya ne i don’t remember gaskiya. A idona Chief yanada matsayi saboda duk lokacin da zanzo OT bai bari na fita bai nuna min cewar aure lokaci bane, no way sede idan aiki yayi mana yawa. Godiya nayi mishi nace

“Gobe munada Dialysis so wannan surgery bazaiyi taking place ba se jibi”

Kanshi ya gyada tareda min fatan alkhairi na fita, tamkar jirana yake ina fita yana kirana, seda nayi murmushi sannan na kara wayar a kunnena ina fadin

STORY CONTINUES BELOW

“Allah ya huci zuciyarka”

Dariya yayi kadan yace

“Me yasa kika shigo lokacin, baki bari nayi knocking senses into their head ba.”

Nima dariyar nayi nace

“Saboda bana son naji wani abu ya taba maka muryarka, that’s why”

“Can i see you? Ko kina aiki ne?”

Kaina Na girgiza tamkar yana gaba na nace

“Zanzo inshaaa Allah”

Daga haka mukai sallama na nufi can a hanya naga anata nuna ni inajin ana cewa ita ce budurwar MD, murmushi kawai nayi na wuce zuwa office dinshi, shi kadai na samu yana zaune akan kujerarshi, idanunshi cikin farin medical glasses wanda ya fito da tsayin hancinshi, dukkan hankali shi  yana kan system dan sallamata kawai ya amsa amma bai dago ba balle ya kalleni, zama nayi na maida hankalina kan plasma dake aiki, MBC 2 ce takeyi ana wani program na The Doctor, zamana na gyara dan bana bari ya wuceni ko online ne se na kalla. Ranar akan hyperlipidemia akeyi so yadda na bada attention dina sosae bansan har ya kammalla aikin ba seji nayi dif an kashe socket din, dagowa nayi na ganshi tsaye yana kallona, mikewa nayi nace

“Shi ne ka kashe?”

Kujerar dake facing dina ya zauna yace

“I can’t help naga dukkan hanklainki ya tattara acan kinga dole na kashe.”

Bakina na tabe irin nayi fushi dinnan se ya gyara zaman shi tareda daidaita fuskarshi shi wadda ta tabbatar min serious magana zamuyi, na zauna tareda bashi dukkan hankalina. Yace

“Asmau kinsan me yake kara miki daraja a gurina?”

Kaina na langwabar ina kallonshi with so much love in my eyes Na girgiza kai, murmushi me kyau yayimin yace

“Kinada hakuri, ni banida hakura most especially if it’s for me to wait. Kin bani lokaci da yawa kin daga min kafa dukda kullum ina gani kina son na karasa maganar Izzy a idanunki amma kinki tambaya”

Na kagu naji amma bana son takura mishi, bance komai ba ya cigaba da fadin

“Seda aka daura aure, ban taba ganin ranar da nayi farin ciki irin wannan ranar ba, nayi murna kamar zan tashi sama saboda I’ve got what i waited for all my life. Kinsan me….”

Ina kallnshi Na girgiza kai yace cikin rauni

“…Kafin na baro inda aka daura aure zuwa family house dinmu aka kiramu Izzy ta rasu…”

Mikewa nayi hannuna akan kirjina idanuna a warwaje nace

“Innalillahi wa inna ilahil rajiun,! Sorry please, I’m so sorry ya Allah!”

Murmushi yayi amma i can clearly see the pain he’s hiding, yace

“Wannan shi ne mummunan labarin da ya taba riskata a cikin rayuwata, i felt it dan a take akai asibiti dani, soyayya ta kayar dani na rasa inda kaina yake, meke damuna ? Me ke min ciwo? Me nake bukata. Asmau nasha wahala kafin nayi fighting zuciyata na kara tashi. Nayi kukan rashin izzatu haka tamkar ta tafi da zuciyata se hoto ta bari. Na zama mafadaci very hostile gaba daya na canja, naki nayi aure, soyayyar na tattara na watsar da ita gaba daya. Hajiya kullum nasihar ta nayi hakuri kowa da yadda Allah ya tsara masa rayuwa amna na kasa fahimta gani nake babu mace kamar izzatu kuma ban samu ba tunda na sawa raina hakan. A hankali aka fara hada ni da yaran abokan alhaji ko na hajiya amma ko kallo basu isheni ba se suka kyaleni, a cewar su dan kaina zan sakko and here I’m about to go crazy akanki.”

Dan dariya nayi tareda zama nayi masa gaisuwa da jaje amma nasan he’s just faking the smiles, hakan yasa nace

“Haka rayuwar yake it’s so unfortunate. Allah ya jikanta”

Murmushi yayi yace

“Amin. So ina jinki fada min taki side of story din naji. Your love”

Kaina Na girgiza komai yana dawo min ina picturing dinsa cikin kwakwalwata sede babu wani labari me dadi ciki amma haka nan zan fada masa especially akan yaya Suleiman.

“Taka soyayyar is more enticing than tawa, babu wani jin dadi dana samu se heartbreaks dana samu…”

A hankali daki daki na bashi labarin yaya mukhtar down to yaya Suleiman, sede bansan meye dalilin wani rauni da yazo min ba lokacin da nake fada masa ni nayi hooking Suleiman da Nadia, kawai se naji kuka ya kwace min. Kaina na kifar ina kuka a hankali wanda baki daya ya rikita shi fadi yake

“I’m sorry, bansan haka kike ji ba , da ban tambaya ba”

Seda nasha kukana har fuskata ta canja launi sannan nace

“It pains yadda yayi wasa da tunani na Amma it’s all in the past”

Hirar kuma duk se babu wani dadi hakan yasa yace naje na huta.

Kamar hadin baki weekend din da muka tafi dashi yana sauke ni, Yaya Suleiman na parking, hakan yasa na leka nace ya fito su gaisa dashi, seda ya harare ni kafin ya fito. Yaya Suleiman cikin sakin jiki da sakin fuska ya mika masa hannu shikam Oga ranshi a bace ya bashi suka gaisa ya koma mota Yaya Suleiman ya shiga ciki. Tsayawa nayi nace

“What was that face for? You barely smile”

Yana bude baki se cemin yayi

“I don’t like him!”

Da sauri nace

“Why? Is not as if kasanshi ko kun taba haduwa”

Dariya ya danyi yace

“Saboda yasa min wannan idanun sunyi kuka kinga laifina? He played with your heart baby”

Rufe fuskata nayi ina murmushi wanda ke ratsa raina nace

“Se munyi waya!”

Shoulder dinshi yayi shrugging sannan yayimin sallama na wuce ciki ya tafi tamkar na bishi!

2

AyshatuuuuWashegari da daddare Abba ya kirani dakin Inna, ina kallo sakon ya sameni daga bakin Ikhramar Adda Meeyna da tazo mana hutu, mikewa nayi na dauki wani plain veil na dauka ash na yafa a kaina sannan na fita bayan nayi kashedi da babbar murya akan kada a taba min system din. Ina zuwa na same shi yana zaune kan carpet gefenshi Ummaah se Inna akan katifa da yaya halifa shima a zaune.

A sanyaye Na zauna dan na san it must be something serious. Seda na kara gaishesu suka amsa inna ta nuna min gefenta na zauna sannan Abba ya fara da fadin

“Na taraku anan saboda ke Asmau, ina cikin matukar farin ciki da Allah ya bani iko na sauke nauyin da ke kaina. Last week da kikazo na tambayeki akan maganar Abbas kin amince kin yadda fully zaki aureshi, hakan yasa cikin satinan na zauna da magabatansa na kuma basu aurenki. Alhamdulillah! Kowacce ‘yata haka na mata amd kema hakan na miki sede it’s a condition on no account should you tell me kin fasa aurenshi sede idan babban abu ne wanda ni ne zanyi deciding hakan, there’s no going back. Ina fata kinsan watanni uku kawai aka saka saboda haka sukai requesting. Allah ya tabbatar da alkhairi ya bada fahimtar juna”+

Gaba daya nasan maganar nan kwwai daga bakinshi ne ban ji ba, inshaaa Allah kawai nace sanoda ji nayi tamkar an zuba min ruwan kankara yadda jikina yayi balain sanyi. Koda yaushe ina fatan ranar da zan budu idanu naga aurena amma yanzun se nake jin I’m loving the house more and more. Idanuna se suka cicciko da kwalla inna na tayimin dariyar wai da girmana meye na kuka? Tasan idan nayi auren mantawa da ita zanyi ai fadar haka se na bare baki na fara kukan da baya min wahala, Ummaah ce ta janyo ni jikinta tana rarrashina Abba yana cemin it’s a normal pace for every lady, so su kyaleni nayi kukana.

Koda na koma daki gaba daya se na kalli wannan na kalla wancan, na shafa gadon na bude wardrobe na kalla dressing mirror dina filled with kayan shafe shafe a lokacin naji wani irin missing gudan nake. Wayata na dauka na fara dialing “Jewel” kamar yadda nayi saving mishi number nake kuma kiranshi dashi, saboda a ganina yafi karfin silver, darajar sa tafi ta gold haka ta diamond, he’s a priceless gemstone. Yana dauka yace

“Cara mia!”

Haka yake kirana dashi, at first banma san menene sunan yake nufi ba se wata rana yake cemin it’s means My beloved in russian language. Duk lokacin da ya fada se naji kamar kara min son shi ake.

“Jewel!”

Na fada muryata cikeda rauni,

“Yaya akai? Me ya faru? Muryarki says it all”

Kamar yana gabana na turo bakina, dole Abbas ya sami zuciyata saboda kallona idan yayi yasan idan akwai matsala haka idan muna waya kuma bazai taba kyaleni ba se ya tabbatar nayi dariya.

“Ni ban gaji da gida ba fa!”

Dan dariya yayi yace

“Ma’u love! So dama yaya halifa ya fadamin wai na shirya rocking baby, se yanzun Na fahimci  menene auren auta! Gidana ma ai is home menene abin damuwa”

Kamar yana gabana na fara bubbuga kafata a kasa kamar me kuka nace

“Kullum sede ba zan kalla Ummaah ba”

“Asmau ai yanzun ma ba kullum kike ganinta ba, ki dauka kamar zakije dutse ne”

Kawai se naji hawaye ya fara zuba min, inajin wani irin damuwa a raina. Nasha kuka dakinnan akan banyi aure ba amma see me crying saboda zan bar gidan. Da tsananin mamaki yace

“Cara mia are you crying? Menene abin kuka, is not like auren dole zaayi miki, i love you so much and you feel the same. Bawai kuma zakije detentions bane, kinsan duk lokacin da kike son ganin Ummaah I’ll grant you that request. Cara mia dan Allah ki bar kukannan haka, kinsan yadda nake ji haba mana baby? Kiyi hakuri I’ll be everything you need ok?”

STORY CONTINUES BELOW

“Mhm”

Na fada ina share hawayena dan murmushi yayi yace

“Smile kinji”

And i smiled like a baby daga haka hirar tamu ta cigaba kusan dukkanta akan yadda zamu kasance ne in 3 months dinnan. Daf da zamui sallama nace

“Jewel na manta ban fada maka zan tafi minna ba next week”

“Minna? Me zakiyi”

Gyara kwanciya ta nayi nace

“Ka manta can nayi secondary school dina, New horizon?”

“Yes?”

Ya fada wanting to hear the details”

“So zamuje old students reunion”

Shiru yayi kamar bai ji ba nima nayi shiru dan na tabbatar yaji abinda nace alamun anya zakije kuwa? Dan tsaki yayi yace

“Flight zaki bi, kin sani ko?”

Murmushi nayi nace

“Awnnnn I love you! Nayi booking ni da Nadia da Rayhana”

“Seems good, alright ban gaji da jin muryar ki ba, but kiyi bacci kinji”

Kaina na gyada nace

“Alright sleep well”

🎵Baby I’m yours I love you much!🎶

Bayan sati daya ranar Wednesday na fara off, tun monday bamu hadu dashi ba and it feels so bad haka nan, bana jin dadi. Gaba daya aiki ya rike shi bashida wani free time haka nima se dan interval da zai samu ya kirani to check on me. Tun dare na hada kayana so muna gama rounds na koma daki nayi wanka na canja kayana zuwa wata loose English gown me kyau color royal blue se touches Na turquoise blue a jiki so se nayi amfani da veil da wani flat clowse half cover me kyau. Fuskata like usual daga kwalli se balm se powder da na shafa. Wayata na ciro nayi dialing number Jewel dan nace masa zan tafi, yana picking yace na sameshi a OT yana can. Mota ta na dauka na tafi bayan nayi parking na shiga ciki inajin kamar na shiga da gudu na ganshi na fada masa how much i missed looking at that handsome face of his. Yana zaune a reception shida Chief gabansu da mug din coffee, bana don wannan coffee din tsakar ranar da yake sha, he’s already addicted to it.

Seda na gaida Chief ya dan tsokane ni wai suna missing dina a OT dake na jima banyi surgery ba. Murmushi nayi shikuma yacemun

“Let’s go”

Bayan shi na bi ya tsaya a inda mota ta take yace

“So se tafiya kenan?”

Kaina na gyada nace

“Yes zan tafi se next week inshaaa Allah”

Kanshi ya gyada yace

“Safe journey, Allah ya kiyaye se munyi waya”

“Amin” na amsa masa na shiga drivers seat tareda fastening belt dina sannan Na kalleshi nayi masa wink, kanshi ya zuro cikin motar yace

“Tsokana ko?”

Dariya nayi ya zuro envelope gefen seat dina yace

“Take care of yourself for me. I love you!”

Akwai lokuta da dama da repetition of abubuwa ko magana se ya saka ka gaji, kaji haushi amma banda wannan kalmar ta “I love you” kullum tamkar sabuwa haka take kullum jin ta nake kamar yau aka taba fada min, it’s enticing….

Karfe uku jirginmu ya tashi zuwa niger state, tunda muka boarding flight din muke hira dasu gaba daya secondary school life muke tunawa munata hira so bamu ga lokaci ya ja ba. A school accommodation dinmu yake aikuwa acan muka sauka, muna zama na fara kokarin kiranshi se gashi ya kira, rayhana tace

“Tab Ma’u this your Doctor oooo”

Hararta nayi na dauki wayar muka fara hira akan tafiyar har suka gama wanka ban gama ba se da Nadia tace

“Doctor zatayi wanka”

Sannan muka rabu inata mita. Munsha hira kafin washegari akai grand reunion kusan dukkan yan class dinmu sunzo da yayansu baifi mu hudu ne bamuyi aure ba. Se naji dadi saboda bani daya bace kuma gwara ni ina aiki na kama kuma dahir amma ita daya daga cikinsu ma babu aikin babu mijin babu komai a haka take rayuwar. So ka dinga kallon rayuwar wasu nan zaka gane kana cikin niima sosae.

Taro ya tashi lafiya washegari muka dauka hanya zuwa airport anan naji message ya shigo min, duk tuannina ya tafi akan may be mtn ne seda na kira Jewel sannan naga wata bakuwar number ce, i didn’t check on the message har seda naje gida nayi wanka na gama wayata sannan na tuna dashi. Wannan message din almost gave me a heart attack ban taba ganin dare me tsayi irin wannan daren ba.

I heard zaki aura Dr Kwaccido, do you ever taught of abinda ya hanashi aure. Bari na fada miki he’s a WOMANIZER!

6

Sorry for the late update, y’all should bear with me. Jiki da jini se a slow

AyshatuuuuGyara kwanciyata nayi tareda sake bude text message din ina karantawa a iya adadin da bazan iya tunawa ba. Lokaci daya naji wata zufa ta rufeni, makoshina ya bushe se gaba na da ya dinga faduwa kamar zai balla kirjina ya fito. Kallon wayar na karayi na kara nanata message din “A womanizer?” Na tambayi kaina for the nth of time. Kwalkwalwata taki aminta da abinda ta gani haka zuciyata fada min take is not possible, he can never ba amma sede na kasa gaskata su dukka saboda ina cikin wani irin rudani da ban taba shiga irinsa ba. Wayar na ajiye a gefe tareda runtse idanuna a raina ina ayyana me yasa haka ke faruwa dani? Me yasa rayuwa take min haka? Me yasa kaddarata take zuwa a haka? Seda na fara son shi, na gina dukkan mafarkaina tare dashi sannan wannan abin zai kunno kai? Se kawai naji kuka ya kwace min, i was helpless tsoro sosae ya kamani, tsoron kada na rasa shi saboda nasan zuciyata will be shattered jinina se ya kai koluluwan hawa. To amma ai anyi bincike, kuma na tabbatar Abba bazai overlooking wannan abin ba saboda yana son nayi aure, kaina Na girgiza. Ni da kaina na bincika iya yadda zan iya amma me yasa se daga baya naji wannan muguwar maganar, ina zan saka kaina. Haka nayi ta tunani har da wanda bashida amfani na rasa me zanyi a wannan daren ga bacci yace bai san zancen ba.+

Na jima ina kwance, numfashi ne kawai nake fitar dashi a dadin rai amma ko hannuna jinshi nake yayi min nauyin gaske, so a haka dai nake kwance hawaye ya wanke min fuskata. Da kyar na kara mika hannuna na janyo wayar na kara duba message din, se lokacin idanuna yakai kan number, it’s a strange 9mobile number not in my contact, hannuna yana rawa nayi dialing number amma se a cemin my call has been forwarded, bansan iya lokacin da na dauka ina gwada saata ba amma wayar nan bata shiga ba. Jefar da wayar nayi ina nanata innalillahi wa Inna ilaihil rajiun! With the hope akan zuciyata zata rage zafin da tske min zanji afuwa a cikin raina.

Kafin gari ya waye idanuna sun tashi saboda rashin bacci da kuma kuka, jikina was very weak da na tada sallah ma nayi tunanin bazan iya ba amma haka na daure nayi sannnan Na kwanta akan carpet dun aikuwa bacci ya daukeni. Bacci marar dadi me cikeda mafarke mafarke duk akan maganar, wai na sameshi akan maganar yace min wai to se me? Da gaske ne haka dai abubuwa iri iri. Amma a haka nayi baccin ban masan ummaah ta shigo ba haka Asiya balle kiran Jewel da yayi tayi se karfe goma Asiya ta shigo ta tasheni da sauri na mike ina fadin

“Ya ilahi! Rana haka ta fito?”

Da sauri nayi bandaki nayi wanka ina fitowa na shirya cikin lace maroon da blue zani da peplum riga. Veil na yafa na dakko komai sannan na fito, jikina duk a mace komai inayu ne dan ya zama min dole nayi shi. A parlon Abba nayi breakfast pancake da tea shima kawai sha nake da korawa amma it was tasteless gaba daya message din ya tafi da dukkan kuzari na, dukkan farin ciki na and it’s left and empty and emotional Asmau. Sallama nayi dasu na dauki hanya na tafi cikeda kewar su. I zeroed my mind yadda zan samu nayi concentrating akan tukin amma i hardly do that. Haka dai na samu na isa lafiya, tun a hanya ina kallon Jewel nata kirana amma na kasa dauka saboda ina jin kamar a muryata zai fahimci halin da nake ciki, it breaks my heart to see yana kira ban dauka ba.

A office na aje kayana, na bude wani shelf na dauka abubuwan amfani sannan na zura lab coat dita na fito, ina fitowa naga Messenger MD yazo akan nazo yana kirana, wannan nasan bazan iya tsallakewa ba, haka na bishi inajin gabana yana wani irin faduwa inajin tsoron haduwa dashi nake all in all. A hankali na tura kofar bakina dauke da sallama na shiga ciki, yana jin muryata ya mike daga kan kujerarshi fuskarshi cike da damuwa yace

“Asmau are you ok? Ina wayrki?”

Saukar da idanuna nayi cikeda rashin jin dadi, he looks disturbed he was looking at me with so much tension a idanunshi. Kallona yayi yace

“Zauna Asmau”

Zama nayi babu wani kuzari a jikina sede kallonshi nake ina hasaso how possible will it be for this soul to be a womanizer, Aniya! Na fada cikin raina I doubt so much hakan bamai yiwuwa bane ba.

Gefena ya zauna yace

“Ina jinki me ya faru?”

Nafi mintina biyar ina hesitating na nuna masa ko kada nayi amma zuciyata ta nuna min gwara na fada amsa ayi shi lokaci daya once for all komai ta fanjama fanjamjam! Wayata na ciro daga lab coat pocket dina na bude message din na bashi, tunda ya karba na tsira mishi idona inga wanne yanayi fuskarshi zata yi, babu wani guilt se tashin hankali da mamaki, ban taba ganin yana stammering ba se a lokacin yace

“As….Ma’u….fr….om where?….ina kika samu wannan waye ya turo miki?”

Kuka na fara me daci saboda i can see his innocence a idanunshi, shiru yayi har seda na daina kukan yace

“Is ok, tell me”

Cikin sanyin jiki na bude baki na fara masa bayani tareda nuna masa yadda nayi ta kiran number ban samu ba. Ranshi yayi masifar baci yace

“Cara mia, idan ina neman mata ke zaki fara fahimta da tuni in any way possible na nuna miki, I’ve never done such wallahil azim, believe me”

Hawayena na share nace

“Ayya na sani Jewel i trust you”

Mun jima yana nuna min bashi bane and se naji hankalina ya kwanta naji nutsuwa tazo min, a haka ya kira wani friend dinsa akan a tracking number. Na fahimci no way ka nemi aure ba tareda yan bakin ciki sun shiga dansu watsa abin Amma Allah yafi su.

Ranar banyu aiki ba daga office dinshi kawai fivewa nayi na tafi gidan kyaftun se dare muka rabu. A kwana a tashi babu wuya wajen ubangiji kafin wani lokaci biki ya gaba to sosae banda shiri babu abinda nake.

Ina zaune a tsakar dakina a dutse mun gama waya dashi ranar ya tafi kwalam gaisuwar surikai, flour na debo cikin wata bowl na kwaba da ruwa yayi kamar batter sannan na cire kayana se wani short da half vest dana bari, dining mat na baza a kai na zauna sannan na fara shafawa ina murzar jikina, seda na gama na fitar da ita tas sannan dakko manja na mulke jikina tas na barshi dan jikina yayi absorbing da kyau shima na murje daga baya, na maida lallae wanda na kwaba da madarar turare me kamshi, seda ya bushe na murje sannan na daura kwababbiyar madara and i did same kafin na tafi bayi nayi wanka babu soso da warm water wanda aka zuba tarare a ciki. Gaba daya na kaure da kamshi me sanyu dama kwanakinnann tunda na fara wannan skin therapy din na kara haske jikina yayi laushi haka Adda tace nayi kafin a kaini gun asalin skin pamper din. Da wannan ruwan na wanka na shafe jikina da humra sannan na tsugunna a garwashi tareda lullube jikina da quilt.

1

AyshatuuuuTafiya ta tafi kamar cikin mafarki ranar da aka saka biki ta karato, shirye shirye ko ina yinshi ake dukda dai na rigada nayi making clear to everyone akan I’m not for a grand wedding, babu abinda nake bukata banda kowa ya tayani addua, wani mugun kallo Adda Sa’ada tayimin itada Anty Bintu ranar munje yiwa Anty Bintu yini.

“Lallai ai se munyi bikin da a fadin nigeria se yayi wata guda yana ringing kunnen jamaa, a YouTube kam shi ne a saman search engine.”

Dariya nayi nace

“Kai haba Adda, we just need a bless full marriage ba wani abu ba”

Anty Bintu tace

“Aa fara kinsan dole zaayi kamu dolen dole ne, kuma Anty (Ummaah) zatayi yini. Me kike daukar kanki bazawara ko me?”

Dariya nayi jin abinda tace, Adda Sa’ada tayi caraf tace

“Dallah can, zawarawan yanzun kina kallon yadda suke grand wedding sannan ke kice ba haka ba, baki isa ba kinga I’ll talk to him myself”

Nidai dariya kawai nayi ina ganin kamar a mafarki abubuwan ke faruwa wai da gaske ni Asmau ni ce zanyi aure bayan shudewar shekarunnan. Bayan na rigada na cire tsamannin zuwan wannan ranar amma gashi dake Allah shi ne Allah I’ll be hitched soon. Dukkan shirye shiryen da suke ina jinsu nidai nawa dariya ne kawai nawa dan dama ba wani sani suke a ciki ba. Se yamma lis muka mawa Anty sallama, wasu kulle kullen cikin leather wasu rubber ko wanne da directives kan yadda zanyi amfani dashi ni dai har na kosa ma wallahi, dan na gaji da shaye shayen nan kamar wata ‘yar ganye. Seda na kai Adda gida kafin na wuce namu so lokacin da na isa already an idar da sallar maghrib ana kokarin yin isha, i was on my period so babu wata damuwa kawai shigewa ciki nayi na sheka wanka na fito parlor inda Ummaah ke zaune Abba yaje Kwalam shi da Inna Ade.+

“Asmau akwai event din da kike son kiyi ne?”

Ta tambayeni idanunta a kaina, girgiza kai na nayi nace

“Ummaah kawai dai zaayi normal traditional kamu, sede idan ke zakiyi wani abin?”

Itama kai ta girgiza tace

“Shi dinma is ok, Abbanku yace da kanshi zai kaiki kinga babu wani taro kenan”

Kaina na gyada ban kara cewa komai ba, se lumshe ido da nayi inajin irin wasu bakin yanayi suna dabaibaye ni. Gyaran murya Ummaah tayi hakan yasa na bude idona ina kallonta, itama dukkan hankalinta a kaina yake tace

“Gajen hakuri bashi da amfani, a cikin rayuwarki I’ve learnt a great lesson. Duk yadda ka kai ga son abu ya kasance indai Allah bai yadda ba hakan bazai faru ba. Na sani na cutar dake Asmau, i wasn’t a good mother actually ban kyauta ba, idanuna sun rufe na kasa lallashinki lokacin da kika fi bukatar hakan se kara miki matsaloli da nayi tayi. Ki yafe min dan akwai hisabi tsakanin da da uwarshi tunda kuwa mu din kamar care takers dinku ne da Allah ya bamu. I’m sorry fara”

Kaina na girgiza mata inajin raunin dake saukar min cikin zuciyata, rungumeta nayi nace

“Ummaah, maganar ta wuce ko a lahira bazaa tada ita ba, ke Ummaah tace fa wannan shi ne kulawar ki, baki zlince ne ba you just wanted me to do it. Ummaah Allah ya kara lafiya”

Hawaye a hankali ya dinga bin kuncina, sosae nayi kuka lokacin saboda nasan na kusa barin gidan na kusa tafiya na bar Ummaah, a lokacin ji nake kamar zanyi hauka, I don’t want to leave!

Na koma Dutse dan se na kara sati biyu kafin na dawo gaba daya, da kaina naje danshi baya gari yaje wani Workshop a ikeja. Kwana na biyu da dawowa ya dawo ina tsakiyar aiki a SCBU an kawo wani neonate me neonatal tetanus muna attending dinsa, wayata ta fara ringing, ko ban ciro ba nasan Jewel ne he got a unique ringing tone a wayata. Murmushin da nayi yasa Dr halima karbar folder daga hannuna tace

STORY CONTINUES BELOW

“Jeki you are excused”

Kaina na girgiza da sauri ina fadin

“Aa ma’am, fada zaiyi ai na bar aiki. I’ll tell him aiki nake”

Kanta Ta gyada tareda mika min folder na cigaba sede fiye da rabin hankalina baya jikina, kina kallona zaki san I’m super excited abin mamaki Allah Allah nake na gama na tafi. Crap muna gamawa kuma se ga wani admission din shikam sepsis ne babu yadda zanyi haka na gama dashi na jira suka kawo drugs dinsu nayi setting line kafin na koma gurin Metron naji ko akwai wani abu tace babu, sallama na mata bayan nace mata duk abinda ya tashi a kirani, tana dariya tace

“Jeki kede nasan wannan murmushi da ake na ganin oga ne”

Fuskata na rufe ina dariya a hankali cikeda kunya sannan na fita tareda ciro wayata na fara kiranshi

“Cara mia! Na dawo”

Har cikin raina sunan nan yake shigar min, inajin farin ciki whenever he calls me Cara mia, yana nuna min da gaske I’m his beloved.

“Jewel sannu da zuwa, ya hanya?”

“Ina OT ina jiranki”

Kaina na gyada kamar wata wawiya haka na tafi inata suppressing ihun da nake son nayi, kamar nayi flying naje na sameshi amma babu dama, kamar mutane sunsan me nake yiwa akai ta tsayar da ni ana min Allah ya sanya alkhairi wai dama sunata zargin hakan se gashi ya tabbata. Nidai nawa smiles ne kawai nawa dan bansan me zance ba.

Yana zaune bansan abinda yake yi a OT ba a wannan time din, most times idan zamu hadu zai ce min na sameshi a OT bansan wanne bond ke tsakanin su ba. Ina shiga OT was calm so straight inda nasan zan sameshi na wuce bayan na gama gaisawa da nurses din gurin sunata tsokanata da amarya nidai sede nayi murmushi inajin kunya tana kama ni. Seda nayi knocking softly kafin naji manly muryar shi yace

“Come In please”

Da murmushi na shiga yana zaune shi da Chief na zauna ina gaishesu, Chief yace min

“Ya gajiya? Jiya nan was hectic”

Kaina na gyada nace

“Gaskiya kam, it was Amma Alhamdulillah gajiya ta tafi”

Murmushi yayi yace

“Hakane”

Se ya mike ya mana sallama, zama ya gyara yace

“Cara murnar nan taki boyuwa fa, anya kuwa zaa dinga bari na ina zuwa assignment kuwa”

Dariya nayi nace

“I was just happy ka dawo lafiya”

Cikeda jin dadi yace

“Yeah i see, I’m so happy seeing you, babu ruwanki your face is glowing ki kalla duk na kode”

Dariya nayi nace

Babu wani fa

“Sadiq yace wai zai hada mana walima or not really walima something like luncheon, gashi kince ke baki san taro sosae I don’t want to disturb you”

Kaina na rausaayr gefe nace

“It’s ok, ai babu dadi nayi turning gayyata. Mun gode mishi”

Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi yace

“That simplicity of you makes me fall for you often.”

Fuskata na rufe inajin kamar I’m immersed in a cool water.

“Yace wai soyayyar tamu a nan OT ta fara so dole ya zama yayi mana something memorable”

Kallonshi nayi nace

STORY CONTINUES BELOW

“Da gaske anan ta fara”

Slamming system din dake gabanahi yayi tareda tsira min idonshi wanda yasa nayi saurin kawar da nawa gefe yace

“Of course my lady, a OT komai ya fara. I started liking your skills ranar da muka fara aiki dake, i dunno nayi ta cewa Dr halima ta kara mana booking aiki tare, i just feel safe working with you and bansan yadda akai your love unfreeze that froze heart of mine, yayi penetrating hakan. Baby I love you”

Da kyar na samu banyi shouting I love you too ba, saboda yadda naji ni on top of the cloud, wani sanyi na ratsa ni. Mun kusan hour muna hira sannan muka fito shi ya fita zuwa office dinshi ni kuma naje nayiwa Chief godiyar luncheon sannan na tafi.

Biki saura sati daya aka kawo lefe, imagine lefe na. Kuyi tunanin all those super dutch, super ABC, exclusives, laces, voiles, materials, shaddas,Abayas. Da na zauna gani kasa irgawa nayi saboda yawa tsada da kyau. Nayi godiya har seda yayi fushi. Bayan an nitsa se shirye shirye suka kara kankama kamar me na gaji likis. Ana saura kwana biyu a fara biki yazo gida akan zamuje zaayi visa ta tafiya honeymoon. Bakina kamar ya yage dan I remembered kamar wasa ya taba tambayata a duniya akwai famous gurin da nake son suwa? Bazaa rasa ba i had them da yawa. Ban kawo komai ba na zauna nace

“Ina son naje naga leaning tower of Pisa, italy. Colosseum of Rome, Italy. Twin towers of malaysia, the sphinx of egypt se the golden gate of San Francisco of USA”

Seda ya gama jina yace

“Duk ina kika sansu haka”

Nayi dariya nace

“I checked on wani littafi tun ina secondary school shi ne naji tun lokacin ina son naje”

Daga nan bamu kara maganar ba koda mukaje yin visas din karshe har Abuja mukaje na samu rakiyar Ikhrama, Baby da Raudha dinshi. Abin manya babu jimawa aka ciku ciku sede ta egypt ce bamu samu ba yace kilan ma zamuyi trans in indai hours din zai isa babu matsala.

Muna dawowa me kunshi na jirana akayi aka gama me gyaran jki tayi nata na karshe ta wuce, da daddare Adda Habiba mukaje salon da ita aka gama komai na dawo a matukar gajiye. Aure yakin mata i said. Da asuba bayan an idar da sallah ina zaune ko tashi akan sallayar banyi ba inata karatun qurani, zuciyata tayimin nauyi inajin wani irin yanayi wanda ni kadai da victims dinne zasuyi bayani amma banda su Shatutu. Na jima ina karatun naji wayata tayi ringing. Seda nakai aya kafin na katse na dauka jikina a sanyaye ganin Abba ne. Ina dauka yace na sameshi a dakinshi. Mikewa nayi bayan na damkawa Kyaftun wayar wadda tun jiya taxo itada Afeeyya se wani cikin dake jikinta, dake mutane sun fara zuwa sannan na fita, tunda na sameshi shi daya nasan abinda nake ta gudu shi ne zai faru wato nasihan auren nan da bana so, tunda Ummaah ta mini last week nafi awa uku ina kuka. Aikam nasha nasiha shiaysa a rayuwata ban taba mantawa da nasihar Abba Ummaah, metron dinsu kyaftun ba. Matar nan ta zaunar dani kafin na tafi ta nuna min yadda zan tafiyar da aure socially, financially, physically, psychologically, sexually and stuffs.

Inata kuka na fito daga dakin nashi saboda maganganun daya fada min tabbas na fahimci aure is not all what it seems to be, hakurinnan da saa ta cewa kayi ba a banza ba, ya nuna min wannan zaman is a boring zama wanda babu wata soyayya da zata kaika, the only thing shi ne mutuncin junanmu da wannan affection din, understanding junanmu da approach na zamantakewa shi ne komai. Same abinda ta cemin aure ba hakuri yake bukata ba juriya, uzuri, kawar da kai, tattali da daraja juna shi ne komai. Metron ta cemin aure shi ne gaskiya da gaskiya duk abinda kake boyewa se an ganshi, idan hali ne lokaci zaiyi da se halin ya fito kowa ya fahimta kuma hakane se bayan da naje na fahimci hakan.

Adda Maryam ta kalleni tace

“To ke kuma kukan me kike kamar zaa miki auren dole? Allah ya kyauta”

STORY CONTINUES BELOW

Ko kulata banyi ba na cigaba da kukana, ita rana irin haka ihu haka ta dinga yi har seda tasa nayi kuka amma see her saying this nonsense.

Tun twelve na tafi kwaliyya saboda karfe biyu ne luncheon din, nasan babu wani babban mutum da zai zo kuma ya jiramu shima seda ya nanatawa Adda Sa’ada da kyaftun akan hakan, muna zuwa aka kaini bridal room, ceo din da kanta ta yimin kwalliyar, lace dina na ranar was Milk with coffee touches so komai da nasa was coffee nayi kyau ni kaina na sani ban taba make up ko bikin kyaftun banyi ba, yanzun ma seea tayi counselling dina sosae kafin na samu kwarin gwiwa and naji dadin ganin kudin daya biya bai tafi a iska ba. Aka kakkashe ni da flashes after much canja style, unlooking styles and stuffs haka nan dai na jure aka gama.

Da kanshi yazo daukata shikadai cikin motar da sanyi da kamshi kawai ke tashi a ciki, yana cikin wani lafiyayyen yadi, milk aikinshi coffee same as mine, nice fara shi baki ne so milk din yayi aiki a fatarshi sosae, yayi kyau babu karya, i was mesmerized by the lovely look in his eyes, yana kallona kamar bai taba ganina ba seda Adda tace

“Ina nan fa”

Dariya yayi yace

“Ke ‘yar sa ido ce fa”

Bata rai tayi dama sun saba fadansu shi da ita kamar ba surukai ba. Seda na shiga aka kakkashe mana flashes kafin yaja suma suka shiga motarsu suka bi bayanmu. A cool music was playing

It’s the way she fill my senses,

Its perfume thet she wears

I feel I’m loosing my defenses,

To the color of her hair

And every little of her is right,

Just thinking about her takes me through the night.

Every time we meet the picture is complete ,

Every time we touch the feeling is too much,

She’s all i need to fall in love with again,

I knew it from the very start ,

She’s the puzzle of my heart!

It was cool, one thing da muke dashi in common shi ne son wakokin west life. Har mukaje gurin sannan yayi waya akan mun iso, kallona yayi na lumshe ido se kawai ya fara min hotuna yace

“Cara mia!”

Dagowa nayi na kalleshi kamar me tsoron kallon nashi se kuma na kara maida idanuna kasa, kafin ya kara magana akai knocking hakan yasa yayi wining glass din kasa se lokacin naga motoci da yawa kusan talatin sunyi parking, Adda Sa’ada ce da Uncle Mamman mijinta, suka gaisa dan ina tunanin first time da suka hadu kenan, se Maman Raudha da mijinta shima. tare muka fito ina jin wani irin bakon yanayi, yana mamaye jikina, Adda Sa’ada da uncle mamman a gaba se Maman Raudha Anty Zainab da mijinta Uncle Labaran a bayan mu. Na tuna lokacinda na tambaya kyaftun yadda ango da amarya ke tafiyarsu tayu dariya tace idan time yayi babu me koya min, I’ll do it unconsciously and here I’m doing it.

Wani soft music ke tashi cikin gurin, decoration din yayi kyau kana kallo kasan medics zasui aure dan harda stethoscope da syringes a decoration din. Anyi hoto kafin muka shiga. A table of four kowanne couples ne, se namu acan sama yayi kyau kamar ba gobe. Kowa ya mike mutanen duka basu fi sixty ba, tare muka zauna babu wanda yazo yimin hoto saboda anyi hiring photographer dan haka mc direct ya fara aikinshi.  Dr. Hannafi shi yayi opening prayers, kyaftun da tazo da Lamin ta bada tarihi na, wani friend dinsa Dr Imran ya bada nashi. Halfway mukaje muka gaggaisa da mutane akai mana hoto har na gaji, kawayena sunmin kara, su Amina Aminu, rayhana, Nadia, Dr fadima, da wasu kukma and abin dadin kowacce da mijinta. Harda friends dina nurses na shekoni dana potuskum inda nayi service se sisters dina, a nashi bangaren manyan medical doctors abokanshi wajen goma kowanne da matarshi suka zo, se cousins dinsa.

Chief shi ya bada tarihin soyayyar mu, wai shi ya hada daga mika scarpel next shi ne, Dr Shahada I’m waiting for you in the OT, mukai ta dariya sannan muna dan hira dukda nawa gyada kai ne but trust me, photographer  baiyi missing capturing moments din da mukai dariya ba ko kallon juna haka. Daga karshe akai closing da addua bayan Adda Sa’ada ta bamu marital advices ita kuma Maman Raudha addua tayi. Muka mike dan sallama da guest dinmu anan wani soft music

Just a smile and d rain is gone

Can hardly believe it , yeah

There’s an angel standing next to me reaching for my hand

Just a smile and theres no going back

But there’s an angel calling me reaching for my hand

Yes, I’ll be ok because this time is real!

I lay my love on you, it’s all i wanna do

Every time I breathe I feel brand new

You open up my heart, show me how you love and walk right through.

I believe it’s ok, cuz this time it’s real!

I lay may love on you , is only i wanna do

Every time I breathe I feel brand new.

Har gida ya maida ni lokacin ana laasar ina shiga aka rikeni mukai pictures sannan na tafi nayi sallah. Ranar gaba daya bamuyi waya sosae ba kowa yana ta bakinsa. Washegari kamu ne, lace dina yellow ne not wannan lousy yellow. Yolk yellow gaba daya zaren da akai designs a jiki black ne me kyau. Munje kwaliyya da nasa aka min ado da accessories bakake se naga i was breathtaking nafi jiya kyau. Maman Raudha ta dinga daukata tana turawa doctor shi kuma yana exclaiming.

A compound din gida akai niyyar yin kamun amma ina bazai yiwu ba saboda baki dole se hall aka kama muka tafi. Anmin kara daga friends din Ummaah, nawa yan kwalam, yan uwan Ummaah, friends dina, yan potuskum, ya shekoni musamman my hearty nurses, yan shatuuu kingdom, Maman Mamaa da zeenert group da group din da shatuuu bata ciki amma labarina ya isa garesu sunyi kokari sosae. Naji dadi haka wata yayar babanshi ta kama ni aka min naira spray sannan se picture session aka tashi lafiya.

I was super tired kamar zan fadi haka naji da muka dawo so ranar da wurwuri nayi bacci shima seda na masa text dan kada ya kira. Friday ce washegari ranar da bazamu taba mantawa da ita ba cikin rayuwar mu daga ni har shi, ranar da Allah ya cika mana burin mu  muka zama officially mata da miji, na zama Mrs Abbas Kwaccido.

Amina Aminu na daura min zani, Dr fadima ta miko wayata, ganin sunan seda naji wata faduwar gaba ta ziyarce ni babu wanda ya kula dani haka na dauki wayar, cikin sanyin murya nayi masa sallama, da kyar naji amsawar da yayai saboda yadda background din ke cike da hayaniya alamun basu bar wajen daurin auren ba. Kamar whisper haka ya sanar min ni yanzun tashi ce, he’s completely mine also, yana mana fatan alkhairi. Wani farin ciki ne ya mamaye ni, instead naji tsoro se naji wani irin safety yayi clouding dina tamkar shield aka rufe ni dashi. Kafin na sauke wayar gidan ya dauki buda alamar zancen ya iso, sadakina da gold ya biya. Adda tasa nayi sujudus shukr sannan nayi sallah rakaa biyu lokacin angwaye suka iso. Suka gaishesu hotunan kadan akai saboda yana sauri ya shirya baifi 3 hours ya rage flight dinmu ya tashi ba. So nima yana tafiya aka sake murje ni da taurarruka, dura wancan sha wancan haka har aka gama nayi wanka aka min turare sannan na shirya cikin wata farar soft abaya, free ce kamar zubun bubu, anyi mata ado da wasu flowers da palse masu kyau. Komai fari nasa. Tunda akace yazo na fara kuka har da Ummaah a kukan balle Asiya. Inna ta saka ni ciki bayan munyi sallama da Abba. Inaji driver yaja muka tafi har lokacin kuka nake, ko rarrashina baiyi ba hakan ya kara tunzura ni, seda driver yayi parking sannan ya matso kusa dani ya shafa bayana bayan yayi hugging dina yace1

“It’s ok, stop crying. You’re safe!”

Dif kukan ya dauke, yanayi bazai fadu ba amma that’s the first closest body contact we had, shima kanshi seda yaji a jikinshi. Tare muka fito bayan ya goge min fuska, akai screening da weighing hand luggage dinmu muka tafi.

You got that smile

That only heavens can make,

I pray to God everyday that you keep that smile.

You’re my dreams

There’s no a thing i won’t do,

I’ll give my life all for you,

Cux you’re my dreams.

And baby, everything that I’ve is yours,

You’ll never go cold or hungry,

I’ll be there when you’re insecure,

Let you know that you always lovely,

Bcux you’re d only thing i got right now.

Apologies

1

AyshatuuuuI’ll love you o my darling

I’ll always be by your side

And I’ll give you all i have

Cux you give me peace and joy

Tunda muka boarding jirgin baccin gajiya ya fara dauka ta, ni ce jikin window shi kuma a gefena. Ganin yadda nake ta lumshe idona yasa ya daura min kaina akan kafadarshi, hakan da yayi min ba karamin dadi naji ba, se bacci ya dauke ni so peaceful dukda ban samu na ware kafata ba amma wannan body contact din is so loving. Daga karshe kaina cinyar shi ya mayar min hakan yasa na kara sakin jikina, idanunshi gaba daya suna kan fuskata ni ban masan yana kallon ba all i know I’m cuddled. Hannunsa yasa yana shafa hancina zuwa lips dina da nayi musu damping lip balm akai. Bansan iya lokacinda ya dauka yana surveying fuskar tawa ba, nasan dai ni ban tashi ba se da aka fara announcement akan kowa yayi fastening seat belt dinsa, the plane is about to land, shi ne yasa ya tashe ni a hanakali. Idanuna na bude na kalleshi sannan na gyara zamana , da kanshi ya saka min belt din yace+

“Kinsha bacci?”

Dan murmushi kawai nayi bance komai ba, saboda normally idan na tashi a bacci bana son magana se naga kamar zaaji bakina yana wari hakan yasa nayi shiru bance uffan ba. Shima bai kara cemin komai ba se hannuna da ya riko yana tracing lallen da nashi hannun, wani irin electrical waves na dinga ji suna shiga jikina, kafin wani lokaci jikina ya mutu kuma bazan iya janye hannun nawa ba. Ana gama komai muka fito akai screening da komai sannan muka bar Riyadh, dama nasan umra zamu fara yi kafin muje states. Kafin ya samo mana cab din da zata kaimu yasa na zauna kan wani bench da luggage dinmu sannna ya tafi. Ina zaune inata kallon mutanen dake ta hada hadarsu not minding harkar kowa.

Numfashi na shaka a karo na babu adadi ina kara yiwa Allah kirari, ni kaina inajin kamar mafarki nakeyi ba gaske bane, ni ce nayi aure ni ce nake da miji har na taho honeymoon? Idanuna na lumshe ina jin komai a rayuwa Allah ya tsara anad timing matters alot, no matter how badly you want something idan Allah bai yarda lokacin abun bane sede ka takura kanka kawai. Aure ba farilla bane, sunna ce me karfin gaske sede you can’t be accountable of what you’ve not done, Allah alhakim ne, yafi kowa HIKMAH yafi kowa sanin menene ya dace da wannan bawan nawa, a rayuwar nan saboda matsin da ake ciki na takurawa akan rashin aure mutane da yawa are into bad marriage, wasu sun bar gida gaba daya.

Mun rigada munsan aure is a mutual agreement between souls, zama ne wanda ake adduar ya zama har abada, what if baka shirya ba ka shiga? Baka san me zaka tarar ba ka shiga? Wannan su ne abunda ke leading to broken homes….. Tabani yayi hakan yasa na juyo da sauri yana tsaye hannunsa da bottled water, se wata leda kuma a dayan hannun. Mika min ruwan yayi na kuskure bakina sannan nasha, se muka dauka kayan wanda shi ya dinga kaiwa ya hanani dauka muka zauna bayan motar, driver ya tada muka dau hanya.

“Tunanin ke kikeyi?”

Kallonshi nayi sannan na dan langwabar da kaina nace

“Rayuwa!”

Kanshi ya gyada tareda kara kamo hannuna yace

“I see, tamu ta rigada ta canja. Munyi addua neman alkhairi se Allah ya mallaka mana junanmu, kinsan me yake ce mana, ni dake we’re perfect for each other. I’ll do everything possible within my reach to make it possible. Inshaaa Allah bazakiyi dana sanin zabin da kikayi ba, I’ll make you the most happiest queen in her kingdom, it will only be possible if you are willing to”

Hannunshi dake cikin nawa na damke inajin wasu irin mixed feelings suna flooding cikin jikina. Kamar mai koyon magana ko kuma me tsoron abinda zata fada nace

“I’m willing to, I’ll be submissive Inshaaa Allah”

Wani bone crushing hug ya bani kamar zai maidani cikin jikin shi, hannuna nasa na rungume shi nima inajin wani sanyi na ratsa zuciyata.

Muna zuwa muka isa masaukinmu, ba suite bane daki ne guda daya hade da bayi a ciki. Shi ya fara wanka sannan na shiga nayi, seda na gama sannan na fara tunanin yadda zan fara fitowa gabanshi a haka. Se naji muryar shi yana cemin ya sauka kasa zai karbo sako, ajiyar zuciya na sauke sannan na fito bayan naji ya rufe kofar, da sauri na saka kaya bayan na shafe jikina da soft scented perfume. Ina zura hijabi yana shigowa hannunsa rikeda tray ashe ba inda yaje, he gave me space na shirya, da sauri na karba na aje a kasa akan rug din dake shimfude. Seda mukai sallar da mukai missing sannan muka ci abinci. Yana cikin farar jallabiyya ni kuma baka se hijab dana daura akai muka tafi harami tareda daura niyyar umra. Seda muka gama abinda zamuyi akai sallar ishai sannan muka fara walk yana nuna min abubuwa wasu nayi dariya wasu na harareshi. A karshe mukaje wani ice cream parlor ya saya min na sha a gurin, shi dama yace min shi bai taba sha ba ai abin yara ne. Ban kula shi ba seda ya sake jiki yana bani labari kawai na ciko scoop din hannuna nasa mishi a baki ina dariya, a zabure ya mike kamar wanda aka saka mishi flagyl a baki, kallonshi nayi ganin ya tsotse tas yana wani yamutsa fuska. Dariya nayi nace

“You like it?”

Kanshi ya gyada kamar wani me zance, cikowa na karayi tareda kai masa bakinsa and babu musu ya karba, karshe dai tare muka shanye. Se ya cemin wai dama haka yake da dadi bai sani ba, nace all thanks to me yanzun ka sani.

Bazan taba manta zaman sati daya da mukai a saudia ba, bai min komai ba a cewar shi se mun fara neman albarkar auren kuma saudiyya ai ibada mukaxo yi. Believe me munyi ibada, munyi yawo ya nuna min duk kulawar da ya kamata ace an nuna min.

Da daddare jirginmu ya tashi zuwa italy instead of states. An canja saboda akwai wani official assignment da zaiyi acan kuma time baiyi ba so shiyasa. Rome urbe airport anan jirginmu ya sauka. A gajiye nake likis dan kayan ma se shi ya dakko, karku manta ni a son jiki har yanzun bawai na daina bane kawai na rage ne. Hotel din da yayi mana booking muka wuce. Tabbas Rome ta hadu it’s an ancient city of historical significance.

Muna tafiya driver da Allah yasa yana jin turanci yana mana bayanin gurare, iyakar building dinsu ma abin kallo ne. Se na ware duk wannan kukan gajiyar da nake ya tafi. Hotel dinmu ya kaimu bayan Jewel ya karba digit dinsa akan zai zama idonmu a Rome. Wannan ma dakinne kamar wancan, ina ganin gadon na fada saboda yadda yayi kyau ya sha gyara Kamar babu gobe. Kwanciya nayi yazo daidai kafata ya zauna yace

“Cara Mia! Kiyi wanka se kiyi baccin”

Kafadata na girgiza ina zumbura baki nace

“Ka fara ni na gaji”

Kanshi ya gyada tareda mikewa yace

“Nidai ban bada gajiya ba amma kullum zancen gajiya kike, I’ll give you the gajiya you crying for”

Bansan na tashi ba se gani na nayi kawai a toilet na fara watsa ruwa abin ma se ya bani dariya, daidai toilet din yazo yace

“Kiyi sauri kinji wasa nake yi”

Turo baki na nayi kamar yana ganina na cigaba da wankan. Ina fitowa na shirya cikin simple skirt da riga na wani bakin material da na taho dashi. Hijab na saka na leka balcony yana tsaye yana kallon gari. A hankali ya juyo yana kallona se na karasa gefenshi na tsaya ina kallon yadda motoci ke ta gewayen su.

“The view is breathtaking isn’t it?”

Kaina na gyada ina murmushi nace

“Sure, kaje kayi wanka to mana”

“Ina wari ne?”

Da sauri na girgiza kaina nace

“Kai, ni ban fada ba fa kawai kayi ko kaji dadi”

Barina yayi a gurin bayan ya min peck a kumatuna, gaba daya na rike gurin ina wani smiling foolishly inajin kamar bai dauke lips dinsa daga gurin ba. Haka ya fito ya taddani tsaye ina sake sake, mukaci abinci sannan muka dan fara hira kadan kadan dukda yawanci hurar ba maganar baki bace, its a soul conversation dan tunda ya ciren hijab din jikina hannunshi ya fara roaming zuwa sashen da ban ma taba expecting bayan hannuna akwai wanda zai iya tabawa, jiki da jini shekaru sunja, ga aikin hormones take naji dukkan jikina ya amsa, kowacce gaba ta jikina was accepting and welcoming that sensation da maraba. Karshe cushion din da muke kai se ya gagara daukar mu haka ya Jani passionately muka koma gado. He gave me something that taste as sweet as honey!

AyshatuuuuSomething as sweet as honey!

Gajiyar da nake kukan ta tun a nigeria, ita ya daura min, danma yace shi a idanunshi nothing is as fragile as I am, hakkinshi ne yayi duk yadda zaiyi yayi protecting dina. Ban taba kawowa ko cikin daydream dina akwai irin wannan kulawar, da Jewel ya bani ba. Tamkar zai tsaga jikinshi ya maida ni ko kuma ya min numfashi haka yayi. Tabbas Jewel worth the wait.

Ranar babu inda muka leka har washegari muna daki daga kan sofa se kan gado se kan rug. Se dare ya fita karbo min pizza anan mukai whatsapp video call dasu Ummaah, tana ta tambayata ko akwai abinda yake damuna nace mata babu amma dukka hankalina se naji yayi gida, naji babu abinda nake so illa na ganni gaban Ummaah, so tun kafin muyi sallama na fara kuka. Cikeda damuwa tace+

“Menene Asmau?”

Kaina na gurgiza nace

“Babu komai”

“To ki daina kuka kinji? Kowacce mace da kike gani da haka ta saba. Kowacce seda ta bi wannan process din. Ki kwantar da hankalinki kinji kar ki daga masa hankali”

Aikuwa dai na kasa tsayar da hawayen se sallama kawai tayi min, tana kashewa kuwa na hada kaina da gwiwa na fara wani sabon kukan, wani abu naji ya tokare min makoshi na. Ina wannan halin Jewel ya dawo, bakin shi da sallama ya shigo. A zabure na mike zanyi toilet amma ina ya rigada ya ganni, aje kayan hannunshi yayi ya karaso inda nake tsaye nasa tafin hannuna na rufe fuskata ina wata sheshekar kukan. Baice min komai ba kawai ya jawo hannuna ya kaini bakin gado na zauna, shi kuma ya dakko min ruwa me sanyi da ya tsiyayo daga dispenser ya kawo min , babu musu na karba saboda many are contemplating on where the soul is, Believe me cold and chilled water knows its location. Inasha naji a hankali wannan kululun na wuyana yana melting down, na saki ajiyar zuciya tareda aje cup din na karba tissue daya miko min na goge fuskata. Shi bai cemin ba se ya wuce toilet sannan ya fito yace

“Je kiyi wanka”

Banyi musu ba nayi stripping kayan jikina se towel na daura na shiga a ciki inata bawa kaina hakuri saboda i can read damuwar da yake ciki kuma na tabbatar gani na a hakan ne. To ya zanyi? Nima I can’t help it I’m missing home kuma normal ne ga kowacce amarya irrespective of age. Yana zaune na sameshi hannunshi yana danna waya, murmushi na sakar mishi wanda yasa dole ya mayar min da martani tareda tasowa ya amsa towel din dake hannuna yana gogen jikina, kunyar  nan ba duka ta tafi ba wata dai ta wuce amma still akwai ta. Da kyar na yarda ya shafa min soft lotion shima da gangan yake tsokanata, kafin na gama shiryawa gaba daya mood dina ya canja se dariya nakeyi. Wani pallazo pant na saka maroon da free shirt me dogon sleeve peach na saka sannan nayi rolling, seda yayi surveying da kyau sannan mukai hoto saboda babu inda shigata ta fitar da surar jikina.

Hannunshi cikin nawa muka fita zuwa ground floor kafin mukai exiting gaba daya daga hotel din, wannan driver na gani a tsaye yana jiranmu. Da murmushi ya gaisheni na amsa sannan muka shiga muka dauki hanya. Na kalli Jewel da suke ta hira da mutumin nace

“Colosseum din zamu je?”

Kanshi ya girgiza yace

“Surprise”

Bakina na tura nace

“Bana son surprises fa”

Girarshi ya dage min yana yar dariya da tasa na shagala hanci baki da ido ina kallonshi, a hankali na kai hannuna kan side burns dinsa da suke kawatar da fuskarshi, Allah ya sani i always admire maza masu side burns se gashi na samu se nyi yadda nake so. Yadda nake ta wasa da hannuna a gurin yasa ya kasa concentrating kan maganar da suke kawai se yayi shiru tare dashi lumshe idanunshi, nayi murmushi na kwanto a jikinshi babu bata lokaci yasahannunsa yayi enveloping dina into a hug.

Trevi fountain mukaje naga water fall, mukai hotuna inata jin dadi kamar zan tashi sama, shikam se murmushi yake yana jin ddin ya sani farin ciki, hannuna cikin nashi munata strolling a gurin inda yamin kyau na tsayar dashi muyi hoto a haka har show din ya kare muka tafi. Muna kwance ni dashi mun gama shirin bacci, ya kawo hannunshi ya kama nawa yace

STORY CONTINUES BELOW

“Tell me me yasa kike kuka dazun? Ni ne? Nayi miki laifi Cara mia?”

Kaina na girgiza nace

“Ummaah ce mukai waya da ita, i was missing her”

Sosae yayi dariya tareda kissing bakina da nayi pouting lips din yace

“Auta, shagwabar ta tashi kenan?”

Hannuna na kwace ina kara zumbura baki, a haka muka shiririce ya cikani da soyayya and i gave him something he’ll never forget. Washegari gaba daya ranar yawo mukai, se ranar mukaje colosseum din, gurin yayi bama yadda nake expecting ganinshi ba. Ancient building ne sosae , mutumin yana ta bamu labarin yadda akai colosseum din haka. A daren muka koma pisa, kwanan mu daya mukaje naga leaning tower, mamaki sosae nake ta kasa a daidai take amma daga can ta karkace wai saboda tsayin ta da ground softness, daga baya tsoro na dinga ji kada ta fadao amma ga mutane nan nata harkokinsu babu wani wanda ke da damuwa.

America ita ce inda mukaje bayan mun bar italy, tunda mukaje bama ya zama saboda wannan seminar din se yamma yake dawowa, so kawai se nake fita zuwa ground floor wajen wani pool ina kallon mutane ko kuma daga balcony inyi tsaye inata kallon gari. Seda yayi sati kafin ya kammalla aikin. Nayi wanka nasa wata off shoulder top thigh length. Gahina dana taje nayi parking dinsa in a bun na kwanta saboda bacci da nake ji. Cikin baccin naji massage with those soft palms of his. Idanuna da suka canja color na bude ina mitsitsika idanu nace

“Ka tashe ni”

Shima yadda nake turo bakin haka ya turo nashi yace

“Inata sauri nazo shi ne kike bacci”

Dariya nayi nace

“Tohm na tashi anything for me?”

Kanshi ya gyada yace

“Sosae ma, lemme bath and come”

Mikewa nayi na bi bayan shi nace

“I’ll help”

Murmushi yayi min muka wuce tare, it was enticing. A sweet moment actually! Munje famous golden gate of San Francisco, brigde din da ya hada Pacific Ocean da francisco peninsula. Ta mota mukaje naga brigde din da gate din. It was a wow mashaa Allah, kana tafiya ruwa a kasanka. Washegari muka koma mukai riding boat na kankameshi kamar zan fadar dashi, nan kuma kana kallon motoci nata wucewa akan bridge din. Kwana biyu muka kara se malaysia anan naga Twin tower gaba daya mun gaji musamman ni so kawai nake na ganni a nigeria. Seda muka huta sosae sannan muka taho nigeria cikeda farin ciki marar misaltuwa.

A Abuja muka kwana sannan da safe muka taho kano, a farawa layout anan gidan yake, yaya halifa shi ya dakko mu daga airport, tunda muka fito daga gurin screening na hangoshi dasu Addas da Maman Raudha tazo harda Hajara sister shi dake sokoto tana aure, dama ba taxo biki ba saboda basu kasar. Har seda na gaji da rungumar da ake min kowa se zuzuta yadda nayi kyau nayi fresh dani kana kallona kaga ta gaban goshin Kwaccido! 😆.

Motar Yaya halifa muka shiga akai sabon convoy na rakiyar amarya. Gidan bayan Ibrahim kunya yake, amma se an shiga ciki. Flat duplex ne me kyau. Dukkansu a waje sukai parking me gadin ya bude yana ta gaishe mu, ban manta adduar da Ummaah tace ba, nayi idan zan shiga. Ko ina ka kalla flowers ne wasu a cikin pot wasu a cikin pits. Ga motata anyi parking ga tashi guda biyu sun saka tawa a tsakiya. Anty hajara ta bude kofar parlon muka shiga . Awnnnnn Allah ya sakawa Abba da alkhairi, tabbas komai yayi. Parlon yayi kyau anan muka zazzauna anata wasa da dariya sunfi awa kafin kamar hadin baki suka tafi. Kowa na mana fatan alkhairi. Muna dawowa na cire mayafin jikina na nufi dining area inda Adda tace akwai abinci. Biyoni yayi yace

“Se ace bana baki abinci ai”

Murmushi nayi nace

“I missed Nigerian dishes”

STORY CONTINUES BELOW

“I see”

Ya fada yana zama gefena, masa na zuba masa da miyar taushe ni kuma na zuba dambu amma ya barni naci se hadewa akai. Gurin na gyara na wuce kitchen yana bayana kamar wani bita zai zai, nanma kitchen din subhannallah! Dakuna hudu ne, uku akai furnishing kowanne da kayan gado dayan kuma aka barshi aka saka kanan sofas da round center carpet, shelves da study table da lamps akai, se books dina da nashi a ciki. Ajiyar zuciya na sauke ina kara yiwa Allah godiya.

Washegari na samu na kira duk wanda yazo bikina, nasha tsokana kyaftun harda cewa zata kawo PT strip bata san lokacin period ma nake, shima da na fada masa yayi ta mita

“Yanzun Cara mia you’re telling me I’m not a good shooter”

Bakina na rufe ina dariya ya girgiza kai yace zaki sani. Kwana uku da dawowar mu ya kaini gida na yini. Dake mostly idan ina period se nayi ta kwadayi so kowa yayi tunanin ciki ne dani aikiwa nasha gata gurin Ummaah da inna wadda tsufa ya kara kamata. Da daddare yazo daukata Abba ya kara mana nasiha akan zaman aure sannan ummaah ma haka. Har mun shiga mota Asiya ta kawo min guntuwar fish sauce din da tunda nazo Ummaah ta min nake ci tace, wai Ummaah tace idan mun dawo zaayi min. Kallona yayi yace

“Me kikace musu?”

“Nothing sunyi tunanin inada ciki ne”

Na fada ina dariya, kanshi ya girgiza yace

“I’ll give you don’t worry, enjoy while it still last”

Sun comes up on this new morning,

Shifting shadows sunbird sings,

If this words couldn’t keep you happy,

I’ll do anything.

When you feel alone I’ll be your shoulders,

With the tender touch, you know so well,

Somebody once said it’s the soul that matters,

Baby who can really tell? when two hearts belong so well,

May be the walls will tumble,

Sun may refuse to shine,

When i say I love you, baby you gotta know…….

Muna idar da sallar asuba na hada mana pancake da tea muka sha muka dauki hanyar hadejia, kusan shi ne lokaci na na farko dana fara zuwa hadejia. Tun ina taya shi hira har bacci ya daukeni dan daga Gujungu bana tunanin na kara gaba, seda ya wuce yan leman sannan ya tasheni wai naga hanya, ni haushi naji ma shima bai kulani ba. A haka ya dinga nuna min wasu garuruwan har muka shigo hadejia ginsau birnin doki masu ruwan atafi kogin….. A GRA gidansu yake babban gida ne haka, an gyara shi, parking yayi muka fito muka shiga ciki, ko me zan tarar shi ne abinda nake ayyanawa.

Masu musu hidima sunata gaishe mu da murmushi a fuskata ina amsawa har yayi leading dinmu wani katon parlor da babu kujera ko daya se wani katon rug a malale a kasan, se kanana a me circle, me square an shimfida a guraren parlon. Wasu dattawa su biyu kana kallonsu kaga iyayen mijina a zaune se Raudha da wasu yara guda uku an zuzzuba musu tea a cups. Raudha na jin sallamar mu ta sheko da gudunta tana fadin

“Uncle Anty oyoyo!”

Hannunta na riko muka shigo kaina a kasa inata murmushi, matar ta mike da ta dan girma Ummaah kadan, shikam datijjon sanye da glasses yafi Abba. Da murnarta tana  fadin

“Yau ga ‘yata tazo”

Rungumeni tayi inata kokarin tsugunnawa tana dariya tace

“Sannu da zuwa ASMA’U FARA’YAR SHEHU”

Zama mukai nace

“Ina kwana Baba”

Yayi dariyar yace

“Alhaji ake cemin, idan kikace Baba se naji kamar ba yar dana haifa ba”

Kaina na gyada ko a iya haka aka tsaya naji dadi. Kafin wani lokaci an kawo mana abinci irin na asalin gargajiya, yan matan da suke riko suka zo ganina duk na kasa sakewa naci abincin seda Hajiya ta lura tace masa

“Yaya Asmau ba ta ci fa”

Kallona yayi yace

“To duk sun makalkale ta ta ina zata ci abinci, come on ku saketa hakanan”

Hararshi nayi su kuma kowa ya baje amma dukda haka se daki aka kaini naci Hajiya na fadin a ina aka taba ganin barebari da kunya. Nace tazo Kwalam ta gani😃.

Satina daya a nan shi kwana biyu yayi ya koma aiki se friday yazo muka tafi inata kewar su Hajiya da muka saba dasu sosae. Mun biya ta kwalam sannan muka wuce sokoto nayi kwana daya a gidan Anty hajara muka dawo kano. Kwanakin hutuna sun kare muka koma aiki.

Ranar monday da sassafe muka karaso, dama tuni kyauftun ta kwadhe min kayana daga dakina an maida shi gidanshi na cikin quaters din. Shi yayi furnishing gidan yayi kyua. Shiryawa mukai sannan muka fito gaba daya kunya nakeji wai ni ce me aure, se nayi dariya ya kalleni ya girgiza kai baice komai ba. Saboda yace wai har yanzun ni yarinya ce nidai jinshi kawai nake.

Ina parking kowa ya nufi office dinshi, ina shiga na cire hijab din jikina na saka lab coat nayi rolling mayafin abayar dake jikina. Glasses dina nasa na dauki ruwa nasha sannan na fito daga office din zuwa ward round. Ranar har gajiya nayi da amsa gaisuwar mutane kowa fatan alkhairi kawai yake min a haka ranar ta tashi na wuce gida danshi ya shiga cabinet meeting.

Ayshatuuuu

Aure ba abu ne me sauki ba, duk yadda na kwaso gajiya daga clinic ina shigowa gidan ko zama banyi ba na shiga daki na rage kayan jikina. Agogo na kalla naga uku harda kwata, wanka kadai zan iya yi na samu sallah a daidai. So kawai se na fada toilet nayi wanka yadda ya kamata. Ina fitowa nayi turare bayan na shafe jikina da humra. Atamfa na dakko wata English wax dinkin kimolly tamkar a jikina aka dinka ta saboda yadda ta yi min gyangyan. Sallah nayi hade da azhkhar lokacin hudu har tayi, Kitchen na wuce bayan na daura dankwalin wadda ba iyawa nayi ba seda Ikhrama da Suad sukazo gidanmu a kano suka kokoya min hade da turan tutorial videos shi ne nake dan catching kadan kadan. Na jima a tsaye ina tunanin abinda zan dafa amma na rasa, yanzun da ni daya ce da sede kawai na dafa noodles. Karshe kawai nayi irish porridge se na soya plantain. Ina cikin gyara kitchen din naji sallamar shi a parlor, hannuna na wanke a sink sannan na tsane da hand towel na fito yana zaune kan sofa looking all exhausted. Komawa nayi na dakko bottled water hade da tumbler na kawo masa tareda zama gefen shi ina massaging kafadarshi. Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya aje tumbler din yace min+

“Allah will bless you Ma’u ta, Kinyi kyau ta gurina”

Far nayi da idanuna tareda mikewa nayi juyi sannan nayi masa wink, hannunsa yasa ya kamo ni na fado jikinsa yace
“Baby!”

Peck nayi masa a kumatu nace
“Kayi wanka muci abinci ko?”

Kanshi ya gyada yayi daki ni kuma na koma kitchen dan karasa aiki na. Daki naje na dakko masa kaya, wani three quarter pant ne da kuma armless top red. A gefen gado na aje masa sannan na kara komawa dan aje abinci.
Seda nayi wata biyar da aure kamar bazan samu ciki ba, period dina smoothly yake zuwa yadda ya nunamin bai damu ba se na kwantar da hankalina tunda nasan auren ma ba karfi na bane ya bani Allah yayi lokaci ne yayi to hakan ma dai cikin da haihuwar shi ma lokaci ne. Ranar monday ce watana na bakwai kenan da yin aure. Da sassafe kamar yadda muka saba muka taho daga kano, gaba daya bana wani jin dadi kawai sede karfin hali saboda bana son ya fahimta. Muna daukar hanya bacci ya daukeni bani na farka ba seda muka zo Fanisau sannan na tashi. Zama na gyara tareda kallonshi nace

“Well done Sir!”

Dan kallona yayi yace

“Sleepy head.”

Sunan kenan na kullum indai nayi bacci. Kamar yadda muka saba a office dinshi mukai breakfast na saka lab coat dita na fita dan ranar surgery zamui ni dashi. Da sauri na hada kan yan team dina muka tafi ward round. Muna zuwa komai set kawai farawa mukai, kafin mu gama nayi matukar gajiya kuma it’s unlike me, dan se na jima ina aiki ban gaji ba, I’m the workaholic Shahada! Ina gamawa kaina kamar zai tsage saboda ciwo kwana biyunnan abinda ke damuna kenan ciwon kai. Nayi tunanin stress ne amma it seems kamar akwai wani abu.

Fanta nasa aka karbo min na zauna a station ina sha, anan na lura da kafata ta fara kumbura, kallon Metron nayi nace mata a gwada min BP na. Da kanta ta gwada min, na kalleta da mamaki kamar yadda take kallona with amazement tace

“Kin gani?”

Da damuwa a fuskata nace

“I can’t believe it, ya BPna haka?”

Kara gwadawa tayi amma reading is still very high, no wonder nake ciwon kai wani lokacin har ina ganin dishi dishi nayi tunanin ciki ne da nake tunanin ya shige ni yasa hakan. Wayata na ciro daga aljihu na jin tana ringing na dauka , Jewel ne

“Cara Mia ke muke jira”

A sanyaye nace masa ganinan haka na mike babu wani karsashi a tare dani na tafi OT, dukkansu sun shirya so ina shiga nayi changing muka fara aiki. Sosae na daure dan kada ya lura and God so kind bai fahimta ba har muka gama. A ciki na barshi naje na zauna nayi documenting komai sannan na fito daidai lokacin shima ya fito yana gyara hannunsa. Kallona yayi yace
STORY CONTINUES BELOW

“Ya dai?”

Kaina na langwabar nace

“Tired”

Kanshi ya girgiza yace
“You look worried muje”

Bayan shi nabi muka tafi office dinshi, seda na zauna sannan ya zauna gefena yace

“Ya akai”

“BPna ne yayi shooting”

Idanunshi ya ware yace

“Haba? How comes? Nawa yake reading”

180/110 fa”

Mikewa yayi yana girgiza kai ya sake gwada min, glasses dinshi ya cire ya zauna gefe na tareda cuddling dina jikinshi yace

“Baby, me yake damunki?”

Kaina na girgiza inajin wani rauni a raina nace
“Allah babu komai. I dunno!”

Se hawaye ya fara saukar min, rungumeni yayi yana bubbuga min baya har Seda nayi shiru dan kaina sannan yace

“To meye abin kukan kuma? Kiyi shiru kinji.”

Hawayena ya share min sannan ya dinga kwantar min da hankali a haka na hakura. Bai daura ni akan drugs ba kawai se yace bari a fara gano sudden rise din. Da muka koma gida ko girki banyi ba se kyaftun ce ta kawo mana dan da kanshi ya fadawa Lamin.

“To kiyi pt mana ki gani ko ciki ne”

Kyaftun ta fada min ina cin abinci, kaina na girgiza nace

“So nake se lokacin period din yayi idan banyi ba se nayi”

Shikenan muka cigaba da hira har dare seda ya dawo sannan ta tafi ita kuma yinin ymin dadi sosae dan na jima banyi irinshi ba. A hankali kuma se yau ya hau gobe ya sauka munata monitoring se daddare yace ya kamata muje ayi pt a gani yana tunanin matsalar daga ni ne. A gida mukayi abinmu and it was positive sede dukkan mu babu wanda yayi murna tunda kuwa yazo da matsala. Bayan munyi sallar ishai muka shiga cikin asibiti don yayimin scanning aikuwa ana yi, ya cemin

“Cara mia molar ne”

Kallon screen din nayi dama jikina ya bani shinkadai ne zai saka BP ya tashi at early pregnancy bayan munsan normally first trimester ana samun low BP. Tissue yasa ya goge min cikina yace

“Sannu kinji”

Kaina na gyada kawai na kasa cewa komai, molar gestation? Ni kuma da abinda zan fara kenan. A haka yana ta kwantar min da hankali mukaje gida. Yana ajeni ya fita se gashi ya dawo da ice cream. Kallon shi nayi nace

“Is that a bribe?”

Kanshi ya girgiza yace
“Not at all, inason naga kina murmushi ne”

Dariya nayi nace

“Gobe se naga Dr halima se ayi booking dina”

Kanshi ya gyada yace

“Nayi mamaki da kika samu molar bayan yafi zuwa mutane below 20years da kuma above 35years”

“A book kenan, Allah a gurinshi it doesn’t matter”

Kanshi ya gyada min yace

“Yeah!”

Molar gestation kamar ciki yake amma tumor ne but non cancerous sede idan baayi da gaske ba zai iya zama cancer din. Mostly yana faruwa saboda anyi fertilizing empty ovum ko kuma sperm cells biyu sunyi fertilizing ovum daya, yaron memakon 46 normal chromosomes zai samu 96 saboda an samu duplicate copy. Scanning ke nuna cewar wannan molar ne. Se terminating dinshi akeyi da zarar ansan shi dinne. Washegari bamu fita da wuri ba se wajen 9am muka tafi, office din Dr halima muka fara zuwa tana ganinmu ta mike tareda bamu guri muka zauna. Seda muka gaisa ya mika mata scanning dina , kamar patient haka tayi counselling dinmu sannan tayi admitting dina a Amenity. Kafin wani lokaci har yan dubiya sun cika na rasa inda zan tsoma raina. Da yamma tazo ita dashi aka kaini OT akamun suction evacuation. Lokacinda muka dawo anesthesia bata sake ni ba inata bacci. Se bayan isha sannan na farka lokacin shi daya ke zaune a gefena. Tashi nayi na zauna bayan ya taimaka min yana ta faman jera min sannu. Abinci ya kawo min bayan nayi brush naci sannan nayi wanka aka shigo serving drugs nurse din tayi sannan tayi mana sallama ta tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Ban tashi da wuri ba se wajen tara na safe, ko ina neat dana tashi so wanka na shiga na fito na shirya cikin abayar da ya aje min sea green se maroon dankwali na daura na zauna tareda daukar wayata na kirashi, yana dauka yace

“Kisa hijabi gamu nan zuwa”

Ya kashe hijab na janyo na saka tareda daidaita nutsuwata. Sallamar shi ta katse ni ya shigo fuskarshi da murmushi bayan shi duk manyan asibitin ne. Cikin nutsuwa na gaishesu sunata amsawa sannan suka dubani, my God kyauta dai na sha ta. Nayi musu godiya suka tafi sannan ya dawo tareda zama gefe na yace

“Na gaji Asmau”

“Ka huta kafin ka tafi”

Hannunshi ya kai jikina danjin temperature sede all normal se ya mike yace

“Bari na tafi kada na hana mutane dubiya”

“Aikuwa dai dan kowa yasan kana nan ba zuwa zaayi ba.”

Dariya yyai ya fice nasha dubiya kuwan, da yamma akai discharging dina hade da bed rest kawai se muka tafi kano. Se lokacin su Ummaah suka sani, washegari se gata tazo ranar kamar bakina zai yage dan murna bata jima ba sega Hajiya daga hadejia, i was super excited.
A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, kamar yadda Allah ya tsara mana. Rayuwa mukeyi cikin aminci da mutunta juna. Na fahimci sosae me rayuwa take nufi me aurenn shi kanshi yake nufi. Akwai lokuta da dama da nake jin kamar na bar gidan, musamman idan muka sami sabani naji kamar wuta ake zazzaga min but dake ni dashi are all matured minds haka muke hakuri mu dangana. Dadin a nawa yafi rashin dadin yawa, so babu abinda zance se godiyar Allah.

Shekara biyu nayi inata bari seda nayi planning na five months jikina ya huta sannan na samu ciki. Zo kuga tattalli dama lokacin na gama course dina akan family medicine so kawai se na zama a consultation room nake. Munyi rainon ciki babu kakkautawa wayaga dan Doctor da Doctor? Yasha kulawa scan dinmu na farko ya bani mamaki, it shows triplets yayi ta murna ni kuma ina kuka saboda ina tunanin ta ina zan fara wannan rainon, seda ya gama murnarshi kafin ya zauna yana ta bani baki da nuna min CS ne ba wani abin ba. Aikuwa dake Allah shi ne Allah, babu wani pregnancy complications banda kumburi shi kenan, ina seven months inna ta rasu. Nayi kuka kamar me seda nayi sati a kwalam kafin na dawo, to rayuwar duka nawa ce ma.

Da kyar na kai 36 weeks babu pain ko daya aka ce mana kawai ayi CS din zaifi, tare dashi aka shiga aka kaimin sede yana gefe na saboda ba GA bace idona biyu. Ana cirowa ana weighing ana miko masa, first one din namiji ne se mata biyu. Mashaaa Allah kawai. Ana kaini na huta kamar kasa mutane naga soyayya ko nace triplets dina sun gani. Kyaututtuka kam har seda na daina gane wannan na waye. Ranar suna ya saka musu Muhammad, Khadija da A’isha. Ba sunan kowa bane se gidan annabi da ahalinsa.

Bayan shekara uku sun girma, duk wanda ya gansu yana shaawarsu not knowing ni irin wahalar dana sha. Shekararsu biyu na dage seda aka kaisu school saboda na gaji, kullum kaina kamar zai tsage ga na patient ga nasu, shidai sede ya kalleni yace I’m his everything, he can’t imagine life without me.

Shekararsu biyar muka tafi Ukraine, dukkanmu karatu ya kaimu. Tun daga kansu ban kara samun ciki ba saboda nasan uterus dina is very weak idan na matsa mata zaa samu matsala gwara na huta da kyau. Asabar ce weekend ne, tun sassafe na tashi na shiga kitchen, it’s Saturday kowa yana da damar da zai zabi abinda yake son yaci, wannan shi ne yancin dana basu dukda I’m a very strict mother amma kuma ina wasa dasu dan idan muna wasa bazaka ce ni ke fada ba. List din na duba, Muhammad nasan noodles, Khadija na son strawberry pancake ita kuma A’isha tace scramble egg da bread zataci. In a jiffy na harhada komai, Daddy dani we always have same choice saboda our hearts and soul are connected komai hakan ke so.

Gyara gidan nayi sannan nayi wanka har lokacin tara da rabi basu tashi ba, seda na shirya sannan na tada daddy ko ta kansa ban bi ba na tafi gurin yarana, yana ta mitar wai na daina kula dashi nidai bance komai ba se dariya naje, ina zaune sukai wanka na shiryasu muka fito daidai lokacin shima ya fito, da gudu suka karasa suna fadin
“Daddy!”
“Kiddos”

Dariya nayi tateda daukarsu hoto sannan mukai breakfast, muna gamawa aka assignment seda suka gama sannnan na kunnna musu cartoon muka fara namu assignment din. Mun kammallla na kalleshi kamar yadda yake kallona, i imagined him a matsayin mijina, idanuna na lumshe ina tuna rayuwata from lokacinda ta rikice bayan kammalla preclinicals dina, nayi hakuri gashi kuma naci riba, yaran na kalla sunata dariya so peaceful hakan ya kara kwantar min da hankali. A wannan gabar ina kira ga duk wacce batayi aure ba kada ta damu lokaci ne, idan yazo se anyi. We all believe aure habo ne haka wasu kance layin markade ne idan yazo kanka se an markada. Nawa suka aje bucket dinsu aka barar, wasu aka sace, wasu aka saka musu gwalagwaji but still seda aka markada. Ina fatan dukkan yanmata zasui koyu da rayuwata su saka ransu the biggest thing will happen, the patient dog eats the fattest bone!

Da daddare muna tsaye ni dashi a gaban balcony, yaran sunyi bacci bayan mun gama video call da yan nigeria, idanuna na daga na kalla sama yadda taurari suka cika sunata haskawa yasa nace subhannallah tareda tabo shi nace

“Come on ina son daya”

Kalla yayi sannan ya kalleni yayi murmushi nace

“Ka kamo min mana”

Kallona yayi cikin idanu, wasu molecules suka samu damar ratsa lens din har retina inda ya tafi kwakwalwata ya tarwatsa komai, shi kadai ne a duniyata no one exist again se shi.

“I’ve already got my star here”

Ya fada yana nuna ni, rungumeshi nayi na fara bashi wani sensual and seductive kiss, da kyar muka koma daki and he gave me something as sweet as honey!

Alhamdulillah!!!

This piece of work is dedicated to any unmarried lady or a spinster, Allah will make it happen so don’t lose hope my dearies. Wanda Allah ya kaddara naku ne suna nan zuwa and they will for sure take you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *