FARHA CHAPTER 13

FARHA




CHAPTER 13




Kullum Idan ya kalli yaron saiya tunada Prince Hafeez wanda a lkcn suna karatu bashi da abokin daya wucceshi dawowarsu gda 9ja ne yasa abotar tasu tayi baya saboda kowa ya kama abinda yake ganin zai fishsheshi amma duk da haka suna gaisawa sosai cikin yan shekarun nan ne komai yaja musu baya.
Ajiyar numfashi yayi ya kamo Sarki ya dora a cinyarsa tare dajaririyar da aka haifah masa yayi musu hotuna sannan yayiwa sarki shi daya ya turawa Prince Hafeez ta Email dinsa, kiransa yayi a waya ya daga suka gaisa yace “ranka ya dade ka manta damu mulki dadi har yasa ka manta da abokin amana” ajiyarzuciya akayi a daya bangaren yace “ kayi hqr My Nass wlh na rasa nutsuwa ta samada shekara uku ni kaina bansan ya ake wasu abubuwan suke faruwa dani ba ka tayani da addu’a kawai” a gaggauce yace “ya Salam nifa naji shirun tayi yawa yanzu meye dai yake faruwa ne?”jan numfashi yayi yace “yarinyar da nake baka lbrnta samada shekara ashirin ina mafarkin naganta a masarauta ta har munyi aure amma ta mutu Nasir an tabbatar min ranar da tabar gda motar Jos tahau kuma motar da tahau tayi hatsari babu wanda ya fita a cikinta ciki harda rayuwata Nima saboda wlh itace rayuwata Nima yanzu zaman jiran ajalina nakeyi saboda banida wani amfani a rayuwarnan”
Cikin tsananin tausayin abokin nasa yace “Allahu akbar na tausaya maka Hafeez amma babu komai kayi tawakkali ka rungumi qaddararka insha Allah komai zai wucce kasan ita qaddara babu Mai gogeta ita kuma Allah ya gafarta mata yasa matarka ce a aljanna” Shiru ce tadan ratsa kafin Nasirya kawar da shirun da cewa “akwai wani yaro dan qanwar Momy da yakemin tsananin kama dakai Hafeez wlh duk sanda na kalli yaron saina tunaka yanzu ma ka ganshi a jikina dake anyimin haihuwa ya gudo yabaro gdan Momy ya dawo gdana shima kamar kai yarone qarami da bai wucce shekara uku ba amma shegen son yarane dashi wlh da ace nasan kana neman mata babu abinda zai hana nace kaine uban yaron nan to amma nasan bakayi Allah ne kawai ya sanyaku iri daya” murmushi yayi yace “dama hakane ai turomin hotonsa naganshi don Allah” dariya yayi yace “na tura maka ta Email dazun kana hawa zaka ganshi” haka sukayi sallama suka ajiye wayar.
Yau ta kama rana ta farin ciki kuma Mai muhimmanci a rayuwar Farha ta yanzu saboda yaune ta gama digiri dinta na farko kuma da samu good points hakanne yasa bayan zamansu jiran result ta fara fafutukar ci gaba da karatu ita kuwa Maryam ‘tace aa batason wani karatu aure zatayi a lkcn da results dinta ya fito ta samu scholarship a Open University Oxford yan gdansu sunyi murna sosai suka hada mata party me kyau akaci akasha kowa ya watse babu wani bata lkc ta fara karatunta akan matsalar zuciya kuma a wannan lkcn ne aka bude wani babban Asibiti a cikin garin Kaduna me suna (QUEEN FARHA CONSULTANCY HOSPITAL ) wanda yake mallakin abokin Yaya Nasir Prince Hafeez shiba mazaunin garin Kaduna bane wannan dalilin yasa ya damqa ragamar asibitin a hanun Nasir hakanne yasa aka dauki Farha wadda ta koma Hanah Usman a yanzu a matsayin ma‘aikaciyar asibitin ita da Maryam Usman ita Hanah tana bangaren matsalolin zuciya ita kuma Maryam tana bangaren matsalolin mata.
Tana karatunta tana aikinta albashinta me tsoka sosai ganin tana daukan albashi me kyau yasa taso daukewa Daddy wasu daga cikin dawainiyarta data shafi Sarki amma flr yaqi dole ta hqr take serving salary dinta babu abinda takeyi dashi sai dan abinda baa rasa ba data tuntubi Yaya Nasir da mgnr tanason daukan nauyin karatun Sarki sai yake gaya mata ai Suma basu suke dauka ba Abokinsa Prince Hafeez ne yake daukan nauyin komai na karatunshi, lkcn daya ambaci sunan Hafeez saida taji gabanta ya fadu haka kawai batasan dalili ba.
Shekarar sarki 9 ya gama primary lkcn dazai tafi secondary tayi mamakin irin makarantar da aka sanyashi mai tsadar gaske a qallah duk qarshen zangon karatu ana biyan 1.5 million abun itadai harya fara bata tsoro batasan mutum ba baisanta ba sai kashewa danta kudi yakeyi, taso dakatar da abin amma ya faskara haka ta hqr ta zubawa sarautar Allah ido lkcn data gama Masters program dinta juyawa tayi PHD duk da Daddy yaso ta huta amma taqi yanzu gashi harta gama sai ya zamana ita da Nasir sune ragamar asibitin take a hanunsu, aiki sukeyi cike da qwarewa sunan asibitin yayi tambari a gda 9ja dama maqota duk wata matsala indai ta zuciya ce to magana ta qare saboda sunada qwararru kuma gogaggun likitocinta Dr Nasir Usman Dr Hanah Usman da Dr Samuel Obafemi sune manyan likitocin da asibitin yake tunqaho dashi hakan yasa sunan Hanah ya fantsama duniya Kowa Dr Hanah Usman, manyan mutane ne daga kowanne yanki na qasar nan suke zuwa neman auranta amma dasun kawo mata mgnr saita sagar musu da gwiwa ta hanyar cewa itafa matar aure ce abin ba qaramin batawa Nasir rai yake ba saboda mutanen da suka biyo ta hanunsa ma adadinsu bazai fadu ba gashi har ansa bikin Maryam ita taqi yarda ta saurari kowa.
Yauma kamar kullum suna zaune a parlour suna hira kasancewar asabarce babu aiki Yaya Nasir ne ya dubi Farha yace “Hanah inason ganinki idan babu damuwa” yana fadin haka ya miqe ya fita zuwa harabar gdan tajima tana mita su Momy nayi mata dariya kafin ta miqe tabi bayansa tsayawa tayi tace “nifah Yaya idanma wani ka kawo wlh tun wuri kace masa bana ra’ayi nida aurena kuma nasan wataran baban Sarki zai dawo gareni nasan abinda ya faru dani shima shine ya faru dashi amma badan hakaba bazai manta dani ba” tunda ta fara mgnr ya zuba mata ido gabansa yana faduwa harta gama saida tayi shiru kana yace “ba wani na kawo ba Hanah wannan karon nina kawo kaina nakeson gwada sa’ata Hanah wlh kwarjini kikeyimin shiyasa na kasa bayyana miki sirrin zuciyata tun ranar dana fara ganinki nake fama da wahalar daqon soyayyarki a zuciyata kada kiyi disappoint dina Hanah ki yarda dani ke likitan zuciya ce kinsan halinda zuciya take shiga idan ta rasa abinda takeso Hanah plz”
Wani irin kallo takeyi masa tanaja da baya yana binta harta shiga parlourn ta kwasa da gudu ta shige dakinta binta yayi yana kiranta amma Ina ta kullo dakin da key ta fada gadon tana haki tana maimata kalmar “Hasbunallahu wani’imal wakil” ‘tajima tana kwance kafin kuka ya kwace mata shikenan Yaya Nasir ya cuceta meyasa zaiyi mata haka shima bayan
yasan Ita matar aure ce meyasa shima bazan mata adalci ba yanzu me yakeson ya mayar da ita?tambayoyin data rinqa yiwa kanta kenan jin yanda ake bugun qofar ne yasata sake shigewa katifar taci gaba da kukanta can taji an daina bugun wayarta ta dauki qara dauka tayi daqyar tace “hel hello Momy” “to” ta kuma cewa sannan ta tashi saman gadon ta bude mata qofar janyota tayi jikinta tace “kiyi hqr wauta ce irinta Yayanku amma nayi masa mgn bazai qaraba babu maiyi miki dole a qyaleki har Allah ya kawo miki wanda kikejira” ajiyar zuciya tayi tace “na gde Momy Allah ya qara girma” amsawa tayi da amin taja hanunta suka fito parlourn bayanan ya fita don haka ta saki jikinta sukaci abinci.
 turawa sababbin qalu-bale suna qara shigowa rayuwarta zamanta a cikin gdan Alh Usman ita da danta sai son barka cikin shekara goma sha biyar dinnan bata da wata matsala saita mutanen da suke damunta a lkcn ne sarki ya gama secondary School. 
Yau takama asabar saboda haka yana tare da Uncle Nasir tun safe saida suka gama yawonsu sannan suka nufi guesthouse house din Prince Hafeez a zaune suka tarar dashi saman center carpet din dake parlourn ya hada kai da gwiwa yana tunani da sauri Sarki ya qarasa ya dago kansa hawaye ya gani sharkaf a fuskarsa hanu yasa ya rungume yaron kukansa ya qara qam shima Sarki fashewa yayi da kukan dan duk sanda yaganshi a cikin irin wannan yanayin shima sai yaji ya shiga damuwa jin qaunar abokin Uncle nasa yakeyi a cikin jininsa a hankali ya rinqa bubbuga bayan yaron da zummar rarrashin shi kansa Nasir baisan sanda hawayen tausayin mutane uku ya zubo masa ba yana tausayawa King Hafeez saboda yasan ciwon son matarsa da kuma kewar rashin haihuwa sune suke cin zuciyarsa ga dukiya har dukiya an tara babu masu cinta saidai yayita rabarwa talakawa da bitalmali matar daya data rage masa ya saketa babu gaira babu dalili wannan wacce irin rayuwa ya zabawa kansa ta kadaici oho duk inda kabi a gidan ya rubuceshi da sunan matacciyar matarsa (I LOVE MY FARHAI MISS YOU MY QUEEN R.I.P LATE WIFE MISS YOU LOVELY WIFE) Abinda zakayita gani kenan a duk inda kasa qafarka a gdan. 
Dagowar Sarki yasa hanunsa ya fara sharewa King Hafeez hawayensa cikin rawar murya yace “meyasa kullum zan hadu dakai cikin damuwa zanganka Dady meyasa bazaka bar rayuwarka ta hutaba meyasa kaima ka hana kanka kwanciyar hankali kamar Momy na kullum itama Momy na saina ganta tana kuka ta rungume wani tsohon hoto idan na tambayeta waye a jikin hoton sai tacemin itama batasonshi ba amma tanajin sonsa a zuciyarta ina tausayawa Momy na kaima kuma ina tausayin ka Daddy ku taimakeni ku daina damuwarnan wlh kona tafl karatun da kace zaka turani Rasha bazan iyayi ba saboda zanke tuna nabaro mahaifiyata cikin damuwa sannan kaida ka daukeni matsayin kake sona da burin ganin rayuwata ta inganta kaima kana cikin damuwa
Daddy inasonka inajinka a cikinjinina inajin dama ba babana ne mahaifina ba dama kaine inajin dama zan iya dauke kaddararku kaida Momyna ta zama tawa inason ganinku cikin farin ciki Daddy plz ka daina Daddy ka daina….” 
Ya qarasa mgnr yana qara rungume King Hafeez shima rungume yaron yayi qamqam a jikinsa yana matso wasu sabbin hawayen masu zafin gaska ya bude bakinsa yace “inda zan iya cire Queen Farha a zuciyata da tuni na cire kodan na samawa tawa rayuwar sauqi amma na kasa Abdallah Queen Farha ta tafi da rayuwata nima gangarjikina kawai tabarmin Abdallah kuka biyu nakeyi kullum a rayuwata na rashin matata farin cikina dana fashin dana dake cikinta da nasan idan na fita daga gda Farha ma zatayi taje tayi hatsari wlh ranar daban fita ba dana zauna ta mutu a hanuna naga gawarta na tabbatar data mutu 
yanzu gashi dai nasan ta mutu amma kullum mafarkin ganinta nakeyi kullum nemanta nakeyi a duniya da zanga koda me kamarta ne tabbas zance Farha tace ta dawo…” 
Yana mgn yana kuka mecin zuciya tashi Nasir yayi ya matso zai janye Sarki daga jikinsa yayi saurin riqe yaron yace “kabarni dashi Nasir inajinsa a cikin jinina qaunar Abdallah daga indallahi take wlh bantaba jin qaunarwani da a duniya kamaryanda nakeson Abdallah ba Nasir ka taimakeni ka barmin Abdallah na nunawa duniya shi a matsayin dana don Allah” Hawaye Nasirya share yace “da ace nina haifi Abdallah da babu abinda zaisa na kasa bakashi amma kash ba dana bane kuma mahaifiyar sa itama shi kadai ta mallaka matsayin da taqi aure bare ta haifi wani mutane dayawa sunason auran Hanah ciki harda ni amma taqi yarda kullum zancenta mijinta ita zataci gaba da rayuwa har ta tadda inda mijinta yake kullum mgnrta irin takace Hafeez yaron nan shine sanyi idaniyarta shi take gani taji dadi idan ka rabata dashi na tabbata saita shiga halin da yafi wanda kake ciki kai saboda ita ta haifa kai kuwa baka haifa ba naka zai zama da sauqi zaka fitajuriya da dangana” 
Kwantar da kansa yayi saman wuyan Sarki yace “haka ne amma Ina neman alfarmar abarshi dani a ransa kada ta rabani dashi kallonsa kadai yana samin nutsuwa” yana fadin haka ya miqe ya shiga dakinsa ya fada bathroom yayi wanka ya shirya idanunsa sunyija sosai saboda kukan da yaci saboda haka ya dauki baqin glass yasa ya fito kama hanun Abdallah yayi ya shigar dashi wani daki yace “saboda kai nasa aka gyara dakinnan ka shiga kayi wanka ka canza kaya akwai kaya a wadroop nakane sunfi kala hamsin ka zabi wanda kakeso kasa kazo ka rakani Emergration office inason ayi maka passport nanda kwana takwas zaka tafi kayi karatu kaji yarona” tsalle yayi ya rungume shi yayi kissing kuncinsa yace “yess farin uba I love it” ya fada tare dajinjina masa ya sakeshi ya fada bathroom din ya fara wankan yana fitowa ya shirya cikin wani yadi fari kalarwanda yaga King Hafeez din yasaka ya fito yana dariya suma dariyar sukayi Nasir ne yace “lallai wannan wariyar launin fata taku ta kai inda takai wato sai kukayi anko ni kuma ko oho ko?” Maqalewa yayi jikin King Hafeez yace “to kaima ai sai kayi da yayanka Nima nida Daddy na mukayi” murmushi Hafeez yayi ya sanya cump ya fara taje masa sumarsa yace “gskyrka yarona amma sumar nan asketa zaayi yau” 
Da haka suka fice suna tafe suna tattana abinda ya shafi asibitocinsu har suka isa inda za akayi musu duk abinda zaayi musu sannan suka wucce asibitin yauma kamar kullum suna zuwa akace ita kuma Hanah ta Fita King Hafeez yana mamakin sabanin da sukeyi da Hanah kullum zai shigo asibitin za,ace ta fita ko tashiga emergency room ko tana Teather room kullum a haka suke samada shekara bakwai din da take aiki a qarqashin asibitinsa. 

Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *