FARHA
CHAPTER 1
Yarinya ce qarama da bazata wucce 14 zuwa 15 ba tana tafe cukin uniform din Islamiyyar ta da yasha guga tana tafe tana yauqi tana yatsina kamar wata macijlya “Farha! Farha!! Ke Farhana wai ba mgn ake miki bane kika share mutane” tsayawa tayi cak daidai wani dan gulbi da ruwan damuna ya tare a gefan titin ta tabe baki zatayi bala’i kenan wata zindimemiyar mota qirar Jeep tazo giftawa kawai bisa tsautsayi taji ruwa facal a jikinta saurin kallon jikinta tayi tare da cewa “ kam ubancan wlh yau zanyi rotse dagowar da zatayi taga motar tayo ribas a hankali, wawurar wani dutsi tayi ta wulwula kawai sai saman glass din motarji kake tatsatsaarr da sauri mutun biyu da suke cikin motar suka fito kasancewar gurin babu yalwar mutane sosai yabawa dayan ma damar fitowa daga motar ya tsaya
jikinta ya zuba musu ido.
Daya cikin mutanen ta sanya hanu ta cukuma tana surfa bala’i tana cewa“ku wadannan irin unliterers ne kuna tafia kamar makafl bakusan haqqin hanyaba balle me tafia a qasa daqiqan banza daqiqan wofi wannan ma ai zalinci ne yanzu kunjamin yauma sainayi wankin uniform bayan…” saukar mari taji a kuncinta tayi saurin dafe gurin tare da cewa”Allah ya isana mugu azzalumi kuma wlh bazan fasa fadaba ku jahilai ne baku da ilimi Kona sisi” sake daga hanu yayi zai yarfa mata mari can a bayansu taji ance “Na’im karka qara mace ce fah kuma yarinya qarama kuzo mu tafi” juyawa tayi ta kalleshi gabanta taji ya fadi amma saboda bala‘in da yake cinta haka ta taka tana daga hijjab dinta saboda tsoron kada ya manne mata a jIki ta qarasa gabansa ta qare masa kallo a to z sannan tayi tsaki tace.
“Aikin banza waishi mutumin kirki daka kyaleshi ya kasheni ai yagani in zai sha kaima din baka wucce in ketaka ba balle shi da qilama taimakonsa kayi ka rage masa hanya dubeka kamar aljani ka wani tara Suma a kanka kayi mata shampoo wai a dole saika zama India toba India ba niko bayahude zaka zama Farha bata da kaico dalla malarn kauce na wucce” kaucewa yayi ya bata hanya saboda tsananin mamakin jarumtar yarinyar tunda yake a cikin rayuwarsa babu namijin daya taba yimasa rabin wannan tsagerancin balle mace
macen ma yarinya qarama irin wannan jaririyar yar.
Damqe hanunsa yayi ya bita da kallo harta shiga wata kwana ya daki saman motar yace “like this girl” wanda ya ambata da Na‘im dazu shine ya rusuna yace “ Allah yaja zamaninka daka barmu mun canza mata halitta ai irin wadannan yaran basuda tarbiyya k0 kadan basusan mudin suwaye bane da mun gwada mata qarfin iko mun gwada mata bata wucce kucakar baiwa ba a sashinka data shiga hankal….”
Daga masa hanu yayi ya dubi na gefensa yace cikin murya mai nuna isa da qarfon iko
“Shahid kaje ka nemo mama Inda gonarmu take tabbas zamuyi shuka a gunnnan” dagowa Shahid yayi da mamaki zaiyi mgn ya daga masa hanu tare da nuna masa hanya, rusunnawa yayi yace“angama yamai Bauchi da jama’ar cikinta dolene nayi biyayya wa umarninku” daidai lkcn wata motar tazo suka shiga suka tafi shikuma Shahld yabi bayan sauran yan matan guda biyu saida yaga zasu shiga wani gida ya tsayar dasu suka juyo a tsorace babu alamun rahama a fuskarsa yace “wannan mara kunyar yarinyar nakeson sanin wacece Ita
kuma inane gdansu?”
Kallon juna sukayi duk a firgice suke dayarce tayi qarfin halin cewa“qanwarmu ce sunanta Farhanah nan…uhm nan shine gdanmu amma don Allah ka taimakemu ka rufa mana asiri kada ka fadawa babanmu wlh duka zaiyi mana Farha ta saba jamana duka ka tausaya mana don darajarwannan watan da muke ciki” ganin yanda suka rikice dinne yasashi juyawa ya tari sahu ya nufi inda zai isar da saqonsa zuciyarsa cike da takaici tare da tambayar kansa meyene dakilin da yasa Mai martaba HAFEEZ yasashi bin diddigin yarinyar a zuciyarsa yace “Allah yasa dai ba wani makircin zai shirya mata ba saboda yasan ta tabowa kanta bala’i duk da a rashin sani tayi itama qila da tasan wayeshi da batayi masa ba”
Tana shiga gdan tajefar da hijjab dinta ta saka kuka Ummah da Mama ne suka fito daga dakin da suke kallo sukace“To yau kuma wa kika tabo ya tabaki uwar rigimammu”jikin Ummah ta fada tace “wasu yan iska ne suka batamin uniform dina kuma wlh bazan wanke ba ke zaki wanke ko Mama ai dama saida nace bazanje ba kuka dage sai naje yanzu ga irinta nan” tsaki Mama taja tace “kyaji dashi wlh” shigowar sauran yammatan ne yasasu juyawa suka kalleta dayar tana shigowa ta jefar da jakarta ta nufi bandaki da gudu dayar kuma ta zube tana fadin “yau mun shiga ukun mu a gidannan Allah ya isa tsakanin mu dake Farha ke kullum saikin janyowa mutane bala’i yanzu gashi har biyomu daya yayi yana tambayar mu sunanki da gdanku na tabbata Baffa zasu fadawa shi kuma ya kamamu ya
zanemu bamuji ba bamu gani ba”
“Uhm ai dama na sani wlh yau bazata jamuku duka ba Anass zai dawo shi zansa yaci qaniyarta tunda Ita bata da kunya” Rahina ce ta fito daga bandaki ta ajiye butar ta koma gefe tayi tagumi tana zubar da hawaye tace “ni takaicina ma Rahmah Farha batasan suwaye tayiwa rashin kunya ba wlh motar data fasawa glass number Emir palace ce da ita ni addu’a ta Allah yasa ba dan sarki bane yasa a koremu daga garin nan ba Baffa baijiba bai gani ba” murguda mata baki tayi tace “idan dan sarkin ne ya tsireni da tsinken tSIre banza matsoraciya kawai toni ko sarkin ubansa zan…” faff taji an zabga mata mari tare da rufeta da duka ehu ta rinqayi tana neman taimako kowa daki ya shige da ita bai qyaleta ba saida yayi mata tllis tayi laqwas sannan yace “duk abinda kikayi ina kallonki to wlh tallahi duk abinda ya faru dake ke kikajawa kanki tunda kika tabo gidan sarautar garin nan dama wani kika taba da sauqi amma fah Mai martaba HAFEEZ da kansa kikayiwa rashin kunya harda
zaginsa to ki jirayi sakamakonki kuma saina sanar da Baffa komai”
Qanqameshi tayi cikin kuka tace”don Allah don Allah Yaya Kada ka fada masa hakama na daku nayi Iaushi wlh na daina har abada bazan qaraba tureta yayi yayi ficewarsa yana fita ta saka sabon kuka tana cewa“kuma wlh wayo nayi maka bazan fasaba gobema idan naganshi saina jefeshi shege azzalumi kawai wayace ya batamin kayan makarantana da shegiyar motarsa…” saurin yin shiru tayi ganin dawowar Yaya Anass din ta kama goge fuska
kallonta yayi yace“ me kikace?” Kada kanta tayi tace “wlh godiya nayi maka ba zaginka
nayi ba” kwafa yayi ya shige Clkln gdan.
Washe gari da wuri ta tafi makarantar yau batabi ta hanyar da sukabi jiyaba ta qofar fada tabi ita da qawarta Binta suna tafe suna hira hira fada fada saboda Farha bata daukar raini k0 kadan yanzun ma naSIha Binta take mata akan abinda tayijiya amma ta hauta da masifa dole tayi shiru daidai makarantarsu ta hangijerin gwanon motocin Emir palace din sun fito daga gdan sarki tsaki tayi tace“ga shegunnan sun fito nifa Allah na tsanesu” tana fadin haka ta shige ajinsu, tana tsaye gaban malamin nasu tana bada hadda saida ta gama tsaf sannan ta koma ta zauna zamanta kenan wani mutum ya shigo da sauri ya qarasa gaban malamin nasu batasan me suka tattauna ba taji malam Nuhu yace “Farhana Usman Giyyade kije ana nemanki a waje” banza tayi dashi kamar bataji abinda yake fadaba, saida ya kuma magantuwa yace “Farha kefa nakewa mgn ko baki jinane?” Miqewa tayi tana qunquni ta fita mutumin yana gaba tana biye dashi a baya har suka fito tsayawa tayi turus gaban wata zundumemiyar mota qirar Annaconder ta jima a tsaye kafin taga anyi qasa da glass din baya wani mutumin sabanin na dazu ya leqo yace“zaki iya amsa kiran Mai
martaba?”
Yanda yayi mgnr da sigar tambaya yasata dariya ta bude baki zatayi mgn sai kuma ta tuna da jibgar da tasha jiya gurin Yaya Anas takawa tayi a hankali harta isa daf da qofar motar ta tsaya bude mata akayi da zunmar ta shiga taja da baya da sauri tace “aa kunga ku dakata ni banason wayon satar mutane saboda wani kiniblbi harda wani budemin mota yo wannan motar da tsautsayi na shigeta aisai buzuna” matsawa tayi ta leqa idonta yayi arba da wanda yake Clkin motar jlkinta ne ya dauki tsima ganinsa zaune a hakimce ya dora qafa daya kan daya yasha rawani irin nasu na sarakai mai kunnuwa biyu shaidar dai da gaske sarki ne qara kallonsa tayi tanaso ta ganeshi kamar na jiyannan wanda yasa qananan kaya yace a dena marinta amma kuma kamar bashi ba miqewa tayi da sauri tayi qasa da kanta tace “am..en gani” tunda tazo gurin ya zuba mata ido yana mamakin fitsara da rashin tsoron yarinyarji yayi tana qara birgeshi da shiga ransa ya rasa meyasa tun jiyan daya
ganta ya kasa samun nutsuwar zuciya.
Daga mata hanu yayi alamar jinjinawa ya dubi wani cikin mutanen dake motarya matsar da kunnensa daidai inda yake dagowa yayi yace “angama sarkin duniya” dubanta dogarin yayi yace “kina iya tafiya” tabe baki tayi ta kalleshi tace “hmn Allah ya kyauta mutum ko zafi bayaji ya wani nade fuskarsa” dogarin ne ya daka mata tsawa yace“ahir yarinya saita bakinki kafin fushin Mai martaba ya sauka akanki” daga masa hanu yayi ta murguda baki tayi gaba tana harararsa” duk da fuskarsa a rufe take amma saida kumatunsa suka lotsa tsiwar yarinyar tana burgeshi kowa tsoronsa yakeyi hauwa matarsa ta aure tana tsoronsa bata iya fada masa komai amma ita babu ruwanta duk abinda taga dama fada masa takeyi daga jiya zuwa yau wani nishadi yakeji saboda a rayuwarsa yanason ya samu wanda zai rinqa sanyashl dariya da nishadi kuma ya lura da gaske yarinyar comedians ce.
Labewa tayi har saida taga tashin motar sannan ta koma ciki ta zauna gabanta naci gaba da faduwa “to waima meye dalllin dayasa yazo ya tura a kirata kuma ma wayene shine kodai da gaske shine dan sarki Hambalu wanda bayan mutuwar sarkin ya zama sarki? Kai bashi bane ba da shine yanda ake fadar izzarsa da qarfin ikonsa aida yanzu yasa anyi guntuwa guntuwa da namanta, tabe baki tayi tace “Hmn sudai suka sani saji da gulmarsu munafukai kawai, da aka tashesu ma su biyu suka tafi suna tafe tana bawa Binta labarin irin
tsagerancin da tayima mutumin daya watsa mata ruwan kwata yau tayi dariya tace
“kuma kinsan wani abu Binta har rawani yakeyi Ina tunanin dai wani mai muqamin sarautar ne tunda yanzu dama ance fadar ta zama ta yara sune suke mulkarta ance shima sarkin ba wani babba bane bai wucce 37 year’s ba” murmushi Binta tayi tace “kinsan babar su Ammi tana aiki a gdan sarautar wlh ance bashida kirki ko kadan gashi dajin kan tsiya da izzah baya karbar uzuri sannan itama matarsa batada mutunci amma mugun tsoronsa takeji bata iya motsin kirki idan yana gdan shekararsu shida da aure amma ko batan wata matarsa bata tabayi ba kuma ance matsalar a jikinsa take kinsan sarakunan nan da kauce hanya wai yanzu yarinya qarama akace ya aura wadda bata fara al’ada ba kuma wai har suffofin yarinyar an fada masa ya zana hotonta yananan qato a turakarsa manyan bayinsa da suke shiga bangaransa sune sukasan wannan sirrin itama maman Ammi jitayi suna hirarta labe” Dariya Farha tayi cike da mugunta tace “shege Allah yasa kada ya samu Allah yasa ranar da zai ganta ita kuma ta mutu basai muga ta tsiya ba” dariya itama Binta tayi tace“wlh Farha ke muguwa ce” murmushi tayi tare dayin qwafa tace “nifah na tsani sarkin nan duk da bansanshi ba saboda rashin mutuncinsa yayi tambari a garinnan.
Hmm yanzu fa aka fara