FARHA
CHAPTER 4
02:00pm aka daura auran 3:30pm jerin gwanon motocin daukan amaryar sukazo tare da kawo kayan lefe kayane na gani a fada babu qarya an zuba naira cikin lefen Farha iyakar ganin me kallo bazai iya qididdige adadin kayan dake cikin akwatunan lefen ba sarqoqi kawai da aka zuba mata na gold sunkai bakwai hakanan badan an gama ganiba aka fito da ita sanye cikin Alqabba milk colour tayi kyau matuqa kamar dama ahlin abun kanta qasa tanata sharbar kukanta wanda ta yini aikinsa Ummah ce ta riqe hannunta har turakar Baffanta ta tsuguna daidai qafarsa tana qarawa kukanta sauti wai don yaji tausayinta yace yafasa aurar da ita, dago kanta yayi da hanunsa yana girgiza mata kai yace. Kiyi hqr Farhanah bawai don bama sonki zamu bayar dake a tafi dake ba aa saidon babu yanda zamuyi haka Allah ya tsara mana tun farko kece zaki riga yan uwanki tafiya dakin mijinki Farha banason jayayya da lamarin ubangiji shiyasa na yarda da aurannan naki amma nasan akwai manufa a cikinsa duk da manufarsa ba haramtacciyar manufa bace amma naso ace ba kece wacce kika zama sirrin manufarsa ba kiyi hqr kiyiwa mijinki biyayya kuma ki zauna da kowa lfy kinga dai yanda Allah yayi dake kin taso gdanku daga ke sai yan uwanki da baku shidda ba gaba daya gdanku mutum tara ne yanzu kuma zaki koma babban gda da yake dauke da mutane sama da dari kuma kowanne da halinsa kowanne da iyayensa saboda haka dole ki nutsu ki gyara takunki karkice zaki tafi da shirman nan naki gdan sarauta zakisha wahalar rayuwar cikinsa kuma karkice zaki dauki girman kai da izza irinta makusanta Sarauta zakiyi baqin jini kuma zaki fuskanci wulaqanci da gori ki tsaya iyakar huruminki na mata babu ruwanki da duk wani abu daya shafi sarauta idan kikayi haka zaki zauna lfy da kowa”
Numfashi yaja tare da sakin kanta yace “tashi kije sunajiranki Allah yayi miki albarka ya kareki daga sharri da makircin gdan sarautar garinnan” kama hanunta Ummah ta kumayi
ta fita da ita har tsakar gdan ta damqata hanun Jakadiyyah kamo hanun Rahmah tayi ta rungume ta suka fita dukkansu suna kuka, ba’a dauki wasu mutane da yawaba mutun shidda ne manya sai yan uwanta guda biyu da qawarta Binta suka shiga motocin suka nufi gidan sarautar tun kafin su qarasa ta fara jiyo bushe bushe da kade kade sake Iafewa tayi a jikin
Rahmah tanaci gaba da rera kukanta Jakadiyyar da tausayin uwar dakin nata ya cikata ta rinqa bata hqr tana lallashinta har suka qarasa batayi shiru ba. ‘
Motocin ne sukayi parking a harabar gdan da yake gari guda kowa ya fito sannan aka bude mata qofar suka fito ita ce qarshen fitowa tana fitowar aka dora saman wata farar godiya sunata kide kidensu da waqoqinsu harsuka isa wata babbar qofa aka bude musu suna shiga bayi da barori su kayita zubewa suna kwasar gaisuwa har suka isa wata qofar nanma aka bude suka shiga sauketa akayi daga kan godiyar Jakadiyyarta sake riqe hanunta suka shiga parlourn tare da sallamarsu parlourn cike yake da mutane aka farayi mata marhabin wata mata ce ta taso ta riqo hanun Farhan tanayi mata sannu da zuwa bata gane komai itadai taji anyi qasa da ita ta russuna sai kuma taji an dafa kanta muryar dattijuwa taji tace “barkanki da zuwa gdan nan matsayin matar Mai martaba Hafeez Farhanah Allah yayi muku albarka ki saki jikinki nan gdanku ne ki daukeni kamar mahaifiyarki kiyi duk abinda zakiyi a gdanku nanma gdane kinji, Hajjah ku kaita sauran bangarorin ta gaishesu”
Sake fita sukayi suka shiga apartment din Hajiya Sogiji suka kwashi gaisuwa babu wata fuska a gurin wadanda suke dakin saboda haka basu dadeba suka nufi part din Hajiya Kilishi nan ne Farhanah taga gata da riritawa anan part din aka barta yan uwan nata sukayi musu sallama suka tafi lkcn shidda da rabi ta wucce yammata biyu ne a bangaren Asiya da Nadiya sune suka sata a gaba sunata yi mata hira da dauke mata kewa amma taki sakin jikinta sai kuka takeyi dariya sukeyi mata wadda aka ambata da Nadiyyarce ta ruqo hanunta tace “wlh Yaya ya more yarinya qarama danyen jini zai bare a leda ina tausaya miki Farha” dariya Asiya tayi tace “nifah kawai tunda na ganta nake ayyana yanda karon zai kasance yanda Yaya Hafeez yake Masha Allah ga tsayi ga qauri Allah idan ya rufeta bazaa hangota ba ko kadan”
Sake qarawa kukanta sauti tayi tace “nidai na roqeku kuyimin shiru banason wannan mgnr” kwashewa sukayi da dariya sukace “zakiyi bayani ne da harda Chinese sai kinyi nidai zan taimaka da ruwan zafi…” toshe kunnenta tayi tana girgiza musu kai ganin tana neman tayar musu da iskoki ne yasasu sauya ragamarzancen, suka farayi mata bayanin kowa a gdan musamman part’s ukun da aka kaita sukace na farko da aka fara kaita shine na surukarta mahaifiyar Sarki Hafeez ita ake Kira da Fulani Hajjah itace babbar yarta sai Hafeez sai Asiya ita kuma Sogiji itama da yayanta biyu Hasheem da Umaima ita kuma Hajiya Kilishi tanada ya daya Nadiya.
Ruqo hanunta Asiya tayi tace “zaki fahimci komai a hankali zakuma muyi qoqarin sanar dake wasu abubuwan Aunty Farha kedai kawai ki shiryawa rayuwa a rikitaccen gdan da wanda yake wajensa baya hango tarin matsalolin da suke cikinsa babban abin damuwata gareki shine kishiyarki Gimbiya Amna batada kirki gata da bala’in kishi yanzu haka rikici suke tukawa da Mijinku saboda batasanma da mgnr auran da zaiyi ba sai yau da safe saboda haka dole ki nutsu ki shiryawa tunkarar qalubale uku mijinki kishiyarki da kuma cikin gdannan musamman Hajiya Sogiji koda wasa karki taba sakin jiki dasu…” mgnr tace ta maqale saboda ganin dawowar Hajiya Kilishi da wata mata tare da Hajjah.
Ruwan wanka suka hada mata sukace taje tayi wankan shiga tayi toilet din tajima tana qare masa kallo kafin ta fara wankan ruwan kamar ruwan madarar turare zallah haka shima sabulun bayan tayi wankan ta dauro sabon towel din da Hajiya ta Kilishi ta bata ta fito matarda suka shigo da Hajjah itace ta bude wata jaka ta dauko wanu Mai ta rinqa matsa mata tana fada mata inda zata shafa harta gama mulke jikinta dashi qamshinsa ya cika dakin ta kuma dauko wani tace ta shafa shima ta shafa sannan ta zauna Hajjah ce ta kama gashinta ta gyara matashi tsafsannan ta daureshi da band aka shafa mata powder tare dasa mata White lips brexia da pant suka bata ta karba ta koma bathroom din tasaka sannan ta sake fitowa Farha akwai baiwar dukiyarsu ta fulani a qirjinta Wanda suke tsaye cak kamar dashe, wata maroon din rigar bacci matarta miqa mata tace tasa batayi musuba ta zura rigar ta sauka har gwiwarta murmushi Hajjah tayi ganin mugun kyaun da yarinyar tayi babban abinda yake burgeta rashin tsoronta wata Alqabba suka Dora mata rufaffiya itama maroon Mai maballi har qasa wani flat din takalmi suka bata tasa a qafarta shima maroon tayi bala’in kyau qarshe barin turare sukayi mata kamar hauka tadau wani mugun kyau da qamshi miqewa Hajiya Kilishi tayi ta fita batajima ba suka dawo da Jakadiyyar
gdan Sarkin.
Ruqo hanunta Hajiya Kilishi tayi ta damqashi ana Jakadiyyar tace “to Ummah ga amana nan kindai ganta kinga yarintar ki zama idonta kuma kunnenta sannan ki rinqa qoqarin nusassheta tare dayi mata bayanin abubuwan da suka shige mata duhu kada ki munafurceta bani nabaki amanar nan ba Mai martaba ne saboda kowa ya gani duk girman gdannan da mutanen dake gdannan bai amince ya tura kowa ya dauko masa matarsa ba saike”jinjina kai tayi tace “nayi gdy na qara Hajiya Allah yaja kwana ya qara lfy” murmushi tayi tace “ki rakata gurin mijinta dare yayi nisa Allah yasa muji alkhairi Farha Allah ya kankaro miki darajarki data Mijinki daya kasa samu tun auran farko”amsawa duk wadanda ke dakin sukayi da amin.. itadai Farha cikin maganganun su babu abinda ta fahimta.
Kama hanunta tayi har suka fito harabar gdan mota tagani a tsaye askarawa sun kewayeta bude mata akayi suka shiga driven yaja suka tafi a hankali suke tafe har suka isa wani katafaran bangare wanda ya gaji da haduwa ko ina dake gdan haskene ya gauraye gdan bude musu get akayi suka shiga sukayi parking suka fito haryanzu hanunta na cikin na Jakadiyyar bayi sunata zubewa suna kwasar gaisuwa abinda yafi bata mamaki shine duk Wanda ya zube saitaji yace “barka da isowa masarautar sarkin sarakuna adalin Sarki Hafeez barka da zuwa uwar sarkin gobe cikon farin cikin shugabanmu” kalaman mugun daure mata kai sukeyi, bangare uku ne a gdan biyu maka maka dayan kuma madaidaici amma shima ba qarami bane shine a tsakiya da an kafa qaton hoton zane na Sarki Hafeez a jiki an rubuta (KING HAFEEZ||) shi kansa rubutun da ruwan gold akayisa sai daukan ido yakeyi da alamun dai gurin mallakinsa ne sai dayan bangaren daman an rubuta PRINCESS AMNA shima da manyan kalmomi akayi rubutun alamar da take nuna bangaren matarsa ne shikuma na hagun an rubuta SARAUNIYA FARHA alamar da take nuna nanne bangaren Farhanan, wani gabjejen dogari ne yazo ya zube a gabanta yace “tuba nake ya shugabata na cika umarnin Mai martaba ne ” Jakadiyya ce ta miqa masa hanu ya bata mukullin apartment din ta bude suka shiga suna shiga Jakadiyyartace “Allah ya taimakeki nan shine bangarenki zanso ki kwanta ki huta amma hakan bazai samu ba saboda dokar masarauta yau dole kiyi kwanan turakar Mijinki” ‘
Gaban Farha ya yanke ya fadi ta dago da sauri ta kalli Jakadiyya tace“turaka fah kikace wacce turaka inane turakar me zanyi a can?” murmushi tayi tace “bazan iya baki amsa ba lkc ne zaisa ki fahimci haka” sake kama hanunta tayi ta nufi wata qofa ta danna qararrawar sau biyu sannan taga wani blue din haske alamar an bata damarshiga murdawa tayi suka shiga tare da sallamarta yana kwance saman wani kushin yayi matashin kai da tumtum gabansa cike da tarkacen kayan abinci da kayan marmari da alamun na musamman ne idanunsa qur akan amaryar tasa yanajin wani sabon farin ciki yana gusar masa da baqin cikin da yake ciki, sannu a hankali har suka iso gabanshi durqushewa Jakadiyyar Ummah tayi tace “tuba nake ya shugabana wannan ya farune sakamakon jinkiri da aka samu wajan shirya Sarauniya amma bazaa qaraba ayimin aikin gafara” jinjina kansa yayi tare da nuna mata hanya harta juya zata fita yayi gyaran murya ta sake zubewa tace “takunka salamun kwanciyarka salamun adalin Sarki mai duniya” tashi yayi zaune ya
sanya hanunsa cikin aljihunsa ya zaro wani abu a qunshe cikin takarda ya miqa mata tasa hanu ta karba tana zuba gdy tare da kirari, shi mutumne meson a yabeshi a kurantashi amma yau baya buqatar wannan soyake kawai yaga fuskar Farha a gabansa yaji irin kurinta na yau saboda haka ya nuna mata hanya ta miqe kanta a qasa tace “kwana lfy cikin salama da amincin Allah ya shugaban talakawa baya goya marayu uban kowa gatan kowa shugaban Jakadiyya Ummah Mijin Sarauniya Farhanah uwar Yariman gobe” idan tayi masa wannan kirarin dadi yakeji tana fita taja qofar ya danna mata password tare da zuba mata ido tana durqushe a inda Jakadiyya ta durqusa tun farko kanta a qasa saida ya qare mata kallo kafin ya miqe ya qarasa gabanta ya zauna tare da sanya hanunsa ya dago kanta, ga mamakinsa sai yaga hawaye sharkaf a fuskarta duk ta dame fuskar dashi tausayinta ne yadan darsu kadan a zuciyarsa ya sake sakin tsaddadan smelling dinsa wanda ya qarawa kyakkyawar face dinsa kyau da kwarjini daidai lkcn ta bude idonta tun isowarsa gurin ta zuba idonta cikin rikitaccen idonsa wanda duk girman mace kuma duk qanqantarta bata iya jure kallon cikinsa, itama lumshe idonta tayi tanajiran taji abinda zaiyi mata.
Saukar lallausan tafin hanunsa taji a saman fuskarta yasa yatsansa yana share mata hawayen a hankali kuma a nutse sannan a mulkance ya bude bakinsa yace “baayimin kuka a fadata saboda haka ki kiyaye” saurin jijjiga masa kai tayi tare da motsa dan qaramin bakinta kamarzatayi mgn, ajiyar zuciya ya fuzgo tare da damqo hannunta cikin nashi yana qara qare mata kallo miqewa yayi ya dagota yana riqe da hanunta har suka qarasa inda ya tashi ya zaunar da ita shima ya zauna dafda ita saukar numfashinsa da takeji ne yasa tsoronta qaruwa ta fara matsawa a dabarance ita a tunaninta kada ya tayi ya ruqota tare dajanyota jikinsa ya hadata dajikinsa sosai bakinsa yasa daidai kunnenta yace “yau ba ranar fada bace ranar sirri ce ni na daina fada koda yake kince bazaki yafemin ba tarani kikeyi saboda haka na baki wuqa na baki nama ni yau nine kedin kece ni ki yanki duk inda yayi miki a jikina” turo baki tayi gaba zatayi masa tsiwa yayi sauri dora hanunsa akan bakinta yace “duk kalma daya da irin hukuncinta saboda haka ki kiyaye” yanda yake magana cikin izzah yasata shiga taitayinta dauke hanunsa yayi daga bakinta ya bude wata warmer yace “kitashi ki daibi abinda kikeso kici banason musu banason gardama saboda haka ki kiyaye” ajiyar numfashi tayi ta miqe zumbur jikinta na rawa ta koma gefe ta tsaya tace. ‘ “Bazanci ba din haka kawai na qoshi don qeta ace bazan fadaba Allah bazanci ba saidai ka kasheni kuma bazan kiyaye badin ko a lahira aka kafa mani wannan dokokin ai nasan aljanna ce akeson yimin qwalele don babi zanyi ba…” bata ankara da tahowarsa ba juyowa tayi ta ganshi qerere a kanta ihu tasa ta kwasa da gudu tayi baya fadawa tayi dakin akwai isasshen filin yin wasan tsere saboda haka yabita a nutse hartakai qarshe ta maqale ajikin bango tana karkarwa, qarasowa yayi gabanta ya sanya hanunsa yayi mata waigi ta dago kanta taga yanda yayi mata rumfa tace “wayyoh na shiga ukuna ka rufeni banashan iska…” matseta yayi a jikin bangon sosai kamar zai shigar da ita ciki kanta a qirjinsa kuka ta saka masa da taji matsar tayi yawa dan sassauta mata yayi ya sanya hanunsa ya fara balle maballin alqabbar ta riqe hanunsa cikin kuka tace “ni banason haka ka bari me zaka gani a jikina idan ba salon kwartancinka ba ai dama daga ganin girmanka zakayi mugunta idan ka kasheni ai ka huta kowama ya huta….”
Sunkuyowa yayi yayi kissing kuncinta tare da dora hanunsa saman lips dinta yace “babu
laifi hakanma idan nayi kwartancin ma aiba lalfi bane tunda kawomin ke akayi nayi duk abinda nakesonyi dake wlh badan inajin tausayinki ba dana gwada miki salon tawa muguntar da kike yawan ambata tunda na fahimci son gani kikeyi amma duk da haka bazakici banza ba…” yana fadin haka ya sunkuceta ya nufi wani guri da ita ihu take tana zillel da dukansa a qirji tana kiran “ni ka saukeni Allah banason irin haka dama ashe kaima haka kake shiyasa kake wani lumlumshe ido na iskanci Allah idan baka saukeni ba saina cijek…” Wata qofa ya shiga ya jefata a saman tangamenen gadonsa ya kashe fitila yace “ ya isa haka oya maza kwanta banasan surutu kiyimin shiru” bargo taja tana haki ta rufa tace “eh dai naji kuma kada a sake a hawomin nan ni banason shisshigi da neman ,,,” murmushi yayi ya nufi wata qofa ya bude ya shiga tayi tunanin dakinsa ya shiga tayi dariya tace “matsoraci kawai ashe izzar taka ta qaryace akwai abinda kake tsoro toba dolema kaji tsorona ba yanzu shekarata 16 nasan idan na qara hudu sai nayi kamarkai kuma irin abincin da kakeci nima shi zankeci na zama katuwar basamudiya irinka yanda bazaka sake cin zalina ba idanma kaci zanke ramawa” da haka bacci ya dauketa yana fitowa yaga tayi bacci ya bude blanket din ya leqa fuskarta yayi murmushi, mai ya shafa a hanunsa da qafafunsa da sauran jikinsa ya zura doguwar rigar bacci me laushi ya raba ya kwata a gefenta ya janyota a hankali ya hadata da jikinsa tare da yi musu addu’a ya rufesu shima bai jima ba baccin ya daukeshi saboda dare yaye lokacin 1:30am…
Hmmm