FARHA
CHAPTER 11
Sannu sannu lkc yake tafiya cike da abubuwa kala kala na dadi da sabanin haka lamarin Farha da mijinta sai son barka inda bangarenta da abokiyar zamanta abin ba’a cewa komai kullum cikin bala’i suke duk yanda Farha takai da kawaicinta dason ganin batayi abinda zai zama bacin ran Mijin nasu ba abin yaci tura ita Farha tunda suka dawo batada gurin zuwa tana part dinta saboda jikinta da yayi mata nauyi saidai qannan mijin nata su shigo mata, sunsha bikin Aminiyarta da yan uwanta duk wani abu da akayi a wajen bikin itace tayi Mai martaba shine yayi mawa yan uwanta duk wani abu da uba yakeyiwa yaya wannan abu ba qaramin martaba da qaunarsa ya qara a zuciyar Farha ba.
Lokacin da cikinta ya shiga watan haihuwa ya hanata fita ko ina a gdan sarautar komai da ake buqata ya siya wani siyayyar harda ta shirme abinda ya qara tunzura Amnah da uwarta Sogiji a gefe guda kuma Waziri Iliyasu shima hankalinsa ba qaramin tashi yayi ba lkcn da yaji labarin samuwar cikin na matar Sarki Hafeez nan fah kowa ya baje qullin mugun nufinsa akan Farha da abinda ke cikinta.
Yau da sassafe Amnah ta tashi kasancewar a bangarenta yake ta shirya cikin kwalliyar data dade batayi irinta ba ta nufi dakinsa yana kwance yana chart da sahibarsa Farha ta shigo ta jima tsaye a kansa kafin ya ankara ya dago ya kalleta taji ciwon ganinsa yana abinda ta tsana amma dake tatace ta kawota sai tayi ajiyar zuciya tace “dama nazo na fada maka zanje taaziyya gdansu qawata Zahra ne” haka kawai yaji gabansa ya fadi ya ajiye wayar ya kafeta da ido yanason gano gskyrta kafin yace “amma baki fadamin ba sai yanzu” ajiyar zuciya tayi tace “ka manta kawai Mai manaba abunne yazomin bakatantan don Allah karka cemin aa” tabe baki yayi yace “shikenan saikin dawo hannu ta miqa masa yasan me take nufu don haka ya nuna mata inda kudin suke dama hakan takeso ta wucce gurin ta bude ta dauki raffers ta dubu dubu guda uku ta jefa a jaka ta fice tana wani murmushi na mugunta daganan bangaran Hajiya Sogiji ta nufa ta tarar da ita ta shirya tsaf suka dauki hanya zuwa wani qauyen Bauchi gurin surquqine sosai dole sai parking sukayi suka nufi cikin jejin a qafa, suna zuwa gurin gaban Amnah ya fadi suka kutsa suka shiga wani mutum ne yana zaune tumbur babu komai a jikinsa sai wani dan kamfai suka zauna ya dubesu yana wani murmushi yace “munsan da zuwanku dama an sanar damu mugun nufinku matsala ce akan kishiyarki da take dauke da ciki haihuwa ko yau ko gobe to mun duba mun gano cewa tabbas gobe zata haihu zata haifi da namiji babu makawa dannan saiya taka doron qasa”
Dagowa Gimbiya Amnah tayi tace “na shiga uku na boka ka taimakeni wlh idan yarinyar nan ta haihu a gdannan na kadai ni ko kasheta ma ya kama ayi ita da tsinannan cikin dake jikinta” Hajiya Sogiji ce ta cafe da cewa “boka ko nawane zamu biyaka a lalata rayuwar Sarki Hafeez da shegiyar matarnan tasa a kashe dan da yake kumbura kai zai samu kowa ya huta”
daga mata hanu yayi ya shiga surkullensa dagowa ya kumayi yace “zamu batar da ita a zuwa safiya duk rintsi bazata haihu a cikin gdannan ba” wata laya ya dauko yayi surkullensa ya miqawa Amnah yace “kisan duk yanda zakiyi ki binne wannan a inda kikasan Mijinku zai tsallaka wannan kuma garin mantau ne ki badashi ta kowacce hanya duk wani abu daya shafi garin Bauchi zai goge a kwakwalwar ta sauran bayanin zaki gani da idanunki” yana gama yi musu bayani suka sauke masa damman nairori a matsayin
tukuicin aikinsa suka tafi shikuma ya duqufa nasa aikin.
Basu koma gdanba sai bayan magrub suna shiga kai tsaye Amnah ta nufi part din Farhan ta jima tana kiranta amma shiru bataji ta amsa ba saboda haka tayi maza taje qofar da zata sadata da bangaren Mai martaba ta daga carpet din gurin ta jefa yar qaramar layarta fice, tana fita sukuma suka shigo ita dashi sunkutarta yayi ya nufi dakinsa da ita tana dariya tana zillewa shima dariyar yakeyi yace “yau dai a taimakeni a bani na taba kusan sati guda idan nazo sai a langwabe ace babyna ya hana lfy gashi shikuma yaqi fitowa sai wahalar min dashi kikeyi” murmushi tayi ta saqalo wuyansa tace “ wato nicema nake wahalar dashi saboda adalcinku yayi yawa k0?” murmushi yayi ya kwanta tare da kara kunnensa a saitin cikinta yanajin yanda babyn cikinta yake motsi dariya yayi sosai yace “motsi fah yake Queen har fa mgn yayimin wai na qara hqr ya kusa fitowa” ita kanta batasan sanda ta fashe da dariya ba ya zauna yayi tagumi yana kallonta ganin irin kallon qurullah da yakeyi mata yasata hura masa iska a idonsa tace “wai ya da kallo hakane?” Ajiyar zuciya yayi ya kwanta ya kamota jikinsa sosai yace “kawai qaunarki ce Farha duk matan duniya kinfisu kyau kin fisu nagarta kuma kin fisu dadi kin fisu iya kula da miji wlh Farha dana rasaki gara na rasa tawa rayuwar zaifimin sauqi…” rufe masa baki tayi tace “tunjiya nakejin gabana yana faduwa Mai martaba don Allah kada ka rabu dani kada ka manta dani a rayuwarka ka rayu da qaunata a zuciyarka inasonka mijina…” ta qarasa mgnr cikin kuka saurin sanya harshensa saman kuncinta yayi yana lashe hawayen nata tare da hade bakinsu yana tsotsa yana girgiza mata kai alamar ta daina kukan bayaso, hadiye kukan tayi ta biye masa suka fara faranta ran junansu suna yiwa juna alqawarirrika kala kala saida dare ya raba sosai sannan bacci barawo ya sacesu suna manne da juna kamar wadanda zasu shiga jikinjuna baccinsa mai dadi yakeyi inda itadai farha nata rabi da rabine data rufe idonta sai taji kamar an tsikareta ta tashi haka tayi wannan kwana na rashin kwanciyar hankali dama taga baccin yaqi kawai saita miqe ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro alwala ta rinqa jera nafilfili
rabin addu’ar ta akan sauqin haihuwa ne da samun yaya na gari.
Kiraye kirayen sallar asuba ne ya farkan da Mai martaba yana tashi ya ganta zaune saman sallaya yayi murmushi ya shiga toilet yayo wanka tare da alwala ya fito lkcn tana rakatainulfajir yana yabawa juriyar yarinyar akan ibada tunda yake da Amnah baitaba ganin tayi sallar naflla ba farillar ma saiya takura mata takeyi idan ba hakaba saitayu sati biyu batayi ba wannan issue din ma na ibada ba qaramar matsala ya rinqa basuba saida taga da gaske zaiyi out da ita akan wannan sannan takeyi shima sai taga yananan idan bayanan batayi,
Yana gama shirinsa ya matsa kusada ita yayi rakatainulfajir din shima sannan ya fita zuwa masallaci bayan ta idan da sallah ta miqe ta gyara masa dakin ta kunna turaruka sannan ta nufi nata dakin ta fada wanka ta fito ta zauna gaban madubi ta soma tsara kwalliyarta ta zuba gwala-gwalai ajikinta hannu wuya yatsu hatta agogon hanunta shima gold ne tayi kyau na fitina sai daukar ido takeyi wata doguwar rigar wani tsaddadan yadi tasa sky blue ta daura dankwalin ta simple styles ta dauki takalmi kalar kayan rufaffe sannan ta fito parlour wata irin muguwar yunwa takeji saboda haka dinning table ta nufa an jera komai yanda ya kamata ta fara budewa tana dubawa idonta yakai kan kunun tsamiya tayi ajiyar zuciya tare da sawa aka zuba mata shi tasha sosai sannan taci Chips din da akayiwa miyan kwai taci sosai ta miqe ta koma dakinta tana shiga taji an qwala mata Kira gabanta ya yanke ya fadi ta juya tana dube dube‘ bataga kowa ba. ‘
Jitayi kamar ana fuzgarta ta bude wadroop dinta ta shiga loda kayanta a trolly babba tare
da bude wani akwati ta dauki manyan sarqoqinta guda uku daya diamond ce biyu gold har ta juya zata fita ta dawo ta janyo wata loccar ta dauki kudi da wasu hotuna da kayan baby masu kyau da tsadar gaske ta zuba a ciki ta rufe taja zuwa harabar gdan tanayi tana dube‘dube tana hawaye tayi wuf ta fada mota ta rufe glasses din da yake baqine tayi baya a guje tana jin kamar ana fuzgarta bata sami matsala ba sarakunan qofar sukayita bude mata tana fita a zatonsu Mai martaba ne saboda itadai bata taba daukan mota ta fita ita kadai ba duk da sunsan motar tace saboda number motar sunanta QUEEN FARHA zuciyarta quna takeyi sosai tana tafasa jitakeyi dama ta bude ido ta ganta a wani garin ba Bauchi ba kai tsaye Tasha ta nuda saboda bazata iya dogon tafiya a motaba tun daran jiya takejin mararta na murdawa darewa aka rinqayi ana bawa motarta hanya harta shiga cikin tashar tayi parking ta fito tana rarraba idanu duk a firgice take kamar daga sama taji ana Kiran “Kano Kano Alh kanone Kaduna Hajiya zo mu tafi ciko mutum daya” dan kamasho din tayiwa mgn tace “can zani ” tana fada masa haka aka fara loda kayanta cikin motar saida suka kwashe komai sannan ta kulle motarta matsa kusa da wani dattijo mai facin taya tayi masa sallama dagowa yayi ya kalleta ta miqa masa key din tace “baba na fito ne zani unguwa kuma naji bazan iya tafiya da mota ba nayi waya drive zaizo ya karba”
Hannu tasa ajakar ta dauki biro da takarda tayi rubutu a gajarce ta miqa masa tare da zaro kudi masu yawa ta bashi ya karba yana zuba mata gdy tajuya ta shiga motar lkcn da aka miqo mata book record din ta tashi cike sunanta haka kawai tasa Hanah Bala number waya kuwa qin sakawa tayi dole haka motarta daga suka dauki
hanya motar na tashi ta fashe da wani kuka me ciwo da batasan dalilin yinsa ba kowa a motar kallonta yakeyi da mamakin kanta tayi da qarfi tanason tuna wasu abubuwa game da ita amma ta kasa tafiyar awa uku da rabi ta kaisu Kaduna a tashar kawo Kaduna motar tayi parking kowa ya fito ya kama gabansa amma banda ita da ta rasa abinyi saida kondastan ya leqo yace “hajiya an sauke miki kayanki Napep din ina zaa tsayar miki?” Wasu mutane ne da suke wuccewa taji sunce Barnawa da sauri tace “Bar..yauwa Barnawa” juyawa yayi ya nemo Napep suka sanya akwatin ta yunqura ta fito da qyar saboda mararta data daure tam kamartanajin fitsari daqyar taja qafarta ta shiga Napep din yaja suka fita daga tashar suna tafe tana cije lebe azabar da takeji na qaruwa sunyi taflya mai tsayi cikin Barnawa Layout ganin suna shirin fita dan Napep din yace “hajiya a Ina zaki sauka ne?”
Daqyar cikin muryar azaba tace “wayyoh… Anan zan sauka” parking yayi ya sauke mata akwatin ta bude Jakarta da qyar ta zaro 1k ta miqa masa yace “banida canji Hajiya ” tace “jeka kawai” lkcn da take durqushewajikin wani gda riqe da cikinta tana fitar da hawayen azaba tana ambaton “innanillahi wa’innah ilaihir raji’un, La’ilaha illah anta subhanaka inni daga gdan dake kusa da ita har motarta wucce sai kuma sukayo baya da sauri wata farar mata kakkara da wani mutum shima sai matashiyar budurwa da bazata wucce sa’ar Farhan ba suka nufota magidancin yace “Subhanallahi Hajiya ku taimaka kamar labour takeyi fah” da sauri suka kamata suka sata a mota shikuma yaja jakar kayanta yasa a but suka figi motar a guje suka nufi wani private hospital dake kusa da unguwar, suna shiga aka karbeta duk da babu katin awo aka shiga da ita labour room lkcn ta gama gigicewa ta fita daga hayyacinta unguwar da bayin Allan nan basujeba kenan, har dare tana abu daya ganin hakanne yasa magidancin ya tafi gda ita kuma matar tasa da yarinyar suka
zauna a gurinta kafin ya wucce saida ya biya komai ya sayo duk wani abu da yasan za’a buqata harda kayan baby.
Abu kamar wasa saida ta kwana tana labour har sun yanke shawararyi mata aiki Alh harya sanya hanu wata Nurse ta fito da gudu ta kira likitan yana suwa ya tarar kan yaron ya danno hamdala yayi tare dayi mata wata allura sannan yasa safa ya zaro mata sankacecen danta kyakkyawan gaske qato dashi tabarakallah danna mata ciki suka rinqayi har suka samu mabiyiyar ta fado sannan suka kwance mata jinin sukayi mata dinki saboda ba qaramar qaruwa tayi ba bayan sun gama komai suka fita suka sanar da wadanda suka kawota dukkansu suka shigo dakin matar ta dauki yaron tana hamdala tare da mannashi ajikinta ta share hawaye ta miqawa mijinnata shi tace “karbeshi kasa masa albarka kayi masa huduba Alh Allah kadai yasan wayeshi amma tabbas yarinyar nan badaga qaramin gda ta fito ba akwai ayar tambaya akanta” murmushi yayi yace “nima na fahimci haka shiyasa tunda wannan tsafaffuyar tsuntsuwarta fado cikin gdanmu na fada miki zamuyi baquwa kuma kinga gata kuwa tazo wlh Momy abinda yake faruwa a duniyar nan ba’a cewa komai yanzu idan kika bibiya bai wucce akan dukiyar mijinta ko wani matsayinsa aka kadota duniya ita da abinda ke cikinta ba kuma fah babban tashin hankalin an goge Mata lissafin kwakwalwar tsaf babu wani abu da zata iya fada miki daya shafi rayuwarta ta baya”
Kada kai momy tayi ta share hawayen idonta ta qarasa gaban Farha dake kwance tana baccin wahala ta zuba mata ido tana qare mata kallo qaunarta na shigajikinta zama tayi ta kama hanunta tana murzawa a hankali Alhj ne ya matso kusa da ita ya dora mata jinjirin a cinyarta yace “mu bari sai mahaifiyarsa ta farka sai ta zabi sunan daya dace dashi ta fada asa masa” jinjina kai Mommy tayi tace “hakanma yayi”
Daidai lkcn yarsu Maryam ta shigo ta saki wani ihu tana tsalle tace “ ta haihu momy? Wow amma naji dadi wlh momy inason baby” hannu tasa ta dauki yaron ta kare masa kallo tace “wow kyakkyawan yaro wannan balarabe ne babansa duk yanda akai ko kuma bature gsky yaron ya cijeni sosai”
Farkawa tayi tayi miqa hade da salati ta fara bude idonta a hankali ta saukeshi akan mutanen dake dakin tabayi musu kallon son tuna inda ta sansu amma ta kasa tunawa miqewa ta fara qoqarin yi sukayo kanta dukkansu sunayi mata sannu, kai kawai ta daga musu Momy da da Daddy suka taimaka mata ta zaunajinta yayi wani iri ta bude idonta akan Maryam da jaririn da yake hanunta shafa cikinta tayi da hanunta taji babu komai murmushi tayi wanda yaja mata wata kwallah me zafl ido ta zubo mata ta miqawa Maryam hanu ta miqa mata yaron ta karbeshi ta zuba masa ido tanason tuna da wanda jaririn yake
mata kama amma ta kasa “Dana ne wannan?” ta tambaya tana rungume shi a jikinta.
Hmm