FETTA CHAPTER 31 KARSHE
Fetta a ranta ta k’uduri amincewa Sultan dan gujewa komawa Suraj, tana matuk’ar jin nauyin Hajiya, tasan ko shakka babu idan ba aure tayi, ba zata barta ba duba da yadda take son zaman su da Suraj, duk da babu soyayyar Sultan a ranta, tafi son auren sa akan Suraj, Shigowar Sanah ya katse mata tunani tace “Sultan yazo”, Ta amsa da “Toh”, tana mik’ewa, ta gyara zaman mayafin ta, ta fesa turare ba ma ik’arfi ba, wanda idan baka zo daf da ita ba, bara kaji k’amshi ba.+ A k’aramin garden dake sashen Azagas ta same shi, bai shigo ciki ba saboda bak’i, Da murmushi d’auke a fuskar shi kamar ko da yaushe yace “Barka da zuwa masoyiyata”, Murmushi tayi wanda bai kai zuci ba tace “Kai zanyi wa sannu da kasha hanya, Ya gajiyar hanya?”, “Bana tare da wata gajiya, idan ma akwai ganin ki yasa na wartse ka”, Tayi murmushi tace “Ya mutanen Yamai?”, “Duk suna lafiya, suna mik’o sak’on gaisuwa”, “Ina amsawa”, Ya gyara zama yana k’ara yin k’asa da murya yace “Ni dai har yanzu ina rok’o a taimaka a sanar dani matsayina”, Jim tayi tana tunanin yadda zata bashi amsa, nauyin amsar ta mata a baki, “Ko baki gama shawarar ba?”, Ta girgiza kai alamar a’ah, “Ina fatan kin amince na zama miji a gare ki?”, Tayi nodding kai, yayin da wani b’angare na zuciyar ta ke nuna mata kuskuren hakan, tana k’ok’arin danne b’angaren, Cike da tsantsar farin ciki yace “Alhamdulillah Allah nagode maka”, Fetta mamakin son da Sultan yake mata yake, duba da yadda yake farin ciki, Ya nisa yace “Gobe In Shaa Allah mutanen yamai zasu zo nema mun auren ki, ba za’a d’auki lokaci ba, bana so na rasa ki”, Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, ta rasa farin ciki zata yi ko bak’in ciki, Sultan yau salon kalaman da yake mata daban, tsantsar k’auna yake bayyana mata, ita kam murmushi kad’ai take masa, wanda ya d’auki hakan kunya, Suraj tun tashin Fetta ya rasa natsuwar sa, d’akin masaukin b’aki da aka bashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye, baya jin zai tab’a iya hak’ura da Fetta, ta zama jinin jikin sa, bugun zuciyar sa, duk wani numfashin sa yana fita ne tare da son ta, zai cigaba da rok’on ta har lokacin da zata ji tausayin sa ta dawo gare sa, Zaman d’akin ya ishe sa, ya fito waje yasha iska, ko zai rage rad’ad’in da yake ji a zuciya, zagaye sashen yake, kamar ance ya kalli gefen sa, ya hango Fetta zaune tare da Suraj, a daidai lokacin da suke dariya, wanda kallo d’aya zaka musu kace masoya ne, Tamkar an soke sa da kibiya a zuciya, yayin da kansa ya masifar sarawa, bak’in kishi ya turnik’e sa, jikin sa ya soma kyarma, bai san yana tsananin kishin ta ba sai yau da yake jin zuciyar sa na barazanar tarwatse, yana jin tamkar ya shak’aro Sultan ya aika sa lahira, a haka ya bar wurin ya koma masaukin sa, kan gadon d’akin ya fad’a, zuciyar sa na tafarfasa tamkar ana hura masa wuta a ciki, Sai ana kiran magrib Fetta ta nufo cikin gida, Sultan ya nufi masallacin masarautar, a nan zai kwana, sai magabatan sa sun zo an saka rana, Suraj jin kiran sallar magrib ya mik’e ya fito zuwa masallaci, A hanya yaci karo da Fetta wacce ta d’auke kai tamkar bata gan sa ba, idonsa ke hango masa ita tare da Sultan, haushin ta yaji ya kama sa, yana jin kamar ya fisgota ta fad’a masa dalilin kula Sultan, haka ya isa masallacin masarautar cike da takaicin ta, A sahu d’aya suka yi Sallah da Sultan, mutum biyu ya raba su, bayan an idar, Sultan ya shiga sallama da na kusa dashi, ya mik’awa Suraj hannu, ya d’auke kai tamkar bai gansa ba, Da kallon mamaki Sultan yabi sa, a ransa yace “Lafiyar wannan”, Ya d’age kafad’a, ya gaisa da sauran, ya fice masallacin, Suraj yabi bayansa da harara, yana jin kamar ya tashi ya karta masa warning ya kiyayi Fetta. Raba dare Aliya da Fetta suka yi suna hira, kace sun shekara basu ga juna ba, sai kusan biyun dare suka kwanta. Suraj bacci ko da wasa bai sace shi ba, tunanin Fetta tare da Sultan ya kasa barin zuciyar sa, idan ya rufe ido su yake hangowa, k’wak’walwar sa su take hasko masa, yayin da zuciyar sa ke tsananta zafi, masifaffan kishin ta yake ji na ratsa shi. Aunty Jummai ce cikin mak’abarta ba tare da tsoron komai ba, ta duk’a bakin wani kabari, ta hak’a rami ta binne layoyin da Boka ya bata, ta mik’e tana karkad’e hannun ta, bata tsaya duba komai ba, ta fice mak’abartar sanin dare ne babu mai ganin ta (Sai Allah wanda babu tsoron sa a tare da ita, zuciyarta ta bushe babu sauran imani), ta tafi cike da farin cikin aiwatar wa, bata san tabar baya da k’ura ba, Mai gadin mak’abartar yana ganin ta lokacin da ta binne, bai yi yunk’urin hana ta ba, sanin ko ya hanata anan zata iya zuwa wata mak’abartar, tana fita, ya taso ya tone ramin, ya fito da layoyin, ya warware komai ya wurgar cike da mamakin rashin tsoron Allah irin nata. Fetta yau ta tashi bata jin dad’in ranta wanda yana da nasaba, da zuwa neman auren ta da za’ayi yau, sam bata farin ciki tamkar auren dole za’a mata, bashi da bambamcin da auren dolen kasancewar bata son sa, “Haka zata k’are rayuwar ta ba zata yi auren soyayya, ta auri Suraj ba dan tana son sa ba”, “Kar ki manta Sultan na son ki, soyayyar sa kad’ai ta ishe ki, sab’anin Suraj da baya son ki, baya son auren ki”, Wani b’angare na zuciyar ta ya fad’a, Ta sauke ajiyar zuciya, tana amsa sallamar Aliya dake shigowa, “Masu neman auren ki sun iso” Cewar Aliya, Ta tsinci kanta da fad’uwar gaba, tayi k’arfin halin cewa “Har sun iso”, Aliya ta amsa da “Eh” tana tsare ta da ido, wanda take hango babu farin ciki sam a tare da ita, Ta nisa tace “Anya Fetta kina farin ciki da auren nan, kada ki k’ara jefa kan ki a auren da babu soyayya karo na biyu”, K’ok’arin b’oye damuwar ta tayi tana dariya tace “Laah Umma, Allah ina so, kawai kaina ke ciwo, sai fargaba da nake ji”, “Toh Shikenan, Allah ya tabbar mana da alkhairi, kuma ki cigaba da addu’a”, Tayi nodding kai tace “In Shaa Allah”Masu neman auren ta sun zo, an aiwatar da komai kamar yadda al’adar buzaye take, an saka biki sati biyu masu zuwa, sun koma da sha tara na arzik’i da yaba karamcin da aka musu, Sultan murna har fili ya kasa b’oyewa, yana ji tamkar yafi kowa sa’a a duniya. Fetta idar da sallar la’asar kenan tana nad’e sallaya, kiran Sultan ya shigo, ta d’auka, “Amarya ta”, Tayi murmushi wanda yana jiyo sautin sa ta waya, “Saura sati biyu ki zama mallaki na”, Tace “Allah ya nuna mana”, “Amin Ya Rabbi, wallahi na k’osa ki zama matata”, Tayi dariya wanda bai kai zuciya ba, bata jin farin ciki ko kad’an a ranta game da auren, “Anjima k’arfe shida jirgin mu zai tashi, kizo muyi sallama”, “Toh”, “Ina jiran ki a lambu”, Ta amsa da “Toh” tana kashe wayar. “Dalilin da yasa na kira ka ya kamata mu koma gida” Cewar Hajiya, Suraj dake durk’ushe gaban ta yace “Amma Mama bamu gamu shawo kan Fatima ba”, “Wane shawo kai, baka da labarin manema auren ta sun zo, sati biyu masu zuwa za’a d’aura mata aure”, A matuk’ar razane ya d’ago yana kallon Hajiya, yayin da yaji kalmar ta tamkar saukar aradu, zufa ta shiga karyo masa, idon sa suka kad’a jajir, bakin sa ya shiga kakkarwa ya kasa furta komai, Tausayin sa ya kama Hajiya, tasan dole zai shiga tashin hankali jin Fetta zata yi aure, amma ya zama dole ya hak’ura, shi ya jawa kansa tak’i sa, “Hak’uri zaka yi, ka k’ara kiyaye gaba”, Yaga bakin Hajiya na motsi but sam bai san me tace ba, kunnen sa basa jin komai, k’wak’walwar sa bata d’aukar kowacce magana, tunanin sa ya tsaya cak, Shigowar Su’ad da Feena yasa shi mik’ewa ya fita, ba dan yasan inda yake jefa k’afar sa ba, Fitowar sa filin gidan yayi daidai da saukar furucin Sultan kunnen sa, “Zan yi kewar ki matuk’a Amarya ta, ina jin kamar kar na tafi nayi ta kallon ki”, “Sati biyu ya rage na zama mallakin ka, kayi ta ganina har sai ka gaji”, Cewar Fetta wanda da gayya tayi ganin tahowar Suraj, Kalman ta tamkar saukar ruwan dalma a zuciyar sa, turnik’ik’in zafi take masa, yayin da yake ganin duhu-duhu na mamaye idon sa, kansa na tsananin sarawa kamar zai rabe biyu, jefa k’afafun sa yake ba tare da yana kallon gaban sa ba, taimakon Allah kad’ai ya kawo sa masaukin sa, “No wallahi ba zan iya jure ganin Fatima da wani ba, ba zan iya ba”, Ya fad’a cikin karaji yana dafe zuciyar sa dake barazanar tarwatsewa, kalaman Fetta ga Sultan na masa yawo a k’wakw’alwa, zafin zuciyar sa na k’aruwa, tuni jikin sa ya d’auki kyarma, cikin mintuna da suka gaza goma zazzab’i mai zafi ya rufe sa, duhu na mamaye idon sa duk da hasken fitilan da ya gauraye d’akin. Hajiya tun fitar sa hankalin ta ya kasa kwanciya da yanayin sa, yayin da zuciyar ta ke hasassa mata taje ta duba sa, Ta kalli Su’ad dake gefenta tace “Kinsan masaukin Suraj”, Ta gyad’a kai sama tace “Eh”, “Muje ki rakani”, Ta amsa da “Toh” ta mik’e ba tare da tambayar dalili ba. Halin da suka gansa ya matuk’ar d’aga musu hankali, kwance yake baya numfashi, Hajiya salati tayi ta sanar da ubangiji, tana kururuwar neman taimako, Su’ad a guje ta koma sashen Azagas ta sanar dasu, babu b’ata lokaci aka nufi asibiti dashi, Hajiya sai faman zirga zirga take bakin k’ofar da aka shiga dashi, ta kasa zaune ta kasa tsaye, tana addu’o’in da suka zo bakin ta, Su’ad, Feena da Samee na gefe na kuka, Aliya da Malam na tausar su, Azagas na gefe da masu tsaron ta, tana addu’ar samun sauk’in sa, Hajiya ba k’aramin tausayi ta bata ba. Fetta na masarautar bata san meke faruwa ba, kukan Mimi ya dameta, tayi ta lallashin ta, ta bata nono amma kukan k’aruwa yake, tana tunanin kai ta asibiti, wanda take kyautata zaton wani ciwon ke damun ta, STORY CONTINUES BELOW “Tumuqqartin bata daina kukan ba” Cewar Sanah dake shigowa wanda itama kukan ya soma damun ta, “Wallahi bata daina ba” Fetta ta fad’a cike da damuwa, “Ko zamu kai ta asibiti”, “Tunanin da nake kenan”, Ta fad’a tana jawo mayafin ta, Suka fita. Bello rashin Karima na damun sa matuk’a, sam baya walwala, ga takurar Tasleem da Mahaifin ta, wanda darajar Kawu Lamid’o take ci da tuni ya saketa ya bar musu gidan su, zaune yake falo yana kallo wanda a zahirin gaskiya hankalin sa baya kai, ya lula duniyar tunani, Tasleem ta shigo babu sallama, k’aramin mayafi sak’ale a kafad’ar ta tana tauna chingum, “Baka ga na dawo ba ne”, Ta fad’a tana tauna chingum yayi k’ara, “Baki iya sallama ba” Ya fad’a yana jin tamkar ya shak’are ta, “Eh ban iya ba, uban ganin laifi, sarkin k’orafi”, A fusace ya d’ago yace “Tasleem daraja d’aya kike ci”, Tayi dariya tace “Kana tsoro a kora gyatumi kenan, k’arya ta k’are, wallahi Lamid’o akwai kwad’ayin ma….” Bata k’arasa ba sakamakon marin da ya d’auke fuskar ta dashi, “Iskancin ki ya tsaya iya ni, kada ki sake sako mahaifina”, Ta d’ago a fusace tana sharb’ar hawaye tace “K’arya nayi mahaifin naka ba kwad’ayayye ba ne, wanda bai san darajar kansa ba a kan kud’i, matsiyac…..”, Naushi ya kai wa bakin ta, ya fashe da jini, Ihu ta fasa tana birgima a k’asa, “Ni ka fitarwa jini, wallahi yau sai kayi kwanan cell, shege matsiyaci dangin talaka”, Bello bai saki ba ta kanta ba, ya fice daga gidan. Fetta tayi mamakin ganin su Azagas a asibitin, Aliya ke sanar da ita meke faruwa, ta tsinci kanta da fad’uwar gaba, yayin da kallo d’aya tama Hajiya taji tausayin ta tsantsa na ratsa ta, itama uwa ce tasan yadda uwa ke ji akan dan’ ta, a zahiri tayi k’ok’arin nuna rashin damuwar ta, but a bad’ini rashin lafiyar tasa ba k’aramin tab’a ta yayi ba, wanda take alak’anta hakan da tausayin Hajiya. Mimi duk iya binciken likitoci basu ga wani abu dake damun ta ba, wanda hakan ba k’aramin mamaki ya ba Fetta ba, zuciyarta ta nasa mata rashin lafiyar Mahaifin nata ne ya tab’a ta, bata tsaya a asibitin ba, ta koma gida cike da damuwa, da fatan masa samun sauk’i, Kawu Lamid’o na zaune tare da Gwaggo suna hira, “Hayaniya nake ji tsakar gida”, Cewar Gwaggo, Kafin Kawu Lamid’o yayi magana suka ji bugun k’ofa tamkar zata b’alle, a tsorace ya bud’e k’ofar, Alhaji Tambari da yan sanda suka danno ciki, “Alhaji lafiya dai” Cewar Kawu Lamid’o a rud’e, “Tambayar lafiya kake, ina tsinanannen yaron ka”, “Me ya faru, bai zo nan ba”, “Kai ku shigo ku bincike ko’ina ku fito dashi”, “Amma a k’aida ai ba haka ya kamata, garadan maza su shiga d’akunan matar aure”, Gwaggo ta fad’a, Matsiyacin kallo Alhaji Tambari ya watsa mata Yace “Mutane masu daraja ake ma haka ba irin ku ba, wanda baku san komai ba sai kud’i, tuni kuka siyar da mutuncin ku”, Ba Gwaggo kad’ai ba hatta Kawu Lamid’o maganar ta sosa ransa, Yan’ sanda bincike na wulak’anci suka musu, hatta kayan su na cikin wadrobe sai da suka zubar k’asa, “Ranka ya dad’e bamu gan shi ba” Cewar d’aya daga cikin yan sanda, Ya kai duban sa ga Kawu Lamid’o yace “Ka fito da dan’ ka ko ka had’u da mummunan hukunci”, Kafin ya basa amsa Bello ya shigo, wanda a take yan’ sandan suka cafke sa, kamar sun kama b’arawo, “Me ya muku wai”, Cewar Gwaggo tana soma hawaye, “Ku tafi dashi, yau zai san ya tab’a mun ya'” Hannu ta d’aura a kai tana fad’in “Wayyo Allah na shiga uku na lalace, Dan Allah ku sakar mun da'”, Kawu Lamid’o yabi bayan su cike da tsananin tashin hankali. Bilkisu yau kwana uku tana kwance babu lafiya, wanda take kyautata zaton malaria ne, ta siyo magani tasha, taje chemist an mata allura, but ciwon gaba yake, “Rashin lafiyar ki ta soma damuna ko asibiti zamu je” Aunty Jummai ta fad’a cike da damuwa, “Eh Umma, ban taba jin ciwon irin wannan ba”, “Bara na fita na samu adaidaita mu tafi”, Ta fad’a tana mik’ewa ta fita. 1:00am na dare Suraj ya farka da sunan Fetta a baki, ” Fatima Dan Allah ki dawo gare ni, wallahi na tuba, na daina halayya ta, na tsaftace rayuwata, ba zan sake wulak’anta ki ba, nayi nadama”, Hajiya ta rungume sa tana fad’in “Kwantar da hankalin ka, zata dawo gare ka”, “Dan Allah ku kira mun ita, ta fad’a mun da bakin ta zata dawo gare ni, ba zata auri wani ba, rashin ta a rayuwata daidai yake da fitar numfashi na”, “Yanzu zata zo, ka kwanta tana zuwa”, Hajiya ta fad’a tana k’ok’arin kwantar dashi, cikin minti biyu bacci ya sake d’aukar sa, Su Su’ad na gefe na zubar hawaye cike da tausayin shi, Azagas kasa magana tayi tausayin sa ya kamata, Aliya da Mallam suma sun tausaya masa matuk’a, Dr ne ya shigo yana tambayar “Waye shak’ikin sa?”, Hajiya tace “Gani”, “Muje office na miki bayanin rashin lafiyar sa”, “A’ah kayi anan, duka yan uwan sa ne”, “Ok ba damuwa” Ya nisa yace “Jinin sa ne ya hau sosai wanda bai kamata ace ya hau haka ba, ma’ana ya kamu da hawan jini, damuwa da tunani sun masa yawa wanda gab yake da kamuwa da ciwon zuciya, ya zama dole a kiyaye duk wani abu da zai rik’a b’ata masa rai da jefa sa a damuwa idan ana son samun lafiyar sa da rayuwar sa”, Sautin kuka da salati kawai ke tashi a d’akin, babu mai cewa komai, “Ba kuka ya kamata kuyi ba, addu’a ya dace kuma ku kiyaye, zamu rik’e shi na tsawon kwana uku ya k’ara samun natsuwa” Yana fad’ar haka ya fice, Hajiya kuka take kamar ranta, dole kowa ya tsagaita da nasa aka koma lallashin ta da ban baki, Da k’yar tayi shiru tana hawaye, Azagas, Mallam da Feena suka koma gida, Aka bar Hajiya, Aliya da Su’ad, Fetta rashin dawowar su Azagas, ya hana ta samun natsuwa, ko kad’an bata runtsa ba, Sallamar su yasa ta sauke ajiyar zuciya tana amsawa, “Baki kwanta ba” Cewar Azagas, “Eh Tanti ina jiran dawowar ku”, Ta jinjina kai tana zama kan kujera, Tana son tambayar jikin sa, bata so ko kad’an ayi tunanin ta damu dashi, “Ina su Hajiya?”, Ta tambaya, “Suna can an kwantar dashi, wallahi ya bani matuk’ar tausayi, yaro kamar sa yana d’auke da hawan jini, ciwon zuciya tana gab da kamasa”, Zuciyarta ta doka da k’arfi tace “Allah ya sawwak’e ya yaye masa”, Azagas ta amsa da “Amin”, Tana mik’ewa tace “Bari na watsa ruwa jikina baya mun dad’i”, “Toh” ta fad’a itama ta mik’e ta nufi d’akin ta, cike da jimamin ciwon sa. Washegari haka Suraj ya tashi da sumbatu wanda duk akan Fetta ne, sai da aka kira Dr ya masa allurar bacci, Hajiya banda kuka ba abunda take, Aliya na k’ok’arin kwantar mata da hankali. Fetta a tare sukayi karin kumallo da Azagas kamar ko da yaushe, Azagas ta nisa tace “Fetta ki shirya muje asibiti”, Kai ta girgiza tace “A’ah Tanti, ku tafi kawai”, “Haba Fetta duk abunda ke tsakanin ku, rashin lafiya ta wuce komai, kar ki manta shine mahaifin yar’ ki, ko dan Hajiya ya kamata kije”, Maganganun Azagas sunyi tasiri a kanta ta amsa da “Toh”, “Yawwa yar’ albarka” “Yanzu fisabillahi tsabar zalunci da rashin adalci ace ba za’a bayar da bailing yaron nan ba, jiya fa kwana suka yi jibgar sa kamar b’arawo” Gwaggo ta fad’a tana sharar hawaye, “Ni naja masa da na had’a sa aure da tsinanniyar yarinya, wanda tunda aka aure ta muke fuskantar wulak’anci da k’ask’anci, rayuwar rufin asirin da muke ciki ta fiye mun rayuwar daular da muka samu ta sanadin auren ta sau miliyan”, “Kaicon mu! ga abunda son abun duniya yaja mana, muna zaune cikin rufin asirin mu da kwanciyar hankali, mun jawowa kanmu masifa” Gwaggo ta fad’a tana k’ara fashewa da kuka. “A bisa binciken da muka yi mun gano tana d’auke da cutar HIV da sank’arar mahaifa” Dr ya fad’a yana mik’awa Aunty Jummai result, Ihu suka saki a tare, suna zubewa k’asa, “Na shiga uku na lalace Zulaihat kin cuce ni da kika jefani a mummunar d’abi’a Wayyo ni kaina”, “Me ya had’a Zulaihat da cutar ki?”, “Ita ta ja ni harkar mad’igo tun ina yi da ita kad’ai, har ta had’ani da matan manyan mutane, muna yi suna biya na”, “Kin cuce mu Bilkisu, kin cuci kan ki, wayyo! wayyo!” Dr jin sun cika mishi office da ihu, ya fattaka su waje, haka suka bi titi kamar masu tab’in hankali, abu kamar wasa Aunty Jummai ta fara cire kaya, Bilkisu na k’ok’arin rik’eta ta ture ta, ta fad’i, Ta tub’e kayanta gaba d’aya tabi titi tana fad’in “Bilkisu sai ta koma gidan Suraj, Fetta zata haukace tabi duniya boka ya fad’a mun”, Yara na jefar ta suna tsokana, tana bin su da gudu. Suraj yana zaune jingine da gado, wanda bayansa pillow ne Hajita ta masa kariya dashi, Hannun sa sak’ale da drip, Tana fama dashi kan yasha ruwan shayi, Dr yayi complain ya rik’a cin abinci dan samun lafiyar sa,+ “Haba Suraj kamar k’aramin yaro Dan Allah kasha ruwan shayin nan, lafiyar ka zaka duba ko kafi so muyi ta zaman asibiti” Cewar Hajiya cike da damuwa, Yasa hannun ya k’arbi kofin shayin yana kaiwa bakin sa, tamkar mad’aci yaji shayin, haka ya had’iye saboda Hajiya, a ransa kuwa yasan ba zai tab’a samun sauk’i ba muddin Fetta ta dawo rayuwar sa ba, babu asibitin duniya da zata magance masa damuwar sa, ciwon so ne da Allah kad’ai zai iya masa magani, Sallamar Fetta wacce ta biyo bayan Azagas, yasa shi saurin sauke kofin da ya kai bakin sa, yana zuba mata ido, yayin da yaji wani sanyi na ratsa zuciyar sa, ganin ta kad’ai rahama ne a gare sa, Kallo d’aya ta masa ta kawar da kanta gefe, karon farko da taji tausayin sa tun bayan sanin ko shi waye, Nesa dashi ta zauna saman k’aton carpet dake shimfid’e d’aki, Suraj ya kasa d’auke ido daga kallon ta, wanda kowa a d’akin sai da ya lura da kallon, Murya a sanyaye tana kallon k’asa tace “Ya jiki?”, Kasa bata amsa yayi sakamakon farin cikin da ya ziyarci zuciyar sa, rabon da yaji irin sa har ya manta, “Baka ji ana ya jiki bane” Hajiya ta katse masa tunani, Yayi firgigit cikin rawar murya yace “Alhamdulillah”, “Allah ya k’ara sauk’i” Ta fad’a, “Amin Amin” “Ku tashi kuje gida kuyi wanka ku canza kaya tunda gamu” Cewar Azagas, Hajiya na matuk’ar jin nauyin ta, ba zata iya mata musu ba, amma ko kad’an bata son matsawa kusa da dan’ ta, Suka mik’e suka tafi driver ya kai su, aka bar Azagas da Fetta, jin ta take a takure, sam bata son zaman su inuwa d’aya, ga masifaffan kallon da ya matsa mata dashi, wanda ya hana mata motsi yadda take so, tana d’ago kai suke had’a ido, Wayar Azagas ta soma ruri, ta d’auka, Fetta bata ji me aka ce ba, sai ji tayi tace “Gani nan zuwa” Ta kashe, tana kai dubanta gare ta tace “Kira ne daga masarauta ne babu lafiya, ki zauna dashi kafin su Hajiya su dawo”, Ta amsa da “Toh” tana jin tamkar ta d’aura hannu a kai ta tsunduma ihu, Suraj hakan ba k’aramin dad’i ya masa ba, Azagas na fita ya nisa yace “Ina Mimi? Kin hana mun ganin ta bayan kinsan ina da hakk’i a kan ta”, Ya fad’a murya a raunane, Ta d’ago cikin b’acin rai da niyyar yab’a masa bak’a, sai dai yanayin sa yasa jikinta sanyi tare da jin tausayin sa na ratsa ta, Ta mayar da kanta k’asa tana danna wayar ta, “Fatima” Ya kira sunan ta cikin k’ank’ar da murya, Bata amsa sa ba, Ya cigaba da cewa “Dan Allah kiji tausayina ki dawo gare ni, nayi nadama sosai, na canza halayya ta, wallahi bazan sake komawa makamancin halayyata ta baya, zuciyata ta kamu da azabtaccen son ki, ruhi da gangar jikina suna buk’atar ki, dukkan numfashi yana fita ne tare da zazzafar k’aunar ki, ciwon da nake d’auke dashi bana jin zan b’ata warkewa matuk’ar baki dawo gare ni ba”, Ya k’arasa yana k’ok’arin fisge drip dake hannun sa, ya sauko daga gadon, Tsintar kanta tayi da saurin hana sa, Ta hanyar mik’ewa tace “A’ah kada ka cire plss”, Da Kallo yabi ta yana jin sanyi na ratsa zuciyar shi ganin ta damu dashi, “Bashi da amfani a tare dani, matuk’ar ban sameki a karo na biyu ba, duk duniya babu maganin da zai warke mun ciwon da nake tare dashi, sai ke kad’ai Fatima, Dan Allah ki tausayawa bawan Allah da ya mutu a soyayyar ki” Idan taji kalaman sa basu tab’a zuciyar ta, suka saukar mata rauni ba, tare da tausayin sa tayi k’arya, sai dai wani b’angare na zuciyar ta na haska mata daren ya umarci a kashe Mahaifin ta, da kashe iyayen Yasmeen wanda ta rasa dalilin sa na aikata haka, “Please Fatima come back to me, i promise bazan sake miki ko kallon banza ba, zan ta miki bauta har zuwa lokacin da zan wanke kaina gaba d’aya a wurin ki, plss ki amince dani”, STORY CONTINUES BELOW Kanta ta shiga girgizawa yayin da hawaye suka shiga ambaliya saman fuskar ta, “Bazan iya dawowa gare ka ba Suraj, taya kake tunanin zan koma ga mutumin da ya zama silar kashe mahaifina, shin meyasa ma ka zab’i kashe iyayen Yasmeen, ka ruguza musu farin ciki, ka mayar dasu marayu” Cikin rawar murya yace “Wallahi ba da son raina na aikata haka ba, ban tab’a kisan kai ba, kuma ban tab’a bayar da umarnin a kashe wani ba sai Mahaifin Yasmeen, Duk da kasancewa ta dan’ fashi da makami, bana fashi a gidan masu imani da tsoron Allah, duk wanda na masa fashi toh ya kasance azzalumi mara tsoron Allah da sanin darajar talaka, Mahaifin Yasmeen Alhaji Adamu azzalumin mutum ne da babu tsoron Allah a ran sa, burin sa da tunanin sa duniya, sam baya tuna lahirar sa, in dai akan duniya ne zai iya aikata komai, bai d’auki rai a bakin komai ba, ya kashe mutane sunfi a k’irga, ya raunana jama’a da dama dan duk cikar burin sa, rashin imani da ya tab’a aikatawa ga wasu bayin Allah yasa na shiga gidan sa fashi, dan na d’aukar musu fasa, yaron sa Haruna dake masa aiki wanda yawanci idan zai aikata ta’addanci shi yake aikawa, ya saka shi ya mishi wani mummunan aiki na samun jariri sabuwar haihuwa, ya farka cikin sa ya saka laya a ciki ya d’inke, ya binne jaririn, Ya bijire masa hakan ya fusata Alhaji Adamu ya aika gidan iyayen yaron nasa, aka sa musu wuta, yana ji yana gani iyayen sa suka k’one k’urmus, hakan bai ishi Alhaji Adamu ba yasa aka kamo yaron Haruna dan’ shekara biyar ya harbe sa a gaban sa, ya gargad’e sa akan muddin ya sanar da hukuma shima zai bak’unci lahira, Alhaji Adamu ya dad’e yana zaluntar bayin Allah, yaran sa basa k’etare umarnin sa, muddin ka sab’a masa zaka fuskanci hukunci mafi muni, jin wannan labari yasa na shiga gidan sa fashi da niyyar na saka a kashe matar sa da yarin sa a gabansa, ya d’and’ani yadda ya saka Haruna a mayuwanci hali, a lokacin da Mahaifin ki ya mana taurin kai, nayi alama ne akan su ladabtar dashi ta hanyar duka, ba ina nufin su harbe shi ba, mutuwar sa ta tab’a ni sosai, sanin bashi da hakk’i, na dad’e ina jimamin wannan rana, ni na bayar da umarnin kashe yaron Alhaji Adamu da Matar sa, taurin kai da ya mana da tijara yasa shima nasa a harbe shi, wanda yazo da ajali ya rasa ran sa, ki yafe mun Fatima, nine sanadin kashe mahaifin ki amma ban bayar da umarni a kashe sa ba”, Ya k’arasa yana buga kansa da bangon dake manne da gadon, Fetta hawaye take sharb’e sharb’e ta kasa tsayar dasu, ta fice d’akin da sauri tana nufar harabar asibitin, taci sa’a driver na nan wanda Azagas ta umarci ya dawo bayan ya kai ta, murfin baya ta bud’e ta shiga, ba tare da tace masa komai ba, Yaja motar ya nufi masarauta. Suraj hankalin sa ya k’ara tashi ganin Fetta ta tafi ba tare da ya samu amincewar ta ba, Ya jingina kansa dake tsananin sara masa da bango, hawaye na bin gefen idon sa, yana ambaton Allah, Hajiya ta turo k’ofar tare da sallama, Suraj da yayi nisa a tunani sam bai ji shigowar ta ba, cike da damuwa ta k’arasa bakin gado tana zama gefen sa, ta rik’o hannun sa, sai a lokacin ya farga, Ya sake matse hannun ta yace “Ki taimke ni Mama, Plss ki taimake ni Fetta ta dawo rayuwa ta”, Cike da tausayin sa tace “In Shaa Allah zan iya iyakacin k’ok’ari na”, Ya jinjina kansa tare da lumshe idon sa, yana sauraren bugun zuciyar sa, Fetta tun komawar ta masarautar ta fad’a kan gado tana kuka, wanda ita kanta ba zata ce ga dalilin sa ba, nauyin da k’irjin ta ya mata take so ta rage, gaba d’aya kanta ya k’ulle, ta rasa wane tunani zata yi, hannun da taji saman gadon bayan ta yasa ta d’ago tana zube idonta kan Aliya, “Fetta tsawon shekarun da muka yi tare dake yasa na fahimci duk wani yanayi da kike ciki, nasan bakya son Sultan kin amincewa auren sa ne dan gujewa Suraj, nasan har yanzu kina son Suraj, zafin abunda ya aikata miki yasa kika kasa gane hakan, Ina so ki zauna ki sake nazari, ki duba farin cikin ki kada ki biyewa zuciyar ki, ki samarwa kanki farin ciki mai d’orewa, kada wani dalili yasa ki tauye kan ki Fetta, bana so ki sake shiga bak’in ciki balle damuwa”, Rungume Aliya tayi tana shesshek’ar kuka bata ce komai ba, ta shiga bubbuga bayanta cikin sigar lallashi. Bayan kwana biyu Dr babu wani cigaba da ya gani dangane da rashin lafiyar Suraj, sai ma k’aruwa da tayi, ya buk’aci ganin Hajiya office d’in sa, “A gaskiya muna iya k’ok’arin mu wurin ba dan’ ki treatment da ya dace, sai dai babu wani cigaba a tare da hakan, ciwon sa ma hasali k’aruwa yake, ya kasa daina damuwa da saka ma kansa yawan tunani wanda hakan ba k’aramin matsala yake k’ara jawowa kansa ba” Cewar Dr, Hajiya ta nisa cike da damuwa tace “Addu’a kad’ai zamu dage da yi masa, amma bana jin Suraj zai tab’a rabuwa da damuwa muddin ba Fetta ta dawo gare sa ba”, “Wacece Fetta?”, “Matar sa da suka rabu”, “Tana raye kuma ta sake wani aure ne”, “A’ah ta kusa auren dai, wanda shine silar rashin lafiyar tasa”, Ya numfasa yace “Ina buk’atar ganin ta ko zaki iya mun hanyar da zan same ta”, Hajiya tayi nodding kai tace “Ai dole na maka hanyar samun ta Dr ko dan lafiyar da’ na, bana so na rasa shi”, Ta k’arasa tana sharar k’walla, “In Shaa Allahu ba zaki rasa shi ba” Fetta a kwana biyun ta zama shiru shiru, ta rage walwala, ta dage da addu’ar mafi alkhairi a rayuwar ta, da istihara neman zab’in Allah, wanda a kwanakin take jin tamkar tayi babban kuskuren na zab’ar Sultan matsayin mijin aure, har bata so ya kira ta, idan ya kira alla alla take ya kashe, ko ta kawo masa wani uzuri. Bello da k’yar da rok’on Allah aka sako sa, a yan’ kwanakin yayi bak’i ya rame, “Ka yafe mana Dan Allah Bello, mu muka jefa ka a wannan musiba” Cewar Kawu Lamid’o, “Kayi hak’uri kaji wallahi munyi nadama” Cewar Gwaggo, Ya numfasa yace “Babu komai, ku kuka yi silar kawoni duniya kuna da iko na sani ko ku hana ni, ku daina rok’on yafiya ta, ni ya kamata na rok’e ku gafara na muku babban laifi ba tare da sanin ku, auren Karima da kuka hana ni, na aure ta a b’oye muka koma garin Abuja da sunan na samu aiki”, Cike da mamaki Kawu Lamid’o yace “Na yafe maka duniya da lahira, tun farko da mun sani ba zamu hana ka auren ta ba”, Gwaggo tace “Na yade maka dukkan hakk’ina dake kan ka, Allah ya maka albarka ya baku zaman lafiya da zuri’a d’ayyiba”, Ya amsa da “Amin” cike da farin ciki, “Sai ka d’auko ta ku dawo nan”, Ya jinjina kai yana jin tsantsar farin ciki na ratsa shi. Dr har masarautar yazo wurin Fetta, a falon Azagas aka sauke sa, sanin shine likitan dake kula da Suraj, ya buk’aci ganin Fetta, babu b’ata lokaci ta fito, suka gaisa cikin mutunci, Ya nisa yace “Dalilin da yasa nazo wurin ki alfarma nazo nema ina fatan zan samu”, Ta numfasa tace “In Shaa Allah in dai bata fi k’arfi na ba”, “Sanin bata fi k’arfin ki ba yasa nazo” Ya fad’a yana murmushi kafin ya cigaba “Kusan shekaru goma ina aikin likita ban tab’a cin karo da patient wanda ciwon sa yafi k’arfina ba irin Suraj, wanda hakan ya bani matuk’ar mamaki, nayi bincike na gano kece silar ciwon nasa, wanda idan ba samun ki yayi ba, ba zai tab’a warkewa ba”, Yaja numfashi ya cigaba “Fatima ki dubi girman Allah ki ceto ran Suraj, duk da cewa ransa ba’a hannun ki yake ba, but a halib yanzu rashin ki a rayuwar sa daidai yake da rasa ransa”, A razane ta d’ago ta kalli Dr, Ya d’aga mata kai alamar yes yace “Wallahi ina mai tabbata miki kece maganin ciwon Suraj, yana cikin mayunwacin hali, maganar da nake miki yanzu binciken da na masa yau na gano ya kamu da ciwon zuciya sai dai bai yi tsanani, idan ya cigaba da saka damuwa ko shakka babu ciwon zai yi tsanani da Allah kad’ai zai k’ubutar da ran sa”, Fetta hawaye suka wanke fuskar ta, tausayin Suraj na ratsa dukkan sassan jikinta, har k’asan zuciyar ta tana jin ta yafe masa duniya da lahira, zata iya koma masa ko dan ceto rayuwar sa, ko ba komai ba zata tab’a manta halaccin Hajiya gare ta ba, ta kuma shaida Suraj na tsananin k’aunar ta, sai dai babban matsalar Sultan, ba zata iya bud’e baki tace masa ta fasa auren sa ba wanda take ganin tamkar hakan cin amana ne, Dr ya katse mata tunani ta hanyar cewa “Plss Fatima ki koma gidan Suraj”, “Ko shakka da babu alk’awarin auren Sultan a kaina zan komawa Suraj, sai dai bakin alk’alami ya riga ya bushe”, Ta k’arasa ta fashewa da kuka mai tsuma zuciya. Bai riga ya bushe ba” Suka tsinci muryar Sultan dake shigowa falon, Fetta ta d’aga ido ta zube kan sa, Ya k’araso ciki ya zauna kan kujera yace “Bai bushe ba Fetta, ba zan yi shisshigin raba masoya biyu da suka jima da soyayyar juna ba, ko shakka babu Suraj yafi ni son ki nesa ba kusa ba, yana miki azabtaccen so wanda samun sa a wannan zamani yana da matuk’ar wahala, kema kina son shi Fetta, na hak’ura na janye ki koma gidan sa ku raini yar’ ku tare”, Fetta kallon sa take ta kasa cewa komai ba, ta rasa farin ciki zata yi ko bak’in ciki, hawayen dake ambaliya saman fuskarta ta kasa tsayar dasu, ko a mafarki bata tab’a zaton Sultan zai janye cikin ruwan sanyi da kwanciyar hankali ba, shin wa ya sanar dashi zancen Suraj, Maganar sa ta katse mata tunani “Ina miki fatan alkhairi a rayuwar ki Fetta, Allah ya baku zaman lafiya mai d’orewa ya kore dukkan shaid’an tsakanin ku”, Yana fad’ar haka ya fice, “Alhamdulillahi komai yazo da sauk’i, ni zan farawa patient d’ina albishir” Cewar Dr yana mik’ewa, har ya fice Fetta bata ce komai ba, jikinta ya matuk’ar yi sanyi, Sultan ya bata tausayi ba k’aramin so yake mata ba, tasan yayi namijin k’ok’arin wurin janyewa ya hak’ura, Haka ta mik’e jiki ba k’wari ta shiga d’aki. Abunda Fetta bata sani ba, canzawar da tayi kwana biyu yasa Sultan shiga damuwa da zullumi, har ya shiga bincike yasan komai, yaje har asibiti wurin Suraj, a nan ya k’ara gaskata k’aunar da yake mata, ya kuma bashi matuk’ar tausayi, dan rok’on sa ya dinga yi akan ya bar masa ita, hakan yasa ya yanke shawarar janyewa duk da d’umbin k’aunar da yake mata, Suraj yafi sa buk’atar ta. Suraj na kwance hannun sa d’aya mara drip rik’e da charbi yana lazimi, Hajiya na sallar la’asar, Dr yayi sallama ya shigo, Ya amsa can k’asan mak’oshi, haushin sa yake ji na k’in sallamar su bayan ciwon sa bashi da alak’a da asibiti, Da murmushi d’auke a fuskar Dr ya zauna kujerar kusa da shi, Yana kallon sa yace “Na zo maka da babban albishir, amma sai ka bani tukwici zan fad’a”, A zaton sallamar sa ne zai yi yace “Fad’i me kake buk’ata”, “Kada na fad’a ya zamana na cancanci fiye da haka, zan fara sanar da kai, sai ka duba kaga wane tukwici ya kamata ka bani”, Suraj da ya soma k’aguwa a dak’ile yace “Ok” “Sultan ya janye daga zancen auren Fetta kuma ta amince zata koma gar….”, Bai k’arasa ba Suraj ya doka tsalle ya mik’e, “Dan Allah kar kace mun wasa kake”, “Kaga alamar wasa a tare dani”, Hamdala ya shiga yiwa ubangiji, farin cikin da ya tsinci kan shi ba zai misaltu ba, “Alhamdulillah Allah abun godiya” Cewar Hajiya fuska d’auke da annuri, “Dr mungode da k’ok’arin ka Allah ya saka da mafificin alkhairi yasa ka gama da duniya lafiya”, Ya amsa da “Amin” “Mama Fetta zata dawo gare ni, mu fara sabuwar rayuwa” Ya fad’a cike da tsantar farin ciki, Dr yace zuwa dare In Shaa Allahu za’a sallame su, Suraj yaji daren yayi tsawo yana son saka Fetta a idanun sa. Bello bai sanar da Karima zuwan sa Abuja ba, suprise yake so ya mata, Yau ta tashi tana jin k’arfin jikinta har girki tayi, sab’anin kwanakin da sai dai suci na siyarwa ko su sha shayi, Cikin yazo mata da laulayi sosai, Sallamar sa taji tamkar a mafarki, ta doka tsalle ta rungume sa, ya matse ta tsam a jikin sa, yana ji farin ciki na ratsa shi, sam sun manta da Abdul a gefen sa, sai da suka ji yana fad’in “Baba oyoyo”, Ya raba jikin sa da nata, ya d’auke shi yana cilla shi sama, yana dariya cike da ganin Bello wanda ya d’auka mahaifin sa, Bayan sun natsa yake sanar da ita abubuwan da suka faru, ta jinjina al’amarin ubangiji ta kuma yi tsantsar farin ciki na jin iyayen sa sun amince da auren ta, fatan ta Allah yasa itama iyayenta su k’arbe ta hannu biyu. STORY CONTINUES BELOW Amanukal ya kira Fetta ya tambaye ta, ta tabbata tana son komawa gidan Suraj, cike da jin nauyin sa ta amsa da Eh, Ya mata fatan alkhairi, tare da cewa za’a yi shagalin aure kamar yadda al’adar buzaye take, auren farko anyi babu dangin ta, wannan auren gata za’a mata, ita idan so samu ne a d’aura aure kawai bata son shagalin biki, but ba zata iya mishi musu ba. A daren ranar aka sallami Suraj, suka dawo masarautar, fatan sa ya saka Fetta a ido, ya tabbatar da ta amincewa koma masa. Fetta na zaune falo tare da Azagas suna hira, wacce rabin hirar akan komawar ta gidan Suraj ne, Azagas na fad’in tsare tsaren da za’a yi, bata wani saki jiki ba ta mayar da hankali kan hirar, Sallamar Hajiya ya katse hirar, Da sakin fuska Azagas tace “Kun dawo”, “Eh shigowar mu kenan”, “Sannun ku, ya mai jikin?”, “Yana masaukin sa”, “Allah ya k’ara lafiya”, “Amin” Ta kai dubanta ga Fetta tace “Tashi ki kai masa abinci”, Kamar ta tsunduma ihu sam bata son had’uwar su a yanzu, jiki a sanyaye ta mik’e, Tana d’aukar tray na abinci, wanda tuni Azagas tasa aka ajiye sanin yau za’a sallame su, Tana tafiya tamkar wacce k’wai ya fashewa a ciki har ta kawo b’angaren bak’i, daidai k’ofar d’akin sa, zuciyarta na dukan uku-uku tana jin kamar yau ce ranar had’uwar su ta farko, basu tab’a rayuwar ma’aurata a baya ba, kusan minti goma tana tsaye bakin k’ofar kafin ta tattaro natsuwa da courage ta murd’a handle na d’akin ta shiga, Yana zaune k’asan carpet, ya jingina da gado idon sa a lumshe, jin bud’e k’ofa, ya bud’e idon sa caraf cikin na Fetta, sanyi ya ratsa zuciyar sa, ya kasa d’auke idon sa a kanta, Ta sunkuyar da kanta k’asa yayin da k’irjin ta ke dukawa, ta ajiye tray gaban sa, ta juya zata fita, Da sauri yace “Fatima”, Ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba, “Da gaske zaki dawo gare ni?” Ya fad’a murya a raunane, Ta kasa bashi amsa tayi shiru, “Please ki bani amsa, dan cire zuciyata daga kokwanto”, Kai ta d’aga masa, tana k’ok’arin ficewa, Yayi saurin shan gaban ta, “Nagode sosai Fatima, ba zan iya misalta miki farin cikin da na tsinci kaina ba, Nayi alk’awarin baki dukkan kulawa, Ina tsananin k’aunar ki Fatima, I Love you! I Love you! I Love you!”, Ya k’arasa yana jefan ta da wani kallo, da yasa duka gabb’an jikin ta saki, Ji yake tamkar ya rungume ta ko zai samu sauk’in rad’adin k’aunar ta, “Please ki kawo mun Mimi na ganta”, Ta d’aga masa kai, ta rab’a gefen sa ta wuce, har ta kai bakin k’ofa ya kira sunan ta “Fatima”, Ta tsaya ba tare da ta juyo ba, “Ina k’aunar ki tsantsa, Zuciyar Suraj ta mace akan sonki”, Ajiyar zuciya ta sauke, tana jin yadda soyayyar sa da kullum take k’ok’arin binnewa na taso mata, tayi saurin ficewa d’akin. A hanya taci karo da Sanah ta fito rik’e da Mimi, tace ta kaita wurin Suraj, Sanah ta amsa da toh. D’akinta ta nufa, ta fad’a kan gado tana runtse ido, soyayyar Suraj na taso mata, soyayyar da ta dad’e da sanin tana masa, soyayyar da take b’oyewa gudun wulak’ancin sa, soyayyar da abunda ya aikata gare ta take ganin tamkar ta tsane sa, sai dai ko kad’an ba haka ba ne, haushin abunda ya aikata gare ta ne, k’aunar na nan daskare a ran ta, pillow ta jawo ta matse a k’irjin ta, kalaman sa na mata yawo a kai. An sanar da mutanen niamey zancen komawar Fetta gidan tsohon mijinta, sai a yanzu suka san ba rasuwa yayi ba, Mummy taso Fetta taje ta musu kwana biyu kafin bikin, Azagas sam tak’i yarda, tace akwai gyaran da za’a ma Fetta a nan, Gyara sosai take sha, kama daga na jiki, gashi da wanda zai matseta ta dawo tamkar budurwa, kusan yan nijar ba daga baya ba wajen gyara, Fetta bata yi k’asa a gwiwa ba wajen kiyaye amfani da dukkan magangunan ta na gyara, Azagas tace su Hajiya su zauna har a gama biki sai su koma nigeria gaba d’aya, Feena da Su’ad girma sosai suke ba Fetta, duk da cewar sun girme ta, kwanakin da suka yi garin ya k’ara tabbatar musu Fetta yar’ asali ce yar’ dangi, gadon arzik’i. Fitowar ta wanka kenan, sai k’yalli take, fatar jikinta ta k’ara haske har wani yellow yellow take, Wayarta ta soma ringing, Yasmeen ce mai kiran, Ta d’auka da fad’in “Tuba nake hannu na a saman wuya, nasan ni mai laifi ce”, “Ashe kema kinsan baki kyauta ba, gaba d’aya kin share ni kwana biyu, kun daidaita kan ku da Suraj amma ki kasa sanar dani”, “Kiyi hak’uri Dan Allah”, “Toh Shikenan, jibi In Shaa Allahu zan zo dan ba za’a yi ba ni ba”, “Kai amma naji dad’i matuk’a, Allah ya kawo ki lafiya”, “Amin”, Suka yi sallama, ta kashe wayar, STORY CONTINUES BELOW Ta shirya cikin doguwar riga ta material, tayi mata matuk’ar kyau, ta fesa turare mai sanyin k’amshi, ta fita zuwa falon Azagas, Suraj kwana biyu bai saka Fetta a ido ba, san tak’i bari su had’u, yau ya tashi da masifar kewar ta, Ya shirya zuwa gaishe da Azagas, yana fatan Allah yasa yaga sanyin idaniyar sa. Shigowar sa yayi daidai da d’agowar kanta, caraf idon su ya sark’e cikin na juna, zuciyar kowannen sa ta buga da tsananin k’arfi ganin abun k’aunar ta, Murmushi ya mata wanda ya saukar mata da kasala, ta tsinci kanta da mayar masa, kusan mutuwar tsaye yayi yadda murmushi ya daki zuciyar sa ya haifar masa da azabtaccen son ta, bata tab’a masa irin sa ba, Ta kawar da kanta gefe tana mayar wa kan Tv dake aiki, ya k’araso ciki, ya duk’a har k’asa ya gaishe da Azagas, ta amsa da sakin fuska, tana tambayar sa lafiyar sa, yace “Alhamdulillah yaji sauk’i”, “Allah ya k’ara sauk’i”, Ya amsa da “Amin”, Maimaikon ya tashi, sai ya k’ara zama yana satar kallon Fetta, wacce shigarta ba k’aramin burge sa tayi ba, yana jin tamkar ya jawo kwanaki biyar da suka rage a d’aura musu aure, Azagas ta mik’e ta koma d’aki, Tamkar jira yake ta tashi, Ya maida dukkan kallon sa da hankalin sa ga sanyin idaniyar sa yace “Nayi wani laifi ne ake hukunta ni da rashin ganin ki”, Fetta ta d’an yi jim kafin ta girgiza kai, “Sarautar ce ta tashi kenan ake ja mun aji, ina rok’o a sassauta mun, zuciyata bata iya hak’urin rashin mai saka ta natsuwa a ido”, Fetta mamakin Suraj take ashe ya iya kalaman soyayya haka, a baya zaka rantse ko ina son ki ba zai iya furtawa ba, Tsintar kanta tayi da murmushi, Ya numfasa yace “Bazan gaji da fad’a miki Ina Sonki ba Fatima, Ina miki son da yafi k’arfin a kira shi da masifar so, ba zaki gaskata haka ba sai ranar da aka d’aura auren mu”, Tace “Uhm” tana jin yadda kalaman sa ke k’ara wutar son sa a zuciyar ta, Shiru ya ratsa falon na tsawon mintuna, yana jifanta da kallo mai cike da tsantar so, Kiran Sallah yasa shi mik’ewa ya fita. Bello ya d’auko Karima sun dawo Kano, tarba sosai ta samu daga iyayen sa, Kawu Lamid’o sai faman fad’in ya’ta yake wanda hakan ba k’aramin mamaki ya bata ba, Bello yace ta shirya suje gidan su, Cike da zullumi da fargaba ta shirya suka nufi gidan. Yelwa na zaune tsakar gida tana tsintar wake, Kawu Sule yana daga can nesa saman tabarma, abun duniya ya ishe sa, babu kwanciyar hankali tsakanin sa da Yelwa, wacce ta d’auki alwashi ya daina samun natsuwa a gidan sa matuk’ar yar’ ta bata dawo ba, Yana cikin damuwa, yanzu baya samun wasu kud’i balle yace zai k’ara aure, abincin da zai ci ma watarana gagarar sa yake, Yana ji yana gani Yelwa ke dafawa ta hana sa, Yayi ta cigiya bai samu wani labari akan Karima ba, Sallamar Karima yasa Yelwa sakin farantin wake dake hannun ta, ta mik’e da fad’in “Karima kece, ko idanu kemun gezau”, “Nice Umma”, Da sauri har tana tuntub’e ta k’araso ta rungume ta, Kawu Sule ya taso yana hamdala ga ubangiji, Yelwa ta watsa mishi harara tace “Wane murna zaka yi bayan kai ka kore ta”, Jiki a sanyaye yace “Karima ashe zaki dawo gare mu duk da irin korar da na miki, ki yafe mun Karima”, Ya k’arasa da hawaye, Farin ciki had’i da mamaki ya dabaibaiye ta tace “Ba komai Baba na yafe maka duniya da lahira” Anan tsakar gidan suka zauna, Karima ta labarta musu abunda ya faru bayan barin ta gidan, Sukayi ta jinjina al’amarin ubangiji, suna yi ma Bello godiya, Yace babu komai ai Karima k’anwar sa, Yelwa ta numfasa tace “Jiya jiya Bashar yazo neman ki”, Take far’ar dake kan fuskar ta ya d’auke, Kawu Sule ya k’ara da “Hakk’in ki ya kama sa, yayi aure babu haihuwa, yaje asibiti likitoci sun tabbatar masa ba zai k’ara haihuwa ba sakamakon matsalar da ya samu, shine yazo neman ki wai ko kin haifi cikin ki, na masa tas na kore sa nace bayan yace ba nasa ba ne, yana kuka yana fad’in wallahi cikin sa ne, nasa matasan unguwar nan suka masa korar kare”, Karima ta nisa tace “Hakan shine daidai, dama shi Allah ai baya zalunci”, “Tabbas hakane” Cewar Bello, Sun jima a gidan kafin suka tafi, Karima zuciyarta fari k’wal ta daidaita da iyayen ta. Yasmeen ta iso jamhuriyar nijar garin Agadez, ba k’aramin mamakin dukiya irin ta dangin Fetta tayi ba, a ranar raba dare suka yi suna hira, tana ta zolayar ta akan Suraj. Washegari Suraj ya buk’aci ganin Fetta, a lambun b’angaren Azagas ta same sa, “Fatima ina neman wata alfarma a wurin ki”, Ya fad’a cikin sanyin murya, Ta gyad’a kai, “Sadakin ki da zinari aka buk’aci na biya ko rak’uma, ni kuma a halin yanzu bani da kud’in da zan iya biya, ki mun hak’uri na biya da abunda ya samo”, Idan tace bai bata tausayi ba tayi k’arya, mutum mai tak’ama da dukiya shine yau yake rok’o a masa rangwame akan wani abu na kud’i da ya gagare sa, Ta numfasa tace “Ba komai ka bayar da duk abunda ya sawwak’a”, “Nagode Sosai Fatima, Allah ya bani ikon kyautata miki”, Ta amsa da “Amin” can k’asan mak’oshi. Bayan kwana uku Anyi shagalin biki wanda ba’a tab’a yi ba a masarautar, kai kace auren fari ne Fetta ne zata yi, ko da yake bashi da maraba da na farin a wurin su, mutanen niamey sun zo, anyi b’arin dukiya, kowa yazo bikin yasan biki ne na yar’ gata, Suraj kansa ya k’ara gaskata Fetta yar’ gata ce yar’ dangi, ya kuma k’ara gaskata dukiya irin tasu, tabbas Fetta ta wuce ajin sa, Allah ne kad’ai ya basa ita, a karon farko da yanzu ma karo na biyu, Feena da Su’ad sun k’ara raina kansu, sun gaskata Fetta tafi k’arfin su ta wuce da sanin su, ashe kallon kitse suke wa rogo, Mallam da Aliya ba k’aramin karramasu aka yi ba, aka basu matsayin iyayen ta, ko a wurin bikin, wuri na musamman aka tanadar musu, Lele bak’in ciki kamar ya kashe ta har yau bata k’aunar Azagas da ahalin ta, sai dai babu yadda zata yi, Allah ya d’aukakata ta yadda bata zato, ta mata nisa na har abada, wutsiyar rak’umi tama k’asa nisa.Yau jumu’ah bayan an taso daga masallaci aka d’aura auren Suraj da Fetta a karo na biyu, dumban mutane sun halarta, Ango Suraj da yasha d’inkin shadda sabuwa dal wacce Amanukal ya bashi a matsayin karramawa, yana ta washe baki, Sultan ma ya halarta, yana ta far’a sam bai nuna wata damuwa ba, ya yarda da k’addara, Allah yayi Fetta ba matar sa ba ce.+ Amarya Fetta tasha ado cikin shadda mai masifar tsada wacce tasha d’inkin nijar, kunnen ta, wuyan ta da hannun ta sun sha adon zinari mai azabar kyau da tsada, kallo d’aya zaka mata kasan amarya ce yadda take k’yalli, hannun ta da k’afa sun sha adon lalle ja da ya k’ara haskata, tabbas wannan auren ya sha bambam da na fari, auren ta na farko sam bata farin ciki kasancewar babu d’igon soyayyar sa a zuciyata kuma babu ahalin ta ko d’aya sab’anin yanzu da take jin tsantsar farin ciki, zuciyarta cike da d’umbin k’aunar sa, ko ina ta waiga yan’ uwanta ne mak’il, “Kizo zaku yi hotona da ango” cewar Yasmeen tana jan hannun ta, Ba tare da musu ba tabi bayanta, a ranta tace “Tamkar auren fari ba na biyu ba”, Auren fari ma bata samu arzik’in yin hoto dashi ba, A babban falon Amanukal ta same sa, yana zaune tare dasu Sultan, Mimi na hannun sa yana mata wasa, Numfashin sa ya d’auke na wucen gadi ganin tsananin kyan da tayi, ya kasa d’auke ido daga kallon ta, Ba b’ata lokaci mai hoto ya shiga yi musu hotona, wanda suka yi different styles, Sunyi hotona sosai da Mimi, Kafin kowa ya watse aka bar su kad’ai a falon, Fetta wani kunya da nauyin sa taji yana dabaibayeta, ya matsa daf da ita, k’ugun sa yana gugar nata, wanda hakan ya sakar mata da jiki, ta kasa ko da k’wakk’waran motsi, hannun ta ya kamu, taji wani yar, “Lallen ki yayi kyau sosai”, Tayi murmushi, yatsan ta na tsakiya ya kama ya saka mata d’an k’aramin zobe na zinari wanda kud’in sa ba zai wuce dubu goma sha shida ba, yace “Ga sadakin ki, kiyi hak’uri da wannan, nasan shine k’arami cikin zobunan dake hannun ki”, “Duk da kasancewar sa k’arami yafi mun duka sauran muhimmanci da daraja” Ta fad’i maganar da ta zata a zuci ne, “Really sanyin idaniyata”, Kunya ce ta kamata jin maganar ta fito fili, ta k’ara sunkuyar da kanta k’asa, “Yau kuma ni ake jin kunya”, Tayi shiru tana murmushi, saitin kunnen ta yasa bakin shi yace “Kinyi masifar kyau Amarya ta, ina jin tamkar na sace ki na gudu” Maganar tasa dariya ta bata, ta fashe da dariya, “Au dariya ma na baki” Ya fad’a yana janyo ta jikin sa, yana shak’ar daddad’an k’amshin turaren ta, sam ya manta a inda suke, itama ta kasa raba jikinta da nasa, sai ma k’ara narkewa da tayi jikin sa, jin k’arar bud’e k’ofa tayi saurin janye jikin ta, Abutalib ne ya shigo yace “Ahh ango kana nan, ana can ana neman ka ayi hotona”, “Yayar ka ce ta rik’e ni” Ya fad’a yana dariya, Abutalib ya kai dubansa ga Fetta yace “Tumuqqartin ai mana hak’uri mu tafi dashi”, Dariya kawai tayi bata ce komai ba, dan yasa ta jin kunya, Suka fice, itama ta mik’e ta koma b’angaren Azagas. Bayan sallar la’asar wanda za’a tafi dasu nigeria ke ta faman shirye shirye, Jirginsu shida na yamma, Fetta na d’aki tana shirya sauran kayan ta da taimakon Yasmeen, wayar yasmeen tayi k’ara, Sunan Habibi Fetta taga yana yawo saman screen d’in, Yasmeen tayi receiving da fad’in “i will call u back”, “An samu mana suriki shine ba sanarwa” Cewar Fetta, Murmushi tayi tace “Ba haka bane, ina da niyyar sanar dake”, “Toh wanene shi?, kuma a ina yake?”, “Wallahi a super market muka had’u shine ya biyo ni har gida, kafin na taho iyayen sa suka zo aka tsayar da magana, wata uku masu zuwa”, Cike da tsantar farin ciki Fetta tace “Allah ya nuna mana lokaci lafiya ya sanya alkhairi”, “Amin”, “Wallahi nayi murna matuk’a”, Yasmeen tayi dariya. 6:00pm Jirginsu Fetta ya d’aga daga jamhuriyar Nijar zuwa nigeria garin Kano, da kuka ta tafi tana jin tamkar kar ta bar ahalin ta, mutane goma suka mata rakiya, Amanukal ya had’a ta da hadimai biyar wanda zasu cigaba da mata hidima a can, Aliya da Mallam ba k’aramin sha tara na arzik’i suka samu ba daga wurin Amanukal da Azagas, Mummy da Daddy suma sun musu alkhairai mai d’umbin yawa. STORY CONTINUES BELOW 10:00pm Suna cikin garin kano, Manyan motoci k’ira’ar prado suka zo d’aukar su, wanda mamaki ya cika Suraj dasu Hajiya, Mamakin su bai k’aru ba sai da suka ga motocin sun nufi wani tafkeken gida cikin unguwar nasarawa Sultan road, Babu b’ata lokaci securities suka bud’e musu gate, Motocin suka danna kai ciki, Mansion house ne da ya had’u ya k’eru, yana d’auke da part uku, Mutanen da aka zo dasu daga Agadez sune gaba, har cikin gida, ganin babu kowa ya k’ara fad’ad’a mamakin su Hajiya, dan a zaton su ko gidan wasu yan’ uwan su Fetta ne, gud’a suka shiga yi suka nufi sama da ita, wani tafkeken d’aki mai d’auke da makeken gado royal, suka shiga tare da zaunar da ita kan gado, Su su’ad gidan suka shiga zagayawa suna yaba had’uwar shi, gida tamkar na gwamna, Aliya ma sakin baki suka yi suna kallo, Suraj yana daga waje yana k’arewa harabar gidan kallo cike da tsantsar mamaki, ya kasa hak’uri ya tambayi d’aya daga cikin securities na gidan, Yake ce masa ba kaine mai gidan ba, Ganin bai samu wata amsa ba, ya koma ya jingina da mota, yana alla-alla mutanen ciki su rage, ya shiga yaji ta bakin Fetta. Sai sha biyu na dare suka fito daga b’angaren da aka kai Fetta, suka nufi d’ayan b’angaren, Hajiya dasu Feena suka koma gida, Aliya da Mallam suma suka koma gidan su. Jin sallamar sa yasa ta k’ara jan mayafi tana rufe fuska, kunyar sa sosai take ji tamkar auren farko, Da murmushi d’auke a fuskar sa ya k’arasu ciki, ya ajiye ledar da ya shigo da ita gida wanda Munir ya kira ya kawo masa, kaji biyu da lemon kwali, ya zauna gefen ta tare da janye mayafin, Yana bin ta da kallo mai cike da tsantsar so da k’auna, kanta na sunkuye k’asa tana wasa da yatsun hannun ta, “Mu tashi muyi sallah ko mu godewa Allah”, Ya fad’a yana mik’ewa ya shiga band’aki, har lokacin yana mamakin gidan da bai san taya suka same shi ba, Bayan sun watsa ruwa, sunyi sallah, ya zauna yana bata kazar da lemo a baki, kad’an taci tace “Ta k’oshi”, Ya janye gefe, ya kamu hannun ta ya saka cikin nashi, Ya nisa yace “Gidan nan da muke ciki mallakin wa?”, Murmushi tayi tace “Mallakin ka ne”, “Jokes apart pls ki sanar dani”, Mik’ewa tayi ta d’auko d’an k’aramin kit gefen gado, ta bud’e ta d’auko takardu, ta mik’a masa, Ya karb’a yana bin su da kallo, takardu na gida ne dake nuna mallakin sa ne, Cike da tsananin mamaki ya d’ago yana kallon ta yace “Taya hakan ta kasance?”, Ta numfasa tace “Sanin a yanzu baku da halin siyar mana gidan da zamu zauna, ko mu d’auki haya, na yanke shawarar sawa a nemar mun gida, harka ta kud’i ba b’ata lokaci na siya da sunan ka, wanda gidan mallakin ka ne, na baka duniya da lahira, part uku ne, d’aya na Hajiya ne, d’aya kuma kayi yadda kake so”, Kafin yayi magana, ta sake jawo wasu takardu ta mik’a masa tace “Wannan na dukiyata ne, na mallaka maka, ka juya ka fara sana’a” Kansa ya shiga girgiza wa “No Fatima bazan karb’a, ki rik’e abun ki, ban cancan…..” Hannu tasa tayi saurin rufe bakin sa tace “Idan har da gaske kana sona to ka karb’a”, “Ina sonki ina tsananin k’aunar ki amma bazan iya karb’ar dukiya mai d’umbin yawa daga gare ki ba”, Mik’ewa tayi a fusace da zummar fita d’aki, da sauri ya rik’o ta, ta fad’o jikin sa, idon sa cikin nata yace “Kiyi hak’uri kada kiyi fushi dani sanyin idaniyata, zuciyata ba zata iya jurewa ba”, “Toh ka karb’i takardun nan”, Hannu yasa ya karb’a, ko kad’an baya son fushin ta, but har cikin zuciyar sa yana jin bai cancani karb’ar dukiyar ta ba, Ya bud’e baki zai mata godiya tayi saurin hana sa, Rungumeta yayi tsam, yana jin tamkar ya fasa k’irjin sa ya saka ta ciki tsabar so, girman ta, k’imar ta da darajarta ya k’ara k’aruwa a zuciyar sa, ya sake tabbata Fetta mutum ce kuma mace ta gari mai kyakkyawar zuciya. Sun raya daren sosai, Fetta taga tsantsar so daga Suraj, wanda hakan ya k’ara dulmiyar da ita fagen k’aunar sa, Suraj kusan haukace mata yayi a daren, har sai da yaso bata dariya, sam sun manta da Mimi, wacce da ita Su’ad ta tafi, STORY CONTINUES BELOW A tare sukayi wanka bayan sunyi na tsarki, Fetta na manne jikin sa tana zuba masa shagwab’a, kunyar sa da take ji ta kau a daren jiya, shagwab’ar tata ba k’aramin k’ara narkar dashi take ba fagen k’aunar ta. “Sanyin idaniya ta” Ya kira sunan ta cikin wani siga, Ta amsa da “Na’am”, “Dan Allah kina sona?” Tambayar tasa dariya ma ta bata, tayi dariya, ya sake narkewa yace “Please ki sanar dani ko zan samu sassauci”, K’asa tayi da murya tace “Ina Son ka, so mai tsanani, son da bai san yaushe na fara ba, na kawai tsinci kaina a fagen k’aunar ka” Rungumeta ya k’ara yi jikin sa, yana kai mata sumba ko’ina na jikin ta, ganin yana neman fita hayyacin sa, Tayi saurin raba jikinta da nasa ta hanyar cewa “Muje muci abinci”, A kasalance ya d’ago yace “Kin dafa ne”, Hannu ta kama tace “Muje”, Kamar sauna ya mik’e yabi bayanta, suka sauka stairs zuwa dining are dake k’asa, Kulolin abinci kala kala ya gani a jera, da kallo mamaki yabi ta, ta d’aga masa kai alamar yes ta k’ara da cewa “Ma’aikatan gidan ne suka dafa, zuwa jibi zan fara girki”, “Ban yarda ba, sai kinyi sati”, “Kar ka manta bafah budurwa ba ce”, “Ni a ruwana budurwa ce sabuwa dal a leda”, Dariya tayi ta shiga serving d’in su, tare suka ci suna feeding juna cike da tsantsar so. Bayan sun kammala ci, suka koma sama, suka dasa sabuwar soyayya, A waya ya kira ya sanar da Hajiya, ko kad’an baya son nisa da rabin ran sa, addu’o’i ta shiga yi ma Fetta, ta buk’aci magana da ita ta mata godiya, sam tak’i yarda ta karb’i waya, ya fad’awa Hajiya wai kunya take ji, Tayi dariya tace “Ai zanzo har gidan na same ta, Allah ya baku zaman lafiya ya kore dukkan shaid’an”, Ya amsa da “Amin” yayi hanging up, Su Hajiya sun tattara sun dawo gidan, Feena da Su’ad har b’angaren Fetta suka je suka mata godiya, ta nuna musu babu komai, suna k’ara yaba kyawawan halayyar ta. Mallam ma ta siyan mishi gida a kusa da nasu, gidan ba k’aramin kyau yayi ba, mai d’auke da falo biyu d’akuna hud’u, ta kuma siyan mishi dalleliyar mota, Aliya ma ta siyan mata mota, har da kukan farin ciki suka yi, sun ga amfanin rik’on maraya, Dukiyar da suka samu daga wurin su Amanukal, Mallam ya bud’e katafaren shago na trader a cikin kasuwar siga, Aliya ta saro atamfofi ta fara siyarwa. Labarin haukar Aunty Jummai yazo ma su Fetta, da furucin da take, Fetta ba k’aramin mamaki tayi ba, ta kuma k’ara tsorata da halayyar dan’ adam, Bilkisu har gida tazo ta nemi gafarar su, ta fayyace musu mugun abun da suka rik’a yi akan Fetta, tace ta yafe musu duniya da lahira, tayi mata alkhairi mai yaba, ta tafi cike da nadamar abubuwan da suka aikata. Bello da Karima sunzo gidan, wanda sun dad’e suna hira gaba d’ayan su har Suraj, ya shiga b’angaren Hajiya, Su’ad da ta ganshi da Karima sun matuk’ar burge ta, taji ina ma lokacin da amincewa auren sa, da yanzu suna zaune lafiya, but kwad’ayi da dogon buri yaja tana zaman zawarci. A gurguje Bayan shekaru uku Motoci uku ne jere masu azabar kyau suka shigo gidan, da sauri d’aya ya fito ya bud’e murfin baya, Suraj ya fito cikin k’asaita wanda a yanzu babu girman kai, sai dai tsantsar kwarjini da haiba, Jin shigowar motocin sa, Fetta ta k’ara gyara powder d’in ta, ta sake fesa turaruka, ta sauko zuwa tarbar mijin ta, ruhin zuciyar ta, Mimi dake zaune falo tana kallo, ganin mahaifinta ta mik’e a guje ta rungume sa tana fad’in “Daddy oyoyo”, Ya d’aga ta sama yana mata wasa, K’arasuwar Fetta yasa ya sauke Mimi, yana bin ta da kallo, doguwar rigar dake jikinta ta mata matuk’ar kyau, ga cikinta wata biyar da ya soma fitowa ya zauna d’as, hannu ya ware mata, ta k’arasa tana shiga jikin sa, ya rungume ta tare da kai mata sumba a goshi, Taja hannun sa zuwa d’aki, Ta kama masa ya rage kayan jikin sa, ya shiga toilet ya watsa ruwa, ya fito ya sanya kaya mara sa nauyi da ta ajiye masa, ta fesa masa turare, “Kinsan me Sanyin idaniya ta”, Ta girgiza kai alamar a’ah, “Kullum k’ara kyau kike tamkar hurul ayn”, Dariya tayi fararen hak’oran ta na bayyana tace “Bai kai ka kunya ba ai”, Ya kama bakinsa yace “Lalala daina wannan maganar kar gidan nan ya rushe”, Dariya sosai ya bata, ta shiga yi, yana kallon ta cike da burgewa da tsantsar so, Bai barta ba sai da ya jagalgalta son ranshi, kafin suka nufi cin abinci. Yasmeen tayi auren da yaron ta dan’ shekara biyu mai suna Yazeed, zaman lafiya da kwanciyar hankali suke tsakanin su, suna yawan kaiwa juna ziyara ita da Fetta. Feena ta koma gidan Fahad, Mahaifiyar sa har gida tazo ta sami Hajiya ta rok’i alfarmar ta komawa, tun bayan tafiyarta basu sake gane kan Fahad ba, kullum ciwo anyi yawan asibitoci a banza, ganin haka yasa ta yarda makaman yak’in ta, ta amincewa komawar ta, Tun komawarta bata sake fuskantar wata matsala daga dangin miji ba. Su’ad ta samu wani mai mata da yara uku, ta aura, yana tsananin son ta, suna zaman lafiya da matar sa, babu wani tashin hankali. Alhaji Tambari Allah ya mishi rasuwa shekara d’aya da ta wuce, Tasleem ta shiga tashin hankali mara misaltuwa, a yanzu ta fuskanci sam ba gata ne ya mata ba, a yanzu ne take fuskantar rayuwa, tana nadamar abubuwan da ta aikata a baya, dukkan wani gata ta nema ta rasa, dan dukiyar Alhaji Tambari yan uwan sa sun handame. A shekaru ukun Allah yasa wa kasuwancin da Suraj ya fara albarka, komai da ya mallaka ya dawo har ya zarce nada, kud’i ta ko’ina shigo sa suke, Fetta ma business take sosai, tana da shaguna na siyar da laces, materials, takalma da sauran su, Arzik’i kam sai dai suce Alhamdulillah, Allah ya basu shi, babu abunda suka nema suka rasa, ko da yaushe cikin yawan k’asashe suke, suna yawan kaiwa su Agadez da Mummy ziyara, K’auna, soyayya da kulawar dake tsakanin su abun ba’a cewa komai, wata zazzafar k’auna suke wa junawa mara misaltuwa, suna jin tamkar su had’iye juna tsabar so, zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakaninsu sai godiya, Suraj ko kad’an baya son b’acin ran Fetta, itama hakan bata son nasa, Duk da tarin dukiyar su basu yi k’asa a gwiwa ba, wurin bautar ubangiji. _TAMMAT BI HAMDILLAHI ANAN NA KAWO K’ARSHEN LITTAFIN FETTA, KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA_🤲🏻