FARHA
CHAPTER 14
Saida ya shiga cikin asibitin ya duba duk wani abu daya kamata ya duba hanunsa yana riqe dana Sarki har suka gama ya shiga office dinsa suka zauna inda Nasirya nufi wani bangare na asibitin domin duba wani patient sun dan jima suna hira da Sarki yana tambayarsa abubuwan da yake buqata shikuma yaron yana fada masa saboda harga Allah Sarki jin King Hafeez yakeyi kamar mahaifinsa.
Shigowar Nasir ce tasasu miqewa suka fita Nasir ne ya dubesa yace “wato King Hafeez Hanah ce take neman dauko mana wani risky a cikin sana’armu wani bawan Allah ne yake fama da wani irin ciwon zuciya wanda yasa wani bangare na zuciyar tasa ya wuje yake fitar da wani baqin jini da ruwa me wari duk yanda za’ayi dashi tun a garinsu Zamfara anyi amma abin yaci tura har Kano teaching hospital aka turashi qarshe suka rubuta mishi takarda zuwa wani asibiti dake Hydrabat saboda aiki zuciyarsa take buqata kuma ba’a taba irin aikin anan qasa 9ja ba, amma da yake itadin yar rigima ce ta karbeshi tace su zasuyi aikin a cikin asibitin su har hukumar kiyaye lfy ta one millions health ta turo takarda akan cewa kada muyi gangancin yin aikin da manyan asibitocin qasa suka kasayi qarshe itama ta rubuta musu cewa tabada rayuwarta da duk abinda ta mallaka fansa ga iyalansa indai ya
mutu ta sanadin sakacinmu wajan aikin da za’ayi masa wannan abu yana damuna”
Murmushi King Hafeez yayi yace “ai ba’a riqewa yaro garma Nasir tunda tace zata iya jagorantar aikin mu barta kuma da babu mai koyo da gwanaye sun jima da qarewa suma
inda za’a kaishi din qarshe zakayi mamaki idan nace maka yarane masu koyan aiki za’a bari dashi suyi masa kuma ya miqe idan bama daukan irin wadannan risky din to tabbas
bazamu taba ci gaba ba a rayuwar aikinmu” yana kaiwa nan ya juya ya kalli Sarki da yaketa
cin cheesen sa yace “ ka qarfafawa mahaifiyar ka gwuiwa akan kyakkyawan qudurinta
nikuma nayi alqawarin duk abinda ake buqata wajan aikin zan kawoshi cikin qanqanin lkc kace tayomin list na komai ta baka ka kawomin ka rabuda matsoracin uncle dinnan naka
kaji kayi jajircewa irinta Momynka da Daddynka kaji yarona” “
Jinjina kai sarki yayi da confidence dinsa yace “yess lovely father I love it” dariya sukayi dukkansu daidai lkcn da sukayi parking suka fito suka shiga cikin parlourn Momy ce kawai a zaune a ciki Farha na dakinta Maryam na gdan mijinta harda yaranta biyu zama yayi suka gaisa Sarki ne ya matsa daidai kunnen King Hafeez yace “Daddy nasan bakasan Momy na ba bari na kira maka ita ku gaisa ko?” murmushi yayi yace “na gde lovely Son” miqewa yayi ya shiga dakin ya tarar tana wankajuyawa yayi yace “Daddy Momy is bathing” ajiyar zuciya yayi ajiyar numfashi yayi yace “wala aibi boy Momynka bataso na ganta ne amma nasan komai girman gona akwai kunyar qarshe idan dai muna raye wataran zamu hadu” yana fadin haka ya miqe yayi kissing lips din dannasa yace “kayi bacci cikin aminci My lovely Son ka isarmin da gaisuwar qarfafa gwiwa ta wa Momynka zanje gda na kwanta gobe zan tafi Bauchi” shima kissing dinsa yayi suka rungumejuna sannan sukayiwa juna bye ya fice da sauri ya hau motarsa ya tafi zuciyarsa cike da ciwo yanzu Farhansa tana raye da yanzu dansu ko yarsu tayi kamar Abdallah wasu hawaye ya share a idonsa yana qarajin tsanar Amnah da Hajiya Sogiji a ransa tabbas badan muguwar baqar zuciyarsu da baqin kishinsu ba da tuni shima babane da yanzu yana tare da Farhansa tana lailayashi tana shayar dashi salon soyayyarta da kulawarta gareshi” irin wadannan tunane tunanen sune suke hana King Hafeez kwanciyar hankali, yana zuwa gda ya shige dakinsa ya fada saman gadonsa ya janyo hoton Farha daya ajiye saman bedsat drower dinsa ya rungume ya kuma sakin wani kuka
A bangaren Farha kuwa tana fitowa ta tarar da dannata kwance saman gado yanata aikin kuka matsawa tayi ta juyo dashi tace “haba My lovely Son me kuma ya faru haka har zuciyar Momy take zubar da hawaye?” ture hanunta yayi yace “ni babu ruwana dake tunda kike gudun Daddy na kullum idan yazo gdannan saiki buya bakyason ku hadu Momy meyasa hakane?”
Murmushi tayi tace “yanzu akan dan wannan abin za’ayi fushi dani Sarki to kayi hqr watarana zamu hadu badaga ni bane Allah ne yake kawo sabanin tashi maza kaje ka hadomin tea a kitchen zanyi wani binkice banason musu banason surutu” miqewa yayi ya fita yana bubbuga qafa shi a dole tayi masa Iaifi bata kulashi ba taci gaba da abinda takeyi tasan ba kawo Mata tea din zaiyi ba saboda ta bata masa rai akan wannan mutumin daya kwallafa ransa akansa.
Zama tayi taci gaba da bincikenta sai dare sosai ta gama sannan ta fita taci abinci ta dawo tayi brush ta kwanta zuwa yanzu kadaici ya fara damunta sosai shekarunta sun fara nauyi 32 years ai tayi hqr shekara sha biyar babu namiji gsky ya kamata tayi wani abu miji takeso sosai. “ Da wannan tunanin bacci ya dauketa washe gari da wuri ta tafi asibiti saboda tunanin patient dinta jiya ya hanata sakat tana zuwa ta dubashi ta bashi magunguna kasancewar komai ita takeyi masa da kanta sai yamma liqis ta fito daga asibitin ta nufi gdan tana shiga ta fada kitchen ta dafa lndomie ta nufi dakinta taci sannan tayi wanka ta kuma fita zuwa gdan Maryam acan Yaya Nasir ya sameta tayi kicin kichin taqi ko kallonsa dariya yayi ya lakace mata hanci yace “yi hqr maida wuqar yar qanwata dama General manager ne yace na isar da gaisuwar sa gareki sannan yace yana qarfafa miki gwiwa akan abinda kika daukowa kanki sannan yace kiyi list na abubuwan da ake buqata idan zai tafi Rasha kai Sarki saiya taho dasu” murmushi tayi ta bude handbag dinta ta dauko wata takarda ta bashi sannan taci gaba da hirarta da wasa da yaran Maryam ganin babu fuskane yasashi miqewa ya tafi tabisa da harara tare da jan qaramin tsaki dariya Maryam tayi tace “nidai Ina mamakin wannan soyayya taku da Yaya Hanah kawai ki yarda ayi kema kya samu Mai sosa miki gurin nan dan nasan yanzu ba qaramin susa yakeso ba” ajiyar zuciya tayi ta share hawayen da suka gangaro mata tace “Sister bazaki gane ba wlh bani naqi aure ba shine ya qini saboda na kasa koyawa kaina son wani da namiji a duniya sai mutum daya shikuma bansan inda zan nemoshi ba Maryam ya zanyi da rayuwata haka Allah ya ‘tsaramin Maryam” bude
jakarta tayi ta zaro wani tsohon hoton kati ta miqawa Maryam tace “wannan shine farin cikina Maryam shi nakeso shi zuciya ta take kwadayi amma na rasa gane inda zanganshi wlh Maryam har shiryawa nakeyi takanas na fita domin nemansa na kasa ganinshi” ta rufe bakinta daidai lkcn da Maryam ta karbi hoton.
Wata zabura Maryam tayi ta miqe tare da zaro ido waje tace “King Hafeez Hanah King Hafeez kikeso meye alaqarki dashi ina kika samu tsohon hotonnan nasa tun yana saurayi?” ltama miqewa tayi tana yiwa Maryam kallon tuhuma tace “su..sunansa kenan Maryam ina kika sanshi Maryam ina zan ganshi Maryam ki taimakeni hqr na ya qare game da bawan Allan nan bansanshi ba amma inajin qaunarsa a cikinjinina” sake riqota Maryam tayi tace “ina kika samu hoton Hanah tabbas wannan hoton King Hafeez ne abokin Yaya Nasir wanda yake da rukunin asibitocin QUEEN FARHA CONSULTANCY HOSPITAL, Hanah a qarqashin sa kike aiki wannan hoton dadadden hotone King Hafeez ya daukeshi ne lkcn farin cikinsa na tare dashi ba yanzu da shekarunsa sukayi nauyi ba kuma ya rasa farin cikinsa Hanah dole akwai dalilin da yasa kika sami wannan tsohon hoton ina kika sameshi Hanah?”
Girgiza kanta tayi tace “wlh iyakar gsky kenan Maryam bansan Ina na sameshi ba kawai nidai na ganshi a gurina ne tare da mahaifi na dana taba nuna muku” shiru Maryam tayi tana jinjina lamarin miqewa tayi ta dauki wayarta ta kira number Yaya Nasir ta fada masa abinda yake faruwa, cikin tashin hankali yajuyo ya dawo gdan yana shigowa ya tarar da ita zaune a qasa ta kifa kanta da kujera tanata gursheqen kuka hoton ya dauka ya zubawa ido shakka babu King Hafeez ne a jiki tun yana saurayi ba yanzu da girma ya fara shigo masa ba tsugunawa yayi a gabanta yace “meye alaqarki dashi Hanah Ina kika samu hotonsa?” Cikin kuka tace “sama da shekara sha biyar nake tare da hoton nan duk iyakar tunanina nason nasan matsayinsa a gurina na kasa tunawa kawai nidai abinda na sani yanayimin kama da dana Abdallah” kansa ne yayi wata muguwar sarawa a tsorace yake furta “ya haka me hakan yake nufi to kodai shine yayi miki fyade har kika samu cikin Abdallah shiyasa shima yakeyi masa so irin na da da mahaifi? Kai aa wannan qaryane nasani King Hafeez bashi da lfyr da zai iya bawa kowacce mace ciki to kodai dan uwanki ne Hanah meye alaqarki dashi?”
Ya fada da qarfi yana qara matsarta tanaja da baya karo yayi da center table ya fadi hakan ya bata damar surarjakarta da key din motarta ta fice da gudu kafin ya taso har taja motar da mahaukacin gudu tayi waje tanayin parking ta futo ta shiga gdan a guje daidai lkcn da shima yayi parking biyota yayi a sukwane ta fadajikin Momy ta qanqame ta tana sake sakin wani sabon kuka me cin zuciya fincikota yayi da qarfi ya hadata da bango ya shaqeta kamar wani zararrare yace “wlh saikin fadamin alaqarki dashi kona kasheki na kashe banza Hanah meye nayi miki da zaki sakamin alkhairi da sharri meye aibina da zaki qini ki so abokina sai kin fadamin alaqarki dashi na rantse da Allah…” kyawawan maruka yaji guda biyu a kuncinsa ya saketa da sauri ya juya Daddy ne tsaye a kansu ya qara kai masa wani marin ya kauce da sauri, nunashi yayi da yatsa yace. “Baka da hankali ne Nasir kasheta zakayi ko anaso dole ne tace batasonka da aure to dole ne ko hakan da kakeyi mata shine zaisa ta soka?” juyowa yayi ya kalli Daddy yace “amma Daddy da bata sona kuma saita rasa wanda zataso sai abokina King Hafeez fah Daddy meye hadinta dashi ina ta samu tsohon hotonsa tun yana saurayi ni tambayar danakeyi mata kenan kuma ita nakeso ta amsamin” Daddy da kansa ya gama kullewa ya kalleta ya juyo ya kalleshi ya kai dubansa ga Maryam dake shigowa yanzu matsowa tayi ta miqa masa hoton tare da basu lbrn duk abinda ya faru da abinda Farha tace tanaji game da King Hafeez, zama Daddy yayi dafe da kansa yana ambaton sunan Allah itama Momy abin ya girmi tunaninta kallon Farha takeyi kawai data keta gursheqen kuka matsawa tayi gaban Daddy ta ruqo qafarsa tace “ku yarda dani Daddy wlh bansan komai game dashi ba nidai kawai na tsinci hotonsa a cikin kayana tare dana mahaifina ne dana taba nuna muku abinda yasa ban nuna muku shiba saboda bansan meye alaqata dashi ba amma nasani tabbas yana kama da dana Abdallah duk sanda na kalli hoton na kalli Abdallah sai naga kamar mutum daya ne Daddy bansan ya akayi na fara sonsa ba kawai nidai na tsinci kaina ne a
qaunarsa inajin kamar idan babushi bazan iya ci gaba da rayuwa ba”
“Aikuwa zaki mutu kiyi mushe Hanah saboda tabbas son maso wani kikeyi King Hafeez babu wata ya mace a duniya dake gabansa sai Farha tsohuwar matarsa data mutu samada shekaru goma sha biyar kullum ita yakewa kuka saboda ita ya kasa zama da matarsa ya saketa yake zaune shi kadai saboda ita ya kasa qara aure kullum mafarki yakeyi zata dawo gareshi bayan yasan duk wanda ya mutu baya dawowa amma so ya makantar dashi ya kasa ganewa Hanah kiyi gaggawar cireshi a ranki ki karbeni a matsayin mijinki nafi kowa sanin darajarki kuma nafi kowa tausayinki plz” yanda yake mgnr ne yasata qarawa kukanta sauti tana girgiza masa kai,
Daidai lkcn Sarki ya shigo da gudu yana tsallen murna da ihunsa ganin yanda sukayi jigum jigum yasashi saita nutsuwarshi ya matsa kusa da Momynsa ya ruqo hannunta yace “Momy meye yasaki kuka?” daukan hoton yayi ya zuba masa ido cikin rawar murya yace “Da…ddy Mom..my wal..lahi Daddy nane wannan…” daidai lkcn shima King Hafeez ya sawo kai cikin parlourn da ledoji niqi niqi a hannayensa yana cewa “kaga sokon yaro ka gudo kabar Daddynka da dakon kay….” mgnr ce ta maqalejikinsa ya dauki rawa ya saki kayan hanunsa a kidime ya daga hanunsa da yake rawa ya bude bakinsa da kyar yace “Qu…een Far..hanah ke…ce dama baki mutu ba…” miqewa itama tayi ta zuba masa ido tana wani irin hawaye ta fara tafiya da sassarfa zuwa inda yake shima takowa yakeyi har suka hade a tsakiyar parlourn ya cafkota da sauri ya hadata da qirjinsa ya matseta yana cewa “mafarki nakeyi Farhanah k0 gaske ne kece a gabana Queen dama kina ra….” bai iya qarasawaba saboda wanijiri daya dabeshi ya yankejiki ya fadi sumamme amma duk da haka tana maqale a qirjinsa ta saki wani kuka me gunji tajanye jikinta daqyar cikin muryar tashin hankali tace “ya sanni shima Momy shima ashe ya sanni wlh nasanshi sosai amma nakasa tuna inda na sanshi Daddy ku taimakeni kada ya mutu shine rayuwata plz Daddy” miqewa tayi da sauri ta janyo hanun Daddy da Yaya Nasir tana kuka tanayi musu magiyar kada ya mum Sarki ne ya matsa ya rungume shi yana kuka me tsuma zuciya yana cewa “kada kayi mana haka Daddy kada ka mutu ka barni don Allah Momy nama ta sanka ka tashi Daddy ka tashi ni katashi nace Daddy….”